Bayan duk sun kammala iftar dinsu suka mike zuwa parlor kafin sallahn isha..ya rage daga Mummy sai Bobby da har yanxun ke dafe da head dinshi a dinning din...kama hannunshi Mummy tayi cikin tsananin tausayinshi tace"dan Allah ka ragema kanka damuwan nan Bobby"..tana rufe baki ya dago jajayen eyes dinshi dake nan kaman ana hura musu wuta yace"bansan yanda zanyi in dena ba Mummy..ya zanyi plss?.."yana rufe baki tace"ka fawwalawa Allah komai..ka kuma yi imanin cewa idan Aysha matar ka ce zaka aureta likewise idan ba matarka bace duk wnn kunchi da damuwan bai isa yasa ka sameta ba"..dagowa yayi yana kokarin boye tarin damuwar dake kan fuskanshi yace"shikenan Mummy amma pls can i see her this once?..i just wanted to make sure bata tareda yunwa ne kinga azumi akeyi and ina kallo daxun ba wani abincin kirki taci ba"..mikewa Mummy tayi tana cewa"don't worry i will take care of that"..da sauri yace"Mummy please..idan ban ganta ba bazan iya bacci ba wlh"..kallonshi Mummy tayi kawai ta ksa mgn..tausayi yake bata sosai..da ganin yanda ya jigata za'a san dama abun ya dade yana cinshi a zuci yanxun ne kawai ya fito sbd kasa cigaba da boyewa da yayi..bata sake hanashi ba ta kama hannunshi suka nufi flat dinta...a tare suka shiga dakinda take tayi saurin mikewa daga kwancen da take tana kallonsu...Mummy ce tace mata"anya kin koshi da abincin nan kuwa Aysha?..idan kina son wani abu ki fada a kawo maki"..girgiza kai ta shigayi da sauri tana cewa"Allah na koshi Mummy"..kallonta Mummy tayi kmr zata sake mgn sai kuma ta saki hannun Bobby tareda juyawa ta fita daga dakin..tana fita ya karasa ciki da sauri yana dubanta a raunane yace"if sbd mgnr dana fada ne yasa kika kasa cin abinci am sorry.. ki fadi duk abunda kikeso i will go out in samo maki yanxun"..girgiza mishi kai kawai tayi tareda komawa ta kwanta murya can kasa tace"na koshi"..legs dinshi yaji sunyi wani irin sanyi kmr bazasu daukeshi ba..murya a hankali ya kira sunanta ta mike tana kallonshi kawai sai ya juya ya fita daga dakin yana jin kanshi na sarawa da karfi...magani kadai ya iya sha snn ya hau gado ya kwanta tareda lumshe ido yana addu'an Allah ya kawo bacci ya daukeshi ko zai samu saukin halinda yake ciki...dukda maganin da yasha baccin bai samu daukarshi da wuri ba sai can kuma ya daukeshi ba tareda saninshi ba...ana kiran sallahn isha ya farka tareda sake dauro alwala ya wuce masjid..bai dawo ba saida suka idar da taraweeh still ya sake komawa daki ya kwanta tun daga nan kuma bai sake tashi ba saida alarm din wayanshi ya buga alaman time din sahoor yayi knn...mikewa yayi da sauri ya sauka daga gadon tareda fadawa bathroom yayi brushing ya fito kai tsaye ya fita zuwa flat din Mummy...yau ko nafilar dare bai iya tashi yayi ba sbd maganin bacci da yasha..a parlor sukayi karo da ita tana ganinshi tace"yauwa ka tashi?.."yace"na tashi..Mummy kin tasheta?.."murmushi Mummy ta saki tana kama hannunshi tace"na tasar maka ita Bobby..nama kai mata abincinta can dakin saida ta fara ci na fito"..ajiyar zuciya ya sauke gamida lumshe idonshi yace"Mummy kar kina fita taki ci fa"..hannunshi Mummy ta kama suka fita daga parlon tana ce mishi"zataci inshaAllah..believe me"..kai kawai ya gyada mata har suka fita...nashi abincin shima ta hada ta kawo mashi snn itama ta zauna cin nata..shi kuwa kasa cin abincin ma yayi gaba daya hankalinshi ya tafi wurinta..bayan mintina kadan ya mike yace ma Mummy zaije yayi nafilah kafin time din subhi yayi..batayi masa musu ba barshi dukda tasan kafin yayi sallahn sai ya fara zuwa inda Aysha tukunna...ilai kuwa yana shiga direct dakin da take ya wuce...ya sameta da mug din tea a hannu tana sha baisan lokacinda ya sauke wani ajiyar zuciya ba..kallonta ya danyi for like 5 mins snn ya juya ya fita don yasan ko yayi mata mgn ma zaiy wahala ta amsa mashi hakan kuma yana iya sa zuciyarshi ta hauro yazo yana mata abunda bai kamata ba.
Karfe goma na safiyar ranar Aunty Munubiya tazo gidan tareda yaranta..gaba daya sun cika parlon Mummy suna labari har Aysha da Mummy tasa dole aka kirata ta fito itama ake labarin da ita..dukda ba wani abu take cewa ba tana sauraronsu tana murmushi..ga Miemie da Nusaiba da suka sanyata tsakiya sun cikata da surutu kmr ba azumi suke ba...dukda labarin da sukey hankalin Mummy na kanta taga yanda take dan smiling idan an fadi abun daria sai hankalinta ya dan kwanta at least dai bata cikin damuwa yanxu...Bobby na fitowa ta wani hade girar sama dana kasa kmr ba ita ke smiling a while ago ba.. ya karasa ciki ya zauna suna gaisawa da Aunty Munu kmr bazai ce mata komai ba shima nashi face din daure can kuma ya kasa hakura yace"come and speak to ur dad"..kallonshi tayi taga shima ya daure fuska saida gabanta ya fadi da ganin fuskan nashi...tayi kasa da kai kmr bata jishi ba shi kuma ya sake cewa"ba dake nake mgn bane?.."mikewa tayi a hankali tana turo baki shima ya mike maimakon ya hadata dashi din sai ya kama hanyar fita itama dole tabi bayanshi kafin ya zazzaga mata masifa kuma...Mummy da mamaki ta bishi da kallo ganin har yanxu bazai dena hade ma yarinyar nan rai ba bayan duk wahalan da yakesha kanta...yana fita kai tsaye motarshi ya nufa ya bude front seat yana kallonta har ta karaso ta shiga ya rufe kofar snn shima ya zagaya ya shiga tareda tayar da motar ya figeta da wani irin gudu suka fita daga gidan...cikin tashin hankali ta juya tana kallonshi taga fuskan nan ba sarari sai ma sake tamkeshi da yayi kmr namijin saniya..kasa cewa komai tayi ta dauke kai daga gareshi...gudu yakeyi sosai ba tareda yasan shi kanshi ina ya dosa ba..kawai haushi yakeji da zata dinga treating dinshi like this sbd yace yana sonta bayan ya tabbata ko bestynta baza tayi treating dinshi haka ba ballantana kuma ace wnn tsohon saurayin nata...ganin yanda yake tsere da motoci akan titi kawai ta fashe mishi da kuka..yanzu idan yaje ya zubar dasu ya zasuyi?..kuka takeyi wiwi yana jinta baice komai ba bai kuma dakata da gudun da yakeyi ba dukda yanda kukan nata ke neman karyar mishi da zucia amma haka ya dake...saida yaje can Arean Naibawa ya hau fly over yabi titinda zai maidashi hotoro snn ya samu silent area da ba motoci ke wucewa sosai ba yayi parking nan wurin yana kallonta...lumshe ido yayi jin kukan nan nata yake har cikin ranshi..duk wnn zafin da ya fito dashi sai ya nemeshi ya rasa kukan nan da takeyi duk ya wargaza su...a hankali yake dubanta murya a matukar raunane yace"do u want to kill me?..so kike kiga karshena koh?.."shiru batace komai ba..ya sake cewa"am asking u..kinaso kisamun ciwon zucia sbd kinga na damu dake ne?.."dagowa tayi tana wiping tears dinta ta girgiza masa kai alamar aah..yace"then why are u doing this?..why are u punishing me like this?..na fada maki if sbd abubuwanda na maki a baya ne u are free to punish me amma am begging u to stop giving me tough times haka nan..na wahala mana..ko a haka kika barni i've learnt my lessons and ko a mafarki bazan sake yunkurin hurting dinki ba plss"..kallonshi kawai take ba tareda tace komai ba..kamo hannunta yayi da sauri ya dora kan chest dinshi yace"feel my heartbeat kiji..bai sake bugawa normal ba tun daga ranan dana fara sonki"..dakatawa yayi tareda dora kanshi kan hannun data yace"Aysha help me plss..am about going crazy"..kallonshi kawai Aysha keyi gabanta na tsananta faduwa...for the very first time taji ya mugun bata tausayi yau..ta yadda da gaske son nata yakeyi amma ita fa tana sonshi?..hannunta taji ya fara sagewa sbd kanshi daya dora akai dan haka ta shiga kokarin kwatan hannun ya sake mata shi da sauri ya dago kai yana kokarin maida tashin hankalin dake fuskanshi yace" am sorry"..yarfa hannun ta shiga yi kafin a hankali tace"it's ohk"..shiru sukayi na wani lokaci kafin Bobby yace"zan baki enough time kije kiyi tunani akai..i promise bazan sake disturbing dinki da mgnr ba amma do help me plss..help me out of this whole mess"..kallonshi har yanxun takeyi tanajin zuciyarta na karyewa..tausayi yake bata fiyeda tunaninta amma ya zatayi?..tasan idan tayiwa baby haka bata mai adalci ba..koda tana son Bobby bai kamata ta wulakanta shi ba ballantana ba sonshi takeyi ba tausayi kawai yake bata...yana gama mgn ya gyara zamanshi snn ya dauki phone dinshi yayi dialing number daddy...yana fara ringing ya mika mata wayar ta amsa tareda karashi a kunne...tanajin yayi picking tayi saurin cewa"daddy ina kwana"..yace"lafia lau..meya samu wayarki ne Najeeb yace tun safe yake kira bai shiga ba"..a hankali tace"kilan network ne..nima tun jiya ina kira bana samunshi"..daddy yace"shknn..yanzu ki zama cikin shiri zuwa gobe flight dinku zai tashi inshaAllah..shima Najeeb din a gobe zai iso"..nan da nan face sinta ya washe da tsananin farin ciki tace"to daddy..Allah ya kawoshi lafia"..daddy yace"Ameen"..snn sukayi sallama..ta mika mashi wayarshi tana cigaba da murmushi tace"thank u"..kallonta kawai yayi bai iya cewa komai ba...ya amsa wayan ya ajiye snn ya tada motar suka cigaba da tafia...bakin wani mall taga yayi parking snn ya bude motar ya fita..after few minutes ya dawo da leda a hannunshi ya ajiye back seat snn ya shiga ya sake tada motar suka wuce..har yanxun babu mai cewa wani abu a cikinsu..shi gaba daya tunaninshi yanaga neman hanyar da zaibi don ya samu soyayyarta yayinda ita kuma nata tunanin ke ga tafiyar da zasuyi gobe zuwa saudi sai kuma asalin tausayinshi daya fara damunta...har suka isa gida ba wanda yayi mgn cikinsu..bayan ya gama parking ya dauko ledan da ya ajiye a baya ya mika mata ba tareda cewa komai ba..batayi gaddama ba ta amsa ta duba sai taga abaya ne a ciki da wani zundumemen hijab da ta tabbata sai yakai mata har kasa..da dan murmushi ta dubeshi tana fadin"thank u"..bude motar yayi ya fita ya saki dan guntun smile shima kafin yace"u are welcome"..daga haka ya wuce gaba tana binshi a baya har cikin gidan...har yanxu suna nan zaune a parlor ya karasa ciki ya zauna ita kuma Aysha gaishesu tayi snn ta wuce daki don Allah Allah takey ta kira Billy da besty ta sanar musu tafiyanta gobe ne...Aunty Munubiya ta bita da kallo har ta shiga flat din Mummy snn ta juya tana kallon Bobby dake zaune kusada ita..ya saki dan murmushi yana shafa kai baidai ce mata komai ba...itama bata ce komai din ba ta maida hankali ga hiran da suke wanda mostly na zuwa Gombe da zasuyi ne cikin sallah.
Lamido na shiga daki daukan waya tayi ta shiga kiran Billy ta fesa mata zancen tafiyarta saudi gobe suna gamawa ta kira besty shima ta fesa mishi..tana shirin kiran Hamma taji karfe nawa ne flight din nasu kiran Prof ya shigo wayarta...dagawa tayi sukasha labari abunsu shima ta sanar mishi zata tafi Umrah gobe amma koda wasa bata fada mishi cewa tana gidansu proprietor ba don tasan for sure hakan zai bata mishi rai...saida suka gama hiransu snn ta kira Hamma shima dai labari sukasha bayan sun gama ta dauki wayan nata ta koma parlour.
Washegari around 11 ta gama shirya kanta tsaf cikin dogon rigan daya siyo mata jiya blue black..tayi veiling da mayafin rigan ta dauki dan small bag daya hado mata dashi duk a jiyan tasa phone dinta a ciki da 'yan abubuwanta snn ta rataya bag din a shoulder dinta ta fito tanata baza kamshi...Aunty dake zaune tareda Mummy a parlor tana ganinta tace"fa tabarakallahu ah'sanul khaliqeen..sannu Aysha"..dan murmushi ta saki kanta kasa ta karaso cikin parlon tana gaishesu kowa na yaba irin kyawunda tayi yau din nan...Bobby da ya gama shiryawa shima yana fitowa daga flat dinshi idanunshi basu sauka ko inaba sai kanta..heart dinshi har wani irin tattarewa yayi ya koma can gefe guda ya cushe sbd tsabar kyau daya ga tayi..duk yanda yaso ya dauke idonshi a kanta kasawa yayi..tayi mishi kyai fiyeda duk tunanin mai tunani...lokaci daya kuma wani irin kishi ya lullu6eshi daya tuna jrgi zataje ta hau a haka har saudia..ranshi yaji ya baci da batasa hijabin daya hada mata dashi ba..a hankali ya karasa cikin parlon fuska a daure yace mata"shi hijabin laifin me yayi maki da bazaki sashi ba?.."kallonshi tayi taga yanda ya wani hade rai sai ta marairaice zatayi mgn ya katseta da fadin"ki koma kije ki daukoshi ki sameni a mota"..yana fadan haka ya maida dubanshi ga Mummy har yanxu ya kasa sakin fuskanshi yace"Mummy zan kaita airport in dawo"..Mummy tace"to saika dawo..Allah ya tsare"..yace"Ameen"..snn ya juya ya fita daga parlon..itama Aysha juyawar tayi ta koma inda ta baro hijabin ta dorashi kan veiling din da tayi snn ta fito ta sake sallama dasu Mummy da suka rakata har bakin kofa snn ta nufi inda motan nashi yake...ko kafin ta karasa ya gama tada motar yayi warming dinta dan haka tana shiga janta yayi suka fita daga gidan...suna hanya ta sake juyawa ta kalleshi har yanxu fuskanshi babu fus cikin ranta sai take mamakin hali irin nashi...jiya jiyan nan fa ya gama marairaice mata yana cewa ta taimakeshi amma yanxu shi yake wani daure mata fuska kmr ba shine yace idan bata aureshi ba mutuwa zaiyi..ita zuciyarta ya fara tantamar anya ma son nata yakeyi kuwa da gaske?..har suka isa airport baice mata ba itama batace mishi ba..duba agogon hannunshi yayi yaga time dinya kamata ace ya iso ma ya wuce dan haka yace mata"call him kiji idan ya karaso"..batayi musu ba tayi dialling number dinshi..yana dagawa tace"Hamma gamu a airport din fa"..daga daya bangaren Najeeb yace"yea gashi na hangoku yanxun nan..am coming"..daga haka ya kashe wayarshi ita kuma ta shiga dube duben inda zata hangoshi..can ta ganoshi yana nufowa inda suke sbd farin ciki kasa hakura tayi ya karaso inda suke saita tafi da saurinta kawai ta kama hands dinshi tana sakin smile...runtse ido Bobby yayi sbd saukan wani abu da yaji mai kamada saukan aradu a cikin zuciyarshi..shi kuma waye wnn da zataje ta cacime hannunshi haka?..anya kuwa Lamido tanada hankali?..Hamma janyeta hannunshi daga nata yayi yana dungure mata kai yace"zanga randa zakisan kin girma wlh"..wani murmushin ta kara saki har dimples dinta suka fito..Bobby kuwa ji yayi kaman zai hadiye zucia ya mutu...shin wai kowa haka yakeji idan yaga yarinyar da yakeso tareda wani ko kuwa nashi ne yake neman wuce gona da iri?..shidai tunda ya fara son yarinyar nan yayi bye bye da farin ciki..bai tsinci komai cikin son nata ba sai tarin damuwa da ciwon zucia...suna karasowa inda yake ta sake kama hannun Hamman nata tace"Hamma wnn shine proprietor dinmu"..kallonta kawai Bobby keyi yanaso yasan alaqar dake tsakaninta da wnn mutumin da taketa kwakwumarshi tun daxu sbd batada hankali..yasan dai zaiyi wahala ace daddy ne ya haifeshi..kallonshi Najeeb yayi yana murmushi ya mika mashi hannun damanshi tamkar yasan tunaninda yake cikin ranshi yace"sunana Najeeb Auwal Lamido"..Bobby ya runtse ido cikin zuciyarshi yace"shikenan cousin dinta ne..ai dama nasan ni na shiga uku"..a zahiri kuma kokari yayi sosai ya dora wani dan guntun murmushi akan fuskanshi snn ya mika mashi hannu shima kafin yace"Dr Bobby Attahir Waziri"..shaking hands dinsu sukayi Hamma na cigaba da murmushi yace"nice to meet u Dr Bobby"..shima wani murmushin ya kara saki da bai kai zuci ba yace"nice meeting u too"..Lamido dai na tsaye tana kallon faces dinsu idan ta kalli na wnn sai ta juya ta kalli na wnn...bayan sun gama gaisawa ya sake mishi godia kan riketa da yayi a gidansu har zuwa yanxu..Bobby bai iya cewa komai ba sai kai daya daga musu..ko tsayawa ganin tafiyarsu baiyi ba ya juya ya wuce abunshi...ciwo yakeji daya kasance shi din cousin dinta ne..yana bude mota ya shiga ya jingina kanshi da kujera murya can kasa yace"here is another threat"..yasan yanda cousins ke taka muhimmiyar rawa wajen ruining relationships..relationship da yake da kwari ma ruining dinshi suke ballantana nashi da ko fara building relationship din baiyi ba...ya tabbata daga shi har son da yake mata suna cikin tsaka mai wuya..on one hand akwai cousin dinta on the other hand kuma akwai bestynta..shikam ya shiga uku da Allah ya jarabceshi da son Lamido..ya tabbata jarrabashi ake sonyi shiyasa aka jarabceshi da matsanancin sonta saidai fatan Allah ya bashi ikon cinye wnn jarrabawa.
Tun daga wnn rana Bobby bai sake mata mgnr yana sonta ba kmr yanda yayi alkawari..kawai jira yakeyi ta gama tunaninta ta fada mishi shi kuma yayi alkawarin zai dauki duk wani decision data yanke...sallah saura sati daya suma suka tafi Umrah gaba dayansu..ko a can ma ya sake haduwa da ita don daddy da kanshi yay inviting dinsu zuwa masaukinsu...duk halin da yake ciki bai bari daddy ya fahimci sonta yakeyi ba sbd yafison ta fara amincewa dash kafin yaji mgnr...kowa ya dukufa sosai da ibadarshi as goman karshe ne kowa yana fatan saduwa da lailatul qadr...addu'an Bobby kusan rabi akan Lamido yake..roko yake idan akwai alkhairi tsakaninsu Allah ya tabbatar idan kuma babu Allah ya cire mashi sonta daga zuciyarshi snn ya hada kowa da rabonshi...a nata bangaren kuma har ga Allah ba karamin tausaya mishi take ba..sau tari tana kamashi yana kallonta idan yaga zaa gani sai yayi sauri ya dauke kanshi..ko a waya ya dena kiranta sbd alkawarin daya dauka na bazai sake disturbing dinta ba har zuwa lokacinda zata gama nazari akan mgnr...ko Billy bata fadama yace yana sonta ba sbd batason yanda Billyn ke nuna dama can tasan yana sonta itace take raina masa hankali...a can sukayi sallah gaba dayansu sai washegarin sallah suka bar Saudi...jirginsu ya sauka a Kano inda daga nan su Aysha suka wuce Gombe yayinda su Bobby kuma suka wuce gida kowa ya fara shirin tafiya Gombe da zasuyi wajen Waziri.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
41
The following day karfe 10 suka dauki hanyan Gombe..mota biyu suka tafi dashi nashi dana aunty sumy sai kuma drivers guda biyu...tunda suka wuce wudil Bobby keta faman kallon hanya yana jinjina buwayar ubangiji wai yau shine ya dauki hanyan Gombe da kanshi kuma da son ranshi ba tareda anyi forcing dinshi ba..ikon Allah knn yafi gaban wasa..ada gani yake kome zai faru bazai iya yafewa waziri da yan uwan dad dinsu ba ballantana har ya dauki kafa yaje har Gombe da kanshi amma yanxu gashi nan kan hanyan zuwa Gomben kuma ba tareda wani ya takurashi zuwan ba...abubuwa da dama yaga sun canxa mishi a hanyar bai san ko sbd shekarun daya dauka baije bane..the more suna kusantar Gombe the more zuciyarshi ke kara sanar dashi cewa Lamido ma fa a Gombe take..to ta yaya zaayi ya ganta shida ba gidansu zaije ba...wani 6angare na zuciyarshi kuma na ce mishi ganin nata sai sanyaya mishi zucia amma sam yaki yadda da hakan sbd yasan ko yanason ganinta ma bashida yanda zaiyi tunda baida wani reason da zai fadama babanta na zuwa gidan nasu..besides so yake ya fara nesanta kanshi da ita don ya fara gajia da walakancinta..banda sharrin zuciyarshi ma data kasa hakura da ita ai da bata isa ta dinga masa wnn iskancin yana shanyewa ba da tuni yayi maganinta..da wadan nan tunane suka shigo garin Gombe..nan ya sake wara ido yana kallon garin da yaji wani irin attachment tsakaninshi da garin ya shigeshi..Allah ya sani shi koda can ba Gombe ya tsana ba..tsanar da yayiwa family dinshi ne yasa yakejin kmr ya tsani garin amma he never hated Gombe domin ko ba komai a nan aka haifeshi...kai tsaye adress da waziri yasa aka turo musu sukabi har kofar sabon gidanshi da bai dade da tarewa ba...bude musu gate akayi suka shiga ciki da motocinsu...waziri daya kagara da zuwan nasu kasa hakura yayi saida ya fito compound lokacinda suka shigo...gaba daya fitowa daga mota sukayi suka nufo wurinshi aiko ya buda musu hannu suna karasawa ya shiga hugging dinsu one by one yana sanya musu albarka..har su Miemie saida ya runguma snn suka dunguma zuwa ciki...Mummy dai na daga gefe tana kallon yanda yake cikin tsananin farin ciki sbd ganin jikokinshi..lumshe ido tayi ita ko a haka Allah ya dauki ranta ta cika burinta tunda ta shirya tsakanin yaranta da yan uwan mahaifinsu..har mamaki ma wazirin ya bata ganin yanda jikinshi yayi sauki sosai kmr bashi ne wanda yayi shekara da shekaru yana jinya ba...babban parlonshi da yake saukar baki ya shiga dasu nan aka shiga kawo musu abinci iri iri daga cikin gidan ana ajiyewa a gabansu...bayan sun gaisa an sake neman yafiyar juna yasa aka kaisu masauki domin su huta kafin 'ya'yanshi daya kira su karaso...Bobby da sab dakuna biyu aka basu dake nan cikin parlon nashi yayinda su Mummy kuma aka shiga dasu cikin gida...daki biyu suma aka basu Mummy da Miemie daya aunty sumy da Ilham suma suka dauki daya.
Lamido's Palace...
Da sauri ta fito daga dakinsu daga ita sai dan towel a jikinta ta shigo parlonsu da akayi decorating dinshi da flowers da baloons kmr dai wani shagali za'ayi a ciki...duba takai zuwa ga wasu set of baloons masu kyau da aka jerasu daga can saman wall din dakin an rubuta Happy Birthday Aysha a jikin baloons din batasan time din da ta saki murmushi tana karema decor din parlon kallo ba...abun ya karamin kayatar da ita yayi ba tun ma ba'a fara celebration din ba..rabonta da celebrating birthday tunda ta cika 15 sai yau kuma data cika 20 ta samu ta lalla6a Ammi da kyar ta amince mata tayi bayan ta gama kafa mata dokoki iri iri...Billy ce ta fito daga dakin nasu ta shiga duban Aysha daketa kallon decorations din parlon tana sakin murmushi tace"ikon Allah..yanxu Lamido bazaki zo ki shirya ba sai mutane sun cika gidan knn?.."juyawa tayi da sauri tana cigaba da murmushinta tace"Billy bazaki gane farin cikin da nake ciki bane..wai nice nake cika 20 years yau din nan..oh Allah Alhamdulillah"..tsaki Billy ta saki tana harararta tace"wlh da Ammi zan hadaki idan baki wuce kin fara shiryawa ba..yanzun mukayi waya da Sa'eed yace har sun kar6o cakes din suna hanyan dawowa fa"..juyawa tayi da sauri ta koma dakin tana cigaba da sakin murmushi kmr ta6a66iya...da kallo Billy ta bita itama tana murmushi cikin zuciyarta tace"Allah dai ya nunamin ranar da zaki girma Lamido"..daga haka itama ta koma dakin suka fara shiryawa.
Karfe hudu da rabi ta gama shirinta cikin straight gown na wani black material sai walwali yakeyi tasa red turban a kanta gashin nan da yasha uban gyara yana kwance luf luf kmr na balarabiya..light make up da tayi applying ba karamin sake fito da kyawunta yayi ba..su Billy da sauran cousins dinta kuwa straight gown suma sukayi na wani red material kowa tasa black turban akai...Husna ce ta shigo cikin irin kayansu itama tasha kyau kmr babu gobe tace"Addah dan Allah kuyi sauri ku fito mutane sun fara zuwa fa"..hannun Aysha dake tsaye gaban madubi sai kalkale takeyi Billy ta kama tana fadin"zo muje dan Allah keda bakya gajia da kallon madubi"..binsu tayi suka fita daga dakin tana kokarin kwace hannunta...parlon yana nan cikeda cousins dinta mata wanda yawanci mates dinta ne sai mates din Husna suma duk suna sanye cikin nasu kayan iri daya dasu Husna suna ganinta suka hada baki suna fadin"happy birthday to you Lamido"..karasowa tayi cikin parlon tana kallonsu da murmushi tama kasa cewa komai...kowa sai yaba irin kyau da tayi yake kafin a fara tace Husna taje ta shigo mata da besty ciki...ba musu kuwa ta juya ta fita kmr dama jira take..jikin motarshi ta sameshi yanata danna wayarshi ta dan daga murya yanda zai jiyota tace"Hamma besty Adda tace wai ka shigo ciki"..maida wayarshi yayi aljihu yana murmushi ya shiga takawa zuwa inda take yana cewa"bazaki dena Hamma bestyn nan ba koh Husna Lamido?.."dan murmushi ta saki tace"to yi hakuri na dena fada..Hamma Sa'eed"..wani murmushin ya kara saki kafin yace"yauwa yanxu kikayi mgn"..daga haka suka shiga cikin parlon..daidai lokacinda Hamma Najeeb shima ya gama shiryawarashi ya fito suka karasa ciki a tare..can dinning suka nufa suka zauna yanda zasuna ganin duk abunda sukeyi daga nan wurin...Billy da Lamido suka karasa kusada table da aka cikashi da manya manyan cakes dinta guda biyu da snacks da drinks kala kala suka tsaya..kafin ta yanka cake din ta dago tana duban su Sa'eed dake dinning ta wani turo baki abunka da an riga an saba tace"Hamma to ku karaso a yanka cake din mana"...ba musu suka taso zuwa wurinda take..Hamma ya tsaya right hand dinta dasu Husna gefenshi..Sa'eed kuma ya tsaya left hand dinta sai Billy gefenshi..gaba daya sukayi extending hands dinsu bayan anyi counting to three suka shiga yanka cake sauran occupants din wurin nata singing mata"happy birthday to u..happy birthday to u..happy birthday dear Aysha..happy birthday to u"..tana gama yanka cake din ta dauko ta sama Hamma a baki tareda Husna da Yusra snn ta sake daukan wani ta sama Billy da besty suma duk a bakinsu..masu daukan pictures da videos nata yi daga nan kuma duk akabi aka shashshafa ma kowa cake din a fuska bayan duk ta basu sunci sai kuma aka cigaba da hotuna...Sa'eed sai so yake ya samu ya fita amma ta hanashi..yana juyawa zatace"besty dan dawo a daukemu da wance"..haka nan ya hakura har aka gama pics din snn suka koma dinning shida Hamma suka zauna...Husna da Billy ne sukaje sukayi mgn da Ammi wai tazo suyi pictures..saida suka hadata da Allah annabi snn ta yadda ta fito akayi nusu pictures din Lamido sai wani rungumarta take Ammi ta danyi kasa da murya yanda ita kadai zataji abunda take fada tace"zakici ubanki ne wlh..kici gaba da rungumana kmr wata sa'ar wasanki"..batasan lokacinda ta kwashe da daria ba...Ammi ta sake cewa"zanyi maganinki"..haka dai sukaita rungumarta suna daukan hotuna har Sa'eed saida Lamido ta kira wai yazo ayi musu hoto da Ammi..ba musu ya taso akayi musu...ana gama pictures din Ammi tayi komawarta daki su kuma suka kunna home theater suka sa kida suka fara dancing abunsu..ko ban fada ba nasan kunsan mutumiyarku gwanar rawa ce dan haka ta gyagije tanata dirkar rawa sauran suna tayata...a takaice babu kalan waqar da basuyi rawanshi ba..anyi naija anyi na hausa musamman Ado Gwanja Fav din nata..basu tashi daga partyn ba sai wajen magrib...nan cousins dinta duk suka watse bayan sun cikata da gifts iri iri..ya rage daga ita sai su Husna sai Billy da besty sai kuma Hamma...sallah suka farayi snn suka zauna suna duba gifts din data samu..Hamma da Sa'eed da suka dawo daga masjid kowa yayi presenting nashi gift din ta karba tana godia...na Hamm ta fara budewa latest jessy ne manchester da baby doll na pogba..sbd tsabar farin ciki batasan lokacinda taje ta rungumeshi ba..bayan ta dawo ta bude na besty shi kuma taga wani hand band mai kyau red color am rubuta besty a jiki..sai locket mai shape din heart shima an rubuta besty a jiki sai kuma wani hadadden diary da pen a jikinshi shima yana daukeda sunan besty...farin cikinta kasa boyuwa yayi sai kallonshi kawai takeyi kaman wata sokuwa..motsi daya biyu zatace"besty nagode sosai"..shi har saida ya gaji da godiyan nata ma wlh...kafin suyi dinner Hamma yaje ya roki Ammi kan yanaso ya fita dasu suyi dinner a waje idan ta amince knn..tace ba damuwa suje amma kada su dade...yana zuwa yace musu duk suje su shirya they are going out for dinner yanxun...ba Lamido kadai ba hatta Billy dasu Husna murna sukeyi...nan da nan kuwa sukaje suka sake shiri kowa ta fito suka fita compound.. Lamido da Husna suka shiga motan besty Billy da yusra kuma suka shiga na Hamma..haka suka fita daga gidan kai tsaye Hamma ya wuce dasu Blue lounge and resto...kai tsaye vip section suka shiga aka kawo musu menu kowa yayi ordern abunda yakeso...bayan few minutes aka kawo musu abunda sukayi order nan kuma suka fara ci suna dan taba hira...Husna ce ke basu labarin wani classmate dinta da yake sonta wai kullum itada friends dinta sai sun sashi ya kawosu nan wurin sunci abinci ko kuma yazo ya musu takeaway sai daria suke suna jinjina wulakancin Husna...a daidai wnn lokacin kuma Bobby suka shigo wurin tareda wani cousin dinshi daya dage kan lallai sai ya rakoshi yaci abinci...wani irin 6acin rai da faduwar gaba yaji sun riskeshi at once sakamakon tozali da yayi da ita tana zaune a tsakiyar maza tana cin abinci kuma tana daria...ranshi ba karamin baci yayi ba..wai yarinyar nan wace iri ce ita?..karasawa yayi ya samu table daga nan bayansu ya zauna yayinda cousin dinshi da sukazo tare ya shiga ciki wurin wani friend dinshi...daga nan inda yake yana iya hango gashin kanta dake waje..runtse ido yayi ya rasa dalilinda yasa batada burinda ya wuce tayi kwalliya ta fito da gashi..sam baisan wace irin fitinanniya bace ita...kamar ance ta juyo yaga ta mike daga seat din da sauri tana rikeda wayarta tazo ta wuce ta inda yake zaune tana amsa waya...riga da skirt ne a jikinta wnn karon ta daura dankwali amma mayafin nata akai ta dorashi dukda cewa ba mai girma bane..kallon yanda each and every part of jikinta ke moving as a resulf saurin da take yayi...wani irin zafi yakeji na fitowa da tayi a haka..yanxu yasan kaf mazan dake wurin nan ba wanda bai kalleta ba haka suma wanda take tare dasu kilan har taba jikin nata ma sunyi...tunanin haka yasa kanshi yai wani mugun sarawa da bai shirya masa ba...juyawa yayi ya kallesu yaga hankalinsu ba kanta yake ba snn yasake dubawa da kyau yaga kowa harkan gabanshi yake dan haka ya mike daga inda yake a hankali ya karasa inda take kawai saiji tayi an fizge wayar dake hannunta an jata da wani irin karfi an fitar da ita daga wurin...daddagewa tayi zata kwada ihu yayi saurin toshe bakinta da hannunshi..da yaga tana neman 6ata mishi lokaci ya wani hade rai ya zuba mata idanunshi da yasan dole su ladabtar da ita..lokaci daya ta hadiye wani yawu kafin yacigaba da janya har zuwa inda motarshi..budewa yayi ya zurata ciki snn shima ya zagaya ya shiga tareda locking kofar daga ciki...cikin tsananin tashin hankali ta sake bude baki zata kurma ihu yayi azamar janyota ya matseta a jikinshi yana kallon cikin idanunta...wara idon tayi sosai tana kallonshi tana mamakin me ya kawoshi Gombe kuma..kodai aljani tayi gamo dashi ne?..nan hankalinta ya sake tashi ta shiga zubda hawaye tana"wa innahu sulaimanu wa innahu..."kasa karasawa tayi saboda kallon da ya tsareta dashi...tabbas shine ba aljani bane don duk dunia babu wanda idan ya kalleta takejin irin haka sai shi..amma meya kawoshi Gombe?..bude baki tayi zatai mgn ya dora finger dinshi akan bakin tareda hade fuskanshi da nata cikin wata irin dacin murya yace"ke har yanxu bakida hankali bakisan ciwon kanki ba koh?.."lamgabewa tayi tana kallonshi a hankali tace"sir ms nayi?.."harara ya watsa mata mai kyau kafin ya nuna jikinta yace"take a look at yourself..ke ko kunya bakiji ba kika fito haka kuma tareda maza"..girgiza mishi kai tayi kafin tace"sir it's my birthday today shine amma ya fito damu muyi dinner amma ni ba haka nake fitowa ba"..kallonta yayi ya danyi yayi shiru jin tace its her birthday..wato tsanar da tayi mishi har yakai da zatayi birthday bata fada mashi ba..kawai sai yaji ranshi ya sake 6aci..nan take ya kuma daure fuska ya bude mata kofa murya cunkushe yace"fita"..kallonshi tayi da mamaki jik abunda ya fada..ta dan rausayar da kai tace"nifa.."bai bari ta karasa ba ya sake nuna mata kofar da har yanxun ke bude yace mata"ki fitamun a mota nace"..kin gita tayi kawai ta tsaya tana kallonshi..kallon nata shima yayi for like 2 mins kafin ya dauke idonshi..ta sauke numfashi kafin a hankali tace"am sorry"..juyowa yayi yana dubanta yace"for?.."tace"for everything..am sorry for everything plss"..kai ya gayada mata kafin ya sske pointing mata kofa yace"naji..now kije..ki tafi kawai bana son ganinki anymore"..idanu ta wara taa kallonshi da mamaki shi kuma ya sake hade rai ya juyar da kanshi gefe..ba yanda ta iya haka ta bude motar ta fita duk sai bataji dadin yanda yayi treating dinta ba..does this mean ya dena sonta?..aikam indai yanda yake nuna yana sonta da gaske bai isa yace ya dena sonta yanxun ba..dole ma tasan yana sonta walakancin ne kawai ya motsa mashi..kallonshi tayi ya lumshe ido tareda jingina kanshi da kujera..yanda ya rufe ido sai lashes dinshi suka kwanta kasan idon nashi kmr na mace...lips dinshi dake nan very thick ta kalla sai kuma idanunshi dake sata nutsuwa ko bata shirya ba...kyau na musamman taga yayi mata dama kuma tasan shi din mai kyau ne amma yau sai taga kaman karo mishi kyawun akayi...runtse idonta tayi da sauri cikin raunin murya ta kuma tace"sir am sorry plss"..bude idanunshi yayi a hankali jin yanda voice dinta ke cracking har yanxun face dinshi daure yace"i said babu laifin da kikamin..ko bakida kunne ne?.."a razane take kallonshi cikin tsananin mamaki..gaba daya sai taga ya birkice ya dawo mata asalin proprietor data sani mara mutunchi..ba shiri ta sauka daga motar tana cigaba da mamakin wnn masifa da yayi mata..duk yau sai bataji dadin sudden change din nashi ba..knn dai tafiso yayita chasing dinta tana walakantashi idan ba haka ba why zataji ba dadi sbd yayi mata abunda dama ba yanxun ya fara ba..masifa dai tun daya fara ganinta yake zazzaga mata shi don haka zuwa yanxu ya kamata ta saba amma sai taga wani daban tunda ta mance when last ya mata wnn bala’in nashi..haka tana tafe tana tunani har ta koma inda ta baro.
Washegari Billy ta koma gida ya rage daga su sai su a gidan...Ammi na kitchen sunata shirin tarban daddy da zai dawo daga Abuja yau...hankalin Aysha duk ba jikinta yake ba as tunda sukayi waya da baby daxun ya daga mata hankali..cewa yake wai indai tana sonshi da gaske saita bashi daman yazo ya nemi aurenta kafin holidays dinsu ya kare idan kuma ta sake dakatar dashi zai dauki hakan da tayi as bata sonshi...hankalinta ya tashi sosai Allah ya sani bata san ta ina zata fara cema daddy za'azo neman aurenta ba..gashi duka duka hutun nasu saura one week ya kare..yanxun daga ina zata fara ne?..tun daxun take tunanin kota fara sanarda Ammi ita kuma ta sanar da daddy amma tsananin tsoro ya hanata tayi hakan dan Allah ya sani itadai tsoron abunda zaije ya dawo take..kilan ma cewa za'ay ba karatu takeyi a Kano ba soyayyanta kawau take..shi kuma baby duk yabi ya birkice mata ko wayanta ma ya dena dauka...a waya ta kira Billy tayi mata bayanin komai ita kuma ta bata shawaran taje ta fadama Ammi duk yanda sukayi da ita saita fadama babyn..tayi na'am da wnn shawara na Billy dan haka bayan ta fito daga kitchen kai tsaye ta bita zuaa bedroom dinta...tana kokarin shiga wanka Aysha ta shigo dakin..Ammi ta shiga binta da kallo ganin yanda tayi wani sanyi kmr ba ita ba tace"menene?.."karasawa tayi ta zauna gefen gado tana duban Ammin fuska a marairaice tace"Ammi mgn nakeso muyi"..komawa Ammi tayi ta zauna tana fuskantarta tace"to ina jinki"..a hankali ta sake dagowa ta kalleta sai kuma tayi kasa da idonta tace"Ammi dama..da akwai wani mutumi da muka hadu dashi a kano"..kallonta Ammi keyi tanaso taji inda zancen nata ya dosa tace"umhum cigaba mana"..saida ta hadiye wani yawu snn tacigaba"Ammi dama cewa yayi yana sona kuma da gaske aurena zaiyi..nace bazan kawoshi gida ba saina gama school shine daxu yace shidai dole yanaso ya turo ayi tambaya kafin na koma makaranta"..ta sakeyin shiru ta kurawa Ammi ido tanaso taga reaction dinta...ganin kallonta itama Ammin keyi tayi saurin cewa"kuma wlh Ammi bani nace mishi ya turo ba..da kanshi yace zaizo wai a fara saninshi a gida"..sauke ajiyar zucia Ammi tayi kafin tace"ke kina sonshi ne?.."shiru tayi tana kallonta..Ammi tace"magana fa nake miki"..a hankali tace"eh.."Ammi tace"shikenan kije zanyi magana da daddy idan ya dawo sai a fadama Lamido ya basu ranar da zasuzo..da yake ke mara hankali ce shine kikaje kika fara kulashi ba tareda ya turo gidanku ba"..itadai shiru tayi kanta kasa dan bata taba zaton Ammi ba fada zatayi mata ba..koda yake dama ance duk wata uwa mace da zarar yarinyarta ta girma batada burin da ya wuce ta sadata da dakin mijinta saidai idan lokaci baiyi ba...wnn mgn na mutane kuwa haka yake don ga alama nan ta gani wajen Ammi...mikewa tayi ta fita daga dakin bayan Ammi ta salameta..cikeda farin cikinta ta kira Prof ta sanar dashi yanda sukayi da Ammi..murna wajenshi tamkar bai taba aure ba...suna gama waya ta kira Billy itama ta sanar mata sai kuma ta jiye wayar tareda fadawa duniyar tunani..babu wanda ya fado mata a rai sai proprietor.. ta tabbata zai shiga mawuyacin hali idan yaji wnn labarin..to amma ita ba sonshi takeyi ba kuma bazata iya auren mai shekarunshi ba..tafi son babban mutum daya kusan haifanta yanda zataje taci duniyarta da tsinke...ta lumshe ido tana sake lafewa kan pillow incident dinsu ya shiga dawowa brain dinta...she remeber how he hold and tell her yana sonta morethan anything...how he made it clear cewa idan ta auri wani mutuwa zaiyi..then she remember his jealousy..ta tabbata level of jealousy dinshi yafi na baby sosai sbd yanda ko wani yaga yana kallonta kishi yakeji...abubuwa da dama ta shiga tunawa game dashi tun daga ranar daya fara mata allura har zuwa lokacin festival da Presentation da abubuwan da ya dinga nunawa a lokacin...ajiyar zucia ta sauke da gaske mgnr Billy haka yake kilan tun ranar daya fara ganinta yake sonta ganewa ne batayi ba...sai yanzu take ganin tsagwaron kishi cikin duk wnn abubuwan da yayi mata a baya...sake juyawa tayi tana rungumar pillow ta tuna how his Mom and siblings treated her time da taje gidansu..they are the most kind and nicest people she've ever come across..sunada karamci sosai likewise shi kanshi Bobbyn saidai shi yanada matsala daya which is masifa da shegen taurin kai...gaba daya tunaninta ranar sai ya tattara ya koma kanshi da ahalinshi kuma ta rasa dalilin hakan don dai ita bata taba tsayawa tunaninshi bama balle kuma na family dinsh..sai yanxu take ganin rashin dacewar amsan data bashi ranar..sam bata kyauta ba..ko bata sonshi bai kamata tana walakanta shi ba ko don sbd karamcinshi a gareta..yanada kirki sosai and yana sonta da gaske..duk sai taji wnn tunane tunanem sun addabeta sun hanata sukuni.
Tun safe kowa ya fito parlon waziri suka gaidashi kmr yanda suka saba gashi har za'a fara breakfast Bobby bai fito ba...parlon nashi a cike yake da Uncles din su Bobby maza da yaransu sai Aunty Munubiya dasu Aunty Sumy suma duk suna nan...Waziri ne ya dubi daya daga cikin jikokinshi yace"Khalid je daki ka dubamun Attahir kaga meya hanashi fitowa har yanxu"..ba musu khalid din ya mike zuwa dakinda aka sauki Bobby..a kwance ya iskeshi can karshen gado ya wani dukunkune kanshi cikin duvet sai rawan sanyi yake...da sauri ya haura kan gadon tareda yaye duvet din yaji jikinshi akwai zafi sosai dan haka ya sauka da sauri ya fita daga dakin yaje ya sanar da waizir..hankalinshi ya tashi sosai dan ko Mummy bazata kaishi tashin hankali ba..mikewa yayi kai tsaye zuwa dakin nashi..ya zauna gefen gadon tareda kai hannu yayi feeling temperature dinshi yaji zafi sosai..dan haka yace a fito da mota su tafi asibiti..ba yanda wasu daga yaranshi basuyi ba kan ya bari a kira doctor yazo ya dubashi amma yace sam bazai iya jira har sai likita yazo ba..ba yanda suka iya dole haka aka fito da mota suka wuce asibitin daga shi sai Bobby sai daya daga cikin cousins dinshi da kuma Uncle dinshi.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
42
Suna shiga asibitin family doctor dinsu ya fara dubashi su kuma suka jira a waje..babu yanda khalid da wani uncle din su Bobby mai suna Lukman basuyi da waziri kan suje waiting room ya zauna ba amma yaki haka yayita kai kawo a reception cikin tsananin tashin hankali kai kace Attahir dinshi ne na asali baida lafia...after like 15 mina doctor ya fito daga dakinda yake..tun kafin ya karaso inda suke waziri yayi saurin juyawa yana dubanshi cikin tashin hankalin dake karuwa a tareda shi yace"ya jikin nashi?.."a nutse doc yace"ya samu bacci yanxu"..waziri yace"amma meyake damunshi?.."daga kafada yayi before yace"well da akwai tests daya kamata a mashi amma dole saiya tashi daga bacci..for now dai few examinations da nayi masa ya tabbatar mun da cewa yana tareda damuwa snn da akwai mgn da yake kokarin fada ban gane me yake nufi ba..ina ganin idan akwai mahaifi ko mahaifiyarshi a kusa ya kamata a kirasu ko su zasu fahimci me yakeso ya fada"..sbd tsabar tashin hankali waziri har wani jiri yaji ya daukeshi kaman zai fadi..uncle lukman dake bayanshi yayi saurin tareshi yana fadin"Dan Allah Baffa ka kwantar da hankalinka..zai samu lafia inshaAllah"..girgiza kanshi yakeyi cikin tashin hankali...bayaso ya rasashi kmr yanda ya rasa mahaifinshi..gani yake kaman wani abu zai faru dashi..ganin halinda ya shiga doctor yace u shiga dashi ciki shi kanshi yana bukatar hutu a yanzu..ba musu suka shiga dashi inda Bobbyn yake kwance..kujera ya samu ya zauna snn ya dubi khalid dake tsaye kusada uncle lukman yace"ka koma gida ka taho da Nadia yanxun nan..kace ma Munubiya da Sumayya suma ina son ganinsu a nan"..da sauri khalid ya juya ya fita don tahowa dasu din...uncle lukman ya karasa ciki ya zauna shima ya zubama Bobbyn ido yana kallo kmr yanda waziri ma ke kallonshi...yana kwance kan gado hannayenshi dafe da forehead dinshi..numfashinshi na fita da sauri dalilin haka chest dinshi keta sama da kasa...kana ganin yanda face dinshi ke a yatsine zakasan ba dadin baccin yakeji ba...bayan 30 mins khalid ya dawo asibitin tareda su Mummy kmr yanda Waziri ya bukata...a rikice suka shigo dakin gaba daya su ukun musamman aunty sumy da Aunty Munubiya duk a figirce suke kmr ance rasuwa yayi Bobbyn..Mummy kuma tayi kokari sosai wajen 6oye tashin hankalin da ta shiga na ganin halinda Bobbynta ke ciki sbd presence na waziri da kuma qanin mahaifinshi a wurin...karasawa ciki tayi ta zauna tana duban waziri kafin tayi mgn ya rigata"likita yace Attahiru na tareda damuwa..kinada masaniya akan abunda ks damunshi?.."shiru Mummy tayi tana tunani..duk dunia dai tasan damuwar Bobby guda daya ne kuma shine Lamido...amma ya kamata ta fadama waziri ba tareda sanin takamaiman dalilinda ya jefashi cikin wnn halin ba?..muryan waziri ya dawo da ita daga tunaninda take..yace"idan kinsan wani abu na damunshi ki fadamin..banaso shima in rasashi kmr yanda na rasa mahaifinshi"..ajiyar zucia Mummy ta sauke kafin tace"eh to da akwai wata yarinya da nasan yana sonta saidai ban saniba ko sanadinta ne ya fada wnn halin"...shima ajiyar zucia ya sauke kafin yayi mgn Bobby yayi wani irin mosti da saida gadon da yake kwance akai ya motsa...da sauri suka yi kanshi gaba dayansu kowa na kiran sunanshi amma sai sukaga ya sake komawa yacigaba da baccin..bakinshi ne ya fara mosti alaman yana cewa wani abu dan haka Aunty Munubiya ta kai kunnenta daidai bakin nashi amma bata fahinci abunda yake cewa ba..ganin hawaye ya faro zubowa daga cikin idanunshi dake rufe waziri yace Mummy takai kunnenta ita ko zata fahimci me yake fada...ba musu kuwa ta kara kunnenta a bakin nashi still itama bata ji me yake cewa ba..ga kuma idanuwanshi a rufe suna fidda hawaye sai kuma legs dinshi da suka fara mosti suma yanzu...hannunshi ta kama tareda zaunawa nan gefenshi ta shiga murza hannun nashi tace"Bobby.."da sauri ya bude idanuwanshi tamkar abunda yake jira knn..sake matsawa tayi kusada fuskanshi tana dubanshi tace"meya sameka?..me kakeso kace?.."lumshe idonshi yayi yayi kokarin dakatar da hawayen dake cikowa idonshi snn ya damke hannunta dake cikin nashi muryanshi na fita da kyar yace"bata sona Mummy"..dakatawa yayi hawaye na sake antayowa fuskanshi kafin yacigaba da cewa"mutuwa zanyi Mummy..wlh duk ranan da ta auri wani mutuwa za..."kasa karasawa yay sbd kukan Mummy daya cika dakin..mikewa yayi zaune da sauri yana kokarin goge mata hawayen yace"Mummy am sorry plss..ki bar kuka dan All.."still ya kasa karasawa sbd ganin sauran jama'an dake dakin..wara ido yayi yana kallonsu sosai..idonshi na tsayawa kan waziri yayi kasa da kanshi da sauri yana sauke numfashi da sauri da sauri...karasowa waziri yayi Mummy ta bashi wuri ya zauna nan kusada dashi shima ya kama hannunshi snn ya dubeshi fuska ba yabo ba fallasa yace"wacece ita Attahir?..wace yarinya ce kake neman kashe kanka sbd ita?.."runtse ido Bobby yayi yana salati shknn asirinshi ya gama tonuwa..baiso waziri yaji mgnr nan ta haka ba..so yayi ya sameshi yayi mishi bayani in person bayan sun daidaita da ita amma she ruined everything..tun jiya daya fahimci da gaske bata sonshi bai sake samun kwanciyar hankali ba..gani yake shknn ya rasata wanda damuwar hakan ya sanya mashi zazza6i da ciwon kai wanda baya ko tantama blood pressure dinshi ne ya hau..ganin yayi tsit baida niyyar mgn Waziri ya janyoshi jikinshi ya rungume ya shiga shafa bayanshi a hankali yace"ka fadamin 'yar gidan waye kuma a wane gari take?..nayi maka alkawarin duk inda take a fadin dunia ni da kaina zanje in nema maka aurenta"..lumshe ido yayi ya bude yanajin yanda zuciyarshi ke tsananta bugu still ya kasa cewa komai saida waziri ya sake cewa"Attahiru"..snn ya hadiye wani yawu daya cika mashi baki from no where yace"a..nan..Gombe take"..dagoshi waziri yayi daga jikinshi yana mishi duba irin na mamaki yace"Gombe?..wnn Gomben da muke ciki?.."gyada kai Bobby yayi idanunshi na kallon kasa yace"eh.."waziri ya sauke wani ajiyar zucia kafin yace"kaga faduwa yazo daidai da zama knn..fadamun 'yar gidan waye a Gombe take neman zautar min da abokina haka?.."ya karasa mgnr cikin sigar wasa sbd yayi cheering dinshi up..su Mummy dai suna daga gefe sun zama yan kallo a tsakaninsu...waziri ya sake kama hannunshi yace"ka fadamun waye mahaifinta a Gombe?.."saida ya runste ido snn ya iya bude baki yace"Col Ahmad Lamido"..wani irin tsit dakin yayi kmr babu masu rai a ciki...waziri da yayi dif shima yana kallonshi kallonda ya kusan sa zuciyar Bobby ya buga sbd wasu abubuwa da zuciyarshi ke saka mishi gameda kallon..lumshe idonshi yayi kmr daga sama yaji waziri yace"Ahmad Lamido fa kace"..a hankali Bobby ya gyada mishi kai..cikeda wani mamakin waziri ya kuma cewa"Lamido dai wnn Adnan Lamido nawa?"..nan ma kai ya sake gyada mashi...lokaci daya wani annuri da farin ciki suka mamaye fuskan waziri...hannu ya budawa Bobbyn shi kuma ya shige jikinshi ya rungumeshi yana sakin murmushi yace"yanzu akan jinin Lamido kake wahalar da kanka haka?..kasan alaqar dake tsakanina da Lamido kuwa?..shi kanshi Ahmad din mutumin mahaifinka ne sosai kafin Allah ya kar6i rayuwarshi"..dagowa Bobby yayi yana dubanshi da murmushi ya gyada mishi kai alaman ya sani..waziri daya kasa dena murmusawa yace"baka saniba Attahiru..daka sani da baka tsaya kana wahalar da kanka kan jinin Lamido ba domin kaima ahalin Lamido tamkar ahali yake a wurinka"...wani irin hamshakin dadi Bobby yaji yana saukan mishi from no where...ya kama duk hannayen waziri ya rikesu gam cikin nashi voice dinshi na rawa yace"yanxu..zan iya..samun..aurenta?.."tun kafin ya rufe baki Waziri yace"da izinin Allah zaka samu..nasan Lamido bazai taba hana jinin Waziri jininshi ba"..wani irin runguma Bobby yayi mashi yana fadin"nagode sosai Baffa Allah ya saka da alkhairi Allah ya kara girma"..waziri na shafa bayanshi yana cigaba da smiling yace"Ameen Ameen Attahiru..Allah ya jikan mahaifinka"..duk suka amsa da Ameen kafin ya dago yana sake duban waziri murmushin fuskanshi na raguwa yace"amma fa bata sona Baffa..da bakinta ta fadamin hak.."bai karasa ba waziri ya rufe mashi baki yana fadin"karka damu wnn a wurin Allah yake..nidai zanyi magana da Lamido da zarar mun koma gida"..gyada kai ya shigayi new tears na cikowa idonshi na farin ciki yace"Allah ya baka aljannah"...waziri ya amsa da Ameen snn yace khalid yaje ya kira doctor..ba musu ya juya ya fita su Mummy kuma har yanxun suna tsaye kowa tana goge hawaye tana kuma sakin murmurshi at the same time..musamman Mummy da take ganin Allah ne ya amsa addu'anta.
Doctor na zuwa ya danyi gwaje gwajenshi kafin yace"da akwai stress a tareda kai so ina ganin zamu ajiyeka a nan for 1 or 2 days sbd ka samu enough rest"..yana rufe baki Bobby yace"don't worry i will take care of myself amma ayi discharging dina dan Allah"..kallonshi likitan keyi kafin yayi mgn Aunty Munubiya tace"he is a medical doctor"..tana rufe baki waziri yace indai yana ganin bai isa ayi discharging dinshi ba kada ya sallemshi har sai ya samu lafia...doctor yace ba damuwa zaiyi discharging din nashi sai ya dinga zuwa gida yana dubashi..yayi prescribing drugs da zaiyi amfani dasu ya bashi snn yayi discharging nashi yace zasu iya tafiya...a hankali yake takawa sbd jikinshi da baijin karfinshi kwata kwata...motan waziri ya shiga suma su Mummy suka shiga wanda aka kawosu snn suka bar asibitin...suna zuwa gida Aunty Munubiya ta hada mashi ruwa ya shiga yayi taking shower ya fito yasa kaya snn aka kawo mashi abinci...kasa cin komai yayi sbd shifa har yanzun hankalinshi ba kwantawa yayi ba sbd rashin sanin takamaimai halinda ake ciki...shin zai samu auren nata ne ko bazai samu ba?..shin zata hakura ta aureshi dukda bata sonshi ko bazata hakura ba..a soyayyan da yake mata shi gani yake ko bata sonshi matukar zata yadda ta aureshi he's ok..kawai yayi feeling kanshi cikin gida daya da ita ma ba karamin abu bane a wurinshi so muddin zata zauna dashi ko bata sonshi he won't complain...haka ya kasa taba komai cikin tarin abincin da aka jere a gabanshi saida waziri ya shigo da waya a hannunshi yace yayi sauri ya gama cin abincin sai ya kira Lamido ya fara sanar dashi abunda ke da akwai kafin yaje har gida ya sameshi...nan da nan kuwa ya shiga tunkuda abincin Aunty Munubiya na kallonshi tana mishi daria...yana gamawa waziri ya kira Lamido a waya as he promised saidai har wayan ya gama ringin baa daga ba..ya sake Kira nan ma no answer dan haka ya jiye wayar yace zuwa anjma zai sake kira kilan yana wani uzuri ne don dai yasan matukar babu babban uzuri ba yanda za'ayi ya kira wayar Lamido har sau biyu ba tareda ya dauka ba.
A daidai lokacinda Waziri ya kira wayar Lamido shi kuma yana tareda daddy da bai jima da dawowa ba yana sanar dashi mgnr da Aysha sukayi da Amminta daxu na cewa wani wanda yake son aurenta yanaso yazo ya gana dasu...tunda daddy ya fara mgn Lamido yayi shiru yana sauraronshi har saida yakai aya snn ya numfasa yace"ka gama?.."a hankali daddy dake zaune nan kasa yace"na gama Baffah"..Lamido yace"to koma waye kace mata ta sanar dashi ba sai yazo ba"..da mamaki sosai daddy ke duban mahaifin nashi saidai baice komai ba...Lamido daya daure fuskanshi yace"saboda nayi mata miji"...sake dukar da kai daddy yace"Allah yasa hakane yafi alkhairi"..Lamido yace"Ameen..gobe idan Allah ya kaimu inaso ka kawomin ita Aishan da Maimuna inason mgn dasu"..cikeda ladabi ya sake fadin"InshaAllah za'a kawosu..Allah ya kara girma"..Lamido ya sake cewa"Ameen..kana iya tafia"..ba musu daddy yayi sallama dashi snn ya tashi ya fita...har ya isa gida bai dena tunanin mgnr da Lamido ya fada ba..ko waye mijin da yayi mata oho?..abu daya dai ya sani shine Lamido bazai ta6a yi mata za6en tumun dare ba don haka tun ma kafin yasan waye yayi na'am dashi domin sanin halin Lamido da kalamu waheed..zaiyi wahala ya fadi mgn kuma daga baya ya dawo ya canza ta..fatanshi dai bai wuce Allah ya daidaita kansu da Aysha ba don yasan muddin aka ce za'a aura mata mutuminda bataso za'aga tashin hankali..Aysha da kan abunda baikai ya kawo bama take kuka balle kuma wnn daya shafi rayuwarta na gaba..ai saidai Allah ya dorashi kanta kawai idan bahaka ba kam za'a ga rashin hankali.
Koda ya koma gida sai ya kasa sanar da Ammi yanda sukayi da Lamido..kawai yana tunanin itama bai zama lallai taji dadin hukuncin na Lamido ba amma ya zaiyi?..bashida yanda zaiyi ne kmr yanda suma basuda yanda zasuyi dan haka ya zama musu dole su kar6i koma waye Lamido ya za6a mata da hannu bibbiyu...Ammi ta lura yana tareda damuwa kuma jikinta ya bata akan mgnr da yajema Lamido dashi ne..bata tambayeshi ba'asi ba saida dare yayi ta shigo dakin nashi cikin shirin bacci kmr yanda ta saba...daddy najin shigowarta yayi saurin rufe ido sbd tayi zaton yayi bacci amma abunda bai saniba shine duk wani 6oye 6oyenshi Ammi ta riga ta fahimci akwai damuwa a taredashi damuwan kuma baya rasa nasaba da batun auren Aysha da sukayi da Lamido...saida ta bari ya gama gyara kwanciyarshi shi bai yadda ba bacci yake snn a hankali tace"daddy.."daddy ya runtse ido yana addu'ar Allah yasa bata gano me yake 6oyewa ba kuma bai amsa mata ba...sake kiran sunanshi tayi still ba amsa dan haka takai hannu ta yaye duvet daya rufe dashi cikin raunin murya tace"wace mgn ce wnn da bazaka iya fadamun ba har kake baccin karya daddy?.."sake runtse ido yayi yana salati..Maimunatu badai fahimta ba..yanxun duk wnn 6oyewan da yake saida ta fahimci akwai wani abu a tattare dashi?..kasa cewa komai yayi sai mikewa da yayi zaune yana kallonta...kallon nashi itama take cikin sanyin murya tace"ka sanar dani abunda kw faruwa dan Allah..me Baffa yace?.."kallonta kawai daddy yake yana mamakin kwakwalwa irin nata..no wonder gaba daya yaransu sukeda brain especially Aysha data dauko komai da komai irin nata..itama bala'in kwanya gareta...kama hannunta yayi yana kallon cikin idonta yace"ki kwantar da hankalinki Maimunatu..ba wani babban abu bane"..tun kafin ya rufe baki tace"da wnn abun da kake yana sawa inyi tunanin babban abu ne daddy..kawai ka sanar dani ya kukayi da Baffa?.."ajiyar zucia ya sauke kafin yace"naje mishi da mgnr Aysha kmr yanda kika fadamin saidai tun ban karasa ba yace ace mata ta fada mashi ba sai yazo ba don yayi mata miji"..ya karasa mgnr cikin sanyin murya...dan murmushi Ammi ta saki tana kokarin 6oye dan rudanin data shiga tace"yanxu akan wnn mgnr kaketa 6oye 6oye bakaso ka sanar dani daddy?.."sake kama hannunta yayi yana dubanta da kyau yace"nasan Lamido bazai taba zaba mata mijin da bai dace da itaba saidai ina tsoron yanda ita Aishan zata dauki mgnr..kinsan halinta"..murmushi Ammi ta kara saki a kokarinta na ganin ta kwantarwa da mijinta hankali tace"wnn baikai dalilinda zai saka damuwa ba daddy..Ayshan nan fa 'yarka ce..da kai da ita kuma duk kuna karkashin Lamido ne so ya zama mata dole tayi mashi biyayya kmr yanda kaima ya zama maka dole"..kallonta daddy keyi yanajin wani irin sanyi a cikin ranshi...yaji almost 70%na damuwar da yake ciki ya gushe sbd maganganun nan nata..shiyasa dai ake cewa mace ta gari jin dadin rayuwa domin komai arziki da mulkin mutum matukar bashida mace ta gari bashida jin dadin rayuwa..duk wnn abunda take yasan itama baza'a rasa ko yayane dan damuwa a tareda ita ba amma ko kusa bata nuna mashi ba..yasan kuma koda za'a aura mata wanda bataso bazata ta6a bude baki tace mishi bataso ba ko kuma ta nuna wani alama da zai tabbatar da hakan...mace ce ita mai tsananin kara musamman akan Aysha data kasance 'yar fari..wnn dabi'un nata yasa a kullum sonta ke zama sabo fil a cikin zuciyarshi..bashida burinda ya wuce yaga ya faranta mata kmr yanda itama bata gajia da faranta mishi...(ubangiji ka azurta duk wani miji na gari da samun mata ta gari🙏🏻sisters kuce Ameen😂).
The following morning tare sukay breakfast gaba daya a dinning dake nan parlor which is so unlike them..zaiyi wahala daddy da Ammi suyi breakfast tare dasu mostly su biyu sukeyin abunsu a can parlon daddyn...Aysha dai sai baza ido da kunne take tana jira taji yanda Ammi sukayi da daddy amma bataji komai ba..so take taji shin Ammi tayi masa mgnr ne kuma ya sukayi da Lamido?..baby gaba daya ya daga mata hankali sai rigima yakey mata wanda batasan sanda ya koya ba..kawai duk yabi ya sata cikin rudani itada takeso ta gama FCNM snn ta tafi abroad tayi furthering karatunta kmr yanda sukayi da daddy shine yanzun yake 6ullo mata da mgnr aure...Allah ya gani itadai ba shiryama auren nan tayi ba kawai ta yadda ne don batada yanda zatayi dashi...har suka gama breakfast dinsu ba wanda yace mata uffan hakan kuma yasa tasha jinin jikinta...Najeeb ne ya mike yayi sallama dasu snn ya fita tareda Husna da Yusra da zaiyi dropping nasu a islamiyya da sukayi resuming yau shima kuma ya wuce wajen aikinshi...itama Aysha mikewa tayi zata bar dinning din daddy ya kira sunanta...gabanta yayi wani irin faduwa na ba gaira babu dalili kafin ta juyo a hankali tana kallonshi tace"na'am"..ba tareda ya kalli inda take ba yace"kije ki sako hijab dinki yanxun nan kizo zamuje wajen Lamido"...wara idanu tayi gabanta na sake faduwa jin abunda ya fada..tabbas tasan akwai wata a kasa..babu yanda za'ayi ace ta shirya aje wajen Lamido a irin wnn lokacin..Innalillahi kawai take furatawa a ranta ta kasa ko mosti..Ammi da taga tayi wani tsaye kmr bada ita ake mgn ba tace"wai badake ake mgn bane?..wane irin iskanci ne wnn?.."juyawa tayi da sauri tana fadin"sorry Ammi"snn ta shige dakinsu...daddy ya mike daga dinning din yana duban Ammi cikin sigar wasa yace"fadanki ya fara yawa fa Maimunatu..inajin yanda kullum kike samun yara a gaba kina musu fada kawaici nakeyi maki"..mikewa tayi itama tana murmushi tace"yaran naka ne ai basajin mgn musamman ita wnn da har yanxu ta kasa fahimtan cewa itace babba"...murmushi kawai ya sakeyi ya wuce zuwa parlonshi tana mara mishi baya...car keys dinshi ya dauka itama Ammi ta zura hijab snn suka fito tare...daidai lokacin itama Aysha ta fito sanyeda katon hijab dinta har kasa...ficewa sukayi daga gidan daddy ya mikama Ammi makullin motar ba musu ta kar6a ta bude musu ya shiga front seat Aysha kuma ta shiga baya sai ita Ammin ta shiga driver seat..dama haka yake bai cika daukan driver zuwa gidan Lamido ha sai dai idan daga can zai wuce aiki bazai dawo ta gidan ba..itama Ammi duj zataje da kanta take driving kanta tareda yaran...motar shiru har suka isa gidan Lamido ba wanda yayi mgn cikinsu...a tare suka bude mota suja fito snn suka nufi entrance din gidan...daddy ne yayi sallama Lamido ya bashi izinin shiga snn suka shiga makeken parlon nashi...as usual yana zaune kan kujera yana kallonsu har suka karaso duk suka zauna a kasa snn suka fara gaisheshi..amsawa yayi cikin dattako da kamala irin nashi kafin yayi shiru yana kallonsu kmr bazaiyi mgn ba sai can kuma yace"Maimuna mgn ce nakesonyi dake"..kai a kasa Ammi tace"ina sauraronka Baffah"..yace"ina fatan Ahmad ya sanar dake yanda mukay dashi jiya"..kai ta daga tareda fadin"ya sanar dani"..Lamido yace"MashaAllahu...yanxu meye shawaranki akai?.."da sauri tace"ai ni banida wani shawara face bin umarninka Baffah..duk hukuncin daka yanke daidai ne Allah yasa haka shi yafi alkhairi"..cikin murmushin jin dadin kalamanta yace"to Madallah Maimuna Allah ya maki albarka"..ta amsa da"Ameen Ameen"..shiru dakin ya sakeyi kafin Lamido ya tsayar da idonshi kan Aysha da taji wani hadadden tashin hankali ya risketa yanxun nan..haka nan jikinta ya bata wnn kiran na Lamido bana lafia bane..gashi sai wani mgn sukeyi a kunshe ta kasa gane me suke cewa...ganin yanda duk tabi tayi tsuru tsuru tana rarraba ido Lamido ya saki murmushi wai tunma kafin taji mgnr da zai fada nata knn..dama yasan zaisha rikici ba dan karami ba da yarinyar nan amma saidai ko mutuwa zatayi bazai canxa mgnrshi ba..cikin muryar daya kusa sata fitsari yace"Aisha"..a firgice ta dago kai tana kallonshi har hawaye sun fara ciko idanunta..Lamido bai damu da hawayen nata ba yacigaba da mgn"kin turo mahaifinki jiya akan mgnr wanda kikeso koh?.."da sauri ta gyada mishi kai kmr mara hankali..Lamido yace"Alhamdulillah to inaso ki sanar dashi cewa ni Lamido na dade dayi maki miji"..wani irin zare idanu tayi tana kallonshi kmr bata gane me yace ba...ganin haka Lamido ya sake daure fuska yanda bata isa ta kawo mashi wargi ba yace"kinji abunda na fada ko in sake maimaitawa?.."nan take ta dawo daga suman zaunen da tayi hawaye suka shiga sauko kan fuskanta tace"na..ji"..yace"MashaAllah saiki kirashi ki fada mashi"..sake gyada mashi kai tayi hawaye na sake tururuwar zubowa fuskanta...har wani sarawa taji kanta nayi sbd tsabar tashin hankali..tunda take zata iya ranstuwa bata ta6a tsintar kanta cikin tsananin tashin hankali irin wnn ba..me Lamido yake nufi da yayi mata miji ne wai?..yanxu yana nufin bazata auri baby ba?..kuma waye shi wnn mijin da yayi mata?..lokaci daya ta kasa daurewa ta saki wani irin kuka tareda dora hannunta a kai kmr wanda uwa da ubanta suka mutu..shknn tasan ta riga ta gama yawo domin Lamido bazai ta6a canxa mgnrshi ba..abune wanda tasan ya zamar mata dole ta auri za6in da yayi mata amma shin waye wnn za6in nashi?..meyasa tun tuni bai ta6a furta yayi mata miji ba sai yanxu?..meyasa saida ta kawo wanda takeso Lamido zaiyi mata haka?..kuka takeyi wiwi tamkar wanda ta rasa iyayenta..Lamido sai yayi relaxing kan kujeran da yake yana kallon yanda take kuka kmr ranta zai fita..ganin haka daddy ya daka mata tsawa yana cewa"Aysha bakida hankali ne zaki tasa mu gaba kina mana kuka haka?..so kike ki nuna ba'a isa dake bane ko yaya?.."da sauri ta hau girgiza kai har yanxu hawaye basu dena ambaliya kan fuskanta ba ko mgn ta kasayi.
Jama’a wa kuke ganin Lamido ya za6a a matsayin mijinda zata aura..Bobby ne?..ko kuma wani ne daban?..🙄
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
43
Kuka takeyi sosai cikin tsananin tashin hankali da rashin sanin tudun dafawa...yanxu wnn mgnr na Lamido na nufin auren dole za'ayi mata knn?..yanxu suna suna nufin ta rabu da baby knn?..innalillahi wa inna ilaihi rajiun...bude baki daddy ya sakeyi da nufin yayi mata masifa sai Lamido ya daga masa hannu alamar he shouldn't say a word..ba musu yaja bakinshi ya rufe yana kallonta..Ammi dama tana zaune ko kai bata dago ba balle tayi mgn...kallonta Lamido yayi fuska a daure ya sake kiran sunanta...ta dago tana kallonshi hawaye nata sintiri kan cheeks dinta...murya a dake yace"anyi maki wani abun ne kikema mutane kuka?.."shiru tayi kai a kasa..a fusace Lamido yace"ba mgn nake maki bane?.."girgiza kai ra shigayi da sauri tana runtse idanunta...yace"to kan wane dalili zaki zauna kina mana kuka?..ko kinga abokin wasanki a nan wurin,?.."nan ma kai ta sake girgiza alamar babu..yace"then wipe off those tears tun kafin raina ya 6aci..kika bari na sakejin kukanki kuma zakiga matakin da zan dauka"..tsit tayi tana toshe baki da hannayenta...shi kuma ya zuba mata ido har saida ta goge hawayen tas snn ya juya yana duban daddy yace"Ina Najeeb yake?.."kai a kasa daddy yace"yaje wajen aiki"..Lamido baiyi mgn ba sai wayarshi daya dauka nan kusa dashi yayi dialing number Najeeb..yana fara ringing Hamma Najeeb ya dauka da fadin"barka da safiya"..Lamido yace"barka dai..kana ina yanxu?.."Najeeb yace"ban dade da shigowa office ba"..yace"to ka dauki excuse ka dawo gida inason ganinka yanxun nan"..da sauri yace"Baffa lafia kuwa?.."katse wayarshi Lamido yayi bayan yace"ka hanzarta ba zaman jiranka zamuyi a nan ba"..su daddy dai na zaune sunajin me yake cewa amma ba wanda yace uffan...zaman kurame suka shigayi a parlon har Najeeb ya karaso...waje Lamido ya nuna mashi kusada Aysha ya zauna snn ya sake daure fuska yanda zai dauki mgnr da zai fada da muhimmanci kafin ya nuna Aysha da hannunshi yace"fadamun ya kake da wnn yarinyar?.."kallonta Hamma ya juya yayi snn ya dawo da kallonshi ga Lamido cikeda mamakin tambayar...cikin tsawa Lamido yace"bada kai nake mgn bane?.."da sauri yayi kasa da kanshi kafin yace"qanwata ce ita"..Lamido ya sake cewa"qanwarka kawai?.."juyawa Hamma ya sakeyi ya kalli su daddy snn ya kuna juyowa ga Lamido yaga yanda ya tsareshi da ido sai yace"kuma tanada sunan Mamana"..duk yanda Lamido yakai da daurw fuska saida mgnr nan ya bashi daria..wai tana sunan mamanshi..amma wnn yaro Najeeb ba dan karamin soko bane...hatta su daddy saida mgnr ya basu daria kuma duk basu kawo komai a ransu ba saida Lamido yace"to itace wadda na za6a maka matsayin matar da zaka aura kamar yanda kaima kaine na za6a mata matsayin mijinda zata aura"..wani irin diff dakin yayi kmr anyi ruwan sama an dauke...daddy da Ammi syka shiga kallon kallo dan ba wanda tunaninshi yazo nan wurin...Aysha kuwa wani irin darammm taji gabanta ya fadi ta shiga zare ido kmr wata zakanya ta juya tana kallon Hamman da shima idanunshi ke kanta yana zare ido...relaxing Lamido yayi yana kallon yanda suke kallon kallo a tsakaninsu..daga reaction dinsu ya fahimci mgnr a bazata yazo musu...har yanxu kuma parlon tsit an rasa mai kwarin guiwar da zai fara mgn cikinsu...baki Aysha ta bude zata sake rushewa da kuka Lamido ya daka mata wani tsawan da batasan sanda ta kankame Najeeb dake zaune kusada ita ba...ba shiri ta hadiye kukan tsaf tana cigaba sauke numfashi gamida rarraba ido kmr shege a rabon gado...wani shiru dakin ya sake dauka kafin Lamido ya juya yana fuskantar su daddy yace"Ahmad ko baku fahimci mgnr dana fada bane?.."daddy ta hadiye wani yawu daga bakinshi kafin cikin karfin hali yace"mun fahimta Baffa..kuma munyi na'am da haka ubangiji ya sanya alkhairi a ciki"...kasaitaccen smile Lamido ya saki ya dubi Ammi ita yace"kema kin amince Maimuna?.."har yanxu kanta na kasa tace"na amince..Allah ya tabbatar da alkhairi"..wanu murmushin Lamido ya kara saki kafin yace"Allah ya maku albarka"..suka amsa da Ameen snn ya sake juyawa ga iyayen gayyar wato Lamido da Hammanta...idanunshi ya tsayar kan Najeeb da yake ganin komai dake faruwa kmr a faraki yace"daga yau inaso ka fara daukanta matsayin matar da zaka aura ba wai qanwa ko mai sunan Mamanka ba..kema kuma ki tabbata kin bashi wnn matsayin don ko mutuwa daya daga cikinku yayi sai an daura wnn auren..kuje na sallameku"...mikewa Hamma yayi da kyar ya juya zai fita daga parlon Lamido yace"dawo ka tafi da ita"..ba musu ya dawo tareda durkusawa ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye snn ya shiga janta kmr mara lafia suka fita daga parlon...juyawa yayi wajen su daddy yace"kuma kuna iya tafia Allah ya maku albarka"..bayan sun amsa da Ameen duk suka mike suka sake mishi sallama zasu fita Lamido yace"Ahmad ka tabbata ka fada masu suyi kokari su fahimci junansu kafin ta gama makaranta don wnn aure ko mutuwa nay banaso a fasa yinshi"...gyada kai daddy yayi before"zanyi kokari in Allah ya yarda..mun barka lafia"..daga haka ya juya yabi bayan Ammi suja fita daga parlon...basu samu su Aysha nan compound ba hakan ya nuna musu cewa kilan sun wuce gida dan haka shima ya bude nashi motar suka shiga wnn karon da kanshi ya jata suka bar gidan...a hanya Ammi tayi tsit ta kurawa waje daya ido tana tunani...gangarawa gefen titi yayi yai parking tareda jama hannunta ya rike cikin nashi...ta juyo da sauri tana kallonshi sai kuma ta sakar mashi smile dinta me kyau...kallonta yakeyi da damuwa yace"kiyi hakuri Maimunatu"..Ammi ta dan wara ido tana dubanshi tace"hakurin me kuma?.."yace"nasan bai zama lallai kiso wnn hadin nasu ba amma inaso kisan babu yanda zamuyi da Lamido tunda ya riga ya furta"..hannunshi itama ta rike tana sakin murmushi tace"ko kusa bana kin auren Aysha da Najeeb wlh..kawai mgnr ne yazomin a bazata kasan ban ta6a kawo a raina wai shine mijinda ya za6a mata ba...Najeeb yaron kirki ne mu muka raineshi sbd haka babu wanda ya dace da auren Aysha idan bashi ba..nasan zai riketa da kyau kuma zai iya bida ita a hankali sbd rashin jinta"...ajiyar zuciya daddy ya sauke yana kallonta da murmushi..gaskia Maimunatu matar arziki ce...da wnn maganganun nata sai yaji duk kokwanton da yake akan batun ya gushe..tabbas shi kanshi yasan Najeeb yaro ne mai hankali kuma bayada wani mugun hali da za'a hanashi aure sbd shi..dadin dadawa kuma danshi ne domin shi ya rikesh tun yana dan karami kuma kmr yanda ta fada zai iya da Aysha sosai sbd ya riga dama yasan halinta ciki da bai so basu da damuwar komai...tayar da motar yayi suka karasa gida kowa ranshi fess dan Allah ya gani sunyi na'am da wnn za6in na Lamido...a parlor suka iske Najeeb din zaune ya buga uban tagumi ga kukan Aysha daya karade dakin gaba daya...yana jin shigowarsu ya mike da sauri ya isa garesu yana cewa"dan Allah daddy babu yanda za'ayima Lamido ya janye mgnr auren nan?.."kallonsh duk su biyun sukeyi kafin su hada baki wajen cewa"baka sonta ne?.."wani irin kunya yaji ya rufeshi dajin tambayan nasu...shaf ya manta fa iyayenta ne and suna iya jin babu dadi idan ya nuna bai sonta..amma shi harga Allah ba kinta yake ba kawai abun ne yazo mishi unexpected sai kuma wnn uban kukan da take sai kace ance za'a aura mata dodo...girgiza kai ya shiga yi da sauri yana nuna kofar dakinsu yace"kawai..banaso ayi mata dole ne..rufe kanta tayi fa a daki taketa kuka daddy kada wani abun ya sameta"..kama hannunshi daddy yayi suka karasa cikin parlor suka zauna snn yace mishi"indai don wnn ne ka kwantar da hankalinka ai ka riga kasan yanda take dama..wnn kukan koma waye akace zan za6a mata sai tayishi so wnn kar ya dameka ko kadan..kawai kacigaba da addu'a"..kai kawai ya iya gyadawa cikin ranshi yana jinjina kalar darun da za'ay da ita don yasan dole ne sai tayishi wlh...mikewa yayi bayan yayi musu sallama ya koma wurin aikinshi yayinda Ammi ma ta shiga kitchen shi kuma daddy yai zaune a parlon yana sakawa da kwancewa..fatanshi kawai Allah ya daidata al'amura kada azo ana samun matsala...Aysha kuwa tana daki tanata rizgar kuka ba wanda yabi ta kanta don a cewarsu idan ta gaji dan kanta zata dena kuma zata bude kofa ta fito ko don yunwar cikinta
kuwa.
A hankali ya bude idonshi daga nannauyan baccin daya daukeshi as a result of drugs dinshi da yasha..duba yakai ga agogon dakin yaga it's almost five dan haka ya sauka daga gadon da sauri ya fada bathroom yayi alwala ta fito snn ya tada sallah yana jin haushin rashin tashinshi da sukayi har time din sallah ya wuce...yana idar da sallah Sab ya shigo dakin yana dubanshi yace"waziri yace wai ya jikinka?.."mikewa yayi daga inda yayi sallahn yace"da sauki..muje"..tare suka fita zuwa parlon waziri shi da Sab din...yana ganinshi ya saku murmushi tareda furta"jiki yayi kyau knn?.."murmushi shima Bobbyn ya sakar mishi har suka karasa ciki..nan kusada wazirin ya zauna yana dubanshi da murmushi..so yake ya tambayi ko sunyi mgn da Lamidon amma baisan ta yaya ba...bayan waziri ya sallami baqin dake tare dashi ya shiga duban Bobby fuska da murmurshi sosai yace"zaka iya rakani wani waje yanxu?.."a hankali Bobby ya daga mishi kai alaman zai iya..waziri ya maida dubanshi ga Khalid dake zaune parlon shima yace"kaje kace a fitomin da mota"..ba musu khalid ya juya ya fita shi kuma waziri ya mike tsaye tareda kama hannun Sab yace"kaima muje kayi mana rakiya mai sunana"..a tare suka fita duk su ukun zuwa motarshi da har an fito da ita...makullin motar ta kar6a daga hannun driver dinshi ya mukawa Sab yace yayi driving dinsu...ba musu Sab ya amsa key din dukda cewa baisan kan garin sosai ba...ya bude driver seat ya shiga su kuma suka shiga baya snn ya tada motar suka fita daga gidan...saida suka hau babban titi Waziri yace"zaka iya gane Gra?.."a hankali Sab yace"da kyar zan gane gaskia"..gyada kai waziri yayi yace"to muje zanyi directing dinka"..haka kuwa Sab yaja motar suna tafe yana nuna mishi hanya har suka shigo Gra...suprise yakeso yaima Bobby shiyasa bai sanar mishi inda zasuje ba..yaso ace yareda uncles dinsu sukazo amma bazai iya jira har su dawo daga aiyukansu ba shiyasa yaga gwara ya fara zuwa shi kadai suyi mgn gemu da gemu da Lamido inyaso daga baya sai su sake dawowa tareda 'yan uwan mahaifinshi don kawo dukiyar aure...waziri nacigaba da nuna ma Sab hanya har suka iso Lamido's Palace...wani irin bugu zuciyar Bobby yayi da yaga an rubuta The Lamido's 6aro 6aro a can saman gate din estate din...duk fadin Gombe kuma yasan Lamido ne kadai mutuminda yayi suna da sunan sosai dan haka ba tareda wani tantama ba brain dinshi ya fada mashi cewa wnn estate dinsu Lamido ne...lumshe ido yayi tareda jingina da kujera knn hakan na nufin Waziri zuwa yayi suyi mgn da Lamido?..wani irin faduwa gabanshi ya sakeyi daya tuna cewa fa tayi bata sonshi..yanxu idan sukaje ta sake tozartashi tace bata sonshi fa?..hankalinshi yaji ya tashi har wani zufa ya faraji na ba gaira babu dalili amma yayi kokari bai bari waziri ya fahimta ba har aka bude musu gate suka shiga ciki...tafia sukayi ba wani mai nisa da yawa ba suka karaso gidan Lamido...daga nan waje Sab yayi parking motar snn duk suka bude suka fito...suka sanya waziri a tsakiya suka shiga cikin gidan...daidai entrance suka hadu da wani brother din daddy ya fito daga parlon Lamido yana ganin Waziri yayi saurin dunkule hannu tareda risinawa yana fadin"Allah ya taimaki Waziri...barka da zuwa"..Waziri ya amsa da"barka dai Mahmoud..ya iyali?.."Mahmoud Lamido yace"suna lafia lau Waziri..a fito lafia"..Waziri ya gyada mishi kai yana murmushi..sai a snn Bobby da Sab suka gaishe da mutumin snn sukabi bayan Waziri zuwa cikin parlon...Lamido na ganinsu ya fadada murmushin fuskanshi yace"Waziri ne a tafe?.."Waziri daya karasa ciki ya zauna kan one of kujerun dake parlon yace"wlh nine Lamido"..Lamido yace"to barka da isowa"..Waziri yace"yauwa..ga jikokinka nan na kawo makasu har gida"...kallonsu Bobby Lamido yayi yana cigaba da murmushi yace"yaran Attahiru koh?.."Waziri ya gyada mash kai shima yana murmushi...Bobby ne ya fara gaisheshi kai a kasa sai Sab shima ya gaisheshi...bayan gaisuwa Waziri yace"jiya na kira wayarka ai"..Lamido yace"na gani wlh..lokacin ne ina tareda Ahmad kan batun auren 'yarsa daya taso shiyasa banga kiran naka bama sai daga baya"..waziri na gyada kai yace"ikon Allah watace zatayi aure cikin yaran nashi?.."Lamido yace"babbar ce wai ta turo a sanar dani wani dake neman aurenta yanaso ya turo shine nace ta dakatar dashi dan na riga nayi mata miji tun tuni"...wani irin faduwa gaban Bobby yayi kirjinshi sai up and down yake fatanshi bai wuce Allah yasa ba akanta ake mgn ba...shi kanshi waziri zuwa yanxu gaban nashi faduwa yake yace"wacce daga cikin yaran wai?.."kai tsaye Lamido yace"Aisha mana..ina wnn yaro Najeeb?.."Waziri yace"dan wajen marigayi Auwal koh?.."Lamido yace"yauwa to shine wanda na za6a a matsayin mijin nata..kasan ubanta shi ya rike Najeeb din kuma nasan ba wanda zai iya zama da ita sai shi shiyasa na tarasu na fada musu ko bayan raina ban yadda a fasa wnn auren ba"...wani irin tari ne ya sarke Bobby kaman wanda ya kware da wani abun...hankalinshi yakai kololuwar tashi har wani zufa ya faraji all of a sudden ga kuma coughing da taketa faman yi non stop..nan take hankalin Waziri ya tashi shima..Sab ya rikoshi yana yana shafa bayanshi amma kmr tunzurashi suke don cough din sai karuwa ma da yayi...da sauri Waziri ya mike yana duban Sab hankali a tashe yace"kamoshi muje asibiti"...Lamido ya mike shima yana dubansu yace"ina zuwa"..daga haka ya shiga wani corridor dake nan cikin parlon..bayan few minutes ya fito rikeda goran zamzam da akayima addu'a a hannunshi..yana karasowa ya bude tareda kafa goran a bakinshi nan da nan kuwa ya shiga shan ruwan kaman an aikoshi...saida tasha almost half snn ya cire baki tareda yin kasa da ido yana sauke numfashi...hawaye ne sosai suke cikowa idonshi amma bayason su zubo...bayason ko waziri yaga wnn tears din sbd ya gaji da zubar da hawaye a gabansu...zuciyarshi wani irin rauni tayi mashi wanda bata ta6ayi masa irinshi ba...kokari yake sosai na ganin ya 6oye abunda yakeji amma abun yaci tura sbd bashi keda control din kanshi ba...runtse ido yayi yana maimaita innalillahi a cikin zuciyarshi har yanxu kuma bai denajin hadadden zufa na lullu6eshi ba...kallonshi Lamido yake cikeda mamaki yace"meya sameshi ne haka?.."Waziri ne yayi karfin halin cewa"dama baida lafia don daxun aka sallamoshi daga asibiti..ina ganin zamu tafi kawai a sake maidashi can"...da sauri Lamido yace"a maidashi gaskia don wnn tarin nashi bana lafia bane..Allah ya baka lafia Attahiru"..ya karasa mgnr referring to Bobby dake dafe da chest dinshi da hannu daya dai kuma daya hannun ya dafe head dinshi da yaketa jujjuyashi from side to side...Sab har ya fara hawaye shima a haka ya kamashi zuwa inda yayi parking mota..bude baya yayi ya sashi ciki snn yayi saurin zagawa zuwa driver seat Waziri kuma ya shiga baya suka tafi...kai tsaye asibitin da suka baro daxu ya shiga nuna masa suka maidashi.
Aysha kuwa yini tayi daki tana kuka ba wanda yabi ta kanta saida su Husna suka dawo..sune sukaita tambayanta meya faru amma ta kasa ko bude baki balle tayi musu bayani...ganin abun nata bana kare bana kare bane gashi har dare zaiyi bata fito taci abinci ba daddy dake parlonshi ya kira Ammi yace mata"Maimunatu je ku duba yarinyar can don Allah..wnn kukan da take ai saiya haifar mata da ciwon kai"..ajiyar zucia Ammi ta sauke Allah ya sani itama tun daxu takejin kmr taje ta rarrashi kayarta amma sbd kara irin nasu na fulani kasa zuwa tayi...yanxu kuma da daddy yayi mgn da kanshi ko musu batayi mashi ba ta kama hanyar dakin nasu...su Husna na zaune sun sanyata tsakiya tana fada musu cewa Lamido ne yace zai hadata da Hamma Najeeb aure..Husna da bataga wani abun tayar da hankali a mgnr ba tace"to Adda wnn ne abun kuka kuma?..Hamman da kinfi kowa sanin halinshi ne kike kuka sbd zaki aureshi?..ai murna ya kamata kiyi ma"..Husna na rufe baki Ammi data shigo dakin tace"Husna kuje parlor ku jiramu zamuyi mgn"..ba musu Husna ta kama hannun Yusra suka fita...suna fita Ammi ta zauna nan kusada ita tareda kama hannunta ta rike kafin tace"ki tsayar da kukan nan mgn zamuyi"..ba musu takai hannu tana share hawayenta...Ammi na dubanta da kyau tace"bakya son Najeeb din ne?.."da sauri ta shiga gyada mata kai alamar eh..janyota Ammi tayi ta rungume a jikinta tana shafa bayanta tace"to ki dena kukan nan indai baso kike kisama kanki ciwon kai ba..so nake ki kwantar da hankalinki zamuyita addu'a inshaAllah idan ba alkhairi bane Lamido da kanshi zaice ya janye mgnr"..luf Aysha tayi jikin mahaifiyar tata tana sauke numfashi..wato dai duk dunia babu inda ake samun irin wnn nustuwan sai wurin uwa...hankalinta taji ya dan kwanta unlike daxun da take ganin duk tashin hankalin dunia a kanta ya kare...kawai har yanxu ta kasa picturing itada Hamma matsayin mata da miji...jin yanda tayi tsit Ammi ta dagota daga jikinta tana sake rike hannunta tace"kinji abunda na fada maki koh?.."gyada kai tayi a hankali Ammi tace" yauwa kuma banaso shima Najeeb din kice zaki nuna masa wani abu..kucigaba da mu'amalarku kmr da inshaAllah indai ba alkhairi bazaki aureshi ba"..sake gyafa kanta tayi tana fatan Allah yasa ba alkhairi din...mikewa Ammi tayi itama ta mikar da ita tsaye tana cewa"muje to kici abinci..haka nan yau duk kinbi kin dorama kanki damuwa ko abincin bakici ba"...daga haka Ammi ta shiga janta suka fita daga dakin..Lamido dai mamaki fal cikin zuciyarta na ganin yanda Ammi take lalla6ata yau..anya kuwa ba kofar rago ake shirya mata ba?..tasan dai yanda Ammi take da zafi zaiyi wahala tazo ta rarrasheta haka kawai...sai kuma wata zuciyar tace mata kilan sbd tasan ba'a kyauta mata bane shiyasa take haka...ko su Husna dake zaune parlor abun ya basu mamaki ganin Ammi rikeda hannun Addarsu har dinning...ba wai Ammi bata sonta bane no kawai dai basu cika jituwa bane sbd halayen Ayshan da kusan gaba daya basu mata ba..ga kuma kasancewarta 'yar fari shiyasa abun ya hade mata biyu amma yau ga Ammi rikeda hannun 'yarta sai sukay kaman wasu qawaye...daddy daya fito don tafia masjid ya hangosu a dinning Ammi na kokarin serving dinta sai ya saki murmushi hade da girgiza kai snn ya fita daga gidan...Maimunatu sarkin kara yau an ajiye karar a gefe knn...yaji dadin yanda yaga Ayshan har ta dan sauko shiyasa akace dai duk fadin dunia mutum baida wanda ya wuce mahaifiyarshi...babu wanda zai soka kaman ita haka kuma babu wanda zai ji tausayinka ya kuma damu da damuwarka kamar mahaifiyarka...itace zata soka kilan fiyema da yanda kake son kanka..(Rabbi ya sakawa iyayenmu da alkhairi ya basu aljannah).🙏🏻
Saida Ammi ta tabbata taci abincin da yawa snn tace taje tayo alwala ta sameta dakinta...ba musu ta wuce dakinsu tayi alwalan snn ta fito..su Husna suma duk alwalan sukayi snn suka wuce bedroom din Ammi kamar yanda tace musu su sameta a can...a tare sukayi sallahn nasu gaba daya bayan sun idar Ammi tace duk su sa 'yar uwarsu a addu'a idan akwai alkhairi tsakaninta da Najeeb Allah ya tabbatar idan kuma babu Allah ya kawo mafita..Aysha dai sam ba wnn addu'an takeso ayi ba tafiso kawai suce Allah ya kawo hanyarda fasa auren inyaso sai kowa Allah ya hadashi da alkhairin nashi a gaba...zata iya hakura da auren baby amma bazata iya auren Hamma da take mishi kallon dan uwanta da syka fito ciki daya ba.
Washegari ta tashi da dan dama dama don batayi kuka ba kwata kwata saidai yawan tunani...tun jiya taje tunanin yanyar da zatabi wajen sanar da Prof halinda ake ciki amma ta kasa...hakan yasan ta sanar da Ammi ita kuma tace idan daddy ya dawo fada mashi sai ya kirashi da kanshi yayi mashi bayani sbd kada ma yayi zaton ko yaudaranshi zatayi...da wnn shawara na Ammi ta dan samu nustuwa amma dukda haka tana tunanin halinda bawan Allahn nan zai shiga duk ya samu labari...daddy na dawowa Ammi ta fada mishi yanda sukayi yace ta kawo numbershi ya kira da kanshi suyi mgn..ba musu ta bashi number nashi snn ta zauna nan parlon daddy ya kira number...yana dagawa daddy yace shine mahaifin Aysha sai kuma ya dora da fadin yanda sukayi da Lamido kan batun zuwa neman aurenta da yace zaiyi...hankalinshi ya rashi sosai wanda hatta daddy saida yaji tausayinshi...ya kwantar mashi da hankali tareda cewa sucigaba da addu'a idan Allah yayi akwai rabo a tsakaninsu zasu auri juna idan kuma babu rabo sai kowa ya rungumi kaddara...Aysha dai na zaune tana sauraronsu tanajin tausayinshi na kamata sosai..bawan Allah dama tasan zai shiga mawuyacin hali...nasiha daddy ya sake mata snn yace ta tashi ta tafi Allah ya mata albarka.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
44
A hankali Bobby ya bude ido daga nannauyan baccinda ya daukeshi as a result of alluran bacci da aka bashi...a take maganganun Lamido suka shiga dawowa kwanyarshi..."shine wanda na za6a mata a matsayin miji..ko bayan raina ban yadda a fasa wnn auren ba"...wnn words zai iya cewa tunda yake bai ta6ajin words da suka tayar mishi da hankali kamarsu ba..kalmomi ne marasu yawa a baki amma tabbas yasan sunada nauyin da zasu iya tarwatsa duk wani farin ciki da yayi saura cikin rayuwarshi...kalmomi ne dake kokarin nesantashi da macen da yafi so duk dunia idan aka dauke Mummy...hakan kuma yana nufin rabuwa da ita na har abada..runtse idonshi da yaji har wani yaji yake mishi sbd tsabar tashin hankali..har yanxun heart beat dinshi bai dawo daidai ba..yanxu shknn Lamido aure zatayi ta barshi?..sake runtse ido yayi zafin da idonshi keyi na karuwa kuma ko alamar hawaye babu a cikin idon..wato shi kanshi kuka ma rahama ne..kawai the taught of her getting married to someone yasa yaji another zazza6i yana son rufeshi...dama tun farkon ganinshi da Najeeb din nan yaji bai kwanta masa ba ashe shine wanda zai zama silar rabashi da ita..dukda ba sonshi take ba yana fatan watarana zata soshi and now Lamido yayi ruining komai...Mummy ce ta shigo dakin tareda Aunty Munubiya da basket din abinci a hannunta..Waziri kuma tin daxun doctor yace a maidashi gida because yana bukatan hutu shima if not yana iya faduwa sbd damuwan daya daurama kanshi..dole haka ya hakura ya koma gidan don shi kanshi yasan idan bai samu hutun ba kaman yanda likita yace yana iya komawa gidan jiya..gaba daya yaron ya tsaya mashi a rai matukar tausayinshi yakeji..ashe dama har yanxun ana samun irin wnn soyayyar?..shikam wane taimako ya kamata yayima yaron nan matsayinshi na kaka kuma waliyyinshi?..wane kokari ya kamata yayi don ganin ya samu wnn jika ta Lamido daya kwallafa rai a kanta?...Mummy na isa ta zauna nan kusada shi tareda kamo hannunshi ta rike cikin nata kawai ta shiga binshi da ido...a hankali yasake bude idonshi a kanta kafin ya kuma maidasu ya lumshe muryanshi na fita da kyar yace"mu..koma gida..Mummy pls..i don't want to stay here anylonger"..damke hannunshi Mummy tayi hawaye na ciko idanuwanta tace"zamu tafi..amma first ka fara kwantar da hankalinka ka samu sauki tukunna"..tun kafin ta rufe baki ya shiga girgiza kai still idonshi a kulle yace"bazaki ganeba Mummy..aure za'a mata..aure zatayi ta barni..kakanta yace ya za6ar mata miji Mummy bazan iya cigaba da zama garin nan ba mu koma kano please!."kuka ne sosai yaci karfin Mumny dake rikeda hannunshi ta kasa cewa uffan...Aunty Munubiya kanta saida kwalla ya cika mata ido..karasawa tayi kusa dashi bayan tayi dropping basket dake hannunta tace"dama sbd ita kazo Gombe ba sbd grnadfather dinka ba?..kana tunanin idan kuka tafi yanxu waziri zaiji dadi ne?.."mikewa ya shiga kokarin yi zaune da sauri Mummy ta taimaka mashi ya jingina da pillow..har yanxun ya kasa bude idanunshi don yana budewa zafin da yakeji cikinsu ke sake karuwa..yakai duk hands dinshi ya dafe forehead dinshi dasu cikin muryanda ke nuni da tsagwaron damuwar da yake ciki yace"Aunty bazan iya zama ba..bazan iya zama bayan nasan zata auri wani ba"..yana rufe baki Aunty Munubiya tace"to idan ka koma kanon kana tunanin ka dena ganinta ne?..karewa ma naga a college dinka take karatu kuma hutu na karewa zata koma tunda ba gamawa tayi ba shima sai kace zaka bar college din sbd ita?..get a grip of yourself mana Bobby..be a man inshaAllah Allah bazai barka haka ba"...sauraronta kawai Bobby keyi without saying anything..bazasu gane bane..bazasu ta6a gane halinda yake ciki ba shiyasa duk zasuyi wnn maganganun...a yanda yakejin zuciyarshi yasan dab take da samun matsala shi kuma baison yacigaba da zama yana dorawa Waziri damuwa kada hakan yayi sanadin da hawan jininshi zai sake tashi...gaba daya Gomben ta fita a ranshi and matukar ba komawa Kano yayi ba yana iya samun matsala...da za'a taimakeshi a cireta daga college din ma shi da yafi mashi yanda idan ya tafi ya dena ganinta kenan for good...sake komawa yayi ya kwanta zuciyarshi na cigaba da bugawa da gudu...Mummy takai hannu tana shafa uban gashin kanshi da bai cika askewa ba tace"ko tea bazaka sha ba Bobby?.."gyada mata kanshi yayi alamar bazai sha ba..da sauri Aunty Munubiya tace"aa ya kamata kaci wani abun gaskia..doctor yace kafin medication ya zama lallai kaci abinci"..banza kawai yayi da ita idonshi rufe don gani yake bazata gane halinda yake ciki ba...da kyar da sidin goshi suka samu yasha tea din snn ya sake komawa ya kwanta before time din medication.
Washegari ma haka ya tashi ba walwala dukda cewa fevern da yakeji ya sauka amma har yanxun bai dena ciwon kai da jiri ba...tunda ya tashi baiyi mgn ba duk yanda aunty sumy taso yace wani abu kin kulasu yayi sai binsu da yake faman yi da ido kmr bai sansu ba..fuskan nan nashi kuwa a tamke kamar na shanu shi kadai yasan abubuwan da yakeji a cikin ranshi...da yamma sai ga Lamido yazo dubash tareda daddy da baima san yana garin ba saida Lamido yace yazo ya rakashi duboshi...mamaki sosai ya kama daddy ganin yanda ya koma cikin lokaci kankani dukda cewa a haka kokari yake yaga bai nuna musu asalin damuwar da yake ciki ba..da yake sun samu waziri a asibtin basu suka tafi ba sai dab da magrib...daddy na zuwa gida yace Ammi ta shirya ita dasu Aysha yanaso Najeeb ya kaisu asibiti su dubo jikinshi a daren...haka kuwa duk suka shirya suka fita inda Hamma ke jiransu...tana ganin shine a motar ta wani hade rai tana muzurai..baice mata uffan ba ya bude motar Ammi da su Husna suka shiga baya aka barta a tsaye alamun ita suke nufi ta dhiga front seat knn...budewa tayi ta shiga tana wani kumbura kamar kububuwa..shikam Najeeb daria ma abubuwan nan nata suke bashi wlh...wai shi Maama takema wnn iskancin kawai sbd ance za'a hadashi aure da ita...ya tada motar suka tafi kuma har sukaje asibiti ba wanda yayi mgn cikinsu sai Yusra daketa damun Ammi da tambaya kaman 'yar jarida...bayan ya gama parking Ammi ta bude mota ta fita yaranta sukabi bayanta...itama hannu takai zata bude yayi saurin danna lock yana kallonta...juyawa tayi tana dubanshi fuskan nan a kwa6e tace"Hamma meye haka?..ni ka budemun mota in fita"..tana gama fadin haka sai kuma ga hawaye ya shiga silalowa kan fuskanta shidai yayi shiru yana kallonta baice komai ba...kamar wanda aka tsikara ta dago tana kallonshi tace"Hamma wai dama kana sona ne?..meyasa Lamido ke cewa zai hadani aure dakai?..dan Allah Hamma kayi wani abu bazan iya auranka ba wlh"..matsawa kusada ita ya kamo hannunta yana cewa"ki nustu mgnr da zamuyi knn amma ki tsaida kukan nan first"..ba musu ta hadiye ragowar kukan tareda kai hannu tana goge hawayenta...saida ya tabbata ta dena kukan snn yace mata"haka kika tsaneni dama ban sani ba?.."da sauri ta hau girgiza tace"ni ban tsaneka bafa"..yace"idan ba tsanana kikayi ba meye wnn?.why kike bani attitude sbd ance zan aureki?.."langabar da kai tayi tana dubanshi a hankali tace"Allah ban tsaneka ba Hamma..kawai ban ta6a picturing kaina matsayin matarka ba..kallon dan uwa na jini nake maka Hamma ba kallon mijina ba"..sake kama hannayenta yayi ya rike shima yana dubanta da kyau yace"na sani Maama..hasali nima kallon qanwata nake maki ba kallon matar da zan iya aure ba amma ya zamuyi?..idan kaddaranmu yazo a haka dole haka zamuyi hakuri mu kar6eshi tunda bamuda yanda zamuyi"..hawaye na sake taruwa idanunta tace"kai bakada wadda kakeso ne?.."shiru yayi yana kallonta kmr bazaice komai ba sai can kuma yace"inada..akwai wadda nakeso Maama amma bankai ga sanar da ita ba wnn mgnr na Lamido ya 6ullo"..da sauri ta sake rike hannunshi tace"then muyi mgn da daddy plss..ka fada mashi kaima kanada wadda kakeso nasan inshaAlla bazai rasa yanda zaiyi ba"..hannu yakai yana goge mata hawaye yace"naji i will think about it amma yanxu ki bari mu shiga muyi dubiyan nan tukun..kada su Ammi su gama bamu je ba"..da sauri ta shiga gyada kai tana karasa hawayenta tace"toh na dena"..murmushi ya sakin mata tareda bude motar ya fita itama ta fita suka nufi cikin asibitin...saida ta kira Ammi ta fada mata room number snn suka isa zuwa dakin...Najeeb ne ya fara shiga snn itama ta shiga kai a kasa...Bobby idonshi ke kallon kofa tun daxu yana jiran shigowanta kasa dauke idanunshi yayi a kanta..yanajin zuciyarshi tayi wani tsalle ta dire sbd ganinta da yayi tareda wanda yasan shi zai aureta baisan lokacinda ya runtse ido yana salati sbd zafin da yaji ba..ba kowa dakin sai shi kadai don haka Hamma ya kara karasawa kusa dashi yana dubanshi da murmushi yace"sannu ya jikin"..kai kawai Bobby ya iya daga mash ba tareda ko bude idonshi yayi ba..a yanda yakeji yasan tsaf zai iya kasa controlling anger dinshi na ganinsh da yayi tareda ita shiyasa ko idan yaji budewa balle yayi mashi kallonda zai jefashi tunani...Najeeb bai kawo komai ba a tunaninshi ko jikin nashi ne shiyasa daya gama dubashi ya juya ya fita daga dakin...wani irin shiru dakin ya dauka har suna iyajin numfashin junansu...kallonshi kawai take ganin yanda ya kara haske ga dan rama da yayi sai taga kaman karo mishi kyau akai don sosai taga yau dai yayi mata kyau...shiko bude idanunshi yayi jin har yanxu batace komai ba sai gashi karaf idanunsu sun sarke cikin na juna..da sauri ta dauke nata tana zare ido sbd wani irin abu da taji ya shiga cikin idanun nata har zuwa zuciyarta..bata taba jin irin wnn game dashi ba tadai san for sure idonshi na sata jin wani iri amma ba irin wnn feeling din bane kwata kwata...lumshe idon ya sakeyi kafin ya budesu fes a kanta yanajin kmr ya mike ya sanyata a jikinshi ko zai samu saukin wnn ja'iban da yake ciki...idanunshi sun kada sunyi jajir ga zuciyarshi daketa faman bugawa da mugun sauri...ido ya sake lumshewa yanajin yanda gaba daya ganin nata ya dirar mishi da wani kasala na musamman...wani irin weird feeling yakeji irin wanda bai ta6a ji a kanta ba...addu'a ya shiga karantowa a ranshi wai ko feelings din zasu ragu amma kmr sake hankado mishi su akeyi...sun dauki kusan mintina biyar a haka kafin ta karasa kusa dashi a hankali har yanxu bata bar kallon face dinshi ba tace"ina yini"..bai bude idonsh ba kuma bai amsa ta ba..ta sake cewa"Sir ina yini"..still bai amsa ba sai takai hannu ta dora kan nashi da nufi ta jijjagashi wai ko bai jita bane aikuwa ya kama hannun nata da sauri kmr magnet ya damke cikin nashi...wara ido tayi tana kallonshi da mamaki ashe idonsa biyu dan rainin hankain...kokarin kwace hannunta ta shiga yi nan take yaji wani karfi yazo mishi kawai sai ya mike zaune yana dubanta da idonshi da ya bata tsoro sbd jajir din da yayi...kallonta yakeyi cikin ido eyes dinshi na shinning as a result of hawaye da cikoshi..tunda abun nan ya faru sai yanxun tears suka samu damar zuwa idanunshi amma jiya sai zafi da idon suke ba hawaye ko kadan...kallonshi itama take tana karantar abubuwa da dama cikin idanun nashi wanda bata ta6a tsaiwa ta karance su ba ada..abubuwa ne masu wuyar karantuwa snn kuma masu wuyar fassaruwa amma dukda haka taji ta kasa dauke idanunta a kanshi...hawayen dake idanuwanshi yayi kokarin maidawa kafin yace"can..i hug..u plss?.."wara ido tayi tana kallonshi without saying anything..voice dinshi na rawa ya sake cewa"for this once Aysher plss..mutuwa zanyi"...lokaci guda itama hawaye suka ciko idanunta ba tareda tasan dalilin su ba...ganin kallon da take mishi ya janyota jikinshi tareda wrapping dinta da hannayenshi ya saki ajiyar zucia mai karfin gaske...tana iya jiyo yanda heart dinshi yake bugawa da mugun sauri nan take hawayen dake idonta suka gangaro fuskanta...Bobby ko wani irin sanyi yaji yana ratsa tun daga kwakwalwarshi har zuwa tafin kafafunshi..idanuwasnhi rufe yayinda hawayen dake ciki suka wanke mishi fuska..ji yake inama zasu dawwama a haka shikam daya gama samun komai na dunia...a hankali yayi breaking hug din tareda kamo fuskanta da hannayenshi ya hada da nashi fuskan still idanunshi rufe saidai ba hawaye yakeyi ba yace mata"ina sonki sosai Aysher..morethan any other thing..you are my whole world..my whole heart..you are my.."kasa karasawa yayi ya sake runtse ido sbd wani abu da yaji ya tokare mishi wuya..sake manne face dinshi yayi da nata yana kallon cikin idonta yace"i will die without you.. i will die for sure"..ya karasa yana sake lumshe ido at the same time yana sauke numfashi...Lamido kuwa kuka ta fara wiwi kai kace uwa da ubanta ne suka rasu suka barta a doron kasa...ita kanta kuma bazata ce ga dalilin kukan ba amma for sure tasan akwai tausayinshi sosai a cikin ranta...ta kuma san da gaske yana sonta fiyeda komai kmr yanda yace...sake rungumeta yayi yana shafa bayanta yace"sorry i made u cry...i just feel like saying what i have in mind but am sorry"..girgiza kai ta shigayi alaman ba reason din kukanta knn ba tace"aure za'ai min"..yace"i know"..tace"Hammana zan aura"..nan ma kai ya sake gyadawa yace"i..know"..a hankali ta bude ido tana kallonshi cikin sigar lallashi tace"am sorry"..yace"u don't have to..i forgave u already"..kai ta shiga gyadawa tana sakin smile da wet face dinta tace"thank u..thanks for loving me"..kallonta kawai Bobby keyi yanajn wani abu na zagayawa cikin jininshi and he couldn't help it saida ya kai lips dinshi goshinta ya manna mata peck a wurin snn ya saketa tareda komawa kan gadon ya kwanta yana fadin"thank you"...kallonshi ta tsaya yi tanajin wani bakon abu na zagayawa cikin jikinta...karasawa tayi kusa dashi idonta akan fuskanshi tace"Allah ya baka lafia..zan tafi"..kai kawai ya iya daga mata tareda dan sakin murmushi wanda baikai zuci ba...saida ta juya zata tafi ya bude ido yana kallonta har ta fita daga dakin snn ya sake lumshe idon tareda kai hannu yana dafe saitin heart dinshi dashi.
Kwananshi biyu a asibiti aka sallameshi a ranar kuma ya dage sai sun wuce kano waziri yace bazasu tafi a ranar ba.. dole suka bari the next day shima kuma bada son waziri ya bari suka tafi ba..ba yanda zaiyi ne kawai sbd yanda yaga Bobby ya daga hankalinshi ne amma da bazai bari su tafi ba musamman daya kasance har yanxu ba gama warkewa yayi ba...shi kuma yayi hakan ne sbd yanaso ya nesanta kanshi da ita and hakan bazai yiwu ba don idan yana Gombe jin kanshi yake yana kusa da ita amma idan ya koma kano zai samu sauki ya sani...idan ta dawo college kuma tsaf zai iya dena shiga makarantan ma gaba daya balle watarana ya ganta abunda yake kokarin 6oyewa ya tona masa asiri...da wnn shawara na zuciyarshi yayi na'am ya kumayi tawakkali tareda mika lamuranshi ga Allan don yasan shi kadai yakeda ikon canxa al'amura a lokacinda yaso.
Kwana biyu da tafiyarsu Aunty Munubiya da bata koma tare dasu ba ta shirya ta tafi gidan Uncle Lukman wanda yake mazaunin babba cikin 'ya'yan waziri tunda shi yakebin mahaifinsu Bobby...bayan sun gaisa dashi ya shiga dubanta da alamar tambaya yace"Munubiya lafia kuwa naganki gidane irin wnn lokacin?.."cikeda damuwa tace"wlh ba lafia ba Yaya Lukman..mgn ce nazo da ita akan Bobby"..shiru yayi yana kallonta kafin yace"to meya faru?.."a nutse ta shiga koro mishi bayanin kaunar da yakema jinin Lamido da yanda sukaje tareda Waziri akan batun neman aurenta sai kuma sukaji Lamidon da bakinshi yace ya riga ya tsayar mata da miji...tunda ta fara bayani yayi shiru yana sauraronta baice komai ba saida ta kammala yace"to yanxu me kikeso ayi Munubiya?..da bakinki fa kikace Lamido ne yace ya mata miji kuma a yanda nasan Lamido dai zaiyi wahala yayi mgn ya canxa musamman mgnr aure"...yana rufe baki tace"na sani amma bai kamata mu nade hannu mu kasa yin komai matsayinmu na 'yan uwan mahaifinshi ba...so nake dan Allah yaya Lukman kaje ka samu mahaifin yarinyar nan in person ka nuna bakasan da waccan mgn ta Lamido ba kace nemawa Bobby auren yarinyar kazoyi wata kila zai iya cewa ya hadaka da Lamido..daga nan nasan shi kanshi Lamidon zai sake nazari musamman idan ya kasance yarinyar ba son wancan auren take ba..ko don alaqar dake tsakaninshi da Waziri nasan zai iya janye waccan mgn da yayi"...shiru Uncle Lukman ya sakeyi yana sauraronta...tabbas gaskia ta fada amma shin zai iya kuwa?..gani yake kmr zasu fahimci drama suka shirya musu tunda ai Lamido yasan Waziri yasan da mgnr amma meye abunyi?.Allah ya sani shi kanshi yaji yana son taimakon yaron ko don ya samu damar goge tarin laifukan daya aikata musu a baya ciki harda kin amincewa ya nemosu bayan rasuwar mahaifinsu...yayi nadama sosai yanxu ya kuma ji gaba daya ahalin Attahir sun shiga ranshi matuka ko don sbd yanda basu nuna wani alama na har yanxu suna rike dasu ba dukda yasan zaiyi wahala ace sun manta duk abubuwan da suka aikata masu a baya...ganin yanda yayi nisa cikn tunani Aunty Munubiya ta sake lankwasa murya tace"dan Allah yaya Lukman ka taimakawa yaron nan a matsayinka na qanin mahaifinshi...ko don zumunchi ka daure kayi hakan bakasan tarin ladan da zaka samu ba"...ajiyar zucia ya sauke kafin yace"shknn zanje inshaAllah..zan fara bincikawa inji yaushe Ahmad din yake gida sai inje in sameshi"..nan take Aunty Munubiya ta shiga washe baki tana cewa"Allah ya saka da alkhairi yaya..Allah kuma yasa muji alkhairi"..shima yana murmushi yace"Ameen..duk yanda mukayi dashi zakiji"..tace"to shknn yaya..bari inzo in tafi Allah ya saka da alkhairi"...ya amsa mata da Ameen snn tayi mishi sallama ta tafi..cikin gida ta shiga wurin matarshi itama tayi mata sallama snn ta koma gidan waziri don gobe take shirin komawa kano itama dama ga dalilinda ya tsayar da ita nan.
Washegari around 4:30 Uncle Lukman ya iso gidansu Aysha bayan sunyi mgn da daddy ya tabbatar mashi da cewa yana gida...daddy ya bude kofar parlonshi ta waje ya shiga dashi nan ciki suka fara gaisawa...bayan gaisuwa kai tsaye Uncle Lukman ya fadi mgnr dake tafe dashi saidai bai 6oye mashi komai ba har yanda Lamido sukayi da waziri kan batun aurenta da Najeeb da kuma yanda shi Bobbyn ya shiga wani hali sbd jin mgnr auren nata...bayani sosai yake mashi dalla dalla kaman yanda ya samu labari wurin Aunty Munubiya...daddy kuwa rsabar mamaki kasa kwakwaran mosti yayi a wurin...gaba daya kanshi ya kulle knn all these while yaron nan yana sonta bai ta6a nunawa ba?..tausayinshi yaji ya kamashi matuka yaji inama yanada hanyar dazai taimaka mashi da yayi haka..inama ikon bayar da aurenta a hannunshi yake da ya bashi ita ko bataso saidai mgn a hannun Lamido yake ba hannunshi ba...har Uncle Lukman ya gama bayani tareda rokon idan akwai taimakon da zai iyayi don a samu sauyin al'amura ya taimaka yayi ko don a ceto rayuwar yaron...hankalin daddy ya tashi sosai ya kumaji tausayinshi ya kamashi fiyeda tunaninshi...yasan yaron baida matsala sam and yanada duk wani quality da iyaye ya kamata su duba wajen za6ama yaransu miji kuma zaifi kowa son ace ya hada jini da Mentor dinshi Col Attahir saidai hakan da kmr wuya tunda bai zama lallai Lamido ya tankwaru ba...hakuri yaba Uncle Lukman sosai tareda alkawarin zaiyi bakin kokarinshi yaga abunda Allah zaiyi saidai suci gaba da addu'a...har ya tafi daddy bai dawo cikin hayyacinshi ba...mamaki kawai yakeyi da har yake mata so irin wnn kuma ya iya 6oyewa har na tsahon lokaci haka...sosai yaji yana son hada zuri'a dashi a daya bangaren kuma yana tunanin shima Najeeb din idan sonta yakeyi fa?..itama kuma Ayshan wanda takeso daban shikam ya zaiyi ya kwance wnn kullin ne?..ya zaiyi ya daidaita al'amuran nan?.."kira Najeeb din zakayi ka tambayi ko shima yanada wadda yakeso"..amsar da wani sashe na zuciyarshi ya bashi knn nan take kuma yayi na'am da ita dan haka ya dauki waya ya dannawa Najeeb din kira yace lallai lallai yanason ganinshi idan ya dawo daga office.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata yafitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
45
Da dare misalin karfe takwas Najeeb yayi sallama parlon daddy kmr yanda yace yazo yana nemanshi...ya karaso ciki ya gaisheshi kafin a hankali ya kira sunanshi"Najeeb"..kai a kasa ya amsa da"Na'am"..daddy yace"tambaya ne nakeson yi maka amma inaso kayi alqawarin zaka fadamun gaskia"..still kanshi na kasa yace"nayi alqawari daddy"..daddy yace"so nake ka fadi tsakaninka da Allah kana son Aysha ko baka sonta?.."shiru Najeeb yayi kai a kasa as tambayar ya masa nauyi sosai..taya zai kalli tsabar idanun mahaifinta yace ba son aure yake mata ba..kai abun da kmr wuya...daddy kmr yasan tunanin da yakeyi knn yace"ka daukeni matsayin mahaifinka ba mahaifin Aysha ba..wata mgn aka zomun da ita mai girma wadda nake sa ran zata iya sa Lamido ya janye mgnr hada aurenku amma fa idan baka so..matukar kana so to ka fada nayi maka alqawarin ko bata sonka zata aureka"..kanshi ya sake dukarwa kasa murya can kasa yace"ni ba son aure nake mata ba daddy...sonta nake tamkar wadda muka fito ciki daya"..wani ajiyar zucia da baisan daga ina ya fito daddy ya sauke cikeda jin dadin wnn amsa ta Najeeb..yanxu dai yasan baya sonta sbd haka zai kai mgn direct to Lamido yaga ko Allah zaisa a dace...nan take ya sallami Najeeb ya tafi tareda ce mishi idan bukatar sake nemanshi ya taso zai kuma nemanshi...haka ya tashi ya wuce yana mamakin wane mgn ne yace ya taso mai girma kuma?..fatanshi dai Allah ya dorasu akan Lamidon ya bar kowa ya auri wanda yakeso.
Daren ranar daddy har sallahn dare yayi yana rokon Allah ya dorashi kan Lamido ya amince da mgnr da zaije mashi da ita..Ammi dai na kwance tana kallonshi har ya idar snn ta sake tambayanshi abunda ke faruwa...bai 6oye komai ba ya fada mata duk yanda sukayi da Uncle Lukman ya kuma fada mata yanda sukayi da Najeeb daxu..ita kanta Ammi tayi mamaki sosai jin wai sbd ita ma ya kwanta rashin lafia..bawan Allah ashe haka yake sonta ba'a sani ba...ita kanta zataso kasancewarshi sirikinta ko don yanda kullum daddy ke yabonshi yana fadar kyawawan dabi'unshi...tana duban mai gidan nata tace"amma daddy kana ganin Aysha tana sonshi kuwa?..naga wanda tace zai turo ai kmr bashi bane"..daddy yace"rabu da ita ko babu wnn mgnr ma bazata auri wancan din ba..wai ashe tsoho yarinyar nan taje ta dauko kusan age mate dina wai shi zata aura?.."wara idanu Ammi tayi da mamaki tace"u mean wanda tace zai turo din ba yaro bane?.."daddy yace"babban mutum ne wlh..wai sunanshi Professor Ahmad Kurawa"..Ammi tace"amma duk a ina ka samu wnn labarin?.."yace"Bilkisu na kira daxun..na kasa nutsuwa ne tun bayan mgnr mu da Alhaji Lukman sai na kira nace ta fadamun idan tasan wani abu tsakaninsu tace ita bata fada mata yace yana sonta ba ta kuma bani labarin shi wnn da takeso din"..ajiyar zucia Ammi ta sauke mai karfi tana fadin"wnn yarinya dai bansan irinta ba wlh..sbd rashin hankali duk cikin masu sonta ta rasa wanda zata kawo as wanda zata aura sai dattijo?..Allah ka shirya yarinyar nan"..daddy yace"Ameen..gobe in Allah ya yadda zan kai mgnr Attahir wajen Lamido muji ko zai hakura da wancan mgnr"..gyada kai Ammi tayi tana fadin"to Allah ya kaimu..Allah kuma ya tabbatar da alkhairi.
The next morning daddy ko breakfast baiyi ba ya tafi wurin Lamido..as usual ya sameshi tareda jama'a saida ya jira ya gama sallamansu tsaf snn ya matsa kusa dashi yana gaidashi...Lamido ya amsa yana dubanshi cikin mamakin abunda ya kawoshi wurinshi da sassafe haka..mostly sai rana ta farayi yake shigowa amma yau gashi da sanyin safiya...bayan shiru na wani lokaci daddy ya gama tattaro duk wani karfin halinshi kafin ya fara mgn kai a kasa"wata mgn ce dama ta kawoni Baffah"..Lamido yace"dama tunda na ganka wnn lokacin nasan akwai dalili..meke tafe dakai?.."kai tsaye daddy yace"akan batun auren yaran nan ne..kayi hakuri ba nufina inyi jayayya dakai ba amma wata mgn Alhaji Lukman Waziri yazomun da ita jiya wanda yasa nayi tunanin in sake kawota gabanka ko za'a samu maslaha"...kai Lamido ke gyadawa yace"ina sauraronka..wace mgn ce wnn?.."daddy yace"ina wnn yaro dan wajen Col Attahir marigayi?.."Lamido ya gyada kai alamar ya ganeshi..daddy yacigaba da cewa"shine wai ashe yake sonta..ya dade yana sonta fada ne baiyi ba sai yanxun..ranar da sukazo nan tareda waziri mgnr ce ta kawosu sai kuma suka ji cewa ka riga ka fidda mata miji..wnn dalilin nema yasashi rashin lafia har ya kwanta asibiti"..wani irin tsit Lamido yayi kmr baya dakin..tabbas biri yayi kama da mutum..shi kanshi yayi mamakin yanda yanayin yaron ya sauya lokaci guda..tausayinshi yaji ya kamashi meyasa Waziri bai sanar dashi ba?..ga kuma shi wancan yaron Najeeb ya zaiyi dashi?..bayan dogon tunani ya dawo da dubanshi ga daddy dake zaman jiran tsammani yace"shi kuma wancan yaron Najeeb ya zamuyi dashi"..da sauri daddy yace"saida na fara tuntu6arshi kafin na kawo mgnr gareka..ya kuma tabbatar mun da cewa akwai yarinyar da yakeso"...numfashi Lamido ya sauke kafin yace"idan Allah ya kaimu dare kazo mun da iyalan naka gaba daya"..cikeda farin ciki ganin ya kusa cin nasara yace"zan kawosu in Allah ya yadda..na barka lafia"...daga haka ya mike ya sake mashi sallama snn ya tafi...koda yaje gida ya sanar da Ammi yanda sukayi dashi ita kanta ba karamin farin ciki tayi ba..sai a lokacin ya samu yayi breakfast din da bai samu yayishi ba daxu.
A can Kano kuwa tunda suka koma Bobby bai sake walwala ba...shi ba mara lafia ba kuma shi ba lafiyayye ba gashi nan ne kawai..gaba daya duniar yake ganin tayi juyin waina dashi daga farin cikin da yake ciki kafin ya santa zuwa baqin cikin da yake ciku yanxu bayan sanin nata...bakin kokarinshi yakeyi wajen ganin bai bar ciwon da yakeji ya kwantar dashi ba amma ko Allah yasan ba karamin wahala yake ciki ba..rabonshi da samun isashshen bacci har ya manta...kullum idan ba sedative yasha ba bai iya yin baccin...yana zuwa hospital dinshi kullum saidai ba wani iya aikin yakeyi ba mostly idan yaje kwanciya yake shima yaji da kanshi...Mummy tayi fadan tayi nasiha tayi magiya kan ya dena dorawa kanshi damuwa amma kwata kwata ya kasa yakice abun a cikin ranshi...kawai imagining yake wai ga Aysha an daura mata aure da wani shikam yasan da kyar idan ba wnn ce ranarshi na karshe a dunia ba...shi kadai yasan halin da yake ciki sai kuma Nur daya fadama duk abunda ya faru...Nur yaji tausayinshi matuka sbd yasan yanda ya kwallafa rai a kan Lamido..ya kuma san irin son da yake mata ba gama garin so bane..so ne wanda zaiyi wahala ta samu maiyi mata irinshi a dunia indai ba iyayenta ba...so ne wanda idan ta kuskura ya su6uce mata to ta tafka babban asaran samun masoyi kamarshi...wnn dalilin yasa kusan kullum Nur na tare dashi tunda har yanxu students basu dawo hutu ba and suna dawowa clinical posting zasu wuce..shike kwantar mashi da hankali tareda assuring nashi cewa komai zaiyi daidai...jinshi kawai yake don yasan zaiyi wahala ace an fasa auren nata.
Yau da wuri ya dawo gida sbd ciwon kai da yake fama dashi...yayi nisa cikin tunani har bai lura dasu Mummy dake zaune a parlor ba kawai ya wuce flat dinshi...gaba daya suka bishi da kallo ganin har yanxu Bobby bazai dangana ya mika komai ga Allah ba...ko Sab da zai koma school wnn karon aunty sumy ce ta maidashi madadin shi da yake maidashi koda yaushe...gaba daya Mummy itama cikin tashin hankali take don ganinshi a wnn halin ba karamin daga hankalinta yake ba...mikewa tayi zuwa dakin nashi..yana zaune kan sofa ya zabga uban tagumi da hannayenshi har ta karaso ta zauna nan kusa dashi baisani ba saida takai hannu ta dafa shoulder dinshi ya dago da sauri yana kallonta...kallonshi takeyi itama kafin tace"so duk mgnn da nake fada maka baka dauka ba knn koh?.."ya wani kwabe fuska yana kallonta yace"Mummy to me nayi?.."tace"kaki ka mika lamuranka ga Allah mana..do u think wnn damuwan daka daurama kanka shi zaiyi sorting things out?..baka yadda da ikon ubangiji ba ne?.."hannayenta ya kama ya rike yana dubanta in a calm voice yace"na yadda da ikon Allah mana kawai zuciata ta kasa daukan rasata da nake shirinyi..inama kokari Mummy Allah kadai yasan halinda nake ciki..ciwo nakeji sosai a zuciata Mummy ban san me zanyi ya dena ba"..kama hannunshi tayi tana cigaba da kallonshi tace"na fada maka ka kwantar da hankalinka jikina yana bani cewa ita din matarka ce..idan Allah ya yadda kuma kai zaka aureta ba wani ba"..kallonta kawai yakeyi kmr bai gane me take fada ba..cikeda assurance ta sake cewa"yes..ina nan ina maka addu'a and bi'iznillah Allah bazaiki amsan addu'a na ba"..dan murmushi kawai ya saki without saying anything..gani yake Mummy na son kwantar mashi da hankali ne kawai amma taya al'amura zasu canxa bayan Lamido da kanshi yace ya tsayar mata da wanda zata aura...shidai fatanshi bai wuce Allah ya cire mashi ita daga zuciyarshi ba koya samu ya huta.
Zaune suke cikin parlon Lamido gaba dayansu kmr yanda ya bukata...Ammi,daddy sai Aysha da Najeeb..gaba daya suna zaune a kasa while Lamido da tun shigowarsu ya kasa cewa uffan yana zaune a usual seat dinshi...kawai tunanin ta inda ya kamata ya fara yake..kmr bazaiyi mgn ba sai can yace"Najeeb"..a hankali Najeeb da har yanxun kanshi ke kasa ya amsa mashi...Lamido ya gyara zama before saying"tambaya nake son maka kuma inaso ka bani amsa iyakar gaskiayarka"..a hankali ya daga kai tareda fadin"InshaAllah"...Lamido yace"shin akwai wadda kakeso kafin wnn mgnr ya 6ullo?.."shiru dakin ya dauka kowa na jiran yaji amsar da zai bada...ganin yanda yayi shiru kai a duke Lamido yace"ko bakaji abunda na fada bane?.."da kyar ya bude bakinshi yace"ina dashi"..Lamido yace"a ina take?.."shiru ya sakeyi ba mgn a fusace Lamido yace"idan ina maka mgn kanamun shiru zakasa in canxa ra'ayina wlh"..tun kafin ya rufe baki yace"kayi hakuri..a nan Bauchi take"..kallonshi duk sukeyi before Lamido ya sake cewa"Bauchi a ina?..bude baki fa zakayi kayi bayani don idan ba gamsuwa nayi da yarinyar ba bazaka aureta bane"..har yanxun shidai kanshi na kasa yace"sunanta Bilkisu Ibrahim Muqaddas..tare suke makaranta da Maama"...wani irin zare ido Lamido tayi kai kace wani mugun abu ya fada..lokaci guda fuskanta ya washe da murmushi cikin tsantsan farin cikin da taji ya diro mata all of a sudden tace"Hamma are u for real?..da gaske Billyna kakeso?.."dakatawa tayi da mgnr tareda matsawa kusa dashi sosai hadda su kama hannunshi tace"bani labari Hamma yaushe ka fara sonta?..ya akayi ma kana son Billy amma ban sani ba..Hamma dan Allah ka..."bata karasa ba Lamido ya daka mata wani tsawan da batasan sanda ta koma inda take ba da sauri tana rarraba ido..sam ta manta wai a gabanshi suke..farin ciki yasa ta manta da hakan jin wai Hamma da kanshi ne yakeson Billynta..knn hakan yana nufin tun tale tale yana son Billy basu sani ba..shin Billyn tasan yana sonta ta 6oye mata kmr yanda itama bata fada mata Proprietor na sonta ba ko kuwa itama bata san yana son nata ba..duk zaman wurin sai taji ya gundureta Allah Allah take su bar wurin ta samu ta kira Billy taji ya wnn batu yake...Lamido dai maida dubanshi ga Hamman yayi yana cewa"kace mene sunanta?.."a hankali ya sake cewa"Bilkisu Muqaddas"..Lamido yace"jikar Inuwa Muqaddas ce knn?.."kai ya gyada mishi..Lamido yace"to Alhamdulillah 'yar manyan Mutane ce ai..shi Alhaji Muqaddas din was a very goon friend of mine and zan tuntu6eshi da mgnr"..da sauri yace"ai bamu gama daidaitawa da ita ba"..yace"wnn duk ba matsala bane zanyi mgn dashi dai..Allah yasa albarka"..duk suka amsa da"Ameen"..daga nan kuma ya maida hankalinshi kan Hajia Indo mai gayya mai aiki..ta sake sinne kai tamkar tana gaban surkai dukda cikin ranta murna ce fal na jin wnn labarin na Hamma da kuma warware wnn auren da Lamido keson hadawa da akayi..she's super excited kawai sai murmusawa takeyi ita kadai kmr munafuka...ganin bata ma san kallonta yakeyi ba yace"Aisha.."da sauri ta dago tana kallonshi kmr mutumiyar kwarai..kofa ya nuna mata tareda fadin"kina iya tafia"..da sauri ta mike ta kama hanya zata fita tace"Nagode Allah ya saka da alkhairi"..Lamido baice mata komai ba har ta fita snn ya dawo da dubanshi ga Hamma yace"kaima kana iya tafia duk yanda mukayi da Muqaddas din zakaji"..kai a kasa shima ya mike tareda yi masa godia ya fita...ya rage daga daddy sai Ammi a parlon..Lamido na duban Ammi yace"Maimuna kin amince da mgnr dan wajen Attahir?.."kai a kasa tace"na amince..Allah yasa haka shi yafi alkhairi"..yace"to madallah zanyi mgn da wazirin anjima..ita kuma Aisha ina sane naki fada mata sbd nasan hauka zataimn..idan kunje sai ku mata bayani"..daria sosai mgnrshi ya basu haka suka mishi sallama suka fita suna sake darian mgnr daya fada...suna fita Lamido ya dauki wayanshi ya kira Waziri suka fara mgn.
dadi sosai daddy yaji da Allah ya sauya al'amura haka?..ya tabbata Attahir zai kasance miji na gari a gareta ko don son da akace yana mata.
Aysha na fitowa daga parlon ta shiga kiran number Billy bata dauka ba..sake dialing tayi tana tafiya tana fadin"Billy pick up the call mana..pick up pls"..har ya gama ringing dinshi Billy bata dauka ba ita kuma bata gaji da jera mata missed calls ba...Hamma Najeeb daya biyo bayanta da sauri ya karasa inda take kawai sai ji tayi ya fizge wayar daga hannunta yana kallonta...juyawa tayi tana dubanshi itama sai kuma ta saki murmushi tace"Hamma dan Allah mgnr daka fadama Lamido gaske ne?..da gaske Billyna kakeso?.."harara ya watsa mata mai kyau kafin yace"ban saniba..kiranta kikayi zaki fada mata kou?.."murmushi ta Kara saki tace"of course mana..so nake inji labarin komai in detail amma batayi picking call dina ba"..ta karasa mgn tana turo baki...hannu ya kai ya dan bugi bakin nata before saying"to ban aikeki kije ki fada mata ba dan itama ba sani tayi ba..idan kika barni da kaina zanje in sanar da ita when the right time comes"..kallonshi take tana murmushi sosai tace"to bazan fada mata ba Hamma..amma dan yaushe ka fara sonta?..does she loves u too?.."girgiza kai kawai yayi yana murmushi jin wai tambaya take if tana sonshi..sai kace ba yanxu yace mata bata ma san yana son nata ba shine take mishi wnn tambayan kmr ba itane ta dauke mishi wuta sbd ance zai aureta ba.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
46
Zaune suke office din Nur tun safe ya baro nashi office din yazo ya tasa shi a gaba shi baije yayi aikinshi ba kuma shima bai barshi yayi nashi aikin ba...kawai yazo ya mishi kwance a office kaman wani mara lafia...for the fifth time Nur ya sake cewa"kaga malam if zaman office din nawa ke maka dadi tell me insan inda dare yayi mun..haka nan kazo Kamin wani kwance office sai kace mara lafia"..banza Bobby yayi dashi kmr baiji abunda yace ba..Nur ya tsaya kallonshi cikeda takaicin wnn iskancin da yake mai...murmushin iskanci ya saki tareda fadin"dont worry nasan maganinka ai..da Lamido zanje in hadaka tunda yanxu naga duk dunia ba wanda kake jin mgnrshi kmr nata"..still Bobby banza yayi dashi idanunshi lumshe sai karkada legs dinshi yake..Nur ya mike tareda tattara papers daya baza kan desk dinshi ya dauki makulli da wayanshi snn ya kama hanya fita yana cewa"to in ka gama saika rufe office din..naga kaman kwana zakayi a ciki"..sai yanxu ya bude ido yana kallon Nur dake neman barin office din yace"wai meyasa bakada mutunci ne Nur..baka ga halinda nake ciki ba da zaka dameni da surutu?.."juyawa Nur yayi yana kada kanshi yace"nine ma Lamido da naki accepting soyayyarka zakazo har office dina ka faramun hayaniya..na tabbata ko ita da tayi turning dinka down bakayi mata irin wnn wulakancin ba sai ni daka gama rainama wayo..don't worry nasan maganinka"..dafe head dinshi yayi yanajin yanda wnn iskancin na Nur ke neman kara mashi tension kan wanda already yake ciki..wayanshi ne ya fara ringing ya dauka da sauri ganin Mummy ce yayi picking tareda kaiwa ears dinshi before yace"Mummy"..a daya 6angaren full of excitement Mummy tace"Bobby guess what?.."dan shiru yayi kmr me tunani kafin yace"Mummy kinsan am not a good guesser kawai ki fadamin"..murmushi ta kara saki before tace wani abu another kira ya sake shigowa wayanshi..dubawa yayi sai yaga Waziri dan haka da sauri yace"Mummy hang on for a minute plss..Waziri ke kira"..Mummy bata ce komai ba tayi hanging call dinta shi kuma yayi picking na waziri tareda fadin"Baffa barka da rana"...Nur da yaji ya ambaci waziri yayi saurin komawa cikin office din ya zauna nan kusa dashi ya tattara duk attension dinshi a kanshi yana son yaji me wazirin zaice?..cikeda farin ciki shima wazirin yace"barka dai Attahiru ya jiki ka?.."yace"na samu sauki"..waziri yace"to Alhamdulillahi haka akeso..Allah ya kara lafia"..Bobby ya amsa da"Ameen"..suka yi shiru na dan lokacin kafin waziri yace"wani albishir ne zanyi maka mai dadi wane tukuici zaka bani?.."dan murmushi Bobby ya saki jin abunda ya fada..to wane albishir ne wnn?..shifa gani yake a halin nan da yake ciki matukar ba cewa za'ayi an bashi auren Lamido ba ba wani albishir da za'ayi ya faranta mashi rai..kawai gani yake ba wani albishir ne da zai sashi farin ciki ba amma dukda haka bai gwale Kakanshi ba yace"duk abunda kakeso Baffah"..waziri yace"to an baka auren Aisha...yanxun nan muka yi Waya da Lamido yake sanar dani yanda akayi"...wani irin diff Bobby yayi kaman baiji abunda yace ba...meyasa waziri zaiyi playing mashi such an expensive joke?..why zaiyi wasa da zuciarshi akan lamari irin wnn..duk sai yaji ranshi ya 6aci yama rasa abunda zaice...jin yanda yayi shiru waziri yace"ko bakaji abunda na fada bane?.."a hankali ya kakalo murmushi tareda fadin"nasan da wasa kake Baffah"..da sauri Waziri yace"na ta6a maka wasa da irin wnn mgnr dama?.."shiru ya sake yi yana tunani lokacin daya wani bright smile yazo kan fuskanshi yana cewa"da..Allah da gaske kake Baffah?.."cikeda assurance Lamido ya sake fadin"da gaske nake wlh..yanxun Lamidon ya kirani muka yi mgn"...lumshe ido Bobby yayi ya bude yana jin wani irin sanyin dadi na cika zuciyarshi kawai sai ya shiga karanta duk abunda yazo bakinshi kmr wanda ya zauce...addu'a kawai yakeyi ba tareda ya bude ido ba kuma ba tareda ya ajiye wayan dake makale kunnenshi ba..banda murmushi ba abunda yake saki sai kuma bakinshi dake motsawa a hankali sbd addu'a da yake...Nur dake zaune yana kallonshi wnn smile da yake saki kadai ya isa ya fahimci dalilin hakan...lokacin daya ya bude idon nashi sbd mgnr waziri da yaji ya mike tsaye yana shafa gashin kanshi still bai dena murmushi ba yace " yanxu Baffa u mean ni zan aureta knn?..i can't believe this?.."murmushi waziri ya kara saki before saying"kai zaka aureta insha Allah sbd haka rashin lafia ya kare"..murmushi kawai yake saki yana gyada kai yama kasa bude baki yayi mgn...kawai mamakin yanda al'amari ya canxa yake..is this really happening ko kuma day dreaming yake?..a hankali ya zauna kan sofa dake nan kusa dashi bayan sunyi sallama da waziri ya sake lumshe ido yayi relaxing kan sofa din murya can kasa yace"i can't believe this?..Allah kasa ba mafarki nake ba"..Nur dake zaune yana kallonshi tasowa yayi daga inda yake ya karaso nan kusa dashi ya zauna yana dubanshi da murmushi shima yace"ba mafarki kake ba Dr Bobby..it's reality..Lamido dai ta kusa ta zama matarka congratulations to u"..tun kafin ya rufe baki Bobby yayi mishi wani runguma cikin excitement yace"i still can't believe this Nur..Anya ba mafarki nakeba?.."Nur yace"i told u ba mafarki kake ba da gaske ne..Allah ne ya amsa addu'anka"..dagowa yayi yana kallonshi har yanxu bakinshi kaman go at auduga yace"Allah Alhamdulillah..Alhamdulillah Rabbi am forever grateful"..yana gama fadan haka kuma ya mike tareda zura wayanshi a aljihunshi yace"lets get going I need to talk to Mummy about this"..Nur baice komai ya mike bayan ya day car key dinshi suka fita daga office din...Motan Nur suka shiga don dama da ita suka zo..kai tsaye ya kama hanyan gidansu kmr yanda Bobby yace..ko a hanya Bobby bai dena hamdala ba..kawai gani yake Allah yana matukar sonshi daya canxa mgnr aurenta a lokacin da ya gama giving up..gaskia ne da masu iya mgn suka ce duk wani tsananin yana tareda sauki kmr yanda duk mai hakuri yana tareda nasara...shidai yayi hakuri ya kuma fawwala Allah lamuranshi dai gashi ya kawo mashi canji a lokacin da bai ta6a tsammani ba..Lallai Allah abun godia...har suka isa gidansu bai dena godia wa wnn ni'ima ta ubangiji ba..gani yake an gama mashi komai a dunia saidai kuma yayi fatan gama wa lafia...ko parking Nur bai gama ba ya bude motar da sauri ya fita zuwa cikin gidan...Nur ya bishi da kallo yana girgiza kai yace"wa yaga ba sabon ba"..karasawa yayi ya gyara parking dinshi snn ya bude motar shima ya fita zuwa ciki...yana shiga yaci Karo da Mummy dake kokarin Shiga parlonta kawai sai ya rungumota ta baya yana cewa"Mummy I can't believe this..waziri yace wai ni zan aureta yanxu..am super excited Mummy Allah yasa ba mafarki nake ba"..juyawa Mummy tayi ta dagoshi daga jikinta tana kallonshi da murmushi a fuskanta itama tace"ba mafarki bane..duk wani da kaji a gaske yake faruwa ba mafarki ba..dama ba nace maka jikina na bani kai zaka aureta ba?.."da sauri ya shiga gyada kai kafin ya lumshe idanunshi ya sake rungume Mummy yace"Mummy nagode sosai..nagode da addu'arki gareni Allah ya saka da aljannah"...hannunshi Mummy ta kama suka karasa parlorn suka zauna tana dubanshi tace"Ameen..kaima Allah ya maka albarka..waziri yace mun gobe zasuje su samu Lamido tareda uncles dinka akan mgnr auren naku"..sake rungumeta Bobby yayi yama kasa cewa komai...Nur dake tsaye tun daxun yana kallonsu sai yanxu Mummy ta lura dashi tace"Nuru karaso ciki mana"..yana murmushi ya karasa cikin parlorn ya zauna yana gaishe da Mummy...kmr wanda ya tunada wani abu sukaga ya mike da sauri ya kama hanyar flat dinshi duk suka bishi da kallo suna daria..daidai lokacin Aunty Sumy ta shigo wayanta rike a hannunta tace"yanxun muka gama mgn da Aunty Munubiya tace tana nan zuwa gobe inshaAllah"..Mummy tace"to Allah kawota lafia".
Yana Shiga parlonshi ya zauna kan three seater tareda dialing number ta yana lumshe ido..har ya gama ringing bata dauka ba ya sake kira still no answer kawai sai ya ajiye wayar tareda mikewa ya shiga bedroom direct ya fada bathroom ya daura alwala ya fito ya shimfida carpet ya tayar da sallah don ya nuna godia wa ubangijinshi for such a blessing da yayi mashi na bashi auren Lamido...har azumi ya kamata yayi don nuna godiyarshi wa Allah...har dare ya tsala bai dena Kiran wayanta ba ita kuma bata dauka ba..ganin ba daga wa zatayi ba yayi sending mata"thank u..thanks for accepting me..I love you"..daga haka ya jiye wayar ya lumshe ido yana tuna duk moments da yayi spending da ita..kaman yayi tsuntsu yakai kanshi Gombe haka yakeji amma ba zaiyi wnn rashin kunyan ba matukar ba cewa akayi yazo ba..afterall saura baifi 4 days suyi resuming school ba so zai na samun daman ganinta duk time din da yaso..he prays Allah ya shirya mashi ita yasa bazata na aikata abubuwanda dole zaisa yayi mata masifa ba.
Gombe..
Tunda Lamido ta samu labarin yanda reshe ya juye da mujiya sai abun yazo mata a bazata sosai..wani irin sanyi taji jikinta yayi zuwa yanxun for sure tasan she does not hate him amma ya zatayi da Prof ne kam?..ba wai aurenta da Bobby ke 6ata mata rai ba..kawai yanda baby zai dauka kaman dama can yaudaranshi take shiyasa ta hanashi zuwa ga parents dinta da wuri..and shi kanshi proprietor nan ba sabawa tayi dashi ba..ita bata San ma ta ina zata fara zama da wnn mutumin as her hubby ba..tasan yana sonta da gaske amma har ga Allah itadai gani take kmr bayan auren zai sake rikidewa ya dawo asalin proprietor data sani a baya..gaba daya ranar yini tayi a daki tana faman kunchi ko abinci bataci ba kuma ba wanda yace mata don me...conference video call ta hada musu itada Billy da besty tana tuttura baki ta fada masu duk abunda ke faruwa ga mamakinta sai taga gaba daya sunyi farin ciki da mgnr don har lissafin biki suka fara kawai ta kashe wayarta tana huci..ita fa har yanxu bata ga ta inda ita da proprietor za’ace suyi aure ba..to ta inama za’a fara?..kawai gani take kmr abun ba mai yiwuwa bane..gashi tun jiya take kiran wayan Prof a kashe har zuwa yanxu kama a kashen yake ta rasa dalilinda yasashi kashe waya..so take ta sanar dashi an samu turn of events ya gwada turowa wai ko Lamido zai sauraresu amma bata samun wayan nashi..duk tabi ta zama wata iri ita ba mai lafia ba kuma ba mara lafia ba..tana gani tun daxun yake kiran wayanta taki dauka don batasan abunda zai fada mata ba kmr yanda itama batasan abunda zata fada mashi ba...kunayanshi ma taji tanaji wlh..tana nan kwance a daki har dare daddy ya turo Yusra ta kirata..ba musu ta mike tareda maida hulan kanta ta nufi parlon nashi..suna zaune tareda Ammi ta karasa ciki a nutse ta zauna a kasa..daddy yace"nasan kin samu labarin abunda ke faruwa wajen Amminki koh?.."ta daga kai alamar ta sani..daddy yacigaba"to inaso ki kwantar da hankalinki kiyi mana biyayya a wnn auren..a yanda yaron ke sonki nasan kema bazaiyi taking naki long time kafin ki fara sonshi ba..kuma ban yadda ki mashi wani rashin kirki ba Aisha..inaso ki girmamashi kmr yanda kikeyi a baya snn kar in sakeji ance kin hadu da wnn mutumin ko waya ban amince kiyi dashi ba..idan Allah ya kaimu gobe zasuzo a tsaida ranar aurenku..Allah yasa haka shine alkhairi a tare daku Allah kuma ya maku albarka baki daya"..a hankali ta gyada kai idonta a kasa..saida ta tabbata ya gama snn tace"daddy dan Allah ina son zuwa Bauchi gidan aunty fiddausi"..daddy yace"ba wnn sunday zakuyi resuming school ba?.."a hankali tace"eh amma kafin sunday din zan dawo..ko kuma a daukemu daga can tareda Billy kawai mu wuce"..shiru daddy yayi kmr bazaiyi mgn ba sai can yace mata"shknn saiki shirya gobe da safe a kaiki..Allah maki albarka"..ta amsa da"Ameen daddy"..snn ta mike ta fita daga parlon..Ammi ta bita da kallo bayan fitar nata tace"ikon Allah..wai Aysha ce tayi wnn nustuwa haka sbd mgnr aure ya 6ullo..wonders shall never end"..ta karasa mgn tana daria yayinda daddy ke girgiza kai shima yana murmushi..shi kanshi yaga wnn canjin tattare da ita fatanshi dai Allah yasa auren nasu shine alkhairi a tareda kowannensu.
Washegari da safe ta shirya kmr yanda daddy yace driver dinsu ya dauketa zuwa Bauchi..tana zuwa gidan ta fashewa small mom dinta da kuka wai za’a mata auren dole..Aunty Fiddausi nata aikin rarrashinta tace"ni banga abun tada hankali anan ba Aysha bayan kowa ya shaida irin son da akace yana maki"..tun kafin ta rufe baki tace"Aunty inyamuri ne fa..kuma wlh bashida mutunci masifaffe ne na bugawa a jarida..shknn ni sai a hadani dashi salon yayitama mutum masifa komai fa shi abun fada ne a wurinshi"...daria aunty fiddausi ta kunshe kafin tace"to kiyi hakuri ni da kaina zanyi masa fada ya dena maki masifa gaskia..kuma shi da yake jikan waziri ta ina ya zama inyamuri kuma?.."da sauri tace"babarshi inyamura ce kuma shima yanayin inyamurancin..kawai sai in haifi ‘ya’ya a dinga koya musu igbo..wlh an cuceni"..daria sosai small mom dinta ke mata don ita bataga abun daga hankali a nan ba...idan ta fahimceta ba ma rashin auren wancan saurayin ne damuwarta ba kawai damuwarta an hadata dashi kuma wai masifaffe ne..ta lura iskanci ne kawai yasa take wnn abun amma ba kiyayya ba don bisa ga dukkan alamu itama tana sonshi kilan ganewa ne kawai batayi ba.
Sha biyu da wani abu tayi sallama da aunty fiddausi ta wuce gidansu Billy..ta iske Ummansu a parlor tareda sauran siblings din Billy maza..ta karasa ciki a hankali kaman wata mara lafia ta shiga gaisawa da Umma..Umma dake dubanta with smile tace"ashe kuma proprietor dinku zaki aura?..dazu Bilkisu ke fadamun..to Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana lokacin Aysha Allah yasa albarka"...juyawa tayi tana kallon Billy kmr zata fashe da kuka kafin ta sake juyowa ga Umma tace"Umma masifaffe ne fa"..daria Umma da sauran brothers din Billy suka sa jin abunda tace...Umma tace"banda abunki Aysha ai ba’a cika son namiji ya zama mara fada ba sbd raini"..turo baki kawai tayi bata sake mgn ba..wani elder brother din Billy mai suna Mubarak yace"naji ance jikan wazirin Gombe ne koh?.."mikewa tayi still tana turo bakinta tace"kuma babarshi inyamura ce"..daria suka kara saki Billy ta mike da sauri zuwa inda take ta kama hannunta tana kokarin kunshe dariar dake cinta itama tace"ki kyale Yaya best friend tsokanarki yake..yanxu mu shiga ciki ki bani labari in detail"..kwace hannunta ta shiga kokarin yi Billy bata sakeshi ba saida suka shiga dakinta..tana sakin hannun nata ta sake fashewa da daria har tana clapping hands dinta tace"wlh ba karamin dacewa kikayi dashi ba..dama garinku daya"..kallonta Aysha take har ta gama iskancinta snn ta karasa ciki ta zauna gefen gado tana duban Billy da wani murmushin mugunta tace"dadin abun dai kema naki yana nan zuwa..kwanan nan na samu labarin wani yana sonki har turowa ma zaiyi gidanku ayi mgn"..tsaki Billy ta saki tareda zama nan kusada ita tace"matsala na dake karya..uban wa ya baki wnn labarin?.."Aysha tace"ba labari aka bani ba kan idona komai ya faru..da gaske kema very soon zakiji ance an fidda maki miji sai ki zama cikin shiri"..kallonta Billy take kmr mai son gano gaskia..sake matsawa jikinta tayi tana marairaicewa tace"bani labari dan Allah..da gaske kike ko da wasa?.."Aysha tace"da gaske nake wlh..Hammana ne yake sonki"..wani kwalo idanu waje Billy tayi kmr taga abun tsoro tace"Lamido kiji tsoron Allah"..Aysha tace"Allah kinji na ranste maki da gaske nake..a gabana ya fadama Lamido ke yakeso shi kuma Lamido yace zaiyi mgn da grandpa dinku”..dakatawa tayi tareda kamo hannayenta tace"Billy i cant believe this wlh..abun yayi mun dadi wai ace Hamma na zai aureki..dan Allah Billy kema ki soshi kinji and kada kije ki fada masa na sanar dake dan cewa yayi bai yadda in fada maki ba"...murmushi Billy ta saki tareda zame hannunta daga nata tace"banza ‘yar rainin hankali"..ta fashe da wani daria tana cewa"ni dake za’a ga dan rainin hankali a ciki..yarinya tanaso tana kaiwa kasuwa"..da sauri Billy tace"ai kema kina son proprietor kuma kina kaiwa kasuwa"...haka dai sukaita tsokanar junansu Aysha bata bar gidan ba sai dab da magrib tayi sallama dasu ta koma gidan aunt dinta.
Washegari Waziri da Uncles din Bobby biyu suka je nema mashi aurenta wajen Lamido...Waziri da kanshi ya bada kudin aure inda Lamido,daddy da uncles dinta suka karba tareda tabbatar musu da cewa an bashi ita halak malak..Lamido yasha godia wajen waziri kaman wani gagarumin abun yayi mashi..an tsayar da mgn kan baza’ayi biki ba sai ta gama makaranta amma zai iya zuwa duk time da yakeso yayi mgn da ita wnn kam an bashi izini batun aure ne dai akace sai ta kammala.
Washegarin ranar suma sukaje Bauchi nemawa Hamma auren Billy a hannun kakanta babu wasting of time suma suka amince suka kuma ce an bashi aurenta lokaci kadai ya rage a shafa fatiha.
Lokacinda labari ya iske Bobby ji yayi kaman yayi tsuntsu ya tafi Gombe sbd farin ciki..bai taba tunanin komai zai faru cikin sauki haka ba..matsala daya da yake fuskanta yanxu shine rashin samunta a waya..ba wai bai samun wayan nata bane aah yana shiga dauka ne kawai batayi wanda baisan dalilin haka ba..duk iya dauriyarshi kasa cigaba yayi sbd yanda take neman ta tarwatsa mashi dan farin cikin daya samu yanxu a dalilin aurenta da yasan an bashi...daukan wayanshi yayi ya kira waziri sukayi mgn dashi yace shidai yanaso yazo Gombe a gobe sbd ya samu ya ganta..Waziri bai hanashi ba yace babu damuwa yazo ya ganta ko don su fara fahimtar junansu.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba... masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
47
Da wuri ya gama shirinshi don ko breakfast bai fitoyi ba saida ya gama..flat din Mummy ya fara shiga ya sameta zaune tana mgn da waziri a waya..karasawa yayi ciki ya zauna kusada ita yana jira ta gama..sun dauki lokaci mai tsayi suna discussing kan mgnr da bai fahimci inda ya dosa ba kafin su gama..Mummy na ajiye wayanta ta jiya tana dubanshi tace"so ka gama shiryawa?.."yace"na gama Mummy..Nur kadai nake jira"...Mummy ta mike tace"to muje kayi breakfast kafin Nur din ya karaso"..mikewa yayi ya matairaice yace"Mummy am not hungry plss..kinsan idan zanyi tafia ba son cin abinci nake ba"..hannunshi ta kama zasu fita daga dakin tace"ko tea ne sai kasha in ba haka ba kuma u will not step out if this house"..bai sake yi mata musu ba yabita har dinning..aunty sumy itama daidai lokacin ta fito don da wuri zata fita aiki...su Miemie ne bai gani ba ya tambaya Mummy ta wani hade rai tace sun tafi gidan kakarsu..baice komai ba sbd yanda yaga ta hade rai..batasan ko bata hade rai ba ba mgn zaiyi ba sbd shima yanxu na gabanshi ya isheshi..Allah Allah yake ya ganshi a gaban yarinyar nan yaji dalilinta na ignoring calls dinshi..koma me zatayi dai daga baya ne tunda an rigada an bashi aurenta so duk ihu bayan hari takeyi ya sani..tea Mummy ta hada mashi ya dauka ya shiga sha cikin ranshi yana tunanin yanda zasu kwashe da ita...kafin ya gama sha Nur ya iso gidan dan haka ya mike da sauri bayan ya ajiye mug dake hannunshi yana duban Mummy yace"zamu wuce Mummy..tafiyan akwai nisa"..murmushi kawai Mummy tace"Allah ya kiyaye hanya..ina gaida ‘yar tawa"..murmushi yayi tareda fadin"zataji"..snn ya koma zuwa flat dinshi don daukan keys..Nur kuma ya karasa yana gaisawa dasu Mummy..aunty sumy dake cin abincinta tace"wnn abokin naka zalamamme ne wlh..haka ake zuwa zance tun sassafe sbd rashin hakuri"..daria Nur yasa kafin yace"ai aunty kinsan qanin naki halinshi sai shi..ita kanta Lamidon fa wai haushinta yakeji bata daukan mishi waya..so nake muje dai inga iya inda fushin nashi zai kare"..daria itama aunty sumy tayi tana cewa"ai matar Bobby ta shiga uku da masifa..koda yake ita wnn yana sonta bazai iya mata masifan ba kila"..Nur yace"ina ya isa ya mata?..daidai dashi ya samu ai"..daria suka kara saki Mummy dai na jinsu tana murmushi..ita kanta wani lokaci takanyi tunanin yanda Bobby zai kare da matarshi da wnn temper din nashi..saurin hawa gareshi kmr farashi gashi kuma da wuyar sakkowa..amma ta bakin na Nur ta lura yarinyar daidai dashi ce snn kuma uwa uba soyayyan da yake mata wanda bazai barshi yanayi mata anyhow ba..sbd wnn fadan nashi yasa a kullum addu’arta Allah ya bashi macen da yake mutuwar so ba wadda ke mutuwar sonshi ba don idan ya auri macen da baiso matsala za’a samu gagaruma..Allah almusawwir kuma sai ya amsa addu’anta ya bashi wadda sonshi yafi nata..fitowa yayi daga dakinshi yanata baza kamshi..Nur ya kalleshi yana wani kashe ido yace"bakaga kyan da kayi ba wlh..manyan kaya na suiting dinka and da wnn wankan nasan dole Lamido ta ajiye ego dinta ta bada kai don zata fahimci kai din fa ba kmr kowa bane"..harara Bobby ya watsa mashi baice komai ba..yana karasowa yayima Mummy da aunty sumy sallama snn ya juya ya fita Nur yabi bayanshi yana kunshe daria...driver na ganin su ya karaso suka gaisa Bobby ya bashi key din motar da zasu fita yana sake trying number dinta bata dauka ba..driver ya kawo motar inda suke snn suka bude suka shiga shi kuma ya tayar da ita suka fita already dama ya sanar dashi cewa Gombe zai kaisu...ko a hanya saida ya sake trying number still no answer sbd tsabar haushi baisan sanda ya wurga wayan nan gefenshi yana fadin"to hell with you"..juyawa Nur yayi yana kallonshi then back to wayarshi dake yashe a tsakiyarsu...hannu yakai zai dauki wayan Bobby yayi saurin daukan kayarshi shima yace mishi"fuck you"..Nur ya kwashe da daria hadda kyakyatawa...Bobby ya kulu iya kuluwa amma baice komai ba..gaban driver dinshi zai dinga mashi irin wnn iskancin?..zaiyi maganin Nur wlh...bai sake ce mishi komai ba har shima ya gaji da daria don kanshi ya bari daga karshe ma baccinshi yayi hankali kwance..a kufule Bobby ke kallon yanda ya wani yi bacci a mota kmr karamin yaro..shiko tunanin dake ranshi ma bazai iya barinshi baccin ba..gani yake kaman ba tafia suke ba don Gomben yaga tayi nisa sosai baisan ko don sbd matsuwar da yayi ya hadu da ita bane...haka yayita sake sake har suka shigo Gombe around 11:45..saida ya fara zuwa suka gaisa da waziri snn suka wuce estate dinsu...suna zuwa bakin gate gabanshi ya fara faduwa da baisan dalilinshi ba...gidan Lamido suka sauka kmr yanda waziri yace daga nan kuma Lamido yasa aka rakasu har kofar gidansu..tun jiya da waziri ya sanar dashi zaizo dama yasa da sassafe akaje aka daukota daga Bauchi don daddy baya gari ya koma wurin aiki...a bakin gate sukayi parking Bobby sai kallon gidan yake cikin ranshi yace"so this is their house?.."ya karasa da wani murmushi kan face dinshi...yaron da ya rakosu ne ya shiga ciki yace ma Ammi sun iso ita kuma ta tura Husna tace ta shiga dasu parlon daddy..babu wasting of time kuwa Husna ta fito tana hangosu ta karasa kusa dasu ta washe musu baki tace"sannunku da zuwa"..Nur ne ya fara cewa"yauwa sannu yanmata..ke qanwar Lamido ce koh?.."gyada mishi kai tayi still smiling tace"nike binta ai..sunana Husna Lamido"..Nur dake gyada kai yace"MashaAllah Husna Lamido"..juyawa tayi tana kallon Bobby daya rungume hands dinshi yana kallonsu..suna hada ido ya sakar mata smile tareda cewa"Sannu Husna Lamido"..murmushinta ta kara fadadawa kafin tace"Ammi tace ku shigo ciki"..daga haka tayi gaba sukabi bayanta har cikin gidan..parlon daddy ta shiga dasu as instructed by Ammi snn ta gaidasu ta fita...Nur ya shiga kallon parlon yana yaba kyau da yayi mashi...shiko Bobby idonshi bai sauka ko inaba sai kan wani picture dinsu gaba daya lokacin suna kanana..ita da Ammi ne a pic din daddy ya dauki Husna Ammi kuma ta dauki Yusra aysha kuma tana tsakiyarsu...tayi murmushi a picture din har dimples dinta sun fito..murmushi da bai shiryaba ya saki yanajin wani weird feeling tattare dashi..sake maida dubanshi yayi ga dayan picture din shima gaba dayansu ne amma wnn sun girma gaba daya snn akwai Hamma Najeeb a jiki..dan hade rai yayi ganin yanda take zaune kusa dashi gaba daya suna daria kawai sai yaji baiji dadin zama kusa dashi da tayi ba..da sauri ya dauke idonshi daga hoton don gudun kada ya karasa spoiling mood dinshi da dama ba daidai yake ba...wani fitinannen kamshi ne ya bugi hancinshi kafin ta shigo parlon a hankali tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki...kallonta kawai Bobby yake yanajin zafin a yanayin da ta fito..is she mad zata sanya turare haka ta fito kuma ba tareda hijab ba?..juyawa ga Nur yaga sai wani kallonta yake yana murmushi nan take yaji 6acin ranshi ya karu akan wanda yake ciki..shi baima san kaddarar data kaishi daukan Nur ya taho dashi ba gashi nan sai kalle mashi ita yake a banza kmr yaga matarshi...karasowa ciki tayi ta zauna hankalinta gaba daya kan Nur fuskanta ba yabo ba fallasa tace"sir good afternoon"..Nur da har yanxu ke murmushi yace"good afternoon amarya Lamido ya hutu?.."dan murmushi kawai tayi tareda cewa"Alhamdulillah”...Bobby daya cika yayi fam ya shiga dubanta da angry eyes dinshi yace"bakida hijabi ne?.."daure fuska tayi ba tareda ta kalleshi ba tace"bani dashi"..yace"then tashi muje a siyo"..banza tayi dashi tana sake dinke fuska..shi wnn irin masifaffe ne wai?..a nan dinma sai ya mata bala’i bazai bari su rabu lafia ba?..mikewa yayi hands dinshi a aljihun wandonshi yace"ki tashi muje a siyo nace"..ko motsawa batayi ba Nur dai da yaga abun na Bobby azimun ne sai ya mike ba tareda ya kalli inda yake ba yace"i will wait for u in the car"..daga haka ya fita daga parlon shi kuma ya shiga takawa a nuste zuwa inda take yayi kata wani tsaye yana kallonta kmr soldier...dan dagowa tayi a hankali ta kalleshi taga kallonta shima yake kmr an aikoshi nan da nan ta sauke nata idon tana kunkuni...zama yayi nan kusa da ita still yana dubanta yace"and wa ya fada maki ana sa turare haka a shiga cikin mutane?.."kallonshi ta juyo tanayi kmr zata sanya kuka..ya lumshe ido tareda jingina da jikin kujerar yana maimaita innalillahi a cikin zuciyarshi..kada kuma ta fara tunanin yana overacting amma Allah ya san ba karamin kishi yake dashi a kanta ba..ganinta a haka shi kanshi saida yaji wani abu balle kuma Nur da bai hada komai da ita ba..shi bayason ana ganin beauty dinta ne and fesa turare ko Allah ya haramtawa mata su fesa su fita sbd kamshi ba karamin fitina yake haddasawa ba..a hankali ya bude idon nashi tareda gyara zama yana dubanta yace"why are you ignoring my calls?.."tace"ba komai"..girgiza kai ya shigayi yana dubanta cikin ido yace"karya kikeyi"..ta wani zaro ido tana kallonshi saura kiris daria ya subuce mata tace"sir karya kuma?.."kai ya sake gyadawa alamar haka yake nufi...ta dan turo baki tace"nidai ba karya nake ba"..kallonta ya tsaya yi kawai kmr baiji abunda ta fada ba...riga da skirt ne a jikinta na lace da yayi matukar amsarta..ta daura dankwalinta as usual saidai wnn karon bata fito da gashi ba don tasan sai yayi mgn sai kuma veil dinta data yafa a kafada...gani yake duk dunia babu macen da zata kaita kyau a idanunshi..ita komai ta sa kyau yake mata shiyasa a kullum kishinshi karuwa yakeyi a kanta...lumshe ido yayi tareda sauke ajiyar zucia cikin voice dinshi da yaji ya dashe all of a sudden yace mata"i love u so much Aysher..plss i beg of u ki bar kin answering calls dina..am about going crazy.i..i am..."kasa karasawa yayi kawai yayi shiru yana sauraran heart beat dinshi...kallonta yacigaba dayi voice dinshi na rawa sosai yace"have mercy on me plss..i promise to love u till my very last breathe..I promise to be a good husband..i will never rufuse u anything in the world just wanted u to love me nor matter how little i wont complain..kawai ki soni ki zauna dani for i dont think i can live without u..i love you dearly"..lumshe idanu Aysha tayi tana sauraran words din nan nashi..bata san why ba amma words din really galddens her heart..sunyi mata dadi sosai ba kadan ba..kawai mamaki take yanda the whole Dr Bobby ke pouring mata love words haka..bata san ita ko tana sonshi ba amma this very moment taji ya burgeta matuka..da dadewa dama tasan son da yake mata ba gama garin so da ake iya samu a ko ina bane sai wanda Allah ya zaba yake bama masoyi mai matukar sonka kamarshi..kawai gani take Allah knows best shiyasa ya hada aurenta da nashi..idan kuwa haka ne ita bazata ja da ikon Allah ba saidai tayi fatan hakan ya zama alkhairi a garesu baki daya...ganin yana mata wnn kallon nashi mai sawa taji wani iri ta mike da sauri har veil dinta yana faduwa ta dauka da sauri ta fita daga parlon ta bar Bobby da lumshe ido yana saqan kamshin da ta tafi ta bar mashi...yana nan zaune after few minutes ta dawo dauke da tray a hannunta ya mike da sauri ya amsa tray din ya ajiye kan table ita kuma ta sake fita ta dawo da wani..a takaice saida ta cika musu gaba da kayan ci dana sha snn ta kama haya zata fita yayi saurin cewa"where are u going to?.."tace"zan kira provost ne yazo kuci abinci"..girgiza mata kai ya shiga yi yana zaro wayanshi yace"don’t worry i will call him..amma haka kike fita Aysher duk mazan dake gidan nan suna kallonki?.."juyawa tayi ta koma ciki ba tareda tace komai ha don bata ma san abunda ya kamata ta fada ba..shi kuma yayi dialing number din Nur yana dagawa yace ya shigo suci abinci..ba musu Nur ta dawo parlon ita kuma ta mike tana fadin"bari inyi excusing naku idan kun gama sai in dawo"..kai kawai Bobby ya iya daga mata yabi bayanta da kallo har ta fita snn ya sauke ajiyar zuciya ya fara cin abincin...sai yanxu ya samu kwanciyar hankalin cin abinci amma daxu ji yake gaba daya tension din dunia kanshi ya kare.
Bayan sun gama cin abincin ta dawo tareda Yusra data dage sai taje ta gaishesu...kanta a kasa har ta karaso ciki ta zauna..Bobby daketa kallon Yusra ganin kamar Ilham dinshi yace mata"hey cutie"..washe baki tayi tana gaisheshi yace"ya sunanki?.."tace"Yusra Lamido..kaine wanda zaka auri Addah?.."dan wara ido yayi yana kallonta da murmushi yace"yeah nine..waya fada maki ni zata aura?.."da sauri Yusra tace"Adda Husna ce tace wai kai proprietor dinsu ne kuma wai kai inya..."Aysha bata bari ta karasa ba ta toshe mata baki...Bobby sai yayi relaxing yana kallonsu..dukda bata bari ta karasa ba yasan inyamuri zata ce..girgiza kai kawai yayi yana murmushi..Aysha ta mike rikeda hannun Yusra suka fita daga parlon tace"ni zaki tonawa asiri Yusra?.."a hankali tace"kiyi hakuri Adda mantawa fa nayi"..Aysha tace"oya wuce ki koma wajen Ammi kar na sake ganin kafarki a nan"..ba musu ta wuce ta bar wurin ita kuma ta sauke ajiyar zucia tareda komawa ciki...bata samu Nur a parlon ba sai shi kadai...tana karasawa ta zauna yace mata"daddy baya gari ne?.."tace"eh yana Abuja"...gyada kai yayi kafin ya sake cewa"inyamuri kike cemin koh?.."wani irin zare idanu tayi hadda su dafa kirji tace"Nii😳"..murmushi ya kara saki yana gyada kanshi yace"yes ba gashi zata fada kin hanata ba"..turo baki tayi tana kawar da idonta daga wnn kallon nashi tace"nidai ba haka nake cewa ba ba ruwana"...daria mgnr nata ya bashi aiko ya shiga yinta kmr me..saida ya gama don kanshi snn yace"ko haka kika fada ma ba wani abu ke bakaya laifi ai..and niba igbo bane..ni bafulatani ne just like you"..shiru tayi tana wasa da fingers dinta..shi kuma kallonta yakeyi yanajin tamkar ya janyota jikinshi yace"ko har yanxu baki yadda nima dan Gombe bane?.."sake turo baki tayi cikin gajiya da tambayoyin nan nashi tace"na yadda"..shiru ya sakeyi for some minutes kafin kuma yace"so yanxu dai ni zan aureki?.."sake sunne kai tayi tanajin wani irin faduwar gaba..shi kuma har yanxun ya kasa dena murmushi yacigaba da fadin"i just can’t wait for ranar da za’a daura mana aure..am eager in ganki cikin gidana as my wife"..wnn karon rufe fuskanta tayi da hands dinta don wani irin kunya taji ya rufeta..shiko murmushi kawai yake saki non stop murya can kasa ya kira sunanta"Aysher"..dagowa tayi a hankali tana kallonshi..shima kallon nata yakeyi kafin yace"i love you..to the moon and back..kuma nagode sosai for agreeing to marry me insha Allah bazakiyi regretting decision din nan ba"..kasa ta sakeyi da idonta tanajin wani baqon al’amari na zaga jikinta...banda yake ba abunda take yau duk uban surutunta nemanshi tayi ta rasa kuma ta rasa dalili..duk wnn rashin kunya data gama planning zata mishi saita kasa sbd kwarjini na musamman da taga ya mata uwa uba kuma wnn words da yake sake kashe mata jiki dasu...duk sai taga ya sauya kaman ba proprietor data sani mai dan karen masifa ba...shiko murmushi yaki yankewa a face dinshi sam sai wani jin dadi yake kmr anyi mashi bushara da aljannah...sake kasa da murya yayi kafin yayi mgn wayanshi dake ajiye kusa dashi ya fara ringing..dubawa yayi yaga wanda ke neman katse mashi wnn jin dadin sai yaga Mummy dan haka yayi picking da sauri yana cigaba da murmushi da igbo yace"Hello Mummy"..da igbo din itama ta amsa mashi da"tun daxu nake kiran wayoyinku bai shiga..ka bani ita mu gaisa idan kuna tare"..mika mata wayan yayi yana binta da wani kallo mai wuyar fassarawa yace"Mummy"..ba musu ta amsa wayan tareda kaiwa kunne..a daya banagaren Mummy tace"daughter"Aysha ta sake sinne kai tana murmushi tace"Mama ina yini"..Mummy tace"lafia lau ya hutu"..tace"Alhamdulillah"..Mummy tace"maasha Allah dama so nake in maki godia for accepting him..Allah maku albarka yasa haka ne alkhairi a tareda ku"..kasa tayi da kanta ta kasa amsawa..ita duk bata san yaushe kunya ya shigeta har haka ba wlh..bata taba zaton zataji wani abu wai shi kunya ba a rayuwarta amma yau gashi tanaji kuma batasan dalili ba...godia sosai Mummy ta sake kwararo mata snn tace ta gaida Mamanta..ta amsa mata da zataji snn ta mika mashi wayar...yana karba ya sake maidawa kunne yana sauraran abunda take fada yanata murmushi...baice komai ba har saida ta gama snn ya ajiye wayar...agogon hannunshi ya duba yaga time na wucewa gashi yau zasu koma Kano dan haka ya wani langabar da kai yana kallonta in a pleading tone yace"tafia zamuyi Aysher..amma dan Allah i beg of u ki bar fesa turare haka da yawa idan zaki fita kuma ki taimakamun ki dinga sa hijabi please"...dagowa tayi ta kalleshi ya sake narke mata idonshi aikuwa ta dauke nata da sauri jin wani abu ya fito daga cikin idon nashi ya shiga nata..itadai ta shiga uku da idanun nan nashi da ba dama ta kallesu ko ya kalleta dasu sai ya sata jin wani iri..ganin har yanxu batace komai ba ya sake kasa da murya yace"kinji?.."kai kawai ta iya daga mashi ba tareda ta kalleshi ba..shiko bai dauke idanunshi a kanta ba ya sake cewa"And dan Allah ki taimaka ki dinga daukan wayana..hankalina tashi yake idan ina kira baki dauka ba kinji?.."nan ma kai ta sake gyada mashi without saying a word..gaba daya yawun bakinta ma taji ya kafe mata all of a sudden..kallonta yake yana so ya samu eye contact da ita amma taki dagowa..yace"to kiyi mgn da Ammi zamu gaisheta kafin mu wuce"...ba musu ta mike ta fita daga parlon shi kuma ya bita da kallo yanajin sonta na sake zagaya duk wani system na jikinshi...after like 5 mins ta dawo tace Ammi tace su shiga dan haka ya kira Nur a waya ya dawo snn suka shiga main parlor gaba dayansu...Ammi na zaune kan one of kujerun parlon sanyeda hijab sai Yusra a gefenta...suka karasa ciki duk suka zauna a kasa Ammi nata cewa su koma kan kujera amma basuyi hakan ba suka fara gaisheta a haka...ta amsa da fara’a tareda tambayan iyayensu duk sukace suna lafia..nasiha sosai tayi musu kafin su mata sallama su fita Bobby na sakejin matar ta kwanta mashi a rai sbd kamalarta..wato ba daddy kadai ne dattijo a gidan ba ita kanta Ammi dattijuwa ce..sunada halin girma sosai ba kadan ba..ya kuma san yayi dace da Allah yasa zai auri diyarsu don mutanen kirki ne..shi sai yau ya samu ganin tsananin kamar da Aysha takeyi da Amminta..irin kama sosai wanda ko mgnrsu ma kusan iri daya ne likewise dimples dinsu...halayyan su ne kawai ya bambamta don yasan da kyar idan wnn fitinan na Aysha a wurin Ammi ta dauko..ita batayi kala da fitinannu ba sam amma ita indo a kallon farko da mutum yayi mata yana iya gane tsantsar rashin jin dake tattare daita dukda ma dai yanxu ta girma ta rage kiriniya...ita kadai ta rakosu har compound don Husna ta wuce islamiyya...suna gama sallama da Nur ya bude mota ya shiga yayinda shi kuma Bobby ya karasa inda take tsaye ya zaro kudi a aljihunshi ya mika mata yana cewa"sorry ban kawo maki komai ba..hankalina ne duk ba daidai ba lokacinda zamu taho amma ga wnn kisai duk abunda kikeso"..girgiza mishi kai tayi alaman bazata karba ba..ya wani langabar da kai yana kallonta yace"dan Allah accept it..bazanji dadi ba in kikamun haka"..shiru kawai tana kallonshi..ya kamo hannunta yasa kudin a ciki snn ya sake kasa da murya still bai bar kallonta ba yace"shknn zamu wuce..ai ranan sunday zakuyi resuming school koh?.."kai a kasa ta amsa da"eh..zamu tafi clinical posting"..gyada kanshi yayi yana murmushi don tuna zai samu damar ganinta son ranshi a asibiti yace"i can’t wait for sunday..i love u sosai"..kasa ta sakeyi da kanta batace komai ba..yace"Aysher look at me mana"..dan dagowa tayi ta kalleshi suna hada ido ta juya zuwa cikin gida da sauri har tana tuntu6e shi kuma ya shiga shafa kanshi yana sakin murmushi ba kakkautawa...shi kanshi baisan ya iya murmushi ba har haka..gaba daya 6acin ran daya kwaso tun daga kano yana zuwa gareta sai ya nemesu ya rasa sai farin ciki daya baibayeshi kuma.."oh Allah nagode maka..Allah Alhamdulillah bazan gaji da godia kan wnn kyauta da kayimun ba..i will be forever grateful"..abunda yake fada knn yayinda ya karasa inda motarshi yake ya bude ya shiga snn driver ya tada ita suka fara tafia...ko a cikin motar relaxing yayi kan kujera yana shafa kai yana murmushi kamar sabon kamu..Nur dai na zaune gefe yana kallon ikon Allah..a fili yace"muma dai mun kusa isowa wurin nan...lokaci karami muke jira muma mu shigo sahun manya"...Bobby dai kala baice dashi ba yacigaba da murmushinshi..idan yace zai biyewa Nur yasan tsaf zai iya harxukashi suzo suna rigima gaban driver shiyasa bazai kulashi ba ko don ma farin cikin da yake ciki a yanxu haka.
Wnn dai page din gobe ne na dawo muku dashi yau so koda kun jini shiru gobe ga abunku nan na baku.😄
0 comments:
Post a Comment