Da fara’a ya shigo cikin gidan saidai mutanen daya gani parlon zaune tareda su Mummy yasa yaji new 6acin rai na neman taso mishi...suna jin shigowarshi suma gaba daya suka maida hankali kanshi kaman dai jiran zuwanshi suke...dauke kanshi yayi ba tareda yace qala ba ya kama hanyan flat dinshi Mummy da aunty sumy suka hada ido kafin Mummy ta mike ta dubi mahaifiyar Isma’il grandma din su Miemie knn tace mata"ina zuwa bari inyi mgn dashi yanxun nan"..daga mata kai matar tayi duk jikinta yayi sanyi..ita gani take kaman shi zai hana su samu yafiyar da sukazo nema wurinsu..dukda already sun riga sun gama mgn har Mummy tace itakam bata rikesu ba dama ta yafe musu itama aunty sumy jin Mummy tace haka itama sai bataja zancen da nisa ba tace ta yafe..su Miemie kuwa ya rage nasu su yafe ko karsu yafe amma sunsan komai dadewa watarana zasu yafe musu tunda duk tsiya dai ahalinsu ne...Mummy na shiga dakin ta sameshi zaune gefen gado ya hada uban tagumi kai kace uwa da ubanshi ne suka mutu..yana ganinta kaman jiran shigowan nata yake yace"Mummy why dan Allah?..why?.."kallonshi kawai Mummy keyi dama tasan za’ayi haka..tun kafin suzo dama tasan rana irin wnn zaizo and gashi yayi reacting exactly yanda take tunanin zaiyi...tasan yanxu ko auren sumayya za’a maida daga wurinshi za’a fara samun matsala sbd wnn dan banzan rikon nashi da bai iya mance abu komai tsahon lokacin daya dauka...karasawa tayi kusa dashi ta zauna tana dan murmushi tace"yau an hadu da Lamido knn?.."tana rufe baki yace"Mummy ba mgnr Lamido ake ba meya kawo mutanen can cikin gidan nan dan Allah?..me sukazoyi mana?.."ajiyar zuciya Mummy ta sauke tareda kamo hannunshi still murya kasa kasa tace"yafiya sukazo nema Bobby..sunaso mu yafe musu dukkan laifukansu na baya kuma nidai na yafe musu..itama Sumayyan ta yafe sbd haka dan Allah kar kace zakayi kokarin causing scene a wurin nan dan Allah"..kallonta kawai yake yanaji yanda 6acin ranshi ke ninkuwa ninkin ba ninkin...kamar zaisa kuka yace"yanxu sbd Allah Mummy duk abubuwanda suka aikata har kun manta knn?..kin manta wulakancin da sukayi mata kawai sbd ba ita sukaso ya aura ba shine yanxu sbd sunaso ya maida ita zasu wani kwaso legs dinsu suzo mana gida..Mummy yanxu ko don sbd su Miemie bazaku duba wnn al’amarin ba..sukayi abandoning dinsu for almost seven years shine yanxu zasu wanizi suce ku yafe musu ku kuma ku yadda dasu?.."yana rufe baki Mummy tace"kaine ya kamata ka hakura kodon sbd su Miemie din..duk yanda muka kai da rashin sonsu fa bamu isa mu rabasu da yaran nan tunda jininsu..snn kuma kowa ya kallesu yasan sunyi regretting abunda sukayi so don me bazamu yafe musu ba?..meyasa bazamu yafe musu ba tunda sukazo har gida neman a yafe musun..kada ka manta ubangiji da kanshi yana son masu yafiya..idan ka kasance mai yafiya sai Allah kaima ya yafe maka..baka tunanin ko don wnn ya kamata a yafe musu?.."shiru kawai Bobby yayi yana sauraronta amma shidai harga Allah baiga dalilinda zaisa kawai daga zuwansu su wani ce sun yafe musu ba..juyawa gareta sai yaga ta daure fuskanta tsaf dan haka yayi kokari ya sassauta nashi tareda yin kasa da nashi muryan kafin yace"Allah ya baki hakuri Mummy..ba haka nake nufi ba"..sassauta nata muryan itama tayi before tace"kuma anjima inason mgn dakai"..a hankali ya amsa mata da"toh"..snn Mummy ta mike ta bar masa dakin shi kuma ya rage kayan jikinshi ya fada bathroom yana sake tunawa da Lamido da duk abubuwanda suka shiga tsakaninsu yau..ya lumshe ido yana sakin wani murmushi daya tuna yanda yayi hugging dinta..he felt kaman ya rike ‘yar jaririya sbd taushin jikinta..ga wani qamshi da shidai bai ta6ajin irinshi ba sai daxu a jikinta..baisan lokacinda daria ya su6uce mishi ba daya tuna yanda ta gwalo idonta a lokacin..yasan she was shocked amma da yake tanada positive mind sai batayi thinking negative a kanshi ba sai ma yabonshi da tayi..shi tunda yake bai ta6a sanin haka mutum kejin dadi idan an yabeshi ba sai yau din nan kuma a kanta..lokacin data yabeshi sai yaji kaman duk dunia ko kowa bazai yabeshi ba nata kadai ya isheshi...nata kadai ya isa yasashi farin ciki...har ya gama wanka ya fito bai dena tunaninta yana sakin murmushi time to time ba...koda ya gama shiryawa sai yayi kwanciyarshi nan cikin dakin yaki fita sbd yasan kilan wadan nan mutanen suna nan basu tafi ba shi kuma baison haduwa dasu dan haka gwara yayi kwanciyarshi a daki...wayanshi ya dauki ya shiga gallery dinshi hoping inama zaiga pictures dinta amma babu..bayada pictures dinta ko daya amma yanada bukatar ya samu ko guda daya ne sbd irin wnn lokacin..kunna data dinshi yayi ya shiga whatsApp wai ko zai ganta online amma she’s offline...ya duba status dinta nan ma batayi updating komai ba sai wani short video na wasan PSG da Manchester..dan ta6e baki yayi cikin ranshi yana ayyana dole ma ya rabata da kallon ball din nan wlh..shi bazai dauki ta wani dinga son ‘yan ball tana supporting dinsu ba..hakan 6ata mishi rai yakeyi sosai...kashe data dinshi yayi ya ajiye wayar ganin har lokaci bata online...yana ajiyewa kuma kiran Nur ya shigo wayan dan haka yayi picking yasa a speaker yana sakin wani murmushi yace"Dr Nuruddeen Ugo"..daga daya 6angaren Nur ya wara idanu yana fadin"ah lallai abu ya tafi yanda ya kamata i don’t even have to ask"...Bobby yace"of course..ka kayuta sosai daka kawomin ita thank u"..da sauri Nur yace"always welcomed angon Lamido..yanxu a bani labari in detail inji abunda ya faru"..murmushi Bobby ya kara saki yana shafa beard dinshi hadda su lumshe ido yace"ka bari kawai Nur..sai yanxu na fara yadda da mgnrka..tanada hankali sosai"..Nur ya fashe da dariya before yace"bana fada maka ba?..tanada hankali wlh kawai idan ba zama kayi da itaba bazaka fahimci hakan ba"..Bobby na gyada kai zai sake wani mgn Ilham ta shigo dakin tace mishi Mummy na nemanshi..sallama yayi da Nur snn ya janyota yana kallon yanda har yanxu bata gama maida jikinta sbd rashin lafiyan da tayi ba yace"mutanen nan sun tafi ko suna nan?.."ilham tace sun tafi dan haka ya mike rikeda hannunta suka fita parlor...Mummy kadai ya samu a parlon ya karasa ya zauna yana kokarin zaunar da Ilham kan laps dinshi Mummy tace"kyaleta taje wurin su Miemie mgn zamuyi ai"..ba musu ya saketa fa nufi parlon aunty...Mummy ta maida hankalinta gaba daya gareshi fuskanta ba yabo ba fallasa tace"ya mgnr zuwa duba Waziri?.."wani irin damm yaji gabanshi ya fadi amma bai bari ta lura ba yace"za..zamu..je mana Mummy..ba kince yana india ba?.."yana rufe baki tace"an dawo dashi jiya..yana nan a Abuja kuma wnn satin nakeso kuje ku duboshi"..Bobby ya hadiye wani irin yawu kafin ya tattaro abunda zai fada mata yace"kenan..Gombe zamuje..mu dubashi?.."kallonshi Mummy tayi rai a dan 6ace tace"bakaji nace yana Abuja bane?.."da sauri yace"yi hakuri Mummy banji ba..amma why not a bari next week sai muje"..tun kafin ya rufe baki Mummy tace"ban yadda ba wnn satin nakeso kuje ku dubashi..idan kuma kanaso ka nunama dunia ban isa dakai bane Bismillah"..kallonta kawai Bobby yake yana mamakin sudden change din nan nata..Mummy ba mace ce mai fada ba sam..zaiyi wahala kaga tana fada musamman ma shi amma yanxu gashi ta daure fuskanta tana mishi fadan akan mutanenda bai daukesu a bakin komai ba..mutanen da basu ta6a kaunarsu tsakani da Allah ba tun mahaifinsu ma yanada rai...yasan duk wnn abun tanayi ne sbd kar yayi mata gaddama kaman yanda ya sabayi a baya amma shidai har yanxu baiji zai iya zuwa wani duba waziri ba..Wazirin da shi kanshi ba kaunarsu yake ba...ganin yanda yayi shiru ya wani kafeta da ido tace"bazaka jeba knn?."da sauri yace"aah ba haka bane Mummy..zanje..amma in..."bata bari ya karasa ba ta dakatar dashi da fadin"kaje ka fara shiru this coming weekend zakuje gaba dayanku ku duboshi"..kallonta yake yace"gaba dayanmu kuma?..wai kina nufin hadda su Miemie?.."kai tsaye tace"ko su ba jininshi bane da baza suje dubashi ba?.."a hankali yace"amma Mummy su meye hadinsu da Waziri da zasuje duboshi"..kallonshi Mummy keyi cikeda takaici tace"kaidai idan bakayi wasa ba sai Allah ya kamaka da laifin yanke zumunta..su Miemien zakace meye hadinsu dashi sbd bakada hankali?.."shiru kawai yayi yana kawar da kai shidai harga Allah wnn abun da Mummy keson tursasa su suyi bai gamsheshi ba..kilan ma suna zuwa Wazirin yasa koresu yace bayaso ya sake ganinsu har abada...ita kuwa Mummy ganin idan tacigaba da zama tana mgn dashi 6ata mata rai kawai zaiyi sai ta mike bayan ta gama mgnrta ta wuce zuwa 6angarenta...sbd iskanci zai wani ce a bari ba yanxu ba sai azumi ya shigo knn yakeso suje dubiyan nashi ko sai bayan sallah?..ta rasa wane irin taurin kaine da Bobby da ko ita data haifeshi watarana bya tankwaruwa ta dadi a wajenta?...yana ganin ta shige ciki shima ya mike zuwa flat din aunty sumy..he need to talk to her about this ko zata iya lalla6a musu Mummy ta bari sai bayan sallah tunda yanxu dab ake da fara azumi...yana shiga kai tsaye bedroom dinta yaje ya kwankwasa kofa ta bashi izini snn ya bude kofar ya shiga...a zaune ya sameta tsakiyar gado tana aiki da system dinta..ya isa ciki ya zauna kusada ita yana dubanta a hankali yace"mgn nakesonyi daks aunty sumy"..ba tareda ta dago ba tace"to ina sauraronka Uncle Bobby"..dan 6ata rai yayi yana kallon kaman zaisa kuka yace"aunty plss be serious mana..please!.."ajiye system din tayi tana dubanshi da murmushi tace"to yi hakuri..ina jinka"..gyara zama yayi kafin yace"Mummy ce take mgnr zuwa dubiyan Waziri"..ajiyan zuciya ta saki kafin tace"kaima ta fada maka knn?.."yace"ta fadamin..yanxu ya kike ganin zamuyi?..nidai bana son zuwa inda suke kwata kwata..bana son ganinsu"..kallonshi aunty sumy keyi kafin ta sake sauke wani ajiyan zuciya tana cewa"na fuskanci wnn karon Mummy da gaske take kan mgnr nan..idan mukace zamuyi kokarin kaucewa umarninta muna iya samun matsala da ita"..shiru Bobby yayi yana nazari shi kanshi yaga alaman hakan zai faru amma ya zasuyi?..yace"yanxu knn kina nufin bamuda wani option dole sai munje?.."gyada kai tana cewa"gaskia dai kamar bamuda wani option din..kasan yanda Mummy take da damuwa Bobby idan bamuyi abunda takeso ba muna iya sawa ta samu wani matsalan kuma kasan yanda bp dinta yake..baason tana shiga damuwa da yawa"...shiru ya sakeyi yana nazari..tabbas mgnr data fada gaskia ne...yasan yanda ta kwallafa rai kan sai sunje din nan idan sukace zasuki zuwa tsaf zata iya sama kanta damuwa har jinin nata yazo yana hawa shi kuma abunda baiso knn har abada...ajiyar zuciya ya sauke tareda runtse ido yasan wnn karon kam bashida wani hanyan tsira..duk wani kauce kauce bazaiyi tasiri akan Mummy ba wnn karon tunda har tasama ranta sai sunje dole...haka nan zai hakura yaje domin mahaifiyarshi amma wlh ba donshi wazirin ko don wani daga cikin ‘ya’yanshi ba...aunty sumy ta dafa hannunshi cikin sigan lallashi tace"haka nan zamu hakura muje wnn karon..koba komai zamu samu ladan da su bazasu ta6a samuba sbd kin nemanmu da sukayi na tsahon shekaru"..gyada kai kawai ya iyayi tareda mikewa ya fita daga dakin...tabbas zasuje amma ba don wani daga cikinsu ba sai domin Mummy..sbd gudun 6acin ranta daka iya haifar mata da matsala amma ba sbd su ba.
Bayan kwana biyar...
Da sallama ya shigo parlon Mummy ya sameta zaune tana answering call...karasawa ciki yayi ya zauna nan kusada ita saida ta gama wayan ya wani kwa6e fuska yana dubanta yace"Mummy am back..Mummy yunwa nakeji wlh ni yanxu duk kin deddena sona"...dan murmushi ta saki tana kallonshi..cikin ‘yan kwanakin nan ta fahimci yana cikin farin ciki..batasan ko sun daidata da yarinyar ba amma she’s happy seeing him like this...sake kwa6e fuska yayi yace"kuma Mummy ko ki tambayeni yanda mukayi da Lamido"..murmushi ta saki tana kama hannunshi tace"ai nasan tunda na ganka cikin farin ciki these days kilan kun gama daidaitawa da ita"..tana rufe baki yace"a ina?..we are still patching things up dai..kawai inaso tasoni koda baikai wanda nake mata ba"...sake damke hannunshi Mummy tayi tace"zata soka inshaAllah..just continue being a good guy"...murmushi ya saki mai kyau yana shafa lallausan gashin kanshi yace"Allahumma Ameen Mummy..I can’t wait to see that"...dan rankwashi Mummy ta kai mashi a kai tana cewa"rashin kunya kou?.."dafe kan yayi yana dan saki kara yace"ouchh..Mummy da zafi fa"..dungure mishi kai tayi tana hararanshi tace"Comot for this place"..murmushi ya kara saki ya wani makale mata kafada...kallonshi kawai tacigaba dayi full of excitement..seeing him like this really gladdens her heart and she prays Allah yasa ya dore har karshen rayuwarshi...Allah ya mallaka mashi yarinyar nan idan har ta kasance alkhairi a gareshi...ganin yanda taketa kallonshi sai ya dan 6ata fuska yace"Mummy wnn kallon fa?.."murmushinta ta fadada tana fadin"am just suprised and impressed..My Bobby is in love i can’t believe this"..murmushi shima ga kara saki yana cigaba da shafa gashin kanshi kaman zaisa kuka yace"Mummy manaaaaa..am shy plss"..daria ta saki sosai kafin tace"ba wani u are shy bayan har rowarta kake mana..tun yaushe nace maka ka sake kawo mana ita mu gaisa amma baka kawota ba"...yana cigaba da smiling yace"zan kawota Mummy inshaAllah..amma dan Allah idan tazo kar kice mata wani abun plss"..murmushi take tace"bakaso ta sani?.."gyada mata kai yayi tareda cewa"not now"..Mummy tace"dont worry she won’t know anything..yanxun dai take these"..ta zaro wasu papers dake bayanta ta mika mashi...amsa yayi yana dubanta yace"Mummy meye su?.."a takaice tace"ur flight tickets"..kallonta yayi da sauri cikin mamakin abunda tace..kafin ma ya tambayi na meye ta sake cewa"to Abuja"..kallonta kawai yake full of surprise..a hankali yace"Mummy badai ke da kanki kikaje airport siyo mana tickets ba?.."harara ta watsa mishi tace"it’s non of ur business..nasan ba son zuwa kuke ba ai shiyasa nayi maku haka..sai kuje ku fara shiri flight dinku is tomorrow by 4"..kallonta kawai yake kafin ya koma kallon tickets din...na gaba dayansu ne including Miemie da Ilham...sbd tsabar mamaki kasa ce mata komai yayi..shi wlh da yaji shiru ta dena mgnr ma yayi tunanin mantawa tayi ashe tana sane ido kawai ta zuba musu...numfashi ya sauke yana cigaba da duban tickets din shidai Allah ya sani ba son zuwa Abujan nan yake ba..sam baison tafiyan shi baima san ta ina zasu fara ba idan sukayi ido da ido da Wazirin shin gaisuwa za’a fara ko kuwa kallon kallo zasuyi a tsakaninsu...itadai Mummy mikewa tayi ta shiga bedroom dinta shima yaja jiki a hankali ya fita daga parlon nata..knn dai gobe i yanxu suna can Abuja tareda Waziri..what the heck shi baisan ma da wane ido zasu kallesu ba wlh..sam baisan ya haduwan nasu zai kasance ba.
Washegari ko fita baiyi ba dan Mummy hanawa tayi..haka ta tsaresu gaba daya kowa ya dauki kayanshi set daya tunda gobe zasu dawo...Bobby na fitowa daga Flat dinshi ta kalleshi from head to toe kafin ta mike zuwa insa yake tana cewa"koma kasa manyan kaya"...kwabe fuska yayi yace"manyan kaya kuma Mummy?.."tace"yes haka nace..hanga dalilinda zaisa ka tafi wajen grandpa dinka haka ba"...kallonta Bobby yake kaman zaisa kuka yace"Haba Mummy kaman wanda zaije wajen surkai?.."kama hannunshi tayi suka koma Flat din nashi tana fadin"komai abunka bazaka tafi a hakaba wlh..kuma idan ma kayan daka dauka na gobe irin wnn ne then ka sake wasu"...kasa cewa komai yayi suna shiga bedroom kawai ya shiga closet dinshi ya sako wani coffee yadi mai taushi ba tareda yasa hula ba ya fito yace"Mummy amma dan girman Allah ba saina sa hula ba koh?.."kallonshi tayi taga yanda yayi kyau saita saki smile kafin tace"da kasan yanda manyan kaya ke maka kyau da ka dena saka wnn suits din wlh..now wuce muje time na kurewa"..ba yanda ya iya haka ya wuce gaba Mummy tabiyoshi a baya...a central parlor suka tadda sauran suma gaba daya sun fito kowa ya gama shiryawa...haka ta hada kansu suka fita zatayi musu rakiya airport..aunty sumy da Mummy da kuma Miemie suna motan Mummy da driver ke tukawa..shi kuma Bobby yana tareda Ilham da Sab shima cikin nashi motan...duk ranshi a 6ace yake sbd tafiyar nan nunawa ne kawai baiyi sbd Mummy...bayan sun isa airport duk dukayi sallama da ita har zasu wuce Bobby ya sake dawowa inda take yana dubanta kaman wanda zaisa kuka yace"yanxu Mummy ke kadaifa zamu tafi mu bari a gidan..dan Allah ni in dawo su su tafi sbd kar a barki ke kadai"..girgiza kai Mummy tayi tana jan cheeks dinshi tace"nafa fada maka ba abunda zai faru ai akwai masu aiki a gidan"...turo baki yayi yace"nidai dukda haka u take care of yourself"..wnn karon rungumeshi tayi gamida manna mishi kiss a forehead dinshi tace"zan kula inshaAllah..Allah ya kaimin ku lafia ya dawo daku lafia"..a hankali ya amsa da Ameen..da sauri Sab ya matso kusa dasu yana cewa"Mummy nima bakiyi hugging dina ba"..bude mishi hannu Mummy tayi yace"come here dan autana"..da gudunshi kuwa ya fada jikinta kafin ta maida hannu ta rungumeshi snn ta dagoshi shima ta manna mishi kiss a goshinshi...daga nan kuma sai Miemie da Ilham suma duk suka dawo tayi musu aunty sumy dai ba tsaye tana kallonsu...Ilham ce ta kalli mamanta snn ta kalli Mummy tace"Mummy to saura aunty"..dungure mata kai Mummy tayi tace"wa yake ta wani aunty...auntyn da ta girma"..daria gaba daya suka saka nan kuma aka fara announcing passengers su zama ready jirgi ya kusa tashi..a gurguje suka sake sallama snn suka wuce itama Mummy ta shiga motanta driver yaja suka koma gida.
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
34
Karfe biyar da wani abu jirginsu ya sauka Nanmdi Azikiwe International Airport Abuja...wani Friend dinshi mai suna Dr Fariq ne yazo ya daukesu daga airport din zuwa Freedom Medical College inda ya ware ma kanshi apartment guda sbd irin wnn lokacin...apartment din na dauke da babban parlor guda daya sai three bedrooms inda shi ya dauki daya Sab ya dauki daya su aunty sumy ma suka dauki daya...gaba dayansu ba wani mai cikakken walwala cikinsu kowa yake kawai yakeyi amma ta ciki na ciki...tunani da kuma zullumin yanda haduwarsu da ‘yan uwan mahaifinsu zai kasance bayan kusan shekaru shidda suke...aunty sumy dai addu’a take Allah yasa karshen komai ke yazo while shi kuma Bobby jikinshi ke bashi ko sunje dinma Waziri ba accepting nasu zaiyi ba har yanxu..kawai ya riga ya sawa kanshi tunda baiyi kokarin sawa a nemosu har tsahon wnn lokacin kilan ba baya sonsu ne..ko kuma bai shirya kar6ansu a matsayin jikokinshi ba...Dr Fariq ne yayo musu takeaway na abinci ya kawo musu dukda basa tareda yunwa...Mummy dake can gida hankalinta gaba daya yana kansu ta kira Bobby tana tambayan ya suka sauka...yace sun sauka lafia sai sunyi sallahn magrib zasuje can asibitin da wazirin yake..dadi taji sosai tareda sa musu albarka..har tausayi yaji ta bashi sbd yanda take mgn..ya tabbata ita kanta tana cikin zullum ko waziri basan amince dasu ba...saida sukayi sallahn magrib kaman yanda yace snn gaba daya suka fito suka nufi asibitinda waziri yake cikin motan Dr Fariq da Bobby ya tuka da kanshi...koda suka shigo cikin asibitin saida gaban kowa ya fadi including Bobby da baisan dalilin faduwar gaban ba...bayan sun fito daga mota suka nufi cikin asibitin da yake nan kaman ba dare ba sbd hasken dake ta ko ina...daida suka tambayi wani sub staff room 105 yayi directing dinsu har zuwa can...a kofar dakin suka tsaya suna kallon kallo an rasa wanda zai fara karfin halin shiga a cikinsu..aunty sumy ce tayi murmushin yake tareda tura kofar a hankali ta shiga da sallama suma duk sai sukabi bayanta...yana kwance kan gado idanunshi a rufe da alama bacci yakeyi..sai wani dan matashi dake zaune kan kujera daga dam gefenshi...kallon kallo aka shigayi tsakaninsu da matashin shi yana musu kallon kamar ya sansu amma ya kasa tuna a ina suma suna mishi kallon saidai ya kasance jika a wajen waziri domin kaf yayanshi sun sansu amd bashida karamin yaro kamarshi...wuri ya nuna musu suka zauna yana kokarin dora murmushi kan fuskanshi yace"sannunku da zuwa"..aunty sumy ta amsa da"yauwa sannu..ya mai jiki?.."yace"Alhamdulillah ya samu sauki"..gyada kai kawai tayi kafin tace"Allah ya kara sauki"..daga nan kuma sai dakin yayi shiru ba wanda ya sake mgn cikinsu...a hankali Bobby ya daga ido yana kallon tsohon da a kallon farko za’a gane jininshi ne sbd kamanninshi daya dauko..mahaifinsu na kama da waziri sosai shima kuma Bobbyn sai ya dauko mahaifinshi...kallonshi kawai yake yana tuna duk abubuwanda suka faru a baya sai yaji ranshi na 6aci..da sauri ya dauke kanshi tareda mikewa tsaye da hannayenshi a aljihu yace"i think we should leave tunda bacci yakeyi da safe sai mu dawo"..babu wanda yayi masa musu cikinsu duk suka mike da nufin su fita sai kawai sukaji am turo kafar dakin wata mata ta shigo sanyeda katon hijab da glass a idanunta...tana dora idanu a kansu ta saki ledan dake hannunta tana zare idanu sosai a kansu bakinta yana motsi alaman she wants to say something...da sauri ta karasa inda suke ta shiga nunasu da finger dinta daya bayan daya har yanxu bakinta bai bar motswa ba amma ko kalma daya yaki fita daga bakin...ta tsayar da idanunta kan Bobby da shima yayi kasake yana kallonta kawai saita rungumeshi hawaye na saukowa fuskanta tace"Bobby is this realy you?..anya ba mafarki nake ba?.."hannunshi yakai shima ya zagayeta dasu snn a hankali yace mata"you are not dreaming"..dagowa tayi tana kallonshi har yanxu bata bar hawaye ba..takai hannayenta tayi cupping fuskanshi dasu tana cewa"my son..where have u been?..ina kuka shiga kuka 6oye nayita wahalar nemanku ban sameku ba?.."kafin yace wani abu ta sakeshi tareda matsawa inda Sabeer shima tayi hugging nashi tightly tana cewa"Sabeer..Sab kaine ka girma haka?..kaine ka zama saurayi haka?..zaka iya tuna ni?.."duk a lokaci daya ta jero mai wadan nan tambayoyin sbd tsabar shock data shiga na ganinsu..bata ta6a tsammanin ganinsu a nan ba..tayi wahalar nemansu na tsahon shekaru amma da yake ita mace ce kuma ba mazauniyar kano ba sai ta kasa samunsu har daga baya ta hakura...shima ta dagoshi tana cupping fuskanshi still tana zubda hawaye tace"baka ganeni ba koh?.."a hankali Sab dake hawaye shima yace"na ganeki"..tace"then wacece ni?.."da sauri yace"Our only aunt...Aunty Munubiya"..yana karasawa ta sake rungumeshi tana fashewa da kuka...su aunty sumy ba gefe suma suna nasu kukan dan hatta Bobby dakeda taurin zuciya yau saida yaji kaman ya zubar da hawayen shima sbd maganganun da take...bayan ta saki Sab saita isa ga aunty sumy...kallon juna suka shigayi kowacce hawaye na tsere a fuskarta ko pump albarka...a tare suka wani rungume juna kowacce tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya...saida suka dauki lokaci mai tsaho haka kafin su sake dagowa suna kallon juna..aunty Munubiya ta saki murmushi da wet face dinta tana dubansu Miemie tace"mu grand kids...haka kuka girma kuma?.."kallonta kawai suke ba wanda yace uffan...hannu ta bude musu tace"come to me kuni?.."ai tun bata rufe baki ba suka karaso da gudu suma suka fada jikinta...shidai wanda ke jinyar Waziri yayi kasake yana kallonsu kaman ya samu movie...hayaniyar da sukeyi ya tada Waziri kawai sai jin tarinshi sukayi..da sauri duk suka karasa inda yake..shi kuma idanunshi na kan Bobby ya shiga kokarin nunashi da hannunshi amma ya kasa...Aunty Munu ta karasa gareshi tana kama hannun nashi tace"Baffa sune..iyalan Attahir dinka ne suka dawo gareka"...har yanxu idanunshi na kan Bobby sai kokarin mgn yakeyi amma ya kasa..a hankali ya dawo da kallonshi ga aunty sumy da Sab kawai sai wani tari ya sake turnukeshi har numfashinshi nayi kaman zai dauke...Bobby da yaga haka baisan lokacinda ya karasa kusa dashi da sauri ta kama hannunshi ba...har yanxu kallonshi wazir yake ya kasa dena kokarin yin mgn dukda breathe dinshi da yake kaman zai dauke..da sauri aunty Munubiya ta fita sai gata ta daw tareda doctor...taimakon gaggawa ya shiga bashi har yanxun hannunshi na rikeda na Bobby daya kasa sakewa...doctor ya samu ya daidaita breathe dinshi snn ya mishi alluran bacci sbd yaga idan ba haka akayi masa ba bazai ta6a dena yunkurin mgn ba and yana bukatar hutu dan haka ya juya garesu yace"you all shoulf go outside plss..he needs to rest bansan ya akayi ma aka barku kukazo har kuka cika dakin ba haka"...ba wanda ya kulashi har ya juya ya fita..suma hada kansu sukayi gaba daya sukayi waje don ya samu enough rest kaman gabda doctor ya fada...suna fita aunty Munubiya tace"amma dai zaku jira har lokacin da zai tashi koh?.."Bobby yace"no zamu dawo safe..yanxu hutu yake bukata"..gyada kai tayi tana kokarin dakatar da hawayen idonta tace"ya kamata mu zauna muyi mgn sosai..a ina kuka sauka?.."aunty sumy tace"Gwagwalada"..zaro wayanta tayi ta mika mata tace"sakamin numberki da safe zanzo inda kuke muyi mgn"..ba musu aunty sumy ta amsa wayan ta saka mata digits dinta snn ta mika mata tayi saving..ta sake mikawa Bobby shima tace ya saka mata nata dan haka ya saka still ta karba tayi saving snn tayi musu rakiya har bakin motarsu tareda alqawin zatazo gidansu gobe da safe su tattauna kafin suzo asibitin...haka suka tafi jikin kowa a sanyaye...gaba daya wani irin feeling sukeji tattare dasu...Aunty Munubiya only sis din mahaifinsu ce..ita kadai ce sis dinshi da suke uwa daya uba daya sauran duk uba kadai suka hada...ko a da can sunsan Aunty Munu bata daya daga cikin wanda suka tsani Mummy dan ko itama Mummyn tana fada...sai yanxu Bobby yaji rashin dacewar abunda yayi at least ita ya kamata su nemeta tunda yasan mai kaunarsu ce kuma bai zama lallai ta iya binciko inda suke ba tunda ita mace ce dole sawa zatayi a bincika mata...for the very first time yaji kaman bai kyauta ba abunda yayi..yaji gaba daya bai kamata ita su kasa nemanta ba duba da kasancewarta qanwar babansu...sai yaji guilty conscience ya rufeshi..tabbas bai kyauta ba abunda yayi mata domin daga yanayin yanda tayita kuka daga ganinsu yasan ba karamin missing nasu tayi ba..kilan ma tayita faman neman inda suke bata gansu ba...har suka karasa gida bai bar tunane tunanen nan ba...suma gaba daya sauran kowa da tunaninda yake dan haka suna karasawa gida kowa dakinshi ya kama yana sake tuntuntuni.
Washegari karfe bakwai ta kira Bobby tace mishi gata nan zuwa gidan nasu..da kanshi ya fita bakin gate ya shigo dasu mota guda itama tayo itada yaranta...a parlor suka zauna gaba dayansu kafin ta shiga kallonsu one by one idonta na cikowa da hawaye tace"why plss?..idan kun kauracewa kowa sbd laifinda akai maku ni me nayi?..meyasa bakuyi tunanin halinda zan shiga ba"..da sauri Bobby yace"Aunty kiyi hakuri dan Allah..it was all my faul..nine na yanke duk wani alaqa daku kuma na hana kowa ya nemeku sbd ciwon abubuwanda akayi mana..nasan bai kamata na hada dake ba amma ina neman yafiyarki on behalf of all of us kiyi hakuri please!.."ya karasa mgn yana hade hannayenshi wuri daya...dan murmushi ta saki da wet face dinta kafin ta yafitoshi da hannunta alaman yazo..ba musu ya taso daga inda yake ya dawo kusada ita..yana zama ta daddage ta rankwashi kanshi tana fadin"this is ur punishment"..dafe kan yayi da sauri yana murmushin jin dadi..at least yasan yanxu ta yafe mishi...aunty sumy ma murmushin takeyi da hawayenta...itama Auntyn Munu bata dena hawayen ba ta sake fadin"ina Mummy?.."Sab ne ya amsada"tana gida"..kallonshi take tanaso tace gida ina?..sai aunty sumy tace"Kano"..kuyawa tayi tana kallonta da mamaki tace"u mean all this while kano kuke zaune?.."aunty sumy ta gyada mata kai alaman yes...tace"ikon Allah..kinga Allah ne kawai baiyi zamu hadu daku ba sbd nima kusan watanmu 6 da komawa Kano da zama"..Bobby yace"yanxu knn kano kuke?.."tace"kano muke..bari inyi introducing dinku wa kids dinku"...da sauri Bobby yace"haba sai kace bamu sansu ba"..ya nuna babban cikinsu da bazai wuce mate din Sab ba yace"ga ma sunan Daddy"..aunty Munubiya tace"umhum.."ya nuna mai bi masa yace"shi kuma wnn Habeeb"..nanma kai ta sake gydawa tana kallonshi...ya nuna ‘yar macen da bazatafi sa’ar Miemie ba yace"ga Nusaiba..wnn kuma itace bansan sunanta ba"...daria sukayi gaba dayansu ganin da gaske bai manta su din ba...Aunty Munubiya tace"ita wnn dama bai zama lallai ku santa ba"..juyawa tayi tana duban yarinyar tace"baby yama sunanki?.."da sauri yarinyar tace"sunana Nadia Usman"...wara idanu sukayi gaba daya jin sunan Mummynsu nema da yarinyar...Bobby ya kalleta yanaso yace da gaske sunan Mummy ta saka ko kuma coincidence ne..kamar tasan me yake shirin tambaya tace"yes sunan Mom dinku nasa mata...inaso ta dauko kyakykyawan hali da hakuri irin na mahaifiyarku and Alhamdulillah ta dauka"..shiru kawai sukayi kowa cikeda Mamaki...ilham da taji yarinyar ta fadi sunanta amma ita baace ta fadi nata ba tace"nima Sunana Nadia Isma’il"..a take suka kwashe da daria jin mgnr nata...Aunty Munu ta janyota jikinta tana murmushi tace"da gaske kema Nadia ne sunanki?.."da sauri Ilham tace"yes amma ana cemin Ilham"..rungumeta Aunty Munubiya tayi tana cigaba da murmushi...daga nan kuma sai labari ya 6arke tskaninsu...kowa ya shiga bada labarin bayan saduwa..farin ciki suke sosai na sake haduwa da juna after six long years...a tare sukayi breakfast daga nan kuma suka nufi asibiti gaba dayansu.
Waziri na zaune tun safe ko bacci ya kasa komawa sai tambaya yake wai da gaske ‘ya’yan Attahir dinshi ya gani ko kuwa dai mafarki ne kaman yanda ya sabayi?..mutum uku daga cikin yaranshi dake wurin dai babu wanda ya bashi gamsashshen amsa don basu san ko su dinne sukazo da gaske ko kuma a mafarkin dai ya gansu shine yake zargin a gaske ne...suna shigowa dakin gaba daya hankalinshi ya koma kansu..kallonsu yake yayinda hawaye ke zarya kan fuskanshi..gabi yake bai masu adalci ba daya kasa nemansu duk shekarun nan amma saidai ba laifinshi bane..babu wanda baisa ya nemosu cikin yaranshi ba amma kowa da labari daya yake dawo mishi cewa ba’a gansu ba..shi kuma ba lafia ne dashi dazaije neman nasu da kanshi ba...yanxu kuma da yake ganinsu gabanshi sai yaga kaman ba gaske ba...da hannu yayi musu alama da suka karasa inda yake...ba musu suka isa suka tsaya jikin gadon nashi...kallonsu yakeyi daya bayan daya yana sakejin kewar mahaifinsu na rufeshi..hannu yakai ya kamo hannun Bobby dake nan kusa dashi muryanshi ba rawa yace"Attahiru.."kawai sai ya rungumeshi yana cigaba da hawaye...ya janyo Sab da other hand dinshi duk ya rungumesu yana zubda hawaye..Sab ma hawayen yake likewise su Aunty Munubiya da Aunty Sumy dake tsaye gefe...Bobby kuwa wani irin different feeling yakeji tattare dashi..bai taba tunanin zasu samu tarba daga wajen waziri balle har yayi kuka sbd farin cikin ganinsu ba...ganin yanda yake kuka kawai ya isa ya gane ba karamar wahala yasha na rashinsu a tareda shi ba..nan take ya sakejin rashin kyautuwar abunda yayi..wani irin tausayi da kuma kaunar kakan nashi suka taru suka cika mashi zuciya..sun dade rungume da juna kafin ya sakesu yana duban Aunty Sumy dasu Miemie suma yace su karaso kusa dashi..suna karasawa haka ya dinga binsu yana runguma ko kalma daya ya kasa furtawa sbd farin ciki..sun dauki lokaci mai tsaho a haka kafin Waziri da har yanxun ya kasa barinsu subar kusa dashi ya shiga neman yafiyar su kan abubuwanda ya aikatawa mahaifiyarsu..ya kuma rokesu da susa mahaifiyarsu itama ta yafe mishi...a take duk sukace sub yafe hadda Bobby da yake sake jin tausayin kakan nasu...yanda yaga yanayi musu ba karamin tausyi ya bashi ba...ya rasa inda zai sanyasu sbd farin ciki duk wanda ya shigo kuwa saiya nuna mishi su a matsayin iyalan Attahir dinshi...uncles dinsu wajen mutum biyar sukazo asibitin and duk cikinsu ba wanda waziri bai nuna masa su yana cewa sun dawo gareshi ba..sbd tsabar farin ciki lokaci daya ciwon daya dade yana fama dashi ya samu saukinshi fiyeda zato dan har hakan yaba doctor dinshi mamaki...koda sukazo tafiya hanasu yayi yace bai gaji da ganinsu ba...haka sukacigaba da zama kowa yana bashi labarin bayan rabuwa...Aunty Sumy da Aunty Munubiya suka tafi gida zasuyi girki su kawo tareda yaran..Sab shima sai yabi Taheer da yayi driving nasu zuwa gidan...ya rage daga Bobby sai kakan nashi a dakin...tambayoyi sosai Waziri keyi mishi na duk abubda ya shafi rayuwarsu shi kuma yana bashi labari daki daki...sunyi nisa cikin labarinsu sosai aka turo kofar Lamido da daddy sai wani yayan daddyn suka shigo dakin a tare...da mamaki Bobby ya daga kai yana kallonsu sai kuma ya mike daga inda yake zaune yana musu murmushi yace"barkan ku da zuwa"..daddy ma kallonshi yayi da murmushi yace"Attahir kana nan knn?.."yace"ina nan daddy..Bismillah ku zauna"..karasawa ciki sukayi suka zauna Lamido da Waziri suka fara gaisawa..baya sun gama su daddy ma suka gaisa da Waziri tareda tambayarshi ya jiki yace jiki yayi sauki...daddy na duban mahaifinshi yace"Baffa wnn shine Proprietor din makarantar su Aysha ai..dan wajen Col Attahir ne"..da mamaki Lamido yace"ikon Allah..yanxu wnn karamin Attahir ne yayi girma haka?.."cikin farin ciki waziri yace"tareda yan uwanshi sukazo tun jiya..ashe duk tsahon lokacin nan suna kano bamuda labari"..gyada kai Lamido keyi yana cewa"ikon Allah knn..Allah ya jikan Attahiru"..gaba daya suka amsa da Ameen..dakin ya danyi shiru kafin Lamido dake duban Bobby yace"kace kasan amaryata knn?.."murmushi kawai Bobby yayi kai a kasa..Lamido ya sake cewa"batajin mgn koh?..nasan kilan kuna can kuna fama da ita"..wnn karon daria ya danyi jin abunda Lamidon da kanshi ya fada still dai baiyi mgn ba...wato ita dai ko yan uwanta ba wanda baisan fitinanniya bace...nan take kuma sai akalar tunaninshi ta koma kacokam kanta yaji duk wani iri yau throughout baiji muryanta ba..ya kamata kuma ya kirata ko don ya bata labarin yau yaga Lamido..hira sosai ya barke tsakaninsu shidai nashi murmushi ne kawai sai idan waiziri ya tambayeshi wani abu ya bada amsa...gaba daya hankali da tunanin nashi sun koma kanta kuma..so yake suyi suyi su tafi shima ya dan samu ya fita waje ya kirata amma basu suka bar asibitin ba sai dab da magrib..bayan ya rakasu yayi sallah masallaci snn ya koma ciki nan kuma ya samu su Aunty Munubiya sun dawo suna cikin dakin...lalla6awa yayi zai fita waziri daya ankara dashi ya dawo dashi wai bai yadda ko nan da can yaje ya barshi ba...haka yayita zaune suna labari duk hankalinshi yayi kanta...sai da kyar suka samu waiziri ya yadda su tafi don da farko cewa yayi saidai Bobby da Sab su zauna su kawan dashi amma sbd ganin wanda ke kwana dashi yazo and bazaiji dadi ba sai suka lalla6ashi tareda alqawarin zasu dawo gobe kafin su wuce kano...ko sanar dashi tafiyan nasu ma basuyi ba sbd basusan kalan rigiman da zaiyi musu ba don sun fahimci yana fama da ita in excess.
Suna kowawa gida ya shige bedroom dinshi yayi wanka sharp sharp ya fito ya saka pyjamas snn ya dauki wayanshi ya kwanta kan gado yana dialing number dinta...kafin ya gama ringing ta dauka cikin muryanta da yake ganin bazai ta6a gajiya da sauraronta ba tace"hello"..lumshe ido yayi ya bude yana jin wani irin feeling tattare dashi a hankali yace"La..mi..do"..tace"sir ina yini"..yace"lafia lau..how are u"..tace"fine"..suka danyi shiru na wani lokaci Bobby baisan lokacin daya furta"i missed u"ba..ta wara idanu sosai kaman yana ganinta tace"sir banji me kace ba"..kai tsaye ya sake cewa"i said i missed u..i missed ur rashin jin mgn"..ta dan turo baki tace"nidai inajin mgn"..murmushi ya saki yana shafa beard dinshi ko ba’a fada ba yasan turo mishi baki takeyi yanxu haka..kawai sai yaji yanaso yaga bakin datake turowan amma babu hali..ita kanta so yake ya ganta ji yake kaman yayi tsuntsu kawai saidai ta ganshi a hostel dinsu amma still babu halin yin hakan...rage muryanshi yayi can kasa yanda bazata jiba yace"i love u..i wish i can tell u"..tace"sir me kace?.."yace"cewa nayi yau na hadu Lamido a Abuja"..ta wara ido kaman yana ganinta tace"Lamido dai namu?.."yace"yea tareda dad dinki sukazo"..tace"amma dai bakace musu nayi wani abun ba koh?.."cikin zuciyarshi yace"nace musu mana..na fada musu kin sacemin zucia"..a zahiri kuma murmushi yayi kafin yace"ke me kike tunanin zan fada musu?."tace"sir ban saniba..kawai dai banso kace nayi laifi sbd nasan Lamido ina komawa gida zai rufeni da fada..kilan ma yace in fito da miji amin aure"..ta karasa mgn tana turo baki...shiko Bobby shiru yayi wani tunanin na darsuwa a zuciyarshi...hakane fa Lamido shine zai bada aurenta tunda yana raye koh..sai yaji inama sun daidaita da ita kawai yacema Waziri yanaso a nema mishi aurenta...yasan kuma bazasu hana ba sbd a yanayin yanda yaga mu’amalarsu ya tabbata ba karamin zumunchi ke tsakanin Familynsu da Familyn Lamido ba...nan take yaji wani kwarin guiwa yazo mishi..zuciyarshi ke fada mishi inshaAllah kaman ya samu auren Lamido ne ya gama tunda yanxu baida wani problem da yake ganin yana iya sawa a hanashi aurenta..problem daya da yake fuskanta yanxu shine rashin sanin actual abunda ke mind dinta..shin tana sonshi ne ko kuwa bata sonshi?.
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
35
Washegari gaba dayansu suka tafi airport bayan gwagwarmaya da akasha da waziri dan cewa yayi fafur bazasu tafi su barshi ba..da kyar da sidin goshi suka samu suka shawo kanshi tareda alqawarin dawowa nan bada dadewa ba...kafin su wuce saida aka zagaya dasu cikin Freedom Medical College suka gani sosai kowa sai santinta yake musamman su Aunty Munubiya da basu ta6a zuwa ba..daga nan airport suka wuce already dama sun siya tickets so suna zuwa duk suka shiga Plane dinsu da is about to flight sbd time din tashinsu yayi...karfe goma da wani abu suka sauka Malam Aminu Kano International Airport..Aunty Munubiya bata yadda ta wuce gida ba tace saita fara zuwa gidansu taga Mummy snn zata wuce..motoci uku ne sukazo daukansu daga airport ciki hadda Mummy data kasa hakuri har su karasa gida..suna haduwa da Aunty Munubiya nan ma suka rungume juna kowaccs tana hawayen tunawa da rayuwar baya..saida aka 6an6aresu daga jikin juna snn suka shishshiga mota suka wuce...ko a mota hiran yaushe gamo sukeyi kowa tana sake neman gafarar kowa dukda cewa ba wanda yayima wani laifi a cikinsu...bayan sun isa gida ma thesame thing ne yaci gaba da faruwa har saida yaran suka koma yi musu daria...Bobby dai samu yayi ya lalla6a zuwa Flat dinshi ya dau car keys dinshi ya fice zuwa FCNM ba tareda sun lura dashi ba..so yake kawai ya ganta ko bai samu yin mgn da itaba its ok amma he really needs to see her...kafin ya karasa College din ya kira Nur ya sanar dashi yanaso ya ganta..Nur yace bashida wani matsala kafin ya karaso ma zai kira mishi ita office dinshi...cikin sauri yake driving har ya karasa college din..yana gama parking ya fito zuwa office din Nur...zaune ya sameta office din suna duba wasu papers itada Nur..baisan time daya saki wani lallausan murmushi yana kallonta ba..seeing her really makes his day..addu’a kawai yake Allah ya karkato da hankalin yarinyar nan zuwa gareshi dan ya tabbata idan bata soshi ba matsala zai samu gagaruma ma kuwa...karasawa ciki yayi ya zauna seat dake opposite to her ita sai a lokacin ma ta ganshi..saita dan saki murmushi idonta a kasa tace"sir good morning"..kallonta kawai Bobby keyi ya kasa amsawa..ta dan dago a hankali ta kalleshi sai taga gaba daya attention dinshi na kanta tayi kasa da idon da sauri tana turo baki..itafa ba son wnn idanun nashi a kanta take ba ya sani amma shine zaiyita wani tsareta dasu salon yasa ta farajin wani iri..kallonta yakeyi sosai kamar yau ne ya fara ganinta..Nur da yaga haka sai ya lalla6a ya mike ya bar musu office din yana kunshe daria...kaman jiran fitan nashi yake ya matso da seat dinshi dab da nata har suna jin kamshin turaren juna..kallonta yakeyi har yanxu kuma baida alamar denawa dan haka Lamido ta runtse ido tanajin yanda gabanta har faduwa yake sbd kallon nan da yake mata..bakin nan kuwa ta gama turoshi tamkar zai tafi Gombe ya barta nan kano sbd tsabar tsinin da yayi...a hankaki yakai hannu yayi cupping fuskanta dasu tareda dora nashi fuskan ya hadeshi wuri daya da nata yana sauke wani numfashi da karfi kaman wanda yayi aikin karfi...sake runtse idanunta tayi and gabanta bai bar faduwa ba...shima nashi idanun a lumshe suke yanajin wani irin abu yana zagaya cikin jinin jikinshi har zuwa zuciyarshi...shi kanshi nashi gaban faduwa yake so yake kawai yajita a jikinshi ko dan yayane amma baisan tayaya ba...a yanda yakeji din nan yasan idan bai samu abunda yakeso ba yana iya zautuwa..wani irin karatu yakeji daga can cikin kwakwalwarshi ya kusa rasa hanyar da zaibi ya biya karatun...da kyar ya daga hannunshi da yayi masifar nauyi ya dorashi kan lips dinta da har yanxun suke a ture tayi wani irin zabura ta kwace face dinta daga hannunshi garin haka kujeran da take zaune a kai yayi baya saura kadan ta fadi yayi azamar janyota ya dawo da ita jikinshi...a tare suka sauke ajiyar zuciya kafin ta shiga kokarin kwace kanta amma ba rikon banza yayi mata ba..ji yake yau idan bai furta mata abunda ke cikin ranshi ba yana iya mutuwa...gaba daya zuciyarshi ta gama narkewa yana kuma da yakinin babu taimakon da zata iyayi mashi matukar bai furta mata what he’s feeling ba...a hankali ya bude baki cikin muryanshi daya canxa completely yace"i..i..l..ov"bai samu daman karasawa ba sakamakon kwace jikinta da tayi da wani mugun karfi har hakan yayi sanadiyyan faduwanta kasa tim kafanta ya bugu da wani table aiko ta kwalla wani mugun kara daya dawo dashi hayyacinshi..ya mike da sauri kafin ya isa gareta cikin kuka tace"don’t touch me"..tsayawa yayi cak yana kallonta da idanunshi da suka canxa launi kaman ba nashi ba...kallon yanda ta rike kafanta tayi tana sakin wani irin kuka yayi nan yake yaji kukan nata na damunshi..sake takawa yayi still bai karasa ba tace"i said stopp..don’t come near me idan ba haka ba zan buga kaina da wnn table din"..da sauri ya tsaya nan inda yake murya a dakushe yake fadin"No..don’t do that plss..am..sorry..i never meant to hurt u"..bata kulashi ba sai kokarin mikewa da take amma ta kasa dan da gaske kafan nata ba karamin buguwa yayi ba..Bobby da yakejin kaman tashin hankalin duniyan nan aka tattaro aka dora mishi ya dan sake matsawa da nufi ya taimaka mata amma wani hadadden kara data saki dole yasashi tsayawa daga nan inda yake gamida runtse idanunshi...ba tun yanxu ba dama yasan ta iya kara sosai yasan kuma idan yace zai cigaba da kokarin matsawa kusada ita tara mishi jama’a zatayi da wnn uban ihun nata...gashi kuma ta kasa mikewa da alama tana jin jiki sosai..hankalinshi yakai kololuwar tashi ya kuma rasa taimakon daya kamata ya bata...Nur ne ya shigo office din ganin abunda ke faruwa ya karasa ciki da sauri yana cewa"Subhanallah meya sameta haka?.."kallonshi Bobby yayi da jajayen idonshi da kyar ya bude bakinshi yace"i..i.."kasa karasawa yayi sbd wani irin sarawa da kanshi yayi kawai sai ya durkushe nan wurin yana sauke numfashi...Lamido dai kukanta takeyi bilhaqqi tana rike da leg dinta..ganin haka sai Nur ya karasa kusada ita shima ya risina nan gabanta yana fadin"Lamido meya sameki?..what happened?.."cikin sheshshekar kuka tace"kafana ne ya bugu..sir bazan iya tashi ba ka taimaka min"..a rikice Bobby ya dago yana kallonta jin abubda tace...yanxu knn ta gwammace Nur ya ta6ata akan shi?..wani irin kishi yaji ya lullu6eshi baisan lokacinda ya mike ya kama hannun Nur dake kokarin taimaka mata ta mike ba kawai sai yajashi sukayi waje...kallonshi Nur yake da mamaki ganin yanda ya wani hade rai yace"meye hakan?.."fuska daure yace"you will not touch her"...idanuwa Nur ya ware akanshi daria na son kufce mishi yace"seriously?..kai meya hana ka taimaka mata tunda kana gani ta kasa mikewa"..a hankali yace"she won’t let me..she is upset sbd na ta6ata and wlh Allah Nur ba laifina bane..kai kanka kasan wnn ba halina bane amma when it comes to her..i dont know what just got into my head..i.."kasa karasawa yayi sbd rauni da muryanshi yayi..idonshi ya sake kadawa yayi jajir ya kamo hannun Nur yace"dan girman Allah kada ka ta6ata Nur..kanayin haka matsala zan samu na sani"...kallonshi Nur keyi duk kuma sai yaji ya bashi tausayi...rike hannunshi yayi shima kafin yace"don’t worry bazan ta6ata ba amma bari inyi mgn da Meena da Billy friend dinta sai suzo su dauketa mu kaita clinic"..kai kawai ya gyada mishi tareda sauke numfashi...lokacin da suka koma office din kuka take wiwi kuma har yanxu bata bar rike kafan nata ba...wani irin sanyi da zafi yaji sun rufeshi all of a sudden..duk wnn abun daya faru laifinshi ne..laifinshi ne daya kasa controlling feelings dinshi har ya janyo mata wnn matsalan...tsoronshi Allah tsoronshi kada taje tayita langabewa har kafan yazo yana rurucewa sbd ya santa sarai da raki da kuma kin magani da allura...duk hankalinshi yayi 6agal 6agal ko mgn ma kasawa yayi...bayan mintuna kadan Billy ta shigo office din tareda Nurse Meena nan suka taimaka mata ta mike kafan nan a dangale ko takashi batayi ba sbd azabar raki...Bobby ya lumshe ido dama yasan za’ayi haka...yanxu Allah kadai yasan adadin tashin hankalin da zata haifar mashi dalilin wnn ciwon...yasan yayi bye bye da kwanciyan hankali idan har ba gani yayi ta koma normal ba...kai tsaye clinic suka nufa da ita Bobby da Nur na binsu a baya...suna kwantar da ita kan bed Nur ya dakko wani muscle pain killer ya mikama Billy yace"ku shafa mata"..ba musu suka amsa suka shiga shafa mata a kafan nata ita kuma sai gursheken kuka take tana cewa da zafi...kallon yanda suke shafa maganin a hankali Bobby yayi yasan indai ba murzashi sukayi yanda zai shiga ciki ba ba abunda zaiyi mata amma kuma shima murzawan yanxu aiki ne tunda ba yadda zatayi ba..ajiyar zuciya ya sauke yana cigaba da kallonsu har suka gama Aysha bata dena kuka ba kaman yanda zuciyarshi bata dena tsalle tana ce mishi bai kyautawa abar sonta ba...suna gamawa Nur ya dakko wani magani ya basu shima aka samu da kyar suka bata tasha snn ta kwanta tayi luf tana sauke ajiyar zuciya kafin a hankali kuma bacci ya sadado yayi gaba da ita...sai a lokacin Bobby ya sauke ajiyar zuciya mai karfi amma har yanxu hankalinshi bai kwanta da yanda yaga kafan har ya fara kumbura ba...ganin yanda duk yabi ya zama wani iri Nur ya kama hannunshi suka zauna ya shiga kwantar mishi da hankali..idonshi sun kada jajir yace"duk ni na janyo mata wnn suffering din Nur..da ban biyewa son zuciyata ba da duk wnn bai faru ba..ji nake kaman zan hadiye zuciya in mutu..ciwo nakeji sosai bazan ta6a yafema kaina idan wani abu ya sameta a dalilina ba"...ya karasa mgn cikeda wani irin rauni da tashin hankali...kama hannunshi Nur yayi yana kallonshi cikeda tausayi yace"ba laifinka bane..dama Allah ya rubuta hakan zai faru so ka kwantar da hankalinka"..girgiza kai yakeyi yace"hankalina bazai ta6a kwanciya idan ina ganinta cikin wnn halin ba"..daga hannun Nur din yayi ya dora saitin heart dinshi yace"ni kadai nasan me nakeji a ciki..ni kadai nasan tashin hankalin da nake ciki"..yana gama mgn ya mike da sauri ya fita daga dakin sbd hawaye da yaji sun cika mashi ido...barin clinic din yayi gaba daya ya bude office dinshi ya shiga tareda kullewa ta ciki..yanada bukatar ya kebe ya zubda hawayen nan ko zai samu saukin nauyin da yakeji acikin zuciyarshi...yana shiga ya wurga kanshi kan sofa kawai sai ya shiga dukan head dinshi da hannunshi yana fadin"why why why plss?..why me"...ya karasa mgnr yanajin wani zafi a cikin heart dinshi..hawayen da yake son su zuba ko zai samu sassauci ma sunki zuwa amma kallo daya zaka mashi ka gano tsantsar damuwa da rudanin da yake ciki...ciwo yake mishi daya kasance sbd shi ta shiga wnn halin..sbd son zuciyanshi..da bai aika abunda yayi ba yasan babu yanda za’ayi garin kwace kanta har taje tana faduwa haka?..ya tuna yanda mahaifinta yace ya yadda tarbiyyarshi shiyasa zai damka amanarta a hannunshi shine yanxu yici amanar tashi haka?.."oh Allah what a monster i have become?.."ya fada a sarari yana cigaba bubbuga kanshi..a takaice saida ya kwashi almost 30 mins yana abu daya kafin ya sarara...bathroom ya shiga ya wanko face dinshi dukda ba kukan yayi ba amma face dinshi ya canxa sosai..yana fitowa ya bude office din ya koma zuwa clinic...zaune ya sameta Billy da wata colleague dinsu na kokarin taimaka mata ta sauki daga gadon ita kuma sai hawaye take yi...wani irin daci yaji har cikin bakinshi yana karasawa ciki ta wani hade rai snn ta dauke kai tana turo baki...murmushin yake ya saki wnda akace yafi kuka ciwo yana kallonsu da kyar suka iya sauko da ita snn suka kama hanyan fita daga dakin...su Billy da basu lura dashi ba sai yanxu suka gaidashi snn suka fice kowacce rikeda hannunta guda suka barshi tsaye yana binsu da kallo...juyawa yayi shima ya fita ya tsaya daga bakin kofa ya rungume hannu yana kallon yanda ko daga kafan da kyar takeyi kilan sbd zafi ne ko kuma sbd tsabar raki ne irin nata...saida yaga sun 6ace ma ganinshi snn shima ya bar wurin ko office din Nur bai komaba ya shiga motarshi ya bar makarantan...a hankali ya tuka kanshi har ya isa gida..yana shiga yayi mamakin ganin har yanxu su Aunty Munubiya nan nan basu tafi ba shidai ya wuce flat dinshi sbd baison ma ya zauna nan cikinsu bare su fuskanci yana tareda damuwa...haka yayita zaune a daki yinin ranan har su Aunty Munubiya sukazo tafia ta aiko a kirashi suyi sallama amma yayi pretending yana bacci yaki fita...har dare bai fito daga Flat dinshi ba ko sallahn magrib da ishaa a nan cikin dakin nashi yayisu sbd fever da yaji ya rufeshi...hankalinshi gaba daya yana kanta so yake yaji halinda take ciki amma tsoron kiranta ma yakeyi sbd yasan ba dauka zatayi ba...yasan Nur ne kadai zai iya taimakonshi a halinda yake ciki dan haka ya danna masa kira..yana dauka ko salam dinshi bai amsa ba yace"Nur inaso inji halinda take ciki plss..kunyi mgn da ita?.."Nur yace"bamuyi ba..ka kirata a waya mana"..da sauri yace"ba dauka zatayi ba..nidai taimako na zakayi zako gida saika kiramin ita a wayanka..inaso inji ya jikinta"...ajiyar zuciya Nur ya sauke kafin yace"shknn gani nan zuwa"..da sauri Bobby yace"nagode sosai friend..nagode"..Nur ajiye waya yayi yana mamakin wnn so da Bobby kema Lamido haka?..duk yabi ya koma kaman wani soko sbd soyayya...shi kanshi daxu ba karamin tausayi ya bashi ba...yaji inama Lamido zata amince ta aureshi kawai a wuce wajen...keys din motanshi ya dauka ya fita daga gidan...su Mummy na zaune parlor lokacinda ya shigo tabishi da kallo kawai..tun daxu ta fuskanci akwai abunda damun Bobby zuba ido kawai tayi taga gudun ruwanshi and wnn zuwan na Nur ya sake tabbatar mata da lallai ba lafia ba...ko zama baiyi nan parlon ba kawai ya gaishesu ta wuce ciki Aunty Sumy da kanta saida tayi mamakin hakan...a kwance ya samu Bobby har yanxu eyes dinshi basu dawo normal ba..yana ganinshi ya mike zaune shima Nur din karasawa yayi kusa dashi ya zauna snn ya shiga kiranta yasa a speaker...har ya gama ringing baa dauka ba ya sake kira wnn karon yaji an daga amma maimakon ita sai yaji muryan Billy na fadin"bacci takeyi sir"..Nur yace"ya jikin nata?.."Billy ta juya ta dan kalli yanda kafan har ya fara swelling tace"sir kumbura kafan yakeyi..yanxu ta gama kuka sai da kyar muka samu bacci ya dauketa"..ba Bobby ba shi kanshi Nur din hankalinshi tashi yayi da sauri yace"i will get back to you"..daga haka ya kashe wayar yana kallon Bobby daya dafe head dinshi da hannu bibbiyu yana jujjuya kan cikeda tashin hankali yace"Nur na shiga uku..zuciyata bugawa zatayi wlh"..da sauri Nur ya kama hannayen nashi ya rike tareda fadin"ba abubda zai faru inshaAllah..ka kwantar da hankalinka yanxu zanje in nemi doc saratu muje can hostel din ta dubata"..mikewa yayi da sauri har wani juwa ke neman daukanshi yace"muje ka kaini in ganta plss..hankalina bazai kwanta ba idan banga halinda take ciki ba"..kamashi Nur yayi ya zaunar dashi yana dubanshi yace"relax dan Allah..kaga yanda jikinka ke rawa kuwa?..kaima kana bukatan medication sbd haka kasha magani ka kwanta ka huta ni zanje inyi duk abunda ya kamata ayi mata"..tun kafin ya rufe baki Bobby ke girgiza kai yace"u won’t understand..kona zauna hankalina ba kwanciya zaiyi ba..i need to see her"..shiru kawai Nur yayi yana kallon yanda yake mgn da kyar sbd tashin hankalin da yake ciki...basu san sanda Mummy ta shigo ba jin mgnrta sukayi kusa dasu...Bobby na daga ido daya ganta kawai sai ya mike tsaye da sauri ya fada jikinta murya a raunane yace"Mummy inaso inje in ganta plss..zuciyata bugawa zatayi"...da mamaki Mummy ke kallon Nur tace"Nuru meya sameshi haka?.."a nustu Nur ya bata labarin iya abunda ya sani itama nan take taji nata hankalin ya tashi..kada dai ace Bobby wani abu yaje yayiwa yarinyar mutane fa...dagoshi tayi daga jikinta tana kallonshi..tambaya take son mishi kan abunda ya haddasa faruwar haka amma sai ta kasa sbd tsantsar tashin hankali data karanto a fuskanshi da kuma yanda idanunshi suka juye lokaci guda tasan tsaf zuciyan nashi zai iya bugawa kaman yanda fada..batayi gaddama ba ta kalli Nur tace"kaje dashi ya ganta..snn duk halinda ake ciki ka kira ka sanar dani and make sure shima kayi mishi treatment sbd zazza6i ne sosai naji a jikinshi"...kallonta Nur yake kafin yace"amma Mummy shima yana bukatar hutu fa"..tace"idanma bakuje dashi hutun da muke so yayin ba samun yinshi zaiyi ba..banason zuciyar nashi ya samu matsala kaman yanda nace kuma nasan halinshi muddin baa kaishi ya gantan ba yana iya samun problem"..gyada kai kawai Nur yayi snn ya kama hannun Bobbyn suka fita...kwace hannunshi yayi daga na Nur yana cigaba da tafiya da kanshi gamida tattaro duk wani sauran jarumta da karfin halin da sukayi mashi ragowa ya dorasu bisa kanshi snn yacigaba da tafiya har zuwa inda Nur yayi parking..da kanshi ya bude front seat ya shiga shima Nur ya shima driver seat snn ya tada motar suka dauki hanyan FCNM..zuciyarshi sai bugawa takeyi sbd baisan me zai tarar a wurinta ba amma ya gwammaci duk wani wulakanci da zatayi mishi akan dai yayi zaune a gida batareda yazo yaga halinda take ciki ba..gani yake kaman Nur ba tafiya yakeyi ba don bai ta6a ganin nisan college din ba irin na yau...suna shiga makarantan direct suka wuce hostel nan ma Bobby yaga nisan hostel din kaman yau ya fara shigoshi...saida sukazo daidai gate na female hostel Nur yayi parking snn ya sake dialing number Lamido...Billy ce ta sake dagawa yace"gamu hostel din naku zaki iya fito da ita?.."juyawa Billy tayi ta kalli Aysha dake rikeda kafan tana sauke ajiyar zuciya cikin bacci itama kaman zatasa kuka tace"sir bazan iyaba..bacci takeyi tun daxu ni bansan yanda zanyi mata ba"...Nur kashe wayan yayi yana duban Bobby daya gama jin duk abubuwanda Billy ta fada...daya daga cikin matrons sukasa akayo musu mgn da ita...ta bada sanarwan zasu shigo hostel din snn ta dawo tayi musu jagora har cikin apartment din da yayi tsit sbd kowa ta shiga daki sbd sanarwar da akayi musu...kai tsaye dakinsu suka nufa Bobby najin each taku na kara masa adadin tashin hankalin akan wanda yake ciki already.
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
36
Matron da Billy ne suka fara shiga dakin snn Nur shi kuma Bobby ya shiga daka karshe...har lokacin bata dena sakin ajiyar zucia cikin baccin da take yi ba...a hankali ya karasa inda take hannayenshi zube a aljihu ya tsaya kusada gadon yana kallonta tun daga fuskanta da yayi jaa as a result of kukan da tayi har zuwa legs dinta da rigan jikinta ya danyi sama kadan sai fair skin dinta daketa glowing...kallonta kanta yayi shima ya ganshi a bude duk gashinta a waje kawai sai yaji ranshi ya baci..kan wane dalili zasu barta a haka tunda sunsan zasu iya shigowa har inda take..kawai sun bar jikinta da gashinta a bude gashi nan Nur yana ta kallo abunshi..kallon Billy yayi da face dinshi dayaji kaman shi yake daure kanshi da kanshi a takaice yace"batada hula ne?.."da sauri Billy tace"sir da kanta ta cire wlh..wai bazata iya bacci dashi ba"..yana sake dinke fuska yace"shi kuma jikinta da kuka bari a bude fa?.."kallon jikin nata tayi da sauri tanaso taga inda suka bari a buden sai taga rigan ta ya danyi sama..batace dashi komai ba ta karasa ta janyo mata rigar har kasa snn ta dauki hulanta data yar nan kasa shima ta shiga kokarin zurawa a kanta daidai lokacin kuma ta dan bude ido snn ta sake mai dashi ta rufe..Billy na gama sa mata hulan takai hannu zata cire murya a cushe Bobby yace"idan kika cire hulan nan sai ranki ya 6aci wlh"..bude ido tayi da sauri tareda mikewa zaune tana kallonshi...ta dauka a mafarki taji muryanshi amma sai taga da gaske shi din ne a gabanta..to me kuma ya kawoshi bayan abunda ya gamayi mata daxu..daure fuskanta tayi ta wani kauda kai gefe tana harare harare..shima ya daure nashi fuskan dan yasan idan ba haka yayi mata ba tsaf zata sake cire hulan ta bar gashi a bude tunda ba hankali ne ya isheta ba..Nur dai na tsaye gefe yana kallon ikon Allah..mamaki yake na ganin yanda Bobby ya wani hade rai yana mata fada kaman ba shine yake kokarin sa mishi kuka ba daxun sbd ita ba..wato har yanzu dai wnn ki fadin nashi yana nan baije ko inaba..idan ba haka ba why kaida ke dab da shiga matsala sbd son yarinya kuma still kanada kafin hali daure mata fuska haka...karasawa yayi ya durkusa nan kusa da ita yana kallon legs dinta dake nan kan gadon yanaso ya gane wadda take ciwon a ciki amma ya kasa..daga ido yayi ya dan kalleta sai kuma ya kawar da kan nashi jin wani bakon abu dake zagayawa cikin jikinshi..duban nashi ya maida ga Billy kafin yace"wanne kafan ne yake ciwo?"..a hankali tace mishi"na dama"..bai sake cewa komai ba ya juya yana kallon kafan damar nata..ganin bai ganin komai sai yakai hannunshi a hankali da nufin ya dago kafan Aysha ta saki wani irin kara tana fadin"Noo"..kallonta kawai yayi baice komai ba sai kuma ya mike still yana duban Billy yace"ki bata hijab tasa muje asibiti"..wara idanu Aysha tayi jin abunda ya fada idonta har ya cicciko da hawaye tace"nidai bazanje asibiti ba wlh..ni bazaa yi mun allura ba banaso"...kallon Nur Bobby yayi cikin sigar ka taimaka mun...Nur ya saki murmushi tareda karasawa inda take yace"Lamido ba allura za'a maki bafa..duba kafan kawai za'ayi ko da akwai matsala ta ciki"..yana rufe baki tace"nidai dan Allah banason zuwa sir..bazan iya takawa ba"..kallonta kawai yakeyi rungume da hannu ita kuma sai tayi kasa da ido tana goge tears dinta tace"to zanje..amma dan Allah banda allura wlh ciwo yakemun"..Nur yace"baza'ayi maki allura ba inshaAllah..yanzu matron da Billy zasu taimaka maki ki mike tunda bazai iya tafiya ba"..batace komai ba sai hawaye data cigaba dayi..tsoro takeji kar suje suyi mata allura ita dai..a muguntan Dr Bobby tasan wlh da kyar idan baiyi mata allura ba tunda baida imani...Billy ce ta dauko hijab ta saka mata snn suka kama hannunta itada matron din don fita da ita waje...taku daya ta iyayi ta saki wani kara da saida Bobby yaji shi har cikin zuciyarshi...nan da nan saiga hawaye a fuskanta ta shiga kokarin durkushewa nan kasa sbd azabar zafi da taji har cikin bones dinta...girgiza kai kawai take murya can kasa tace"bazan iyaba"..kallonta duk suka tsaya yi harda Bobby da yakejin kukan nata har can cikin ranshi..ji yake kamar yaje ya sungumeta yayi waje da ita amma ba halin yin haka...sai da kyar da taimakon Billy suka samu ta yadda ta mike suka riketa har zuwa inda sukaƙi parking...kafin su karasa Nur ya bude musu kofa dan haka suna zuwa suka Sanya ta ciki Billy ma ta shiga suma suka shiga snn Nur ya tada motar suka tafi...Bobby dake zaune front seat jingina kanshi jikin kujeran yayi tareda lumshe idanu..jin kukan nan nata yakeyi har cikin zuciyarshi yayinda wani irin zafi da kunchi suke sake rufe shi..Allah kadai yasan yanda yakeji nunawa ne kawai baiyi amma yana cikin matsala gagaruma ma kuwa...kasa cigaba da hakuri yayi ya juya yana kallon yanda take rikeda kafan tana kuka..murya can kasa yace"kukan ya isa haka dan girman Allah"..ko kulashi ba tayi ba ta cigaba da kukan ta...a takai ce har suka isa Freedom bata bar kuka ba...Bobby duk ya rikice ya tasa inda zai tsoma kanshi yaji dadi..Nur na gama parking duk suka bude mota suka fito banda ita da ko motsawa ba tayi ba...Billy ta zagayo ta bude mata kofa tareda kamo hannunta tace"ki daure mu karasa ciki"..rike hannun nata tayi snn ta sakko da kafan a hankali sai kuma ta gagara mikewa..Nur dai na tsaye yana kallonsu shi kuma Bobby ganin sake bata musu lokacin take kawai ya karasa wurin baiyi wata wata ba ya daga ta cak ya nufi cikin asibitin da ita..sai ihu taka tana ita ya sauketa amma ko tanka mata baiyi ba har ya karasa office dinshi su Billy na binsu a baya..Nur ya karasa ya bude office din suka shiga..kai tsaye ya direta kan gadon dake nan cikin office din fuskan nan a daure kamar bai taba dariya ba...yana ajiye ta ya bude wani drawer ya dakko wani muscle pain killer ya ajiye kan trolley snn ya shiga bathroom ya zuba ruwa cikin wani bowl mai zurfi ya hada da towel dan karami snn ya dawo dakin..daga Nur har Billy kallonshi kawai suke ba wanda yace kala..kujera ya janyo ya zauna nan kusada ita snn ya zaka towel din cikin lukewarm watare daya debo ya matseshi snn ya kama kafan nata ya rikeshi da kyau yanda bazata iya kwacewa ba ya shiga danna mata towel din a wurin..banda ihu da musu mutsu ba abunda take amma ta kasa kwace kafar daga hannunshi sbd rikon da yayi mata bana wasa bane..danna mata kawai yakeyi ba tareda ko kallonta yayi ba sbd gudun abunda hakan zai haifar mashi..yasan idan ba haka yayi mata ba ba bari zata yi ayi mata abunda ya dace ba and Allah ya sani bazai taba samun sukuni ba idan ba gani yayi kafan nata ya warke gaba daya ba..idan zai biye ta zuciyarshi nan ma bazai iya mata abunda ya dace ba kuma shidai akan ya bari wani ya tabata gwara shi yayi mata duk abun daya kama ta idan yaso daga baya sai yayi aikin rarrashi dan dai yasan rigima ne zai sashi kamar ba gobe..tunda ya fara bai saurara mata ba sai da ya tabbatar kafar ya gasu snn ya kyaleta..ya dauki towel da bowl din ya maida su bathroom ya dawo sai kuma ya dauki maganin da zai shafa mata a kafar yana kallonta..kuka take yi sosai har numfashinta na seizing kamar zai dauke..ga wani uban zufa data hada sharkaf kaman wanda aka gasata a oven..tausayinta yaji ya kama shi ganin yanda take kuka yasan dole zataji zafi amma ya zaiyi?..shima ba a son ranshi yayi mata haka ba babu yanda zaiyi ne kawai..janyo kujeran yayi a hankali ya zauna still yana kallonta duk sai yaji ya kasa aikata komai..juyawa yayi ya kalli Nur wai ko zai taimaka mashi amma sai yaga shi dariya ma yakeyi abun shi sai kuma ya juya ya fita daga office din...Billy ma ba tayi wata wata ba tabi bayanshi don Allah ya gani bazata iya zama nan ciki ba...juyawa yayi yana kallonta suna hada ido ya dauke nashi da sauri ya shiga matsa maganin a hannunshi..sam baison wnn raunin dake kokarin dakatar dashi ne...runtse ido yayi ya bude snn yayi watsi da raunin dake dake kunno mishi kai ya kamo kafan nata a hankali zai shafa maganin kawai sai yaji ta kanakameshi tana sakin wani marayan kuka..lumshe ido yayi yanajin wani irin yanayi a cikin jikinshi...wani irin weird feeling da bai taba tsintan kanshi ciki ba..cikin muryanta da bai fita sosai tace"sir dan Allah..dan Annabi kayi hakuri"...lumshe ido ya sakeyi yanajin zuciyarshi na wani irin tattarewa ya cunkushe can wuri daya yana bugawa da mugun karfi...a hankali yakai hannunshi ya zagaye bayanta dasu bakinshi saitin kunnenta yace"am..sorry..plss"gyada kai kawai takeyi tana cigaba da kuka tace"toh bazaka shafamin ba koh?.."dagota yayi daga jikinshi yayi cupping fuskanta yana kallon cikin idonta yace"hakan bazai yiwu ba Aysher..kiyi hakuri a shafa maki ko yayane zakiji sauki"..girgiza kai ta shiga yi tana cigaba da hawaye tace"dan girman Allah No..mutuwa za.."bata karasa ba ya rufe mata bakin yana girgiza kai duk ya gama goge maganin hannun nashi a jikinta...kamata yayi ya kwantar da ita kan gadon snn ya sake matsa maganin a hannu yayi saurin kama kafar ya shiga murzawa a hankali..banda kuka da ihu ba abunda Lamido take har wani shidewa take sbd azaba shi kuma bai saurara mata ba saida ya tabata maganin ya shiga ciki snn ya ajiye kafar..har yanzu kuka takeyi tana sauke ajiyar zuciya shi kuma ya kama hannunta a hankali ya sake cewa"am..so..sorry love"..ko sauraranshi ba tayi ba ta kwace hannunta tana cigaba da kuka shi kuma yayi tagumi kawai yana kallonta..Allah kadai yasan yanda kukan nan nata ke daga hankalinshi..ita kanta da tasan yanda yakeji idan tanayi da batayi ba ko dan sbd shi...haka yayita kallonta tana kuka da yayi yunkurin taimaka mata zatace bataso..duk tabi ta sake daga mishi hankali da kukan nata..saida bacci ya dauketa snn ya sauke ajiyar zuciya..mikewa yayi daga inda yake zaune ya leka ya tabbatar baccin tayi da gaske snn ya gyara mata kwanciya a hankali yanda bazata tashi ba..lumshe ido yayi yakai lips dinshi forehead dinta ya manna mata peck a hankali murya can kasa yace"get well soon love..i love you"..daga haka ya gyara mata kafar snn ya janyo kujeran dab da ita ya zauna tareda rike hannunta cikin nashi ya dora kanshi gefen gadon shima daga haka bacci ya sadado yayi awon gaba dashi.
Nur na barin office din dama kai tsaye inda ya ajiye motarshi ya nufa ya bude ya shiga ciki sai ga Billy itama ta karaso ta dan langabe kai tace"sir nima ka ajiyeni hostel plss"..kallonta yayi kafin yace"why?..bazaki bari ku koma tareba?.."da sauri tace"nasan proprietor zai dawo da ita sir dan Allah ka mai dani"..bai sake cewa komai ba ya bude mata motar yace"to shigo"..ba musu ta shiga ciki Nur ya tayar da motar suka fita daga asibitin.
Karfe sha daya da kusan rabi Lamido ta shiga bude idonta a hankali har ta waresu fes akan Bobby da har yanzun kanshi ke kife nan kusada ita yana nashi baccin..zare idanun tayi da kyau tana kallonshi da mamaki ganin ya wani kwakwume mata hannu ya rike cikin nashi..daddagewa tayi ta kwace hannun nata tana zabga masa harara kamar idonta zasu fadi kasa..daidai lokacin shima ya farka tareda dago kanshi a hankali sai yaci karo da nata idon tana hararanshi...baice komai ba ya mike da sauri ya fada bathroom..wanko face dinshi yayi ya fito sai yaga ta hade kai da gwuiwa kamar zatayi kuka...da sauri ya karasa inda take ya zauna nan gefen gadon yana dubanta a hankali yace"what again?.."dagowa tayi tana kallonshi fuska daure tace"ni ka mai dani hostel"..kallonta ya tsaya yi for some secs kafin ya hada hannayenshi waje daya in a pleading tone yace"nace fa am sorry..da gaske bazan kara ba kiyi hakuri plss"..batace komai ba sai juya mishi baya da tayi zata fara hawaye yace"idan Allah noo..please am sorry..ki yafemin"..goge hawayen tayi kafin ta juyo ba tareda ta kalleshi ba tace"to ka mai dani hostel nidai"..yace"zakiyi hakuri ki dena fushi?.."gyada mashi kai tayi..da sauri yace"thank u so much"..tana turo baki tace"kuma kada ka sake tabani nidai"..yace"ban karawa inshaAllah..ki tayani da addu'a"..da mamaki ta kalleshi tace"addu'an me?.."shiru kawai yayi yana kallonta dan baisan yaushe mgnr ya fito ba..a hankali yace"kafan yayi sauki?.."still kai ta daga mishi tana cigaba da turo baki shi kuma sai yayi kasake yana kallonta kaman wani soko..kallonta yakeyi full of love and affection..yarinyar na burgeshi fiyeda tunanin mai karatu..komai tayi burgeshi yake sai yaga tana kyau da duk wani abu da tayi shiyasa yake kishinta sosai...a yanda yake kishinta shi ko cewa za'ayi babu wanda zai na kallonta duk dunia sai shi kadai so zaiyi amma yasan hakan ba mai yiwuwa bane...agogon hannunshi ya duba yaga its almost 12 and Allah ya sani yana tunanin yanda zai maidata hostel cikin daren nan dan yasan Nur da kyar idan ba tafiya yayi ba..dagowa tayi ta kalleshi zata sake mgn wayanshi dake cikin aljihu ya fara ringing..ya zaroshi da sauri ganin Mummy ke kira yayi picking tareda kaiwa kunne..a daya bangaren Mummy tace"kana kina Bobby?..ya jikin nata?.."yace"da sauki Mummy"..tace"ka tabbata da sauki ba wani problem din?.."yace"yes Mummy"..sai kuma ya juya yare zuwa igbo yace mata"Mummy babu mota hannuna and inaso in maidata hostel yanzu..Nur ya wuce tun daxu"..Mummy tace"saidai in turo Sab ya kawo maka..amma why not ka bari ta kwana asibitin sbd a sake tabbatar da samun saukin nata..kuma ga dare yayi"..ajiyar zucia ya sauke yana kallon Aysha da tayi masa kuri da ido tana kallonshi jin ya wani canxa yare cikin ranta tace"dan kyar idan ba gulamana yakeba wlh..inyamurin banza"..ba tareda ya dauke idonshi daga kanta ba yace"bazata yadda ba Mummy..nima kaina ba son zuwa hostel din nasu nake da daren nan ba amma idan ban maidata ba daga min hankali zata yi nasani"..shiru yaji Mummy tayi kafin can tace"ko zaka kawota nan gida ta kwana zuwa safe ka maidata hostel din?.."shirun shima yayi kamar me nazari yace"anya kuwa zata yadda Mummy?..rigima zatai tayi wlh"..dan murmushi Mummy ta saki jin abunda ya fada kafin tace"ba rigiman da zatai inshaAllah..if tana kusa ka bata wayan muyi mgn"..bai sake cewa komai ba ya mika mata wayan yana dubanta a hankali yace"My Mom..wants to..talk to u"..batayi musu ba ta karba tana turo baki tasa wayan a kunne..Mummy tace"daughter ya jikin naji?.."da sauri tayi kasa da kai kmr Mummy na ganinta tace"Mama ina yini"..Mummy daketa faman smiling tace"lafia lau daughter..ya jiki?.."tace"Alhamdulillah"..Mummy tace"MashaaAllah..dama ce mishi nayi ya kawoki gida sbd dare yayi bai kamata yaje hostel dinku yanzu ba..snn ya sake duba kafan naki to make sure ba wani problem kuma..hope bazaki ce aah ba?.."Lamido tayi shiru tana tunanin amsar da zata bata..gani tayi gwara ta kwana gidan nasu akan dai ta kwana asibiti..afterall ba daki daya zasu kwana ba dan haka bazata damu kanta ba...saida Mummy ta sake mgn snn a hankali tace"toh Mama"..Mummy tace"nagode sosai daughter Allah miki albarka..yanxun zan turo Sab da mota yazo ya dauko ku"..Aysha tace"toh"..daga haka kuma Mummy ta kashe kiran..ajiye wayar tayi tana kallonshi kama zatasa kuka tace"shine zaka hadani da mamanka koh?.."murmushi ya saki kafin a hankali yace"am sorry"..turo baki kawai tayi ba tace komai ba..shi kuma sai ya cigaba da kallonta before saying"kinci abinci?.."banza tayi mashi kamar bataji ba..ya sake cewa"Aysher am talking"..nan ma shiru ba mgn dan haka ya dan daga murya yace"Lamidooo"..juyowa tayi a fusace tana kallonshi tace"ni banaso"..kmr wani abun tausayi yace mata"am sorry tou..zakici abinci?.."ta girgiza kai alamar no snn ta sake komawa ta kwanta..shima baice mata komai ba sai kallonta kawai da yakeyi kamar yau ya fara ganinta...after like 20 minutes Sab ya iso asibitin bai shigo ciki ba ya kirashi a waya ya fada mashi ya karaso dan haka ya mike ya isa inda take bayan ya tattaro mata takalmanta dake kasa yace"get dawn mu tafi..ya iso"..ba tace komai ba ta sauka daga gadon ta zura takalmanta snn ta shiga takawa a hankali sbd zafi da taji kafan na mata..daxun da yake kwance take sai bataji ciwon komai ba amma yanxu zafi takeji sosai saidai bai kai na daxun ba tunda tana dan iya takawa...ita ta wuce gaba Bobby na binta a baya har suka fita waje..ko yaya ta danyi kwakwaran mosti sai yaga kaman faduwa zatayi bai dai yi kokarin riketa ba har suka iso parking lot..Sab na hangosu ya fito ya bude musu motar..tana karasowa ya nuna mata front seat yana fadin"sannu"..wani harara Bobby ya sakar masa kafin ya bude back seat ya zurata ciki shi kuma ya shiga front seat din Sab dake murmushi ya shiga driver seat snn ya tayar da motar suka tafi...baya cikakken minti biyu bai juya ya kalleta ba..gaba daya hankali da zuciyarshi suna gareta..gani yake kmr wani abu zai faru da ita idan baya gani shiyasa yake juyawa akayi akayi..Sab dai driving dinshi yakeyi amma a karon farko yau yaga wani irin canji tattare da yayan nashi kuma dukda Mummy bata sanar dashi wacece Lamido a wurinshi ba shi ya gama tabbatarwa kanshi matsayinta sbd wnn special attension da Bobby yake bata bana wasa bane..ba ko wane ordinary mutum ake bama wnn attension din ba sai mutumin da ake mutuwa so da kauna shi kuma ya tabbata Uncle Bobby son yarinyar nan yake...haka har suka karasa gida ba wanda yace tak a cikinsu sai Bobby daketa faman juyawa yana ganin halinda take ciki sai kace wadda take labour...Sab na gama parking ya bude mota ya fita shima Bobby ya fita snn ya zagaye ya bude mata kofa yana dubanta a hankali yace"to sauko"..ba musu ta fito daga motar tana wani dangale kafa kmr mai karaya a jiki..taku daya biyu tayi sai ta koma da sauri ta zauna cikin motar da bai riga rufe kofar ba tana girgiza kai idonta har sun ciko da hawaye tace"bazan iyaba"..kallonta kawai Bobby keyi yana mamakin taki irin nata..durkusawa yayi nan inda kafan nata yake yana kallo shidai baiga wani alamun har yanzu yana ciwo ba tsabar langwai ne kawai irin nata..shi baisan yanda za'ayi duk ranar da akace ga Lamido a labour room ba..kilan saita daga hankalin kowa kafin ta haihu..tunanin haka ya sashi sakin murmushin da bai shirya masa ba kafin ya kama kafan a hankali ya shiga tofa mata addu'a akai ita kuma ta wani lumshe ido tana jin abunda yakeyi...saida ya dauki almost 5 mins yana mata addu'a a kafar kafin ya gama..ya ajiye kafar tareda mikewa yana dubanta yace"to yanxun ki gwada mu gani nasan zaki iya"..ba tace komai ba ta sake sauka daga motar ta shiga takawa a hankali kmr mara laka a jiki..shi kuwa murmushi kawai yakeyi yana bin bayanta cikin ranshi yana jinjina tsananin raki irin nata..yasan da baiyi mata yanda yayi daxun ba da wlh haka zatayi ta zama kafar yana sake rurucewa shi kuma tana daga mashi hankali amma da bai bari raunin da yake dashi yayi tasiri a kanshi ba yayi mata abunda ya kama ta ai gashi yanzu har ta mike tana taka kafar...har suka shiga parlor bai dena kallon yanda take tafia yana sakin murmushi ba..Mummy da Anty Sumy dake zaman jiransu a parlor suna ganinsu duk suka mike aunty Sumy tayi saurin kamota ta karaso cikin parlorn da ita tana cewa"sannu Aysha"..Mummy ma bayan sun zauna tace"sannu daughter"..murmushi kawai Aysha tayi tareda dan dukawa tace"Mama ina yini"..Mummy tayi saurin mikar da ita tana fadin"lafia lau..ya jikin maki?.."kai a kasa tace"naji sauki"..Mummy tace"toh Allah ya kara sauki"..tace"Ameen"..sai kuma ta juya tana gaishe da aunty Sumy..itama ta ansa da ta bayanta ya jiki tace da sauki..Bobby dai na zaune yana kallonsu feeling relieved sbd ganin da gaske jikin nata yayi sauki..shi kanshi yafi son ta kwana a nan din yanda ko wani matsalan zai tashi cikin dare bazai rasa abunda zaiyi ba unlike in tana hostel da bai zama lallai ma yasan halin da take ciki ba..Mummy ce ta dubeshi ganin yanda yake smiling tace"ya jikin naka kaina?.."murmushi kawai ya kara saki maimakon ya amsa mata sai cewa yayi"Mummy ba taci abinci ba"..yana rufe baki Lamido tace"banajin yunwa fa"..Mummy tace"ya kamata kici wani abu kafin ki kwanta..Sumayya shiga kitchen ki hada mata ko tea ne tasha bari na shiga da ita ciki tayi wanka"..Anty Sumy ta mike zuwa kitchen ita kuma Mummy ta kama hannun Aysha suka nufi flat dinta...other bedroom dinta da ba amfani takeyi dashi ba ta shiga da ita ta ajiyeta kan gado ita kuma ta shiga bathroom ta hada mata ruwa mai dan zafi ta fito mata dasu towel da komai da zatai amfani dashi snn ta fito tana dubana tace"toh shiga kiyi wanka zakiji dadin jikin ki"..ba tace komai ba ta mike zuwa bathroom din Mummy tabita da kallo tana murmushi..zuwa yanxu ta tabbatar ita din farin cikin Bobby ce shiyasa a kullum addu'anta bai wuce Allah ya karkato da hankalinta gareshi ba...tana kokarin fita daga sakin aunty Sumy ta shigo da tea da omalet ta ajiye sai kuma ga Bobbyn nan shima ya shigo hankalinshi kan Mummy yace"Mummy batada kayan sawa ko in fita in samu mata wani kayan yanxu?.."kama hannunshi Mummy tayi tana murmushi tace"ka kwantar da hankalinka bazata rasa kayan da zatasa ba a gidan nan"..murmushin shima yakeyi kafin yace"nagode sosai Mummy"..ta sake kama daya hannunshi tace"sai yanxun nake sake tabbatar da cewa my son is in love..Allah ya karkato da hankalinta gareka"..ya rungumeta yana cewa"Ameen Ameen Mummy na..wlh ina sonta sosai..ni kaina bansan irin son da nakeyi mata ba"..shafa kanshi kawai Mummy keyi tana murmushi...Anty Sumy da tun daxun take kallonsu tace"ina ganin wariyar launin fata a gidan nan"..harara Mummy ta wata mata ita kuma ta fita daga dakin tana dariya...Mummy ta dagoshi daga jikinta tace"oya kaje ka samu kayi wanka kaima sai kaci abinci"..baiyi mata musu ba ya juya ya fita daga dakin itama Mummy ta fita don samo mata kayan da zata saka.
U people should include me in ur prayers plss..am seriously sick😣😢bana son nayi keeping naku waiting shiyasa nayi wnn amma if kun jini shiru gobe kuyimun uzuri plss...ina gama warwarewa zuwa jibi zaku jini..thanks and love u all❤️
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
37
Yana shiga bedroom dinshi direct ya wuce bathroom bayan ya rage kayan jikinshi...wanka yayi sharp sharp ya fito zuwa closet ya saka pyjamas har zai kwanta sai kuma yaga he needs to see her ko don sbd ya tabbata taci abinci...fita yayi daga dakin zuwa flat din Mummy..ganin ba kowa a parlorn ya nufi dakinda take ciki..kan gado ya isketa zaune da zumbulelen hijab dinta tayi tagumi da hannunta...ya karasa ciki da sauri ya zauna kusada ita kafin yace"what again?.."kallonshi ta danyi sai kuma ta dauke kai tana turo baki...yakai hannu ya juyoda fuskan nata gareshi yana kallonta yace"Lamido plss..menene ya faru again?..nayi maki wani abun ne?.."girgiza kai ta shiga yi kmr zata fara hawaye tace"ni bacci zanyi"..ajiyar zuciya ya sauke mai karfi yana kallonta..har kullum yana mamakin yanda hawaye sam baiyi mata wahala..kan dan karamin abu zata fara kuka kuma saika rantse wani gagarumin laifin akayi mata...ganin ta juya tana neman kwanciya yayi saurin dakatar da ita da fadin"ki tsaya to kici abinci plss"..ture hannunshi tayi tana cigaba da turo mishi baki tace"ni na koshi"..daga haka ta juya mishi baya ta kwanta abunta shi kuma sai yayi zaune yana binta da ido..baisan ta inda ya kamata ya fara rokonta taci abinci ba..yasan ko a hostel din ma da kyar idan taci wani abun shi kuma baiso ta kwana da yunwa ko kadan..suna zaune haka Mummy ta shigo dakin rikeda sabon dogon riga na bacci a hannunta...tana ganinta a kwance taga tea kuma a ajiye tace"Aysha bakisha tea din ba?.."mikewa tayi da sauri tana sunkuyar da kai tace"yanxu zansha"..daga haka takai hannu ta dauki mug din tea din ta kai bakinta ta fara sha...Bobby sai kallonta yakeyi yanajin wani irin relieve sbd shan tean da take..wato sbd shine yayi mata mgn tace bazata sha ba amma da yake yanxu Mummy ne shine ta dauka tana sha..shi ko a hakan ma yaji dadi at least dai bazata kwana da yunwa ba...tunda ta kada mug din a baki bata ajiye ba saida ta shanye Mummy ta karasa tana mika mata rigar hannunta tace"to ga wnn ki sa zuwa safiya..naga bakici omalet din bama"..a hankali tace"na koshi"..Mummy tace"to amsa rigan kisa..idan kina bukatar wani abun karkiji komai kizo ki fadamin kinji?.."kai kawai ta gyada tareda amsan rigan..Mummy ta maida dubanta ga Bobby dake kallonta har yanzu tace"to tashi muje kaima ka samu ka kwanta"..baiyi mata musu ba ya mike suka fita daga dakin..suna zuwa parlor ya wani marairaice yace"Mummy kina ganin zata iya kwana ita kadai kuwa?.."kamo hannunshi Mummy tayi tana murmushi tace"bana son a takurata ne shi yasa na barta ita kadai..ka kwantar da hankalinka nothing will happen inshaAllah ba gani nan kusa da ita ba?.."gyada mata kanshi yayi kafin ya rungumeta yana cewa"nagode sosai Mummy"..tace"nima nagode..yanxu kaje ka kwanta saida safe"..dagowa yayi yana kallonta da murmushi yace"ka chi fo"..murmushin itama takeyi mishi tace"ka chi boo"..sake rungumeta yayi hadda yi mata peck kafin ya juya ya fita Mummy tabi shi da kallo tana cigaba da smiling..zata iya rantsewa rabon da ta ganshi cikin farin ciki irin wnn har ta manta..fatanta bai wuce Allah ya daidaita tsakaninshi da yarinyar ba..ta fuskanci so ne yakeyi mata matsananci.
Washegari ringing din wayanshi ne ya tada shi daga baccin da ya koma bayan yayi wanka...ya mike zaune a hankali yana murza ido ya dakko wayan ya daga tareda karashi a kunne ba tareda ko sunan wanda ke kiran ya duba ba..muryan waziri yaji yana fadin"Attahiru"..da sauri ya wartsake daga baccin yana sake rike wayan da kyau yace"Baffa kaine?.."Waziri yace"nine Attahiru..ya kukaje gida?.."yace"mun sauka lafia Baffah..ya kafin jiki?.."yace"jiki yayi kyau sosai cikin satin nan nake sa ran komawa Gombe..ya mahaifiyar taku take?.."yace"tana lafia Baffa..na fada mata sakonka kuma tace ta yafe maka duk abunda ya faru"..waziri yace"nagode sosai amma dukda haka ka kai mata Waya inason mgn da ita"..da sauri ya diro daga gadon yana fadin"ohk bari in bata"..daga haka ya fita zuwa flat din Mummy...a bedroom dinta ya sameta ya mika mata wayan da sauri yana cewa"Mummy Waziri ne ke mgn"..a hankali ta karba wayan tareda komawa ta zauna kan sofa tana gaisheshi...ko gaisuwar nata bai amsa ba ya shiga bata hakuri da neman yafiyarta kan duk abubuwa daya aikata mata a baya...nan da nan Mummy data fara hawaye tace ta yafe mishi dunia da lahira dama ita bata taba rikeshi a rai ba...sun jima sosai suna mgn duk akan abubuwanda suka faru a baya..Mummy tace zataje Abuja da kanta ta dubashi itama yace ba sai tazo ba shima cikin satin nan zai koma Gombe and yanaso ya fara biyowa Kano yaga inda suke...Bobby dai na zaune yana kallon Mummy data kasa dena zubda hawaye har suka gama wayan...mika mashi wayan tayi tana share hawayen idonta tace"ka gani ko Bobby?..yanxu ka yadda da abunda nake fada?.."kama hannunta yayi kafin a hankali yace"na yadda Mummy..shiyasa hausawa suke cewa abunda babba ya gano yaro ko ya hau kan tsauni bazai iya ganoshi ba...ni kaina nayi mamakin irin tarbar da muka samu a wurinshi..ban taba zaton yana sonmu har haka ba sai yanxu Mummy..kuma duk laifina ne dana hana ku mu'amala dasu"..ya karasa mgn da wani irin rauni a muryanshi..kamo hannunshi itama tayi tana kallon cikin idonshi tace"ka bar damun kanka anything happpens for a reason..kilan hakan ya faru ne sbd ya zama darasi wa mutane irinka wanda basu yafe laifi komai qanqantarshi da kuma masu yanke zumunta..yanxun tunda komai ya wuce mu bar tunawa dashi sai muyi duba zuwa ga future kuma"..kissing hannunta dake rike da nashi yayi yana fadin"shiyasa nake sonki Mummy..Allah ya yafe mana baki daya"..tana murmushi ta amsa da Ameen sai kuma tace"kaga yanxu kuna daidatawa da Aysha sai ayi mgnr aure kawai..nasan waziri bazaiki nema maka aurenta ba"..da sauri yace"and Mummy kinsan me?..da Lamido da Waziri fa abokan juna ne?..na hadu dasu a Abuja sunzo dubashi tareda dad dinta"..Mummy tace"ai ba abota kadai ne a tsakaninsu ba..akwai alaqa mai karfi tsakanin ahalin Lamido dana Waziri tun zamanin yarinta..alaqa ne irin na gidan sarauta so inshaAllah bazasuki baka aurenta ba"..Bobby daya kasa dena smiling sbd farin ciki yace"Allahumma Ameen Mummy..Allah ya amsa bakinki"..dungure mishi kai tayi tana hararanshi tace"mara kunya kawai...ya jikin nata ma?.."yace"Mummy ai ke za'a tambaya ya jikinta tunda a flat dinki ta kwana"..Mummy tace"ai nayi tunanin wurinta ka fara zuwa kafin kazo nan"..da sauri ya shiga girgiza kai har yanzu bai dena smiling ba yace"haba Mummy..haka nan sai in fara shiga mata daki this early morning?.."mikewa Mummy tayi tace"ai gwara da bakaje ba sbd kada ka fada mata daki tana bacci..yanxun muje mu duba jikin nata"...baice komai ba ya mike suka fita dan Allah ya sani tun daxu dama yakeson zuwa ya ganta...zaune suka sameta gaban mirror tana shafa cream a jikinta Allah yaso da hijab dinta a jiki da shknn haka wnn mutumin zai gama ganin jikinta...ajiye cream din tayi tareda mikewa a hankali ta koma gefen gado tana kokarin durkusawa tace"Mama ina kwana"..Mummy ta mikar da ita tsaye tana cewa"ki dena wnn durkuson keda baki da lafia..ya kafan naki?.."a hankali tace"yayi sauki"..Mummy tace"kin tabbata yayi sauki?.."ta daga mata kai alama Eh..kamata Mummy tayi ta zauna gefen gadon snn ta isa ga wardrobe din dakin ta dakko wani sabon abaya data ajiye mata nan ciki tun jiya ta mika mata rigar tace"maza ki shiga bathroom kisa sai ki fito muje muyi breakfast koh?.."ba musu ta amsa rigan snn ta juya ta shiga bathroom...bayan mintina uku ta fito sanyeda rigar da yayi matukar amsarta...ta yafa mayafin a kanta sai kyawunta ya fito sosai kmr balarabiya...kallonta kawai Bobby keyi harta karaso ciki ta zauna kanta kasa..dukda ba kallonshi takeyi ba zata iya rantsuwa kallonta yake sbd yanda takejin eyes dinshi na zagayawa a jikinta..ba tareda ta kalli inda yakeba tace"ina kwana"..ko jin abunda ta fada ma baiyi ba hankalinshi gaba daya yayi nisa yana kallonta...saida Mummy ta tabashi snn yayi firgigit ya dawo hayyacinshi yana shafa kai...tace"bakaji ana gaisheka bane?.."shafa kan yacigaba dayi yana dan murmushi yace"am..la..lafia lau"..mikewa Mummy tayi tareda kama hannun Aysha tace"to taso muje muyi breakfast daughter"..ba musu ta mike ta shiga binta suka fita daga dakin Bobby ya sauke wani wawan ajiyar zucia yana cigaba da shafa kai..wai me yake damunshi ne haka?..meke faruwa dashi?..mikewa yayi daga kashe shima ya fita daga dakin...a dinning ya samesu gaba daya...Miemie na zaune kusada Aysha sai zuba mata dan banzan surutu take ita kuma tana murmushi sai ta ganta kmr Husna...karasawa Bobby yayi ya zauna yanata kallon dimples dinta dake fitowa sbd murmushin da take..sai yaji kaman an yaye mashi duk wani baqin ciki da yake tare dashi an musanya mashi da farin ciki..ganin murmushin nan nata kadai ya isa yasa ya mance da duk wani damuwa daya tsinci kanshi a ciki...Anty Sumy da Sab da Mummy sai satan kallonshi suke suna dariya..gaba dayansu zuwa yanxu ba wanda baisan irin son da yake mata ba...Miemie ce tayi serving dinsu kmr kullum snn kowa ya shiga cin abincinshi..Lamido dai a hankali takeci dan ko Allah yasan jinta takeyi a takure wlh..gashi ta baro wayanta a can hostel da ko baby saita kira ya rage mata damuwa..kafanta kuwa ya warke garau sai dan abunda baza'a rasa ba...ita ta riga kowa gamawa amma bata tashi ba saida Miemie ta gama suka mike tare..suna tashin kuma wayan Bobby daya ajiye kan table ya fara ringing..yana dubawa yaga daddy ne ke kira dan haka ya mike shima ya koma parlor ya zauna idanunshi a kanta yayi picking da sallamar..a daya bangaren daddy yace"Ameen wa'alaika salaam Attahir..ya aiki?.."cikeda respect yace"Alhamdulillah daddy..ya naka aikin?.."daddy yace"mun gode Allah..ya jikin Aysha?..daxun na kira wayanta ai Bilkisu ke sanar dani kuna asibiti"da sauri yace"eh tama ji sauki daddy..bayan na gama mata treatment sai na kawota nan gida wajen mahaifiyata ta kwana sbd dare yayi lokacin"...daddy yace"MashaAllah sannu da kokari kaji Attahir..Allah ya maka albarka"..Bobby ya amsa da"Ameen Ameen..bari na bata wayan kuyi mgn"...daddy baice komai ba shi kuma ya mike zuwa inda take ya mika mata wayar...kara tayi tareda kaiwa kunnenta a hankali tace"daddy goodmorning"..yace"morning..ya kafan naki?.."tace"ya warke..daddy ina su Yusra?.."daddy yace"gasu"..daga haka ya mika masu wayan Husna ce ta fara cewa"hello Addah"..Aysha ta saki wani murmushi kafin tace"sunanki Yusra dama?.."a fusace Husna tace"idan bakiyi haka ba ai ba kece Adda ba..ga Yusran nan ai sai kuje kuyita yi"..dariya ta saki wanda bata shirya ba..Husna badai saurin hawa ba wlh..sam bata iya wasa ba...kmr daga sama taji muryan Yusra na fadin"Addatah"..nan da nan ta sake sakin wani murmushi tana cewa"habibty na..ya kike ya school"..tace"lafia lau Addah ya ciwonki?..Adda Billy tace mana baki da lafia kin kwana asibiti"...tana cigaba da murmushi tace"hakane amma yanxu na warke habibty..ina Hamma na?.."tace"Daddy ya aikeshi Bauchi..Ammi ma tace idan zamu tafi Umrah zamu biy.."bata karasa ba taji tayi shiru and zata iya rantsewa dakatar da ita akayi..tana jin muryan Husna a background tana cewa"ke Yusra ba Ammi tace kada mu fada mata ba?.."daga haka kuma sai taji an kashe wayar..ta dagota da sauri tana dubanshi duk ta wani maraifaice ta mika mashi wayan tace"sake kiramin dan Allah"..amsa wayan yayi yana kallon yanda ta tsuke fuskanta yace"wnn kuma na menene?.."da sauri tace"cewa fa tayi wai zasu je Umrah su barni"..yace"kuma saiki yadda da mgnr ta..ba yarinya baice?.."girgiza kai takeyi tace"da gaske ne wlh..ai dama duk Ramadhan muna zuwa..nidai ka sake kiramin inji"..bai sake cewa komai ba yayi dialing number ya mika mata..a maimakon Yusra sai taji daddy ne ya dauka..tayi shiru tana tunanin me zata ce sai taji yace"bakida abun cewa ne?.."runtse idonta tayi tanajin kaman ta rushe da kuka tace"ba..komai"..yace"then sai anjima..Allah ya kara sauki"..daga haka daddy ya kashe wayar shi..itama ta mika mashi nashi tana sake daure fuska kai kace wani gagarumin laifi akayi mata...tasan wlh da kyar idan ba da gaske Umran zasuje ba..ai dama suna zuwa da azumi and idan ba mantawa tayi ba yau baifi saura one week a fara azumin ba...ta rufe fuska da hannayenta kmr zata fara kuka Bobby yayi saurin rike hannayen nata yana girgiza mata kanshi yace"dont cry plss..inshaAllah ba inda zasuje su barki"..bata iya cewa komai ba sai bude fuska da tayi nan kuma yaga ba kukan takeba...daidai nan su Mummy suka shigo parlorn ganin yanda taci kunu Mummy tace"Subhanallah meya faru haka?."a hankali yake duban Mummyn yace"wai 'yan gidansu zasuje umrah banda ita"..Mummy ta zauna nan kusada ita tana dubanta da kyau tace"haba stop frowning ur face mana daughter ba sai Azumi zaaje umran ba?.."Aysha ta gyada kai alamar Eh..Mummy tace"then don't cry inshaAllah baza suje su barki ba kinji?..kiyi hakuri"...su aunty Sumy dai na zaune suna kallon ikon Allah..cikin ranta fadi take"lallai Bobby zaiyi fama da shagwaba a wurin nan"..shi kuwa gogan kallonta kawai yakeyi yana mamakin yanda batayi kuka ba..shidai Allah ya kawo ranar da zaiga ta dena saurin kukan nata..ya rasa wace irin shagwabace da ita wlh...bayan ta dan saki fuskanta ya mike zuwa Flat dinshi ya sake shiryawa ya fito...har lokacin suna zaune parlorn sai janta da hira suke...yana duban iwacth dake hannunshi yace"Mummy bari in maida ta hostel in dawo"..Mummy tace"dan wuri haka?..baka bari sai zuwa yamma?.."yace"gwara in maida ta yanxu sbd kada tayi missing lectures dinta..ba dadewa zanyi ba ina ajiye ta zan dawo"...Mummy tace"to shknn Allah ya tsare..Aysha sai yaushe kuma?.."shiru tayi kanta a kasa..Mummy dake murmushi tace"idan inason ganinki zan cema Bobby ya kawoki mu gaisa..Allah ya kara sauki kinji?.."a hankali tace"Ameen..nagode Allah ya kara girma"...da murmushi Mummy tace"babu komai daughter"..juyawa tayi ga aunty Sumy itama tayi mata godia..duk suka bita da adduan samun sauki snn Miemie tayi mata rakia har compound bayan sun cikata da abubuwa iri iri...driver dake zaman jiranshi a compound yana ganin fitowarsu ya mike da sauri zuwa inda motar da zasu fita yake...Bobby na karasawa ya mika mashi hannu yace"bani kyes din kayi zamanka yanxu zanje in dawo"..da sauri ya mika mashi key din tareda komawa ya zauna..shi kuma ya bude motar ya shiga itama ta shiga bayan Miemie ta sa mata kayanta a booth yaja motar suka tafi...baisan meyasa sam bayason driver yayi driving dinshi idan yana tareda ita ba..gani yake kaman zaiyita kallonta ne ta mirror shi yasa yafi gane yayi driving da kanshi idan yana tareda ita...har suka iso hostel babu wanda yace komai a ciki su...ta bude motar zata fita bayan tayi mishi godia ya dauko ledan wani magani ya bata yana cewa"kici gaba da shafawa a kafan har zuwa lokacin da zai dena ciwon"..karba tayi tace mishi"nagode"..ba tareda kallonshi ba..shi kuma kallon nashi yakeso tayi amma sam taki yin Hakan kmr dai tasan yanda yake son ganin fuskanta da kyau...bai takura ta ba yace ta shiga ciki tasa uniform sai ta fito ya ajiyeta area classes..ba musu ta shiga ciki tasa uniform din snn ta fito ya sake maidata cikin school din...har wajen class dinsu yayi parking snn ta bude motar ta fita bayan ta sake mishi godia shi kuma yaja motar ya koma gida.
Tun daga wnn lokacin ta fara bashi cold attitude..ba wai dena kulashi tayi ba saidai kwata kwata ta dena sakewa dashi...zataje har office ta gaisheshi kmr yanda ya bukata amma fa bai cika ganin dariyarta ba...haka zatayi duk wani abu daya sata amma dai bazai ga walwala da farin cikinta ba...ya rasa me yayi mata take bashi wnn traetment din don ko Allah yasan ba karamin damuwa ya sakashi a ciki ba...tun yana tambayan if yayi mata wani abun ta fada har ya hakura ya bar tambaya sbd amsa daya kullum take bashi shine ba komai...duk hakurinshi saida ta bashi haushin dan haka shima yayi alkawarin cigaba da treating dinta yanda takeso tunda ita batasan mutunchi ba...ita kuwa tanayi mishi haka ne ba don komai ba sai dan abubuwa biyu data fahimta tare dashi..cikin dayan biyu dole za'a samu daya..ko dai sonta ya farayi kmr yanda su Billy ke fadi ko kuma mutumin banza ne shi kmr yanda tasan yawanci inyamurai haka suke...wnn dalilin yasa ta daukan ma kanta alkawarin yin baya baya dashi sbd gudun koma mene a cikin zuciyarshi gameda ita don itadai tasan ko daura mata shi akayi a kafa zata kwance don ko kusa baya daga cikin jerin mazajen da takeso...kuma da taga shima ya fara sha mata kamshi sai abun yayi mata dadi dan dama so take ta yadda kwallon mangoro ta huta da kuda.
Har aka fara azumi suna a wnn halin yayinda ita Lamido take harkokin gabanta hankali kwance don har mantawa takeyi dashi..shi kuma yana can zuciyarshi na neman bugawa sbd tarin matsalolin da sukayi mashi yawa...bai taba tunanin haka ya damu da yarinyar nan ba sai yanxu..ya damu da abubuwanda takeyi mishi fiyeda tunanin mai karatu...rayuwar kawai yakeyi a haka ba don yanajin dadinta ba..ya zamana baijin dadin duk wani abu sbd wnn attitude da take bashi...gani yake idan bai samu daidaitawa da itaba yana iya mutuwa amma taurin kai bazai barshi yayi abunda ya kamata ba...ya gwammace idan ma mutuwa zaiyi ya mutu akan dai ya cigaba da binta tana walakantashi haka.
Ranar da aka kai azumi na goma ana gobe zasu fara exam din first semester daddy yace yana son idan ba damuwa Bobby ya kawo mishi ita airport suyi sallama sbd daga Kano zasu tashi...baiyi musu ba amsa mishi da zai kawota saidai cikin ranshi yana tunanin yanda tafiyan nasu zai kasance bayan ba wani jituwa sukeyi ba yanzu...ranar da safe ya danna mata kira abunda shi kanshi ya manta yaushe rabon daya kirata...tana dagawa ko sallamarta bai amsa ba yace"ki shirya zanzo daukanki by 1..ur dad wants to see u"...yana gama fadin haka ya kashe wayarshi ko tsayawa jin amsarta baiyi ba...yana yi mishi ciwo idan ya tuna yanda take treating dinshi kmr wani stranger...kilan dan taga ya fara damuwa da ita take mishi haka so Its better ya koma old self dinshi yanda zasufi daidaitawa da kyau.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
38
Karfe dayan nayi kuwa ya kama hanyan FCNM...tareda da driver dinshi suke amma haka nan ya sallameshi sbd baison ya tukashi if suna tareda ita...yana isa makarantan ko ciki bai shiga ba yayi parking daga nan waje snn ya kira yace ta fito ta sameshi bakin gate...duk yanayin haka ne sbd jin ciwon shariyar data tsiri yi mash...da tasan yanda ya damu da ita da batayi mishi haka ba wlh...ita kuwa shiryawa tayi cikin long doguwar rigarta na wani cotton material orange da qananun flowers lemon green a jiki...bata sa dankwali ba as usual tayi rolling dan karamin veil dinta daga kai zuwa shoulders dinta...bata dauki bag ba sai phone dinta a hannu snn ta saka flat shoe dinta ta fita tanata mitan ya sata tafiyan kafa..da bestie na nan ne tasan batada matsala duk inda tace ya kaita zai kaita amma now that he is not around dole ta zage ta koyi tafiya da kafafunta tunda dai tasan baby bazai yiwu ya dinga kaste aikinshi yana zuwa kaita ko ina da ina ba...kafin ta bar first gate dinsu taga wani mota yazo ya wuceta da gudu sai kuma taga yayi slowing down tareda yin reverse ya dawo inda take...dauke kanta tayi kmr bata gani ba sai taji wanda ke cikin motan yace"Hajia Lamido"..dan juyawa tayi tana kallonshi sai kuma ta saki murmushi ganin shine tace"Tajuddeen ashe kaine"..yace"yeah nine..ina zakije haka a kafa?.."tace"cikin college zan shiga wlh"..yace"amma why bazaki kira bus ya kaiki ba?.tafiyan akwai nisa fa"..dan murmushi kawai tayi batace komai ba...hannu yakai ya bude mata kofan kafin yace"to bari nayi dropping dinki"..girgiza kai tayi da sauri tana cewa"no nagode"..kallonta yake sosai yace"i insist..if kina tunanin wani abu ne ki dena don na dade da hakura ni kam..nasan ba sona kike ba amma for this once ki bari na taimaka maki"..bata sake mashi musu ba ta karasa ta shiga motar shi kuma yaja suka wuce...ganin bata ga motarshi a premises ba tace ya fita da ita waje kilan ta sameshi a can...suna fitowa kuwa ta hango motar nashi a tsallaken titi dan haka yayi dropping nata ta tsallako titin...tunda ta fito daga motar yake kallonta bacin ranshi na sake karuwa fiyeda wanda yake ciki already...wato da yace ta fito shine ta kira one of samarinta ya fito da ita sbd batada hankali...ta zauna gaban motarshi tanata washe mashi baki sbd batasan ciwon kanta ba ga wani shegen riga da tasa da bai gamsheshi ba sam..gaba daya rigan ya bayyana surar jikinta instead of tasa hijab shine ta dakko wnn dan veil din tayi rolling sbd rashin nustuwa...ranshi yaji yayi wani irin 6aci baisan lokacinda ya hada kan nashi da starring motar ba...yana rantsuwa da Allah idan har yarinyar nan zata cigaba da abubuwa haka mutuwa zaiyi...yasan for sure ko wulakancin da take mashi bai kasheshi ba to duk ranar da aka daura mata aure da wani nashi ya kare...a yanda yakejin zuciyarshi tamkar tana dab da fashewa ne sbd ciwon da yakeji cikinta ya fara mishi yawa...kiri kiri wai kana son mutum shi kuma baya sonka wani yakeso...duk ya tunada wnn abu sai yaji kmr yayi commiting suicide ya huta...har ta karaso inda yake bai iya dago kanshi ba..ganin tanata knocking ko dagowa baiyi ba kawai ta bude motar ta shiga fuska daure kmr wanda tayi ido hudu da makiyinta...duk abunda take yana jinta amma ko dagowa baiyi dan shi kadai yasan what is taking place in his heart...addu'o'i yayita karantawa iri iri har yaji ya dan samu relieve snn ya dago kan nashi ba tareda ya kalleta ba ya tada motar suka tafi...a hankali ta dan saci kallonshi taga fuskan nan a dinke kaman na saniya dan haka ta shafawa kanta salama tayi kasa da kanta tareda cewa"ina yini"..ko kallon inda take baiyi ba balle tayi tunanin samun amsa daga wurinshi...ta tabe baki tana gyara zamanta dama ba gaisheshi tayi dan ya amsa ba dan rainin hankali kawai...haka suka cigaba da tafiya in silence har suka isa Malam Aminu Kano International Airport...mamaki ya cikata ganin airport ya kawota ko me zasuyi a nan kuma oho?..bata dai tambayeshi ba tanaji bayan ya gama parking ya dauki wayanshi yayi dialing number daddy...bayan ya dauka Bobby yace"mun iso airport din sir"..daga daya bangaren daddy yace"muma gamu nan shigowa ciki yanxun nan"..daga haka ya kashe wayarshi snn ya bude motar ya fita...itama ta bude daya side din ta fita...suna fita kuma motan daddy yazo yayi parking a kusada nasu...ta wani zare ido tana kallon motar kmr bata taba ganinta sbd mamaki...kenan daddy ne yace ya kawota airport zasuyi tafiya ne ko kuma yaya abun yake?..daddy ne ya fara fitowa daga motar sai Ammi sai Husna da Yusra suma suka fito a tare...da sauri ya karasa inda suke yana kokarin durkusawa daddy yayi saurin kama hannunshi ya hada da nashi sukayi musabiha yana fadin"bana hanaka durkuson nan bane Attahir"..murmushi kawai Bobby ya saki kanshi kasa yace"barka da isowa"..daddy yace"barka dai..ya aiyuka?.."kai a kasa yace"Alhamdulillah sir"..sake kama hannunshi daddy yayi yana nunawa Ammi yace"to Maimunatu yau dai gaki ga Attahir"..ya juya yana duban Bobbyn shima yace mishi"itace Maman Aysha"..kokarin durkusawa ya sakeyi still daddy ya hanashi...ba yanda ya iya haka nan ya mike saidai ko kusa ya kasa dago kanshi ya kalleta a hankali yace"Ina yini"..Ammi dake kallonshi tana murmushi tace"lafia lau Attahir..ya aiki ya kuma akaji da fama da Aysha?.."murmushi kawai ya saki kanshi a kasa...daddy ya sake nuna mashi su Husna kafin yace"ga sisters dinta nan..wnn sunanta Asma'u karamar kuma Yusra"..kallonsu Bobby ya shiga yi yana murmushi..Husna ta fara gaisheshi snn Yusra duk ya amsa musu smilingly...yaji gaba daya ahalinta sun shiga ranshi don sunada karamci sosai...ita kuwa Aysha da tayi mutuwar tsaye tun daxun tana kallonsu sai yanxu ta samu sararin karasawa inda suke hankalinta duk ya tashi kar ace tafiya zasuyi ba tareda ita ba tac"daddy sannunku da zuwa"..daddy yace"yauwa..ya karatun?.."tace"fine daddy gobe zamu fara exams"..yace"Allah ya bada sa'a"..ta amsa da Ameen snn ta juya tana kallon Ammi jiki a sanyaye tace"Ammi ina yini"..itama ta amsa mata da"lafia lau..ya mkarantan?.."tace"fine..Ammi tafiya zamuyi?.."murmushi Ammi ta saki gamida girgiza kai tace"tafiya zamuyi dai..keda zaki fara exams waye zaiyi tafiya dake?.."nan ta marairaice tace"Ammi dan girman Allah zanje kinga ko last year ma da banje umrah ba..kuma ai Friday zamu gama exams din"..kafin Ammi tayi mgn daddy yace"yanxun ma ba cewa akayi bazaki jeba ai..zakije amma sai kin gama exams dinki zaku taho tareda Najeeb"..shiru tayi batace komai ba itadai Allah ya sani tafi son ta tafi tare dasu...Yusra ce ta matsa kusada ita kmr zatasa kuka tace"daddy nima zan zauna da Adda"..daddy yace"no itada take makaranta a ina zata ajiyeki"..da sauri ta sake cewa"daddy nidai zan..."bai bari ta karasa ba yace"stop it Yusra bazaki zauna nan ba"..ba musu tayi shiru tana turo baki Ammi dai kallonsu kawai take tana murmushi...hannun Bobby daddy ya kama yace"zo muyi mgn son"..ba musu ya bishi a baya...Aysha kmr jira takeyi su bar wurin ta matsa kusada Ammi kmr zatasa kuka tace"Ammi dan Allah ki cema daddy ku jira in gama exams plss"..harara mai kyau Ammi ta watsa mata kafin tace"sbd ke kika haifemu sai mu zauna zaman jiranki ki gama exams koh?..idan kika cigaba da damuna wlh gaba daya zan soke tafiyan naki saiki koma gida ki jiramu kafin mu dawo"..ta wani tale baki kmr zata sa kuka tace"kai Ammi dan Allah"..harara ta kuma watsa maka before tace"just dare me and see what will happen..keda har yanxu bazakiyi hankali kisan kin girma ba"...shiru tayi bata sake mgn ba sai turo baki da take...juyawa tayi taga yanda suke mgn cikin kwanciyar hankali har wani smiling taga sunayi duk su biyun cikin ranta tace"ai dole kayi daria tunda kana neman shiga tsakanin da mahaifina..mugu dakai kawai"...bayan kmr 5 mins suka dawo wurin...Bobby yayi sallama da Ammi dasu Husna snn ya bar wurin...itama Aysha sallamar tayi dasu idonta har ya ciko da hawaye ta juya zuwa inda yayi parking...tana bude motar ta shiga saita hada kai da guiwa ta shiga sauke numfashi...Bobby yayi shiru yana kallonta baidai ce komai ba...lumshe ido yayi ya jingina da kujera yana jin wani irin zafi na neman rufeshi...wai after duk wulaknci da ignoring dinshi da take still bayason ya ganta cikin damuwa...ya rasa wani irin al'amari ne wnn ace wai duk bata maka rai da mutun zaiyi even for once bazaka iya fita sabgarshi ba...ko kuka yaga tanayi sai yaji kaman da idanunshi takeyi...baya son jinshi ko kadan kuma yasan ko yayi mata mgn ma zaiyi wahala ta dena..baisan meyasa ta tsaneshi to this extent ba...bude idonshi yayi a hankali tareda tada motar suka bar cikin airport din...driving yakeyi a hankali yanajin yanda har yanxun kukanta bai bar taba zuciyarshi ba...ganin abun nata bana kare bane sai ya gangara gefen titi yayi parking shima ya hada kanshi da starring motar yana sauke numfashi...duk duniyar sai yaji tayi mashi wani irin kunchi da zafi da baisan daga ina hakan ke fitowa ba...saida ya dauki lokaci mai tsayi a haka kafin ya dago kan nashi da kyar yana kallonta...cikin muryanshi da yaji ya disashe all of a sudden ya kira sunanta"Aysher"...banza tayi dashi bata amsa ba kuma bata dago kanta ba..ya sake kiran sunan nata still bata amsa ba baisan lokacinda cikin karaji yace"idan baki denamin kuka a mota ba saukeki zanyi wlh..are u small kid da zakisa mutum a gaba da kuka sbd an tafi an barki.."..shiru tayi still bata dago kan nata ba..da karfi yakai hannunshi ya dago fuskan nata sai yaga ko digon hawaye babu..iskanci ne kawai yasa tayi hakan ashe ba kuka take ba..kallon cute face din nata ya tsaya yi without blinking...rabonshi daya kalli face dinta haka har ya manta..a hankali yaji wani irin nutsuwa na sauko mishi sbd ganin fuskan nata...ya lumshe ido yana sake budeshi kan face din nata da har dunia ta nade yasan bazai taba gajiya da kallonta ba...sai ya nemi duk wani haushinta da yakeji ya rasa..baisan ko magic take using a kanshi da baya taba iya dogon fushi da ita ba..duk yanda zata kai da bata mashi rai yana kallon face dinta sai yaji ya yafe mata komai sbd tsabar farin cikin da kallon fuskan nata ke sanyashi musamman idan tana cikin farin ciki...lokaci daya kuma ya dauke idonshi daga kanta ya wani sake dinke fuska snn ta tada motar suka cigaba da tafia...wani babban super market taga yayi parking yace ta jirashi nan ciki snn ya fita daga motar...bayan few minutes ya dawo da babban leda a hannunshi yasa back seat snn ya shiga ya tada mota suka cigaba da tafia....ko a hanya bai iya cikakken minti uku ba tareda ya juyo ya kalleta ba...haka nan sai yakejin ganin nata na tafiya da duk wani kunchi da damuwarshi...babu wanda yayi mgn har suka isa FCNM Hostel...daidai gate dinsu yayi parking kafin ta bude motar ta fita yayi saurin dauko ledan daya ajiye a baya ya mika mata cikin wani irin kaushin murya yace"ina iya neman wani alfarma wurinki?.."juyawa tana kallonshi wai alfarma zai nema shine fuskanshi cunkus haka..kai kawai ta daga mashi alamar eh...ledan ya sake mika mata kafin yace"hijabai ne nan ciki..inaso ko dan darajar amanarki da mahaifinki ya bani ki dinga sawa idan zaki fita..ko cikin college zaki shiga ki dora akan uniform dinki idan kinje class sai ki cire tunda na fuskanci ke har yanxu bakisan ciwon kani ba"...kallonshi kawai takeyi kmr mai tunanin wani abu sai kuma can ta numfasa tareda karban ledan da yake miko mata tace"nagode"..da sauri yace"banji kince zaki na sawa ba"..a takaice tace"zan sa"..ya saki wani murmushi yana binta da ido yace"nagode"..komai bata sake cewa ba ta bude motar ta fita shi kuma yayi relaxing nan ciki yana kallonta har saida ta shiga ciki snn yaja motar yayi reverse ya wuce.
Ranan Thursday suna kwance hostel bayan sun fito daga exams kowa tana fama da azuminta musamman Lamido da sai juyi takeyi kan gado wai tanajin yunwa...sbd tsabar haushi Billy ko tanka maka tabayi ba har ta gama surutunta ta hakura...tana nan kwance har bacci ya fara daukanta taji wayanta na ringing...hannu ta mika ta dauko wayan daga kan study table dinta tareda dagawa takai kunne...muryan Sa'eed taji na fadin"my bestyyyyyy"...wani irin mikewa zaune tayi da sauri tana zare idanu tace"besty is this really you?.."full of excitement yace mata"its me besty...ur very own best friend"..tun kafin ya rufe baki ta wani turo baki tace"ba wani my very own best friend..yanzu tsakani da Allah haka ake rayuwa besty?..tunda ka tafi ba hello ba hy kaman dama ka gaji damu"...tana rufe baki shima yace"dadina da besty rigima wlh..to yanxu dai ku fito gani bakin gate ina jiranku".. sake zare idanuwanta tayi tamkar wanda tayi gamo da aljani tace"are u serious besty?."yace"come outside mana zaki gani ai"..daga haka ya kashe wayar ita kuma ta diro daga kan gadon ta rarumi hijab dinta ta zura snn ta karasa gadon Billy ta fara tashinta daga bacci...a fusace ta mike zaune tana cewa"Lamido wai meye baka plss?..meyasa bakyaso kiga nayi bacci a hostel din nan"..kama hannunta Aysha tayi ta mikar da ita tsaye ta dauko mata hijab ta mika mata snn tace"wai besty ne yazo yana bakin gate..kinji dan rainin hankali zaizo ko fada mana baiyi ba"...tabe baki Billy tayi tana kokarin momawa gadonta don sake kwanciya tace"kuma shine zaki tasheni daga bacci sai kace besty na ne yazo?.."sake kamata Aysha tayi ta shiga turata waje tana cewa"ai wlh baki isaba sai kinje"..daga haka ta ja hannunta suka fita daga dakin bayan Billy ta zura hijab dinta itama...suna fita suka hangoshi daidai inda ya saba tsayuwa idan yazo dan haka suka nufi wurin da sauri...har suka karaso inda yake kallonsu yakeyi yana murmushi...bai taba sanin da akwai friendship irin wanda yake tsakaninshi da su biyun nan ba...jinsu yake a jikinshi tamkar sun zama family...suna karasowa Lamido data wano hade girar sama dana kasa tace"nidai ba kulaka zanyi ba wlh"..murmushi ya saki kafin yace"idan besty taki kulani kuma ai sai in samu matsala..yanxun kiyi hakuri mu zauna sai in fada maku uzuri na nasan kema idan kikaji zaki hakura ki dena fushi"...ba musu gaba daya suka nufi inda suka saba zama nan cikin hostel din as usual...bayan sun zauna ya shiga musu bayanin tafiya sukayi zuwa Canada tareda Dad dinshi shine dalilinda yasa basu samunshi a waya...shima kuma bai samu yayi roaming ba and bai hau social media ba har suka dawo shiyasa sukajishi tsit kmr baya existing...kmr yanda ya fada kuwa nan da nan ta sauko daga fushin nata sai kuma aka hau labari na yaushe gamo..hatta Billy da ba wani dasawa sukeyi ba yau labari na musamman sukeyi dashi sbd missing juna da sukayi...bashi yabar hostel din ba sai around 4 yace su shirya kafin magrib zaizo ya daukesu su fita don akwai special iftar daya hada masu for the three of them...murna wajensu kmr ba gobe haka suka koma hostel kowa ta fara shirin fita tunda yace before magrib din zaizo yayi picking dinsu.
6 nayi kuma yazo yayi picking dinsu sai Cilantro...wurin har wani decoration yasa akayi mashi specially for them dama already yayi reserving so daga su sai su zasuyi iftar dinsu...tun kafin asha ruwa aka cika masu gabansu da kayan ciye ciye iri iri...sunata hiransu abunsu har aka kira sallah Sa'eed ruwa kadai yasha ya wuce masallacin dake nan ciki yayinda su kuma suka gabatar da sallahrsu a inda suke...yana dawowa suka shiga iftar dinsu hankali kwance kowa ka gani cikinsu is full of happiness and excitemet sbd kada cewa tareda junansu after a long period of time...Sa'eed sai snapping dinsu yakeyi wani su biyu kadai wani kuma yayi musu selfie gaba daya..a takaice sunyi having fun dinsu yanda ya kamata suna barin wurin kuma ya kaisu gidan Hajia nan ma taji dadin gani su sosai daga nan kuma yayi musu siyayyan kayan kwalam snn yayi dropping nasu a hostel as usual.
A daren ranar Dr Bobby yana parlonshi yana karatun Qur'ani kiran daddy ya shigo wayanshi...ajiye alqur'anin yayi tareda dagan wayan da sallama..bayan sun gaisa daddy yace"wani nauyin dai zan sake dora maka son Allah yasa bazaka gaji dani ba"..da murmushi Bobby yace"not at all sir..ka fadi kome kakeso zaayi inshaAllah"..cikeda jin dadin amsan daya bashi daddy yace"nagode sosai Attahir...mgnr Aysha ne dama gobe zasu gama exams koh?."yace"yeah gobe zasu gama"...daddy yace"so nake if it's ok by you ka kaita wajen mahaifiyarka ta kwana biyu zuwa sunday wanda zasu tafi dashi ne har yanxun Passport dinshi bai zama ready ba amma yacemin zuwa sunday komai zai zama ready inshaAllah..banson ta koma Gombe ne snn ta sake dawowa Kano tunda dole ta kano flight dinsu zai tashi"...da sauri Bobby yace"no problem sir..zan kawota inshaAllah"..daddy yace"i hope dai ba wani matsala koh?.."yana gyada kanshi yace"babu wani matsala inshaAllah"..murmushi daddy ya kara saki kafin yace"to nagode sosai Attahir..zuwa sunday din komai inshaAllah zai zama ready ita dama passport da visa dinta duk basuda matsala so ticket kawai zaa sai mata"...gyada kai kawai yakeyi yama rasa abunda ya kamata yace...sallama sukayi snn daddy ya kashe waya..shima ya ajiye nashi yana sakin wani numfashi da karfi gamida dafe kanshi...farin ciki ya kamata yayi sbd zata dawo kusa dashi amma what he's feeling is not close to farin ciki at all...yasan zamanta a kusa dashi din ba abunda zai amfaneshi dashi saima karin damuwa da zai sanya mishi tunda yasan ba sonshi takeyi ba...duk sai yaji damuwan da ya fara raguwa a tare dashi yana neman dawowa sabo...dunia yanxu babu abunda ke bata ranshi kmr idan ya tuna yarinyar nan bata daukeshi a bakin komai ba bata kaunarshi...dukda har yanzun ba bai furta mata yana sonta ba yasan ko a can kasan zuciyarta babu wani abu makamancin sonshi shiyasa idan ya tuna haka yakejin kmr zai hadiye zucia ya mutu...ganin damuwan na nema yi mishi yawa sai ya dauki alqur'aninshi yacigaba da karatun da yakeyi...nan take kuma yaji ya samu saukin damuwar daya fara rufeshi.
Washegari bayan ya gama shiryawa kafin ya fita ya nufi Flat din Mummy dan sanar da ita yanda sukayi da daddy jiya...tana zaune itama tana karatu ya shigo dakin..ya karasa kusada ita ya zauna har takai aya snn ta rufe Qur'an din tana dubashi tace"har ka fito?.."yace"na fito Mummy..dama wata mgn ce nazo muyi dake"..Mummy tace"to ina jinka"..saida ya lumshe ido ya bude kafin a hankali yace"baban Aysher ne dama yace in kawota tayi kwana biyu a nan wai wanda zasu wuce Saudi dashi passport dinshi bai gama zama ready ba"..full of excitement Mummy ta wara idanu tana cewa"da gaske?..to Allah ya kawota lfy yaushe zasu gama exam din?.."a takaice yace mata"yau"..sake wara idanu tayi tana murmushi tace"to Allah ya kawota lfy kace mishi babu wani matsala zatayi zamanta tare damu a nan"...kallonta kawai yakeyi ganin how happy she is kawai sbd zatazo gidan tayi kwana biyu...baisan meyasa ba shidai tun jiya da aka fadi mgnr nan yakejin jikinshi wani iri kmr dai ba nashi ba...Mummy ta kamo hannunshi tana dubanshi da kyau tace"wnn damuwan kuma na menene Bobby?.."dan matsala yayi ya dora kanshi kan shoulder dinta murya can kasan makoshinshi yace"bata sona Mummy..har yanxun bata kaunata dan Allah Mummy me zanyi mata ta soni..ko bai kai yanda nake sonta ba at least itama ta soni"...Mummy dake rikeda hannunshi tace"inaji a jikina zaka auri yarinyar nan kawai ka kwantar da hankalinka"..sake lafewa yayi a jikinta yace"na gaji ne Mummy..na gaji da chasing dinta tana nuna banida muhimmanci a wurinta..Allah kadai yasan halin da nake ciki these days ko bacci wahala yakemin..ji nake idan abubuwa suka cigaba da tafia a haka mutuwa zanyi"..girgiza kai Mummy ta shiga yi tace"nace maka ka dena fadin haka amma ba kaji..ajiye duk wani pride and ego dinka zakayi a gefe ka fada mata how feel..tell her that you love her and you can die for her amma ba kazo kana tambaya yanda zakayi ba"..lumshe ido kawai yayi yana sauke numfashi da kyar..baisan meyasa when it comes to love yakejin brain dinshi na toshewa ba..gaba daya sai yaji ya rasa me ya kamata yayi...abu daya daya sani shine ya dena chasing dinta infact yama dena nuna yana son nata tunda batasan yanayi ba.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ta fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
39
The next day which is Friday tunda suka fito daga exams Lamido keta trying number din Hamma amma bai shiga...duk ha kalinta yabi ya tashi kada dai ace shima wucewa yayi ba tareda ita ba...ta dubi Billy dake zaune kusada ita kmr zatayi kuka tace"Billy anya kuwa ba binku zanyi mu tafi ba?..kinga fa wayar Hamma har yanxun bai shiga ba"..Billy tace"tunda kika ga bai shiga ba kilan wani abun ne ya faru shiyasa nace ki kwantar da hankalinki kinsan Hamma bazai iya wucewa ya barki ba"..ta bude baki zata sake mgn wayarta ya shiga ringing ta duba da sauri don a tunaninta ko Hamman ne amma sai taga proprietor..dan bata rai tayi tana turo baki tayi picking call din ba tareda tace komai ba...shima sai yayi shiru na dan wani lokaci kafin yace"are u done with the exams?.."a hankali tace"eh.."yace"am coming right away to pick u up..if u like kije ki shiga motan saurayi kiga abunda zan maki"..yana gama mgn ya kashe wayarshi..itama ta ajiye nata tana 'yan mitocinta..Billy dake sauraronta tace"me yace wai?.."rai a bace tace"wani wai he's coming to pick me up ko gidan ubanwa zai kaini oho?..na fara gajia da halin mutumin nan wlh..mutum sai shegen zafin rai"...murmushi Billy ta saki kafin tace"ni salon love dinshi nema yake burgeni"..da sauri Aysha ta juya tana kallonta fuska a daure tace"what do u mean?.."girgiza kai Billy take tana cigaba da murmushi tace"aah ba abunda nake nufi nikam..kidai cigaba da rainama kanki hankali"...sake dinke fuska tayi ta cika tayi fam tace"kinga Billy bana son irin wnn abun da kikemin..na meye zaki dinga hadani da mutuminda kinfi kowa sanin yanda na tsaneshi"..har yanxu Hajia Billy bata bar smiling ba tace"shine nace kici gaba da rainama kanki hankali ai..kiri kiri kinsan mutumin nan sonki yake amma kina wani nuna baki saniba kina raina mana hankali kawai..continue deceiving yourself"..kallonta Aysha keyi fuskan nan ba sarari kmr zatasa kuka...dunia ba abunda ta tsana kmr wani ya bude baki yace proprietor sonta yake hakan ba karamin bata mata rai yakeyi ba...ita kuma Billy da gayya ma take mata haka sbd tasan yanda ta tsaneshi..idan ma ba wulakanci ba ta ya za'a kalli tsabar idonta ace wnn mutumin wai yana sonta..bayan duk wulakancin da yake mata shine mutane har suke da bakin cewa yana sonta?..ita bata taba ganin inda akayi soyayya haka ba..a iya saninta dai idan mutum na sonka baison bata ranka amma fa shi ko yanxu daya kirata a wani tsatstsaye ya fada mata mgn babu irin tausasa murya amma still sukeda bakin cewa yana sonta sbd basuda hankali...wnn dalilin ne yasa shi kanshi take dauke mashi wuta dan sai tayi sati bataje inda yakeba sbd kwata kwata bata son yanda mutane ke tunanin soyayya sukeyi...Billy kuwa kallonta kawai takeyi tana kunshe daria..al'amarin Lamido ba karamin daria yake bata ba wlh..ai ko makaho zuwa yanxun ya kamata ace yasan Dr Bobby sonta yakeyi amma ita kullum sai taita wani nuna batasan me yake faruwa ba...haka sukaita zaune a wurin babu mai cewa kowa komai ita Aysha na daure fuska yayinda Billy kuma ke daria kasa kasa...bayan wani dan lokaci akazo daukan Billy daga Bauchi nan kuma hankalin Lamido gaba daya ya tashi da taga da gaske Billy tafia zatayi ta barta..to ita ina zata zauna ne wai?..yaushe ne kuma zasu wuce Saudi don har yanxu bata samu mgn da Hamma ba...haka ta rakata har mota sukayi sallama snn suka wuce ita kuma ta koma ciki idonta na cikowa da hawaye...tana kokarin haurawa sama zuwa class dinsu wayanta ya sake daukan ringing...ta dakata da hawa stairs da takeyi snn ta dauka still batace mishi komai ba...a takaice taji yace"where are u?.."tace"Sir ina class"..a dan fusace yace"ni kike jira inzo in sauko dake knn?.."tayi shiru tana turo baki..yace"if u like ki fito nan premises ina jiranki and don't waste my time"..kmr zatasa kuka tace"wai ina zamuje?.."baice mata kala ba ya kashe wayarshi ita kuma ta sauka kasa zuwa premises din tanata banbami cikin ranta...can inda ta hango motarshi ta nufa kai tsaye ta bude front seat zata shiga taji ya daka mata wani tsawa yana cewa"ba nan akace ki shiga ba"..rufewa tayi snn ta bude na baya ta zauna nan kusa dashi driver ya tada motar suka tafi...shiru cikin motar babu wanda ke cewa wani abu a cikinsu...Bobby ya jingina kanshi da kujera tareda lumshe ido yana sauraran heart beat dinshi yayinda ita kuma ta rakube can karshen mota tana kallon window fuskan nan a tamke...kawai tunanin inda zai kaita takeyi..ita batasan meyasa ma Allah ya hadata dashi ba at the first place..kawai gashi nan yasa mutane na tunanin suna soyayya...maimakon gida sai taga hanyar Hospital dinshi ya dauka..ta tabe baki bata dai ce komai ba har suka isa Freedom Specialist Hospital...kafin driver ya bude mashi kofa ya bude ya fito da kanshi...itama ta fito suka shiga ciki..office dinshi ya bude suka shiga ya nuna mata seat yace ta zauna nan ta jirashi theater zai shiga..batace mishi komai ba har ya fita daga office din sai a snn ta bishi da harara tana fadin"da azumin ma mutum bazai dena bakin hali ba..wani wai zai shiga theatre sai kace dai a kanshi aka fara zama doctor bashida aikin daya wuce theatre"...haka tayita zaune nan office din tana jiranshi har kusan magrib bai dawoba duk ranta yabi ya gama 6aci..knn a asibiti yakeso tasha ruwa ko a ina?..kawai yazo ya wani ajiyeta office dinshi kmr wata gantalalliya...har ta cire ran dawowarshita gama sadakarwa yau a nan cikin asibitin zatayi iftar dinta sai kuma gashi ya dawo hajaram majaram dashi kmr wanda ya kwana yana theatre😂bai tsaya wasting anymore time ba yace ta tashi su wuce...su A'i ba musu ta mike tabi bayanshi...suna shiga mota driver ya tayar da ita suka tafi...har suka isa gida ba wanda yayi mgn cikinsu..driver na gama parking ya bude mota ya fita ya rage su biyu a cikin motan..har ya bude shima zai fita sai yaga hankalinta na wani wajen..kallonta ya tsaya yi for like 5 mins kafin ya dauke kanshi a hankali ya bude motar ya fita..ga mamakinshi har ya kama hanyar entrance bata fito daga motar ba..yayi kmr zai wuce ya kyaleta nan ciki sai kuma ya fasa tareda juyawa inda take...bude kofa yayi yana kallonta ba yabo ba fallasa yace"fito"..kallonshi tayi da sauri sai kuma ta shiga duban inda suke taga gidansu ne ya kawota..to me kuma zatayi a gidansu fisabilillahi...kallonta yakeyi har ta gama kalle kallenta snn yace"don't let me repeat myself"..saukowa tayi daga motar tana sake tura mishi baki kmr zai bar muhallinshi...hanya ya nuna mata ta wuce gaba yabita a baya har cikin gidan...a central parlor suka iske auntu sumy da Mummy tsaye suna mgn and bisaga dukkan alamu mgn ne suke mai muhimmanci dan har suka isa kusa dasu basuji shigowarsu ba...Bobby ya dan daga murya yace"Mummyy"..juyowa tayi da sauri tana kallonshi tace"aah har kun karaso?.."bai amsa mata ba sai cewa yayi"me kuke discussing ne haka?.."shareshi Mummy ta nufi wurin Aysha tareda kamo hannunta tana murmushi tace"sannu da zuwa daughter"..Aysha da taji wani irin nauyin Mummyn ya kamata tayi kasa da kai tace"Mama ina yini"..Mummy tace"lafia lau Aysha ya exams"..tace"Alhamdulillah"..Aunty sumy ma ta karaso inda suke da fara'a kafin tayi mgn Lamido tace"Aunty ina yini"..tace"lafia Aysha..ya azumi?.."kai a kasa tace"Alhamdulillah"..anty sumy ta juya ga Bobby daya wani daure fuska tace"wnn bata ran wai duk na menene?.."baice mata komai ba sai juyawa da yayi zai wuce flat dinshi Mummy tace"itama ka rakata ciki ta samu ta huta nasan tana tareda gajia kafin time din iftar ya karasa"..dakatawa yayi da tafiya baice komai ba..Mummy tace ma Aysha"jeki ya rakaki daki ki huta kinji?.."batayi musu ba tabi bayanshi zuwa flat din Mummy...kai tsaye dakinda ta taba kwana ya kaita tana shiga ya juya zai fita tayi saurin cewa"Sir ni yaushe zan tafi?.."baice mata komai ba ya sake taking two steps forwad kafin ya fita ta kuma cewa"to ni banida kayan sawa"..still baiyi mgn ba ya fita daga dakin...flat dinshi ya wuce direct ya shiga bathroom yayi wanka yana fitowa yayi changing zuwa kananan kaya snn ya dauki key din mota ya fita zuwa flat din aunty sumy..alwala ya samu tayo tana kokarin fita daga dakin ya shigo ganin zata fita yaui saurin dakatar da ita da cewa"aunty riga zaki dan bani in kaima yarinyar can tasa"..kallonshi aunty sumy tayi da mamaki tace" kayana ai sun mata yawa Bobby saidai ko na Miemie"..tun bata rufe baki ba yace"na Miemie matseta zasuyi nasan naki shine bazai fito da jikinta ba"..kallonshi ta sakeyi taga yanda ya wani hade rai kawai ta saki daria cikin ranta tana jinjina zafin kishi irin nashi..bata sake cewa komai ba ta isa gaban press dinta ta bude tareda dauko wani peach abaya daya mata kadan ta mika mashi..ya amsa yace"thank u"snn ya fita daga dakin..dakinda ya kaita ya nufa daidai lokacin ta fito daga bayi kenan ya shigo dakin...ta wani runtse ido tareda durkushewa nan kasa cikin wani irin tashin hankali tace"Noooo"..kallonta kawai Bobby ya tsaya yi daga ita sai towel a jikinta..gaba daya jikin nata na digar da ruwa alaman dai daga wanka ta fito..a take yaji wani irin faduwar gaba ya riskeshi...ya shiga kallonta with his eyes wide open tamkar wanda yaga abun tsoro..wani irin abu yaji yana gangarowa tun daga brain dinshi ya shiga yawatawa a cikin jinin jikinshi...gashi kuma ya kasa dauke idanun daga kanta duk kuwa da yanda yake son yin hakan...sai yaji kmr idanun ne suke controlling kansu da kansu ba wai shi yake controlling nasu ba..a hankali yaji legs dinshi sun fara motsi and he know for sure motsawa suke saidai kwata kwata baiyi tunanin tafia sukeyi ba saida ya ganshi a gabanta...hannu ya mika a nutse ya kamata tareda mikar da ita tsaye..ta sake runste idanu gabanta na tsananta faduwa sosai...kallon hannunta dake zagaye da chest dinta yayi har zuwa legs dinta da suke nan kusan duk a waje don towel din iya guiwarta ya tsaya...gabanshi yaji ya sakw faduwa lokaci daya idonshi suka canza launi..wasu baqin al'amura yakejin suna zagayawa cikin systems dinshi da shi kanshi baisan yana dasu ba sai this very moment...numfashi ma da kyar yake iya daukanshi sbd yanayin daya shiga...jin har yanxu baiy mgn ba kuma bai kai hannunshi jikinta ba sai tayi tunanin kilan tafiya yayi dan haka ta bude idanunta aikam tana budewa idanun suka fada cikin nashi...ta wani zare ido ra shiga ja baya kmr zatasa kuka tace"Sir..dan..Allah..ka fita"..bai iya ce mata komai ba sai takawa daya shigayi zuwa inda take...hankalinta ya sake tashi ganin yana biyota tacigaba daja baya har tajita jikin bango alaman taje karshen dakin knn..ta wani manne jikin bangon hawaye na ciko idonta tace"sir i beg of u plss"..ta karasa mgnr hawaye na silalowa fuskanta..da sauri ya sake matsawa dab da ita har jikinshi na gogan nata aiko ta bude baki zata kurma mashi ihu yay saurin dafe bakin da hannayenshi dan yasan tana sakin ihun nan ta cuceshi...fuskanshi ya matso dab da nata yana sakin numfashi da karfi..so yake ya bude baki yayi mgn amma yau sai yaji bakinshi ya kafe kaf ko word daya ya kasa furtawa...wani irin nauyi yakeji cikin heart dinshi tamkar wanda aka dorama mountain a ciki...soyayyarta yake ji yana sake zagawa cikin ilahirin jini da tsokar jikinshi tamkar zaiyi ajalinshi..lokaci daya ta fashe mishi da kuka baisan lokacinda ya lumshe ido tareda hadata da jikinshi ba..wani irin rauni yakeji tun daga cikin heart dinshi har zuwa lips dinshi hakan yasa har yanxu ya kasa bude bakin yayi mgn sai kyakykyawan runguma da yayi mata kmr zai ballata...only Allah knows irin soyayyan da yakema yarinyar nan..he loves her to the core..he loves her to the moon and back amma ita ya fuskanci sam bata kaunarshi...jin yanda kukanta ke kara tsananta sai ya dagota daga jikinshi yayi cupping fuskanta tareda hadata da nashi fuskan har yanxu ya kasa cewa komai...ji yake idan bai furta mata what he have in mind ba yau yana iya rasa ranshi dan abunda yakeji is beyond him..gaba daya oxygen din dakin yaji yayi mashi kadan sbd yanda breathe dinshi ke fita da kyar kmr asthmatic patient...sun dauki tsahon lokaci a haka tana kuka yana aikin share mata hawaye kafin a hankali cikin wani irin murya da shi kanshi baisan yana dashi ba yace"i just..can't hide it..anymore..mutuwa zanyi"..itadai kukanta kawai takeyi tana sheshsheka..a hankali ya sake dago fuskanta ya kuma hadewa da nashi yana kallon cikin idonta da nashi idon dake shinning yace"Lamido ki taimakamin plss..I LOVE U..i love u with my whole heart ki ceci rayuwata dan Allah"..duk kukan da takeyi yana furta kalmar i love u taji kukan ya tsaya cak..ta bude baki tana kallonshi da mamaki dan bata taba zaton abunda zai fada ba knn...ganin yanda take kallonshi kaman wanda yayi sa6o ya sake hade fuskansu pointed nose dinshi na gogan nata yace"yes ina sonki..ina sonki tun ranar dana fara ganinki"..tun kafin ya rufe baki tace"No plss..stop saying this to my face dan Allah"..murya a raunane yace"why..it's what i feel"..da sauri ta toshe kunnuwanta tana girgiza kai tace"stop it plss..bana sonji"..tausayinshi da taji ta faraji yasa batason yacigaba da fada don yana iya raunata mata zucia..kallon yanda take rusa mishi kuka yayi yace"then mutuwa zanyi..i will die for sure"..still kanta tacigaba da girgizawa tana kokarin durkushewa a wurin yayi saurin kamata ya rungume a jikinshi...idanunshi na cikowa da hawaye yace"Aysher ki taimakamin plss..ni kadai nasan yanda nakeji a kanki..inajin ciwon ganinki tareda wani fiyeda yanda nakeji idan kina wulakanta ni..i love u so much"..tureshi ta shiga yi daga jikinta tana dukan chest dinshi amma kememe yaki sakinta kmr wani magnet...saida ta gama dukan kirjin nashi dan kanta snn ya kamata suka zauna gefen gado ya sake hade fuskanshi da nata yace"stop crying plss..sorry if i hurt u amma it's what i feel..Aysher idan kikace bazaki aureni ba mutuwa zanyi..zucia ta bazai iya juran ganinki in the arms of another ba..ki taimakamin ki soni ko bai kai sonda nake maki ba wlh i won't complain..i promise to be the most perfect hubby plss"..dakatar da kukanta tayi tareda daddagewa ta janye jikinta daga nashi ta mike da gudu ta fada bathroom tana banko kofar da karfi..Bobby ya dafe head dinshi da yaji yayi wani mugun sarawa yanxun nan...ya kwashi almost 7 mins yana zaune nan kafin ya mike da kyar ya fita daga dakin...a bakin kofa suka kusa karo da Mummy tana ganinshi ta kama hannunshi har cikin bedroom dinta snn ta saki hannun nashi tace"Bobby kana hauka?..why zakaje ka tsare 'yar mutane haka?..baka tunanin shaitan ya shiga tsakaninku?.."kama hannunta yayi ya dora chest dinshi yana dubanta da eyes dinshi da sukaui jajawur yace"Mummy bazan iya cigaba da boyewa ba anymore.. zucia ta bugawa zatayi"..kama hannunshi Mummy tayi suka zauna kan sofa ta dan kwantar da murya snn tace"kuma sai kaje ka tsareta ba ko kaya a jikinta?..bakasan shaitan is real ba koh?.."dora kanshi yayi kan shoulder dinta yace"Mummy bazan taba aikata abunda kike tunani ba..a yanda nake kishinta bazan taba bari shaitan ya shiga tsakanina da ita kafin aure ba..kawai na kasa controlling feelings dina ne..Mummy ji nake idan yarinyar nan bata aureni ba bazan iya cigaba da rayuwa ba"..shafa kanshi Mummy ta shigayi without saying anything..bata ma san me zata fada ba..wnn wane irin so ne yakema yarinyar nan haka?..wane irin sone yake neman zautar mata da Bobby haka?..anya kuwa ya kamata tayi folding arms dinta tana gani yaronta ya shiga wani hali akan soyayya?..anya kuwa bai kamata tay making wani move da zai taimaka masa ba?..wnn tunane tunanen ne suka taru suka cika zuciyarta..zuwa yanxu ta gama tabbatar da yake cewa idan bai aureta ba mutuwa zaiyi...tsaf tasan hakan zai iya faruwa amma wane hanya ya kamata tabi don tayi preventing faruwar hakan?..duk brain dinta ya cunkushe tama rasa wane tunani ya kamata tayi...mikewa tayi da sauri tunawa da tayi lokacin iftar yayi itama ko ruwa bata sha ba tazo kiran Aysha shine ta iskeshi a dakin..kama hannunshi tayi tana kallonshi tace"yanzun ka tashi muje muyi iftar sai muyi mgn later"..baiyi mata musu ba ya mike don yasan idanma yace ya koshi Mummy ba rabuwa dashi zatayi ba dole sai yaci and shi kashi yanada buqatan yasha ko ruwa ne sbd yayi breaking fast dinshi...hannunshi na cikin nata suka fita daga dakin..a dinning suka samu Miemie da Sab har sun fara iftar dinsu sai aunty sumy da itama ta fito yanxu...Mummy taja mishi kujera ya zauna snn ta koma ciki don fitowa da Aysha..har lokacin tana bathroom bata fito ba saida Mummy tayi mgn taji voice dinta ne da gaske snn ta bude kofan..riganda ya wurgar a kasa Mummy ta dauka ta mika mata ta koma bathroom ta sakoshi abjikinta snn ta kama hannunta suka fita dinni g..da kanta taja mata seat ta zauna snn itamata zauna tayi serving dinsu..wurin sai yayi tsit banda karan spoons ba abunda ke tashi...daga Bobby har Lamido babu mai cin abincin kirki kowa tunanin da yake zuciyatshi daban..ita tsananin tsoro da kuma mamakin yanda har yakeda guts din da zai bude baki yayana sonta take yayinda shi kuma yaketa kallonta yana sauraran yanda zuciyarshi keyi mishi ihu tana sake jaddada mashi cewa matukar bai sameta ba mutiwa zaiyi..ya lumshe ido ya bude duk hankalinshi na kanta yaga a kasa cin komai a wurin banda jujjuyawa da take sai yaji sam hakan baiyi mishi dadi ba..ko kusa bayason ta kwana da yunwa especially not yanxu da ake azumi..Mummy yayi da ido yayi mata alama da tayi mata mgn..murmushi ta saki tareda juyawa tana dubanta tace"Aysha meyasa baki cin abincin ne?..idan kuma wani abun kikeso yamxu sai a shiga kitchen a dafa maki"..daukan yamballs tayo da sauri tana kaiwa bakinta tace"zanci"..daga haka ta shiga tunkuda yamballs din kmr an aikota..saida taci guda 4 snn ta dauki kunun gyada dake gabanta shima ta kafa a baki tanasha kmr mai shan magani...duk Bobby na lura da ita dan even for once bai dauke hankalinshi daga kanta ba..kawai jinshi yake yakai limit din da bazai iya cigaba da hiding feelings dinshi ba..idan kuma ya dage sai yayi hakan then definitely zuciyarshi zata samu matsala...Lamido kuwa dukda ba kallonshi take zata iya rantsewa taji pearcing idanun nan nashi a kanta..ajiyar zucia ta sauke har yanxu gabanta bai bar faduwa ba ta dauki drink dake gabanta tasha snn ta ajiye goran tareda mikewa zata bar wurin shima yayi saurin mikewa don ya koma daki Mummy tace"dawo ka zauna"..kallonta yayi da sauri yace"Mummy bafa binta zanyi ba"..bata bari ya karasa ba tace"i said sit"..bai sake mgn ba ya koma seat din da ya tashi ya zauna hade da dafe kanshi da hannu..Mummy da tasan yanda yakeji da batayi yunkurin hanashi tafia bawlh..shi ba wajenta zaije ba kawai yanaso ne yajishi a kwance ko zai samu saukin abunda yakeji.
0 comments:
Post a Comment