AGOLA Page 31-35
.
Wani irin murmushi Ogansu yayi, yace nadade ina tunanin wata rana zamu hadu, segashi cikin sauki nasameki ahannu. Kai, ya daka masu tsawa, a ina kukasan wannan matar tajikin hoton nan, mesuna Hajjo? Cike da fargaba Asabe tace wlh ba ita bace amma de itama mamarta sunanta Hajjo, kuma tarasu da dadewa, wannan sunanta Falak.
.
Murmushi yayi yace tabbas yarinya kingirma, harkin kai minzalin aure, kinzo adede dama ina bukatar abokiyar hutawa. A wane gari suke? E to dama de AGOLAH ce agidan diyar mijina, kuma bayan mamanta tarasu itama tayi aure. Mene? Aure? Wlh dasake, kinsan koni wanene agurinta? Kai Asabe tashiga girgizawa tana hawaye.
Kawun Babanta ne ni, kinga ko inada hakki akanta, to wai ku inama zakuje da makudan kudi haka, kuma mezakuyi da wadan nan hotunan, kode wannan shine mijin nata? Dan Allah yallabai kayi hkr, wlh muma bamu akayi mukaisu gurin boka shine mukuma mukace bazamuje ba, shine mukayi kokarin guduwa da kudin.
To waya aikeku? Diyar mijina ce, itace kishiyar Maman Falak, wannan kuma mijinta ne, shine takeso amallake, ita kuma Falak akasheta. Hahhhhh, kawai kicemun kuma maciya amana ne. Lallai tunda hadaku za,a hada baki akashemun jinina, lallai kuma zaku amshi rabonku, danni bana yafema wanda yashiga gonata.
Dije tace kawa Allah kayi hkr, mude kudauki koda rabin kudin ne, kubamu sauran mutafi, wlh dama can bamuyi niyar zuwa gurin wani boka ba, muma muna tausayinsu ai..... Saukar marin datajine yasata yin shiru, ke harkin isa kizo gabana kina fadin indauki rabin kudi inbaki sauran. To bara kiji, ko wadanda suka kawo kudin basuda hurumin karbar rabin kudin bare kuda muka kama, wanda lokaci kadan yarage maku aduniyar gaba daya.
Wayyo Allah nashiga 3,ni Asabe, ina zamana Dije kinja mani, gashi nan nibanyi kudiba, zan rasa raina abanza, nide Allah ya isa tsakanina dake, duk kece kika sakani cikin wannan bala,i. A,a kada kidoramun laifi, dama can da bakin halinki kikazo garinmu, keda kika kashe mazajenki har 2, kuma kike fadin nina koya maki bakin hali.
.
Ya isa,,,,,,,., Ashe de kuma kananan yan ta,adda ne. Lallai kunyi kokari. Duk ku saurara, banida lokacin batawa, ke a ina zan iya samun Falak? Wlh nima bansan gidansu ba, amma de nasan gidan diyar mijina. Ok, fadamun dan sauri nakeyi.
Idan kaje Unguwar sarki kaduna duk wanda ka tambaya Alhaji Abba Bala, yasan gidan. Da kyau, kai mugu gama masu aiki kasan ni bana barin baya da kuurah. Tasssss kakejin karar bindiga andauke Asabe da Dije. ( se ince karshen Asabe da Dije kenan, dama duk wanda ya gina ramin mugunta, wata rana shine ze fada. Allah yatsaremu, sunyi 2 babu).
Mazaje, kowa yafara shiri, gobe da asuba zamu dauki hanyar kaduna, bansan ranar dawowarmu ba, harsena cika burina na tahowa da Falak, tunda munsamu isassun kudi bamu da damuwa, kudauki jakar kudin muware, lallai yau munyi babbar sa,a. Daukarmun hoton fuskarsu awayata, hakan zemun amfani idan naje gidan, diyar mijinta.
Sedare Sameer yazo yadauki Falak suka wuce gida, Zarah ko sallama bata bari sunyi ba, har mota Jalila da Alh, suka rakosu, Alh, wani irin farin ciki yakeji. Sameer yace Alh, gobe zanzo indaukeka a office kawuna yana son ganinka, yace lallai muje tare akwai wani temako dazeyi maka. To to babu komai, Allah yakaimu, bara insamaka no ta idan kazo seka kirani, yauwa gata, zantura maka da address din office din. Sallama sukayi masu, Falak kamar kada ta tafi takeji.
Kwance Jidda take abisa gado tana tunanin halin datake ciki, gashi cike take da bukatar namiji idan takira Viju akashe, tarasa yanda zatayi, murmushi tayi, tace wlh bazan tausaya ma duk wanda yanemeni da bukataba, yanda aka likamun cuta kowama yasamu badamuwata bace, Allah yakaimu inkara samun sauki, dole insamo me biyamun bukatata, meza,a fasa, tunda harnazo gargara, ai gara kawai incigaba da shakatawa ta. (Lallai kinyi kuskure Jidda, Allah yashirya). Tashi tayi tabude jakarta tadauko maganinta tasha sannan ta kwanta.
Zarah kuwa aranar kasa zuwa dakin Alh, tayi adakinta tayi kwanciyarta sbd batason yawan tambayar da Alh, yake mata, ga abin duniya yafara isarta, takira no wayar Asabe yafi akirga, amma bata shiga, gaba daya ta gama shiga tashin hankali, addu,a kawai take Allah yasa lfy. Amma ta kudira aranta dole gobe taje Zariya. Da wannan tunanin tasamu bacci yadauketa.
.
Karfe 9 na safe Zarah tagama shiryawa tasami Alh, afalo yagama cin abinci yana shirin fita. Bayan sun gaisa, tace Alh, dama zuwa nayi infada maka inaso inje gidan, dan jiya mafarki Baba nayi wai beda lafiya, shine nace gara inje indubashi na dade banje ba. Mamakin kalamanta yayi, dan a iya saninshi Zarah bata taba cewa zataje taduba Babanta ba, sede idan wani uzurinta ya tashi, yace tofa, ai mafarki ba gaskiya bane Zarah, insha Allahu zaki sameshi lfy. Shikenan sekin dawo, amma dan Allah kada kiyi dare kinsan banason tukin dare. Kudi yabata yace tayi mashi siyayya, yakaramata wasu yace idan taje tabashi kuma tace yana gaisheshi. Godiya tayi mashi yatafi itama tayi masu Jalila sallama ta tafi.
Alh, yana zuwa office bayan yagama abinda yakeyi, yaji kiran Sameer, nan yahada kayanshi yafita yasameshi awaje, bayan sun gaisa, Sameer yace ina ganin ka aje motarka semu tafi atawa, haka akayi suka nufi gidan Kawu.
Bayan sungaisa, Kawu yafara magana, agaskiya Alh, ka tsallake rijiya da baya, tun ranar da mukaje neman auran Falak na ganka, nasan akwai abinda yake damunka, gaskiya Alh, kana sakaci da addu,a kasan ita makamin mumunice, duk wanda yariketa, to koda wani abu zesameshi yakan zomashi da sauki. Hakan yasa asirin da akayi maka yayi tasiri akanka. Amma alhamdulillahi yanzu babu komai ajikinka, sede muce Allah yakara karewa, kuma kaima kadage da addu,a.
.
Alh, yanisa yace tabbas Malam nima naji alamun haka tunbayan da muka hadu da Falak a asibiti, kuma naji labarin da bansan ya akayi ba, adaren jiya sam banyi bacci ba, duk da nace bazan tsananta binciken halin dana shiga ba, amma ajiya nayi nazari sosai, kuma zuciyata tafara zargin wani abu, sede kasan ance zargi beda kyau koda yakasance gaskiya ne, hakan yasa nabar abun kuma nima nayi alkawarin dagewa da addu,a tabbas nasan nayi sakaci abaya, amma yanzu hakan yazamar mani darasi.
Kuma ina baran addu,a awajenka, Malam yace babu damuwa Alh, muna temakon wasu ma, bare kuma nagida, kuma nima shawarar dazan baka kamar yanda kace kana zargin wani abu, to kabarshi ahaka, kada kayawaita bincike, kasan kome mutum yakeyi Allah yana ara mashi rana ne, wata rana dole asirinshi ze tonu.
Abu nafarko dazaka farayi shine karika tashi cikin dare kana sallar dare, kasan Allah yace yana saukowa akowane karshen dare kuma yana amsar addu,ar duk wadanda suka rokeshi a wannan lokacin, ka yawaita karatun alkur,ani, da sadaka suma suna temakon mutum, yawan ambaton Allah safe da yamma, azkar dinka kullum dummin saurin da kakeyi kada kabari suna kubucemaka, koda kana tafiya amota ne, idan ka haddacesu to kasamu kafin ka isa inda zakaje kayisu. Allah shine mafi sani, wannan ruwan addu,a ne danayi maka tunjiya, kashanye yanzu, wannan kuma idan ka koma gida kazubashi aroba kawanke jikinka duka, insha Allah zakaci nasara akan duk wani menemanka da sharri.
Godiya sosai Alh, yayi mashi hada kukanshi, yakawo kudi yace gashi ayi sadaka, daga nan sukayi sallama Sameer yamaidashi office, yana zuwa ya dauki motarshi yanufi gida. Yana zuwa yashiga yayi wanka da ruwan maganin da aka bashi yadauro alwala yazauna yana karatun qur,ani.
Zarah kuwa tana zuwa gidansu taci karo da Babanta yana shirin kulle gida. Tsayawa yayi yana kallonta cike da mamaki, danshi har yamanta rabon daya ganta, tana fitowa daga mota tace Baba ina kwana, yace lfy lau Zarah ashe kina duniyar? Dukar da kanta tayi tana wasa da makullin motar tace wlh kuwa Baba kasan aiyuka ne sukamun yawa. Yace e gsky kam naga alama.
Yanaga kana shirin kulle gidan ina Innar take? To shigo daga ciki tukunna.
Bayan sunzauna, ya kalleta yace Asaben bata fada maki abinda yafaru ba? Saurin kallonshi tayi tace aini rabona da ita tun ranar litinin, kai ya jijjiga yace to ai tundaga ranar nima bankara ganinta ba, dan yanzu bama tare da ita, aranar lahadi tazo tace insaketa zata bar garin, nikuma na sawake mata tundaga nan bankara ganinta ba. Wata irin zufa ce tarika keto mata, tafara fifita tace nashiga 3 yanzu Baba bakasan inda ta tafi ba? Murmurshi yayi yace ai kunfi kusa ni ina zansan inda taje, dama ni asama naganta, bansan kaddarar data kaini aurenta ba, kuma gashi Allah yarabani da kaya, bana fatan musake haduwa da ita.
.
Shiru tayi tafiddo wayarta tana kara kiranta amma haryanzu shiru. Abinda bata saniba, tun atasha Asabe ta karya sim dinta tace setaje Lagos zata sayi wani. Baba kuma wayarta kullum akashe, dariya yayi yace toni Zarah yakikeso incemaki, kowa yasayi rariya ai yasan zatayi zuba, saboda haka kije gidan kawarta Dije kozata fada maki garinsu. Ai Baba Dije bata nan, kuma bansani ba kota dawo, gashima ni bansan gidanta ba. Kanshi yagirgiza yace waini Zarah me Asabe zatayi maki ne kike nemanta? Babu komai Baba, kawaide ina nemanta ne, kasan banida wata. Uwa data wucemun ita shiyasa hankalina yatashi danaji kace bata nan. Seda yaji kwalla tacika mashi ido jin kalaman Diyarshi, tabbas tausayinta yashigeshi, sede Asabe tayi mata mummunar huduba. Share kwllar datazubo mashi yayi, yace shikenan Zarah, amma de inaso kisani Asabe ba macen kirki bace, kada kicigaba da nemanta babu abinda zaki saku agurinta se halaka, kiyi hkr kamar yanda Allah yarabani da ita kema kidauka rabuwarku alkhairi ce.
Kallonshi tayi cike dajin haushi tace Baba nide kasa wani yarakani gidan Dije sauri nakeyi zankoma. Murmushi yayi yace Zarah kibi duniya ahankali wlh ina tausaya maki duk ranar da duniya zata juya maki baya. Tashi tayi tace nide zantafi, dubu 1 taciro tace ga wannan kayi cefane, yace A,a kirike kudinki zasuyi maki amfani ahanya niyanzu bana bukatar komai, Allah yayima Jalila albarka, tabbas yarinyar nan yar halak ce, tayi mani abinda wadda na haifa takasa.
Tashi muje innuna maki gidan, kudinta tamaida jaka tana gungunai tayi gaba, har kofar gidan Dije yarakata, ya hadu da wani abokinshi makwabcinta, shi yatambay ko tadawo. Yace ai malam Garba Dije da kawarta sunyi hijira bazasu dawo garin nan ba, dan harta saida gidanta da komai nata, nima kiya medakina take fadamun tashiga gida tasamesu suna ta shiri, suke fada mata sukam sunci gaba. Zarah jitayi kafafuwanta suna rawa, zufa kawai take fito mata, da kyar tace to Baba nizan koma, yace to yayi kyau, Allah ya kiyaye kigaishemun da Jikanyata Jalila, haka tanufi mota yana binta da kallon tausayi. Da kyar taja motar ta tafi, ikon Allah ne kawai ya kaita gida, tana zuwa tashige dakinta ta kulle tafara kuka.
Karfe 4 na yamma su Figo kawun Baban Falak suka shigo kaduna, cikin shiga ta mutunci, idan kagansu sekadauka irin manyan yan shiyasa ne, hotel suka nema suka kama daki 2 shi yadauki daya yabasu daya su 3.
Se karfe 6 suka fito shida babban yaronshi Jungle suka tari taxi suka fada mashi inda ze kaisu, suna zuwa unguwar suka sami wani suka tambayeshi gidan Alh, Abba Bala, nan take yanuna masu gidan, godiya sukayi mashi, Figo yaciro wayarshi yasa akunne kamar mekiran waya, can kuma yacire yace wayarshi akashe take kawai muje ma dawo gobe, banason shiga baya gida kasan matarshi bazata barni infito ba, zatace sena jirashi. Kallonshi Jungle yayi Figo yayi mashi signal da driver, murmushi yayi yadaga mashi hannu, suka koma hotel, bayan sun sallami driver Figo yace kasan bana aikina da ka, haka kawai muje guri da driver kuma mu tambayi gidan mutum ana nuna mana kawai mujuya ai kowaye ze iya zargin wani abu. Jungle yace gsky Oga aiki da kai akwai karuwa.
Zaune suke afalo Falak tayi matashi da kafar Sameer, shi kuma yana wasa da cikinta, yace dear idan kika haifa mun mace sunan Ummanki zansa, Idan kuma na kiji ne, sunan Babana zansa, shiru yaji tayi batace komai ba, dukowa yayi yana kallon fuskarta, gani yayi hankalinta baya gurin, girgizata yayi, tayi saurin kallonshi. Meye haka kikeyi Falak, bakisan yanzu bake daya bace, kike irin wannan tunanin, kuma ko ke dayace ma aikinsan banason dogon tunani ko. Murmushi tayi tace kayi hkr wlh ina tunanin Dady ne, ina tausayinshi, nasan Ummi bazata kyaleshi haka ba. Babu abinda zata iya kara yimashi, domin yanzu yafi karfinta, kawai mucigaba dayi mashi addu,a. Shikenan, Allah yakara tsaremu, yace yauwa kokefa, ameen, tashi muje kibani abinci dagata yayi suka nufi daki suna dariya.
Washe gari da misalin karfe 10 nasafe, Jungle da Figo suna daga gefe suka ga motar Alh, tafita. Figo yace yauwa, yatafi muje, suna zuwa suka kwankwasa kofar, megadi yabude, bayan sungaisa, Figo yace ni suna Lado, munzo gurin Alh, ne. Megadi sewashe baki yakeyi yaga manyan kutane, yace yanzu kuwa yatafi office, amma ku kirashi mana. Aa, barshi kawai idan hajiya tana ciki kafada mata zamu bata sako seta aje mashi, yace toshikenan kushigo ga banci nan kuzauna, dasauri yanufi cikin gidan, Karo sukaci da Jalila bayan sungaisa yace tayima Hajiya sallama wasu mutane suna son bata sako ta ajema Alh.
Adaki tasameta kwance tana tunani, tace Ummi wai kizo wasu kutane zasu baki sako ki ajema Dady, tace kash nifa banason yawan damuwa kije kawai subaki, tace a,a Ummi idan kuma sakon kudine fa, ai kinga keyakamata subama, saurin tashi tayi jin ance kudi, gyalenta ta dauka tafita.
Bayan sungaisa Figo ya matsa kusa da ita ahankali yace bagurin Alh, muka zoba gurinki mukazo kuma munzo da magana me mahimmanci amma idan kinasonji zamu iya matsayawa daga nan, harararshi tayi tace nikuma a ina nasanka, murmushi yayi yace amma idan baki sanni ba, kinsan Asabe da Dije ko?
.
Cike da fargaba tacee kushigo, murmushi yayi yace abokina muje ta matsa semunsha ko ruwane, megadi yace ai gaskiya ne, sekunfito. Bayan sunzauna afalon baki tace dan Allah ina kasan Asabe da Dije? Wayarshi yaciro ya nuna mata hotonsu yace kobasu bane wadannan, jiki narawa ta amshi wayar tafara dubawa, dasauri tace bade sun mutu ba, to ina jakar dasuke tare da ita? Yace tonide bansan wata jaka ba, munshiga mota atare dasu zamuje Lagos, se yan fashi suka tare mu, suka kwace mana kayanmu da kudinmu duka, to ita Dije tana kusa dani, alokacin da aka bude jakarta senaga wasu hotuna sunfado, ina dauka naduba senaga macen jikin hoton nasanta, ita da mamanta, garinmu daya dasu, kuma masu laifine, sunan mamarta Hajjo ko? E ita kuma Falak, haka suke, to bazan boye maki ba, agaskiya mutanen banza ne, mijin Hajjo abokina ne, yanada kudi, shine ita da niyarta suka hada baki suka kashe shi suka gudu.
Nayima yan sanda alkawarin nizan nemosu aduk inda suke, na dade ina nemansu bangansu ba, harna hakura, segashi Allah yakawomun su cikin sauki. Bayan natambayi Dije a ina suke tacemun Hajjo tarasu, ita kuma Falak tayi aure, shine nace tayi mani kwatancen inda zanganta, shine take cemun ai kekika san inda take, kema kinso akasheta kika basu kudi sukaisu gurin boka, shine sukuma ashe karya suka maki guduwa sukaso suyi da kudinki shine yan fashi suka kamamu. Ita ta fadamun sunan mijinki da unguwarku.
To dayake ansamu kudi agurin kowa sune suka boye nasu da kaya, koda yan fashin suka gano kudin suka tambayi masu su, shine suka kashesu, mu kuma suka maida mana kudinmu, nikuma nadaukesu hoto dan innuna maki. Yanzu nazo kitemakeni ki nunamun gidan Falak domin hukuma tayi saurin cafketa.
Bakin ciki tare da farin ciki ne, suka hadema Zarah, jin za,a kashe Falak cikin sauki.
.
Cike da sauri Jidda tabama me taxi kudinshi tashiga gida, da Zarah suka fara cin karo tace ke lafiyarki naganki kamar arikice? Harzata fada mata, se kuma ta tuna da maganar da Figo yafada mata, akan tabada kudi akai dadynsu gurin boka. Murmushi tayi tace wlh Ummi ba komai ina Jalila? Baki ta tabe tace tana ciki, kinsan yau za,a kawo lefenta amma kika ki tsayawa akarba.
.
Uhm wlh Ummi wani uziri ne, yataso mun, shine nafita dawuri nadauka bada wuri zasu zo ba. Ai shikenan kishiga ciki sunan ki kalla, Jalilan ma tana falo, yauwa Ummi, da kallon tausayi tabita, aranta tace dole insama maki mijin aure kema, damma Asabe ta munafunceni ai da naje gurin boka asama maki miji medan maiko, ita de Jalila Allah yasota batare dana kashe kudina ba tasamu me kudi.
Jidda tana zuwa falo tasamu Jalila tana kara duba kayanta, cike dasauri takamo hannunta har seda Jalila ta dan tsorata, lfy de Yaya Jidda? Lfy lau kede kawai biyoni muje daki muhimmiyar magana ce bata bukatar bata lokaci, daki suka nufa Jidda ta kulle dakin taja Jalila saman gado.
Ita de Jalila kallonta kawai take cike da mamaki. Inajinki Yaya Jidda Allah de yasa lfy. Uhm Jalila inaso kibani aron hankalinki, ayau inaso infada maki wata magana wadda babu wanda yasan da ita, kuma inaso idan kinjita ki temaka mun domin insamu inyi aiki alkhairi guda daya nima arayuwata. Jalila tace inajinki.
Tun daga farkon shigarta harkar banza harzuwanta London da irin wahalar data sha, har zuwa haduwarta da Viju da irin yanda ya yaudareta, ta cutar datake dauke da ita, harzuwa haduwarta da Figo da abinda yafada mata, seda tafadama Jalila. Kuka sosai sukeyi ba kamar Jalila wadda tausayin yar uwarta yakamata, jin irin abubuwan data aikata. Jidda tace wlh Jalila tun lokacin da Umman Falak tarasu naso intuba, amma rudin duniya tare da irin halin da Ummi take nunamun yasani komawa ruwa. Tabbas Al,amin masoyine nagari, yaso inbar London indawo muyi aure amma nakasa fahimtar abinda yake nufi, seda narigada nakamu da cuta sannan yace baze iya aurena ba, tunda shi beda ita, yanzu haka bansan inda yake ba, ko no shi nakira bata shiga.
.
Nayi nadamar abinda na aikata, nacuci kaina da kaina, kuma hakan yasamo asaline dalilin Uwa dabamu samu tagari ba. Ko kinsan cewar Ummi dasu Inna Asabe sune silar mutuwar Umman Falak da Ameer, kuma itace ta mallake Dady, yarika yin duk wani abu dayake ma Falak. Gsky nide tsakanina da Ummi sede ince Allah ya....... Saurin rufe mata baki Jalila tayi tana kuka tana girgiza mata kai.
Kada kice haka Yaya Jidda, Uwa Uwace koda kuwa yar mafiyace bamuda wadda tafita, domin itace tayi sanadiyar kawomu duniya, dataso lokacin fitowarmu data kashemu, dataso tun muna jini datayi barinmu. Da jinin jikinta muke rayuwa acikinta, dole mudauki duk wani abu dazata mana, dan bekai rabin rabin wahalar datayi damuba. Ayanzu ko zama mu tsareta na awa 3 tayi bacci bazamu iya ba. Amma ita takan hana kanta bacci domin mu muyi. Saboda haka kada bacin rai yasa kifadi wata mummunar kalma akan Ummi, Allah ze iya kamaki da laifi akan hakan.
Addu,a itace abinda yakamata muyi mata wadda itace nake mata kuma gashi tafara canzawa, yanzu haka neman yafiyar Falak ta aikeni rannan nayo mata. Jidda tace Uhm Jalila ke yarinyace bakison kissa irinta Ummi ba. To wlh yaudararki tayi tayi amfani dake tanunama wadan nan mutana gidan Falak. Dan haka yanzu ba lokacin labari bane, kitashi muje mufada masu halin da ake ciki. Kuma akan labarina dana baki banason kowa yaji, kibarni ni nasan tawa tazo karshe, dan haka zankarbi duk wani hukunci da Allah zemun.
Jalila tace amma Yaya Jidda kinashan maganinki kuwa? Yamutsa fuska tayi tace wannan duk wahalar banza ce, tunda de ba,a iya ciremun ita gaba daya ba, babu amfanin shan wani magani, ada nafara sha daga baya kuma naga beda wani amfani, gara kawai incigaba da rayuwata haka har mutuwa ta tasameni. Jalila tace amma dakin cigaba da shan magani koba komai zaki samu lfiyar dazaki nemi yafiyar Ubangiji. Mikewa Jidda tayi tace kitashi mutafi banason dogon zance.
Adaki suka sami Zarah tabuga tagumi tana tunani, Jalila tace Ummi tunanin me kikeyi kuma? Murmushi tayi tace bakomai kawai ina dan tsare tsare akan bikinki ne, kinga saura sati 2. Hakane Ummi amma banason inga kina tunani. Yauwa Ummi zamuje mukai dinki nida Yaya Jidda.
Zarah tayi murmushi tace amma naji dadi dazaku tafi tare, sekun dawo, driver yana waje kusashi ya kaiku, to Ummi amma sede ya ajemu yadawo dan akwai inda zamu wuce. Tace toshikenan sekun dawo.
.
Suna zuwa gidan Jalila taga motar Saleem, tsayawa tayi Jidda tace muje mana, tace Motar Saleem nagani. Jidda tace to menene, bazaki shigaba kome? Nifa banason gulma. Jalila tace bahaka bane, inajin kunyar yaji labarinki sede idan bazaki fada masu yanda kikaji za,a dauko Falak daga gurin Figo ba. Murmushi Jidda tayi ta goge kwallan dasuka zubo mata, tace babu sauran jin wata kunya, kuma ni nadaukesu abokana shawarata, kada kidamu kobasu ji labarina ba sun riga da sunsan koni wacece sbd sunsan abinda nake aikatawa. Nasan Saleem yana sonki dan yaji labarina baze taba son dayake maki ba. Kuma dole nasan Sameer yafada mashi halin Ummi, tun kafin asamaku rana, kuma tunda kikaga bedena neman aurenki ba, ai yasan kinada hali me kyau. Kasancewarmu nida Ummi marasa hali me kyau baza,a ce dole kema ki kasance haka ba. Kinsan Allah yana fitar da shiryayye daga wanda ba shiryayye ba. Jalila tagoge kwallan idonta tace shikenan muje.
Kuka kawai Falak takeyi, Sameer kuwa gaba daya zufa ce tarufeshi, hankalinshi bakaramin tashi yayi ba, jin wai wani banza yanason zina da matarshi. Kallon Jidda yayi yace tabbas yanda kika kwatan tamana shi shine kawun Abban Falak, kuma daga gidan nan yake, Lallai biri yayi kama da mutum, tunda yatafi muma bamu yarda dashi ba, kuma aniyarmu gobe da safe zamu tafi gidanmu, sede yanzu dole mubar gidan nan, sbd meson abunka yafika dabara, yana iya canza shawara.
Jidda tace dan Allah Falak kiyafemun da duk irin abinda nayi maki, tabbas rayuwa takoyamun darasi, kuma kwadayi yakaini yabaroni, babu abinda nake nema daga gareku se addu,arku kobayan raina. Sameer yace meyasa kike fadar haka Jidda? Cikin kuka suma tafada masu labarinta.
.
Duk irin dauriya ta maza seda Sameer da saleem sukayima labarin Jidda kuka. Falon ya dade shiru kukan matan kawai akaji, sukam mazan sede hawaye a ido. Jidda tace narokeka Saleem kada labarina yasa wani abu yashiga zucuyarka na game da auranka ko soyayyara da Jalila. Wlh ko Qur,ani zan iya dafawa akan shedar halin kirki irin na jalila, Allah ya shiryata, duk irin yanda Ummi take nuna mata halin ko inkula lokacin da ina kawo mata kudi hakan besa ko samari Jalila tafara kulawa ba. Duk da bansan rayuwar datayi a makaranta ba, amma zan iya cemaka kaine mutum nafarko da Jalila tafara kulawa.
Dan haka inaso kada jin labarina da kuma halin Ummin mu yasa wata rana ka goranta mata. Saleem ya goge idonshi yayi murmushi yace Yaya Jidda kada kidamu. Allah ne yahadani da Jalila, bantaba son wata halitta ba kamar yanda nakeson Jalila, bayan Uwata da mahaifina zan iya cemaki Jalila itace mutum ta 3 datakeda muhimmanci arayuwata. Kima dena tunanin zan goranta mata, har abada, kuma wannan labarin naki insha Allahu daga nan yagama zuwa wani guri. Kuma batun maganinki dole zaki cigaba da shan shi, sbd rayuwa da mutuwa agurin Allah suke, idan yaso seyabarki da cutar harzuwa wani lokaci. Kifadamun idan baki shan magani kuma taci karfinki harta kaiki last stage wanda ko likitoci bazasu iya maki komai ba. Gashi Allah yaki yadauki ranki yazakiyi da wahalar dazaki sha? Alokacinne seme kaunarki sosai zeiya zama dake.
.
Dan haka kimun alkawari daga yau zaki cigaba da shan maganinki. Shikenan Saleem insha Allahu zancigaba dasha, dama na wata 1 aka bani kuma yana nan. Sameer da tundazu seyanzu yayi magana yace insha Allahu kema zakiyi tsawon rai harkisamu lokacin tuba zuwa ga Allah. Jidda tace Falak kinyi shiru bakice komai ba. Dan Allah kiyafemun.
Falak tagoge idonta wanda yayi ja sbd kuka, tace babu komai Yaya Jidda, niban rikeki da komai ba, kecema zanyima godiya, badan keba bansan yanda rayuwata zata kare ba. Saleem yace kutashi mutafi gidan Umma seku kwana acan, kai kuma Sameer daga can seku wuce gurin abokina D,P,O ne dan musan yanda zamu bullomasu, banason gobe tayi haryazo besameku ba, ze iya tunanin wani abu. Kema Yaya Jidda dake zamu tafi dan dole dake zamuyi amfani musamu mu cafkeshi. Tacebabu komai, ashirye nake dabada gudummuwata dama ina da no shi. Sameer yace Allah yadoramu akan sa,a sukace ameen.
Falak tace amma inaso kafin kutafi kusami Dady kuyi mashi bayani dan bazeji dadi yaji abun daga sama ba, dan yafi kowa sanin labarin Kawu. Saleem yace kinyi gsky, idan muka aje ku semu sameshi mutafi tare dashi ma.
.
Kaf suka fadama Alh abinda yafaru, sede sunboye abinda yashiga tsakaninsu da Jidda, sunfada masa saurayinta ne, yarage mata hanya shine taga hoton Falak amotarshi har yake bata labarin abinda zeyi mata. Kuma basu fada mashi abinda Zarah tayi ba.
Sosai Alh, yayi mamkin jin wannan al,amari, yace lallai dole mudauki mataki cikin gaggawa, dan akowane lokaci ze iya aikata abinda yayi niya, dan beda tausayi. Allah sarki Hajjo babu rabon kiga wannan rana, banyi tunanin wannan mutum yana nemansu haryanzu ba.
Abinda zefaru kai Sameer kuyi gaba zuwa gurin abokin shi Saleem kome kenan kuyi mani waya, amma dole ayau za,a je aka mashi, tunda Jidda tanada no shi kutafi da ita nasan zatayi maku rana, nima dana gama abinda nake zanzo.
Kwance Zarah take, hawayene kawai suke zuba a idonta, zumbur tayi saurin tashi lokacin data kara tuna maganar dasukayi da boka ta karshe lokacin dataje karbar maganin mallakar Alh........... Ina me tambatar maki da duk lokacin da mijinki yasan irin halinki marar kyau, wato asirinki yatonu agurinshi daga ranar zaki haukace. Tace babu damuwa boka bazan taba yarda yasan halin danake ciki ba, inde inada kai ai baxetaba dawowa cikin hankalinshi ba.
Komawa tayi bisa gado tacigaba da kuka, saboda tarasa yanda zatayi tasamu wata hanya dazata temaketa kada Alh yasan halin datake ciki. Seyanzu take danasanin rashin yin kawaye, dayanzu tasan dole tasamu wadda zata kaita gurin wani bokan. Hannu tadaga sama tace ya Allah katemakeni ka rufamun asiri, kada Alh, yasan halin danake ciki.
Zaune suke aOffice din D,P,O bayan sungama kora mashi bayani. Kallon Jidda yayi yace awane hotel yace maki yake? Tace a Hamdala hotel. Kince kina da no shi ko? E gatanan, good, kirawoshi yanzu kinsan de irin kissar dazakiyi mashi yabaki damar zuwa anjima da dare. Shiru tayi tana wasa da wayarta. Saleem yace Yaya Jidda kidan fita daga waje kuyi wayarku nasan kunya kikeji ko? Murmushi tayi tajuya tafita.
.
D,P,O yace insha Allahu acikin daren nan zeshigo hannu dashi da yaranshi abunma yazo dasauki ai, tunda mayen mata ne. Wani guri Jidda tasamu sannan takirashi, yana dagawa tace Jidda ce, washe baki yayi yace Jidda kamar kinsan kenake tunani wlh, tundazu nake jiran kiranki, gashi banda no dinki naso inkiraki ince anjima kidawo bazan iya hakurin gobe ba.
Murmushin mugunta tayi tace kamar kasan abinda nakira infada maka kenan, nima tunda nadawo gida nake tunaninka, da na hakura se goben amma naji nakasa shiyasa nace bara inkiraka insheda maka anjima zanzo. Kara washe baki yayi yace kai amma naji dadi, gaskiya kinada kyauta me tsoka sbd wannan albishir din da kikamun. Tace shikenan nagode, karfe nawa zanzo? Yace ni wlh koyanzu ma kitaho dan amatse nake. Tace a,a kaide kawai kayi mana babban tanadi anjima karfe 8 zanzo ana ma zan kwana. Dariya yayi yace kai amma nagode, kinsan dama gobe ina da abokiyar kwana, yau semu kwana tare. Tace yauwa ni namanta room no, ok room 102 dakinzo kawai ki kirani. Sallama tayi mashi tana me hararar wayar.
Tana shiga tafadi masu yanda sukayi dashi, sosai sukayi farin ciki. D,P,O yace yauwa zansa yarana suzama cikin shiri anjima semu tafi. Godiya sukayi mashi. Sannan suka tafi. Ahanya Sameer yakira Alh, yafada mashi duk yanda sukayi, yaji dadi sosai yace Allah yakaimu daren.
Jungle ne yashiga dakin Figo, yana shiga Figo yayi saurin zuge jakar kudin daya daga, yamaidata, Jungle ya washe baki yace Oga ko kudin kake kara kirgawa? Ya daure fuska yace a,a wani abu nadauka abayan jakar. Zama yayi yace wlh Oga dama zuwa nayi infada maka ko cikin kudin nan zaka dan bamu wani abu munaso mudan shiga gari muyo siyayya.
Wani irin kallo Figo yayi mashi, yakara hade rai yace, kaga malam sauraramun, tunda mukazo kaga nadauki kudin nan nayi amfanin kaina dasu? Kuma duk abubuwan da kukeci ai acikin kudin ake maku, shine yanzu zasu turoka, kai me baki kazo ka amsar maku kudi ko? To babu wanda zanba ko sisi harsemun gama abinda yakawomu sannan aduba abinda yayi saura se abama kowa kasonshi. Sbd haka katashi kabani guri, kuma kafada masu gobe, akwai aikin dazan turaku kuzama cikin shiri. Tashi Jungle yayi ranshi abace yafita. Figo yace ashema wahalar danakeyi abanza indauki kudi inbaku.
.
Baba mairo tace kai duniya, lallai idan baka mutu ba, zakaga abubuwan mamaki dayawa, wai wannan tabewa dame tayi kama ace Kawu mahaifinka yake nemanka, ada yaso yanemi mamanka yanzu kuma yadawo gurin 'Ya. Sameer yace wlh kuwa Baba, nima kaina abun yana damuna, shiyasa ana kamasu baza,a bata lokaci ba, za,a turasu kotu. Saleem yace wlh da za,a barni da dukansu kashe su zanyi. Umman Sameer tace a,a ka kyalesu shari,a ma ta ishesu. Allah de yabaku ikon kamasu.
Kawun Sameer yace duniyace yanzu babu gaskiya, shiyasa komai ya lalace mana, tunda har aka iya samun Uban da yayi zina da yarshi babu abinda baza,a iya samu ba, mude mudage da addu,a akan yayanmu. Allah yakara tsaremu baki daya. Suka ce ameen.
Jungle yace wlh wannan karon hakurina yazo karshe, kutumar....., yama gama raina mana wayau, dazu fa inajinshi zanshiga dakin naji yana tare da mace, sena tsaya kusan dubu 100 yabata, kuma acikin kudinne. Shine muda mukasha wahala baze bamu ba, ti wlh sede kowa yarasa, amma bazan barmashi kudin ba. Suduka sukace ai dama Jungle kaine kake hanamu, da tuni mun gama mashi aiki, dammu munfison kazama Oga da wancan tsohon maci amana ne, mukam babu wanda yataba cin amanar wani nashi, wama yasani ko abinda yayi ma dan yayanshi ne alhakin yake binshi shiyasa kome muka samu baya zama, amma shekarar mu nawa muna fashi ace haryanzu ko yar mota babu wanda ya mallaka.
Kana ganin wadda muka siya akayi hadari da ita, tundaga ita bamu kara samun wata ba, sede musami kudi shikuma yabama mata. Jungle yace ka kyaleshi kawai wlh shima tashi tazo karshe, ayau zamuyi mashi abinda yayima yaron yayanshi. Ayau zesan zafin cin amana, kuma mu dauke kudin muyi tafiyarmu, babu wani gidan dazamuje, dama can rashin tausayi ne irin nashi amma ace wai diyar danka ita zaka nema saboda yana dan akuya. Kuzama cikin shiri, karfe 8 zamu dirar mashi, kuma ayau zamu bar garina nan.
.
Da misalin karfe 7: 30 D,P,O yagama tara yaranshi yayi masu bayanin komai, su Sameer kawai suke jira, basu dade ba, segasu sunzo hada Alh, da Jidda, bayan sun gama gaisawa yayi masu bayanin yanda suka shirya komai. Alh, yace amma kasan dole semun fara samun Manager na hotel din sbd aka ida bekamata police su shiga gurin mutum babu izininshi ba. D,P,O yace wannan Alh, ba matsala bace, nasan manager din damunje se yaran su tsaya awaje mufara samunshi, nasan baze bamu matsala ba. Tashi sukayi kowa yashiga motarshi suka nufi Hamdala Hotel.
.
Kwance yake daga shi se kajeran wando, wayarshi yadaga yakira Jidda, bugu 2 tadaga, Haba yan matana naga har 8 takusa amma najiki shiru kada de kicemun kinfasa. A'a ban fasa ba, ina hanya. Toshikenan sekinso.
Turo kofar dakin da akayi ne tasashi saurin kallon kofar. Jungle lafiyade zaku shigomun daki haka? Abinci ne, nasa ankawo maku, idan kuma aikin danace zansaku ne, bayau bane se gobe. Wai lafiya inata maku magana amma kun mani shiru? Hahhhh Oga Jungle yimashi bayani. Oga? Waye kuma wani Oga? Akwai Ogan daya wuceni?
Ada ba, amma yanzu Jungle muka sani da Oga. Jungle wai meye haka kamun magana mana. Kafa yasa yataka saman gadon da Figo yake kwance yayi, sannan yaciro sigari daya daga cikinsu yayi saurin kunna mashi ita. Seda yazuketa ya fesa mashi hayakin sannan yamikama na bayanshi hannu, wata sabuwar wuka mesheki yadora mashi ahannu.
Ganin wannan wuka bakaramin tsoratar da Figo yayi ba, lokaci guda yatashi zaune yace haba Jungle kasan fa bama irin wannan wasan, daga magana kuma meyako afito da wuka? Murmushi Jungle yayi yace aikai ba abokin wasa na bane bare inyi wasa da kai, kawai munzo muyi maka abinda kayima dan uwanka ne.
.
Zufa ce tafara keto mashi tako ina, yace dan Allah kuyi hkr haba jama'a yau shekararmu nawa muna tare amma ace rana daya kuzo mani da wannan magana. Idan ma matsayina kakeso wlh yanzu zan sauka inbaka, Jungle yace a,a kawai mungaji da tafiya da kaine, kuma ashekarunka yakamata ace kaima kana kabarinka yanzu kasamu ka kwanta kahuta.
Dariya suka sa, Jungle yace ina jakar kudinan take? Da hannu yayi mashi nuni, dan bakinsa yakasa magana, daukota yayi ya bude. Lallai kam kaci kudi dayawa, to bara kaji wlh kaci rabonka, mikama nakusa dashi yayi yace aje mana ita, yanzu zamu bar garinma.
Su Sameer suna zuwa bakin hotel din sauran yan sandan suka tsaya daga waje, su D,P,O da Alh, dasu Sameer ne suka shiga ciki, tambaya sukayi ko manager yana nan, akace yana ciki, kaitsaye suka nufi office dinshi. Bayan sungama gaisawa anan D,P,O yayi mashi bayani. Cike da tashin hankali manager yace ikon Allah, wlh bansan dasu a hotel din nan ba. D,P,O yace kada kadamu, kasan ba'a gane mugu afuska, mugodema Allah daya tona asirinsu ma. Manager yace amma gsky naji dadi, kuma nagode. Awane room kukace suke?102, Ok babu damuwa zaku iya zuwa. Godiya sukayi mashi suka fita.
Kafa Jungle yasa yatake cikin Figo, sunsa kyalle sun kulle mashi baki, hawaye kawai suke fita a idonshi. Hannu yahada alamun suyi hakuri. Wani yace Jungle muna bata lokaci fa, kawai aikata mashi shima. Yauwa abokina yama wannan AYAR danaji wani malami yana fadama wasu? Wace kenan? Kaini larabcin ne yakemun wahala, abinda kayi za,ayi maka ko? E e hakane, nima namanta Larabcin. Kuka sosai Figo yakeyi sede babu sauti.
Wuyanshi Jungle yakama babu tausayi yasa wuka yayi mashi yankan rago, jini yafara zuba, dede lokacin wayarshi tafara kara, daukarta Jungle yayi yace Hahhhhh mace ce, kashewa yayi yace kawai muware.
.
Suna murda kofar suma su Sameer suna tsaye, saurin komawa ciki sukayi, nan D,P,O yayi ma sauran yan sandan waya yace sushigo, Rarraba idanu su Jungle suka fara zarowa. Kwance suka sami Figo acikin jini, nan sukayima manager waya, shima yazo, bed sheet sukasa suka rufeshi.
Jidda kuwa kasa shiga dakin tayi haka tajuya takoma cikin motarsu, se kuka takeyi tana kara danasanin irin rayuwar datayi. Cikin lokaci kankani aka tasa keyarsu aka nufi station dasu, shikuma Figo aka nufi asibiti dashi, gaba daya mutanen Hotel din mamaki sukeyi kowa yana Allah wadai da halinsu.
Gaba dayansu zaune suke a babban falon dayake kusa da office din D,P,O sukuma su Jungle suna tsugunne, D,P,O ya kallesu yace banason mubata lokaci, kunsande munkamaku dumu dumu acikin laifi ko? Dan haka banaso kubama kanku wahala muma kubamu, kai, yanuna Jungle, inaso tsakaninka da Allah kayi mana bayanin abinda yakawo garin nan, da kuma bayani akan wanda kuka kashe.
Jungle yace tabbas yau nasan asirinmu yagama tonuwa, saboda haka bazan tsaya batama kaina lokaci ba, nine nan nakashe shi, kuma tare muke dashi shinema Oganmu............. Anan Jungle yafada masu komai da Figo yayi ma Baban Falak, sannan yafada masu yanda akayi suka san inda Falak take, da kudin dasuka samu, har yanda akayi sukaje gidan Alh, da abinda Zarah tayi. Kuma yasheda masu ita tabada kudi da hotonsu akaisu gurin boka.
Nan take Alh, yaji wata zufa tana fito mashi. Jungle yace muma yaci amanarmu shiyasa muka kashe shi, kuma ashirye muke damu amshi duk wani hukunci daza ayi mana. Kowa agurin seda yayi mamakin irin halin rashin tausayi na Figo. D,P,O yace to Alh, kunje de abinda yafaru, dan haka bazamu bata lokaci ba zamuturasu kotu, wannan kuma tunda yarasu, kawai zamuje ayardashi. Wadannan kudi kuma Alh, Allah ne yamaido maka da abunka, dannasan nakane, babu ta inda matarka zata samesu haka, amma zaka iya kaimata seta fada maka inda tasamesu. Sauran hukunci kuma yana gurinka, sede muce Allah ya kyauta.
Gabadaya Alh, kunya takamashi gashi agaban sirikanshi har 2 duka sunji bakin hali irin na matarshi, nan take yai tsanarta tashiga zuciyarshi, fita yayi batare dayace komai ba, yanufi motarshi yanufi gida zuciyarshi tana zafi.
Sameer da Saleem sukayima D,P,O godiya yabasu jakar kudin sukatafi, amota suka sami Jidda se kuka takeyi, Saleem yace dan Allah yaya Jidda kukan nan ya isa haka, keme yayi zafi maganinshi Allah. Sameer yace zakija ma kanki ciwo, kiyi hakuri hakanan. Tace haba Saleem, yanzu idan Dady yaji abinda na aikata nasan kasheni kawai zeyi, gashi zamu hada mashi zafi 2, dole yanzu yasan abubuwan da Ummi ta aikata, ina zesa kanshi? Wannan tashin hankali dame yayi kama? Kaiconmu, Dady beyi sa'ar mata da diya ba, gashi yarinyar dana raina na tsana yanzu itace zata zama abun alfahari agurin Dadynmu bani ba. Jalila kam taji dadinta dabata bari shedan yayi mata hudubar banza ba. Suduka seda sukaji tausayinta. Sameer yase ya isa haka......
Wayarshi ce tayi kara, yana dubawa yaga Alh, ne yake kiranshi yana dagawa yaji muryarshi tana rawa, yace hello, Alh, yace yauwa Sameer kadauko Falak da Kawunka, kuduka de kutaho gidana inason ganinku, yace to.
Sameer yace Saleem muce gidanmu tunda mota ta tana can se indauketa Alh yace mutaho dasu Umma , Falak da Kawu. Jidda tace innalillahi Wa inna ilaihir raji'un. Shikenan watan tonan asirinmu yakama,
0 comments:
Post a Comment