Jinjina gareku
HEENDU
RAMCY MAKE UP
MOMMYN ZAHRA
HAJIYA ABOU
AUNTY SUMEE
HUMAIRA
ZULAIHAT
SAFEEYA AHMAD
Ina muku fatan Alkhairi tare da godiya da Sharhi.
Masu Sharhi na ko wanne Gp da wanda kuka min magana ta pc ina gani kuma zaku ganni Online wlh Simcard dina ne yake da matsala sai kun min Uzuri kafin na gyara,sako yana shigowa ina gani Amma ni Idan nayi reply baza su zo da wuri ba,kuyi min Sharhi ina gani kuma zan bawa ko wacce amsa Fatana kuyi min Afwa da Uzuri.
Kamar an sanar a gidan Radio haka muka dinga ganin yan gidan suna shigowa mata da Maza wasu na taba ganin su wasu kuma ban sansu ba,Kowa da kallon wulakancin da suke mana,ni kuwa ko magana banyi ba ko ina wuni bance da kowa ba nima kuma na cewa su Meenat karsu kula kowa,kaf yan gidan nan sai da suka sheda bani da mutunci bare kunya Sabo da zaman kawai da nayi a kujera ya isheka amsa, manyan ne kawai suke min kallon Banza ina kyalesu Amma indai mutum matashi ne ko budurwa yaro ko yarinya indai suka min sai na mayar musu da matartani ina daga zaune abina nima kuma basu Isa na gaishesu ba bare su Sa rai da mutunci na shigo.
Wasu manyan samari ne su Uku za suyi basu kai Aayan shekaru ba sunji labari ance musu Amaryar Aayan kyakyawace ta karshen gaske sai dai bata da kunya ko kadan,gata kuma kalar kauye ce duk iyayin Aayan ya kare a yarinya karama kamata kuma ba yar gayu ba,da sallama suka shigo bayan Sallar Isha Sabo da su Maza ne kuma suna da dan hankali,kallo daya na musu na dauke kai tare da amsawa a hankali,Ganin basuyi min kallon Banza ba yasa na saki fuska tare da cewa ina wuninku,suka ce lfy sannu Amarya ya gajiya nace Alhmdllh babu wanda ya kara magana,Sai kare min kallo sukeyi musamman wani a cikinsu kallo kamar maye hakan ma da Hijab dina,Sai ko naji yace Amarya ya kamata a mana girki muci mu ji,nace sai dai ku shiga kitchen da kanku ni yanzu sai na huta nasha gajiyar hanya daga wancan gidan zuwa wannan na jigata a Cikin mota Driver ya jijjigani da yawa a hanya na fada ina yatsina,mamaki ya kashe su abinda sun san gidan ba wani nisa da wannan unguwar Amma wannan yar rainin hankali ce wai mu shiga kitchen ma,
tasan ko mu su waye,kaji yar talakawa cewar daya a cikinsu ya fada a hankali bai san naji ba,daya kuma yace min kannen Aayan ne mu ni sunana Khaleel,ga Ameer sai wannan Mujaheed, nace good bari na shiga daga ciki,wanda ke yawan kallo na wato Ameer kenan yace a haba ko hira ba ayi ba,zama nayi kawai nayi shuru suma suna zaune sun dade sosai har wurin 8:30pm
Sai ga Aayan ya shigo rai a bace kamar zai daki mutane kadan yake jira,suna ganinsa suka min sallama suka fita,ni kuma na kalleshi yanda ya wuce da Sauri yana bin steps,Saman bed ya fada tare da kwantawa ruf da ciki ko me yake tunani oho ko wani abu akayi masa ban sani ba ni dai,nasan dai bazai wuce matsalar yan gidansu bace ni kuma ban san mene dalili ba bare nayi wani abu a kai,shi baya kulani bare nasan matsalarsu,ban ma san ko tarihin gidansu ba sai wanda na tsinta ranar ganina dasu na farko sai kuma abinda na fara gani yanzu a gidan kamar dai shi Aayan kadai shi suke warewa basa so Amma dai ban san komai ba,duk da haka sai naji tausayinsa,naji ba dadi me ciyar da kai ace yana cikin wani Hali dole ai kaji ba dadi sai kawai na wuce kitchen,Sharp sharp na dafa Indomie da kwai kar ma yazo yasa a kwashe su ya kawo mana su garin danwake shi yasa nace bari muci rabonmu,na bawa su Meenat na zuba wata a plate na nufi dakinsa can sama a nan na sha kallon haduwa.
Saman Bed na hangoshi a kwance ban san me yake yi ba bacci ko tunani,Aayan...Aayan na fada a hankali,a hankali ya bude idonsa tare da cewa Lfy? Abinci idan zakaci Indomie naga ka dawo daga Abuja baka ci komai ba,ko kaci? Kansa ya dago a hankali tare da kallo na ya dauke kai yace ni bana cin Indomie yanda ya fada kamar dan yaron goye a shagwabe,nace to me kake ci? Ai nasan baza ki dafa min ba bakya jin magana,fada zan dafa ma ai nayi hankali na daina, yaushe kikayi hankalin? Na daga kai ina tunani sannan nace an dade fa tun shekaran jiya, murmushin da bai shirya ba yayi kana yace Kosai nake so da kunun gyada sai danwake,nace to ai nan babu kayan yi a wancan gidan ne akwai,Waya naga ya dauka nan take naji yace a kwaso kayan dake kitchen da store na abinci a kawo masa part dinsa,wani bakin ciki ya dirar min shike nan mu baza muci abincin zamani ba,kamar yasan me nace sai naji yace shi kuka saba ci ai a gidanku idan na baku na yan gayu baza ku iya ci ba,nace mu dai zamu iya dan Allah,yace to ba yanzu ba sai watarana idan naga dama, cike da takaici nace shike nan ai,su Meenat basu da kudin Napep na zuwa schl,sannan nima dan Allah ka sani a schl,budar bakinsa sai yace ni bani da time idan kina da wani zan baki kudi ki zabi schl me araha private ya kaiki zan biya ni Bazan iya biya miki private me tsada ba,sabo da na raina basirarki, nace wai mene amfanin kudinka? Kallona yayi tare da Sa Headphone a kunnensa irin na takura masa haka na fita na kyaleshi cike da tunanin to wai me yasa ya aureni yana kallo ko kayan sawar kirki bamu da Amma ko Ya siya mana wasu to bai bamu abincin kirki ba ma sai wasu kayan sawa kawai dai raini ne ya jawo mana a danginsa.
Ina zaune a palo sai gashi an kawo komai na girkinmu irin na can gidan su dawa gero masara etc,Kitchen na shiga na fara shirin hada gyada da danyar shinkafa tare da lemon tsami na kunun gyada,ina cikin aikina sai ga samarin nan Ameer me kallon tsiya,khaleel da Mujaheed har kitchen suka ce Amarya girki ake shirya mana nasan ganin kwakwaf suka zo kuma sun gani su masara dasu geron,dan masifa suka ki fita daga kitchen din sai suka ce wai sai sun taya ni,nace a'a bana so kannena zasu tayani,sai ga Meenat ta shigo kitchen cikin English wears riga da skert tayi kyau Sabo da wanka tayi tare da fesa kwalliyarta da ta saba,aiko suka bi ta da kallo sunga me kyau da diri,ni kuwa a hijab nake baza su gane komai ba sai fuskata da take da tsananin kyau,Meenat tace Sis kawo na hada waken muna ta aikinmu tare suna kallo don zama sukayi a kitchen din wai sai an fara girkin sunci sunji,Ina tsoron tambayarsu gidan da ake markade na hakura mukayi a blender sai suka ga kosai mukeyi da kunun gyada,basa cin kosai su Amma suna shan kunun gyada,Aayan ne ya fito daga dakinsa Ya taho kitchen da niyyar daukan ruwa abin ya daure masa kai ganinmu gaba daya da rida ridan kannensa a kitchen muna yar hira jefi jefi sai tambaye tambaye suke mana akan girkin nan,ina tunanin zanga ya bata rai ko yaji haushinsu ko Ya musu magana su fita Maza bai dace su dinga shigewa mace me aure ba Amma sai naga ko a jikinsa ruwansa ya dauka tare da ficewa.
Muna gamawa naga sun zaro cups zasu fara eba,nace ku tsaya mijina fa? nasa ne dole sai na fara ebar masa,Ameer yayi murmushi tare da cewa Amarya ai ko nasan ne muna da yancin shigowa mu eba ko shi bai Isa yace kar mu eba ba,Kallonsa nayi nace to ni na Isa dan shi yasa ni nayi masa sai na ebar masa,Na gano ba so suke su sha ba takura min suka zo yi don kamar ma turo su akayi su Sa min ido.
Sai da na dauki wani jug me kamar flask na zuba ma Aayan, meenat bata ce mana komai Sabo da na hanasu magana akan dangin Aayan kosanta take soyawa,naje na ebarwa Aayan na ebar mana namu tare da kai mana Bedroom,na dawo lokacin Meenat ta gama soya kosai muka gyara kitchen sannan nace to zaku iya eba dan bakar jaraba suna palo sai da suka shigo kowa ya eba a cup suna sha duk wanda nayi suka shanye ba ruwansu da tambaya,Khaleel ma da yafi su rashin kunya Na Aayan yazo wai zai kara a ciki ya masa dadi, nan take na dauke komai tare da jerawa a wani tire me kyau sannan nace bazai yuwu ba kunsha rabonku nayi gaba na Barsu a palon,sama Na haura tare da knocking sannan na shiga yana zaune saman Sallaya yana addua na ajiye masa zan fita naji yace wait,ina tsaye ina jiransa ya gama tare da shafawa sannan naji muryarsa yace Zauna,can gefe na durkusa yace me suka ce miki su Ameer? Na bashi labari har abinda nace musu,yace to daga yau ko me suka ce ki musu kiyi musu ko nawa ne ki basu,nace ni Allah Bazan basu ba,nasha wahala kace na basu,to ba nawa bane nace ki basu,to me ya hanasu suyi auren su ko su tafi wajen iyayensu ni na haifesu da zan dinga wahala suna raina min Hankali,ina matarka tunda kannenka ne ai kamata yayi su dinga girmamani kuma sai suzo kitchen su tsaya min a kai ai duk kai kake basu kofa,kamar wanda ke jin tsoronsu ni ban gane maka ba,kace rannan na dinga ramawa yanzu kace na daina na bari kenan su takani ko? Shuru yayi bai ce komai ba,sai can yace nima kinga ban san me ke damuna ba ths month ina jin bani da lfy ni ban san ma meke damuna ba gaba daya,ina ke maka ciwo? Yace babu a jikina nake jin kawai da matsala bani da lfy ban san ya zan iya fada miki ba,tunanina mutuwa zaiyi sai na fara hawaye nace ni dai karka mutu dan Allah irin Ammah yanzu wa zai bamu abinci gashi muna ci muna koshi,kallona yayi da mamaki shi da yake bamu abincin talakawa Amma har dadi nake ji a haka ina fata kar ya mutu Sabo da wannan.
Miko min abincin,mika masa nayi sannan na zuba masa da Sauri wai dan kar ciwo ya kamashi ya mutu,ya karba a hankali yana cije lips ni tunanina ko jikin ne yake jin bazai iya karba ba,sai nace tsaya tsaya na karbi cup din nasa spoon a ciki ina juya sugar din sannan na rike masa a hannuna nace to bari na rike ma a haka kai kuma sai ka dinga sha ko na baka yanda nake wa su Meenat tunda baka da lfy? Banza ya min tare da bata rai yana ta fushi kuma yanzu kamar yaron da aka Zane,Sai ji nayi yace rike abinki ki sha,na fasa, yi hakuri gashi rike abinka Allah Sarki sha abinka kaji,ni kar na baka? Yace ae bana son naki, nace to gashi nan ni na tafi ma,na mike tare da bar masa dakinsa,na rigada na saba da Yiwa su Ma'eesha irin abun Yara idan zan basu abinci ko ina basu sai na dinga ta lallabasu shi yasa,ko ina basu ta dole.
10pm muna daki muna karatunmu ya shigo Bedroom dinmu tare da cewa zo,Maeesha tace Hi Uncle,murmushi ya mata tare da daga mata hannu,Meenat ma ta gaisheshi ya amsa da sakin fuska kadan,Hijab dina na Sa tare da binsa a baya har Bedroom dinsa yana Saman Bed ina kasa a tsugune yana ta faman cika yana batsewa ga jarabar takama,yace gobe ki shirya 8am kuje ku gaisar da Hajja kakarmu ko me zata ce karki mayar mata da martani kiyi biyayya,nace to Insha'allah,yace muje yanzu wajen Abbana,nace au kana da Baba mahaifi? Yace of Course ai ni dan gata ne Umarninsa nake bi,murmushi nayi nace kuna kama? Yace mene kika tambaya? Idan kuna kama to nasan Babanka ma me kyau ne ko Ummanka ka biyo?ke dadina dake shirme,Ummanka ta rasu ita? Ya daga kai tare da cewa kuma nafi son Abbana ba tun farko,Nace tab ni kuwa nafi son Ammah,Abbanka yana Sonka kenan da yawa gani nayi yana ta farin ciki kawai akan nayi zancen Abbansa lallai yana sonshi,fuskarsa na leka nace Dan Abba zan dinga ce ma yanzu,muje na ganshi ma zan dinga kai masa abinci,yace ai ba komai yake iya ci ba,bashi da lfy ya fada kwalla kamar zata zubo masa,nace eyya ai Insha'allah zai warke ne,lets go kawai yace min,nabi bayansa falau falau da hijab muna ta sheka uban tafiya yana gaba ina bayansa har muka je wani building a Cikin gidan katafaren me kyau,ciki muka shiga kafin ma mu Isa inda zamu hau steps duniya ce guda ko ina kuma Securities ne masu tsaron Daddyn Aayan, sannan muka haura sama can wani Bedroom shima nan duk sune suke tsaro har cikin dakin,saman Bed na hango shi dattijo kyakyawa irin Aayan suna kama sosai sai daí Aayan ya fishi farar fata,sallama mukayi masa da mamakina naji ya amsa yana murmushi tare da cewa My Son kazo ke nan,Aayan ya karasa jikin Bed din tare da rike hannunsa yace Daddy ya jikin? Alhmdllh Son yanda kasan jikin kullum haka yake ina so na taka kamar kowa Amma bazai yuwu ba,kana gani komai sai dai ayi min haka nake ba inda ke motsi a jikina sai baki na,addua kawai itace Mafita tunda ba inda ba aje ba ciwo yaki ci yaki cinyewa,to hakanma mun godewa Allah.
Ina mamaki yanda yake fes haka cikin koshin lfy ace wai baida lfy komai nasa baya motsi gashi shar dashi muryarsa ras haka,a hankali naga Aayan ya rada masa magana a kunne nan take ya fara murmushi tare da cewa Yata matso kusa ya kika tsaya nesa,Da Sauri na karasa gaban gadon tare da durkusawa har kasa nace Ina yini ya jikin?Yace Alhmdllh,nace Allah kara lfy,Ameen yata Gashi nan sai kinyi hakuri kin ganshi baya jin magana na dade da cewa ya kawo min ke sai ya dinga min hanya hanya,Murmushi nayi ina jin kunya nace ai yanzu ya kawoni kuma kullum zanzo ba sai ya kawo ni ba yanzu tunda na gane hanya,Murmushi yayi tare da cewa na gode Allah ya muku Albarka,ya albarkanci aurenku ya baku zuria ta gari,Ya sunan yar tawa nace Mufeeda,Alhmdllh naji ance da kannenki ko?nace ae yace to Allah rayasu ya musu Albarka nace Ameen,Allah yaji kan mahaifiyarku nace Ameen Daddy, ki kara hakuri kinji,zaman gidan nan sai hakuri,wannan dan nawa baya ji kin ganshi ina fama dashi sai kinyi da gaske saurin fushi gareshi ga zurfin ciki,ki rike min shi da Amana yata kinji,nace Daddy ai shine sai ya dinga fada yana fushi, Dariya yayi sannan yace to zan masa fada,nace to Daddy,Harara Aayan ya zabga min nayi shuru dani,Mun dan dade a dakin Aayan suna ta hira sannan yayiwa Daddy sallama muka dawo part dinmu,na wuce dakinmu shima yayi samansa.
Cikin dare 2am na farka da ciwon Mara sosai naji kamar abu ya zubo min a pant,mikewa nayi da Sauri na shiga toilet,sai naga period nima na fara dan ban taba yi ba sai yanzu,Meenat kanwata kuwa ita tun tana Jss 2 ta fara dama ta fini kiba, fitowa nayi tare da tashin Meenat nace Meenat tashi ki bani pad nima na fara period,cikin magagin bacci tace Sis ta kare tun last month wacce kika siyo min na karar da ita,To fa yanzu ya zanyi kenan,ki Sa tsumma kafin gobe,ke da rushing na fara fa wlh tsumma bazai daukeni ba kinji yanda yake tsiyayowa kuwa,to yanzu ya za ayi kenan,nace bani dankwalin tsohuwar a tamfar nan taki na Sa naje Wajen Aayan ya san ya zaiyi dani,Meenat tace baki jin kunya? Kuma kin san bazai je ba sai dai yasa me gadi,a'a zai iya karbo min ko wajen yan matan gidan nan ne kema kin san Bazan iya kwanciya haka ba gashi dare yayi dole tunda lalura ce kuma yasan mata sunayi ai dole gunsa zan je.
Haka ne kam jeki to muji,nan na karbi karamin dankwalin na koma toilet tare da gyara jikina don nasan kafin naje sama Na dawo na bata kayana ko ma ya dinga saukowa saman tiles.
Cike da tsoro na masa knocking shuru har sai da nayi yafi sau goma sha sannan naji yace Am coming yana jan tsaki ya bude min kofar daga shi sai wani dan tight short karami ko riga babu a jikinsa,daki ya koma nabi bayansa Sabo da ya kunna light din haske ya gauraye dakin,lfy ciki dare? Na fara ina ina uhm...uhmm..na juya baya tare da tamke idona kawai na maze kamar bani na fada ba nace ehmmm wai..Wai,yace to fitar min tunda baki da abin fada,da Sauri nace period na fara kuma bamu da pad gashi dare yayi ko zaka karbo min wajen kannenka na karasa tare da matse idona kam na juya masa baya.
Tsaki yaja tare da cewa sai ki bari sai gobe kya siya ni me ya shafeni a nan fitar min a daki na zata wani abu ne,Marairaicewa nayi ina rokonsa dan Allah Dan Abbansa ka amso min pls haba Na Daddy,kallona ya tsaya yi yanda nake shagwaba kamar yarinyar yaye, hannu ya daga min hey..hey Hold it thr ban son shirme see u ko kunya baki ji kina min shagwaba ya fice fuuu ya barni,murmushi nayi tare da cewa oho dai ni dai ka karbo min shike nan.
Yana fita na fada saman Bed dinsa nace sai na more naji dadinsa yau dai na dinga birgima a kai ina tunanin zaman da zamuyi wanne Hali zan aro na daurawa kaina dan naga karshen yan iskan gidan nan,tsawa naji keee...Ban san sanda na fado kasa ba dan na manta a Bed dinsa nake,yace Iskancin naki har ya kai Bed dina nan take ya bude wardrop tare da dauko sabon bedsheet ya jefo min tare da cewa cire min wannan kazantar zaki shafa min a Bed shimfida min new, ban bata ma bafa kalla ba komai a kai fa,i wl slap u,ba shiri na cire wancan na shimfida masa wanda ya bani tare da dame masa yayi kyau,wani turare ya miko min ungo fesa a saman Bed din,haka na fesa,yace to jeki da wannan ki wanke min gobe ki dawo min da Abuna Kazama,nace haba Ranka ya dade ka rage irin wannan ni fa matarka ce Amma kwata kwata baka kyautata min,ko Auren business ai ka bari dai mu rabu lfy Amma ba komai bani abun na tafi,naje sunyi bacci ban samo ba,To su manyan matan su Abbi fa? Ko lokacinsu ya cika basa yi su? Baki ya tabe tare da cewa bama shiri taya zanje nace su bani sun san ke zan bawa baza su bani ba,kuma dare yayi bare a siyo,sun tsofe ma wanne period zasuyi ai sai yayansu, nace to ni yanzu ya zanyi na fada kamar zanyi kuka ina doka kafafu,tafi ki san me zaki Sa sai gobe,ni Bazan tafi ba ya kake so nayi dan Allah,tunda farko ne ai bazai miki da yawa ba kije kawai,nace to ni nawa ba haka yake ba kana ta sani ina fadar badala da rashin kunya a baki na,baka san yanda nake ji ba idan ina ambata irin wannan lafazi na Badala a gabanka, murmushin da bai shirya ba ya saki,oh nan kunyata kike ji kenan,wlh da kyar nake iya magana lalura ce ta kawo ni dan Allah a san yanda za ayi dani Na Daddy Allah dai yaji kan Mommynka ya dauraka akan makiyanka,jin nayiwa iyayensa Addua sai naga ya saki ransa kamar wanda aka Yiwa Bushara da Aljanna yace to yanzu ya za ayi kenan? A raina nace na gano lagonka,nace babu 24hrs ne a Kano?Yace da dai Abuja ne sai a samu kuma kinga 2am ba kyau fita ko fitsari tsakar dare nace haka ne,amma muje mana wajen yan matan ka rakani ni zan san yanda dole ma su bani.yace to muje a Cikin wardrop ta jikin Bed suke ajiyewa,nace an gama muje.
Tiryan tiryan muka je har kofar dakin daya,yace wannan dakin Hanifa ne,ai ko na dinga knocking kamar dakina ta bude sai ta ganni tare da Aayan da har zata min masifa ganinsa yasa tayi mukus don tsoronsa suke ji,ni kuma da tsokana kawai nayi ciki da ita tare da tureta na banka cikin dakin,direct na bude wardrop Aiko na gansu a jere na dauko sinki daya na bude na kwashi guda uku sannan na watsar da ragowar a kasa nazo zan wuce na bata rai,tace wlh baki Isa ba ni zakiyiwa wulakanci har Bedroom,na kalleta sama da kasa nayi irin gwanar nan nace How Dear u zaki na min magana any how duk wanda yaji zaice na gama kwarewa da Turanci,taki Sakina kuwa,na kira Aayan Babyna da Sauri ta sakeni tana hararata na fito nace masa muje to,muna Tafiya a hanya nace nayi fashi da makami kaga abinda baza ka iya ba,kai kullum sai ka dinga zura musu ido kamar wanda suka Yiwa asiri danma suna jin tsoronka ai da tuni ina ga kowa ma taka ka zaiyi.
Ki shirya gobe zasu zo daukan fansa wlh harda iyayensu,nace dan Allah ina son muyi magana da kai Na Daddy Allah ya karawa Daddy lfy da nisan kwana, ina binsa a baya da Katon Hijab dina har Bedroom dinsa,ya fada saman Bed dama yasa jallabiyarsa,a hankali na zauna a gefen Bed din ina jin tsoro,ina jiran naji tsawa sai naji shuru,ina zama ina cewa Fatana Allah ya bawa Daddy lfy wlh a gidan nan,da anga yanda zaifi kowa Sonka ai da kafi karfin kula mu ma Sabo da ka zama Gold,yanda naga Daddy na Sonka abin sai wanda ya gani inama Abban mu haka yake irin naka na furta tare da kwanciya na mike sambal a gefensa,tunanina wayo zan masa shi kuwa tuni ya san me nake nufi Amma sai ya shareni ya gama ganin iya wayon nawa me nake nufi.
Dan Daddy wai ya maganar schl din tawa,yace anzo wajen,nace dan Allah Oga kwata kwata ka kaini schl,yace hmm yana dariya a ransa wai shi yar wannan Jaririyar zata Yiwa wayo,yace dama Arabic da boko kika shiga a hade tunda naga kinfi kokari a Arabic sai ki hada biyu abinki,nace ah gaskiya a'a nima nafi son na zama yar boko sosai,to ki zabi wacce kike so sai na biya miki,Nace to, Amma ai sai dai wani ya kaiki,bani da time ki samu wani a yan uwanki ko frnds su kaiki zan baki kudin,nace to zanje Amma dan Allah kasa a kaini a mota kaga raina ni za ayi a gidan nan,yace an gama,duk tunanina da gaske yakeyi sai murna nake yi nayi masa wayo,nace saura kayan sawa zamuje shopping Sabo da goge raini,yace nawa ne zai Isa a goge rainin?nace ko dubu goma sun isa,ya kyalkyale da dariya ku Uku dubu goma to kaya kala nawa zaku dinka kenan nace kala Uku Uku ko hudu,yace lallai dasu zaku goge rainin kenan? Nace to ni ban san kaya ba tunda ai kasan ba siya muke sosai ba.kawai biye min yake yaga iya wayon nawa.
Dan ya nuna min na masa wayon sai yace bude can,naje na bude wata Wardrop,nan take na kusa sumewa kudi ne a jere a jere bundles da yawa na Dubu dubu da dollers,yace ebi yanda zai isheku,nan take gumi ya keto min na rude na rasa yanda zanyi jikina yana rawa na ja baya tare da cewa ni dai sai dai ka bani da kanka, ba yanda baiyi dani ba kan na dauka Amma na kasa sai ma shagwabewa danayi zanyi Kuka kudin sun tsoratani,mikewa yayi tare da kwaso Bundles goma yan dubu dubu ya zube min a gabana yace jeki dasu ai sai na fashe da kuka nace bana so ni,kamar naga wani Dodo na dinga ja da baya,yana dariya a ransa a fili yace kefa kike son kudi,nace ni ba irin wannan nake so ba,tunda kace sai na Eba da yawa to bani dubu ashirin sun ishemu komai da Komai,yace naga ai an baki kudin Sadaki har dubu dari Uku ya kikayi dasu?lokacin ai bana cikin hankalina Sabo da rashin lfyar Ammah da rasuwarta duk a nan suka kare.
Bundle guda ya bani na yan dubu da kyar na karba na tsaya ina tunani,kafaduna biyu ya rike tare da bude kofa ya jefa ni waje tare da rufe kofarsa,Bedroom dinmu naje da murna na nunawa Meenat tace gaskiya Sis tsakani da Allah kin damemu a wannan tsakiyar dare 3am ta wuce kinki bacci sai labarin mijinki kike mana ki kwanta mana ki huta,ni dama idan labari na Cina to komai dare sai na tashi mutum na fada masa,bayan na shirya kaina duk sun koma bacci har na kwanta nima na tuna ban fadawa Meenat labarin Daddy Baban Aayan ba.
Tashinta na fara yi Meenat Meenat ku tashi kuji banza suka min nace wai ina magana kun rainani ko,muna ji ki fada mu wlh bacci muke ji ke bakiyi ba kin hana kowa yi,ina basu labari suna uhm..eh...to...har bacci ya kwashe mu,kafin asuba wayata tayi kara ta tasheni ban dauka ba Amma sai na tashi Meenat,kawai sai ta fashe da kuka wai na hanata bacci,nace to yi shuru kwanta jaraba bakwa jin maganar Ammah tace kuyi min biyayya Amma bakwa yi,Maeesha ta farka itama tayo fitsari muka koma bacci,ni dai banyi wani baccin kirki ba sai na dinga tunanin Mijin Kasuwanci na.
Washe gari da Safe lafiyayye tea na hada mana Sai kwai na hadashi murtuk dashi naga banza ta fadi irin muci rabonmu kafin yasa a kwashe mu koma Koko,sun sha Uniform dinsu ni kuma doguwar riga da dan hijab karami,tun Safe yan gidan suke ta buga mana kofa ina ji naki budewa,bugun duniya naki budewa sai ma kara Sa lock da nayi,Ina jin Abbi yana zunduma mana ashar akan naki budewa yaransa kofa,wai nice ma zan musu breakfast kuma abinda suke so haka kowa zai fada na dafa musu,ai kuwa bugun duniya muka ki bude kofa gashi suna jin motsinmu,Abbi na gani ta jikin window ya leko yace sai kun bar gidan nan wlh tunda ba yar arziki bace ke,yar Iska,guntuwar shegiya haka ya dinga zagina ta window,na kalleshi ido da ido tare da Galla masa harara na murguda masa baki,yace zaki ci ubanki wlh sai naga waye ubanki a kasar nan,tafi nayi da hannuna na kara Harararsa ina gatsina masa goshi da gira,ni dai bance komai ba,yana ta zagina,ke yarinya ki shiga hankalinki,a nan nayi magana nace Yarinya tana bayan Uwarta ni dama haka nake idan naji haushi bani da mutunci ba kowa nake iya dagawa kafa ba ko za a kasheni,Meenat tana ta dariya Abbi ya kara kulewa,ya bar wajen a fusace yana baza babbar riga.
Aayan ne yake saukowa yasha wankan gaske cikin kana nan kaya,kamshi na tashi,Meenat tace ina kwana suka gaisa,Maeesha ya rikewa hannu tare da cewa ba gaisuwa yau?tace ina kwana tana dariya,tace kayi kyau Yaya,tnx yace sannan ya kalleni tare da cewa Abincina fa? Ai ban san zaka ci ba bari na hada ma tea,yace a'a Kunun gyada nake so ko Koko ni,idan babu kuma sai ki bani Tea,ai dole nayi maka,yo Allah na tuba ko ba gasara ai dole a nemota kamar Dan Daddy guda yana so akanta ba sai ayi yaki ba a gidan nan,Dariya na bashi sosai yanda nake maganar cike da girmamawa kamar Ina gaban Sarki,kun san wasu mazan akwai son a yabesu ko a girmamasu,wasu kuma suna so a daraja musu iyaye ya dace mata su dinga fahimtar mazajensu.
Shi Aayan a ransa yace zan gama kure wayonki yarinya har yaushe aka haifeki,Kitchen na shiga dama jiya na tace mana markaden koko,sharp sharp nayi masa tare da soya masa Chips tunda ba time din yi masa kosai,a Dining na ajiye masa sannan na dawo palo wajensa nace Ranka ya dade an gama,a ransa yace zanyi maganinki soon wai ke me wayo.
Ni na zuba masa da kaina,yana shan abinsa yayi nisa nace da sha nace Dan Allah ina neman wata Alfarma idan da hali ba damuwa kuma ban takura maka ba,yace ina jinki,nace so nake ka bani Driver daya da mota za a kaini unguwa zanje shopping sannan zamu je schl din da zan shiga,waya naga ya dauka tare da danna kira Malam Garba shugo ina son ganinka,minti kadan sai ga Malam Garba Driver yazo,Key din mota ya miko min na karba,yace gasu nan daga yau in zasu je unguwa zasu dinga kiranka kana kaisu inda suke so,ga key din mota nan a hannunta idan zaku fita ka karba idan kun dawo ka bata key din a hannunta,har schl zaka na kaisu,Malam Garba yace an gama Alhaji,nace ga key din ka kaimin su Meenat schl da yamma kuma zamu fita na fada ina wani mazewa irin matar Alhaji,Aayan yana kallona duk abinda nakeyi.
Yana gamawa ya mike tare da kara ajiye min Bundle guda na yan dubu yace gashi ki biya kudin schl din ragowar ku kara a shopping karki dawo da kwandala gidan nan duk ki tabbatar kin karar dasu a shopping,nace da gaske mu kashe duka zaka kara mana na cefane?Yace yes.
Yana fita na dinga tsalle da ihu tare da su Meenat,nace ai na fada muku ni ba a ja dani duk jarabarka sai na ma wayo,gashi dai kwana biyu har na samu abinda nake so,Meenat tace to bari mu dawo muje shopping wlh za a buga damu har mota ya bayar ana kaimu unguwa fa,Meenat tace Sis yau sai munje tsohuwar Unguwarmu a motar munyi musu birga,nace ke banza ce ba yanzu ba sai mun siyi kaya masu tsada mun koma yan gayu sai muje a gaisa ayi zumunci
Muje na rakaku mota daga nan mu ganta,gaba daya muka fita har inda Aayan ke ajiye Cars nasa,Malam Garba muka hango a wata shegiyar Benz yar gaske sabuwa dal wai itace zamu dinga hawa,su Meenat suka gaisheshi ya amsa yana me fara'a don gidan kaf babu wanda ke Saurarar dan aiki bare a gaisar dashi komai girmanka.
Meenat suka kame a gidan Baya,sai ga yan matan nan sun fito zasu tafi schl suma ina ganinsu nace pls Baba Driver ka kular min da motata ,ido suka zaro yaushe na samu matsayi har Aayan ya bani mota.da Sauri naga Hanifa ta koma ciki tana zuwa ta zayyanewa kakarsu dasu Abbi.
Ina ciki ina aiki naji bugun kofa na leka ta yar kafa na hango su Aiko naki budewa bugun duniya naki aikina kawai nakeyi.
Aayan na gani ya dawo yace na bude ina budewa Hajja kakarsu ta wankeni da Mari,ga hannunta kamar jikin bishiya Sabo da fatar duk ta tsofe ta bushe.
Zata kara min na goce,nayi niyyar magana haka nayi shuru ganin Aayan na kusa.
Abbi da Maza da mata sun kai su goma kowa da kalar zagin da yake min,Aayan na gefe ya kalleni na kalleshi,matar Abbi tace ke har kin Isa matsiyaciya daga kawoki cin arziki,na kalleta idona a bushe nace yo ai bake kika auroni ba,kema ai ba gidanku bane aure ne ya kawoki,kuma wlh Bazan ragawa kowa ba tunda ba aurenku nakeyi ba,Hajja tace iyye au Iskancin naki ya girma haka ina magana kina magana kin san dawa kike magana,nima ai baku san wace ba,Aayan ta kalla tace kai saketa yanzu na bada Umarni,maza rubuta mata saki,nace ku kuke tsoron saki idan an sakeni sai me rayuwa zan fasa ko me,Kaka tsohuwa Hajja ta rike baki dan tunda take babu wanda ya taba mata ko musu Amma gashi ni tana fada ina fada,tace saketa nace,Aayan yace baku kuka Sa na aureta ba ni ne naga dama kuma da dalilina Bazan saketa ba ya juya yayi ficewarsa tare da cewa idan kin gama ki kira Malam Garba a waya na ajiye miki Number dinsa a Dining,nace to Ranka ya dade a dawo lfy Allah ya tsare min kai,yace Ameen,nace Million dayar daka bani sunyi kadan Yanlabai,yace kin san inda suke kije ki kara yanda zasuyi,na Gode Allah ya kara budi,yayi gaba na kalli Matar Abbi Hajiya Karima nace kiji dan Allah Baby bashi da dama wlh common shopping a baka yafi million ga kyautar gida ga mota yau da Safe,tsaki naji sunja Hajja tace a sannu zan shayar dake mamaki wlh sai na canja miki kamanni ba a takani da yarana a zauna lfy.
Na kalleta nace aiki ya ganki ga tsufa ga shiga rayuwar wani Allah ya taimaka,wlh dan ina ganin girmanki ne ko ba komai zaki ci darajar tsufa da kuma matsayinki na Mahaifiyar surikina kakar Mijina idan da mutunci ke kakata ce Amma baku san haka ba,ku tambayi wace Mufeeda a Unguwarmu kowa yasan yarinyar kirki ce kuma ta wanni fannin bani da mutunci wlh da ace haka kawai ne da kun san wace ni Amma kunci darajar Mijina,ba tabani a zauna lfy dan ma ba akan kudi bane,bana yarda a taba lafiyar hanyar cin Abincina akan wannan bana dagawa kowa kafa.
Matar Abbi ce ta fisgoni suka hadu da Sauran matan suka fara dukana,sai da suka fasa min gefen bakina kadan hakan ma dan na gudu ne da Allah yasan irin Illar da zasuyi min.
Daki na fada na kulle nayi Kukana boye a fili nace wlh kun jawowa kanku dan ni indai ba lallabani akayi ba to kara lalacewa nakeyi, musamman akan kasuwancina dan yanzu auren nan ta hanyarsa muke ci muna sha shine kasuwancina kuma kowa yasanni akan Business ba mutunci zan iya ja da kowa.
AsmaBaffa
[1/9, 4:55 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖
KASUWANCI NA
41-45
Official
By
AsmaBaffa
MMN BASMA,SALMAT BASHEER,SUBYUSMAN ga page na baku Sabo da kauna ina Godiya.
Gaisuwa cikin Trailer zuwa ga
HAFSAT KHAIRAN
OUM FAROUG
MUM SUHAIL
MAMAN HAIDAR
HAJIYA JAMILA
MAIMOUNA MATER ta NIGER.
Kuna Raina
MEENAL SIDI
YA SALAM
DJU LUV
NANA KHADIJAH
OUM SALM@
Ina jinjina muku da Sharhi na gode.
Bayan na gama gyara gidan kaf ko ina yana sheki da kamshi,tuwon danyar shinkafa nayi tare da miyar egusi harda naman Kaza Sabo da a kwai a fridge,a dining na shirya mana komai cikin Food flask masu shegen kyau,wanka nayi na shirya cikin material cotton riga da skert nayi kyau sai ka rantse me tsada ne,dan Mayafi kawai na Sa a saman kaina wanda yasha gyara,1:30pm Sabo da a motar gida ne ba bata lokaci sai ga su Meenat sun dawo suna kwala min kira,Ku karaso mana ina ciki kuma sai kirana kukeyi,Sis yanzu muka ga Yaya Aayan a Compound su Abbi sun sashi a tsakiya tare da tsohuwar nan kakarsu sai masifa suke masa,ko saurararsu baiyi ba kawai jinsu yakeyi,Baki na tabe nace saji dashi can kuje kuyi shirin Islamiyya ga abinci nan a Dining,Bari na kira Malam Garba ya karbi abinci yaci sai muje unguwa, a waya na kirashi ya shugo na bashi abinci a flask dama na ware masa nasa daban Aiko yaji dadi sai murna da godiya yakeyi don ba a basu abincin gidan yan aiki suke burkuta musu ko wanne kwamacala ko dadi babu,fita yayi yaci ya koshi sannan ya kawo min flask din,nace in ba damuwa mu fita ka kaini unguwa,yace ai ba matsala,kudi na zuba a jakata na yafa gyale na me dan girma kalar kayana,can na hango dandazon Family ana meeting akaina irin yanda za a dauki mataki a kaina,Aayan yana zaune gefe yana latsa waya,kamar ance ya dago muka hada ido dashi, hannu kawai na daga masa irin na fita,baki ya tabe irin ina ruwansa,bayan tsadajjiyar motarmu na shiga na wani lafe a kujera ina game da yar Nokia ta wacce dan gidan Comissionar ya bani ,wata Aisha College nace ya kaini kana na Yiwa Malam Garba bayanin ya Zama wakilina a matsayin Babana ya kawo ni schl nan na tsara masa komai,yace ba damuwa yata.
Schl din 2 to 5 pm ce yare biyu akeyi Arabic da boko,Kafin ka gamata ka kware wajen Turanci da larabci tare da Sauran karatun addini dana boko,tana da kyau sosai,bayan munje wajen Pc mun masa bayani yace kinci Sa'a saura kwana Uku mu rufe daukan student na wannan shekarar,da kansa Yamin tambayoyi a lokacin na nutsu na Bada amsar wasu wasu na fadi,yace Ss1 zai sani nace to na gode,haka na biya 15k kudin schl fees,na Bada kudin Uniform har kala Hudu,sai kudin littatafai,nace Ina da aure ayi min Hijab me dan girma,haka aka gwada Size dina da komai na mikawa Malam Garba kudin ya biya a matsayin shine Ubana,aka Sa min sunana Mufeeda Adam Fatima yanda muke amfani dashi.
Bamu zarce ko ina ba sai inda ake siyar da schl bags da su Sandals na siya kala Hudu hudu suma tare da Sauran kayan karatu da komai,komai me kyau me tsada na siya,muna Tafiya a mota naga masu saida Glass na fuska,nace ya tsaya na siya,haka na zabi maka makan glass na yan gayu na gwada sunmin masifar kyau,da baki,da Brown sai farare biyu wanda ake yayi na zamani latest,yanda suka min kyau ba a magana,tun a motar na kara gyara fuskata na sa bakin nan faskeke kowa ya kalleni sai ya kara ya min kyau gashi kuma No respect.
Yanda na fita na barsu haka na dawo na samesu ana ta maganganu an hana kowa tafiya tsohuwar banza tana ta isa da Mulki ita ke magana har da wata jaka ta yan mata a gabanta wai itama fa bata tsufa ba,ganin suna wajen koda mukayi parking ban fito da wuri ba sai da na dauki lokaci yanda naga Aayan yana yi,sannan na zuro kafa daya da sabon cokeken takalmina me tsada dana siyo a wajen masu takalma na ganshi ya birgeni Dubu Bakwai na siya da jakarsa me kyau,irin zanen dake jikin material din Golden,ba wani iya tafiya nayi da me tsini ba amma karfin Hali yasa nace ai dole a je damu muma,ina fitowa sai da kowa ya Bini da kallon kurilla,yanda naci uban acuci da gashina kuma ba dankwali na daura ba kawai gyalen me dan girma da dan kaurinsa na mutunci na yafa a kaina sannan ga glass dina,Malam Garba ne ya kwaso min kayan a ledojin store din dana je,karba nayi nace na gode kaje kawai Baba sai zuwa bayan Magrib zamu fita again sabo da zamuje shopping da kannena na,yace ba matsala Allah ya kaimu,nace Ameen sannan na bashi Dubu Dubu biyu nace a saiwa iyali Alawa,ya dinga godiya nace No Need Baba Ai ba komai.
Su kuma dangin Aayan tunaninsu wasu kudi Aayan ya fara sakar min yanzu,nan take bakin ciki ya rufe su,musamman yan matan nan yau daya sunga na fara komawa wata Baturiya, Aayan yana ganin irin tafiyar da nakeyi ni ga yan mata,kwas kwas na cuno lips gaba irin yar gayun nan,nazo ta gabansu na makale Murya tare da Sallama ba wanda ya amsa nima ban damu ba dama na sani,na matsa kusa da Aayan yana zaune na sunkuya tare da rada masa taso Kaci abinci tuwo ne nasan kana ci ko? Yace zanzo kije yanzu magana akeyi min na Family,nace wanne family? anan tashi mu tafi ni dan Allah wannan har wasu dangin kirki ne,Yana so ya Harareni ko ya min rashin mutunci amma ba Hali sabo da Idan ya min haka zasu gano gaskiya sannan zasu kara wulakanta mu.ganin yaki tashi still ina tsugunne a gabansa nace ko tsoro kakeji? Naga Alama wlh tsoronsu kakeji muje ni zan tare ma fadan ko me za suyi ma zan amshe ma,tsaki yaja kadan tare da mikewa yace muje naga kin fara rainani dan kinga ina sakar miki fuska,ko kallonsu baiyi ba suka ga na janyeshi munyi tafiyarmu,Hajja makirar Tsohuwa tace kar kowa ya masa magana Ku kyaleshi ai Ubansa ya isa dashi zan yi maganinsu,kowa yaje yasha sha'aninsa zan nemeku,
Haneefa tace wannan kwai tsinanniyar Yarinya wlh,Allah ya dau ran shegiya a huta da yar Iska,Dayar a ciki tace shike nan na kasa cika burina sai da nace wa Abbi yasa Aayan ya Aureni yace baya so naje na fada sonsa na kasa cika masa burinsa,Sauran yan matan suka ce ke dai bari ai Allah ya yarda sai an saki yarinyar nan shegiya ko Nono bata dashi bata fi 16yrs ba fa,Ameer yace 17yrs take amma wlh ta iya girki dan baku jiba ne gata me kyau da tsafta inama ni na aureta,ai ni wannan ko Haihuwa nawa tayi burina Aayan ya saketa ko ta halin yaya sai na aureta,Dariya sukayi dukkansu suka tafa da yan matan,Khaleel yace mayen mata yaga kayan Dadi kana jin Aayan zai kyale yarinyar nan ko Sufi ne shi? Ameer yace ina ai wlh ko abarshi bata motsi indai bata motsa akan yarinyar nan ba to ina tabbatar ma har abada babu kuma macen da zata gani ta motsa a kanta,Dariya suka kara shekewa da ita su Haneefa harda shewa,Mujaheed yace ka manta Aayan din yanzu ne fa dan bashi da lfy ya rage amma sha'awarsa ta kai karshe,jarababbe ne na karshe kullum cikin chargi yake baya Free dan bura uba ai yanzu ya gama da wannan yarinyar fitsararriya sai shegen baki kamar gidan tsutsa,Ameer yace ai zaiyi dadi ne lips din,Haneefa tace Ameer da Alama ka kyasa fa,yace tuni ni wlh sabo da ita nake shiga part dinsa so nake ko hannunta ne watarana dole na shafa dole sai mun raba jikin nan nata da Aayan,Mujaheed ya jinjina kai to ka dai bi a hankali kasan halinsa wlh kana ganin kamar baya damuwa ana abu kasan ba a taba masa mata ko zai shekara dubu bai taba abarsa ba indai wani ya taba masa mata wlh yaki kawai za ayi gidan nan,dan kasan shegen akwai kare mutuncin iyali,za kaga kamar bai damu ba yana sani kai kasan yanda Khaleel sukayi akan matarsa Bilkisu wacce Daddynsa ya fara aura masa Sabo da karfin sha'awarsa aka masa aure da wuri tun bai gama Degree ba,kuma duk da haka bai ko taba jikin Amaryar ba ya gano cewar da yarinyarka ce tun tana waje kuma kun sheke da ita,ya akayi farko sanda kake zuwa har Bedroom dinta kuna shoshalewa ya sani Amma ya muku banza kalli dai irin yanda ya gasa mata aya a hannu ga na Family sannan kuma ya mata saki mafi muni,sai a lokacin muka san ko yatsanta bai taba rikewa ba,hmm kai dai bari ashe matsiyacin ya sani tuni,Ameer yace ai ni so nake ma na kulla mata sharrin da zai saketa ni kuma na koma wajenta,ina nan ina hada mission dina.
Ni kuwa tare muka jera muka shiga ciki ba wanda yayiwa wani magana ya wuce Bedroom a matukar gajiye,nima na samu su Meenat basu dawo daga Islamiyya ba,a gurguje na cire mayafin da glass dina tare da takalmin,na dauki kayan gaba daya nayi saman Aayan dasu,sai da na shiga naji karar ruwa yana wanka,ajiye ledojin nayi na koma tare da kawo masa abincin na ajiye,ina Zaune ya fito daure da dan Towel yana goge jikinsa da wani karami a hannunsa,kaina na dukar kasa ina wasa da yatsuna ban dago ba,shi kuwa ko a jikinsa har ya gama shirinsa sai kamshi naji yana tashi,ina dagowa naganshi Sanye da 3qrt da t-shirt yasha kyau yana jikin Mirror yana gyara gashinsa,na kalli Namiji yanda yake ta shafa man gashi masu tsada kala kala yana tajewa, sabo da bana gani na kyale nace to ai ya isa haka wannan ai sai ka karar dashi da wuri kunfi so kuyi ta asarar kudi amma wannan shanana mayuka da kake haka ko Mace albarka,naga ya bude wani kala yana fesawa shuuuu,na Mike nace dan Allah ka barshi haka yanzu idan kasa kadan ka adana abinka gobe ma ai sai ka dauka ka sa amma rana daya ka kusa karar dasu a dinga tausayawa kudin mana.
Kawo na karasa ma,ya fisge abinsa,nace nafa iya naka ma da yake na maza da wuri zan gyara ma shi kuma wlh ko fita kayi sai an San kana da mata,kasan shi gwauro idan ya fita tun daga shigarsa ake ganewa sabo da babu me nuna masa inda aka samu matsala,wani sai kaga gashi a wuyan rigarsa ya zuba,murmushi yayi Bai ce komai sai yace ai bakinki ne Gwauron gashi nan yi min naga iyawar taki kuma karki min da zafi,Ina murna nace ai nasan har kyauta yau sai kayi min,sunkuyawa yayi tare da miko min kan,nace zan gaji da wuri a haka,na zauna Saman Bed shi kuma na shimfida masa Sallaya nace zauna ka gani ni da nake me kitso,Kamar bazai Zauna ba sai kuma ya zauna,na ware cinyoyi kamar zanwa wata kitso dai yace ke hade wannan cinyar taki kina period,nace sai na fasa ma dan zan maka shine zaka fada min magana.
A hankali na dinga taje masa ina fesa masa abun gashin,sai wani lumshe ido yakeyi zaiyi bacci,nace kudi biyu zaka biya ga na gyaran gashi ga kuma na hannun mace yana taba ma kai kasan hannun mace daban ne sai an biya,wannan hannun naki kamar Dutse gwara na maza dashi,ni kaina ba wani yi nake ba kawai tajewa nakeyi ina wasa da gashin dama karya nake ban iya ba,bacci ne ya fara kwashe shi har na gama,nace na gama tashi ga abincin can,yana son yayi bacci na mika masa,yace Hannuna da Mai ban son tashi kisa spoon ki bani naci,ba da wani abu ya fada ba nima haka nasa spoon ina bashi har yaci ya koshi nace lemo zaka Sha?yace Ruwa ni ban fiye Shan lemo na kwali ba nafison fruits ko ruwa,ruwa na mika masa yasha,na kwashe komai na maida,su Meenat suna dawowa nace su shirya muje shopping,wanka muka Sha nasa doguwar rigar da Aayan ya bani nasa lokacin da ya kawoni wajen Family dinsa shiri mukayi sosai Meenat ce tayi mana kwalliya mun Sha kyau,mun fito nace suje jikin motar Driver yana can bari na fadawa Aayan.
Knocking nayi masa sannan nayi Sallama na shiga yana zaune yau magazine yake karantawa,nace zamu fita Shopping,hannu kawai ya daga min irin muje kawai,katon store muka je munsha siyayya sosai da sosai,Cosmetics,shoes,bags,mayafai,jelweries,Night wears,sai atamfofi kala biyar biyar,shadda kala Uku uku,sai materials tare da laces suma,Ready made dogayen riguna da riga da skert,mayafai dasu Inner wears duka masu kyau yan tsakiya dan yan tsakiya za ace baza ace masu tsada na karshe ba kudin baza su kai ba,wajen telanmu muka wuce duk Wanda za a dinka muka bayar,lokacin har dare yayi kusan ma 8:30pm,nace yau ba girkin dare nace Baba Driver dan kaimu Yahooza suya sai murna su Meenat sukeyi,mukaje na fita na siya mana muka zauna inda aka tanada don Zama ga masu son ci a wajen,muka ci abinmu muka koshi tare da ice cream,na siyowa Aayan ma nasa harda kilishin da suke siyarwa, Malam Garba ma na bashi nasa harda shi na siyawa,ya dinga godiya da addua,
Wasu sai kaga suna cin abu ma a gaban yan aikinsu wai baza a iya bashi yaci ba,bare aje dashi waje shima a dan siya masa ko kadan ne babu me kulasu Sabo da son kai su tunda talakawa ne suci irin nasu,
sai 9pm muka dawo gidan,a gurguje nayi wanka nasa rigar baccina kamar T-shirt take amma yar doguwa iya rabin cinya tsayinta,powder na murza nasa lipgloss sai dan turare na Amtek na shafa na dauki Take away na Aayan na wuce Samansa.
Da Sallama na shiga Yau ma yana saman Sallaya Sanye da Jallabiya yana karatun Qurani,ina zaune gefen Bed dinsa ya gama adduoin nasa sai lokacin ya juyo ya kalleni tare da cewa ya akayi? Ko ka tambaya mun dawo lfy? Gashi to na mika masa take Away,ledar ya bi da kallo sannan ya kalleni da baki ya nuna ledar tare da cewa bude na gani,da sauri na sakko kasa yace to Ustaziyya gyara Hijab din kina samun a fuska,Dariya nayi kawai na tsuguna tare da bude masa ledar duk kamshinsa ya cika min hanci me dadi ji nake kamar na fada jikinsa na shako kamshin da yawa,na bude yaga package na kilishi,daya ledar kuma Kazace da yawa tasha hadi,sai Fura da ruwa harda yoghurt,son jin dadi na da kwadayi na ya jinjina a ransa duk wata hanyar cin dadi na Santa har na iya na siyo masa wannan.
Muryarsa naji yace ina naku?nace ai mu a wajen muka zauna muka ci Namu kawai sabo da nafi so muna dawowa yaran nan suyi bacci su kyaleni na huta,Murmushin da bai shirya ba ya saki gaba daya ya tafi da Imanina don idan yayi murmushi wani masifar kyau yake karawa na musamman,ke ba yaranki ba amma feeling kikeyi kamar yaranki ne kika haifa sai son girma,
Fari nayi da Ido wanda ban san nayi ba nace ai ko Ammah na da rai nice kamar uwarsu,rufe wannan ledar bari na gyara farce na,nace au baka zuwa a yanke ma farce?yace a'a basa min yanda nake so ne a Abuja nakeyi ko kuma lokacin dana zauna a London,amma nan garin Sam nasu bai min ba tsoro ma nakeji kar su samin cuta,na kalleshi nace iyye kaji Manya Ashe har a London ka zauna uhm lallai dole kayi yanga,kallo na kawai yayi ya mike tare da dakko abun da yake yanke farcensa kalarsu ma daban ne, kawo na yanke ma kaji na iya sosai,Ba musu ya mika min na gyara Zama a gabansa, nace to fa sai ka koya min yanda ake amfani da kalar Nail cutter en nan ban gane ta ba,
gwada min yayi tare da cewa indai kika lalata min Nails sai kin biyani farce na in dai bai min kyau ba,ae naji kawo kafar to, kafarsa na jawo wani mugun laushi ba duk mace ba, na daura saman cinyata da na rufe da hijab, na mika masa take Away din tare da cewa to ci mana, naman ya fara ci ni kuma na dukufa ina yanke masa Farce,yana ci yana latsa waya yana murmushi ko chat yakeyi oho, ji nayi yana dariya nace mu gani me kake gani na dariya haka,ba komai kawai yace, da na dan shigar da zafi zai ce karfa ki yanke min precious skin dina, wannan kayan da kika cike min Bedroom dasu fa,nace au na manta ne na schl ne na kawo ma ka gani na bashi Labarin komai gobe ma zan fara zuwa,ba sai na gani ba kawai ki kwashe abinki,nace to ba damuwa.
Ina gama yanke masa na kafa ya gama cin abincin nasa,hannu ya goge da tissu ya miko min yatsun hannu masu shegen kyau dasu,na fara gyara masa farce ina cewa Dazu mun siyo kayan mun kai wasu dinki,du na karar da kudin Dubu uku ce kawai ta rage.
Ok yace ke kika bawa Malam Garba Abinci? Nace ae har ba dare ma,ya min waya yana ta godiya Ashe kina da hankali dai? Murmushi nayi nace Kai wai nufinka bani da hankali?to ba karamin Hankali da wayo ne dani ba,yace sai dai kiyi wa wani wayon na ki,harda kai ma zan mawa,Sau nawa nayi ma wayo kaine dai baza ka gane ba,a ransa yace lallai yarinya zan nuna miki baki da wayo soon,ina gama masa ya kalli yatsun tare da cewa uhm ba laifi,toilet ya fada yayi Brush dama yayi wanka kaya ya canja zuwa na bacci,yana fitowa yaga na kwashe kayan dana kawo du na tafi dasu,light ya kashe ya kwanta abinsa tare da Addua.
Washe gari ina gama aikace aikace na shiri nayi cikin riga da skert English wear nayi kyau na yafa mayafi na fita na tafi har part din Daddyn Aayan,securities basu barni na shiga ba sai da suka sanar masa matar Aayan ce yace daga yau indai itace a barta ta shigo kawai.
a saman Bed dinsa na ganshi an canja masa kaya yana kwance abinsa,cike da ladabi na durkusa har kasa na gaida shi ya amsa da fara'a,daga nan yace zauna ya ta,a gefen gadon na zauna,nace Daddy da har zan kawo ma abinci na tuna Ya Aayan yace ba komai kake ci ba,murmushi yayi tare da cewa ae ni abu me ruwa nake ci sai kuma vegetables sai ko snacks amma duk sauran abinci basu Dameni ba,tun farko haka nake ni dama abincinmu na Hausawa basu Dameni ba sai Fura da Kunu kawai amma na turawa nake ci,me girki na ma daban take yata,nace Daddy shi kuma Aayan ko yana yaro amma na Hausawa gargajiya yafi so,yace ai wannan kyaleshi kawai Uwarsa ya gado ta nan.
Kuna zaune lfy dai ko?ae Daddy lfy Alhmdllh,to idan ya miki wani abu kizo ki fada min kinji,nace to,idan kin samu lokaci kizo watarana zan baki labarin tarihin gidan nan namu kaf sabo da ki koyi Zama dasu,ranar da bani da schl zanzo,Allah ya kaimu,na mike nace na tafi zanje makaranta,yace na gode Mufeeda Allah ya taimaka,na fito a hanyar dawowa part dinmu na hadu da Ameer a hanya yana kallona zan wuce amma yaki matsawa sai ma hanyata da ya kara tarewa,na kasa gane masa kawai na matsa can na wuce abina tare da ja masa tsaki,a ransa yace zanyi maganinki.
1:30pm ina bedroom na fara shirin zuwa schl ina cikin sa sabon Uniform dina sai naji knocking ba zato,da sauri na zura hijab dina na fito da tunanin ko Aayan ne ya dawo to in ba shi ba waye zai min knocking a Bedroom,ina fitowa naga Dan iskan nan Ameer, ina ina ya fara ahm...ahm...abinci zaki bani,harara na maka masa nace banyi da kai ba don ba auro ni akayi dan na dafa ma abinci ba,na koma Bedroom tare da sa key,abin nasa ya fara tsoratani tun daga irin kallon da yake Bina dashi.
Cikin Uniform na fito ba karamin kyau nayi ba black and white komai nawa har jaka da takalmi kowa ya kalleni a uniform din sai ya kara nayi matukar kyau,Sallamar su Meenat naji Ma'eesha tana Faman Kuka,lfy Ma'eesha ina Meenat din na ganki ke daya,Sis wannan matan ne suka Mareni kuma ga Meenat can a Compound wai shoe maker ya tareta wai sonta yakeyi,wanne kuma me wankin talkami, wannan su Haneefa yake wankewa takalmin schl baki ganshi ba cikinsa kato hannunsa da jikinsa siriri kamar tsinke cikinsa kuwa katon gaske kamar zai fashe,sunce wai Meenat sai ta kulashi dole.
To shine kike mana kuka haka,to ai marina wannan Haneefa din tayi akan nace Meenat tazo mu tafi,ok wuce kiyi wanka ga abinci nan a Dining na tafi schl ni daga can zanga Meenat,maza Ku fara shirin Islamiyya,Bye Sis nace Bye, na fita rataye da jakata,saida nayi tafiya kadan sannan na Iske Meenat Tsaye tare da wannan mutumin me gyaran takalmi,ni tunda na ganshi ma dariya ta kamani don cikinsa girmansa ya isa ga jikinsa siriri kamar a bushe shi ya fadi,su Haneefa suna zaune suna faman latsa waya.
A fusace na karasa wajensu nace Malam mene haka lfy kazo ka tare min yarinya anan ko kunya baka ji idan kudin magani kake nema ai sai kayi magana a baka kaje Hospital,Meenat tace ba ke bace Sis nace ki bamu dama amma kince kar mu kula su ko me zasuyi mana dole kece zakiyi kawai,Yan matan nan ne suka taso kanmu,ke wace da zamuce ayi abu kice zaki hana wannan ya gani yana so kuma dole ta kulashi in dai tana gidan nan,sabo da shine dai dai ita,Haneefa tace au Ku nan har kunfi karfin wannan kuna yayan talakawa,dama kadan nake jira Mari lafiyayye na zabgawa Haneefa dama kin Marar min kanwa wlh ba wanda ya isa ya taba mana lfy ya kwana lfy,nasan in suka hadu zaneni zasuyi Marin ma da kyar nayi ta maza na shammaceta na fesa mata shi, Cikinsu Sukace KWAJA jeka ka dawo gobe dole sai ka auri wannan suka nuna Meenat,Meenat tayi dariya tare da cewa au dama sunanka KWAJA? Lallai Kaci sunanka ta kara sakin dariya,nace wuce to ciki yar iska idan kika kara tsayawa dashi wlh zan miki rashin mutunci,to ba ke kikace kar na dau mataki Kansu ba,motocin Aayan ne suka shigo ya hango Su Haneefa sun rike min Hijab gashi nayi kyau, har gabanmu yazo yace sake min mata yana gyara wayar Usb da ya Ciro a motarsa,Haneefa ya damko ya dinga tsula mata wayar tana kuka da ihu,su kuwa sauran tuni sun Arce,wlh duk ranar da kuka kara taba jikin matana sai na kusa kasheku a gidan nan kuma kinsan ba abinda zai faru,nasan kin san da haka,kallona yayi tare da takowa wajena zai damko ni nima na kwashe da gudu,ya biyo ni taku biyu ya damko ni Ransa a bace ya kalleni ido da ido sai yayi murmushi matsoraciya yi mata dariya zance shine kika gudu,aiko Nace Haneefa tana Kallona na kyalkyale da dariya nace wooo ayi mata gwalo,Aayan yace fara frog jump dan ubanki kafin nazo nan na halaka ki,da Sauri ta fara yi,yace yi mata dariya ke kuma Aiko na dinga yi ina wooo harda tsalle,muna Haka sai ga Hajja kakarsu ta fito kamar zata make mutane,Aayan yace jeki schl tana cewa tsaya dan ubanki Karuwa Amma ko kallonta banyi ba na shige mota abina Malam Garba yaja,ta glass tana Kallona ina kallonta na mata gwalo,Aayan ya daga min hannu bye,tana zuwa ta daga hannu da niyyar sharawa Aayan Mari ya rike hannun caraf tare da matsar da ita gefe ya wuce ya bata waje bai ce kala ba,Kuka da kara tare da ihu ta fara yi a gaban yan aiki,Sai ga Abbi yana huci an taba Uwarsa.
Tunda na fara zuwa schl yau Sati guda kenan lfy nake zuwa ina dawowa abina cikin jin dadi,haka su Meenat ma,Aayan kuwa tun daga ranar da ya Zane Haneefa ban kara ganin Sa a gidan ba,ashe wai ya tafi Umrah Saudiya bamu sani ba sam,koda kudina suka kare Bedroom dinsa na shiga na duba inda yake ajiye kudi na ebi dubu biyar idan ya dawo sai na fada masa.
A schl dinmu har kawa nayi yar gayu wayayya MARYAM ga hankali ga sanin ya kamata,kullim tunda taji ina da aure take fada min yanda ake Tafiya da Imanin me gida,nace ai ni kullum da Hijab nake zama a gida idan zanje unguwa ne nake Sa mayafi watarana,aiko ta dinga dariya tana wayar dani ni kuwa dan kar ma Aayan yace Dan shi nakeyi nace ko Ya dawo bazanyi ba.
Yau da yamma su Meenat sun dawo kenan daga Islamiyya KWAJA me gyaran takalmi ya biyota tun daga wajen gate,dama su Haneefa sun fadawa Securities in dai Kwaja ne a barshi ya dinga shigowa yana da budurwa a gidan bayan haka ma yana goge musu takalmin schl.
Direct Kwaja ya shigo yana wargaje baki da wata falkekiyar T-shirt,hannun rigar Sabo da ramarsa kamar skert hannu tsilili a ciki, kansa har wasu jijiyoyine ke tashi kamar me kwoshokwo, wuyansa kamar mirkin laima,dan kirjinsa kuwa kamar Allo,hakoransa guda biyu manya a waje na gaba,bakinsa yake dargajewa shi tunaninsa ai dole ma ya auri Meenat tunda yayyenta sunce sun bashi ita.
ta window din sama Na hangosu yana tsaida Meenat yana Meenatu Meenatu yan mata dan Allah ki tsaya,haba Meenatu so kike sonki ya kashe ni? Meenat ta ja tsaki tare da hararsa Malam Kaja mituncinka mun san darajar Dan Adam shi yasa nake daga ma kafa Amma tunda kaki ji zaka ga abinda zanma.
Kwaja yace ko me zaki min ni Bazan ji haushiba tunda ina sonki,da wlh ba da gaske nake ba Amma na yaba da hankalinki da nutsuwarki,gaki kyakyawa ni yanzu ba zancen yayyanki nake bi ba wannan da gaske ne daga makwallaton zuciyata a daina maganar wasa, to bana sonka kaja Life dinka ka kara gaba Malam cewar Meenat,Murmushi yayi yace yan mata bani da Lifan ni bana karya dan a soni,karki kiyi tunanin Ina da Lifan kice Naja Lifan dina na tafi wlh Allah ko Keke bani dashi idan zaki soni ki soni dan Allah nasan ku manya ne kun wuce ayi muku karya,Takaici ya kama Meenat tace ina ruwana da karyarka ka ja rayuwarka kayi Out a gidan nan,Haushi KWAJA yaji yace na fuskanci Ku kunfi son dan karya azo ana muku birga da mota kullum idan nazo zance na baki Dubu daya ko Dubu daya da Dari biyar koma fiye da haka,to ni ba haka nake ba gaskiya da gaskiya nakeyi wlh da zaki aureni kullum sai na dinga siyo miki kifin gona kina soya mana,watarana ma Miyar zabo zaki dinga yi mana,Taliyarmu guda da macaroni da wake gongoni guda ya ishemu na na kwana hudu zuwa biyar, tsaki Meenat taja tayi gaba ta barshi nan,ina jikin Window ta sama ina ta dariya gaskiya Su Haneefa yan Iska ne,Meenat ta shigo na dinga mata dariya,nace Allah sarki kanwata duk iya kwalliyar nan kuma taki sai ki kare a KWAJA tumburarre,Dariya tayi itama tare da cewa ai Allah ya tsinewa su Haneefa yanzu idan nayi wani Saurayin yazo ya ganni da wannan ai wlh rainani kawai zaiyi ya daina zuwa,ina ta dariya harda kwalla Meenat tace dan Allah ki daina,har dare muka kwanta ko farkawa nayi sai nace ta KWAJA tashi na baku lbr,banza tayi min tace wlh sai na fadawa mijinki idan ya dawo tunda haka kike min.
Yau nayi shiri tsab ba schl zanje wurin Daddyn Aayan ya bani labarin gidan nan da yace zai bani,koda naje Sallah ya idar daga kwancen,yana murmushi muka gaisa,nace Daddy yau na shirya a bani Tarihin naku. Yace to yata bude kunnuwanki kiji.
Next page is very Important readers ku tsaya ku karanta da kyau shine zamu san waye Aayan.
Raffa
Asma Baffa
[1/10, 10:37 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖
KASUWANCI NA
46-50
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne MADINA ALEEYU
MAMAN SAMHA
NAJA'ATU ALIYU
Jinjina gareku na wajena
MOMMY ARFAT
AYFA
MARYERM MUHD
HAJARANCY
HAULATU KAMBA
QUEEN KK
Zaune nake na nutsu Daddy ya fara bani labari,
Mu yan Asalin Kasar Algeria ne sabo Dama kasar suna da yawan farare duk kusan larabawa jar fata,har yau muna da ragowar dangi acan kawai zumunci ne da yayi karanci yanzu bama yi dasu suma haka,Babana Mahaifi kakan Aayan shine Jabeer Muhd Jabeer tunda suke dama su masu kudi ne sun gaji dukiya me tarin yawa,a tarihinsa kaf ba aji talaka a jininsu ba tun zamani me tsawo,komai sun hada ilmin boko da kasuwanci,Jabeer Muhd Jabeer Allah ya Yoshi me son yawon zaga duniya har Allah ya kawoshi Nigeria can cikin wani dajin Fulani dake Taraba sunje yawon bude ido a rugar fulanin Allah ya hada shi da Mahaifiyarmu Hajja kenan wacce kike gani a gidan nan tana zuba mulki sunanta Karimatu,Karimatu Hajja basu gaji arziki ba don a rugar ma su talakawa na karshe,Allah yayo su da son kai tare da son abin duniya ga tsafi da bin Malamai,Sau daya suka hadu da Jabeer taga yana da dukiya dama bata da burin da ya wuce ta auri me kudi wanda zai kaita kasar waje su zauna,tun daga tambayarta ina ne gidan me gari shike nan ta koma gida ta sanarwa Babarta cewa taga wani tana so Bature ne,sunansa Jabeer,nan Babarta Larai ta shirya sai gidan bokanta,Lokacin Jabeer ya bar kasar nan ma Nigeria yana Ghana,yaji son Karimatu ya shigeshi babu bata lokaci ya dawo a gigice sabo da tsafin da suka masa,yana zuwa da maganar Aure Larai da mijinta Usmanu Baban Hajja suka amince sabo da son abin duniya.
Ko dangin Jabeer babu sai wakili aka yi masa a kauyen aka daura Auren Karimatu Hajja da Jabeer,sabo da aikin bokanci ya tafi da ita Algeria sunyi shekara daya ya dauketa suka koma London inda a nan aka samu Cikina ta Haifeni naci sunan kakana Muhd,ana kirana Muhd Jabeer Jabeer, a London na taso cikin Jin dadi gata tare da kwanciyar hankali,ga ilmi sosai na zamani dana Islama,sabo da Babana akwai son Musulunci,y anda ta mallake Babana yasa take masa abinda taga dama,wulakanci iri iri da cin mutunci,tana ta sace masa dukiya da kadarori amma duk da haka arzikinsa karuwa yake,ita kuma tana ta sace wasu tana adanawa.
Bayan na kwashe shekaru biyar a duniya asirin da Babata Karimatu Hajja tayiwa Jabeer Babana ya karye,nan fa Jabeer yace Bai San zance ba baya son Hajja,ya dinga wulakantata,gashi sabo da kudi bata so su rabu tana kasar waje tana cin daula,haka take jure wulakancinsa sabo da kudi har ya kara Aure ya auri Masoyiyarsa Hafsat Balarabiyar kasar Jordan,mata ta gari suna zamansu lfy tana sonsa tsakani da Allah ba irin mahaifiyata ba da son kudine kawai,a haka take zaune har ma abin yaci tura ya saketa saki har uku,sabo da ta Saci kudi da yawa yasa ta san yanda zata yi dan kar ma a gano ta sai tattara ta gudo Nigeria da dunbin dukiya a wancan zamanin.
Ni kuma ina wajen Babana hannun Hafsat Balarabiyar matarsa ta Jordan tana rikeni Amana da gaskiya,tun kuma daga kaina Babana bai sake haihuwa ba har aure ya kara amma Bai kuma haihuwa ba a duniya,bayan shekara Uku da sakin Karimatu ta samu wani mutum da take matukar Kauna da gaske amma bashi da ko sisi can cikin wani kauye yake shima a Taraba state Fulani ne sosai,sabo da tana sonsa ta gina katafaren gida na more rayuwa a cikin birnin Taraba,ta aure shi suke zaune tare da shi.
Dama ni bata son Babana sai don kudinsa,bare da asiri ya karye ya wulakantata sai ta kara tsanarsa bata da makiyi sama dashi sabo da kudin basu isheta ba tafi so ta yashe shi tas, sabo da wannan har ni da ta Haifa ta tsaneni kiyayyar Mahaifi ce ta shafeni nima bata kaunata da abinda ya shafeni, shekara biyu da auren Yusuf ta Haifi danta dashi Namiji Mustapha shine da kike ji ana ce Masa Abbi a gidan nan, bayan 2yrs ta kara Haifar kaninsa Sani shine zaki ji ana ce Masa Abbin Ameer, sai dan Autanta Awwal shine Abbin Khaleel tare da kannensu. tana ta juya dukiyarta amma basa wani karuwa sosai sai rufin asiri,Katsam Mijinta sai ya rasu Baban su Abbi kenan,ita ta Sha wahala dasu ta dauki nauyin karatunsu har iya Secondary da komai sabo da tana masifar sonsu kamar ranta sabo da yanda take kaunar Mahaifinsu,ni kuwa Abbin London kenan ko waiwayenmu bata kara yi ba,har dai iyayenta suka rasu sai dangi,haka Iyayen Babana ma sai dangi ana ta karewa.
Na gama Degree da Masters dina duk muna London,Babana yana ji dani sabo ni kadai gareshi,Har ya hadani Aure da wata budurwa Balarabiya yar Jordan cikin yan uwan matarsa Hafsat lokacin ya Damka min dukiyarsa baki daya da komai ga kuma aikina ina yi,na zama hamshakin me kudin da nayi suna a duniya kaf a wancan lokaci,Muna zaune lfy da Matata Asiya Wacce ta Haifar min Dan Albarka na Da daya tamkar da dubu Aayan kenan,dukkanmu a london muke rayuwa,har Aayan ya gama Primary lokacin kuma Su Abbi su Uku suma da matansu sun Haifi yaransu Maza,Abbi Mustapha mijin Hajiya Saratu Mami shine Baban Mujaheed,Haneefa,Sajeeda,da kuma Minal karamar yarinya,Awwal mijin Hajiya Zarah Ummi suna da Yara su kuma Biyar Khaleel,Farida mate din su Haneefa shegu Uku,Maryam,Nura sai dan Auta yaro mate din Minal wato Ahmad. Sani mijin Hajiya Haleema Anty yaransu uku Ameer fitinanne, Zahraddeen dan Wiwi,sai Yusrah.
Yanda iyayensu suke da hadin kai haka suma yaransu suke da hadin kai ba a jin kansu, Sabo da Hajja ko yaro taga yana bijire mata sai ta tafi gidan boka ta kai sunansa cewar Danta wane baya jin maganarta ayi masa magani ya koma sai yanda tayi dashi,haka Matan yayanta ta gama dasu sai abinda tace,jikokinta ma haka, ni ne kadai da Dana muka gagareta, kuma a halin yanzu hausawa haka suka koma,wai ko dane sai iyaye suyi masa asiri su mallake abinsu sai abinda suka ce,sai kaji ana in ka zauna yanzu zaki haifawa wata ta gaje miki da,ko shaye shaye,ko dai wani banza idan yana yi maimakon ayi masa addua wai sai a tafi gidan malam,dana wane ko Ya ta na rasa yanda zanyi tana Kaza a canja mata ra'ayi,ko miji ne bata son auren sai iyaye su kai sunanta kaga kawai ta koma sonsa,yana karyewa kuma shike nan Allah kyauta.
kin san yaro tarbiyyar daka dorashi da ita zai tashi,ni da Dana da basa sonmu har yayansu basa sonmu,shi yasa ko yaro yana ma kallon Banza maybe sunji iyayen su sunce wani abu a kanka,wasu ma in kaga suna daraja ka to iyayensu ke yabonka gabansu a kula iyaye,daga kun samu matsala da yan uwanki ki kwashe ki fadawa Yara wane dan uwana ko yar uwata tayi min Kaza sai kiga har abada baza su sota ba,ko kin dawo kin gyara bazai gyaru ba,a guji gulma da zagin yan Uwa da mutane gaban Yara.har Matan su Abbi basa kaunarmu kuma nine nake musu komai na rayuwa har daukan Nauyin karatun yaransu da komai na duniya har yau har gobe har yanzu da aka kawoki gidan nan yata.
Lokacin da Aayan yana secondary ya gama lokacin Allah ya karbi rayuwar Jabeer Babana tare da matarsa Hafsat sunyi Hatsari a jirgin sama.
Muna zamanmu da Dana har ya shiga University lokacin Nazo Nigeria neman Mahaifiyata Hajja don Babana ya bani Address kafin ya rasu,bata yi wani farin ciki ba Amma ganin nine yanzu me kudin sai ta saki kuka tace dole sai mun dawo Nigeria da iyalina ko ta tsine min nabi duniya,ba yanda zanyi da dukiyata da komai nawa na dawo Nigeria tare da Gina katafaren gidaje har Biyu a Abuja nace daya na dana Aayan daya nawa,ga motoci na Alfarma,har karatun Sojoji nayi shi yasa kike ganinmu da Securities a gidan nan harda jiniya in ta kama Sabo da nayi aikin soja na shekara Uku a kasar nan da Babban matsayi Sabo da tun ina yaro soja nake so shi yasa nayi aikin.
Ni da Matata Asiya mun dawo Nigeria dasu Hajja tare da kannena su Abbi duk na kwashe mu muka koma katafaren gidana dake Abuja,kudin Hajja data sata sun kare dama,ni na dauki nauyin su Abbi duk da sun girma suma da iyalansu sai da na Sa su sukayi Degree,na basu aiki a Company na nake biyansu albashi me tsoka,na siya musu motoci still ban fasa daukan nauyin iyalansu ba,amma sam ko me nayi musu basa taba Cemin ko an gode hasali ma sai daí su nuna bana musu komai a duniya,ko yaushe burinsu suga na tsiyace na talauce,burinsu ace a cikinsu ne daya yake da wannan arziki,haka Hajja ma komai nine me laifi su basa taba yin laifi Sabo su take so,abu kadan in nayi zata fara zagina,tana min baki,amma su ko me zasuyi baza ta musu Fada ba,kullum burinsu su ganni cikin halin bala'i, ba irin asirin da basuyi min ba Sabo da na talauce su gaje dukiyata Amma Sabo da karfin addua tare da tsoron Allah da kyakyawar zuciya,bana nufin kowa da sharri,bana shirka sai Allah ya kareni duk abinda zasuyi a banza,tunda na gane halinsu na dage da addua,ita kanta Hajja bata so ace nine me kudi ba cikin yaranta ta fi so ace Awwal,Sani ko Mustapha sune masu kudin ba ni ba,sabo da dama bata so na da ubana kuma bugu da kari ba ita ta raineni ba, sam babu wannan shakuwar ta raino tsakanin Uwa da Danta,nima ban damu da ita ba nafi son matar Babana Hafsat data rasu nafi Jinta a raina Sabo da mun shaku ta rikeni da Amana.
Makirci kulla tsiya ba wacce basa min,har Hajja ke Goya musu baya ana bin malamai akan dukiyata ta koma wajensu,kawai dai Hajja bata yarda ayi min asiri na cutar da lfy ta ba,tace duk da haka ni Danta ne na cikinta ko bayan ranta idan suka cutar da lfy ta ko raina bata yafe ba,duk abinda zasuyi na karbe dukiyata sunyi Amma ba abinda ya faru,su kuma Sabo da ita tasha wahalarsu suna jin maganarta amma shedan yafi karfin zuciyarsu don ko taya ma so suke suga bayana,hassada suke min ta gaske,ni kuma da yake dama a goge nake na waye nasan me nakeyi bana kulasu duk wata hanya na tosheta wacce zasu iya samun dukiyar tawa ko kadan ne sai daí in ni na basu da kaina, Aayan yaro ne me hakuri da kawaici tare da danne bacin rai Amma ta wani fannin yana da zafin zuciya,tun yana secondary na fuskanci yana da karfin sha'awa har cuta yake kwanciya a asibiti Sabo da sha'awa.
Saura shekara daya ya gama Degree a London mu muna Nigeria lokacin Hajja su Abbi sun zugata dole tace sai na dawo da Aayan Nigeria nayi masa aure mun zauna gaba daya Sabo da suna bakin ciki shi yana waje yaransu basa kasar waje bayan har saudiya da Dubai na kai yaransu sosai baki daya,da kudinsu ma suna fita kasashe suke duk ta silar arzikina, Asiya Matata kullum cikin kuntata mata suke tana ta hakuri har Mari tasha a wajen Su Abbi ban taba ce musu komai ba,wahala ba wacce bata gani ba,duk aikin gidan nan na abinci ita ke dafawa shi yasa ta iya girkin hausawa sosai,Hajja ta wahalar da ita sosai tare da matan su Abbi suka hade mata kai kamar zasu kasheta kullum kalar abinda zasuyi mata daban.
Ganin matsalar Aayan ta sha'awa gashi kyakyawan gaske kuma tana turai ina tsoro kar ya lalace sai na yarda nace ya fito da mata zan aura masa idan ya karasa Degree ya dawo Nigeria,ya kawo min wata musluma yar turkysh yana so,Amma Sai Hajja tace ban isa ba idan har na aura masa ita bata yafe min ba,nayi masa bayani ban boye ba,da yake Aayan akwai biyayya sai yace ya hakura to kar mamana tayi fushi da ubansa.
Su Abbi ne suka zuga idan Aayan ya auri Jar fata zamu kara yin kudi mufi haka arziki,dan danan suka nemo wata budurwa kyakyawa Bilkisu yar gidan Minister itama budurwar Khaleel ce,suka hada baki dasu Abbi domin a aurawa Aayan sai ta san yanda zatayi ta yashe mu tas,koda suka ce ga mata sun samowa Aayan sai da na bincinka na tabbatar ba yarinyar kirki bace Amma Hajja tace sai an aura masa ko ta tsine min,haka na hakura aka daura auren Bilkisu da Aayan yana London nace Hajja tayi hakuri Bilkisu tabi mijinta ya gama karatu sai su dawo tare,kafin Bilkisu ta tafi sai da suka gama tsafeta a gidan boka yanda zata mallake Aayan ta samo musu kudi,to na rigada na sani ina Yiwa dana addua shima kuma akwai addini yana yi na kara ja masa kunne kan rike addua,koda Bilkisu taje baiji yana sonta ba,ya kasa kusantarta,har ya gama Degree lokacin ya dawo Nigeria kullum da sha'awarsa muna hanyar asibiti ga na Hausa muna yi,kuma ya kasa kusantarta,har ya gano cewar tana fasikanci tare da khaleel,bai sake ta da wuri ba sai da ya tabbatar da ita ta gane kurenta,su kuma su Abbi ganin bata samo kudin ba ta kasa komai sai suka tsaneta suka koma azabtar da ita,duka zagi ba abinda basuyi mata ba har Aayan yaga zalunci yayi yawa ya bata hakuri tare da kudi me yawa suka rabu,yanzu haka ta dade da aure harda yaranta biyu.
Lokacin kuma Asiya Matata bakin ciki yayi mata yawa,lokacin kuma Hajja da kanta taje gidan boka ta samu nasara wajen Yiwa Asiya asiri tace dole sai na saketa,naki yarda don ina sonta,rigima mukeyi sosai,ta daina kula Aayan sam ta tsani Danta,tace indai ban saketa ba sai ta kasheni haka Aayan na rokarta tayi hakuri yana kuka nima haka na saketa saki daya ta ta koma kasarsu,bayan asirin ya karye na maida ita ba tare da kowa ya sani ba har Aayan,Shine ma dalilin da yasa yake jin haushin mahaifiyarsa har yau,na fada masa gaskiya Amma yaki fahimta yata,muna tare shekara daya da dawowarta ta samu ciki wajen haihuwa ta rasu Allah ya karbi abarsa,munyi kuka ni da Aayan sosai haka muka hakura.
Daga nan Hajja da kanta tace ta samowa Aayan matar aure Nafisa ita kuma yar talakawa ce Amma bata da tarbiya ni kaina tasha zagina a gabana,lokacin Aayan ya hakura bai sonta Amma dole ya bata hakkinta na matarsa,a lokacin kuma su Abbi sun masa asiri kwata kwata ya daina sha'awar mata ko kadan dan kar ma ya haihu a duniya zuriarmu ta yadu mu kara arziki,ba asibitin da bamuje ba,akace lfy yake,har na Hausa da addua anyi Amma sam,ganin haka yasa Nafisa ta bude bakin rashin mutunci wanda akan Aayan take saukeshi ya kasa Control dinta zagi da komai ba wanda bata yi,su Abbi na zugata dan a bangarensu take,lokacin Hajja ta matsa min ita Kano take so mu koma da zama Abuja ba dadi,haka na zabi unguwa mafi kyau na tsantsara mana wannan gidan da muke ciki wanda duk shekara sai an canja masa fasali, Sabo da bacin Rai Aayan ya tafi yin karatun masters dinsa na Electrical engeneering,Nafisa tana nan tana sheka rashin mutunci har da ni,yana gama Masters a london ya dawo ya mata mugun duka ya saketa sakamakon zagina da yaji tayi.
Suka kara nemo masa mata wata Rukayya ana ce mata Ruky lokacin Aayan bai warke ba na dage masa da addua Allah ya taimake mu ya warke don baya boye min komai nima bana boye masa yace min yanzu yana jin Sha'awa, Ruky da Farko tazo da mutunci tasha wahala hannun Hajja duk cikin Matan da suka aurawa Aayan Hajja bata son Ruky Sabo da taga kamar tana Son Aayan,shi kuma Aayan bai son Ruky ya dade da ganowa Ruky Makaryaciya ce gata kawai sha'awarsa takeyi dama tuni tasan Maza tun a waje,amma duk da haka nace yayi hakuri ya bata hakkinta,yaje mata da niyya kawai sai kuma ya kasa aikata komai gashi yana sha'awa Normal Amma ya kasa aikata komai,Ruky dai taga no way itama tace a saketa,wannan da yake Hajja bata sonta sai da tasa wasu suka Zane Ruky tas wai ta ci kudinsu a banza bata yi zaman aure ba,Da kanta Ruky tace a saketa,na bata hakuri Amma tace ina sam Allah ya karta baza ta zauna ba,Aayan yace taje itama,daga sannan kawai yace wa su Abbi bashi da lfy bazai taba haihuwa ba,an gwada shi hasali ma bazai iya Yiwa mace komai ba,sannnan ya kara daurawa kansa cuta yace ai ciwon sugar da Hawan jini ne dashi wai duk dan su kyaleshi haka ya huta don ya rantse bazai kara auren matar da zasu zabo masa ba ko me za ayi.
Muna rayuwa haka kullum kiyayyarsu Karuwa takeyi akanmu musamman Aayan sunfi takura masa har Hajja cikin jikokinta bata son Aayan,Shi kuma baya shiga harkarsu baiyi rayuwa dasu bama bai taso dasu ba sam basu saba da juna ba,Sabo da basa sona da Dana nace Abbi ko kannensa su bawa Aayan auren Yarsu daya ayi yar gida sukace sam basu yarda ba Sabo da a zuciyarsu suna da manufa a kanmu.
Muna ta rayuwa kwatsam Aayan ya birkice min shi Barin kasar zaiyi bai son gidan nan,aikinsa ma Shi bari zaiyi ya daina komai,na rude muna ta addua watarana ya fita shike nan bai dawo ba,Kowa har Securities basu ganshi ba,sati daya,biyu,uku,wata daya har wata Uku,babu nema cigiya har kasashe ba a ganshi ba,addua sosai har masallatai na raba,ana ta yi sai aka ganshi can wani kauye a gindin bishiya ya dawo hayyacinsa,ashe su Abbi ne suka masa kucciya,ganin haka nace dole mu Barsu,ai kuwa Hajja tace idan na tafi bata yafe ba ta tsine min,Aayan yace mu zauna kawai Amma shi zai koma Abuja da zama shine Aayan ya koma rayuwa a Abuja lafiya yana min aikace aikace na Business tare da fita kasashe,yana yawan zuwa Umrah Sabo da addua ko yaushe zaki ji ya tafi idan ya Zama less busy.
To Daddy wannan cutar taka fa? Ai yau kimanin shekara daya da rabi kenan ina haka har na saba ma,shima sati daya ina dan jin jikina ba dadi nazo wucewa Naji yan uwana su Abbi suna shawarar yanda zasu kashe Aayan mijinki Sabo da su gaji dukiyata su da yaransu,har yanzu a wannan kudirin suke,kuma duk yaransu sun san da wannan,dalilin haka na yanke jiki na fadi shike nan komai ya daina motsi shima ba kasar da ba aje ba har na gargajiya da addini anyi,masu irin cutata da yawa suna tashi suna warkewa Amma ni tun muna yi har mun gaji ma na hakura na barwa Allah.
Aayan yace bai hakura ba na hanashi har haushina yake ji yaki zuwa gaisheni Sabo da naki yarda mu ci gaba da neman magani,kin san mijin naki ba dama.
To Daddy ni kuma me yasa ya aureni? Nine nasa aka auroki yata ke zabina ce,watarana kafin kuyi aure yazo nan yana ta fushi da masifa wai daga ya kwanta a kasa wata tazo ta haye masa jiki Kazama,watarana ya kara zuwa yana fushi wai wannan ce ta zageshi wlh sai ya halakata,da kyar na lallashe shi,watarana kuma yazo yana dariya yace min kece dai ya kara ganin ki son kudi ya kaiki wani gida ko wani ya biyoki ko me kina dai ta sheka gudu kika kasa tsayawa da kanki sai da kika bigi bishiya,wata rana kuma yazo nan yace min Daddy naga mayyar nan nace wace mayya yace me son kudi taje Maula gidan Yarima tana ta shan fura a leda a gaban Maza.
Shine na bashi Umarni nace lallai lallai dole ne yaje ya aureki,sabo da ina so ko Allah zai sa yayi dacen mata ko ma ya samu haihuwa ya tara zuri'a.idona na rufe gaban Daddy sabo da kunya,yace min ke yarinya ce,nace ae a hakan,ba fushin da baiyi ba shi baya Sonki bazai aureki ba nace dole ya aureki duk yanda zaiyi ma ya aureki amma nace zai iya aurenki na Kasuwanci zuwa dan wani lokaci sai ku rabu idan zaman bai yuwu ba,bana son a cuci wani,lokacin yace indai dan na wani lokaci ne ya yarda zai biyaki kudi ya aureki tunda ina son yayi aure,ko yaushe kike so kasuwancinku ya kare ki fada masa zai rabu dake yata baza a cuceki ba,bazan miki dole ba,nasan aure a haka bazai yuwu ba,shima na fada masa.
Ya akayi su Abbi suka yarda? Sai da muka biyasu kudi me yawa sannan suka sa Hajja ta yarda suma suka yarda suka Zama maneman aurenki,kudi aka biyasu in ba haka ba sai sun zuga Hajja tazo tace bata yarda ba, ko auren da basu zuga Hajja tayi masa ba shima Contract sukayi Deal aka biyasu kudi suka kyale zancen,sun san kuma zamu iya kwace kudinmu tunda a tafin hannunmu suke,sabo da sun San baza su iya sawa a sakeki ba an rigada an biya shi yasa suka zuga Hajja tace ki dawo gidan nan da Zama,wannan securities din ma duk Aayan ne yasa suke tsaro na sabo da makircinsu,to Daddy dukiyar taka fa? Tana hannun dana Aayan na bar masa komai tuntuni shine me kudin shi yake komai kawai taimaka masa nake da shawara,mijinki young millonier ne da an San abinda yake dashi a duniya to da duk duniya sun San da zamansa,amma duk da haka da dama sun sani kasashe nayi suna shima haka.
Yarima Bobo fa Daddy?shi kadai ne abokinsa dan Nigeria da sukayi karatu tare kuma ya yarda dashi sun aminta da juna,ranar danaga ya Zane su Haneefa fa? Waya tayiwa Abbi kuma yasan ba mai iya taka musu birki sai shi shi yasa yace yaje ya Zane masa su.babu wanda suka tsana yanzu sama da mijinki da kuma wanda suke tare da shi,suna nan akan bakansu karki ga suna miki dariya ko sunyi luf kice sun shiryu wlh wani kullin suke kullawa,da bana raye da tuni Aayan ya bar kasar nan tunda ko tayi masa baki bazai bishi ba to amma ina raye ni zata yiwa kinga akwai matsala,ki nutsu yata shi yasa na baki labari ki san yanda zaki zauna dasu da basira tare da gogewa,fada da zage zage ko duka ba shi bane use ur Upper ki kwaci yancinki da na mijinki, idan kuma Kun shirya rabuwa baku da matsala Ku kuke zaune sa juna ba ni ba,yanda kukayi dai dai ne,a takaice na baki labari dan na yaba da tarbiyarki,nasan Aayan bazai fada miki ba shi yasa na sanar dake,idan kin zabi business za a biyaki ko nawa ne karki damu tashi kije a sannu kuma zaki ci gaba da gano halayensu daya bayan daya,abinda da ma ban sanar dake ba duk zaki gane nan gaba,a takaice na sanar dake.
a raina naji tausayinsu sosai har kwalla nayi sannan sai naji tausayin kaina da yan uwana,garin neman gira zan rasa ido,haka kawai son kudin jaraba ya kawoni inda za a ruguza mana rayuwa,yanzu ya zanyi?Me zanyi,lallai fada da masifa ba shine kadai zai kwace mu ba,ashe Aayan yana da gaskiya da baya saurarsu yake cewa na sharesu kawai,irin wannan kiyayya haka wacce zuciya ce dasu,ba a saduda ba dana sani tun tuni kayi ta abu daya akan wani,har Aayan suka batar dashi lallai,to tunda suka Yiwa yan Uwa haka ai nasan ma wajen Kudus zasu cilla ni shike nan zan bace ko a halakani,a raina nace ni na fasa auren na hakura da Kasuwancin kawai bari ya dawo ya sake ni kawai mu tafi,bazan iya wannan rayuwa ba wannan gidan ai sai su ni kam yafi karfi na.
Muryar Daddy naji yace tunanin Me kikeyi yata?nace ba komai kawai mamaki nake yanda kuka iya Hausa haka bayan ba anan kuke ba,yace lokacin Hajja bata wani jin turanci da Hausa muke magana har na kai 5yrs daga nan ina son yaren akwai wani bahaushe abokinsa yaci gaba da koyamin na iya sosai,Aayan ma na koyawa Mamansa duk da bata wani iya ba haka muke masa Hausa ya tashi da yare biyu,da ya dawo nan kuma sai ya kara gogewa da yaren.
Me kike so kiyi da kudi yata idan kin samu da har kika amince da wannan aure ba tare da bincike ba duk da cewa Aayan ya min bayanin halin da kuke ciki? Daddy Sabo da muyi Karatu Meenat ta zama Likita,Maeesha ta zama lauya,sannan nayi mana gida me kyau,mu dinga cin kayan dadi,sannan idan munyi aure mu dankara kayan daki masu kyau shike nan,Murmushi yayi yace to wannan tunanine me kyau,me yasa kike son Kanwarki tayi likitanci ke kuma fa? Nace ni abinda yake birgeni da Likita Daddy naga sun gwalewa mutum ido sai ayi zuruuu ana kallo sai ace yana da cuta Kaza hhhh na karashe ina dariya shi kanshi Daddy yaji kuruciyar tayi yawa sai dariya yakeyi.
Yace Allah me iko to Lauya fa? Shi Lauya Daddy Allah hular nan da suke sawa wata tum tum kamar gashin tinkiya itace take bani dariya,kuma da glass dinsu yana birgeni,sannan idan suka tsaya suna zuba karya gaban alkali sai ka rantse gaske ne,shine suke birgeni sun iya sheko ta,Daddy yayi dariya to ai ba kowa ke yin karyar ba a cikinsu,amma dai sunayi ga shedar zuuur a karbi kudin mutum,Yace Allah ya shirya su,ke kuma fa me kike so ki zama ?nace ai ni nawa yafi nasu dadi malamar Makarantar primary na dinga shiga aji gaba daya a mike ace Good morning Aunty,nace morning student How are u,suce we are fine thnk u Ma,sannnan ni kuma ina bata rai ina yanga tare da tsawa nace Sit down,kuma na dinga koya musu A babba a karama,Baba ya tafi Gona,malam yana karatu,Inna tana Girki.Daddy ya dinga dariya yace ah lallai naki yafi dadi,tashi ki tafi Yata gashi 4pm tayi Sallah zanyi, 8pm Aayan zai dawo yau daga Umrah,cikin Kasuwancin naku da kukeyi ki dafa masa abincin gargajiya yana son wainar shinkafa da miya.
Na mike nayi masa sallama zan tafi yace Yata yau kin sani nishadin da na dade ban samu ba shekarunki nawa ne haka? Tunda kaine Daddy na gaskiya zan fada ma 16 nake saura wata biyu na shiga 17yrs Amma karka fadawa kowa Sabo da har Aayan 17 nace masa bana so a dinga min kallon yar yarinya.
To Bazan fada ba sai kin sake zuwa yata nace to Daddy Allah kara lfy na fito na dawo part dinmu.
Sallah nayi na fada kitchen na fara hadin wainar shinkafa da Miya,Su Meenat sun tafi karbo mana dinkunan da muka kai wurin tela, bani na gama Wainar ba sai wurin 7:30, ina kitchen su Meenat sun dawo tare da Driver duk na zuba musu sunci har Driver,Ni kuwa ina kitchen a kaskon ma naci na koshi da naga na soya wata tayi min kyau sai nace wannan tawa ce ni zan cinye ta,saai na jefata a plate na zuba Miyar taushen na cinye ina yarfe hannu,ga zafi ga Dadi,miyar tayi dadi harda naman Rago,ina gamawa na masa kunun gyada,na yanka masa Fruits a wani glass Bowl me kyan gaske nasa a fridge,Meenat da Ma'eesha ne suka wanke abubuwan dana bata tare da gyara kitchen fes bayan sun gyara ko ina na gidan sosai yana kyalli ko ina kamshi ke tashi,Dakin Aayan na kara gyarawa duk da cewa sun gyara sai da na kara tisawa na kunna Ac ga sanyi ga kamshi,na kulle,nayi Sauri na shiga wanka,na fito yau Salo zan canja a gidan nan.
Meenat ce ta gyara min gashi da mayuka,na shafa lotion me kyau da kamshi,dama gashi na kara haske abinka da fara dama ta samu waje, yar kiba da kyau nayi Sabo da ina ci ina koshi a kan lokaci,Cikin dinkunan na zabi wani Lace me kyau pupple and Brown riga da skert nasa,yanda na fito a dinkin ba a cewa komai,mazaune sun cika fam dinkin das a jikina,Meenat ta shafa min powder sama sama ban son kwalliyar nan me yawa ni,maroon jambaki ta sa min sai kwalli tare da samin eyeliner a saman ido harda nayi tsananin kyau,gira kuwa na hana tayi min da brush na taje na gyarata ba tare da na kara komai ba Sabo da girarta baka ga yawa,tace saura sarka aka Sa min wata yar karama pupple da dankunnenta,nasa agogo na wani me kyau na yan gayu da muka siyo Brown,Meenat tace sai na Sa zobe ma yana kara kyau a hannu,haka nasa wani me kyau,ta zauna ta tsantsara min dauri tare da sakin gashina ta baya kyau ba a magana ni kaina sai yanzu na kara son kaina,naji kamar na lashe kaina Sabo da yanda na hadu,nace kai ashe nakai haka kyau,Meenat tace bakya fito da kyan naki ne ai ke kullum ke kike maida kanki baya.
Nace a haka dai duk kwalliyar taki aka hadu da Kwaja kuma,Dukana tayi a baya da wasa muna dariya,tace Allah sai na kai kararki,nace yawwa gobe zan kaiku ku gaisar da Baban Aayan,Allah ya kaimu.
Nace bari nasa takalmi ko?tace ae kisa me tsini ki Bada mamaki yau,ai ko na dakko cikin sabbabinmi wani Brown me tsini wow wow na gama birgewa yau ko uban waye ya ganni yau sai yawunsa ya tsinke indai Namiji ne.
Ina cikin gwada yanda zanyi Tafiya Meenat tana gyara mana dakin muka ji Karar motoci,nan take na zaro Hijab Meenat ta fisge ke wai mene haka bayan kin gama kwaye cinya ya gani dan Allah muje palo,duk sunyi kwalliya Meenat cikin Doguwar rigar arab,Maeesha English wear tasa riga da Wando suma sababbi sun sha kyau,mun baza turaruka,ni kuwa kamshin nawa daban ne da nasu.
Knocking muka ji nace wayyo kunya nakeji gashi nan zai ce sonsa nake,Meenat taja tsaki tace tonawa kanki asiri ki huta,Maeesha ce ta bude kofa ni kuma na hakimce a kujera na maze ina danna yar nokia ta ka rantse wata shegiyar waya ce nake chat ko wani abu.
Wow wani Balarabe ne ya shigo Aayan sanye da farar fitted jallabiya yasha kyau kamar me don ya canja style din gyaran gashi na ala tsine uwar me karya.
Kamshi ya cika gidan,cikin Securities wani ya taho zai shigo masa da akwatuna sai muka ga ya juya da Sauri ya bude kofar yace jeka daga nan ma is ok,da kansa ya shigo da akwatuna har Uku masu kyau na gaske.
Sallama muka amsa Meenat ta kifta min ido na mike jin karar takalmina ya kalleni muka hada ido,na tafi da shi Amma sai muka ga ya tamke fuska,naje har gabansa na makale murya can kasa nace sannu da zuwa Aayan.
Bina yayi da kallo yanda na sheka kyau ba a cewa komai,akwati daya na karba,Meenat ma tazo tace Sannu da zuwa yaya,da fara'a ya amsawa Meenat yace ya gida ya schl,tace lfy,Maeesha kuwa hannu ya bata suka tafa har suna dariya,tace yaya dama tuntuni Meenat take nemanka zata kawo ma karar Sis Mufee wani me Katon ciki ne cikinsa kamar Randar Ammah yake zuwa wajen Meenat wuyansa Allah kamar bulalar malaminmu,shine Sis take ta tsokanarta tana mata dariya.da gaske ya tambaya yana kallon Meenat da yake duk yarane da Sauri Meenat tace ae wlh tun rannan kullum sai ta min dariya har da dare dan Allah yaya ka koreshi in yazo,ba damuwa in yazo ki fada min yace tare da Haurawa Sama,daya bayan daya na dinga kai masa akwatunan har Bedroom,ya shiga wanka lokacin na sakko kasa naji ana buga mana kofa nasan bazai wuce jarabar yan gidan ba,ina lekawa na hangosu kuwa mata da maza manya da yara na bude tare da cewa lfy? Basu gane ni ba sabo da kyau,Ke dalla matsa gidan ubanki ne? Juyawa nayi dan su kara ganin yanda na hadu,gaba dayansu da kyar suka gane ai nice, da mamaki sukace wajen dan Uwanmu muka zo ko kina da gado ne a gidan nan? Na yatsina fuska nace ku koma sai gobe da Safe a halin yanzu Bazan iya Barin me gidana yaga kowa ba dan karma a bata mana Mood, yanzu na boye abina na Adana mijina,na killaceshi baza kuzo ku Sa masa tention ba aikin banza sai roko da san abin duniya duk abinda ake muku bakwa gani sai kun shiga hakkin iyali ba dama mu gabatar da Sunna cikin kwanciyar hankali Naja tsaki kafin suce komai na banke kofa na kulle nasa lock nayi tafiyata.
AsmaBaffa
[1/13, 12:33 AM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖
KASUWANCI NA
51-55
Official
By
AsmaBaffa
Ina matukar baku hakuri fans na rashin posting dina jiya ayi min Afwa bana nan unguwa naje,yau kuma baki nayi shi yasa ban samu dama ba.
Wannan page dina ne AsmaBaffa🤣🤣🤣nima na bawa kaina da kaina.
Meenat suna ta karatunsu na wucesu na shiga kitchen tare da shiryo abincin Aayan na kai har Bedroom dinsa yana wanka bai fito ba dama wankansa dade wa yake sosai,ina zaune Saman Bed dinsa sai gashi ya fito daga shi sai dan gutun towel a kugu karami a wuyansa,jikinsa abin kallo ne ya hadu da yawa ko kai waye sai ka kalleshi sabo da kyau,dan kar yace ina kallonsa kawai sai na sa yatsana na tsakiya a baki ina ta tsotseshi na sadda kaina kasa,har ga Allah ban san ma na sa Yatsan a bakina ba, ina ta yi ya juya baya yana ta shirinsa don bazai iya kallon tsotsar yatsan nan da nake ba bilhakki abin so childish.
Tunawa nayi da salona na wayo da zan masa tunda na Canja taku na,sai na Mike a hankali na taka har gabansa dama na cire takalmin dana sa Already,kunya da tsoro suka taso min sai na dake na matso lotion din da yake tsafawa na murza a hannuna cikin wata murya da ban san na iya ba nace kawo na tayaka baka iya bama sam kawai ban jira amsar sa ba na daura hannuna a kirjinsa tare da cewa mutum kato bai iya kula da kansa ba,suman tsaye yayi amma kuma sai naga yaja baya da sauri ya matsa tare da cewa kee mene haka,na nuna ban gane ba nace da akayi me? Ka tsaya mana na kara matsawa da sauri yaja baya again kamar yaga dodo, na bishi zan kara damkoshi sai naga ya ja da baya da gudu,na fara dariya ina binsa yana guduwa,na bishi muka fara zaga dakin da gudu dan sosai yake guduna kamar kamar yaga wani zaki ko Damusa,ina ta binsa ina dariya shi kanshi dariyarsa yake kunshewa yana yin kadan yana ke wai mene haka bana so, nace Allah sai na shafa ma,muka zaga ta bayan sofa ya daga kafa zai haura ta saman Sofa lokacin na kamo Damtsensa da hannu biyu sai ya fada saman Sofa nima na bishi muka fada kai gaba daya ba shiri ya saki dariyarsa,nima haka na cikwikwiyeshi yana so ya cireni a jikinsa amma na rikeshi kam gaba daya a jikinsa na Dafe,da kyar dai ya kwace ya Mike ya gudu Saman Bed gaba daya ya shige blanket,sai kansa a waje,nace dan Allah ka tsaya mana wai mene? Yace ke tsaya a nan karki matso nan,Na tsaya a hankali nace shike nan tunda baka so bari na zauna a gefen Bed din naka,yace no sai dai in baza ki taba min jiki ba to ki zauna,ai nace na fasa Zama kawai zanyi.
Ka tashi ka karasa shirinka Kaci abinci sai kayi baccinka,kaje wurin Daddy? Harara ya mako min ke wai nan nufinki wata mace ce har wani sani abu kikeyi kina tambayata abu kanki tsaye,ni da Daddy na me ya shafeki a ciki ki daina min shishigi tam.
Allah ya baka hakuri dama tuna ma nayi,sakkowa yayi daga saman Bed din ya karasa shirinsa cikin kayan bacci masu kyau na maza ruwan toka,s aman carpet ya zaune dake dan gefen bed din,yana bude flask din yaga Waina da miya nan take ya dinga zuba murmushi maimakon ya min godiya kawai sai yace dan sunkuyo zatona wani abu zai ce kawai sai na ji rankwashi a kaina kwasss Gift ne wa ya fada miki ina son wannan? Anyway tnx da sauri na Dafe wajen nace ouchhhh ina turo baki cike da shagwaba nace da zafi Allah yanzu da kai na yiwa haka da tuni ka fara fada,abincinsa ya fara ci bai ce min komai ba,har ya gama yayi Brush ya fito tare da yin Nafeela raka'a biyu,lokacin na kwashe kwanikan na maida tare da gyara wajen,lokacin yana shafa addua ya idar.
Saman Bed ya haura bai ce min komai ba dan ni Jarida nake ta buduwa ina kallon hotunan labarai,tunawa nayi ban fadi me ya kawoni ba,nace dazu mun dade da Daddy Muna ta hira,gaskiya Daddy yana da kirki sosai,kayi sa'ar uba Allah yaja kwana ya kara masa lfy me amfani,sabo da na yabi Daddy tare da masa addua sai naji yace dawo nan ki bani labari me yace miki ya furta yana nuna min gefensa da Hannu,naso naki zuwa amma kwarjininsa baza su bari na masa musu ba Sam,haka na Mike naje tare da hawa saman Bed din sosai har tsakiya kusa da jikinsa,kawai naji yanayina yana canjawa sai na tsinci kaina da son kwanciya a jikinsa musamman da naji laushin fatarsa dazu ga kamshi,du sai na diririce abinda nazo da niyyar na fada cewar a sakeni na fasa auren sai na kasa na manta ma da zancen Sam,sai naji kuma shagwaba ta motsa ba abinda nake so irin nayi abata na samu me biye min amma ba dama,a raina nace ke kina yar yarinya haka,muryarsa ce ta katsemin tunani da cewa ina jinki, kawai sai na susuce na rude abinda ya rambayeni daban abinda nake bashi amsa daban na riga da na zauce sabo da ya hadu da yawa.
Na jingina da jikin Bed din nace hmm dama Ashe Umrah kaje bamu sani ba? Yace ae mana,me kika yi wa Daddy? Nace kudina ya kare nazo nan na dauki 5k ciki ka irga abinka kar kaga babu kace nice shima ba yanda zanyi su Meenat zasu je schl,yace Ok Daddy yace miki wani abu? Ni dai ko jinsa bana yi wani iri nake jin jikina nace uhm...uhm...turarenka ma jiya nazo na fesa maka,amma kadan na fesa kar kaga ya kare kace nice, kalau kike kuwa ko aljanun sun motsa, kamshinsa ya gama gigita min rayuwata sam na kasa gane kaina,duk Ac da ke wajem gumi na fara yi,a hankali jiki ba karfi na zame dankwalina gashina me uban tsayi ya watsu ya kara wani kyau, bai kawo komai a ransa ba tunda yasan shirmena kuma kallon yarinya yake min har na Isa ma wani feeling,a hankali ya juyo kamar me rada yace ko baki da lfy?, Nace ni ina zan sani lfy nake ko kalau bazan iya ganewa wanne yanayi ake ba,sanyi ne ko Zafi,zamewa nayi tare da kwanciya a saman bed din tare da lumshe ido nayi shuru ban kara magana ba nayi shuru,tasar min a bed ki tafi to tunda ke ba a abin hankali da ke,shuru bance komai ba,ya matsa na bar masa bed ni kuwa tuni jikina yayi weak da yawa bana son ko nayi motsi ina daga kwance nace kawai labarin gidan nan fa Daddy ya bani, to shine kike min shirme abinda na tambayeki daban amsarki daban? Banza nayi dashi,shima bai sake magana ba ya juya min baya tare da kashe light ina jinsa yace tunda baza ki tashi ba sai ki shekara a bed din,shuru na masa har ban san bacci ya kwasheni ba shima haka.
Karfe daya na dare na farka na tuna maganar da zan fada masa ni ko dama komai dare idan na tuna zan fadi magana ban fada ba indai mutum na kusa dani sai na tashe shi,ba bata lokaci na kai hannu saman gashinsa na ja da dan karfi firgit ya tashi da masifa,hannu na kai da niyyar nace Aayan zan dan bigeshi,caraf ya rike min hannu tare da juyowa daf dani muna facing din juna har muna jin numfashin juna,a hankali yayi magana ki daina taba min jiki,kinzo kin dameni menene,sai na kara mantawa da maganar da zan fada ta a sakeni,yanda naji hannunsa cikin nawa me laushi ga kamshinsa dake kashe min jiki sai nace ruwa zan sha,Ke haka kike dama kamar yar 4yrs ki hana mutum sakewa kuma haka kike kwanciya da kayan jikinki ke? Nace a'a yaune kawai,haka kawai kizo ki takura min ya Mike tare da kunna light ya miko min robar ruwa daya,ba shiri na bude na Sha ta dole,akwatin da yazo dasu daga Saudiyya ya bude tare da Zaro min wata sabuwar rigar bacci hadaddiya amma fa tayi tsaraici gata fara wata silk ce yar guntuwa me hannun bra,in kasa komai sai an gani duk wani tudu da gangare,ina gani nace zan tafi Dakinmu ni,Murmushi yayi tare da komawa jikin kofa na dauka bude min zaiyi na tafi sai naga yasa lock ya dawo yace ungo tashi maza ki cire kayan nan,a ransa yace zaki takura min gwara nayi maganinki.
Hade rai yayi kamar baya dariya ba yanda na sanshi tun farko,na tsorata yace get up ko yanzu nazo na fara ball dake tunowa nayi da yanda ya taba min farkon ganina dashi,da sauri na Mike na karba na kasa cire kayan na tsaya kawai,a hankali ya matso tare da rungumoni na kwanta a jikinsa ina ta salati a raina don wani zirrrr nakeji tun daga kaina zuwa kafa ta,zip din rigata ya zuge na kwace jikina da sauri na ja da baya zan tsere da zafin nama ya biyo ni tare da jawo rigita na dawo baya ina dariya shima haka,har mamaki nake dama yana dariya,ido muka hada sai naga idonsa kamar ruwa a ciki yayi dan red,ganin ina kallonsa kawai sai ya dauke kai tare da juya min baya yace na baki 2mnt ki canja idan kika sake na juyo wlh sai na miki sintir.
Da sauri na cire kayana daga ni sai pant nace kar juyo na kusa da sauri na zura rigar a jikina dukiyar Fulani na yan matasa ana kallonsu da adadin girmansu,Na ninke kayan dana cire harda bude Sip side daya na adana abina kun San ni akwai tattali sabo da an saba da babu don wata tsaftar ma akwai babu a cikinta.
Juyowa yayi yaga yanda nayi mugun kyau a ciki yace cire min a bata na fasa dama lefen wacce nake so zan aura na fara hadawa shine na baki daya sai naga ma bata miki kyau ba Ciro min a bata ba size naki bane nata ne, wani bakin ciki ya kamani tun ba ayi nisa da business ba za a ce aure za a kara,sai na tuno dama fa yayi aure ba sau daya ba yana saki,a raina nace me auri saki ne nima Sakina za ayi,da kyar na daure bacin raina na kakalo murmushi nace Allah ya sanya alkhairi kace zamu Sha biki ai ranar za a ga yanda zan kwashi rawa,kai amma naji dadi sosai kaga an samu me Kula da kai wacce rake sonka kake sonta haba ai Alhmdllh naji dadin wannan magana ka kuma birgeni da sauri da sauri nake maganar ina murmushi harda yar dariya kamar na zare, muryarsa naji yace tnx lallai kina da hankali na yaba da hankalinki kwarai ba ruwanki baki dauki duniya da zafi ba,sai ki dinga min abin cin gargajiya tunda nan kika kware ita kuma dama tafi iya na bature,cikin bacin rai da fusata na hayayyako masa da masifa dake ni tsinanniyace ko? Sama na zaga ko me? Kanwa na kawo? Wlh bazan kara kulaka ba bare har nama girki,auren Kasuwanci mukayi dan haka duk kudina ka tattarosu ka biyani gaba daya na kara gaba,kawai ka sakeni na gaji dama sai kawai na fashe da kuka sosai,da mamaki ya kalleni,cikin kuka nace bani takadda ta,wannan gidan naku bakin gida du ba na gari a ciki sai Daddy kawai gaba daya bakin Uwa ne a gidan banda Daddy,dariya ce ta kamashi ya dinga yi ni kuwa ina ta jin haushinsa,yace to kwanta gobe Insha'allah zan baki komai da kike so har sabon gida sai ku koma can da zama sannan na baki takarda abinda kike bukata yanzu,k karki damu kwantar da hankalinki indai wannan ne baki da damuwa,tunowa nayi da maganar Daddy cewar duk Wanda ke son rabuwa ba matsala za a rabu,naji wani mugun bacin rai ni rabuwar bata Dameni ba sai da naji yace wai aure zaiyi.
Hannuna ya jawo zuwa saman Bed tare da cewa kwanta ki huta kiyi baccin karshe a gidan nan gobe zaku tafi,bazan huta din ba nace cikin fushi, kwanciya yayi a gefe na tare da kwantowa a samana yace tsaya kiji ina da nauyi? Nan take naji wani shock na gaske a dukkan jikina,nayi luf ya kwanta flat a samana kirjinsa saman nawa,wasu tsutsotsi naji yam yam a jikina ko nauyin nasa banji ba duk da cewa Bai sakar min nauyinsa ba, hannayena na zuro ta bayansa tare da sakalesu na rungumeshi nace baka da nauyi wai wayo nayi kar ma yace dadi naji gaskiya kuma abinda nakeji ne yasa na kasa daurewa sai da na dangana da rungumeshi.
Gashina ya kalla me kyau da kamshi ya shafa a hankali yace ba laushi ma kamar ganyen bishiyar Dabino,murmushi nayi nasan ba gaskiya bane,na nutsa hannuna a cikin gashinsa me matukar santsi da laushi na kalleshi nace ina Sam taka Sumar kamar ta gyartai me gyaran tukunya da karfe,ni a raina dama so nake na taba Sumar shine na samu hanyar nayi masa wayo, hancinki yayi fadi da yawa duk bana ganewa me yake nufi ai nice kawai nake masa wayo,naja dogon hancinsa nace ai nawa yafi naka,yana karewa Lips dina kallo yace ke a tsorace na kalleshi yace ai bakinki yayi girma da yawa sai kace kofar gari,lips dina na turo tare da shegiyar Shagwabar da na zuke masa jini nace ai gwara nawa Allah,kalla na bude masa ka gani dan karamine wa zai ce spoon zai shiga nan? Ba wani nan cewarsa,ido na juya masa yana kallo na idonsa kamar ruwa ruwa ciki,ido muka hada da sauri yayi sama da kansa dan kar na gane yanayin da yake ciki,Aayan mene?na tambaya a hankali,murmushi yayi da saurin yana goge idonsa yace nothing me kika gani? ba komai I just ask never mind ok na furta irin naje schl fa,murmushi yayi tare da cewa kin san me yasa kike bani mamaki? Nace a'a duk wannan abun da muke yana samana a kwance,yace karfin halinki ne yake bani mamaki yana maganar yana kallon lips dina,a hankali ya gangare gefe daban yana cewa Good night ga key nan ki bude idan zaki tafi.
Ban so ya koma ya kwanta ba sabo da ina jin dadin hakan banki mu dawwama a haka ba, munyi shuru kowa da abinda yake tunani,muka ji ruwa me karfi ya tsuge kamar da bakin kwarya,mikewa yayi tare da bude duka windows din nan take sanyin ruwan da ake da iska ya ka dakin gaba daya,Ac ya kashe da light,walkiyya fal fal tare da tsawa taratsatsa ake ta yi ba tsayawa,na tsorata dan ban son walkiya da tsawa ga window a bude muna hango komai,blanket ya jawo ya rufa mana gaba daya harda ni,ina ji ana tamfatsa tsawa,da aka saki wata ban san sanda nayi sauri na matsa kusa da jikinsa ba daf dashi kamar zan shige masa amma sai ban ko taba jikinsa ba,bai san na matso ba ya juyo zai tatsileni duk girmana yar karama nake tashi a gabansa,kaina ya koma sam kirjinsa,kamashinsa ya bigeni, tsawa aka kara rankatawa me karfi na shige jikinsa sosai tare da kankameshi,duk dauriyarsa kasawa. Yayi sai da yayi hugging dina back,fuskata a saitin tasa a hankali na tsinci muryarsa yace tsoro?nace yeah wai ni baturiya,kina so ki daina Ji? Kai kawai na daga dan yanayin da nake ci bazan iya magana ba.
Tafin kafarsa yasa a nawa kafar yana gogawa a hankali,cinyarsa ma tana gugar tawa,laushi da laushi sun hadu sai wani lumus kake ji,gashin jikinsa me santsi yana min wasu rubutu me lankwasar dadi😄 dadin ma Kun San har da me Lankwasa
Ni ba gane me yake nakeyi ba dan nauka tsoron da nake ji na tsawa yake min maganinsa har ga Allah na manta ana wani abu idan anyi aure,kuma bayan haka ma ai nasan shi ance bashi da lafiyar da zaiwa mace wani abu,shi yasa na kara samun nutsuwa bana tunanin komai, fuskarsa ya daura saman tawa yana goga hancinsa a nawa,da kyar naji yace baki da hanci Ashe, kasa magana nayi sai da kyar nima na kara goga masa nawa back nace wannan kaine gashi me tsayi,bakinsa naji kawai cikin nawa sai da numfashina ya dauke yanda naji abinda yake min me tafiya da nutsuwar dan Adam,tuni ni na manta ma ana wani tsawa da ruwa tana ta rugiginta ni kuma muna rugurguzar juna,bakina yake tsotsa kamar zai cinyeshi,gaba daya na susuce shima haka,a hankali yace a barshi haka kin daina Jin tsoron? Nima naji dadi bana so a daina sai na shirya masa wayona shine da shagwaba nace ni dai tsoro nake ji zan iya suma gaskiya kuma har yanzu ina ji, dariya kawai yayi a ransa tare da Hamdala yace kai duk wannan abun amma kike jin tsoro gani a kusa,ni har na ma gaji amma dai shike nan bani tongue dinki, like how? Na tambaya,Ya ake mikawa mutum hannu ko wani abu,zaro tongue din kadan nace uhmm,Hhh dariya yayi yace sai kace miciji ya zaro harshe, karba yayi yaci gaba da gudanar da kiss dinsa sosai har lumshe ido nake ban san sanda na fara taimaka masa ba, wuyana yake shafawa tare da Sakkowa saman kirjina,nan take ya birkice ya koma wani iri,Nima haka nayi mukus dani ina ji yana murzasu ba da yawa ba naji kwakwalwata baza ta dauka ba sai na janye jikina da sauri nace na daina Jin tsoron,dake Ya kai karshe a duniyanci sai yayi murmushi tare da cewa har kin daina Jin tsoron? mace ae ni dai bacci zanyi,bai kara ce min komai ba ya juya ya fara addua ban san sanda bacci ya kwashe mu ba.
Washe gari muna yin Sallar Asuba na tuna akwai schl yana Azkhar nima nayi nawa na Mike tare da maida kayana da sauri ina ka tashi ,yace Alhmdllh nayi waje abina Kitchen na shiga,sharp sharp na soya mana chips da egg sai ruwan tea na shirya komai a Dining,sai ga su Meenat sun fito cikin shirin schl dinsu,Sis ina kwana? Cewar Meenat kun tashi lfy? Sukace lfy Alhmdllh.
Ma'eesha tace a Palo kika kwana sis jiya bamu ganki ba,Kunya ce ta kamani nace ae a Palo bacci ya kwasheni,Meenat tace a fadi gaskiya dai sis a kunne ta rada min ya akayi ne daga cewa kin canja salo sai ki dawowa har palo na fito bakya nan,Dariya nayi nace hmm ai ke dai bari Meenat ai na fada miki so nake mu bar gidan nan,zuwa nayi na takura masa kwana nayi ina masifa sai ya bani takarda ta, fada mukayi sosai,Meenat ta dauka da gaske ne tunda tasan Mufeeda bata musu karya,nan take gabanta ya fadi kamar zatayi kuka tace haba dan Allah Mufee kamar baki da ilmi wannan ai tsarin addini bane bai dace ba,dan Allah karki tozarta mu muna rufin asiri samun miji kamar Aayan sai an tona,ki tuna da shawarar Ammah sis,Maeesha ma tace dan Allah sister karki bari mu bar gidan nan,ni kuwa bata rai nayi kamar gaske nace karku dameni na gaji duk ma yanda za ayi ni bazan zauna dashi ba,shi yasa jiya ban bari mun kwana lfy ba
Meenat ce ta fara hawaye tace bakiyi halacci ba wlh.kuyi sauri Kuci Ku tafi schl,sai suka ce mun koshi su wai sunyi fushi baza suci ba,ku zauna to bari na fito,zama sukayi ni kuma na shiga wanka da sauri na shirya kaina cikin doguwar riga ta Atamfa dama na iya dauri yanzu wajen Meenat na kafa shi na zuba kyau,ina fitowa kamar mun hada baki sai gashi shima ya fito cikin shadda milk color ya Sha kyau kyau kamar a saceshi,agogon dake hannunsa ya kalla yana sakkowa daga steps,Dining ya nufo kamar bai sanni ba,kallona bai yi ba,abin ya bani mamaki mutumin da jiya muka kwana lfy,Su Meenat kawai yake kulawa suna magana yana cin abincinsa,Meenat ganin hakan da yayi y nuna sai ta tabbatar da gaske jiya rashin mutunci nayi masa,nan take taji tausayinsa tare da jin haushina, ina lallashinsa suci abinci amma suka ce baza suci ba har haushinsu ya kamani nace Ku tafi ai cikinku ne kuma sai dai ku tafi a motar haya yau ko napep hukincinku kenan na bijirewa maganata,Hararata Meenat tayi ina kallonta Shima Aayan ya gani yasan suna min biyayya suna da tarbiya tunaninsa ko wani abu nayi musu, nace Meenat me kikayi ba dai ni kika harara ba? Kunkuni tayi,nace I saw u now zaki san ni kika yiwa rashin kunya ke kina ganin kin girma ko nawa kike har ina miki magana kice zaki harareni sabo da ina wasa daku,nifa ba hararki nayi ba,tsawa na daka mata ni irin Babba din nan dalla jeki stupid Girl,Maeesha tace amma kin San munyi late zamu makara da yawa,shi dai yana Shan tea yana jinmu, baiyi nisa da fara sha ba ya Mike shima tare da cewa ga tea dinki nan nima bana sha muje na saukeku a schl Meenat.
Ina tsaye suka tafi ni kuwa dadi naji yana kula yan uwana ko bai kulani ba in dai ya kula yan uwana Alhmdllh,akan ya wulakanta min yan Uwa gwara ni yayi min ko mene,sabo da wasu kai kadai suke so duk Wanda ya shafeka basa saurarsu bare su taimaka musu sai iya matarsu ko budurwarsu,Meenat suna fita suka hango Kwaja yana wankewa su Sajida takalmin schl,da Sauri Meenat tace Yaya Aayan ka ganshi to dan iskan da suke hadani dashi shegen ciki kamar an kifa kwarya.
Koda Aayan ya kalli Kwaja bai San sanda ya saki dariya ba tare da cewa lallai an cuceki am so sorry su Hanifa yan iska ne,kamar ya sani sai ga Kwaja ya dago kansa wanda ke dauke da keya me shegen tsini goshi rafkeke ya bude baki hakoran gaba cako yana sakin murmushi yasha uban askin kwal kwal jijiyoyi a kansa rada rada ya dago sirisiri hannunsa saitin Meenat yana kifta mata Ido kamar na Kwado, Kuka Meenat tasa sabo da takaici,Aayan da kansa ya kira Kwaja ya masa warning kar ya kara ganinsa ya kalli ko fuskar Meenat,kuma ko gidansu ya daina shigowa ya dinga tsayawa bakin gate,a gigice Kwaja ya dinga bada hakuri kan ba zai sake ba.
Bayan na gama komai nawa dana saba na gida shirin schl nayi 1:30pm Driver ya kaini schl tare da kawata muka hadu Sayyah,Muna hira Sayyah tace tunda kina da aure ki dinga zuwa gidanmu ana miki gyaran jiki,Maman Mu tanayi har shagon gyaran jiki ne da ita,idan kika je a gida ma zata miki naki,kuma gaki best frnd dina naga ke yarinya ce baki ma san auren ba,zata koya miki komai ta dinga tsumaki Oganki yaji zam zam,yanda kike me kyau fara idan ta gyara miki jiki sai Oga ya zauce wlh.
Baki na tabe tare da cewa ke ni bazan yi ba Natural wanda Allah min ya isheni yanzun ma a haka kinga yanda yake bani wahala ina ga na kara wani abu,Karya nayiwa Sayyah dan karma taji sirrin aurena amma sai ta dage wai dole na samu time a dinga yi min ko duk wata sau daya ne,sannan a bani na tsumi nasha,a raina nace hauka nake na Sha tsumi me gida baya ko kallona kuma ko yaushe zai iya Sakina mu rabu,jiya ne ma kadai muka taba hada makwancin shima hakan nice na je tsautsayi yasa kuma ban fadi maganar data kaini ba na bige da kwana a can,a fili nace Sayyah kenan zanzo to amma sai na sanar masa,kirashi a waya ki fada masa yanzu muji,sai yanzu na tuna bani da Number sa shima baida tawa amma sai nace yana Office yanzu he is busy sai na koma gida,tace to shike nan zan fadawa Umma ,nace ba matsala Insha'allah.
Muna cikin class 4pm Saura 1hr a tashemu sai naji wani malami ya leko ta window wace Mufeeda Adam Fatima?nace Sir tare da daka yatsa sama,yace zo kinyi bako,Mamaki ya kamani bako kuma ni to wa na sani,Haka dai na daure muka Mike ni da kawata Sayyah cike da tsoro na fito motocin Aayan na hango mamaki da tsoro ya kamani ina ta Addua a raina nace Allah yasa lfy dai,Sayyah tace waye wannan haka wani hamshaki? Mijina ne,Sayyah tace kut dama kece matar Aayan Muhd Jabeer ta yanzu? Nace ae mana kin sanshi ne? Tace a labarai muke ganinsa a TV kuma akwai wata yar kawar Umma yar gidan Minister of finance ta Dade tana binsa tana sonsa sosai ta dinga kiransa duk inda yake sai ta nemeshi amma Sam ya dinga Wulakantata baya sonta,har yanzu bata hakura ba wlh sonsa takeyi,akwai ke yan mata da yawan gaske da na sani suna bibiyarsa don kawai ya kulasu amma ko sauraransu baya yi,nan take gabana ya fadi, bakin ciki ya taso min na fara masifa wlh idan ma kin Santa ki fada mata kar ta kara kiran wani da namiji a waya,aikin banza amma wannan kwai jaka, dabba, Akuya, tinkinya inba tsinanniya ba mene na bin mijin wasu a waya asararriya wacce ta rako mata duniya.
Sayyah shuru tayi tana kallon yanda na dage nake ta zazzaga masifa da zage zage,tace lallai kishinki yayi yawa,nace ai ba kishi nake ba kawai haushi ta bani mace na bin maza tana zubar da ajinta,Dariya kawai Sayyah tayi tace to nidai na koma class tunda mijinki ne bye ta juya abinta,a hankali naci gaba da tafiya kafin na karasa motarsa kawai ya fito ya tako har inda nake tare da kamo hannuna ya jani ya sani cikin mota ya shiga Suka ja motoci muka bar schl din gaba daya.
Nace lfy?bafa mu tashi ba,yace ae ni na tashi daga Office yau kuma abinci nake so kiyi min 5pm Yarima Bobo zaizo, shuru nayi ina gefensa a baya nayi shuru har muka karasa gida muka fito da sauri ya rike hannuna yana Jana fiiii,har cikin part dinmu,Hijab ya zare min ya kaini har kitchen yace fara masa Abinci me kyau yana son Founded yam da miyar kwai,nace to da sauri na fara aikin shi kuma ya fita,nan danan na shirya lafiyayyan Sakwara da miyar kwai tasha nama da alayyahu tayi dadi sosai,na hada lemuka kala biyu na zallan fruits me dadi yayi Sanyi,na shirya komai a Dining sannan na gyara kitchen din tare da kara gyara part din sosai.
Bedroom na koma tare da fesa wanka na shirya cikin wata Atamfa cotton Orange riga da skert na Sha kyau sosai nayi kyau na gasken gaske,ina kamshi na hau Saman bed dinmu na kwanta ina hutawa 15mnt sai gashi ya shigo sanye cikin jallabiya fara yace muje Ku gaisa,na Mike haka nayi hanyar fita,
Ya riko hannuna tare da juyo dani baya yace haka zaki fita? Nace mene to a nan?nayi waje abina a haka,da sauri ya jawo ni tare da cewa ki canja kaya bakiyi kyau ba kisa doguwar riga,banyi musu ba nasa Arabian Gown tare da mayafin kamar Balarabiya na fita har Palon da suke.
0 comments:
Post a Comment