Mikewa sukayi har Dining suka zauna nayi Serving dinsu, Yarima sai murna yake yi abin cin da yake so ne,suka fara ci Lauma daya Yarima ya fara Santi uhmm kaga yar yarinya da iya girki shi yasa naga mutumin sai kiba yake yi da kyau, Dariya nayi wace tasa nayi wani mugun kyau.
Tsaki muka ji ya ja tare da gasa min harara,shuru nayi tare da sadda kaina kasa,kallona yayi tare da cewa je bedroom ki dauko min wata paper saman Bed,ok nace tare da mikewa zan tashi kawai na bige flask din miya ta dan zubo min a hannu ga Zafi sosai,hannuna na yarfe tare da cije lips dina,da sauri ya Mike tsaye tare da rike hannun nawa yana min sannu ya tsotse min yatsun da miyar ta zuba yana hura min da bakinsa kuma fuskarsa ba alamar rahma Sam sai ma fushi da yakeyi,ni dai kallonsa kawai nakeyi har ya gama ya kalleni tare da cewa ba Zafi? Kai na daga tare da cewa yeah,jeki to ki kawo min.
Ina tafiya Yarima ya dura masa ashar yana cewa amma kace min wani fada ma kukeyi munafuki,to me nayi na wani soyayya a nan? Ku fa bakwa ganewa Hausawa ba dama aga mace da namiji sunyi ko magana sai ace wani love ni zan iya kwana da mace same Bed naked ma ba abinda zai faru.
Dariya Yarima ya dinga yi yace Allah ya taimakeka ba kyau ganin sirrin wani da sai an gwada na gani a gabana,kai har kana da bakin magana dan Iska da ban sanka bane sai ka fadawa wani abinda har wani Fyarfadiya kakeyi idan ta ciwo ka shine zaka zo kana min kuri,Dariya Aayan yayi tare da lashe lips din kasa kamar an tuno masa wani dadi daya taba ji yace lfy ce yaro,Kai aka bawa wahala wlh tunda kana iya sha'awa amma baza ka iya aikata komai ba akwai wahala abin har tausayinka nake ji frnd,Aayan yace kama daina tausayina yaro ni ba abinda nake ji,suna ganin na fito sukayi shuru tare da canja hira basu San naji komai ba,mika masa nayi na zauna kusa dashi a Dining din nima harda leka cikin paper daya bude nace mu gani,miko min yayi sai da ya bari na karba yace to ki rike du tunda Sa'idon naki ya kai haka,Murmushi nayi tare da mika masa nace amma da niyyar karantawa nayi tun a dakin zan tsaya na duba yanzu ma izininka nake nema,yace bazai karba ba Sam yayi fushi na masa shishigi, mikewa nayi da paper zan tafi ya jawo hannuna ta bayan kujerarsa na zagayo tare da zuro kaina a hankali ta saitin kansa fuskata na daura a wuyansa nasa hannayena tare rungumesu ta kirjinsa sannan na rada masa a kunne ina dariya ga paper dinka Dan Daddy mene na fushi na daura saman table din na juya tare da barin wajen na shige Bedroom.
Yarima yana ta dariya yanda yaga Aayan yana jin kunyarsa,yace ah to yarinyar nan naga Alama wise ce kai a boye kake yi kana mana karya gashi ita wlh ta birgeni baka taba auren ma irin wannan kalar ba sauran tsoronka suke ji magana basa iya yi maka,haka idan munzo basa iya zama a kusa da kai tare da bakinka lallai kana kwasar Harka wlh ga shawara ka fara tunanin fara Sex da wannan maybe ma ka warke kake batawa kanka lokaci, Allah kiyaye da wannan yarinyar karama ai sai na balla mata Hips cewar Aayan, nan dai suke ta faman zancensu ban san me suke shiryawa ba sai tafawa suke suna dariya.
Bayan kwana Uku muka shirya dasu Meenat mukaje tsohuwar unguwarmu tare da gaisawa da abokan arziki a dalleliyar mota,kowa mamaki yake,Nawwara ma yanda taga mun canja mun koma yan gayu ga hutu ya nuna a jikinmu ta dade tana mamaki, na bata Address na gidan mijina,Haka Uwaliya still suna zaune a gidanmu nace su zauna sai nan gaba zan gyara gidan.
Mun shirya dasu Meenat idan anyi Hutu zasu je Maiduguri dangin babanmu tare da Rimin Gado dangin Ammah can zasuyi Hutu sabo da zumunci kuma muna kiransu a waya muna gaisawa.
Tun daga Ranar da Aayan yayiwa Kwaja magana bai kara yiwa Meenat magana ba sai dai idan ya ganta a gefen gate ya fara lashe lips yana mata signa da ido ita kuwa sai tayi kamar bata gani ba.
Ana haka wataranar Asabar sun dawo daga Islamiyya sai ga wani ya Parker a motar eban kaya wacce ake cewa yar Kurkura ya fito ya taresu a hanyar gida,wani dan Gajere daf da kasa kamar a kifeshi da kwando me kwalelen kai sai ka rantse baza a samu Hula size din kansa ba,harda sa wata barmemiyar suit tsohuwa tasha duniya,Handkerchief ya zaro tare da goge wani kwafjejen takalminsa ya kalli Meenat yace Hajiya Meenat ko? lfy Malam idan tambaya kakeyi kayi sauri muke,murmushi yayi tare da cewa yan mata kenan wato Allah ya zuba baiwa a nan wajen yana maganar yana watsa hannayensa kafta kafta yan gajeru dasu kutuf ,ya kara cewa Allah yayi Kudirarsa anan,baki ya rike yace kai Kudirar Allah kenan,harara Meenat ta maka masa,Maeesha ma taja tsaki yace ahh harda ke yar ficika? kema kin hadu har kinfi babbar ma naga kinji haushina ke ban yabeki ba mata akwai kishi to kema kina da kyau ai baki sani ba kinfi ma babbar kyau shike nan ko?
Saura kadan Meenat tayi dariya kawai taja hannun Ma'eesha sukayi gaba,da gudu ya datse gabansu,in kina kaunar Allah ki saurareni in dai akan nace kanwarki ma me kyau ce to na janye dama dan kar ranta ya baci ne ace kamata bata ji yabo daga gareni ba naga tana kumbura shi yasa amma ai kin fita komai,kinga gaki fara,gaki doguwa yar tsakiya,ga sura,ga idanu,ga kamshi gaki me ilmi wayyo sai naji dama munyi aure,Meenat ta kara hade rai tace bamu hanya mu wuce,ya wani shagwabe fuska tare da canja murya kamar dan iska zan miki shagwaba Allah wayyo Baby,ai basu San sanda suka sheke da dariya ba,shi kuwa gani yake ai yaci gari ya birgesu,yace kin gani tun ba a je ko ina ba,ina me tabbatar miki zaki san Allah ya baki miji na gari,zan miki soyayya,zaki ji dadi,zan baki kulawa,zan miki duk wani abu wanda mace take so take nema a duniya komai,kawai ki bani dama,ki kula dani ki yarda dani zaki ji dadi,sai kinyi alfahari da wannan rana ta Asabar da muka hadu,da ace ana harba namiji sama ina tabbatar miki idan muka yi aure nasan sai kin harbani sabo da yanda zaki koma sona da ganin mutunci na,
Bari kar na dameku da surutu sunana Nasuru ko kuma ki kirani da OPERA,amma a unguwarmu anfi kirana da Nasuru me Hali, yayi dariya ya kara goge rigarsa yace Business man ne ni ina da yara dasu ke ci a karkashina sanadiyar wannan motar da kika ganni da ita domin daya a yarana shike Jan wannan motar,mutum biyu kuma sune masu tayashi lodi da saukewa,ba inda basa kai kayan miya da fruits,irin su tomatoes,Kankana,ke in baki a takaice har yalo suke daukowa daga Sumaila zuwa Lagos Agege, da sauransu,Meenat taji baza ta iya ji ba ta figi hannun Ma'eesha suka barshi nan tsaye bakin gate,suna shiga suka hango Haneefa da Sajeeda sun labe ta jikin gate suna ta dariya da alama Nasuru Opera ma su suka turowa Meenat shi tunda sunga an kori Kwaja.
Meenat ta hararesu su, sai kuma suka sheke da dariya Sajeeda tace a haka zaki kare in Allah yarda sai dai ki auri irin wannan wai ku masu kyau,anzo gidan daula za a ce sai me kudi zaku gani wlh nan gaba da kafarku zaku bar mana gida.
Meenat tayi murmushi sannan tace masu gida manya gidan wasu dai har iyayen naku basu da gado a nan bare Ku,a haka zaku kare banzaye marasa class,tass Meenat taji saukar mari tana dagowa taga Mujaheed ne ya mareta gasu Ameer nan a tsaye suna huci,Ma'eesha tace Allah ya isar mana,aiko Mujaheed ba imani kato dashi ya zage ya dinga Marin Ma'eesha yar yarinya karama ya Ciro takalmi ya fara kwada mata ta ko ina tana ihu,Meenat bakin ciki yasa ta dauki wani dutse kato ta buga masa a kai nan take jini yayi tsartuwa a kansa ya fashe,ya Dafe wajen yayi baya Su Ameer sukayi kansa suka rikeshi,Kafin kace me gida ya dau Alert sai kowa ya fito harda Hajja,Su Meenat tuni sun arce part dinsu da gudu,lokacin Mufeeda ta fita shopping,Hajja Bala'i take zubarwa kawai a tsakar gida an kashe mata jika,haka Ma su Abbi sai gasu duk sun dawo da motocinsu gida,haka ma iyayen su Mujaheed mata har da kuka,aka daukeshi sai asibiti don tuni ya Sume,sabo da hauka gaba daya suka bisu asibiti kamar wani Gomna haka dukkan yan gidan,Matar Abbi da Hajja sai Haneefa su kadai ne a Compound suna jimami tare da shirin daukan fansa,suna cikin wannan Hali sai kicif ga Driver na mun dawo daga shopping tun daga yanayin da na gansu gabana ya fadi haka na daure na fito ban fito da kayan dana siyo ba sabo da nima cikin shirin ko ta kwana na fito,ina taku dai dai nasha wanka sosai,
Ban san me ya faru ba,ba zato naji sun rufeni da duka,sunfi karfina ma'aikata si hakuri suke basu amma suka ki ji musamman Hajja kamar mahaukaciya ta dinga dunkule hannu tana dukana,Haneefa da takalmi me tudu,Matar Abbi ma ta ko ina,har sai da Hanci na ya fara jini ina habo, ana haka matar Abbi ta kara dauko Wayar charger tace duk kowa ya kyaleta dani sai ta ramawa Danta haka ta dinga tsula min wayar nan sai da suka min lilis,da kyar nake iya numfashi,sai lokacin hankalinsu ya kwanta suka koma can part dinsu suna murna.
Ina kwance a wajen hancina na fitar da jini sai ga Aayan ya dawo ya iskeni haka,da sauri ya daukeni kamar Jaririya don shi yasan yan gidan ne suka min haka,kawai ya sani a bayan mota shima ya shiga gefena Driver yaja da sauri sai Hospital,a motar ya kwantar dani saman cinyarsa yana min sannu duk ya damu ya rude,Hadadden asibiti ya kaini,suka min allurai da karin ruwa sannan suka bamu magunguna ya siya,na danji sauki da karfin jikina,ina tsaye zamu tafi ina cije lips ya tsuguna a kasa yace hau baya na, na kaiki cikin mota,bayansa na hau na lumshe ido sakamakon wani dadi da sanyin Ni'ima naji ya ratsani shima bangarensa hakane,haka ya dinga taka Steps ana ta kallonmu har mota ya kawo ni ya sani ciki a hankali shima ya zaga ya shiga Driver yaja muka tafi,a hankali ya min magana ko zaki kwanta cike da shagwaba ina Hawaye nace ae zan kwanta da muryar Kuka,saman kirjinsa ya kwantar dani kaina yana kirjinsa ina shakar kamshinsa ina Kukana wanda ba iya na ciwo bane harda shagwaba ma ta samun waje, hannunsa naji a fuskata yana share min Hawaye tare da lallashina to kiyi shuru haka ya Isa Ok, kai na daga Amma ban daina Kukan ba,yasa harshensa cikin kunnena nan take na dauke wuta wani mugun azabar dadin da ban taba ji ba shi naji,da Sauri na kankameshi tare da cewa wayyo ka bari yanda nayi maganar kamar me rada,nan take jikinsa ya wani amsa yarr, a hankali na daura lips dina saman wuyansa ina ta shagwaba, yana lallashina kiyi shuru kinji zan rama miki,nace to ka rama min ka samu Haneefa ka zaneta a gabana, yace zanyi miki sai nan gaba idan ta manta tayi miki haka,dole zan rama miki kinji, nace to sosa min gashina, ba musu ya fara sosa min gashina ina lumshe ido. Muna karasawa gida nan ma ya goyani suna kallonmu don lokacin sun dawo daga asibiti suma,ba damar yi mana magana suna tsoron Aayan haka muka wucesu, muna shiga yace ebo kayanki tare da su Meenat kowa akwati daya daya Sauri ku fito,gabana ya fadi ko korarmu zaiyi Amma sai na shiga muna hada kaya suna bani labarin abinda ya faru tun farko nima na fada musu abinda suka yi min.
Muna fitowa da akwatunanmu Uku shima muka ganshi ya sha wanka da trolley ya fito,duk muka kashe kayan wuta da komai sannan ya kira wasu ma'aikata suka zuba kayanmu a mota,yace muje wajen Daddy, muna zuwa muka gaishe da Daddy yana ta murna ya amsa yana tsokanar su Meenat,yace sai kun dawo Allah kiyaye hanya,ban san inda zamuje ba nace Ameen kawai na janye hannun su Meenat muka fito Sabo da mu basu waje suyi sirrinsu na yaro da Mahaifi.
Muna palon kasa ya dan dade sannan ya fito yace muje,ni da shi muna mota daya,Meenat da Ma'eesha ma suna mota daya can wata unguwa muka nufa me shegen nisa gata ba wasu gidajen kirki,kalar gidajen kamar na yan mafiya ban taba sanin da irin wannan unguwa ba sai dai ta hadu karshe.
Wani rantsatsen gida muka shiga idan na tsaya fada muku yanda tsaruwarsa take zaku sha mamaki ina kuma mamakin yanda Aayan zai dawo damu nan tunda Daddy yace Hajja baza ta bari ba zata iya tsine masa,ashe kuma Hajja ce da kanta ta sanarwa Daddy ta gaji da jarabata ta gaji da ganina a dauke mata mu daga gidanta zuwa wani dan lokacin da zata bukaci a dawo damu Family House Amma yanzu mun gallabi rayuwarsu a gidan,wanda ba kowa bane yayi wannan zugar Sai Ameer Sabo da yana wasu shirye shirye a kaina.
Gidan da ma'aikata masu kula da komai babu wani gyara da zamuyi komai Neat,Daki daya na sama muka dauka shi kuma Aayan yana hawa na biyu,Meenat tace Sis shawarata anan dayace ki koma ku dinga kwana room daya da Mijinki ki rungumi abinki ki fara auren nan da gaske,kisan damuwarsa yasan taki,ki kula da abinki,tunda yana da lalura baki sani ba ko zai warke,amma wannan abinda kikeyi ba mafita bane,meenat ance miki so na yake? So kike na kai kaina ya wulakantani watarana,wlh bazai miki ba Sis ki duba yanda ba so tsakaninku Amma kalli yanda yake mana Gashi mutimin kirki karki bari wata ta kwace miki miji ki dage ki koya masa sonki Sis.
Harara na watsa mata nace Allah ya kiyaye na zubar da class dina zan dai dinga zuwa ina tayashi hira iya abinda zan iya kenan 11pm na dawo muyi bacci tare daku,Meenat ta dinga rokona nace Bazan iya ba ni iya kacina tayashi hira idan baya bukata itama na ki zuwa,haka ta kyaleni.
Da ruwan zafi nayi wanka Allah yasa habo kawai nayi basu fasa min jiki ba banyi rauni a jikina ba,kamar ma basu dakeni ba tunda Habo nayi sai ciwon jiki,Meenat kuwa sun fita kallon gida suna zagawa,na fito daga wanka Daure da guntun towel ya shigo tare da ajiye min ledojin take away har guda biyar yayi gaba ba tare da ya kalleni ba, sai da muka ci muka koshi sannan nayi brush na shirya cikin riga ta dan wuce gwiwa kadan,karatu mukayi sosai Amma Meenat ta dameni sai naje dakin Aayan wai ko hira na tayashi,Maeesha ma ce min kije pls Sis,na zura hijab zan fita ina cika ina batsewa,Meenat tace haba Mufeen Ammah kamar baki waye ba me yasa kike abu kamar yar wajen gari ne wai? Shi yasa akace akwai dan birni a kauye a birni akwai dan kauye, ai sai ya dinga raina ki yana ganinki a baki waye ba,ni kuma sai nace ae haka ne to ya zanyi kenan? Meenat ta mike tare da dauko wata yar Ficikar riga da wando wanda da kadan ya rufe mazaunai rigar ma iya mazaunai take me hannun siririn hannu ba sai da bra ba domin an mata abinta,ba karamin kyau nayi ba dama gasu green dasu, Meenat ta kara gyara min gashi tare da fuskata, kamar wata Baturiya haka na fito,dan girgiza Mazaunan naki mu gani,hararar wasa na balla mata sannan na shafa turaruka na sa Hijab dina har kasa na musu sai da safe Meenat tasa key a kofar su ni kuma nayi samansa.
Koda na je ban san wanne Bedroom ne nasa ba haka nayi ta duba dakuna sai can na bude wani naga Hadadden Palo na gaske yasha kayan alatu kida na tashi sosai har tsakiyar kai da alama speaker ce a palon,a 3seater na hango shi kwance yayi wani dai dai dashi yana karanta Magazine,sallama nayi kusa dashi ya amsa ba tare da ya kalleni ba naji yace ya jikin? Nace da sauki,shiga kitchen gashi nan ki hado min Ginger tea,dama ban zauna ba na shiga kayataccen kitchen nasa na daura tukunya, wata waka ta Yan Nija ta ratsani sabo da shegen dadinta na cire Hijab din na ajiye gefe ba wata rawa na iya ba amma kidan wakar yaci ace ko kaine an girgiza mata,nan take na fara rawata nace in dai hakane zan koyi rawa kwanan nan, can na manta da wani tea saman gas ina ta shagalina a jikin fridge,har ya gaji da jirana ya nufo kitchen din da kansa sabo da so yake ya Sha ya kwanta bacci,yana zuwa yayi arba da shegiyar shigar dake jikina sai girgiza jiki nake ni dole sai na iya rawa,dariya abin ya bashi har wakar nake bi da bakina dan abinda naji suna cewa,saida ya gaji da kallo na kawai ya tako lokacin ina jikin gas din amma rawa ta nake,hannun mutum na gani ta gefe na yasa tare da kashe gas din ya dauke Pot din dake kai ba tare da yace min komai ba,ni kuwa kunya ce me tsanani ta kamani da sauri na maida Hijab dina ina kame kame kamar nayi karya,A kitchen din ya zuba sugar sannan ya dauki abinsa yayi waje ya barni a nan tsaye cike da kunya sai da na Dade sannan na fito Palo baya palon da alama yana Bedroom,Na dade a Palon daga karshe na Mike na kashe komai na nufi Bedroom dinsa,lokacin tuni yayi shirin baccinsa yana saman Bed amma ba bacci yake ba System ya kunna yana aiki, a jikin kofa na tsaya ya kalleni yace shugo mana ki kwanta ko ba a nan zaki kwana ba? Kunya ta rufeni na daure dai na karasa Saman Bed din tare da haurawa can sama,muryarsa naji yace ba a sa Hijab a saman Bed dina,a kunyace na cire tare da linkewa na Mike na saka cikin Sip sai kallona yake yanda kayan suka min tsantsan kyau.
Dawowa nayi ta gabansa na koma saman Bed din kansa ya sosa ya dan tsaya da danna system din sai kuma naga yaci gaba abinsa, zo ki gani naji muryarsa a hankali na zauna a bayansa tare da leka kaina cikin System din wasu zanen gidaje guda uku yace wanne yafi kyau a nan na kalla nace wancan Blue din yafi,ashe kin iya Zabe yace,ina bayansa bai San na zo daf da shi ba ya juyo da niyyar yi min magana ai ko ya gogi kirjina da gadon bayansa,ban san sanda numfashi na yayi sama ya dawo ba,shima wani shock yaji kamar electricity da Sauri ya kashe Laptop din ya ajiyeta gefe, duf naga ya kashe light duhu dundum ya gauraye dakin sai kamshi da karar Ac ke tashi,gaba daya jikina ya mutu ji nake kamar na shige jikinsa ina wannan tunani naji shi kusa dani ya kwanta tare da cewa kwanta mana me kike tunani,nace ba komai na kwanta nima gaba daya rabinsa a jikina ya kwanta tare da daura kansa saman Boobs dina,ban san sanda na daura hannuna saman sumar Sa ba me uban yawa da laushi,a hankali nake wasa da ita,kara makaleni yayi sannan a hankali yace yau me kika yiwa su Hajja haka? Cin Zaline kawai na bashi labari har abinda ya hadasu dasu Meenat tare da dukan Ma'eesha da sukayi.
Ransa ya baci yace Ok zanyi maganinsu so sorry for tht ya furta kamar me rada tsigar jikina ta tashi yarrrrrr nace ba komai ya wuce, yanda ya haye min jiki da Alama son jiki ne dashi kamar mage maimakon ni ya daurani saman jikinsa sai dai shi ya hau nawa ya wani lafe yana narkewa.
Gefen fuskarsa ya fara gogawa a tawa yana kara kankameni yana shidewa,ban san sanda na lalubi lips dinsa ba yana jin nawa saman lips dinsa da Sauri ya amshe ya fara tsotsar bakina kamar zai tauneshi ya huta,Wuyansa nake murzawa a hankali da hannuna,hannu yasa tare da zame rigata kasa,na
Tsorata Amma na tuna bashi da lfy bazai iya min komai ba sai Romancing shi yasa ban damu ba na saki jiki,Hannunsa naji a kirjina yana shafasu cike da Salo na kwarewa,na gama fita daga hayaccina dan ban san abin haka yake ba sai yau,taimaka masa na farayi sosai nima ina masa abubuwan da ban san a ina na koyesu ba,kokonto na fara yi anya kuwa wannan bashi da lfy? Gashi gaba daya gawurtaccen lafiyayye komai yana matsawa ace bashi da lfy,kai ban yarda ba,jikina na zame daga nasa ya kara shigar dani jikinsa gaba daya ya haukace kalaman da yake fada sun zarta hankalina ni nasan na karya ne dan kawai yana cikin mayen dadi ne,
Ganin da gaske bana so sai ya hakura ya kyaleni Amma yana jikina ya hanani maida rigata daga mu sai dan wando wasa kawai yake da kirjina Salo daban daban wanda karfin hali kawai nakeyi ina daurewa Amma na kai karshe da zan kasa Control,a hankali murya na rawa yace Ki bari a gwada ko na warke pls,na fashe da kuka ni ban yarda ba, to mene abin kuka tunda bakya so Bazan miki dole ba,shuru nayi sai ya bani tausayi yanda ya dade yana shan wahalar mata data rayuwa kawai sai nace na yarda ka gwada tunda hakkinka ne, da zafi zafi yake sarrafani nima Sabo da abinda yake mun na kasa Control nima biye masa nayi bare nayi Control din kaina,tunda ya fara sucking mini Down na zauce na susuce na fara yabon halayensa, ina Common Baby u r so Sweet, ina kukan dadi iri iri wanda na kara birkita masa lissafi har nan take ya fara neman hanyarsa,amma gaba daya nan take ya dawo normal ya daina sha'awar ba tare da ya biya bukatarsa ba,naji ya kwanta a gefena kawai,nace lfy?Yace kawai i can't, wani tausayinsa ya kamani,nace dama haka kake? Yace hmm kin gani da idonki,shi yasa ban son aure Sabo da zan zalunci mace,amma Daddy yace na aureki,kiyi hakuri kar ki soni ni dama Bazan so wata ba Sabo da bata lokacina zanyi kawai wace zata zauna a haka dani,yana ta Surutai da gani cikin bacin rai yake,na koma jikinsa tare da shigewa kasansa nace kwanta ina lallabashi kamar kwai ya kuwa kwantar da kansa a kirjina yana tunani,ina shafa bayansa na Lallashi nace zan zauna da kai haka,in dai akan wannan ne ni ban damu ba iya wannan romancing ya isheni,yarinya ce ke shi yasa kike ganin iya wannan ya isheki,kirjina na hada da nasa nace Allah zan iya kawai ka daina damuwa Insha'allah watarana sai lbr zaka warke yace Ameen tare da kara nutsar dani a jikinsa, yanzu me kike so na kara miki irin na dazu?, Nace ae amma Idan kaima kana so sai nayi maka cike da kunya nake maganar,shi kuwa murmushi yayi tare da cewa alright.
Wannan ba ance sai ana son mutum ake masa ba? Yace me? Nace abunda mukayi dazu kuma ai mu ba soyayya muke ba,au haka ne fa? ya fada yana shafa wuyana zuwa kirjina, kwanciya yayi tare da kwantar dani a kirjinsa,a hankali nace a Sa min riga ta pls,Yace to ya dauko kuwa ya saka min a jikina,kina so mu rabu kika ce ko? Gaba na ya fadi sai naji bana son rabuwa dashi sam,dan kar ya gano ni sai nace taya zaka ce haka bayan ka gane min Tsaraici ka tabani,Murmushi ya saki tare da cewa ni fa da kika tabani? Nace tunda Business mukeyi sai ka biya kudi shike nan,nawa zan baki? Na tsaya na gama tunani nace tunda ka biya Sadaki an yafe maka wannan,dariya ya dinga yi tare da cewa Na taba na alakoro,No Sadaka na maka iya yau banda gobe,ni kuma wanne na baki? Ai ni banji komai ba,uhm karya ko kinga me kike min kuwa ko na fada kiji ya bude baki zai gwada yanda nayi masa da Sauri na Sa baki na saman nasa, murmushi yake tare da cewa yaushe kika iya abubuwan nan a ina kika koyi wannan abun bayan ke yar yarinya dake ba wayo ba? Dariya nayi tare da cewa ka bar ganina haka wannan ai ba sai an koyawa mutum ba kawai ji ake an iya,na iya da yawa ma da ace shiri mukeyi da kai ko Love to da sai na kwance ma kwakwalwa,Dariya yayi tare da cewa to mu fara shirin mana daga yau,ko love din ne sai ayi na kudi kullum zan biya mu fara Drama kamar film a gaban kowa kuma,amma a zuciyarmu mun san Business ne ko? Sabo da naki dadin abin sai na wayance irin zan masa wayo mu dinga shan dadi ,sai na karbi maganar nace to na yarda yanzu soyayyar wasa zamu dinga yi kuma itama cikin kudina na kasuwanci,a ransa yana tuna rashin wayona yana dariya yace lallai zaki sha kudi karfa ki karar min da kudi,dadi ya kamani zan masa wayo da yawa na dinga shan dadi na,nace karka damu kadan zan dinga amsa,yace to cikin kudinki gobe zamu fita shopping da kaina zan kaiki.
Ai kuwa farin ciki ya kamani nace Allah ya kara budi Ranka ya dade,a hankali nace Yanlabai a Sa nayi bacci cikin kudina ka zame dubu Uku tunda na saka aiki nima,dariya abin ya bashi yace to shike nan cikin kudinki na Kasuwanci zan cire kudina tunda yanzu ke kika nema,nan ya fara min wasu Salo a kunne na yana lallabani kamar masoyan gaskiya,na kara yin wata mika yace har naci dubu biyu,nace a'a ai banyi bacci ba dubu daya da dari biyar kaci dai,Dariya yake ta min ni ko lokacin hankalina baya tare dani ban san sanda nayi bacci ba.
Washe gari da Safe Hajja tayi shiri sosai ta je wajen Daddy yana kwance ta dinga zuba masa masifa da zage zage karshe tace wlh wannan yarinyar da kasa ya auro mana Sabo da mugun halinka Sabo da baka kaunar yan uwanka to wlh sai nayi fata fata dasu,ka fadawa Danka tunda ka Isa dashi tun wuri ya fara shirin sakin wannan matsiyaciyar ko kuma kai ka fuskanci fushina,kar ma kasa ya saketa kyaleshi da kaina zanyi maganin abin ka sanni kuma ba a taka ni a zauna lfy,haka Hajja tayi ta sambatu har da na mahaukata ma kamar sabon kamu,ficewa tayi a fusace sai wajen Matar Abbi nan ma tana takama da gadara tace Karimatu jiya wanne yan iskan ma'aikata ne suka dafa min cabbage soup dinn nan me bauri Maggi har saman kaina,ke kuma da yake shashasha ce kika bari suka kawo min Sabo da kun rainani,nice na Haifa muku Mazajen da kuke aure dai baku Isa kun canja musu Uwa ba yan iskan surukan Zamani mutum da yayansa ace za ayi maka iko dasu,matar Abbi da yake Hajja ta shanyeta haka ta durkusa tana ta bata hakuri,tsaki taja ta figi Jakarta tare da fadawa kitchen ta dinga cin uban yan aiki kamar zata yage bakinta sai da ta gaji tace ta canja dokar gidan taga cewar yan aiki suna nema a hada baki dasu a kasheta jiya an mata girki da farin Maggi me hawa kai dan ta kusa suma.
Tana gama masifarta ta hau mota Driver ya kaita har Airport sai Taraba state can kauyensu zata je wajen bokayenta wanda take ganin kamar malamai ne na Allah ka h.
Bakwa Sharhi fans
AsmaBaffa
[1/15, 8:41 PM] Asmabaffa: ππππ
ππππ
KASUWANCI NA
61-65
Official
By
AsmaBaffa
Page nakine Zainabsanusi78 Allah ya bar kauna.
Godiya da jinjina me tarin yawa TASKAR SURAYYARHMS na gode da Sharhi kuna kokari, haka ake son gp.
Bata zarce ko ina ba sai wani kungurmin kauye wanda mota bata shiga sai dai ka sauka ka hau machine a karasa da kai wata hanyar ma sai dai ka karasa a kafa,wata yar bukkar kara ce kamar ta Fulani, daga kofa Hajja ta tsaya tare da cewa Gafara dai Malam,yace Allah ee Mana Hajiya kece tafe yau? Hajja tace ae Wlh Malam ta furta tare da shiga dan karamin dakin,gefe ta zauna suka gaisa yana ta faman washe baki,tsoho gashi wani mugun kazami bakinsa duk goro yana yauki,hakora Yellow dasu shar in banda wari ba abinda yakeyi, farcensa zako zako kamar na kanti duk dirty a ciki,suma duguzum da wani lalatattun kayansa,yace Hajiya da Alama wata rigima ta taso ko,Hajja tace kwarai kuwa abinda ya kawoni kenan da waya zan maka Amma zuwa da kai yafi Sako, ko ina a dakin wasu litattafan ne na sunayen taurari da Alama taurari yake bautawa dasu yake aikin shirkarsa.
Hajja tace Malam kasan idan aiki babba ne bana bukatar a duba min,bana bukatar a hango min meke akwai dan kar ma naji wata matsala,kawai aiki na kawo cikin Uku ayi daya,wannan takadarin jikan nawa Aayan,kasan yayi aure to matarsa naga tafi karfina irinsa ce bata da kirki,nan take yace ba sai kin karasa ba na san komai, tace to aikin da nake so shine ko Ya saketa har abada kar ta dawo hannunsa,idan bai yuwu ba ya kara aure ta koma baiwa,idan bai yuwu ba ya tsaneta inda take kar ya raba ko ita ta tsaneshi da kanta,Malam ya dago yace me sauki kenan Amma bari muji abinda su zasu ce ayi wato aljanun da yake aiki dasu kenan,littafin taurarinsa ya bude da carbi sai wata kwalabar turare yayi shuru yana kallon littafin sai daΓ kaga bakinsa na motsi yana magana shi kadai yana to..to...ae...yawwa...ae...uhum...uhum..suna bashi Umarni kenan.
Sai da ya gama sannan ya dago yace Hajiya baki taba kawo aiki me wahalar wannan ba,da farko dai sunce jikanki kullum cikin addua yake baza su iya shiga jikinsa ba ko sun shiga wahala zasu sha,na biyu kafin ma su shiga jikin nasa zasu kwashe shekaru suna fakonsa sai ranar da ya shagala da duniya sannan su shiga,ko sun shiga din dole fita zasuyi da kansu, aikin kuma bazai yuwu ba sai dole an shiga jikinsa,sannan ita yarinyar idan an Sa ta bar gidan Jikanku shi zai sha wahala ta dalilinta zai iya rasa ransa ita kanta yarinyar ba a zaune take ba kullum Azkhar take ba fashi,kuma kin san asiri ma yana tadda hali wannan taurin zuciya ce dasu gaba daya idan ma anyi suna da karfin zuciya,amma abu daya za ayi shine a hanasu kwanciyar hankali da zaman lfy idan kin yarda idan kuma kina ganin bai miki ba to fa a wannan lokaci sai daΓ kije wajen wasu duk rashin Imani na wannan yaron yasha kaina,dama kuma nasha fada miki,Hajja ta nisa tace ita yarinyar a batar da ita ko a haukatata mana gaba daya in yaso Shi ya kashe kansa dan ubansa,Malam yayi dariya yace Hajiya har yau kina nan da Halin nan naki na mugunta Amma kije zamuyi iya kokarinmu,ni kuma har India zan kira manyana dole ko ta yaya ne sai an miki abinda kika ce kina so,tunda kin yarda ko mutuwa ma jikan naki yayi baki da damuwa, Nan Hajja tace da dai yafi a dage sosai ta zube masa makudan kudi ta bar wajen,tayi waya da malamai da dama duk akan aikin sannan taje wajen wasu ma sunfi biyar Sabo da a hada karfi da karfe kuma sun bata tabbacin ba matsala.
Makara mukayi don har rana ta fito bamu sani ba muna manne da juna muna bacci,lokacin Meenat har ta hada Breakfast da komai,Maeesha kuwa gyaran gidan ta fara kasancewar yau Ba schl,ni na fara bude ido na da kyar na iya zare jikina cikin nasa sabo da gaba daya ya makalkaleni ta ko ina ko juyi bazan iya ba,wannan ne ya tashe shi daga bacci,muna hada Ido na runtse ido, kawai sabo da kunya,Murmushi ya saki har ina jin sautinsa da sauri na sauka daga Bed din na shige hadaddiyar toilet dinsa nayi Brush da wanka kana na dauro Alwala na fito dan guntun Towel dinsa na daura na fito ina goge gashina,yana Saman Bed ya tsaya sai kallo na yake sannan ya mike shima ya shiga wanka,kafin ya fito na idar da Sallah na shafa Lotion dinsa tare da turarukansa har gashina na gyara shi sosai ina haka naji muryarsa yace kawo min Towel dina ko ki bude Wardrop ki miko min new, wai dan kar a bata kaya da yawa nayi Sauri na dauko Jallabiyarsa fara nasa dan tight short dinsa na Sa Jallabiya ba karamin kyau nayi ba duk da tayi min yawa kowa ya kalleni yasan nayi kyau.
Toilet din na nufa na manta kawai na murda Handle na shige gaba daya da Sauri ya juya min baya yana ta masifa ban kalleshi ko daya ba na fito da gudu nace kayi hakuri mantawa nayi wlh na kara dan tura kofar na dan tura hannu na tare da mika masa ya karba ya zuba su a washing machine sannan yace miko min wasu ki bude part din karshe,da Sauri na bude na dauko tare da kara miko masa ya amsa ya daura sannan ya fito ina dariya nace na gani dai abin tsoro ma, murmushi yayi yace ke kika sani kuma,Wajensa na karasa kawo na tayaka Allah na iya ni nake shirya su Meenat ma fa, na zuba Lotion a hannuna nace to juyo mana ni ko dama wayo zan masa dan na taba masa jiki ne Sabo da yana birgeni,shafa to kiyi kuma Sauri sallah zanyi na fara murza masa Lotion ina ta murmushi dan fatarsa sai laushi kawai,nazo waist dinsa na tsokaneshi Sabo da naga baya so a kalle masa tsaraici nace kwance towel din nayi Sauri mana dariya yayi yace a'a ki kwance da kanki kai.
Ina gamawa yace saura kaya to ya dauko wani Yadi shara shara fari me shegen kyau karamin dinki fitted na Maza yan gayu,da Singlet sai short ya miko min karasa aikinki, na karba kuwa ya dauka zan wani kasa sai ya karbe yasa Boxers dinsa,nasa masa singlet yasa wandon kayan na Sa masa rigar, da Sauri ya gyara sumarsa tare da fesa turaruka ya tayar da Sallah,ni kuma na fita tare da sauka kasa na duba na ga me su Meenat suka dafa idan basuyi ba nayi,tea suka sha da Doya da kwai kawai,sai farfesun kaji,na dinga masifa kun san dai bazan fito da wuri ba dan Iskanci sai kuyi wani Doya kawai da tea mijina yana ci ne? Ba sosai yake ci ba,Meenat tace au bamu birgeki ba a hakan? Ke da kika ce hira zaki je kuyi kawai ki dawo sai yanzu zaki fito duk hirar ce tun jiya? Shike nan bacci bazai kwasheni ba nama kwana din ina ruwanki ke zaki tsara min abinda ya dace nayi kece gaba dani ko nice gaba dake? Daga yau ma acan zan dinga kwana sai me kuma? Dariya Meenat tayi kawai tace ah mun gane, to gyaran gidan fa? Ya kika gani ya miki ko shima mijinki bazai masa kyau ba? Dubawa nayi nace wannan ai nasan kun iya dama kuma na gani kunyi kokari,bari to zo ki tayani muyi masa Kunun Gyada,da su muka shiga kitchen din suka taimaka min Dan danan muka shirya lafiyayyen kunun gyada,na fara soya dankali suka ce sun gaji su nace to kuje ku huta,suna fita sai ga Aayan ya shugo kitchen din a bayana ya tsaya kamar zai shige jikina ina jin kamshinsa a saitin kunne na yayi magana a hankali yunwa nake ji fa ki danyi Sauri,yana fadan haka ya fita ya barni nan ina jin jikina wani iri.
Tunowa nayi da zan fara yanga ta na daina cin abinci a gabansa da yawa Sabo da kar ya rainani gashi kuma bana koshi da wuri sai na shirya dabarata yanzu duk girki sai na samu na zuba a kitchen din in ci abina na koshi sai na rage space kadan idan anzo ci a dining sai aga ina ta yanga naki cin abincin da yawa sai dai na dan ci kadan,
Cikin rashin Sa'a yau nace zan fara tunda tare zamu ci a dining,na zauna na ebi chips din na zuba kunun gyada ta,farfesun kajin dasu Meenat sukayi nan ma na zuba Naja gefe ina cin abina a nutse,Kawai Aayan yazo zai shigo kitchen yaganni kicif ina cin abina,nan take ya gane me zanyi don Allah ya zuba masa basirar gane abu,dariyace ta kamashi me karfi ya danneta,ya juya palo dan kar na ganshi naji kunya.
Saida na koshi sannan na sha ruwa na gyara lips dina na fito na shirya Dining na gyara kitchen din na fito,Aayan yana Dining yana jirana nazo na zuba masa ni kuma na zuba komai dan kadan kamar dan yaro ne zaici irin yar gayun nan, yaga ina ta wani juya cokali a ciki ina tsakura,shiko yana ta cin abinsa har farfesun,ya kalleni yace kici mana wannan dan abincin nufinki zaki ci? So kike ace bana baki abinci ko so kike ki rame? Baki na tabe ina yatsina fuska na ce ya isheni haka,ya kalleni tare da danne dariyarsa yace me yasa kika daina cin abinci ko baki da lfy? Na shagwabe fuska nace ni...yanzu bana son wani ciye ciye da yawa,yace to kiyi hakuri kici kinji yanda ya zage yana ta lallabani sai naci abinci ni kuma ina botsewa haba sai naji wani dadi nace lallai Aayan ya fara sona sosai ji yanda yake ta kula dani yana damuwa sai naci abinci,ni kuwa sai yanga nake wai ni a dole na masa wayo ban san shike min wayon ba.
Kusa dani ya dawo yace Dole sai ya bani da kansa nafi ci na koshi yaga wasa nake da cikina so nake cuta ta kamani,nan take na Tsorata Sabo da na koshi taf cikina ya cika,ina ji ina gani ya zauna ya dinga dura min abinci da kansa,kamar zanyi amai Amma yaki saurara min,Dankali da Kunun gyada ya dinga danna min,ya dawo kan farfesu,tun ina dannewa nace dan Allah na koshi Amma dama Sabo da mugunta ya shirya min yace sai na cinye ya san ina da ci,Idona ya kawo Hawaye na fara kuka ina bashi hakuri Amma yaki yarda sai cusa min yake,sai da naci me uban yawa wanda kwakwaran motsi nayi sai nayi Amai,ya miko min yatsun Sa da ya bani farfesu dasu yace tsotse abinki,haka na tsotse yatsun tas shi kuma yanda nake tsotsar yatsun ne ya tayar masa da hankali nan take ya birkice,Sha'awarsa ta motsa da kyar ya dan danne yace ku shirya da yamma zamu fita zan dawo na daukeku,hararsa nayi nace to ina turo baki akan dura da yayi min.
Ameer dasu Mujaheed ne zaune a katafaren Palonsu suna game suna hira,Mujaheed yace ni fa guys wlh ina son beb din nan kanwar matar Aayan Meenat take ko wa? Khaleel yace ai yarinyar tayi ne ina fada ma gaba dayansu Allah ya zuba baiwa Barin ma matar Aayan gaskiya Ameer Banga laifinka ba,Ameer yayi dariya irin ta yan duniya sannan yace baza ma ku gane ba sai nan gaba,ni na hango abinda na hango,kullum da ita nake kwana nake tashi,Sajeeda dake gefensu taji haushi dan ita Ameer take so yanzu, rai bace tace haba Ya Ameer mene haka wannan cin fuska ne ina wajen fa wlh zan fadawa Abbi kasan dai yace Aure zai mana,Ameer ya kalleta shekeke ke dalla rufe min baki me zaki kaimin gidan nawa? Har daki kike bina muna aikata abubuwa zaki zo kice wani na aureki,Amma kasan dai ai kaine kace ba komai zaka aureni tunda kaine ka lalata ni,Mujaheed yace ko kunya bakwa ji ku rufe mana baki Hajja in ta dawo ku fada mata mana a fasa can da matsalarku,Cousins kenan dama haka akeyi ko mai ace cousin dina ne Kaza Kaza kullum kayi tunanin yan uwan ashe ana nan ana aikata masha'a tare,Mata har gidan kani ko wan babansu zaka ga sun tafi hutu an samu Cousin mace ko namiji ana ta shekewa,su kuma iyaye tunaninsu zumunci akeyi sai suyi ta jin dadi Allah kyauta.
Hajja ce sanye da glass dinta na ido ta zauna a Cikin jikokinta nan Fa Sajeeda tana kuka tace Hajja kinji wai Ameer bazai aureni ba, Hajja ta gyara zama fatarta duk tayi yaushi tace shi din banza,ya Isa ma,shi waye shi wlh wlh Allah daya sai anyi wannan aure kwanan nan ma kuwa ko sama da kasa zata hade,waye kai? Ka Isa nayi magana nasa doka da hukunci ka tsallake ko Ubanka Mustapha bai Isa ba bare kai karamin shege,nan Hajja tayi masa tatas yayi shuru yana ji Amma ya rantse indai Sajeeda ta shiga gidansa sai ya kusa hallakata da muguntarsa ita kuwa Sajeeda murna takeyi don tun da ta taso a duniya take son Ameer sosai Sabo da ya hadu shima ba laifi.
5:30 muka gama shirinmu tsaf mun hadu karshe yau kamar wata Sallah haka muka dau wanka,Aayan kuwa bamu san a inda ya shirya ba haka muka ganshi ya shigo cikin dakakkiyar shadda sea blue yanda yayi kyau ya zarta hankali ma,Maeesha ya kalla yana zuba kamshi yace kinfi kowa kyau yau,nan take naji haushi ni bai yabeni ba ai ni ya dace yace nayi kyau ba su ba,Meenat kuwa yace Yau kamar Queen haka kika koma nan take Meenat ta fara dariya tana tnx Yaya,Ma'eesha kuwa ta makale a jikinsa,ni da yau nafi kowa haduwa yanda nayi kyau har ya wuce misali Amma bai ce nayi kyau ba sai su Meenat,kasa danne fushina nayi sai kumbura nakeyi haka na karasa Sa sarka ta na dauki mayafi na da jaka nace muje Meenat da Ma'eesha suka yi waje ni kuma zan fito yana Bedroom din namu ya jawo hannuna na fisge abina,ya kara jawoni na fado jikinsa gaba daya,na sadda kaina kasa a saitin kirjinsa,hannaye biyu yasa ya dago da fuskata yana kallon lips dina tare da cewa wa kika sawa jambaki kuma? Nace masu sona na cikin gari idan mun fita nake Sa ran zasu kalla suji dadi, bakin ciki ne ya ziyarce shi me tsanani Amma sai ya danne ya hade bakina da nashi ya dinga sha,sai da ya shanye jambakin tas sannan ya dauki wipes a saman mudubi na dinga tsalle ina son guduwa amma ya rikeni tam da kansa ya goge min fuska tas ba abinda ya bari na kwalliya ta,hakan ma yaga baiyi ba sai ya jani toilet fuska ba walwala ya danna kaina a saman sink yasa soap ya wanke min fuskar tas ya goge min da towel nayi wani mugun Fresh jajayan lips dina suka fito natural sai na kara wani kyau kowa yasan Natural kyau na gaske nayi,ga kayan sun hau jikina,dankwalin dana kafa kamar gogoro ya zame ya jefa shi saman Bed ya dauki Hijab ya sa min duk da haka nayi kyau sosai sai ya cire Hijab din ma tare da cewa baki da kyau sam sam Bazan iya fita dake ba bari muje da kyawawana su Meenat,dama haushinshi nakeji ya bata min kwalliya kuma baice ina da kyau ba yanzu kuma wai ya fasa zuwa dani,ban san sanda na fashe da kuka ba me karfi, ba shiri yace taso taso mene haka wannan uban kuka zaki fasa min kunne,gyalena na dauka ina share Hawaye yace Sa Hijab na kara sakin kuka yace to yafa gyalen haka muje wannan masifa haka,ina dariya na yafa haka nabi bayansa,sai da na kara tsayawa a bayansa na zaro Powder a jakata muna tafiya bai San ina ta shafawa ba,na gama nasa jambakina red,kafin mu karasa mota har na gyara ribbom din gashina nayi acuci sosai na gyara mayafin aiko na dau kyau kowa ya ganni yaga yar gayu,nasa glass dina dan Brown nayi kyau ba a magana,yana juyowa sai da ya firgita kamar aljana kafin aje mota har na sake kwalliya yace zanyi maganinki a ransa tunda bakya jin magana dai dai nake dake.
Gaba na shiga Meenat da Ma'eesha suna baya shike Driving yau,katafaren store muka tsaya Meenat sai jin dadi muke muma mun Zama yan gayu,sabo da neman suna sai da na karasa tare da rike Hannunsa muka jera sabo da naga Yan mata sai shige da fice suke a wajen ko wacce ta Sha wanka, hannuna ya rike yana murzasu muna tafiya duk inda muka keta sai an kallemu,Kayan sawa iri iri yace mu zaba,dana tashi sabo da tausayin kudi abinka da ba a saba ba kawai sai na zabo atamfofi dasu laces materials dasu Ready made duk ba na sama da Dubu biyar daka biyar sai kasa,gani nake na gama kure karyar kudi, yana duba kudin yace a maida su wannan ai wanke kudinka ne Hajiya,da kansa ya dinga jidar mana kaya masu matukar tsadar gaske komai latest,haka takalma ma,bags ma ba a magana,har su cosmetics yana zabo me tsada muma muna daukan wanda muke so,har jewelries, muka je bangaren Inner wears yace su Meenat su zabi nasu aiko suka jida masu kyau iri iri,ya jani wani bangaren can daban na inner wears yace zabi size naki naga ko Bra kuwa kina sawa? kullum daga an dage miki riga direct ake tafiya can,Kunya naji na rufe ido nace Ina sawa mana amma a boye nake sawa na wanke a boye bana so ace kamata ina sa Bra,to mene a ciki dan kinsa yaja tsaki tare da cewa anya kuwa jinin birni ce ke? Nace a'a daga garinku nazo murmushi ya saki sannan yace mu bamu da dangi a Rimin Gado mu gaba da baya dan birni ne ni,muna ta Zaba iri iri masu kyau ya dauko min wata yar karama yace ga wata me kyau,Hararar wasa na masa nace kaima kasan sunfi haka wuce nan sai kace yarinya,muna dariya sai ga wata yar gayu tana kwas kwas da takalmi ga kamshi tana zubawa muryarta muka ji tace Aayan kaine a nan we finally meet here ohh,Dagowa yayi tare da zuba mata idonsa me matukar kyau ya danyi murmushi kadan sannan yace Sameera kece How u?longest time,tace am great ina ta so mu hadu wlh amma ba dama tun aurenka na farko fa gaskiya mun dade.
Wani kishi da bacin rai ya taso min na bata rai nayi kicin kicin na tashi hankalina gaba daya ina Harare harare,itace second wife din naka? Ina Yarima yana dariya yace yana lfy yar duniya kin buya amma dai kin sake aure yanzu ko? a'a aure ai sai na huta ina aiki ina samun kudina matsalar maza ta isheni baku da kirki Sam ni sai na huta zan yi Insha'allah,Jin bata da aure yasa na kara fusata na daure fuska na dawo gaban Aayan na juya bayana tare da kwantar da jikina a jikinsa muna facing juna da Sameera sai kallon Banza nake mata,Hannunsa na jawo guda biyun na sakalosu ta kafaduna ina wasa da yatsunsa,Murmushi Sameera tayi tare da cewa am sorry to say Aayan kasan bana boye abinda ke raina amma wannan tayi maka yarinya da yawa Aayan kamarka da auren kamar wannan da gani ma baza ta wuce 15yrs ba,ga mata a gari zunduma zunduma da ka fada mana ai da mun zabo maka manyan yara amma irin wannan ai kuruciya zaka sha baza kaji dadinsu ba.
Dariya sukayi gaba daya tare da wani tafawa abinda ya bani haushi kenan ya kara kuleni mene nasa na tafawa da mace,nan take naga fa ta fada min baka zata barni da takaici ban san sanda nace uhm Allah sarki kuma a hakan bashi da kamata dan ina masa abinda Babba bata isa tayi masa ba,tunda tsab nake daukeshi wanda nasan ko uwarki yafi karfin.....kafin na karasa yasa tafin hannunsa ya rufe min baki da karfi dan yasan sai na karasa ko za a mutu sai na rama,ina so na kwace baki na amma yaki Sakina ya toshe min da tafin hannunsa yana fada min a kunne kina magana wlh yau na lahira sai ya fiki jin dadi bakya jin magana ko ke ba a isa an miki abu kin hakura ba sai kice sai kin rama wannan wacce magana ce ta marasa kunya uwarta fa kika ce,Sameera ta kalleni sosai tace da Sameera kike zance yarinya zaki san kin zagi uwata,wlh sai kin San wa kika cewa haka,Allah ya taimakeki yanzu Kinci darajar Mijinki amma a sannu zan goge miki abinda ke kanki,Bakina na kwace nace Ba Sameera ba Allah yasa kece Sameeran Gayaπ€£ wlh nafi karfinki kina magana kina cijewa ke ga yar daba karewar Daba munga Amana ta Alim maπ Sameera dama irin Masu takama da yan daba ne har yara ne da ita yan daba,bata da kunya duk abinda taga dama haka zata fadawa mutum shi yasa ko zaman aure bata iya yi,sabo da ko yaushe a shirin daba take kana mata zata sa yara yan daba suyi ma kaca kaca tana takama da kudi sabo da ubanta ita kadai ya haifa ya rasu ya bar mata dukiya me tarin yawa,Tun kafin ya mutu ya raba gado yaba yan uwansa ya barwa yarsa komai,shi yasa take abinda taga dama,kuma bata San mutunci ba duk inda take da kai zata iya ci ma mutunci ta ko wanne hanya,Aayan kuwa Business ne ya hadasu tsakanin Company nata da nasa tun da dadewa.
Ni kuwa nace komai dabancinki baza ki bude min ido ba kiyi duk abinda zakiyi nima baki San ko ni wace ba shi yasa har kike magana dani haka ina kyaleki,ki Bari watarana Business ya hadamu anan zaki gane true color dina,Tsaki taja ta bar wajen a fusace,Aayan yana ta kallon yanda nake tsiwa yar ficika dani gaban sangamemiya irin Sameera ko tsoro bana ji,na kalleshi nace girma ya fadi wlh ka ba dani ina ma kallon Ustaz har wani hannu kake hadawa da yan tasha,da gani wannan yar tasha ce gaka da fyallelliyar budurwa me zaka ji a hannun wannan me suffar mazan, kayi dacen mata amma baka godewa Allah kana wani rikewa wata hannu bayan ga hannun da zaka samu lada Allah kyauta ka daina irin wannan a gabana dan wlh ni bazan dauki a wulakantani ba dan baka darajani ba Sam,ka zubar min da mutunci ace Namiji yana da kamata yana rike hannun wata banza,wannan babban matsalace dole na tuntubi kaina Ashe ma ban kai mace ba.
Yana jina ina ta masifa kamar uwarsa yana dariya a ransa,yace to yi hakuri masifaffiya tunda bakya so na daina,wai nice budurwa shi baya daukana a budurwa Sam,yace wai ke nan budurwa ce? Bacin rai ya kamani sai na danne a fili nace a'a kwaila ce,a na dinga masa masifa ina zan rama zaka San ba budurwa bace ni daga yau na Canja salo again na fasa wannan Business din da mukace za muyi wani zanyi daban sai na sa kayi nadama har ni za a wulakanta dan anga ina biyayya ina cusa kaina ina kokari naga an zauna lfy shike nan za a gani,dariya yayi yace a'a dan Allah tsokanarki nakeyi fa muyi Business dinmu zan biya kudin,nace anki din sai na rama nima.
Mun gama siyayyar komai yasa aka kai boot din mota ya biya muka fito kenan sai ga Ameer da Khaleel tare da wasu yan mata masu suffar karuwai sai chewgum suke taunawa su a dole manyan yara,na kalli Aayan na bata rai nace kalli Meenat a gabanmu tsaya kaga abinda sukeyi kalli,ya kuwa kalla sosai ni kuwa wai dan kar ya kalli yan mata nayi masa wayo,Muna zuwa Ameer sai kallona yakeyi zasu shiga mu kuma zamu fito na bi ta tsakiyar yan matan nan a hankali yanda zasu ji nace yan iska sun dauko yan iska su a dole yan mata ana yaye baki a titi na wuce fit na koma kusa da Aayan,Khaleel ya fusata kwarai da maganata haka yan matan ma,Ameer kuwa so yasa baya ganin laifina sai dai ma birgeshi da nakeyi aransa ma cewa yayi wannan gaskiya kika fada Mufeedata tabbas yan iska ne suka dauko yan iska Allah ya baki basira tare da saurin ganewaπ€£
Yan matan zasu zageni Ameer yace wlh duk wacce ta fadi ko bakar magana a kaina sai ya mata illa har fada suka so yi da Khaleel..
Muna shiga mota na tuna zanyi girki kuma kayan miyarmu ya kare nace Aayan kayan miya na manta,Yace to mu koma store din nace a'a danyi gaba wajen yar kasuwar can zamu samu.
Muna zuwa yayi parking nace sai ya fito munje tare,yace a'a nifa ban taba siyan abu a kasuwa ko gefen hanya ba a store nake siya,Na fara rokonsa dole haka ya fito muka karasa wajensu,sabo da tattalina da son kudi nace Malam kwano nawa nawa? Aayan yace nidai a zuba kawai mu tafi,nace a'a so kake ayi mana tsada bazai yuwu ba yo ni akan barkono kwano daya idan nazo sarowa Basai na yini a wajen ba ana ciniki ba kuma karshe kaga na siya arahar banza,Dariya Aayan yayi yace yini guda fa? Nace Cass ma kuwa, Agogon Dubu biyu ina siyoshi a Dari biyu da hamsim ni highest Dari biyar zan siyi shege,ka dinga zuwa dani siyayya kaga araha,Aayan kallona kawai yake yana dariya,Nace kai me kayan miya kwanon tattasan ne dari biyar a garin gaba gaba muke da zan siya haka,yace gaskiyar magana Dari hudu da hamsim baya tsada bana nawa kike so a siyar miki,Nace to ka rage,nafa San kan kasuwar nan,Aayan yace Haba Ke kuwa har kwano guda Dari hudu da hamsim kacal a kasa siya mene na tsada a nan? Harara na watsa masa tare da dan zungurinsa nayi masa magana a hankali bana son haka ba a yiwa yan kasuwa haka,zaka kashe min ciniki idan kasan haka zaka min ka koma mota yanzu duk ragi ai ragi ne,Aayan yace Malam zuba mana kwano biyar ga kudin ya zaro kudi ya mika,na fara rigima na cumimiye a jikinsa baza a biya ba kwano har Dari biyar gwara Ku tafi gida ni Ku barni a nan nayi cinikin ko Dari hudu na siya sai na samu Dari Dari ta Zama tawa,na dawo a taxi, ko kulani baiyi ba yace to tumatir fa,nace a tsaya ni zan Zaba da kaina,me kayan miya yana ta dariya yace kudi kudi ne ga gwalagwaje wanda ya gama lugwiguwicewa daf yake da rubewa kudinsa daban,ga masu kyau manya da kanana,nayi layin marar kyau gwalagwajen nace duk tumatir tumatir ne tunda dafashi za ayi mu sharbe miya Malam ga me sauki ba sai anyi asarar kudin ba a bamu wannan,Aayan dariya ta kamashi ta gaske ya dinga yi yace wlh baki isa ba gwara da Allah ya kawoni na gani dama abinda kike sawa muna ci kenan? Nace to sau nawa ka shanye miyar sa kana Santi ai ni in kaga lafiyayyan tumatir a fridge to na cin salat ne,ai ko harda kwalla Aayan yake dariya ni kuwa ko a jikina,yace Allah na gode ma da na gani da Ido na shi yasa Ashe ba kya yarda a bawa kowa yayi cefane sai ke Ashe Guba kike bamu muna ci.
Aayan yace Malam me kyau wanda yafi kowanne tsada zaka zuba, na hangame baki ina jimami shike nan za a ci kudinmu a banza,akan dan tumatir har yan Dubu Dubu na fitowa naji kamar na fisge kudin,na bata rai ina ta fushi nace ai gwara ni ka bani na dinga tara ma kudin watarana sai mu dakko a siyi abu me amfani dasu amma wlh wannan Almubazzaranci ne, mukaje layin Albasa nan ma dan yaga yanda zanyi yace zabi da hannunki one by one ki dinga zubawa a ledar mu gani,me Albasa yace ai kwano kwano muke saida wa,Aayan yace bari ta Zaba sai a auna zan biya ko nawa ne,aiko na fara Zaba sai na duba wacce ta tsage ko ta kusa lalacewa ko marar kyau sai na dauka na nunawa me kayan miya nace kaga dai wannan araha zata yi ehe,wannan ma ba me tsada bace,Aayan yana murmushi yace pick the nice one mana,na kai hannuna kan me kyau sai na koma na faki idonsa na jefa marar kyan a leda yana kallona yana dariya har na gama sannan yace to Malam juye wacce ta bari bata Zaba ba su zamu siya,haka aka auna ina gani kamar na fashe sabo da ni kudin da aka kashe kawai nake jin haushi da an tattala su ai sai a moresu watarana Rayuwar Manage na iya a haka na taso da ita na saba.
Na dauko shima ya dauki wasu muka zuba a mota ina ta harararsa yana kallona ta gefen Ido yace daga yau tsinke baza ki kara siyowa da kanki ba da kaina zan siyo ko na bayar a siyo,nace girkin ma ba sai kayi abinka ba,wlh ya kamata ka koyi adani sabo da rayuwa ni gaskiya nake fada ma.Maeesha dama suna gani sun San halina sun San yanda nakeyi a kasuwa dariya suma sukeyi Meenat tace Yaya Aayan ya kaga mutuniyar taka ta iya Zabe ko?
Dama kadan yake jira ya dinga dariya yace ai naga Zahiri yau Meenat,haka takeyi ko a gida Ammah ta dinga ta mata fada amma baza ta ji ba cewar Ma'eesha.
Meenat tace ai baka San abin haushi bama shi yasa bama Rakata kasuwa watarana akan egusi da zamu siya wlh sai da muka yini a table din me egusi har fada sukayi ya koremu gaba daya,kai ai kadan ka sani, turmi ma ba a cin arziki a gidanmu ko daka wasu sukayi a ciki sai ka biya ashirin, haka gugan Rijiya ma ko kurar Ciro guga duk na haya ne hhhhh Aayan ya dinga dariya Meenat suna ta bashi labari suna min dariya,sai da na saki Kuka sannan sukayi shuru.
Haka ma Ya Aayan watarana ta siyo min jakar makaranta me kyau ina ta murna wata kawarta Nawwara tace gaskiya jakar tayi kyau nima zan siyo aiko Mufee na jin haka tace Dari uku na siyo ta bani Uku da hamsim na siyar miki,ina kuka haka ta siyar da jakar nan taci ribar Hamsim,Aayan yana driving yana dariya.
Malamin Hajja ya hado mata muggunan da za a sa min tare da Aayan a abinci,da sauran wasu iri iri na wajen Malamai shi yasa yanzu ta saka rigima wai Daddy ya fadawa Aayan a dawo damu ai muma jikokinta ne taga abinda tayi bai dace ba bata kyauta ba
Daddy yasan ba gaskiya bane amma yasan Allah na nan ba matsala ya Sanarwa Aayan.
AsmaBaffa
[1/16, 5:51 PM] Asmabaffa: ππππ
ππππ
KASUWANCI NA
66-70
Official
By
AsmaBaffa
JANNAT wannan page naki ne.
Godiya gareku House of Hausa Noveld kun iya Sharhi.
Bayan yayi parking a cikin gidan fitowa mukayi tare da jidar kayan muna kaiwa muna dawowa har muka kwashe komai ya rufe motar take away na abinci da ya siya mana na karba ina ta masa godiya da addua ya wuce abinsa nima na shiga Bedroom dinmu, Bayan munci mun koshi wanka nayi na shirya cikin sabuwar Nighty dina iya cinya me siririn hannu peach color na fito fes ina kamshi Meent ce ta shigo Sis kije inji Ya Aayan amma fa yana compound jikin motarsa da alama fita zaiyi,Hijab nasa har kasa kamar zai ja kasa na fita lokacin tuni munyi sallar Isha,saman Motar na ganshi a zaune cikin kana nan kaya ba karamin kyau yayi ba,wani abu ya tsirga min na tsinci kaina cikin wani yanayi na shauki wanda bazai misaltu ba wani dadi yana ratsani, kallona yake cike da tsantsan nishadi kwance a fuskarsa zuciyarsa cike take da farin ciki wani Sanyi na ratsashi.
Ina murmushi na karasa tare da cewa au akace fita zakayi kuma naga ka zauna saman bayan mota,yana murmushi yace zance fa nazo kinyi sabon saurayi kuma kina wani cewa fita dariya nayi nace kaima dai baka rabo da tsokana a haka zubin mugaye gareka, am serious ni fa zance nazo dama gori kike min kece kullum kike zuwa zance,Dariya nayi nace to nan gaba idan zaka zo ka dinga bugo waya sabo da ai banyi kwalliyar zuwa wajen saurayi ba na fada kamar gaske, muryarsa naji yace duk fa cikin business ne ki daina tunanin da gaske ne kudi za a biya ki wannan fitowar ma da kikayi kin ci kudade masu yawa,dadi ya kamani nace an gama ko kalma daya ce duk kudi ne? Yace of course, murmushi nayi tare da gyara tsaiwata yana sama na matsa jikin kafafunsa, yace yan mata suna na Aayan duk da cewa baki tambaya ba,ban san lokacin dana fara dariya ba ni abin ma kunya ya bani amma na daure nace ai yanzu gashi ka fada, yaci gaba da tunda na ganki kika shiga raina naji bazan iya bari ki wuce ba batare da na miko Kokon Barata ba gareki, uhmm nace tare da tunani sannan nace kasan me ni ban iya so farar daya ba dole sai mun zauna da mutum idan naga halayensa sun min sai na yarda amma yanzu bazan amince ba, sama naji yayi dani ya daudarani saman motar nima kusa dashi jikinmu na gugan juna,baki na bude tare da cewa wannan saurayine ko dan Shan minti ne kawai,dariya yayi ai an daura mana aure da Budurwar kawai bata sona ne shine nake zuwa zance sabo da na lallabata.
Murmushi nayi nace to naji game din tayi kyau back to our business nawa na samu? Yace ai Dari biyar kika samu sabo da kin kasa magana baki fadi kalamai masu sanyi ba taya zaki samu kudi.
Masu Zafi zan fada yanzu ma kuwa na irin fuske ba wasa nace look in to my eye aiko ya kalla da mayun idonsa I was kidding u but u I knew I love u,i wish I can show u how much I love u,i care for u,my heart is full wth ur love my Prince, yana murmushi yace proof what u have just said, nan take da gaske nakeyin kalamai na ni, bana karya bane amma a boye a raina nace na samu Damar jin dadi na sai na fake da kudin,a fili kuwa sai na ce ka tabbata zan samu kudin nan da yawa,kai ya daga min tare da kara matsowa jikina sosai yatsunsa ya sarke da nawa tare da jawo ni jikinsa, hannayena na sakalo ta wuyansa a hankali na rungumeshi a jikina sannan na dago kaina tare da shigar da bakina cikin nasa ya fara tsotsa kamar ba gobe, tunawa nayi ko yan aiki na zirga zirga a wurin nace yan aiki fa?yace ai basa kwana a nan gidan da safe suke zuwa nemi kudinki na Business yarinya,dariya nayi a raina nace Ina ta masa wayo ya kasa ganewa,nace ni dai mu koma bedroom,lallai kudi zaki nemo da yawa karfa ki karar min da dukiyata,ina dariya nace hau dani baya wannan ni zan baka kudin cikin nawa ka cire Dubu guda,baki isa ba sai dai na daukeki,nace ni dai baya nake son hawa,ko baka da karfi ne? Hannu yasa ya daga ni sama sosai kamar ya dauki tsinke ya dauri a kafadarsa naga ya mai Dani bayansa kamar yar jaririya,nace kai karfinka yayi yawa amma a haka dan Lange Lange da kai, murmushi yake har bedroom dinsa karki cire Hijab din, why? Zaki gani ya furta yana dorani saman bed sannan yazo ya daga hijab din tare da shigewa ciki,dariya nayi yanda yake min abubuwa a ciki don tuni ya zare min rigata tare da kashe light, gaba daya ya gama haukatani ni kaina abinda nake masa ba a cikin hankalina nakeyi ba, ba komai a jikinmu haka muke murzar juna, kalamai yake sabo da sucking na fara masa ko gidan ubanwa na koya oho wannan abu kamar da Aljanu sai kaji ka iya kaimaπ€£
Kukan dadi yakeyi yana zazzagar da kalamai amma ni bana yarda kawai dama na karya ne tunda nasan Business yace ayi,nice nakeyi da gaske a raina, boobs dina yake murzawa har shidewa nakeyi,kiss kuwa yau ina jin sai lips da tongue dina sun kumbura maybe dan sun tsotse a wajensa,yau wani abin mamaki sai ga Aayan yayi releasing sosai abinda Bai taba yi ba tunda yayi aure sai dai a mafarki, bai taba tunanin zaiyi ba Sam shi yasa ma bai yi tunanin sexing dina ba Sam, ya dinga bakin ciki yana jin haushi yace ya zubar da yaransa a banza,za a wankesu a ruwa,na dinga dariya nace yanzu haka ma yan biyu ne ko yan uku ma,ya kara Jin haushi yana kwance gefe,na ce yanzu haka akwai me Sunan Mommynka a ciki ko me Sunan Daddy, dariya yayi tare da cewa wlh ba a wanke Daddyna ba ai Me sunan Daddy yana nan zuwa nan gaba bakiyi abinda zai fito ba,sai Abbansa yaji dadi da yawan gaske sannan me Sunan Daddy zai yo waje,haka kace ko? Ya jawoni jikinsa tare da cewa tnx Baby kinci kudi me yawa yau mota sabuwa dal da dalleliyar waya me tsada kika samu,ni haushi ma ya bani maimakon murna bai San dadin dana ke ji ba na faranta masa burina na ganshi cikin Jin dadi amma shi tunani yake ma dan kudi nayi ni Sam yanzu ba kudin bane a gaba na ba so nake ya so ni kawai.
Shuru yaga nayi bana murna kamar baya can,ko sunyi kadan a kara miki? Nace a'a na gode hakanma sun isa,murmushi yayi yana kallon yanayi na,nayi miki kema kiji dadi? Jin dadine yasa nayi murmushi nace ae,ya fara gwangwajeni da salonsa nima saida na ji zam zam,garin kuma sani naji dadi shima ya sake dawowa ruwa nan na kara masa abubuwan da kawai ya kara kawowa,kamar yayi kuka sabo da takaici yace next time kawai Sex zaiyi shi kam,ina ta tsokanarsa har bacci ya kwashe mu,tun daga Ranar kuma ko me zamu yi bai kara kawowa ba,dama kuma baice ma zaiyi xxx din ba.
Ameer kullum shi yana wajen Hajja sabo da sun shaku sosai duk wani plan din ta ya sani,duk bai damu ba dadi ma yakeji shi za a sa Aayan ya sakeni,kawai sai yaji Hajja tana cewa za a sa min ciwon hauka ko kuma wata cuta ko wacce za a rabani da gidan su Aayan gaba daya,nan hankalin Ameer ya tashi ya za ayi a haukata masa Mufeedansa,shi da yake so ya Aureni yana kauna ta baya kaunar abinda zai cutar dani ko ya ganni cikin wani Hali,nan take yace dole na dau mataki kan Hajja na hanata aikata abinda take niyya,nan ya dinga sawa Hajja ido har ya gano magungun nan data ajiye tana jira na dawo ta aikata abinda bokayen suka ce mata,Ameer murna ta kamashi ya kwashesu gaba daya harda wata yar tukunya da wani ruwa a ciki,ya zubar da ruwan a tsorace,ya fasa tukunyar,garin maganin da ruwan rubutu duk ya samu jikin katangar gidan ya haka rami me zurfi jikin flowers yanda baza a gane ba ya zuba rubutun ciki garin maganin ya juye su daga ledar a cikin rami sannan ya maida kasar ya binne su sosai yanda ba za a gane ba ya kwashe ledojin ya zuba cikin Dustbin.
Bayan kwana biyu Hajja ta duba taga ba komai,kamar me ciwon hauka haka ta fito tana ihu da masifa,ta tambayi kowa amma ba wanda yace ya gani,Ameer kuwa dama tasan na wajenta ne bazai ma dauka ba sai dai ya goya mata baya shi yasa dashi ake tambayar yan gidan yana masifa kamar gaske,Hajja ana sa masa albarka ga wanda ya gajeta,haka a gaban Ameer ta kara buga waya wasu malaman sunce baza su sake samun irinsa ba bare su bata,wasu kuma sunce ta koma ta karba,Ameer ya makale mata tace ai shi zai kaita ma su karbo,kafin su tafi ya tara yan iska ya biya su kudi kan a tare motarsu su kwace jakar Hajja kudin dake ciki nasu ne masu aiki sauran maganin da suka samu kuma su bashi a hannunsa zai nemesu,haka suka tafi gari gari har wanda a jirgi sukaje daga nan suka je na kauyukan kano duk suna jakar Hajja tana murna,Ameer yana Driving tana gaban mota suna ta hira tana fada masa tsare tsarenta wanda zata shiryawa Mufeeda,suna tafiya hanyar daji daji ba kowa sai ga yaran Ameer sun tare motarsu kamar gaske suka kwantar da Ameer a kasa Hajja kuma suka kwace jakarta tana rokonsu suna ganin makudan kudin da suke ciki suka dinga murna suna godewa Ameer a Ransu,suka kwashe kudin tas,magungunan kuma sukace wato gidan bokaye kuke zuwa ko? Kune masu hana mutane Zama lfy a duniya Allah ya tonaki tsohuwar banza ke da jikanki yau karshenku yazo,Hajja ta fara magiya tana rokon kar a taba mata jika sabo da tana son Ameer sosai ita tun asali tafi kaunar Ameer da kowa,Ameer ya kifta musu ido su kyaleta haka su kwashe komai su tafi,ai kuwa suka kwashe komai suka jefawa Hajja jakarta,Ameer ya tuna da rubutu jarka har biyu a gaban mota yana sani yace Hajja maganin sun kwashe Allah yasa muna da biyu a gaban mota,kamar gaske suka take mishi wuya sukace au harda wasu a mota kuka boye Allah ya Toni asirinka dauko mana su ko mu fedeka,Ameer ya tashi yana kunshe dariyarsa ya ebo yana kuyi hakuri gashi kuje dan Allah,sai dai suka kaiwa Hajja masga daya sannan suka kara gaba.
Hajja jiki na rawa tana kyarma a firgice tace Allah ya isanmu kaga shegun yara wannan turosu akayi,Ameer yace sannu Sannu Hajja ta Allah ya saka mana muje muyi mu bar nan kar su dawo ko wasu kalar suzo su harbemu,Hajja tace iceko baka ji rauni ba Ameer dina naga sun take ma wuya,ai munyi arziki da basu taba min kai ba,yana Driving Hajja tace yanzu me zan cewa malaman nan? da wanne baki zance an kara sacewa? Ameer a ransa yace kai Allah yayi muguwa a nan wajen sai son kai amma bata son Mufeedata,a fili yace shawara ta ki Bari sai an kwashe kamar wata daya ko biyu ki koma muce mun aikata baiyi aiki ba Sam bamu ga canjin komai ba sai su bamu wasu kalar kinga me zafin ma zasuyi mana tunda sunji wannan baiyi ba,Hajja taji dadi tana dariya ta balli goronta tace hakane Jikana shi yasa nake sonka akwai dabara amma idan suka ce sun San karya ne fa?,kasan fa duba sukeyi sun San komai,Murmushi Ameer yayi yace karya ne Hajja ba wanda yasan gaibu duk raina muku hankali sukeyi idan kina so ki san karya ne kije da jakarki ba komai a ciki kice ya duba miki mene a ciki idan ya fada ki bude wlh bazai San mene ciki ba wani abin ma da zaki ji sun fada Aljanu ke fada musu wani karya wani gaskiya amma sai ku dinga yarda,ai kamar Hajja zata daki Ameer ya karyata malamanta tace Wannan sabo kakeyi Ameer malamai magada Annabawa kake fadawa suna karya,Ameer ya dinga dariyar Jahilci n Hajja dan sunyi Islamiyya sun San komai,amma ganin baza ta gane ba kawai ya canja zancen ya kyaleta,ita ko sai masifa take masa,har ya gaji yace Hajja ke dai baza ki gane karyar mutanen ba a hadisi aka rawaitosu ko a Alqurani?, Salati Hajja ta saki tace yau naji dan iskan yaro to yi min Wa'azi Allah ya taimakeka kaine da Mujaheed ne ko Khaleel wlh yau da basu kwana a gidan mu ba,ka kiyayeni rakani kayi ba Wa'azi nace kazo ka min ba,kai din abin arziki kake aikatawa? Wanne iskanci ne baka yi,ai ni nasan wlh ba dan iska bane tunda ni bana bin mata duk a baki kike ji ina surutuna ko kin ganni da mata wlh ni ba zina nake ba,ban taba yi ba,ko kinji nace Ina son mace wlh da aure nake sonta ni bada iskanci ba,bana fata na ajiye mace don kawai naji dadi da ita sai dan na aureta gaba daya har karshen rayuwata,Hajja tace Sajeeda fa ai tace ba abinda bakayi da ita ba? Wlh sharri ta min don na aureta amma ni ban lalata mata rayuwa ba kuje asibiti a dubata,idan ma an ganta a lalace to wlh Allah wani ne ba ni ba,ke kin San ni ba irin Khaleel bane ko Mujaheed wanda basa fada sai dai aga sun aikata sune masu son ayi fasikanci da mata, Hajja tace uhm naga Alama ai nasan halinka Ameer kai dai a barka da masifa ga kawo shawara wajen iya hada tuggu,to amma mene hadinka da mata tunda gashi duk inda za a ganku da mata kuma Sajeeda nima ai ina ganinta a dakinka,Hajja kenan kina son Gulma,zan ci ubanka wlh karka kawo min raini,ayi hakuri Hajja mata da kika gani Allah daya dan rage Zafi nake dasu ina dan tabe tabe a jikinsu idan na danji sai na kyalesu,Sajeeda kuwa har room take Bina na kwanta da ita naki yarda,tace na aureta naki shine take talla da kanta ganinta hakan ne zai sa na sota ni kuwa kara tsanarta ma nayi wlh ba wacce na tsana sama da ita,kuma ban aikata komai da ita ba sharri take min,Hajja dan Allah kar a aura min ita wlh zan iya mutuwa,banza Hajja tayi dashi sai daga baya tace amma kasan tana sonka,ae amma ai badan Allah take so na ba cewa fa tayi don duk gidan nan ni kadai nake kama da Yaya Aayan daga Aayan sai ni a kyau na yan gidan nan shine fa dalilinta dama nasan Aayan take so ba ni ba,ba sai ku aurawa Aayan ya kara ta biyu da ita ba,Hajja tace halina da kai basira haka za ayi aure za a kara masa ta nan zamu samu Damar wulakanta Mufeeda,Ameer najin haka yace ai kuwa bazan bari a aura masa Sajeedar ba tunda za a taba min lafiyar Mufeedansa ta nan za a dinga kai maganin bokaye,wa ya sani ma ko Sajeeda ta dinga dukan Mufee dinsa kullum ina Sam da sake bazai yuwu ba dole ya canjawa Hajja shawara amma sai ya nutsu ya samo dabara.
Washe gari naje schl na dawo wanka nayi na shirya cikin wando pencil brown riga Maroon na gyara gashina kamar wata Baturiya ba karamin kyau nayi ba, zaune nake a kujerar dake kitchen ina yanka cabbage, kamshin Aayan naji kafin na juyo naji ya tsaya a bayana tare da dafa kafaduna da hannu biyu a hankali yayi Sallama na amsa tare da mikewa tsaye nace sannu da zuwa, na kwanta a jikinsa ba tare da na tallabeshi da hannayena ba sabo da akwai cabbage a jiki,kallona yakeyi sosai yanda nayi kyau amma Bai ce nayi kyau ba,lemon Fruits dana hada yayi Sanyi na tsiyaya masa a glass cup na mika masa ya karba ya shanye na karbi Cup din shi kuma ya bar kitchen din ya haura samansa,na dan Dade a tsaye ina tunanin ko lfy? Dan naga kamar yana cikin bacin rai amma ya zan masa tunda baya iya fada min matsalarsa sabo da ba sona yake ba nice dai nake wahalar da kaina a raina nace wlh bazan iya ba kaje kayi ta fushinka da kaina kuma nayi wa kaina fada ni da nake so ya soni back kuma in Zama jigon rayuwarsa na tsaya wasa gwara idan na sace masa zuciya sai na shareshi yanda zaita wahala a kaina yessss na fada da karfi wlh haka za ayi yanzu bari na kwantar da kaina first yanda Meenat tace nan ma da karfi nace shegiya Meenat yarinya da fusaha,da sauri na ajiye aikin da nake na wanke hannuna na bishi samansa sabo da irin su Aayan son girma garesu suna bukatar biyayya sosai.
Ina shiga na iske wanka yake sabo da na sanshi ya sanni don ba kaya ma muna romancing juna me yayi Saura kuma kawai Toilet din na Murda handle din sannan nace na shigo,shigo mana kinga na huta ma,Shiga nayi da towel a jikinsa ya shafa shaving cream a kirjinsa zai fara aski, na karbi a bar askin na jawo masa wata doguwar kujera ya zauna nace aske gashin kirjin zakayi harda shi gaba daya? yana kallon shiga ta wacce tayi matukar yi masa kyau yace kinyi kyau idonsa har ya canja nace tnx amma yanzu har kirjin zan aske? Kina so ne? Hmm in ina so ma ai baza ka barshi ba tunda baya cikin Business dinmu, murmushi ya saki yace sai a zame wasu kudin cikin naki tunda ke kike so kece zaki biyani kudin ajiye miki shi,kuma yana da tsada kin sani,nace a'a karka taba min kudi aske abinka na hakura,in kina so zan bar miki kyauta,to ina so a bar min,hanci ya lakace min Hajiyar kudi kenan,dariya nayi nace to an fasa askin ai sai kazo ayi wankan,jansa nayi yace ai baki isa ba yarinya sai dai ki tube muyi tare amma baza ki min wanka ki kalleni ba bazan yarda ba sai dai ayi 50-50,Dariya nayi nace a'a to mene na jin kunyata abinda nasan komai na kai hannu zan janye Towel din ya ja gefe da sauri tare da Jana ya tura ni bedroom ya kulle kofar yace je ki kawo min abinci kafin na fito,lallai Aayan yana da kunya wasu mazan kuwa ba ruwansu amma shi ya sanni na sanshi amma kunyar na kalleshi yake.
Kafin ya fito na shirya masa komai a dakinsa ina zaman jiransa dama wankan sa dadewa yakeyi sosai yafi mata ma,yana fitowa nace nazo? Yana dariya yace a'a dan Allah zauna abinki zan yi da kaina nasan halinki kice zaki cire min towel,ina zaune ya gama shirinsa tsab cikin kaya marasa nauyi,nace Ohh kayi kyau shi kuma ya dawo inda nake zaune a kasan Carpet dake dan gefen bed na sa abinci gaba,ya wara kafafuna tare da Zama a gabana ya jingina bayansa a fuskata,kayi kato ai Sai kace wani yaro zaka zauna min a gabana kalli fa ta ya zan baka abincin kato da kai a gaban karama haka ka fiye son jiki,ni a Sanina mace tafi Namiji son jiki sai gashi kai kafi macen ma,sauri ki bani abincin wajen Daddy zan je yanzu,nace da dare nan haka? Ae mana dan Allah kaje Dani pls kaji,Su Meenat fa? sai mu tafi dasu ko a barsu a gida,hmm ina tunanin ma fa Family House zamu koma again tunda naji abinda Daddy ke nufi kenan,Nan take hankalina ya tashi,raina ya baci,muna jin dadinmu shike nan amma ya za muyi ko dan sabo da Daddy sai mu koma,a fili kuwa ban nuna damuwata ba sai ma nace ah kace mu shirya kayanmu amma an gyara mana part ko tunda har almost 1wk bama ciki,yace an gyara komai neat amma ban san me yasa ba ban son komawa amma Kin San Hajja zata takurawa Daddy ne ta fara fushi dashi a kaina,abincin na fara bashi me shegen dadi fried rice tasha hadi da kaji sai fruits da sauran kayan ciye ciye,nace ba matsala karka damu zamu koma ko dan Daddy ba abinda zai faru,kin san ma mene? Nace sai ka fada yace Ameer shike zuga Hajja akan komai na tabbata ma yanzu shine yace sai an dawo daku gidan,nan take na kara Jin tsanar Ameer a raina,Aayan yace Ameer shi ya gaji Hajja a mugunta komai shike tsara mata da Alama ya tsaneki kamar haka nake gani,baki na tabe ta Allah ba tasa ba,ya zaiyi dani ai ni Duwawu ce dole a zauna dani,shegen dan iska,jaraba annamimi da fuska kamar yalo, dariya Aayan dinga yi yanda yaga sai zagin Ameer nakeyi ba ji ba gani yace zagin ma harda Raps Baby ba a tsayawa a huta,dariya nayi nima nace Allah dan iskan yaro sai iyayin jaraba yana gadara da takama sai kace shine Aayan,to ko shine Aayan ma ya isa ya min na kyaleshi,Dariya Aayan yake au nine ma me gadara da iyayi? Nace a'a misali nayi hhh,Allah mutuncinsa daya da yasa nake dan raga masa yanda kuke dan kama dashi kadai kuke kama a gidan nan ni ban san ma ya akayi yayi kyau ba matsiyaci,Nan take naga Aayan ya hade girar sama data kasa kamar zai dakeni,lfy? Allah Baka hakuri in dai akan na zagi dan uwanka ne,Allah dan kuna kama....Tsawa ya buga min rabon da naji irinta har na manta tun farkon haduwarmu dashi,masifa ya fara ni bama kama zaki ce yana da wani kyau baki da hankali idan sonshi kike ba sai kin fada min haka ba ya ja tsaki ya haura saman Bed abinsa.
Firgita nayi kaina ya daure daga ana labari sai fushi kuma ni mene hadina da wani Ameer kuma,mikewa nayi nace kayi hakuri ba haka nake nufi ba ni,da sauri ya Zabura ya Mike hado kayanku a kaiku can sai ki dinga ganin Ameer me kyau,Ka fahimceni bafa nufina kenan ba wlh,mene abin fushi a nan ana lbr to kayi hakuri na furta cikin sanyi na,shekeke ya kalleni yace na rantse yau sai kun koma Family House Hajja bata isa tasa na Canja muku gida ba ra'ayina ne ganin damata ne dan kawai hankalinku ya kwanta muje kawai na rigada na rantse,gani nayi ina lallabashi yana wani kara hawa nace fine mu koma mana mene to, na fice na bar masa Bedroom din naga cikin fushi yake gaba daya yau.
Su Meenat suna shigowa na sanar musu su Kansu basu ji dadi ba,nace su hada mana kaf kayanmu,Meenat tace sis dazu naga wani wlh kamar Abbanmu a mota wani me kama dashi tsaki Naja tare da cewa sai me to dan kin ganshi tunda bai neme mu ba me zamuyi masa,Sis kamar fushi kikeyi lfy? Ko fada kukayi da mijinki? Nan take na fara hawaye ina sanarwa Meenat,Meenat tayi dariya tace Sonki yakeyi kishinki ne,ke komai kiyi fushi ai ba haka akeyi ba,ki daina cewa zaki rama abu ko dole sai kin maida martani kinji mene abin Kuka ai zaku shirya ne,idona na goge muka shirya,Sai ga Aayan ya leko fuska a tamke yace let's go,muka bishi har mota da kayanmu,Driver ne yaja mu har gidan sai da ya tsaya a inda ake siyar da wayoyi ya siyo guda biyu masu kyau da shegiyar tsada ya bani daya ya bawa Meenat daya,sai Meenat ce kadai tayi masa godia ni shuru nayi masa muka je har gidan,Ameer yana so zai fita da mota kawai ya hangoni wani farin ciki ya kamashi Bai San sanda ya tsaya ba ya fake da gaisawa da Aayan,Bro ya kk? Aayan yana fushi kamar zai tsage yace am ok,ya kalleni kawai yace Sis barka da zuwa ko kulashi banyi ba Meenat ce ta amsa,sai da ya kara yi min magana sannan na amsa da kyar ina fitowa da kayanmu,yace Bari na tayaku kaiwa ciki,Aayan yace no need jeka abinka,murmushi ya saki a ransa yana ko banza zan dinga kallonta ina jin dadi na.
Hajja tana sama tana kallonmu sai murna takeyi burinta zai cika,Abbi bakin mugu yana kusa da ita yana tsara mata muggun nufi,matarsa ma haka tare da sauran kannen Abbi,Ameer kuwa ganin na dawo sai ya fasa fita kawai ya koma part dinsu.
Aayan sai fushi yakeyi nima haka aka shigar mana da kayanmu, komai Neat a gidan yasha gyara sai kamshi,muna Hutawa muka wuce bangaren Daddy har Meenat muka kwashi gaisuwa sai murna yake yana jin dadi tare da sa mana albarka,bamu zauna ba muka dawo part dinmu tare dasu muka fada kitchen kamshi ya fara tashi a bargarenmu,sai ga jaraba sun fara shigowa,Sajeeda da Haneefa sunzo harda lekowa kitchen suna tabe baki Sajeeda tace yara ana ta jagwalgwalon ne? kamshi na tashi kamar gaske a baki ba dadi bari yau zamu dan dana muji,Aayan yana jinsu basu San yazo sakkowa kasa ba,yace kafin nazo nan waje Ku tabbatar kun bace min a part Nonsense ya furta yana Jan tsaki,da sauri suka fice Sumi Sumi sai suka tafi wajen Hajja,tana ganinsu tace to fa Allah kawo mu jaraba ta dawo na shiga uku da kawo kara me tayi muku,nan suka shirya karya wai nice nasa Aayan ya zagesu kuma nace ya koresu,Hajja da kanta tace muje wajen nata na daina saurara mata.
Suka taho Aayan ne ya bude musu kofa Hajja ta fara ta kansa kamar zata cire bakinta tana zagin Aayan,Haneefa tace daga munce idan ta gama girki ta sanmana sai zagi,Hajja da karfi tace ina makirar take tana shigowa kitchen tace gidan ubanki ne ko kayan abincin uwarki ce ta zuba mana,to dole suci idan naga dama ma part dinsu zaki je ki dafa musu abinda suke so,Aayan yace wlh basu isa ba ai ba baiwarsu bace ni na biya sadaki na aureta ba wanda zai sata ko ya hanata sai ni,Hajja ta fashe da kuka Wlh sai na fadawa ubanka yiiiiiiii,muna jinsu a kitchen tace ke dan uwarki wlh sai jikokina sunyi abinda suke so baza ki raba min kan zuria ba,matsiyatan bayi a gama a zuba musu suci,Meenat tace ga danye nan shine naku shi kuka siyo da kudinku wannan kuwa mun rigada mun dafa,kuma hakki ne a kan miji ya ci da matarsa muma tunda ba mutunci baza mu basu ba basu kai matsayin da zamu dafa musu abinci suci ba,Hajja tace iyeeeeee kana ji da girma na suke fada min haka? Yace ai Hajja kin dade da zubar da girmanki shi yasa suka take amma matata me tarbiya ce,Haneefa Hajja ta kiftawa ido tare da cewa Ku zubar da abincin uban kowa ya rasa,Aayan yace wlh duk wacce ta zubar sai gaba daya kun bar gidan nan yau ba gobe ba ai ba gidan ubanku bane,akan Mufee ba abinda bazan iya ba dama darajar Daddy kuke ci gaba daya zaku bar min gida wlh kunji na rantse,haba wani dadi ya kamani a kitchen mijina ya tare min fada ya nuna yana sona a gaban kowa,Muna haka sai ga Ameer da zureriyar wayar wuta,yace ke Sajeeda dan uwarku abin naku har ya kai kuzo kuna zagin matar Aayan,a ransa kuma matarsa yake nufi tunda sona yasa baya so ko sauro ya cijeni,Sajeeda zata masa rashin kunya ya fara tafkarsu son ransa sai da ya Zane musu jiki Hajja na tsine masa tana kuka.
Gaba daya fadan ya koma kan Ameer Hajja ta sanarwa Abbi,nan fa Ameer aka hadu a kansa suka masa tatas,a ransa kuwa yace babu wanda zai taba Mufee na kyaleshi,ta nan bangaren soyayyar Ameer a gareni rahma ce sabo da shi ke Tsarawa Hajja komai baya bata me kyau a kanmu yanda zata ci mana mutunci,shi kadai ya samu Hajja ya lallasheta ta hakura yace Hajja Ku baku iya mugunta ba ai ba a nunawa mutum a fili ba a sonsa ta kasa zamu bullo musu ki daina bari ana musu a gabansu sai su dauki mataki suma fa suna zuwa gidan malamai nan Ameer yasa Hajja farin ciki ya gama tsarata tsab,yace Asiri muka yiwa Aayan yanzu abinda zasuyi a karya asirin dake jikinsa sai a dora sabon aiki,Hajja ta fara kiran malamai tana so a karya asirin dake jikin Aayan ko wanne iri ne,maganin tsari take so ayiwa Aayan sannan ta sake sabon kalar nata.
Hajja ta manta Sam anyiwa Aayan asirin da bazai Haihu ba bazai iya komai ba,Kuma tace a karya komai dake jikin sa ko zai karye din oho?
Abbi Kansu suna mamakin Ameer bai fiye shiga harkar su ta makircin da suke aikatawa ba sai jefi jefi amma kuma yanzu yafi kowa bawa Hajja shawara a kanmu,sai sukayi tunanin Ameer ya tsane mu ne da yawa shi yasa,suma murna sukayi za ayi maganinmu sunga muna nema mu canjawa Aayan zuciya kamarma ya fara sona tunda sunga yana bin umarnina sabanin wancan matan nasa na baya,amma Abbi yace shima dole ya shiga harkar nan dan ganin ya raba ni da Aayan.
AsmaBaffa
[1/17, 9:08 PM] Asmabaffa: ππππ
ππππ
KASUWANCI NA
71-75
Official
By
AsmaBaffa
Ina matukar Godiya ga masu Sharhi Allah ya bar Kauna,kuma Insha'allah daya bayan daya sai kunga sunanku a Novel din nan na Kasuwanci na,sai dai ko Halin mantuwa,ina ganin sharhin ko wacce kuma kuna cikin list dina,sai dai duk wacce taga kamar na manta da ita ta tuna min pls love u all❤❤
Sai masu Sharhi wanda zasuyi watarana ban kula ba suga banyi musu reply ba kuma nayiwa wasu to ayi min Afwa ban kula bane, wacce taji ban kyauta mata ba kar tayi shuru tazo taci kwalata sannan ta tsige min dankwali ta wankeni tasssssπ€£π€£π€£na baku dama.
Ga page dinki ta gidana,Al albarka, masoyiya ta gaske me Sharhi kamar ruwa,kina birgeni KHADIJA A HAMZA
Gaisuwa ta zuwa ga babbar me kaunata HANAN ta Gp na gata nan na Cillo ta ki cafketa.π
Abbi cikin takaici ya ja Hajja bedroom dinta yana cewa Hajja munyi sake,wlh munyi sakaki,taya zamu bari mu rasa dukiya muna ji muna gani,kin san yaron nan ya fara son yarinyar nan shike nan wlh sai abinda tace dashi talaucewa zamuyi dan naga Alama yarinyar nan bata da imani ko kadan, nan Hajja ta fada masa tsarinsu da suka shirya ita da Ameer,Nan take Abbi ya Dafe kai,yace shike nan kun kashemu iceko baku aikata ba? Ya zaki biye wani Ameer ai Rusa mana aiki ne wannan kin San mene a jikin yaron?dama da kyar muka samu wannan ya zauna a jikinsa,Hajja tace mene abin yi? Abbi da yan uwansa sukace ki bar komai a hannunmu,Ameer yazo shigowa wajen Hajja ya dau wanka so yake yazo part dinmu na ga kwalliyarsa.
Yana jin me su Hajja suke yi hankalinsa ya tashi tabbas yasan sai sunga bayan Mufee amma yace ina Sam ba a isa ba baza a Rusa masa farin ciki ba,Shiga Bedroom din yayi tare da Zama gefe yana jinsu suna ta tsare tsare dan kar su gano shi sai ya dinga kiftawa Hajja ido yana mata signa da ido,ko idan Abbi yace ga abinda za ayi sai Ameer ya makewa Hajja kafada wai kar ta yarda,Hajja kadai ke gane me yake nufi,su kuwa su Abbi basu sani ba,sai ji sukayi Hajja tace me kuka sani,me kuka iya,har nawa kuke a duniyar,ni na tsuguna na haifeku zaku zo kuce ni zaku canjawa tunani,to baku isa ba iyyeee wato Ku ga wayayu wayonku yafi nawa?Ni wato bani da tunani ban san me nake ba ko? Abbi cike da ladabi ya Dafe kai yana Oh Hajja ki saurara kiji,Ameer ya kara makale mata kafada yana mata signa,Sani Kanin Abbi yace kai dan ubanka me ya sameka ne ko kafadarka ke ciwo ko tabin hankali ka hadu dashi,Abbi yace Lfy? Yace gashi nan Ameer sai wani makale kafada yake yana wani farfari da Ido ko dan daudu ka dawo bamu sani ba,kaga dan iskan yaro to uban me kake yi, pink lips dinsa ya turo yace to ni me nayi daga abu ya cijeni sai ace bazan sosa ba,Abbi yace to zaka bar dakin nan dan uwarka,Hajja tayi gazal tace kar Ku Zagar min shi ba ruwanku yaron kirki irin Ameeru dan albarka,Abbi ya tabe baki yaci gaba Hajja ki Bari muyi tsarinmu,Hajja tace sam bazai yuwu ba ni zanyi haka kawai na zauna jiranku wankin hula ya kaimu dare komai naku na yan boko sai anyi lissafi an tace an rairaye sannan a aikata,mu kuwa sha yanzu magani yanzu,Abbi suna matukar yin biyayya ga Hajja basa tsallake maganarta haka suka kyaleta cewa tayi nata suma za suyi nasu,Ameer ya kara kallon Hajja ya makale mata kafada Hajja tace a'a ban yarda ba Ku bari idan na gama kalar nawa Bai yi aiki ba sai na baku dama kuyi naku mu gani,a haka suka tsaya amma Abbi yace karta je a karya asirin jikin Aayan pls sabo da akwai shirinsu a jikinsa,A nan kawai Hajja ta yarda cewar ta fasa karyawa kawai zasu ci gaba da nasu,a nan Ameer bai hana ba tunda ya hana abubuwa da dama kar Hajja ta ganeshi ne kawai ya hakura.
Direct part dinmu Ameer ya zarce irin dole fa naga wankansa wanda ni ban san me yake nufi ba, ya kuwa yi dace muna zaune tare da Aayan a Palo yana fushi dani tun kan maganar Ameer dan nace yana da kyau,yaki cin abinci yau fushi yakeyi,har yamma 5pm yazo ya zauna a Palo,kuma nasan yunwa yake ji sai chat yake a waya,har sabon girki na masa kala biyu yaki ci,Yanzu haka ma Kunun gyada na masa na Dade banyi masa ba sai kosai naga yana sonsa,wanka na fesa Malam kamar a London cikin Wando tight iya rabin cinya Maroon,sai rigata fara me arnen kyau gashi yasha gyara na sakeshi na danyi masa style a gaban goshi kadan,Allah tsine wanda zai ce ban hadu ba yau ko mutum dutse ne yau ya kalleni sai jini ya fara gudana a jikinsa.
Sabo da haka ma na kalli Meenat da suka dawo daga Islamiyya nace to ku zauna a Bedroom kar naga yar iskar da fito palo Dariya Sukayi Meenat tace to kin manta zamuje birthday party din kawata yau ni da Ma'eesha zamu wuce ta palon, wanne which kind party ba inda zakuje kun San dai ko Ammah na da rai bata bari muje wani party,bafa wani party bane na kirki sis,Driver baya nan kun sani schl ma yau banje ba kun sani dai wa zai kaiku,zamuje a napep,fine amma kafin Ku fita kuje Ku fadawa Aayan shine ke rike mu yanzu kamar yayanku ne ko ma uba idan ya yarda kuje idan yace no shike nan.
Meenat tace uhm lallai Sis yanzu mun koma hannun mijinki ma? To kici da kanki kiwa kanki Sutura sannan ki zauna a gidanki Meenat,duk wannan shike mana ai ko dole baza muyi gaban kanmu ba,ni macece Allah ya rufa mana asiri mun samu me Kula damu shike nan kuma komai sai muyi ba saninsa?
To fa wasu idan ana rikesu a gida ganin wanda ke rikesu ba shine ya haifesu ba,kuma suna tunanin in ya tsine musu ko ya musu baki baza ta kamasu ba,kana gani zaka ciyar da mutum,ka shayar dashi,tufatarwa ka bashi ilmi da sauran abubuwa wasu ma ko yayansu basa yiwa rikon da sukewa dan riko sabo da su kyautata sai kaga kuma wanda ake rikewa yafi ma dan gidan iko,gadara,da rashin mutunci a gida,ayi ta ganin laifin masu rikon da ka zauna a gidan zaka ga yaron Ashe kwallon shege ne,ba wanda ya isa ya fada masa yaji,abinda yaga dama shi yakeyi baka isa dashi ba,da ka takura ace ka zaluncesu,kana gani zaita abinda yaga dama karshe ma wasu kaji a gari suna zaginka suna kala ma sharri cewar baka musu kaza kaza gari ayi ta tsine ma,karshe ma wasu su dinga cewa marikan nasu iyayen banza,ko a gidan suyi ta shirya ma mugunta iri iri suna zalintarka baka sani ba,more especially ace matar me gidan ce ta dauko wani ko wata take rikewa,suna ganin kamar itace da gidan ma ko saurarar mijin nata basa yi bayan komai shike yi a gidan suna cin arziki,kawai matar zasu fadawa itace take rikesu itace yar uwarsu mijin nata ko gaisuwa sai sunga dama,itama kuma tana kallo gani take ma ita ke musu komai ba mijin ba,bayan da dama zaka ga komai shi za a fadawa yayi musu amma Bai isa dasu ba,wani ko aikene sai dai ya aiki nasa ko na waje,da yawa ana magana kan azzalumai masu rikon yara ko yayan kishiya ko na yan Uwa ba a fadar laifin yaran,duk da cewa akwai masu zalincin Amma ya kamata mata masu dauko rikon Yara ko mijin ya kawo miki a daure a nuna musu muhimmancin me rikon nasu.ba kawai ayi ta yin abinda aka dama ba ana ganin ba iyayen da suka Haifa bane me zasuyi ya bika.
Fita nayi ina sheka uban Kamshi Aayan zaune a palo yana danna waya na karasa dauke da hadadden tire jere da abinci iri iri,gaba daya bana jin dadin fushinsa yau,duk sai naji duniyar tayi min zafi,tun kafin na karaso ya zuba min ido yana kallona kamar ya hadiyeni naji dadi a raina ko bai fada ba nasan ya yaba kuma nayi kyau,kafin na gama tunanina ya juya min baya a saman 3seater tafkekiya,ni dariya ma ya bani kamar yaro na fushi,
Ranka ya dade ga abinci ka daure kaci kaji,dama ni na saba da lallashin mutum kan dole yaci abinci ji nakeyi kamar nice banci komai ba shi yasa nake nacin sai anci abinci,Muna haka muka ji bugun kofar Ameer,na manta shigar dake jikina nayi hanyar Door zan bude, muryar Aayan naji a hankali yace kuma a haka zaki fita again? Da sauri na koma daki na saka Katon Hijab sannan na fito na bude kofar,Ameer yasha wanka gaskiya ba karya yayi kyau cikin kana nan kaya,Murmushi yayi min na bashi hanya ya shugo,Aayan tunda yaga shine ya kara hade rai da kyar ya amsa masa gaisuwar tasa,Yau Ameer harda ce min Aunty ya gida,ganin da mutunci yazo da fara'a na amsa masa nima sannan na koma kusa da kafafun Aayan inda yake kwance na fara masa tafiyar tsutsa a kafafu ina wasa da yatsunsa,Ameer yana satar kallonmu ransa ya baci sai kishi yake taso masa Amma ya danne, Aayan yana kallon yanayin Ameer shi bai yarda dashi ba sam yayi kicin kicin.
Cike da shagwaba nace Yanlabai Abincin pls,wani shock yaji a jikinsa yanda nayi maganar shi kanshi Ameer sai da yasha mamakina a haka yar yarinya dani sai iya shege fal ciki,Ameer a ransa cewa yake ina ma nine Aayan gaskiya ya dace wlh irin wannan kulawa haka ga shagwaba kai da sake,a fili kuwa kamar baya jinmu danna wayarsa yake ya hakimce a kujera,Damun Aayan nayi da pls kajiii har sai da ya gaji ya mike zaune tare da ajiye wayar gefe can yace Bani zanci,da murna na zuba masa tare da mika masa,kin karba yayi yace hannunki aikin me yake? Da Sauri na gyara zama kusa dashi,yace ba fa a dining bane bazanji dadin ci ba,Nace ya zanyi to? Ke kika damu naci ai sai kiyi yanda kika ga dama ya fada cike da gadara, cinyarsa kawai na zauna samanta sosai bai ce komai ba sai lumshe ido da yayi ma,
na fara bashi a baki da hannuna idan na bashi bazai ko hadiye ko taunawa ba sai nace to ka ci mana sannan zai fara taunawa yana yanga yana kumbura wai fushi yakeyi shi fa,Ameer Kamar Tv yake kallonmu ya wuce gaban a share abin,yanzu ma waya Aayan yake dannawa yaki dago kansa bare na bashi abinci nayi nayi lallashin ya dago yakiya,sai ma ya kara yin can gefe da kansa ina binsa da kyar na rike kan da hannu na biyu na saitashi nan kuma ya tsaya Kikam a haka yaki bude bakin,Sai da nasa daya hannuna na bude masa lips sai ya datse hakoran nasa kuma suma,Yatsu nasa na ware su da kyar ya hangame dan mitsilin bakin nasa ya barshi haka,Ai Ameer tagumi ya rafka tare da Sa mu gaba kamar Tv yana ta dariya, na Sa masa abincin yaki kulle bakin bare ya hadiye nan ma Hannu nasa na rufe na matse bakin sannan ya cinye, haka yake ta bani wahala idan nayi wannan sai nayi wancan duk ya gajiyar dani ni kuma kamar dole sai yaci.
Ameer ganin gatan Aayan yayi yawa ma haushi da kishi ya dameshi gashi wani abin yana sashi dariya ma watarana Amma kishi ji yake kamar ya mutu ko Ya batar da Aayan ace yau shine ake masa haka ai da yafi.
Muna zaune na zubawa Ameer nace gashi Ameer kana shan kunun Gyada na sani ko? Ga abinci ma ka zuba ai ko ba ya sha sai ya sha yau tunda ni nayi girkin kuma daga hannuna ya fito, ya karba yana sha ko kallon Aayan baya yi Sabo da haushinsa yake ji ya aure masa Mufee Amma ta wani fannin yana godewa Aayan dan ta silarsa ya sanni kuma zai kwace ni nan gaba.
Muna zaune sai ga Meenat da Ma'eesha sun dau wankan Material dinsu na ankon Birthday da zasu je yanda suka sha kyau ba a magana,Kamar yanda nace haka suka zo gaban Aayan tare da durkusawa suka gaisheshi cike da Ladabi sannan sukace Yaya Zamuje Birthday din kawarmu ta schl a gidansu akeyi idan ka Amince,mamaki yayi sannan kuma yaji dadi ga Sis dinsu basu nemi izininta ba sai shi gaskiya suna da tarbiya sun san me sukeyi,da murmushi dauke a fuskarsa yace shine kuka sha kyau haka salon a dinga kalkemin matana gaskiya am gealous dariya mukayi gaba daya har Ameer,Ameer yace Wannan Ma'eesha ai tafi kyau ma wannan Meenat ta fiye iyayin tsiya wai ita me kwalliya shi yasa bana kulata ni,Dariya nayi nace Wannan ai tsokanace Ameer kana ganin Yan mata an hadu,Ameer ya tabe baki tare da cewa masifaffiya dai ta fasawa Khaleel kai rannan wannan ai Dukan mijinta zata yi watarana, shi yasa ma bata da saurayin kirki sai irin su Kwaja da Nasuru Opera,Aayan ya sheke da dariya Kai Ameer wanne Nasuru Γpera din kake nufi? Ameer yana dariya yace Opera daka sani wanda su Haneefa suke aikensa Sa ido wajen wanda suke fada ai Camera suke bawa Opera Sabo da shige shigensa ake ce masa Opera kaga ko ina ka shiga ta Opera kayi Searching,Dariya muka dinga yi banda Meenat da take son yin Kuka.
Ma'eesha tace wlh mantawa nayi Sis ban fada muku ba rannan ma a hanyar schl wani ya dinga bin Meenat yace sunansa FELA me GALA wai shi dan rawar gala ne a kasuwannin kauye baku ganshi ba kafafunsa kamar na sauro yasha wandonsa Fela kato sai uwar Kafada kamar ansa riga a hanger ,Ameer yana dariya yace baki da sa'a Meenat Allah yayi a cikinsu zaki samu miji wai ya akayi ke duk wankan naki da iyayinki kike karewa a yaran su Sajeeda,Nima nace dama Yaran su Haneefa ne? Ameer yace sosai ma ai Fela Gala shike sanar musu duk wani wajen chasu idan za ayi show Saturday sunday irin su Haneefa ai duk basa muamula da manyan Yara,ki kula ki gani duk wata yar duniya me ji da kanta zaki ga mace har mace ga kudi ga kyau Amma indai lalatacciya ce bata taba kula mazan kirki sai daΓ ki gansu da maza kazamai,garori,munana, tabbas zancen Ameer hakane na fada a raina duk haka yan bariki suke kuma mace na ji da kanta Amma in kaga wanda take kulawa suna harka sai ka kusa kuka.
Aayan yana dariya ya kalli Meenat da ta hade kamar yar Minister ya kasa rike dariyarsa duk ya san yaran nasu Sajeeda,karku damar min mata Kunji na fada muku kai Ameer tashi ka kai min su Driver dinsu dama baya nan kaga kaima kaci wanka kuje ko zaka samu wata Operiya a can kaima, wannan yarinyar da bata da kunya zaka ce na kaisu,Magana nayi nace haba Ameer ka kaisu mana kuje ku dawo yanzu ko dan ni ka taimaka,Ameer yace a ransa dole na kai tunda Umarninki ne Queen Mufee ta,Tunda zan faranta miki ai zan kaisu dole,A fili yace Sunci darajar Ya Aayan da ke kuzo mu tafi kuma ku tabbatar takalminku fes yake kar a bata min mota,Meenat sai Harara take zuba masa har suka fita tare gaba daya,da Sauri ya wuce wajen Hajja yace ku je jikin mota ina zuwa,
yana Zuwa wajen Hajja tana ta faman kurbar kunu yace Hajja Albishirinki na samo babbar hanyar maganin matsiyatan nan,Hajja tace mene abinda ka samo fada min Dan Albarka, yace yanzu zan shiga jikinsu sosai zaku ga muna mutunci dasu sosai,zan kwantar da kaina a wajensu yanda zasu yarda dani kinga kafin mu karbo maganin da zamu Sa musu na kulla alaka dasu me karfi ni sai na shige na aikata komai da Komai ko Ya kika ce,amma in ba haka ba za a samu matsala wajen aikata abinda malamai suke so a kansu tunda basu yarda damu ba,don haka yanzu zan fara kullum zaki dinga ganina a part dinsu zamu dinga mu'amula har su yarda dani cikin kankanin lokaci sai kawai mu gama dasu,Wani farin ciki ya kama Hajja,tace haka za ayi yanzu ka kawo magana me kyau,amma da ubanka yazo min da maganar banza ba basira ba wayo a ciki,to Amma kana ganin zasu yarda ka shige musu jiki har su yarda dakai? Ameer yace har nayi nisa ma yanzu ma sun yarda dani gashi nan sunce na kai mata kannenta wani party na dawo dasu,Hajja ta mike tsaye da murna dan Manzon Allah fa? Ko wasa kake?Yace da gaske leka ta window zaki gansu shi yasa nazo na sanar miki kar a kawo miki gulmata ki yarda kin san muna tare ke nakewa aiki,Hajja tace yo wa Isa ya kawo min gulmarka dan Albarka ai kasan bana yarda da maganar su a kanka,dariya Ameer yayi a ransa yace tsohuwa kenan nima kaina nake gyarawa hanyar samun Mufeeda na aureta ina ruwana da wani kudirinku ke dasu Abbi can da yawarku,a fili yace Hajja me zan siyo miki? Hajja tace abinda ka saba siyo min kullum dan Albarka,Ameer yace ai yau ba Hantar Rago kadai zaki ci ba harda yan shila idan ma dawisu kike so shi zan kawo,Dariya Hajja ta saki tace Ko mene ma duk ina so tunda kaine dan Aljanna.Ameer ya fito ransa fes ya tsara Hajja Sabo da yasan ana ganinsa tare da Su Meenat za a kai gulmarsa wajen Hajja ta daina yarda dashi,yanzu kuwa ya kashe bakin tsanya.
Yana fitowa ya harari Meenat ke zaki shiga baya Ma'eesha ta ce zata shiga gaba tafi kyau baza a ganni da mummana a gaban mota ba,Meenat tayi banza dashi ta shiga bayan felleliyar motar Ameer, Ma'eesha a gaba,Ameer shi irin yan Tsabtar nan ne da shegen iyayi shi a dole Saurayi wankan ma da yake irin na mawakan turai matasa irin su Justin Bieber etc kowa yaga Ameer zaiyi tunanin kwallon dan iska ne ko ta askinsa kawai ba sai an tambaya ba,wandunansa kansu na zamani samari masu ji da kansu,Duk da cewa duk matasan yan wanka ne a gidan su Ameer Amma Ameer shi mata ma rubibinsa suke gashi da wanka Tsabta ga kamshi kuma yana da kyau wanda ke jan yan mata Uwa Uba ga diri me kyau.
Aayan ne kadai bazai jΓ‘ dashi ba dan Aayan shi halittarsa ce ba kakalowa yayi ba haka yake komai in yayi me kyau ne,shiga kuwa dama shi a turai yake kana gani komai a jikinsa yake ba wasu yan dabaru akayi ba zallar baiwa ce,Shi kuwa Ameer tsabar kakale kakale ne da jarabar son iyayi ace Babban yaro sai da ya tsatso kyansa ya fito fili,Su Mujaheed ma haka suke shegun duniya ne wajen gayu,Suna Tafiya a hanya Ameer ya daga waya wata cikin yan matansa ta kirashi yanda ya kanannade murya kamar Sardaunan Ramlat yana Rapping English kamar wani Dj khaleed,Baki Meenat ta tabe tana jin iyayin da yake faman Digawa,aranta tace wannan wlh irin mijin Sis ne har kusan Halinsu ma sai daΓ Aayan karshe ne a komai,bayan ya gama wayar ya wani rare kidan Nija kawai tashi yake kamar zai fasa mana kunne,Maeesha ce mayyar rawa har ta fara yi a motar tana ihu uhhhh tare da dage hannaye sama,Shi kuwa idan kida yayi kida sai daΓ kaga ya bugu sitiyarin yana juya kan mota komar ma motar yakewa rawar,yanayi da kansa gashi duk Baiti ya iya abinda suke cewa kamar shi ya rerata, dama ga motar tasha tint ta samarin zamani,Maeesha yin abinta take wata tana shigowa me dadi tace ohhh yeee taci gaba da yi tana bi itama shi kanshi Ameer ta bashi dariya,ya kalleta yace ashe dai ke yar gari ce kin waye,duk kin san wakokin nan haka Amma kin iya rawa? Ma'eesha tace sosai ma ai wayar Sis Mufee nake sacewa naje schl da ita na turo latest a wayoyin classmate dina,duk wacce ta shigo bata wuceni har rawar,Ameer ya mika mata hannu suka tafa yace kin birgeni ta gidana,ai kawai a Shana,tace tunin ma ai Baza a barmu a baya ba ina jss3 fa going to ss1 ai dole aje damu,Ameer yace yessooooo Baby,
Meenat tana jinsu suna tayi sun cika motar ga kida ga surutu suna ta yi da baki gashi ana jin wakar ana bi kuma da baki ga rawa anayi a zaune gaba daya sun gigita motar.
Meenat kuwa wayarta take latsawa wacce Aayan ya siya mana tare katuwar gaske.
a wani karamin hole akeyi Amma ya tsaru sosai wajen sabo da yarinyar dangin masu kudi ne shi yasa aka tsara abin,ashe yarinyar Cousin din Sameera me yan daba ce,itama Sameera tana wajen itace ma ta hada mata Birthday party din,Yan mata irin su Meenat duk sune a wajen ansha wanka da samari na schl Yara tare da wasu kuma manya sai yan Uwa,Yarinyar Husna tasha wanka ana ta pics wasu na rawa,su Meenat ma suka Parker a wajen,Ameer yace ki bari yarinya na kankaro miki girma yanzu,Harara Meenat ta watsa masa,yace ni da zan taimaka miki nayi featuring dinki a wajen,Maeesha tace muje tare Yaya Ameer ni kayi ft dina ko a pics din da za muyi,kina ja Baby kanki na kawo light muje,ya rikewa Ma'eeshah hannu Meenat na gabansu duk inda suka wuce sai an kallesu,abinda Meenat bata sani ba an san Ameer sosai shima yanda yake nuna kudi da kalar Naira yana karyar arziki,kusan dama Daddy na Aayan ya makalewa lokacin Aayan bai dawo Nigeria ba,Ameer yake likewa Daddy sai da yayi suna sosai,ko a Tv za a nuna Daddy zai bude Abu sai kaga Ameer a wajen tun yana karami yake son ace shi wani ne yayi suna duniya ta sanshi shi yasa da farko bashi da Kamar Daddy shi yake masa labadi,ganin haka su Abbi suka juyawa Ameer hankali da ya girma sosai sai ya daina Saurarar Daddy gaba daya yake bin iyayensa.
Ai kuwa Meenat tasha mamaki yanda taga ana ta kallon Ameer ana girmamashi ,mata na rubibinsa,Har uwar gayya Sameera tazo wajensa suka gaisa tace Ina Aayan?Yace yana gida,ka gaisa min shi,wannan yaran fa?ta furta tana mana wani kallon Banza,tana ta kallonmu tace Amma wannan sunyi min kama da wata sosai,yawwa yarinyar da Aayan ke aure,Ameer yace kannenta ne,Sameera tace kai Amma yarinyar bata da kunya ko kadan ina nan zan gyarata soon,nan take Ameer ya canja fuska yace ban gane ba? Tace kwarai tayi min laifi wanda ni kuma sai na nuna mata duniya ba kowa ake tabawa a kwana lfy ba,Ameer ya fusata yace lallai kema kuwa da kin tabbata wani in ya tabaka ya taba banza kuma ba kowa ake tabawa ace za a iya ramawa ba,wani in ya taba har abada ba a iya daukan fansa a kansa,Sameera tayi murmushi tace ba irinmu ba wlh,Meenat ma tace to ke har wace da baza a miki ki hakura ba wata tsohuwa ma dake,Sameera tace duk sai kun maimaita abinda kuka ce,Ameer yace Sameera kin san Halina ke a yan daban naki kanana ne kawai kallonki ake ana tunanin kin wuce haka Amma baki kai ba,wlh wlh kika sake wani abu ya samu Mufeeda ki fara irga kanki cikin wanda suka sheka lahira kin san mu kin san Halina try me.Dariya Sameera tayi tace Ameer kenan ko Aayan da take matarsa bai ce min komai ba sai kai? Husna ce tazo ta janye su gaba daya tana kuzo muyi pics nan fa suka dinga daukan hotuna Har Ameer dan shishigi cewar Meenat,yan mata kuwa jikin Ameer suke faman mannewa ana daukansu,anyiwa Ameer ma haka inaga Aayan uban kyawawa da daukan wanka Meenat ta fada a ranta.
Tunda su Meenat suka tafi naci gaba da bawa Aayan abinci yana min yanga,Yana karba da kyar har na gaji na mike na barshi a nan yana fushinsa,Kwashe komai nayi na gyara ko ina aiki yana kallona har Magrib tayi na shiga kitchen zan mana Dinner,Ban san sanda yaje masallaci ba kuma bai dawo ba har bayan Isha sosai,
Su Meenat Suna gamawa Ameer ya dawo dasu gida sai da ya tsaya ya siyo musu ice cream sai yace banda Meenat bata da biyayya nawa dana Ma'eesha ne,Meenat tace sanda zansha ma ka sani ne,kuma sai na sha sai dai ka mutu.
Ina gama girkin na gyara komai na gidan nayi wanka nasa rigar bacci ta da turare na kaiwa Aayan abincinsa yana dakinsa ya dawo ina ajiyewa na juya na bar dakin,Bedroom naje tare muka ci abincin mu dasu Meenat muka koshi bayan ina dafawa naci wani kitchen Sabo da tsaro ko Aayan zai ce muci tare sai yaga ina cin kadan irin yar gayu ni.
Muna gamawa mukayi Brush muka kwanta tare dasu kamar yanda mukeyi da,Meenat tace to yau kuma baza aje hirar ba?Nace ina ruwanki Sa ido,Meenat tana dariya tace a'a maida wukar bani na kar zomon ba,Sis yau ba jin dadi?Dan Allah da zafi ko dadi ne dashi nasan yanzu an gama kwashe ki,Dukan wasa na kai mata ina dariya nace zan ci uwarki wlh uban kwasheni akayi ki bari idan kinyi auren kyaji naki kalar, kwana nan zan fara zuwa gyaran jiki idan munyi hutun schl zan karbi kudi wajen Aayan Amma bazance gyaran jiki zanyi ba kar ma yayi tunanin shi zanwa ko sonsa nake,Meenat ta dinga dariya tace Sis wa zakiwa gyaran jikin to? Kyaji dashi can sai kizo nan ki tamana zancen da bashi kenan Ba can kuma da kinje ki zage ku sha love,oh karya nake miki kenan? Meenat tace to mu dai kiyi bacci dan Allah mun gaji da labarinki ke Sis sai za ayi bacci kice zaki bamu labari,ko tsakar dare ki tashe mu,
Nace Meenat kinfa rainani wlh tam,ai kuwa sunyi Baccinsu wurin 12 na kasa bacci sabo da tunanin Aayan Yamin yawa sai juyi nake ina tunano yanda muke murza juna ina murmushi ni kadai, na tuna da abinda nake so muyi shawara da Meenat Aiko ba bata lokaci na juya jikin Meenat dake shakar bacci nace Meenat ina girgizata tsaki ta ja tana sosa gefen kunne,nace Meenat ki tashi mana na daka mata duka ta mike a firgice, nace mantawa nayi ban fada miki ba wai don Allah rannan kika ce kinga alamar Aayan kamar yana so na?
Wani takaici ya kashe Meenat tace yanzu akan wannan zaki tasheni kusan karfe dayan dare?Nace ae gwara na kara jin gaskiya,cikin magagin bacci Meenat tace baya Sonki ko kadan,yaaaa tsaneki ne Sis kin kasa ganewa bakya birgeshi ko kadan ta koma ta kwanta sai baccinta takeyi,ni kuwa gaba daya naji duniyar ta kife min.
Nan danan zazzabi ya fara kamani me zafi ga bakin ciki Meenat ta gano Aayan baya sona bana birgeshi,nan nayi tunanin yes gaskiya ne tunda ko yabo na ba yayi bai cewa ina da kyau na hadu,wannan ya nuna ya tsaneni sosai ne kawai sai na fashe da kuka na dinga yi da karfi a saman Bed cikin bargo,duk na hana Ma'eesha da Meenat bacci da Kukana sai ma kara karfinsa da nayi,sai tsaki sukeyi suna juyi su fa sam basa kaunar bacci tare dani dama tun Asali tun Ammah na da rai Sabo da tashinsu nake na hanasu bacci,lokacin ina Sana'a a gida tare da da Ammah cikin dare zan tashe su nace sai munyi lissafin kudi ko na fara basu labarin ya za ayi a tara kudi,ko tattali,idan kuwa nayi Sana'a banci riba ba ko jarin ya karye to fa sunga ta kansu kwana zanyi ina kuka a kan gadon mu,Ammah watarana sai ta jawo sandarta ta kwandala min sannan nake shuru dan ni bacci bai dameni da yawa ba,na riga na saba da jarabar neman kudi ban fiye bacci me yawan gaske ba.
Suna jina kalar Kukan da nake harda me jiniyar motar yan kwana kwana,Meenat tasa Hijab ta fice har saman Aayan dan ita ta manta ma tace Aayan bai sona,cikin magagi ta fada min,knocking tayiwa Aayan ya zata nice sai yaji muryar Meenat,a firgice ya bude tunaninsa wani abu ne ya sameni tace wlh Yaya mudai kazo ka tafi da ita ta damemu wlh sai kuka take ta hana mu bacci,ko ka canja mata dakinta ita kadai mu takura mana takeyi,me ya sameta? Ba komai mu bamu sani ba dama haka takeyi ko a gida idan ta fadi a Business ko jarinta ya karye to sai ta kwana tana uban kuka har sai tayi Zazzabi,Aayan yace akan kudin? Meenat tace sosai ma watarana akan Naira darinta ta fadi a kasuwa sai da ta kwana tana kuka karshe sai da aka mata Allurar zazzabi Sabo da kuka,Duk daren nan sai da Aayan ya dinga dariya,Meenat tace ranar da jarin Awarar ta ya karye aka rasa dubu daya mun zata wlh ta samu tabin kwakwalwa,ni dai kaje dan Allah ka daukota a can ta damemu mu,maeesha ma tana zaune ba bacci kuma gobe muna da Test a schl.
Meenat na gaba Aayan yana bayanta suka je har Bedroom din yanda nake haka nake ta barka kuka na,muryar Aayan dana ji ce tasa na kara ci gaba da kuka na yafi na da karfi ma,na cukwikwiye kaina a bargo ga uban gumi na hada,yace ke mene haka? Amma anyi girman banza babba dake to wa zai wa wani fada kenan? Na dauka ma lallashina yazo ya lallabani mu tafi dakinsa sai kawai naji ya rufe ni da bala'i, Kamar me Aljanu na dinga shure shure a Cikin bargon na kara ci gaba da kuka na,ina wayyo Marainiya ni,Zan mutu, Meenat tace baza fa tayi shuru ba wlh sai a kwana a haka da ita gwara ka dauketa kuje can in yaso ko zaneta ma kayi mu muyi baccin mu,Maeesha tace wai me akayi mata ne tana dariya tace wlh sis Mufee baza ta girma ba ko ni na fita wannan kuka dama ta saba abinta,Aayan yace Dan kune kawai zata hanaku bacci Amma da Bazan kalleta ba ta shekara tanayi,Meenat tace dan Allah ka rufa mana asiri ka dauketa muyi bacci,Aayan ya fara kokarin janye bargon dana ke ciki yana tsaki nace wlh tunda yayi tsaki Bazan je ba a barni nayi Kuka na,da karfi ya fisge bargon ya hau saman Bed din yanda nake kwacewa ina burburwa hannayena ya rike biyu na kasa motsi sai Kukana nake harda hawaye kwara kwara,ya samu bakina yasa yatsun hannunsa dan mugunta ya dinga dalla masa yatsansa kamar Harbin kunama ba shiri nayi shuru,tashi mu tafi yace, nace Bazan je ba,ai kuwa ya make min baki naji zafi ba shiri nace zanje wlh kayi hakuri,meenat sai dariya suke ya figeni yana jana fii yace kusha baccinku yau zata gane kurenta,Meenat ta rufe kofa tace wanne zata gane kurenta wai mu za awa wayo kuje dai ku sha iskancinku kuyi luf abinda shi kanshi kasa bacci yayi dama hakan yake so na ganeku.
Ai kuwa kamar Meenat ta sani yana kaini Bedroom ya fara masifa yana min fada ke baki san kina shiga hakkinsu ba? Ba kyau takura rayuwar wani Yara suna so suyi bacci kuma a gabansu kannenki kike musu kuka,ai ba su akewa ba matan aure me gida sukewa kuka ba wani ba,idan shagwabarki kikeji kizo kiyi min ni zan dauketa ba su ba,nace to ni me nayi abinda fushi kake dani, yace ba dole nayi fushi ba muna Business dinmu kinzo kince Ameer yana da kyau ke yanzu zaki ji dadi nace Meenat ce me kyau ba ke ba,to ai nima sau nawa kace Meenat ta fini,wannan ai cin fuska ne,to ki kiyaye yanzu duk kinsa ma na fasa baki kudin Business sai an sake sabo,nima dadi naji zan masa wayo naji dadina nace to a sake sabon mana wa yake jin tsoro tunda kudi zan samu sai na samu wanda yafi na da ma.
A ransa yace lallai Mufeeda yarinya ce yanzu ta yarda,nima a raina nace dadi a banza kuma a bani kudi nice da riba ka hadu da ni,Muryarsa naji yace to yanzu duk kukanki da shagwabarki Maza sauketa a kaina ki samu kudi kuwa da yawa yarinya,Nace ai ba sai kace ba yanzu zan nemo hanyar arzikina mota,gida da kasar waje ko da kafar katako,jikinsa ya jawoni muka fada saman Bed ba kunya na fara kuka na irin na dazu,shi kuwa lallabani ya farayi yana mene ne Pretty na? Na koma shagwaba kala kala yana biye min tare da fara sarrafani,a raina nace da haka kawai ina can zanyi kwanan kunci tunda hakane Meenat na gano yanda zan dinga baki aiki idan ta baci,Aayan kuwa a ransa dadi yake ji marar misaltuwa yana godewa Meenat dama ya kasa bacci ko kadan ni kawai yake bukata.
AsmaBaffa
[1/19, 12:07 PM] Asmabaffa: ππππ
ππππ
KASUWANCI NA
76-80
Official
By
AsmaBaffa
Ina mika dubun godiya ta gereku
MAMAN 2 KIDS
AUNTY SUMEE
MEENAL SIDI
MRS HAMZA
ADABIYA ISAH
SAMEERA AHMAD
JAMILA SULE
MAMAN MEENAT
Sai manya manyana ina jinjina muku
MAMAN MEENAT
MUM SUHAIL
MAMAN HAIDAR
QUEENMERMU
MAMAN WALEEDA
JIDDER ZARIA
MARCYCOOL
PHERTIMARH
AUTA
FLOWER ina kike kwana biyu Allah yasa lfy?
BIBA
HEENDU
HUMAIRAH
Page naki ne AYSHATABDULLAHI Me hadarin Sharhi na gode.ππ
Kwance nake a jikinsa na lafe luf muna huce gajiyar harkoki da muka kwasa,kin taba soyayya Ne Mufeeda? Naji muryarsa yana tambayata,wow yanda ya furta Mufeeda kamar wasu Aljanu ne suka fada Sabo da dadin sunan ba a cewa komai, kamar gaske nace ae na taba yi,gabansa ya fadi sosai ya shiga damuwa har kishi ya cika shi ya daure yace da wa? KUDI nace ina na san wani so ni ban san komai ba ai ni imani na kudi,ni kudi ne masoyina,Dariya yayi a ransa yasan ban san ma kudin ba ban san dadinsu ba Amma ina kirarin nasan kudi,a fili kuwa yace yanzu idan na baki million daya a hannunki me zakiyi da ita? Yanzu duk kuna ci kuna sha da Sutura ga schl baku da matsala da ita,ta ya zaki kashe million daya fada min naji? Kwanciya ta na gyara a jikinsa tare da fadawa tunanin ta yanda zan kashe kudin da ya fada,na gama tunani na nace na dinga cin kayan dadi,na fantama na Sa kaya irin na matan shugaban kasa,na dinga zuwa wajen da ake gasa kaji ina ci,na siyi fili kato,da mota,dariya yayi yace to kuna da motar hawa duk wacce kuke so akwai,me kike so kici wanda babu a gidan nan?Sannan kuna cin na wajen ma ai ko? Ae to ni dai ina so ace nima ina da nawa na kaina ba na wani ba,sabo dame?kayan mijinki ai naki ne, a'a ba nawa bane kafin a baka ma sai kayi yar murya,ko kuma a dinga bata rai ko kasa mutum ke ebowa ya baka watarana sai ya gaji,sannan Maza dan suna ma abu sai suyi ta juya ka ana ma kallon wata shatara, matan Hausawa kenan kike nufi duk abinda yasa suke karatu da aikin Gomnati don kawai su samu kudi ba sai sun saurari na mijinsu ba,kuma most of them badan Allah suke so su samu kudin ba kawai biyayya ce basa so suyiwa mijinsu shi yasa suke neman kudin, ya fita kin fita,bai Isa ya saki kiyi ba,wani ma in kudinta yafi na namiji zai sha wulakanci dole shi zai kwantar da kai yana mata biyayya.
Nace hakane ko Ilmi macen tafi namiji sai kaga ko kudin albashi ya dauka ita zai kawowa sai yanda tayi dashi,shi yasa Maza suke tsoron auren macen da ta fisu Ilmi ko ta fisu albashi,sabo da matan Hausawa basu iya samu ba,mace daga tana daukan dan Salary sai kuga ta fara wulakanci kowa taka shi takeyi ita me kudi,dan Allah mata mu gyara halayen mu,wasu gidansu kaje da kyar suke kallonka ma bare mutunci ya hadaku Sabo da tana daukan Salary,mazan sam basa jin dadinsu,ga jarabar son kudi da neman kudi aje nan aje nan ba hutu ba lokacin me gida kuma bai Isa yace komai ba tafi karfinsa sai abinda taga dama,idan ma kishiya zaiyi cewa zatayi ya kara me ya dameni suje can su karata da kudina me nake nema a wajensa ko Sakina yayi zan iya rike kaina da Yara na,abin haushin kuma da zasu rabu sai aga ta koma bin Maza kanana tana kashe musu kudin da ta kasa taimakon mijinta dasu.
Mun dade muna hirarmu dashi yana wasa da dukiyar fulanina wani dadi na shigata na juyo ina facing dinsa tare da kara shigewa jikinsa,yace ya dai? Wani sonsa nakeji yana ratsani ta ko wacce gaba dake jikina,baki nasa ina lashe lips dinsa kamar mayya nan ma haka muka kara birkita kanmu mun dade muna farantawa juna rai,ni kam yanzu son Aayan ya gama ragargaza min zuciya,kwakwaran numfashi banayi sai da tunaninsa,komai nasa birgeni yakeyi,ji nake kamar a hademu na zauna cikin jikinsa har abada abin fa ya wuce gona da iri yanda nake jin son Aayan ya zarta hankali har mamaki nakeyi,bani da burin da ya wuce na ganni tare dashi ina jikinsa,kallon Aayan kadai idan ina yi a Cikin gidan gaba daya sai naji dadi da sanyi marar misaltuwa,nayiwa zuciyata fada abin yaci tura,ko schl naje ba komai nake ganewa ba kawai tunanin Aayan yafiye min komai a duniya.
Kwanaki sun dan ja,Ameer ko yaushe yana part dinmu kusan kullum sai yazo,a nan yake cin lunch da Dinner haka kullum suke fada da Meenat,Ma'eesha ce kawarsa kullum suna tare suna danna waya da jin wakoki aikinsu kenan, Meenat bata da time yanzu karatun waec da Neco sukeyi,Ma'eesha kuwa za a shiga Ss1 kwana nan,ni kuma ina ss1 going to 2 Sabo da ya tsallakemin jss3 ban karasa ba aka sani a ss1 shi yasa Amma da Ma'eesha ma ta fini class.
Ma'eesha ta zama yan mata Sabo da kansu daya da Meenat kusan ma tafi Meenat girma ta kamoni Sabo da dama tana da saurin girma tsayin kafa tayi sai ka rantse ma ba Meenat ce yayarta ba,Sabo da zama da suke yawan yi da Ameer Ma'eesha har ta fara son Ameer sosai Amma boyewa takeyi dan kar mu gane sai dai kullum bata da zance sai Na Ameer.
Kudi masu yawa Aayan ya bamu muje mu sake uniform tare da schl bags da takalma amma sai yace yasan idan nice me araha zan siyo mu tafi tare da su Meenat Driver ya kaimu.
Muna mota Driver zai kaimu store nace canja hanya Baba ka kaimu Kasuwar kofar Wambai yafi araha,Meenat tace wlh mu store za a kaimu masu tsada yace a siya mana,Baki na make mata tayi shuru,ya kaimu Kofar Wambai muna gaban table din masu takalma ina ta zabga cikiniki yaki daidaita,na daga wani baki nace nawa wannan Malam? Dubu uku yace,a garin ina za a siyi wannan dubu uku Malam Dubu daya da Dari biyar idan ka siyar, Ma'eesha ce ta matsa gefe tare da kiran Aayan a waya Hello Yaya taki kaimu store wlh muna kasuwar Kofar Wambai kuma a kasuwar ma table din masu araha wai dan Dubu daya da Dari biyar kuma suna ta Surutu da masu saida kayan dan Allah da aurenta fa Yaya.
Mata masu zuwa kasuwa a zauna ayi ta Surutu da masu saida kaya,da aurenki zaka ga wasu har canja murya suke suna lankwasheta abinda basa yiwa mazajensu sai siyiwa yan kasuwa sabo da suna neman a rage musu ayi musu araha su siya a banza.
Aayan kuwa kishi ne ya sokeshi da bacin rai wai yacewa yarinyar nan suje Mall amma ta kaisu kasuwa cikin maza ana ta cakudewa yanzu haka ma wani ya gogar masa jikin matarsa nan take bai San sanda ya shiga mota ba ya bar Office driver ya ja suka tafi,a hanya ya kira Ma'eesha ta fada masa inda suke minti kadan sai ga Aayan ya danna musu Horn tare da sauke glass.
Ina ganinsa hankalina ya tashi na rude ko ta kan me kaya banbi ba nayi sauri na isa motar mu na fada ciki,Meenat da Ma'eesha suka shiga bayan mota kusa da Aayan da Kansa ya kaisu Shopping ya siya musu wanda suke so masu tsadar gaske komai har ni ma suka siya min nawa,ni kuwa tuni nasa Baba Driver ya maidani gida.
Da suka dawo da kyar na fito palo,Ranar da dare nasha warning wajen Aayan sai da ya min ba dadi ina bashi hakuri.
Anyi mana hutun schl Meenat tana zana waec da Neco dinta,yau Sunday muna zaune a palo ina yankewa Aayan Farce,Ma'eesha na karatu a wayarta da Ameer ya siya mata me kyau,Meenat kuwa abinci take ci dawowarta daga schl kenan yamma lisss,wayar Aayan ce ta fara ruri,da hannuna na daga kiran naga ansa Bobo nasan Yarima ne na kara masa a kunne yace Hey frnd ya kk,Yarima yace gani a gidanku fa bude min kofa, Ma'eesha yayiwa magana yace budewa Yarima kofa Angel dama haka yake cewa Ma'eesha,Meenat kuma yace mata Preety, ni kuma daga ke shike nan sai ta mugun baci zai ce Mufeeda ina takaicin wannan abun da yake min Amma ya na iya tunda ni ba a sona.
Ma'eesha na bude kofa Yarima yayi arba da ita wow ya furta a ransa da gani ba sai an fada ba yasan ma kanwar matar Aayan ce Sabo da kama da muke kawai haske zan fisu kadan shima idan baka sanni sosai ba baza kace na fisu haske ba,ba wani me yawa bane,Maeesha akwai fara'a ta gaisheshi tana murmushi sai kallonta yake ta gama Tafiya da Imaninsa gaba daya, bashi da burin auren yarinya karama Amma akan wannan kuwa sai dai a mutu, da sallama dauke a bakinsa ya shigo,Gaskiya Yarima ya hadu Chocolate ne me haske karshen kyau yana da shi dan fulanin Asali ne,ga wanka iya wanka dama duk irin abokan su Aayan ai haka suke basa muamula da garori, Ma'eesha kuwa kunya ma taji irin yanda ya mata Kwarjini gashi ya hadu sai kuma irin kallon da yake mata.
Yana zuwa ya mikawa Aayan hannu suka tafa shegen gari kwana biyu Aayan ko Saudiyya banga kaje Umrah ba last wk ina can ina ta jiranka kace zaka je har na dawo bamu hadu ba,Tabe baki Aayan yayi tare da cewa gwauro shike yawo lokacin da yaga dama,dariya Yarima yayi lallai Aayan ka canja,juyawa nayi muka gaisa dashi a mutunce yana tsokanata da Abokinsa yayi kiba ya kara kyau me nake bashi ne,Meenat kawo masa ruwa,Kallon wacce aka kira da Meenat yayi tana can Dining tana cin abincinta da alama bata San anyi bako ba,Yarima a ransa yace su wannan gaba daya kama sukeyi da juna amma Ma'eesha irin muryata ce da ita sak,Meenat ce muryarta tafi tamu siranta sabo da iyayinta ta maidata siririya,kayan sanyi ta kawo masa iri iri kana ta gaisheshi a ladafce ya amsa tare da cewa Mufeeda wannan duk kannenki ne? Ae mana wannan Ma'eesha wannan Meenat,yace ke kuma Mufeeda triple M kenan yeah Ma'eesha ta amsa muna dariya,Meenat yan mata uwar iyayi tana ji da yan matan ci sai girman kan tsiya watarana kamar wata yar sarki aka take komawa magana ma sai taga dama,watarana kuma ta zage ayi da ita,Muna zaune ana hira sai ga Ameer ya shugo an ci wanka yazo dan ya birgeni ni Mufeeda wacce ban san me yake bama,Maeesha har taji sanyi data ganshi kusa da ita ya zauna ta gaisar dashi,Yarima ya fara kishin Ameer ya zauna kusa da Ma'eesha kuma yaga Ma'eesha sai wani Fara'a take masa sun fara surutunsu da alama sun saba da juna,s hi kuwa Ameer gaba daya Hankalinsa na kaina yanda na hade cikin Lace riga da skert ba karamin kyau nayi ba,abinda ya bashi haushi ganin ina yankewa Aayan farce gashi kuma kafafun Aayan gaba daya saman cinyata ya dorasu yana kwance dan naji dadin yanke masa farcen.
Muna zaune daf da Magrib wata yar aiki ta shigo wai Meenat tazo tayi bako,Meenat tace ita bata da bako baza taje ba,tun kafin ta fara magana Ameer ya fara dariya,haka Aayan ma,nima na gane me suke nufi ko irin su Kwaja ne suka zo,Yarima yace mene haka daga ana kiran yarinya zaku fara mata dariya bai dace ba,Yar aikin tace a wata fyallelliyar mota yazo Hajiya da gani dan wanine,Nace mu ai bamu damu da wani me mota ba ko talakane indai yana da aikin yi,halaye masu kyau to alhmdllh zamu bashi ba wani sai me mota ko kudi etc,Aayan yace Pretty jeki kiji idan Bai miki ba ki dawo,kawai sabo da Aayan ne yace shi yasa ta figi Hijab tana fushi zata fita,nace ba kwalliya haka za a je? Kallona tayi kamar zatayi kuka ta fita abinta haka, taga mota iya mota tana jira taga wani Handsome ya fito sai taga Fela Gala da gani ba motarsa bace arota yayi, fitowa yayi tare da tsayawa yasa Hannu a aljihu harda Harde kafafu ya basar a jikin mota sai yanzu ma ta gane Ashe Motar tana ganin su Haneefa a cikinta,wato sune suka bashi aro azo a raina mata hankali.
Ko saurarar Fela batayi ba tayi gaba abinta sai gata ta shugo kamar zata fashe tana wa Aayan magana dan Allah Yaya ka ganshi can ya biyo ni har gida wlh dan Allah ka koreshi sune suka kara turoshi, Ma'eesha tace Fela Gala ne wlh tun daga sunan Yarima shima ya fara dariya bai Sha dariya ba sai da ya leka ya ganewa idonsa harda rike ciki sabo da dariya,Ameer kuwa ba a magana,Aayan ne ya fita ba shiri yayiwa Nasuru fata fata da gudu ya fice daga gidan ya bar motar dama ta gidan ce.
Meenat ta kalli Ameer tare da zuba masa Harara ta wuce Bedroom ta barsu suna bawa Yarima labari duk kwalliya da iyayin Meenat irin su Nasuru Fela ke zuwa wajenta,Yarima ya kalli Ma'eesha tare da cewa to ke yar ficika wanne kala ne naki? Dariya sukayi Sabo da Fela Gala ne yace mata Yar ficika,Maeesha tace ni yarinya ce ba yanzu ba,wani dadi Yarima yaji a ransa,Maeesha kuwa a ranta cewa take insha'allah Ameer ne ma,Shi ko Ameer tunani ma yake yaushene zai mallaki Mufeedansa,Ni kuwa ina nan zuciyata dankare take da son Mijina Aayan wanda naga Sam bai damu dani ba.
Sallah sukaje masallaci har Isha basu dawo ba,lokacin na tattara su Meenat muna kitchen muna karasa abincin da muke,suna dawowa na fito da ludayi a hannuna ni ga uwar girki na manta ma da Ludayin juya miyar na fito,Ameer yace ina zaki abun miya kuma? Nace na manta sauri nake nasan Babyna yanzu wanka zaiyi,Ameer nan take mood dinsa ya canja amma ni ban gane ba nace bari ka gani na koma kitchen na ajiye ludayin na fito naji muryar Ameer yace mu dai ki koma ki karasa mana abincinmu yaran nan jagwalgwalo zasuyi mana,murmushi nayi nace sun iya sosai ba matsala,ya kara magana pls Aunty kije ki karasa da kanki,nufin Ameer dan kar naje wajen Aayan shine ya hada min wayo wanda ban sani ba ni kuma sai na koma kitchen din,n a tayasu muka karasa komai na barsu su gyara kitchen tare da shirya Dining,dana fito nace Ameer ina Aayan fa? Baki ya tabe yace suna wancen palon shi da Yarima,palon da ya fada min na nufa
Direct naje shiga palon naki muryar Aayan yana cewa kyaleta ai wahalar da kanta takeyi bari nayi ta gama shiga hannu zata ga wulakanci,sai suka tafa da Yarima,nan take naji jikina ya dauki rawar sanyi,tsoro da fargaba tare da bakin ciki ya dirar min,ban san wa suke nufi ba,ban san akan me suke maganar ba sai na fassara maganar da naji kawai ba bincike ban tsaya naji dalili ba ko da wa yake nufi kawai sai na yanke hukunci cewar ni suke nufi dani suke,wato ni ya gano ina sonsa wahalar da kaina nakeyi,ya bari na shugo hannu ya wulakantani,ni zai wulakanta ma tab lallai dan Adam,duk abinda nakeyi Ashe baya gani a banza sai ma mugunta da yake hada min,nan take na fara tunano tun farkon haduwarmu irin tsanar da ya nuna min,Ammah ta da suka kashe min tunda sune suka jawo duk so yasa na manta,har aurenmu irin abinda ya dinga min a farko na wulakanci ina ta binsa,so yasa na manne masa nake kai kaina har dakinsa na sakar masa jiki,nasa yaji dadi,na godewa Allah da yasa ba ayi sex ba.
Mata da dama suna irin wannan daga jin magana bata kai ta kawo ba,basu san ma akan me akeyin ta ba,amma da yake kullum a zargin mazajensu suke irin ko sun daina sonsu,ko suna kula wata,musamman ace suna da kishiya ko zai kara aure,ko wani dalili yasa dai taga mijin ya dan canja to zargi zata kasance a ciki iri iri,komai yayi laifi ne a wajenta,magana idan ta ji ko da abokinsa sai ta fassarata ta koma tashin hankali Babba,wata ma har abokin zata daina kulawa,ko ta masa rashin mutunci,miji na neman aure abokin dole shine a gaba wai dan me zaiyi nan fa zata kulla masa wata ma sai ta rabasu sun bata sun daina abotar,wata kuma duk abokansa ta daina kulawa ko ta ci musu mutunci wai sune suke zuga mijinta,duk da cewa ana samun masu hakan amma mata mu daure mu daina zargi tare da saurin yanke hukunci,ko magana akayi sai a dinga fassara ta bai bai sabo da ba a son zaman lfy.
Ni dai ina tsaye naji kamar ma zazzabi zan fara sabo da yanda nake son Aayan ko kaina ban so haka,bani da burin da ya wuce naga ya soni back amma sai gashi abinda naji ma daga bakinsa,Hawaye na share na daure na shiga palon fuskata ba walwala nayi Sallama suka amsa,Nan take Aayan ya kafeni da idonsa yana ganin yanda lokaci kadan na fita daga hayyacina,dazu lfy lfy muke,kamar ma kuka nayi,ganin yana kallona nayi kasa da kaina,tunaninsa ko yan gidansu ne suka yi min rashin mutunci ya tabbatar idan kuwa sune suka sa na dawo haka yau sai anyi yaki a gidan nan,baya son a taba masa ni yanzu ko kadan, kasa jurewa yayi yace ina zuwa Yarima yaja hannuna mukayi waje dashi muna fitowa a jikin kofar yasa yatsansa tare da dago da fuskata yana kallona sannan a hankali yace lfy? Me akayi miki? Nayi shuru,Hajja ce? Su Haneefa nan ma shuru sai Hawaye dake biyo min a kumatuna a raina ina kara cewa yanzu wannan zankadeden rabuwa zaiyi dani,shike nan baya sona? Yace am asking u me suka miki ya fada da tsawa,duk ya shiga damuwa lokaci guda ya rude Allah sarki So,so banza ne kawai sai ya bani tausayi kuma na batawa wanda nake so rai,har bana ganin laifinsa sai nawa sabo da Aayan baya laifi a wajena so hana ganin laifi,tunowa da maganarsu dana jine yasa na kara birkicewa,kawai nace ni ba wanda ya min komai kawai ji nayi bana son auren Kasuwancin nan ko nawa zan samu,ko yanke talauci ne wlh bana sonsa dan Allah ka sakeni na tafi, wani dum yaji maganar a bazata to ko dai itama sun mata wani asirin ne ko kuma sun sa mata wani abu taci ai ko wlh bazai iya sakinta ba har abada sai dai duk inda zata je da aurensa,jikin Bango ya Dafe kawai yayi shuru yana Innalillahi kawai yake maimaitawa duk zarginsa tunaninsa Su Hajja ne ko asiri ko kuma wani abu suka mata wanda baza ta iya zama ba, da kyar ya dago muka hada Ido sai da na rumtse Idona yanda bazan iya kallonsa ba ya Zama wani iri idonsa yayi jajir,Hannu na ya figa kamar zai tashi sama ya jani muka Haura samansa har Bedroom ni dai kawai binsa nakeyi,a ciki ya tsaya tare da rike kugunsa da hannu biyu kansa ya daga sama yana danne lips dinsa na kasa da Hakoransa yama rasa ta ina zai fara, maganarsa naji a hankali yace Mufeeda! na kalleshi tare da sadda kaina kasa,yace ki fada min me ya faru dake me kike ji me yake damunki ko kuma a gidan ne wasu suka ce miki wani abu ni dai nasan ban miki komai ba,ko kema sabo da bamuyi Xxx ba zaki tafi? Da sauri nace a'a wlh ba haka bane,yana kallona yace to ko bana Haihuwa kike nufi? Nan ma kafin ya rufe baki nace wlh ba wannan bane,to mene tell me,karki rufeni ko ki cuci kanki just tell me what's is going on? Ina Hawayena nace ni kawai na gaji da auren ne Bana son kudin yanzu,Wait bafa Business muke ba wannan wasa ne kema kin san aure ne na sunna aka yishi ba wai akan kudi ba,nace ae na sani kawai bana son auren ne nace ma ni bazan zauna ba kawai,ok yace ko gidan nan ne bakya so? Fada min sai na Canja muku gida,kai na girgiza a'a, yace ko Wacce kasa kike so fada min wlh zamu koma can indai kina so,a raina nace jibeshi kamar gaske salon ya kara mallake min zuciya yaji dadin wulakantani da kyau to bazan je ba,nace bazanje ba ni a fili,Abuja fa?nace ko villa ne banso,to kiyi Hakuri idan wani abu aka yi miki addua akeyi akan komai ba fushi ba haba yan mata nan ya dinga lallashina,sai nayi kamar zan Yarda naji tausayinsa sai kuma na fasa nace nifa bazan zauna ba.
Yana gajiya ya tamke fuska ba mutunci yanda na sanshi tun farko,nan take naji tsoronsa jikina ya fara rawa, tahowa yayi kamar zai makeni na fara ja da baya yana Huci yace bari kiji bude kannenki wallah kinji na rantse har uku bazan sakeki ba kuma ba inda zakije idan kika fita ma ko gate ne bada izinina ba sai munyi Shari'a dake a gaban Allah ban yafe miki ba,kiji ni da kyau ba wani Business auren za ayi as from today ni kuma duk Hakkin ki daga yau zan fara baki,yana gama fadin haka ya kwanta a saman Bed yana Dafe kansa dake Sarawa, tausayi kuma ya bani sosai yanda ya nuna ya damu a kaina gaba daya sai na tsani kaina me yasa nayi haka,amma dai zuciyata ta hanani na hakura,ido ya rufe sosai still yana Dafe da kansa ya rike sosai da alama ciwo yake masa da yawa,Hankalina ya tashi nima,mikewa yayi tsaye kamar wanda yasha giya yana maye da tangadi,haba ban san sanda tausayinsa ya gama rufeni ba gaba daya naga ya fini shiga damuwa yazo ya ratsa ta gefen zai wuce ya fita tuni na damko hannunsa ya tsaya cak tare da juyo da fuskarsa ya kalleni gabansa na koma tare da fadawa jikinsa na rungumeshi kam kam sosai da sosai kamar za a kwace min shi, baiyi hugging dina back ba,da kaina cikin kunnensa na rada masa Rug me back am so sorry, bai kulani ba babu zato naji bakinsa cikin nawa ya fara tsotsa ya rabani da kasa dan dagani yayi sama yanda tsayinmu zaizo dai dai ba sai yasha wahalar sunkuyoba,haka muke tsotse bakin juna kamar mun samu wani kayan dadi na tsotsa,wannan kiss din yafi na kullum dadi,gardi,tare da nishadi,yanda nakeji ya zarce na fada muku,muna ta yi ba ji ba gani kamar zamu cinye kanmu ko nayi kamar zan kwace bakina sai ya kara rikeni kam ya hanani sai da muka dauki dogon zango a haka sannan da kyar na zare jikina daga nasa,amma duk da haka kara jawoni yayi jikinsa tare da fara lashe min wuya,tsigar jikina tashi take kawai gaba daya ya gama kara min sonsa a zuciyata, da kyar nake iya tsaiwa da kafaguna shima haka,ya fara kokarin cire min kaya na tuna yayi maganar hakki dazu da sauri na rike masa hannu tare da cewa abinci still dai ban saki raina ba bana wani nishadi kamar dazu,kyaleni shima yayi fuska ba walwala yace let's go,sai da muka saita kanmu sannan muka sauka kasa,Gaba dayansu Har Yarima da Ameer suna Dining suna ta cin abincinsu muka sakko duk kayanmu ya nuna da gani anyi yamutse yamutse,ga T-shirt din Aayan Fara kar ce duk jambakina red da Powder a jiki duk na shafa masa ba tare da mun sani ba sabo da murzar juna,Yarima da Ameer duk sun gane me akayi,Meenat ma ta gane gani ba jambaki a bakina sannan duk ga wani nan a bata gefen bakina,Aayan harda digon jambakin a hancinsa duk sai yanzu ma muka kula da hakan,Yarima sai dariya yake kunshewa yana kallon Aayan, dan Iska wlh zaka bar gidan nan banza munafiki Cewar Aayan,Yarima yace to me nayi kuma? Bayan ka shanyani,Ameer kishi ya hanashi kallon kowa kawai tura abincinsa yakeyi,Aayan har yau yana cikin damuwa ya kasa cin abincin kuma yunwa yake ji,ni kuwa bakin ciki baya hanani cin abinci ko cuta nake sai naci na koshi haka nake bare kuma kafin naji Maganar da su Aayan sukeyi tun a kitchen muna girkin na cika tumbina, ganin ya kasa ci na Mike tare da Zama kujerar dake kusa da tashi zan bashi da kaina,kafin na fara Ameer ya ajiye spoon yace ina zuwa bari nayi waya ya fice da sauri zuwa part dinsu,Yarima yace nima tafiya zanyi Ma'eesha zo ki rakani mota nan yayi mana Sallama suka fita,Aayan yace sai nazo zanyi maganinka ya furta da alama kawai danne bacin ransa yakeyi,Meenat ma tuni tayi Bedroom zata fara karatu,daga ni sai shi ya Dafe kai tare da rafka tagumi da gani yana cikin damuwa me yawa.
Hannun da yayi tagumi na janye a hankali ba tare da nace komai ba na ebo abincin a spoon na fara bashi da kaina yanda yake ci zaka San baya jin dadinsa ko kadan,kamar kurame haka muke har yace ya koshi nace ko spoon biyar baka ci ba fa? Zan fara masa magiya ya Mike kawai ya haura sama ya barni a nan,ban damu ba na tattara komai na kai kitchen tare da gyara komai na shiga Bedroom dinmu nayi wanka da duk wani abu da zanyi nayi nasa Night gown dina da kawata Sayyah ta bani wai inji mamanta kala Uku hadaddu amma basu fiye tsaraici ba nasa light blue din masha Allah nayi gaskiya karshe na daura ta samanta na fita lokacin Ma'eesha ta dawo daga wajen Yarima tana nuna min chocolate masu Uban yawa da kudi masu yawa wai a bani inji shi,na karba nayi godiya nace bari na nunawa Aayan kafin Ku fara sha nayi waje zuwa Bedroom dinsa,gefen Bed na hangoshi a zaune yayi shuru kawai yana kallon sama da alama tunani yakeyi yaji Sallama ta,amsamin yayi kawai tare da kwanciyarsa saman Bed ya barni a tsaye,banji dadi ba ni kaina muna zamanmu lfy na jawo bacin rai kuma shi dama kafin a lallasheshi aikine.
Haneefa ce Zaune tare da Mommynsu suna hira,Mommy tace Ameer naga fa kamar kwanan nan ya Mannewa wajen yan iskan can a part dinsu ban san ko Hajja tasan labarin ba,Haneefa tace Mommy ki barshi ai da alama bata sani ba gwara ma da kika tuna min bari naje na fesa mata tayi maganinsa ya daina zuwa na tsani Su Mufeedan nan Shegu wai su masu kyau,Mommy baki ta tabe tare da cewa je ki sanarwa Hajja ni ma yau zan fadawa Abbi abin na Ameer yayi yawa, da sauri Haneefa ta tafi part din Hajja,ta samu Hajja sai Mulki take zubawa tana wani takama da isa tare da bawa yan aiki umarni.
Haneefa ta zauna gefenta tare da cewa Hajja wani labari na kawo miki marar dadi so sad wlh abin kunya ma,Ina jinki Hajja ta furta tana gadara,Haneefa ta gyara Zama tare da sanarwa Hajja yanda Ameer ya koma bangarensu Mufeeda.
Hajja da masifa tace to azukwi uwar munafunci me yasa kuke takurawa Ameeru ne,ina ruwanki Algunguma to nasan da zuwansa aikina yake ni na turashi,kinzo da guntun munafuncinki ai zai shigo ne zan fada masa me kika ce ya farfasa miki jiki,Haneefa ta fara bata hakuri daga fadar gaskiya sai a lullubeni da fada to daga yau bazan kara fada ba ko mene zai faru ya faru,Hajja ta dakko yar sandarta ta karfe tayi kan Haneefa da gudu ta fice ta bar Hajja na Masifa ta gaji da Gulmar Ameeru da akeyi a gidan nan.
0 comments:
Post a Comment