"Abba......yunwa nakeji,tun dazu mommy tace zata dafa mana indomie......bata gama bane har yanzu?" Idanunsa ya zubawa yarinyar,a nutse yace
"Bakuci abinci bane yau?" Kai ta gyada masa
"Eh,momy tace tana jin bacci,kada mu dameta,musha tea,idan ta tashi zata dafa mana,har nawwara ma ta zuba ruwan tea din a qafarta,tayita kuka" lumshe idanunsa yayi,wani abu ya taba ransa,sai ya duqa a hankali tana laluben qafan yarinyar yana son ganin wajen,dai dai sanda yaji an murda qofar an kuma budeta,sanin waye ya sanyashi qin waiwayo yaci gaba da duba qafar nawwaran.
Matashiyar macace,wadda a qalla zata doshi shekara ashirin da takwas ko kuma da tara,wankan tarwada ce wadda kalar fatarta ta kusa juyewa ta baqaqe,banda hutu da jin dadin data samu,mai matsakaicin tsaho ce,tana da 'yar qiba kadan da tudun hanci,idanuwanta basu fiya girma ba,saidai tana da 'yar cikar gira da kuma fararen haqora da suka sake bayyana duhun fatarta.
Sanye take da kayan bacci a jikinta,kanta saye cikin wata hular zaren lilo da qabilu sukafi amfani da ita,zaka tsammaci qarfe bakwai ne na safiya a lokacin,saboda yadda fuskarta ke nuna alamu na bacci,uwa uba kuma sleeping dress din da take sanye dashi.
Tsaye tayi daga bakin qofar tana qare masa kallo,fushi takeyi dashi sanda ya tafi,ta kuma ci alwashin sai yaga fushin nata,saidai tun bai jima da tafiyar ba kewarsa ta dameta,idanuwanta kuma suka damu da son ganinsa,ta ajeshi qololuwar matsayi a rayuwa da kuma zuciyarta,shi din na musamman ne,tunda har yana da qarfin ikon juyata da sauya mata ra'ayinta zuwa wadanda yakeso,abu mafi girma kenan dake haddasa sabaninsu,kowa da alqiblar da yake kalla tsakanin shi da ita,hakanan kowa yana ganin akan dai dai yake.
Ci gaba tayi da kallonsa har ya gama duba qafar yarinyarshi,ya kuma tofa mata addu'o'i,tayi tsammanin zai waiwayo gareta ne tunda yaji shigowarta,amma sai taga yana yunqurin miqewa hadi da sake baiwa qofar baya,don haka ta saki hannayenta data rungume tana qarasowa cikin dakin,bayan ta dan bata fuska
"Dama kuna nan kuka sanyani inata bulayin nemanku cikin gida?,sai dana fita gate sule yacemin ya ganku tare?" Maganarta ta qarshe ta sanyashi waiwayowa,idan ba gizo idanunsa yayi masa ba yaga shacin kayan bacci a jikinta,tana nufin haka ta tafi wajen sulen nemansu,mutum ne shi mai tsananin kishi,ko kusa ko alama baya daukan sakaci ko ganganci akan iyalinshi
"A hakan kike tafi cigiyarsu har waje?" Ya jefa mata tambayar a nutse,saidai kuma wani bacin rai na daban bayan wanda yake ciki ke bijiro masa.
Sai a sannan kwanyarta ta ankarar da ita zallar wautar data tafka,duk yadda taso taja zarenta itama har sai ya gane yayi mata laifi ya bata haquri take komai ya rushe mata,saidai cikin sa'a ta kama zaren qaryar da takejin zata qwaceta
"Ta yaya zan fita a haka?,na cire hijab dina a falo" tana gama fada ta kauda qwayar idanunta daga cikin nasa,tana jin yadda yaketa kokawar ganin sun hada idanun,hanya guda daya da yake iya karanto qarya ko gaskiyarta,ta saara masa ta wannan fannin,kuma tasan ba banza ba,tunda aikinsa ne.
Bayason ya sake dagula al'amuran,dole shima ya janye nasa idanun
"Koda wasa,koda ganganci kada ki sake hakan ta faru" ranta ya baci,ta zumbura baki gaba,daqyar kamar wadda aka yiwa dole tace
"Tom" saita maida dubanta ga yaran ba tare data wani damu da yi masa sannu da zuwa ba ko tambayarsa hanya
"Kuka sani dafa muku indomie ashe ma ba yunwa kukeji ba kuka katsemin bacci na" sai taja dan siririn tsaki
"Saiku tashi muje kuci,idan kuma bakwaci a bayar da ita" mimi ce ta maqale kafada
"Nidai mommy banason indomie" ta hasala sosai,dama ga fadan da yayi mata
"Baki isa ba tunda na dafa sai kunci"
"Ji mana" ya dakatar da ita,saita waiwaya tana dubansa,ya ritsata da idanun nan nasa dake kassarata,bata buqatar ta sauko don haka ta kauda kanta
"Babu lallai yaro sai yaci abincin da ya riga ya ginsheshi,ki deba musu cikin abinda kika dafa min,sauran ki kawomin shi falo na" fuska ta bata,cikin jin shakka murya ciki ciki tace
"Ni ban dafa maka komai ba" ya zuwa yanzu mamakin hafsat ne ya kamashi,cikin son danne bacin ransa yace
"Saboda me?"
"To ai bakacemin ka taho ba"
"Bakisan yau zan dawo bane?"ya jefa mata tambayar cikin salo na tsitsiye,saita rasa amsar bashi,saboda wayar qarshe da sukayi bayan sun gama ya tura mata tex na date da time na dawowar tashi,kawai ta share ne saboda tana jin haushinsa,tazo kuma ta raba dare tana kallo,shi yasa da safen ta dinga barci kamar matacciya,sai da yaran suka dameta da kukan yunwa sannan ta rarrafa ta dora musu indomie,ta rage wutar ta koma baccinta bayan ta zuba komai da komai,da nufin ta sake matsewa kafin ta dahu,a wannan tsukin ya shigo,kuma har ya kwashe yaran bata snai ba,uwa uba ma kuma manta shaf da batun dawowar tashi.
Idanunsa ya lumshe yana jinjina kai,ya taka zuwa gaba kamar bazaice komai ba,sai kuma ya dakata ba tare da waiwayo ba yace
"Ki gyaran sashe na,sannan ki dafa min abinda zanci kafin na gama" daga wannan ya wuce bandaki.
Da kallo ta bishi har ya kammala wucewar ya rufe qofa,janye idanunta tayi tana sauke gauron numfashi,sai kuma tsaki ya biyo baya,bata dauka zai dauki abun da sauqi haka ba,duk da tasan halinsa,yakan iya share laifi yayi kaman ba'ayi masa ba,amma horonsa kuma sai yafi miki ciwo fiye da komai,a duniya babu namijin da ya taba yi mata abinda abbas din yake mata,batasan wanne irin so take masa ba daya samu dama da yawa yake juyata har haka ba,saita dakata da tunanin ganin bata da isashen lokaci,ta tarkata kan yaran ta sauka dasu zuwa sashenta,ta juye musu indomie din duk da sunce ba zasu ci,ta kunna musu kallo ta wuce kitchen tana tunani me zata dafa wanda bazai jaa mata lokaci ba.
Sai data kwashe mintuna kusan biyar tana dawurwurar abinda zata dafa masa cikin kitchen din,daga bisani ta yanke dafa masa jallop din taliya,duk da tasan cewa kwata kwata bata cikin lissafin abincinsa,hasalima saboda ita da yara yake ajjiyeta,banda haka tasha zamanta,to amma kuma bata da wani sauran option,hakanan bata da idea din wani abu me sauqi da sauri baya ga taliyar,kuma koma meye dai oho,indai ta dafa ta bashi ai ta fita ko babu sabulu.
Sai data wanke tukunyar da zata dafa abincin a ciki,saboda tun jiya datayi baqi qawayenta ta bata su gaba daya,ta kuma jiqasu sa zummar yau idan ta tashi aiki ta tsaftacesu,sai gashi kuma yayi mata dawowar ba zata.
Tana hada girkin tana mita cikin ranta,taja tsaki yafi a qirga
"Dole ne ma na samo 'yar aiki gaskiya,haba dame zaka ji?,kashe kanka zakayi?" Ta dinga gunaguni ita daya,tuntuni takeson daukar mai aiki,amma saboda wani banzan ra'ayi nashi da kuma kafiyarsa yaqi aminta,alhali kuma aiki yayi mata yawa,ga yara gashi karan kansa.
Sanda ta gama ta juye masa a plate ta sanya wani ta rufe ta fito,a falon ta samu su mimi duka sun sheme barci ya daukesu,bacci dama sukeji,amma yunwa da rashin kyawun tsaftar jikinsu ya hanasu yin baccin,ga indomie dinta nan sunci wadda zasuci sauran sunyi wasa da ita sun sake d'aid'aita falon,sai a sannan ta lura da wankan da yayi musu,baki ta tabe
"Kwado sarkin tsafta,ni wallahi bazan kashe kaina da wannan shegen son tsaftar taka ba" daga haka ta sanya kai tana ficewa zuwa sassansa.
Zaune ta sameshi saman kujera riqe da remote yana kallon labarai,armless white shirt ce a jikinsa da three quarter wine color,ya miqa dogayen qafafunsa saman center table din yana kadasu a hankali.
Kallo daya yayi mata ya amsa sallamarta yana maida dubansa ga tv,ta qaraso dab dashi ta janyo daya table din ta dora plate din abincin ta matso masa dashi,a gajiye take jinta tubus don bata sanyawa ranta wannan aikin ba,don haka ta koma kan daya daga cikin kujerun ta zauna
"Sannu da zuwa" hankalinta ya bata tayi masa a sannan,sai daya sauke qafafunsa qasa ya zauna sosai sannan ya isa amsa mata,ya bude abincin yana kallonsa yayin da ita kuma take kallonsa tana jiran me zaice,kamar bazaici ba,sai kuma ya sanya fork a ciki ya debo yakai bakinsa.
Idanunsa ya ragewa girma yana tauna taliyar cikin bakinsa,kamar mai tauna mutuwa haka yaji,baisan ya zaima hafsat ba,baisan sai yaushe zata nutsu ta gyara tukunyarta ba,kudade da yawa ya kashe wajen ganin ta iya abubuwa da dama saboda inganta rayuwar aurensu amma har yau babu riba,tana sane?,mugunta ce ko kuma meye?,idan kishi ne da nuna masa zallar soyayya a baki ita din tana kan gaba,amma ya rasa abinda yake damunta.
Salin alin ya maida murfin ya rufe sannan ya miqe ya wuce bedroom dinsa,binsa tayi da kallo tana jiran taji me ya faru?,ba jimawa ya fito sanye da jallabiyya mai santsi dinkin qasar morocco mai gajeran hannu
"Ina key din mota ta?" Ya tambayeta yana sanya qaramar hula saman kansa,maimakon ta amsa masa saita miqe ta wuce gaba zuwa dakin nasa,ta jawo locker inda ta zuba muqullan ta dauko ts miqa masa,saiya karba
"Banaso na dawo na samu wajen nan a haka" ya fadi yana yin gab,tana son tambayarsa ina zashi amma bai bata damar wannan ba,tun daga fuskarsa har yanayin yadda yayi mata ya fice ba tare daya bata hanzari ba.
*_ASSALAMU ALAIKUM_*
_Barkanmu da dare da fatan kowa yana cikin qoshin lafiya_
_Akwai abinda muka turo tallansa na WOMEN EMPOWERMENT PROGRAM(KUDI KE KIRA),so please duk wadda batayi pyment ba ta jira tukunna kada tayi,akwai wani CONFIRMATION da mukeso mu samu a kansu_
*Idan komai ya daidaita zamu sanar muku*
*_idan kikaci gaba da pyment kuma bada yawunmu ba_*
*Muna godiya sosai*
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 12
*Widad*
Dole qanwar naqi ta fara sakin jikinta,duk da cewa gaba daya hankalinta yana kan gida,abu daya ke mata burki ya sanya mata ko kwanto da kuma qaunar komawa idan ta tuna case din data bari a gidan.
Satinta guda uncle muhsin ya maidata makarantar dasu nujood ke zuwa,baiyi shawara da kowa ba,hakanan bai gayawa kowa ba,yayi dai karambani ne,yana fatan karambanin nasa ya samu nasara.
Makarantar boko ce hade da islamiyya,qarfe hudu ake tashi zuwa biyar yawanci duka yara suna gida,sosai widad tayi murna,don ita dinma akwai son karatu,cikin sati guda ta sake sosai abinta,zaka dauka tsohuwar daliba ce.
**********
K'arfe takwas da rabi na dare ne,bayan su widad sun gama cin abincinsu su wuce daki,daga hajjaa sai uncle muhsin kawai a falo din,ta qaraso tana ajjiye masa zobon data dafa masa,ya dauka yana mata sannu ya fara kurba,sai ta gyara zamanta
"Abba na cike foam din nan fa" ba tare da ya dubeta ba yana ci gaba da aikinsa bayan ya tura glass dinsa baya kadan yace
"Ma sha Allah,to Allah yasa a fara a sa'a" fuska tadan bata kadan
"Amma fa abba akwai matsala" sai a sannan ya waiwayo ya kalleta
"Matsala wacce iri?"
"Yara abba,bansan ya zanyi dasu ba,babu kowa a gida bare nace driver ya kawosu nan su zauna tare,kuma daga qarfe hudu zamu dinga farawa zuwa shida" ajjiye cup din hannunsa yayi yana dubanta
"To yanzu ya za'a yi kenan?" Shuru ta danyi tana juya hannunta,sannan daga bisani tace
"Eh to,da wai cewa nayi ko gidan hajiyan gida dubun zansa driver ya dinga ajjiyesu,tunda babu nisa wajen namu daga nan,idan yaso in mun tashi qarfe shidan sai na shiga na daukosu mu zarto gida?kaga kwana biyar kawai an gama" Kai ya jinjina
"Qwarai kuwa,hakan ma yayi"
"To abba ko zaka gaya mata kada suga yara kawai?" Dan dubanta yayi
"Ke hajiya,ai fada zatayi tace don zasu zo sai an gaya mata?,ta wuce duk yadda kike zato,kamar uwa take a wajenmu,ba damuwa idan kinje kyayi mata bayani"
"to shikenan ba matsala,godiya nake oga"
"Baki da damuwa" ya fada yana murmushi tare daci gaba da aikinsa,ita kuma ta soma tattara kayan abincin da ya gama dasu ta wuce dasu kitchen,sannan ta biya ta dakinsu nujood din ta gaya musu gobe kowa ya dauki kayan gida cikin jakarsa zata saukesu ne gidan hajiyan.
***********
Yau din tun safe da ya tashi dukka wayoyinsa na akashe,bashi da niyyar fita sam sam sam kamar yadda ya qudurta tun jiya,zaunawa yaso yayi a gida ya huta,saidai ra'ayin hutun ya kau daga ranshi daga sanda gari ya waye,sai kawai ya hau sanitation na gidan da kanshi,yana yi su mimi na biye dashi yana tayashi da aikin surutu,surutunsu bai dameshi ba,duk da kasancewarsa mutum marason hayaniya,sai surutunsun ya zame masa tamkar abokin hira.
Sanda ta tashi ta taddashi yana aikin sai tayi kamar bata ankara da me yakeyi ba,ta qaraso inda yake tsaye saman wata stool yana cire yana,rungume take da hannayenta,tadan rusuna kadan tana fadin
"Ina kwana" kansa yadan sauke kan,ya dubeta da manyan idanunsan nan masu kwarjini,a dai dai wannan lokacin kamata yayi ace ta kammala gyaran gidan gaba daya,ta kuma shiryawa iyalinta abun buda baki,shike kwance yana hutun da takeyi amma reshe ya juye da mujiya
"Lafiya lau" ya amsa mata yana maida kansa ga aikin da yakeyi,sai taji sam sam ba dadi,tunda ya dawo babu wannan tarairaya da soyayyar tasa mai tsaya mata a zuciya,gaba daya fushin ma data tanada zatayi kamar ma ya fita yin fushin
"Dame zan taimaka maka?" Tayi qarfin halin fada,batason ya soma nuna mata halin ko in kula din nan nasa dake mata ciwo,bai iya miskilanci ba ko kadan,idan ya fara sai kinji babu dadi
"Inajin yunwa yara sukeji,ki sama musu abinda zasuci" ya amsa mata,sai ta sauke hannunta dake wuyanta,ta wuce kitchen dinta,tunda tuni ya gama da sassansa ya dawo nata.
Tea ta hada musu da bread ta soma basu,amma da yake sun gaji da cima daya sai suka watsar suka kama gabansu
"Ubanku ya bataku da cima,bazan iya wannan bautar ba,idan na gama kwaci gaba daya" ta fada tana nazarin abinda zaga dafa.
Da yake tasan ita din mai laifi ce,duk da batajin tayi laifin har cikin ranta,saita zage ta bata lokaci ta shirya breakfast mai kyau,gasashen kifi tayi da chips,ta dafa masa ruwan tea din da yafiso,sanann ta dama masa kunun gyada still.
Sanda ta gama bata gansu falon ba,sha biyu saura,sai ta jere komai a dining sannan ta wuce dakinta.
Wanka tayi ta shirya kanta da kyau cikin wata atamfa,ta feshe jikinta da turarukan da tasan yafiso,wadanda takan jima batayi amfani dasu ba,duk da ya siyo su din amma sun zama kamar decoration saman mudubinta,takan ce bata da time na wannan qaqale qaqale din,bata shafawa fuskarta komai ba illa mai,ta taje kanta tana bata fuska saboda yadda yadan dunqule waje guda,ta manta when last data tajeshi,tunda yasa qafa yayi tafiya ta sauke 'yan gyaran da takeyi saboda matsawarsa da kuma qoqarin ganin ta hanashi qorafi a kanta. Daurinta ta kawo gaban goshi saita zari wayarta ta fito.
Har yanzu babu kowa a falon,don haka ta zarce sassansa,tana tafe tana duba saqonnin wayarta har ta isa sashen.
Ita kanta sai data shaqi iska ta fesar,yadda ya gyara sashen yayi matuqar burgeta,komai yayi fes yana fidda qamshi,tun bai iya wasu aikace aikacen ba har ya zamana ya koya ta dole,yanayin aikinsa karatu uwa uba yanayin matarsa,mutum ne shi sa baya shiri da qazanta sam,duk yadda yakai gason abu ko zama a waje yakan iya haqura idan yanayin baiyi masa ba.
A falo ta samu su nawwara,sunyi fes dasu yayi musu wanka ya canza musu kaya,hakan yayi mata dadi sosai,ko banza ya rage mata wani aikin,dama tunanin yadda zata gyarasu takeyi a yadda ta gaji din nan,shi yasa bataso yayi tafiya wasu lokutan,duk da cakudewar aikinsa da yawan ayyuka wasu abubuwan shike dauke mata
"Bari na fito da abban muje muci abinci,ku zauna anan" ta fada tana sanya kai zuwa bedroom dinsa.
A nutse ta tura qofar ta sanya kanta bakinta dauke da sallama,idanunta suka sauka a kansa,yana tsaye gaban mudubi daure da guntun towel iya qugunsa,faffadan bayansa dukka yana a waje hadi da murdadden dantsensa,ya amaa mata ba tare saya waiwayo ba,jikinsa yake gogewa da wani qaramin towel din,saita maida qofar ta rufe a hankali ta soma takowa zuwa inda yake tsayen,tana jin qaunarsa da kewarsa na motsa mata.
Ta baya ta rungume shi,ta kwantar da kanta a tsakiyar bayansa tana sauke ajiyar zuciya
"Fushi kake tayi dani abba?" Kansa ya kalla a mudubi,tana bashi mamaki idan tayi wata maganar,kamar batasan komai ba,sai ya girgiza kai kawai yana qoqarin zareta daga jikinsa,don baya son ta bar masa wani feeling da zai dameshi,ya tabata kuma zance ya canza salo
"Me kika gani?"
"Abun ya motsa" ta fada a ranta,sai taqi bashi damar matsar da itan daga jikinsa ta riqesa gam gam
"Nidai don Allah kayi haquri koma meye,duk da kasan kaine kayimin laifi,amma a barshi ya wuce" ta fadi tana qanqamesa gam a jikinta.
Rainin hankalinta ya isa,baisan sai yaushe zata fara hankali,ta kuma fara gyaran kurakurenta ba,baisan sai yaushe zata gane haquri yake da ita ba,baisan sai yaushe zafa fahimci yawan uzurin da yake bata ba,sai ya sanya hannunsa ta baya ya jawota zuwa gabansa ya zaunar da ita saman kujerar mudubi yana kallon fuskarta,cikin tattausar muryarsa wadda a boye daga bayanta take cike da bacin ran da yaketa qoqarin binnnewa ya soma mata magana
"Saboda nace bazan biya bashin dubu talatin da kika ciyomin ba a matsayin ankon da bansan da zamansa ba bayan sati biyu da suka wuce na miki dinkunan da suka tasamma dubu tamanin shine na zama mai laifi?,wannan shine dalilin da zai sanya ko sau daya ki kasa daga waya ki kirani kiji ya nake bayan kinsan aiki na tafi mai hatsarin gaske?,banda ina da uwa kenan babu wanda ya damu dani?" Yadda ya aza mata idanunsa sai taji sun mata nauyi,cikin jininta ta dinga jin rashin kyautawa na tsarga mata,amma bataso tayi giving up da sauri,saboda tsabar qi fadi dake damunta.
Idanun nata ta zare tana kauda kanta gefe guda sannan ta soma magana
"Amma dai tsakani da Allah,a wadatar da Allah yayi maka meye a ciki?,ka zabi ka kunyatani cikin qawaye na akan fiddani kunya kenan?,idan yaso duk fadan da zakamin ma kayimin shi daga baya" kai ya girgiza,mai hali baya taba fasa halinsa
"Bazan karba abinda bani nace kiyi ba,bayan nasan ban gazawa gidana da iyalina da komai ba,suturar da zasu sanya ko mai matsayin mijin mace iyaka kenan,bazan yarda ki dinga daukomin basukan da basu da tushe bare makama ba,har yanzu wuyana baiyi wannan kaurin ba" ya fada muryarsa na qara nuba bacin ransa,dole tadan sassauta muryarta
"Yanzu dai tunda na mayar kuma baka siya din ba ba shikenan ba?"
"Eh shikenan,amma kada ki qara,ko meye kike da buqata ki gayamin,idan naga akwai sarari nayi miki,idan babu ki jira sai zuwa sanda ya samu"
"To ai shikenan" ta fada tana kauda kanta gefe,ranta yana suya tana qoqarin dannewa,shuru ya ratsa dakin,yana ci gaba da shiryawa,yasan abu ne me wahala ta buda baki ta bada haquri,ba yau ya fara ganin hakan ba,yanason mata magana kan yadda take watsar da kula da gidan dama jikinta amma kuma yasan koda yayi dinma kamar busa ce a iska,babu lallai ta dauka,don haka yayi mata zance mafi muhimmanci yanzu a wajensa
"Banga kina shirin komai ba,ko babu abinda zaki tafi dashi?"
"Zuwa ina?" Ta fada tana waiwayowa da sauri,kafeta yayi da ido kafin ya dauke ganinsa,ya soma gajiya da wannan kayan takaicin,saboda tsabar rashin damuwa tana nufin har ta mance da maganar su dashi kafin ya tafi?,ko tsabar rainin wayo ne?.
Bai amsa mata ba saboda baya jin akwai buqatar yi mata tuni,sai yaci gaba da shirinsa kawai,ita dinma ta tuna,duk da ba mancewa tayi din ba,amma tayi zaton zai bar maganar ne,tunda ta gaya masa ita babu inda zata bishi,ba zata iya barin bauchi ba.
Tana zaune ya gama shirinsa tsaf cikin qananun kaya,binsa ta dinga yi da kallo,ba banza ba take tsakanin kishinsa,tasan ko kusa ko alama babu marching ko kadan tsakaninta da abbas,tako ina ya zarta mata,sau tari qawaye da 'yan uwa kan furta kamar ba mijinta ba,kalmar data tsana kenan,wadda duk wanda ya fadeta sai sun haura dashi,idan kuma tana ganin mutuncinka ta bika da harara ko baqar magana.
Tsayawa yayi yana jifanta da wani kallo hannayensa zube a aljihun wandonsa,ya lura da yadda take binsa da wani mayen kallo
"Zan samu abincin ko na zauna kiyita kallo na?" Ya fada da dan tsokana kadan cikin muryarsa,duk da fuskarsa bata nuna hakan ba,dama kuma yawanci ita daya ke ganewa wasan tsokanarsa, mmurmushi ya subuce mata,ta miqe tana cewa
"Kaci abincin tukunna sai na zauna nayita kallon naka".
Har yanzu dai still taste na girkinta bai kai masa yadda yakeso ba,amma hakanan ya kama yaci,yana mai bata uzurin wataran zata qware,tunda a yanxun abincin yana ciyuwa alhamdulillah.
*RUMBUN K'AYA*π₯
*DAUDAR GORA*π₯
*IDON NERA*π₯
*A RUBUCE TAKE*π₯
*KI KULANI*π₯
*_uhmmmm_*ππππππππππ
*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*
*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*
*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️
*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*
*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*
*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*π₯π₯π₯π₯π₯
0022419171
Maryam sani
Access bank.
Shaidar biya tananππ»
09033181070
*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*
09166221261
π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+227 90 16 59 91
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*Thanks for choosing us*π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 13
Kusan suke cin abincin,ita dai tana ta biye musu ne amma cokalin kawai take juyawa cikin plate din,tuntuni sun jima da raba plate din cin abinci dashi,tare dai suke ci,amma kowa kwanonsa daban,tunaninta gaba daya yafi karkata kan yadda zata sake jaddada masa ba zata bishi kaduna ba.
Har ya kammala cin abincin ta rasa kalmar kamawa,ganin yana qoqarin tashi sai tayi gyaran murya,ya dakata da shirin tashin da yakeyi ya aza mata hankalinsa
"Abban mimi,nifa gaskiya ba zan iya binka kadunan nan ba,don Allah ka janye tafiyar nan dani" ta fada tana jin nauyin maganar,a mamakance yake kallonta,tsahon wasu sakanni sannan yayi gyaran murya
"Nayi tunanin mun gama maganar nan dake ko?" Kai ta girgiza
"Bamu gama ba gaskiya,bazan iya tafiya wata kaduna ba" ransa ya sosu,ta yaya yana son kare mutuncinsa da martabarsa ya tafi da iyalinsa don samun kariya daga sharrin shaidan amma tanason ingizashi zuwa ga hallaka?,kadunan bariki zai tafi shi kadai alhalin da iyalinsa ba gauro bane?
"Koda bakiso hakanan zaki tafi,kuma bama kaduna ba,duk inda aiki ya jefani hafsat haka zaki bini muje,wannan shine tsarina" yana kaiwa nan ya miqe tsaye yana shirin sauka daga dining din,sai itama ta miqe,wai me yasa ya fiya kafiya da taurin kai ne?,haka kawai tana cikin garinta cikin dangi da 'yan uwanta zai cizgeta ya tafi da ita wata uwa duniya?,itakam sam bata ga dalili ba
"Gaskiya babban mimi bazan iya barin dangina da kowa nawa da dan business dina dana fara ba na bika garin da bansan kowa ba,babu kowa nawa ba" ta fada adan hasale,kallonta yayi sai ya dauke kai ya gewayeta ya wuce,bashi da lokacin tsaiwa tanka mata ga yara zaune a wajen,sannan ma shi din ba mutum bane mai yawan son magana,banda Allah ya hadashi da ita mutum ne marason hayaniya,yafi qaunar zaman shuru da kadaici wani lokacin,shi yasa ko sabani suka samu bai fiya damunsa ba,yakan kebe yayi zamansa yana karance karance,idan kuma yara suna nan yayi sabgarsa dasu.
Binsa tayi har cikin falon tana maimaita maganar,yasan idan ya zauna ciwon kai zata sanya masa a banza,don haka sai ya dauki key din motarsa dake gefan tv stand ya fice abinsa kawai,yana amsa adawo lafiyan da mimi ke masa.
Komawa tayi ta zauna jabar saman kujera tana tuje daurin dankwalinta tayar gefe,wannan wanne irin maqalallen aiki ne da basu da aiki sai sassauyawa mutum gurin aiki?,daga can sai nan?,yaushe ma duka duka sauka dawo bauchin tana ta murna ta dawo gida?,to itakam wallahi ta gaji,tana son abbas matuqa tana tsakanin kishinsa,to amma aikinsa zai zama babban tarnaqi a rayuwarsu.
Tana nan zaune tana saqawa gami da kwancewa,mimi nata gaya mata nawwara na wasa da abinci amma hankalinta bai wajen,har sai da yarinyar ta fado da tea flasks dinsu ya fashe a wajen sannan ta farga,sai a sannan ta miqe tana banbamin fada ta nufi wajen,sai data durma mata dundu sau biyu a baya sannan tahau aikin gyara wajen,tanayi tana mita,yarinyar kuwa ta fashe da kuka,mimi ce ta matsa ta ruqo yar uwar tata tana goge mata fuska.
***********
Ranar da driver ya ajjiyesu gidan hajiya tayi mamakin ganinsu,ta danji fargabar ganinsu da uniform ba kayan gida ba,tana zaune a falonta tana lazumi bayan ta idar da sallar la'asar,da yake takan kwashi awa guda kafin ta kammala,ta amsa gaisuwarsu tana maida idanunta ga widad da take baquwar fuska a wajenta,saita dauke dubanta tana tambayar nujood ko lafiya
"Mommy ce tace muzo nan mu zauna,qarfe shida zatazo ta daukemu,makaranta ta shiga"
"To alhamdulillah" hajiyan ta fada tana jin hankalinta yana kwanciya.
"Bari muneera ta zuba muku abinci kuci"
"Zanyi alwala banyi sallah ba" widad ta fada,wadda tun dazun take jinta a takure,saboda yau nujood ta matsa musu basuyi sallah a makaranta ba.
Dubanta hajiya tayi,sai taji yarinyar ta burgeta,a shekarunta amma tasan kiyaye sallah,duk da tasan idan bata fara haila ba kadan ya rage ta fara,amma ko su muneera da suke 'yammata sosai wani lokaci sai tayi fama da su kan sallar,kiran muneera hajiya tasa nujood tayi,ta kaisu dakin baqi tace suyi sallar sai su fito suci abincin,duka suka miqe suka bita.
Ba jimawa suka gama sallar suka fito,muneera ta kawo abincin,hajiya na zaune daga gefansa tana lazuminta,jifa jifa tana kallonsu sanda suke cin abincin.
Yaran uncle muhsin din suna da nutsuwa da tarbiyya,amma sai taga nutsuwar widad ta fita daban,ita tafara tsame hannunta daga abincin,ta kuma gyara wajen takai kwanon kitchen,wannan duka aikin ummu ne,duk da bata aikin komai irin ta horas da ita qananun abubuwa irin wadan nan da kyau,kwata kwata widad din ba maison jiki bace,da karambani ma ta iya wasu abubuwan sosai,wanda take koya wajen anty madina,ko idan ta shiga sassansu Aafiya ko ramziyya.
Sunata sabgarsu amma tana zaune waje daya,ita gaba daya jinta take a takure,bata son baqon waje,tana da wahalar sabo kuma,wannan yasa ta qara tsumewa waje daya,Allah Allah take momy ta iso su tafi gida.
Zaman daya isheta sai ta fara taya muneera ninkin kayan hajiya,sun kusa rabi muneeran ta miqe tayi kwanciyarta,widad din ita ta qarasa muneera ta kwashe takai mata daki.
Shida da mintuna hajjaa ta iso a motarta,suna jinta suka fita da sauri tararta,widad ko murmushi tayi tana gyara zamanta,tana jin zama yazo qarshe sai gida.
Da sallama ta shigo falon hajiya na mata sannu da zuwa fuskarta da murmushi
"Hajiya ai ke za'a yiwa sannu,yau na hadaki da hayaniyar yara"
"O'o,o'o,aini deben kewa ma sukayi,yau babu zaman shurun nan" murmushi hajjaa tayi tana maida dubanta kan widad
"Kamar kiyi tsuntsuwa ki janyoni ko?,gani na iso sai gida" dariya ta danyi,hajiya ta dubeta
"Da alama kam,don tunda sukazo ta kasa sakewa,tana zaune waje daya"
"Ai akwaita da baqunta da rashin sabo,duk da dai dama bata da hayaniya sosai,ga oganni nan" dariya hajiya tayi sannan suka fara gaisawa,ta gaya mata aikin da zasuyi na kwana biyar din,tare da alfarmar zama da zasu dinga yi har na kwana hudu a wajenta
"Kin jiki hadiyya,banda abinki ba jikokina bane,har sai kin nema alfarma,ai nan dinma gida ne,Allah ya taimaka yayi jagora"
"Ameen hajiya,Allah ya qara girma".
Hajiyan nata tsaidata suyi sallar magariba amma tace sayi a gida,ta tattara yaran suka wuce gida suna yiwa hajiya sallama tare da cewa sai gobe,don dama su nujood gidan zuwansu ne su,suna kuma jin dadin zuwa gidan sosai saboda kirkin hajiya.
*********
Yammaci ne sosai daya kamata ace a lokacin yana cikin gida yana hutawa,tare da shirye shiryen barinsa bauchi zuwa kaduna,saidai bai samu wannan sararin ba,saboda fitinar da hafsat din keson tsirowa dashi,tun batun zuwanta kaduna da yace lallai sai tayi,ko a yanzun ma ya fito gidan ne saboda yadda ta tasashi gaba da nacin roqo harda qwallarta kan ya barta a bauchin,shi baisan wanne irin tunani ke gareta ba,baisan me yake damun kanta ba,kin gwammace kibar mijinki ki zauna da dangi?.
Wasu lokuta matsalolinta caza masa kai suke,sai ya samu ya kebe tukunna yake samun kwanyarsa ta huta,don haka ya zabi fitowa daga gidan.
Tun asali ba mutum bane shi mayawaci,idan ka ganshi a waje dalilin aiki ko kuma wata lalura ce ta kaishi,sau tari abokan aikinsa na yawan tsokanarsa,sam dabi'unsa kamar ba na dan sanda ba,saidai ya murmusa kawai,ba kasafai yake basu amsa ba.
A hankali yake tuqin nasa,kwanyarsa cike fal da tunani,sannu a hankali har ya qaraso junction mai bada hannu ya tsaidasu,motarsa na sahun gaba,yana iya wucewa idan yaso,to amma sanin doka da qa'ida ta sanyashi tsaiwa kamar yadda ya dace ace kowanne mutum ya tsaya din.
Hankalisa nakan radio din motar yana son kamo daya daga cikin tashoshin gidajen radio da yakan saurari labaran yamma,baisan me ya faru ba yaji tashin hayaniya,ya daga kansa da sauri yana duban gefansa inda hayaniyar ke tashi.
Matashin saurayi ne tsaye kusa da motarsa qirar 206 yana zazzagawa wani tsoho dake saman mashin masifa,yayi tsai yana duban matashin yadda yake haqilo kamar zai kaiwa mutumin duka,mutane har sun fara taruwa ana bashi haquri,ci gaba yayi da nazarin matashin dake dukan saman motarsa yana fadin shifa sai an biya shi,daga gefe daya wani jami'in dan sanda ya fara ratsowa cikin mutanen yana fadin a bashi hanya,abbas din ya bisu da kallo yana son ganin abinda zai faru.
Yana daga wajen yake nazartar komai,yadda dan sandan ya shiga maganar suka hadu da matashin suna son bauwa dattijon rashin gaskiya,sai ya sanya hannu ya bude murfin motar ya fito ya nufi wajen.
"Assalamu alaikum.....lafiya me yake faruwa?" Yayi tambayar yana duban matashin da yaketa faman daga jijiyar wuya
"Wannan tsohon ne ya gogar ma mutane mota da wannan tsohon mashin din nasa,dubi yadda ya gogewa mutane fentinsu" idanu ya lumshe kana ya bude kusan lokaci guda yana duban inda yake fadin an goge masan,duka duka gugar ba wata me girma bace
"Kayi haquri kayi masa uzuri kuma,tunda nasan yana sane bazaiyi haka ba"
"Wallahi dan nan tun daxu ma naketa bashi haquri,bansani ba,sauri nakeyi ina da uzuri a gida"
"Baba ina ganin mutuncinka fa da tuni na zageka,da haqurin ya mutu sadakar nawa ka bayar?,ka biyani kawai" dunqule hannunsa abbas yayi cikin aljihunsa yana qoqarin hadiye bacin ransa
"Kayi haquri tunda shima ya baka haquri"
"Kaga malam bazan fa haqura ba,idan ma tsaiwa kayi a nan don ka bani haquri gwara kayi gaba abinka"
"Is okay,nawa ne kudin gyaran?" Ba kunya ba tsoron Allah ya karkace ya tsuga kudi,kallonsa abbas yayi na tsahon wasu mintuna yana karantar zallar qaryar dake qwayar idanunsa,sai ya saka hannunsa a aljihu ya ciro kudi,ya irga ya miqa masa.
Kunya da haushi suka kama matashin,bai taba zaton zai iya biyan kudaden ba shi yasa ya saka da nauyi,cikin borin kunya yace
"Ni ba kudi nake buqata,muje a gyaran motata"
"Ko ka karba ka tafi,ko kuma kayi asara ba kudin ba gyaran"
"Wai kai waye da zakazo kana cikamin baki malam?,bazan karba ba gyaramin mota nakeso ayi" matsowa dan sandan yayi kusa da abbas ba tare daya lura da waye ba a tsaye
"Kai meye naka ne a ciki zaka zo kawai ka shiga rigimar kan hanya?,ka qyale mut....." A nutse abbas ya juya suka hada idanu da dan sandan,gabansa yayi mummunan faduwa,yayi baya babu shiri,gumi ya fara yanko masa,abbas din baice komai ba ya maida dubansa ga matashin
"Ina me shawartarka ka karba"
"Idan kuma naqi fa?" Wani qaramin murmushi na gefan baki abbas ya sake,hankali kwance ya maida kudinsa aljihu gami da fito da wayarsa a madadin kudin,ya danna kira.
Baice komai ba illa adreshin titin da suke kai daya bayar ya maida wayar aljihunsa,ya kuma harde hannuwansa yana kallon yadda yake ci gaba da zuba rashin mutunci,jikin dan sanda yana rawa ya matsa kusa dashi
"Bawan Allah kayi haquri ka tafi,zaifi maka alkhairi,tunda nasan zuwa yanzu ko kudin ma ka rasasu ba samunsu zakayi ba,gwara ka tsira da lafiyarka da mutuncinka"
"Dalla malami sakeni,wallahi yau sai naga wanda ya tsaya masa" ya fadi yana kumfar baki,maganar tasa ta sake hasala abbas,saidai bai nuna hakan ba koda a saman fuskarsa,yana ji ya zama wajibi ya bashi tarbiyya da bashi da ita,sai ya juya ga tsahon
"Kada ka sake bashi haquri baba" hannu ya saka a aljihunsa ya fidda dubu uku ya miqa masa
"Hau mashin dinka ka tafi,Allah ya tsare" zaburowa yayi yana fadin
"Idan ka barshi ya tafi rigimar nan ta koma kanka wallahi"
"Na karba"ya amsa masa yana sawa tsohon muqullin babur dinsa ya kunna masa,dai dai sanda motar 'yan sanda ta iso,hakan ya baiwa tsohon hanyar wucewa,yana tafe yana jerantawa abbas din addu'o'in samun albarka da gamawa da duniya lafiya.
Matashin bai fahimci waye abbas din ba sai da jami'ai suka cika hannu dashi shi da dan sandan dake goya masa baya,sai a sannan ya nemi russunawa ya fara roqon ya saka a sakeshi,ko kallonsa baiyi ba ya dubi Samuel
"Ku sakayamin su a bayan kanta saina nemesu,mato ya tuqa motarsa a kaita station a ajjiye"
"Consider it done sir" ya fada yana saluting nashi.
*MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*
*DAUD'AR GORA* Billynabdul
*KI KULANI* Missxoxo
*IDON NERA* Mamuhghee
*RUMBUN K'AYA* hafsat rano
*A RUBUCE TAKE* Huguma
*ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number
09033181070
*MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*
09166221261
*YAN NIJER ZASU TUNTUBI WANNAN NUMBER*
+227 90 16 59 91
*Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*ππΎππΎ
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*_Arewabooks:huguma_*
Page 14
Ta tsakiyar mutane da suka cika a wajen 'yan kallo ya samu ya ratsa ya koma motarsa,yabar mutane suna ta tattauna maganar,da yawansu hakan da yayi ya sake burgesu saboda diban albarkar yaron tayi yawa,yan bani na iya kuma na ganin baiken hakan,suna ganin kamar yayi amfani da qarfin ikonsa ne.
Abinda ya faru akan hanyar ya qarawa kansa zafi,ransa ya dinga sosuwa duk sanda ya tuna girman shekarun mutumin da abinda qaramin yaro yayi masa,a nutse yaci gaba da tuqinsa har ya shiga unguwar tasu,qofar gidansu yayi parking,yana shirin fita a motar sukaci kacibus da qanin mahaifinsa suka tsaya suna gaisawa,wannan yaja masa jinkirin shiga gidan,sai bayan la'asar sa wasu 'yan mintuna bayan sunyi sallar la'asar a masallacin qasan layinsu sannan suka taho tare da kawu hassan din,yanata masa godiyar uban gudunmawar daya bayar na auren diyar kawu hassan din,har suka iso gida,kawun ya shige gidansa dake jikin gidansu abbas din.
Tun a harabar gidan ya fuskanci kamar gidan yau ba iya mutanen gidan bane kawai a cikinsa,muneera dake wanke alayyahu cikin famfon dake baiwa shukokin da suka qawata harabar gidan ruwa ta amsa sallamar tasa gami da gaidashi ya amsa mata,har yaa taka zuwa gaba sai ya tsaya cak ya waiwayo ga muneera
"Hajiya na ciki ne?"
"Eh sallah takeyi" fasa shigar yayi,saboda hayaniyar daya danji,a yanzun kuma ba abinda yake buqata sai zaman shuru,don haka ya juya akalarsa zuwa sitting room din baqi dake harabar gidan daga gefe
"Idan ta idar ki gaya mata na shigo,amma zan dan kwanta kadan"
"To uncle" ta amsa masa tana daukan kwandon alayyahunta tayi ciki,shi kuma ya murza key din daya gani a jiki ya bude falon ya shiga.
Yasan tsaf falon yake,duk da ba shigarsa akeyi akai akai ba,babu inda hajiyarsa ke bari da qazanta cikin gidanta,koda kuwa ba'a amfani da wajen,bata lamutar datti ko qura,wannan yasa babu haufi ya nufi daya daga cikin kujerun Three sitter ake falon yayi kwanciyarsa,ya miqe bayansa sosai saman kujerar yana lumshe idanunsa hadi da sakin ajiyar zuciya,yanason baiwa kwanyarsu hutu,bayason tuna komai da zai dameshi.
Minti kusan goma yana a haka,yanata kokawa da tunane tunanen dake kwanyarsa,saidai surutai da 'yan iface ifacen dake gilamawa kadan kadan ta wajen nadan damunsa lokaci bayan lokaci,bai wani dameshi da yawa ba,wannan ya sanya yaci gaba da barin idanuwansa a rufe.
Gigitaccciyar qarar data cika harabar gidan ta sanyashi durowa daga saman kujerar ba tare daya shirya ba,muryar nada matuqar kaifi da zaqin da zata iya huda kunnuwan duk wanda ke wajen,zaman dirshan yayi saman kujerar yana rufe idanunsa jin yadda qarar taqi tsagaitawa,ya rintse idanunsa yana jin yadda kansa ke sara masa sanadiyyar qarar,tsaki yaja dabmugun qarfi ya kuma miqe a fusace ya nufi qofa yaje yaga wanda ke qarar kamar wanda ake cirewa rai.
A hankali ya yaye labulen ranshi a bace idanuwansa a farfajiyar gidan yana son ganin wanne tashin hankalin ne haka yake faruwa,idanunsa suka sauka a kanta,a lokacin ta jima da fara tsalle tana runtuma ihu hadi hadi da hawaye face face saman fuskarta,tuni 'yar hular dake saman kanta tayi nata waje,gashinta da koda lafiya lau yake sabulewa daga jikin ribbom ya baje abinsa iska tana daukarsa.
Idanunsa ya zube mata,yana qare mata kallo,me ya sanyata wannan tsallen a gigice?,kunama ce ta harbeta ko maciji ta gani?,saidai kunamar,don ya tabbatar cikin gidan nasu ba za'a samu maciji ba,sai ya rasa me ya kamata yayi,ihunta yana sake cika masa kunne,baikai qarshen tunaninsa ba hajiya ta iso wajen da hanzarinta ita da muneera,a rude take qoqarin kama widad tana tambayarsu nujood me ya sameta?,sai ya harde hannayensa a qirji,ya zauna a hankali saman hannun kujerar dake daura da qofar yana kallo da sauraren abinda yake faruwa
"Kyankyaso ne ya shigar mata riga" idanunsa ya lumshe yana jin wani haushinta yana cikashi,kyankyason takema wannan kamar wadda taga mutuwa?,bai bude idanun nasa ba yayi shuru yana sauraren muryar hajiya tana cewa
"Kyankyaso?,riga kuma?,garin yaya?"
"Musaddiq ne ya saka mata(qanin nujood dake binta)"
"Ashsha musaddiq baka kyauta ba" hajiya ta fada tana qoqarin kakkabe mata rigar.
Hannu daya ya sanya ya sauke labulen,ya kuma tura qofar da qafa sannan ya koma saman kujerar ya kwanta kamar dazun yana sake jan tsaki,ko a ina hajiya ta samo su suka cikawa mutane gida da hayaniya?. Still idanuwansa suna rufe,yana jinta cikin sheshsheqar kuka tana gayama hajiyan yadda abun ya faru,ta yima musaddiq fada sosai sannan ta hada kansu suka wuce cikin gidan.
Ana kiran sallar magariba ya wuce masallaci yayi sallah sannan ya shiga cikin gidan,zuwa sannan babu kowa daga hajiyan sai muneera
"A'ah,shigowar magariba kuma yau kayi abbas?"
"Ina nan tun sanda wannan tsanyar ke ihu" dan shuru tayi na sakanni,sai kuma ta saki murmushi
"Wai widad?,aikin musaddiq ne wallahi"
"Musaddiq din muhsin wai?,dama sune?"
"Sune,a nan hajjaa ke barinsu,idan ta taso daga makaranta take daukansu,widad kam ai bata da hayaniya ko kwaramniya,shaqiyancin musaddiq dinne,yasan yadda take tsoron kyankyason ya saka mata shi" kai ya jinjina kawai ba tare da yace komai ba,sai a sannan hankalin hajiya kuma ya dauku ga fuskarsa,ya akayi har ya shigo gidan tun yamma bai nemeta ba,fuskarsa ta nuna akwai damuwa tattare dashi
"Allah dai yasa lafiya" ta fada bayan sun gaisa,furzar da iska yayi daga bakinsa,ya motsa baki zaiyi magana ta datsi numfashinsa
"Kada kacemin babu komai" shuru ya ratsa falon na wasu sakanni,sai ya buda baki a hankali yana gayama hajiyan zancan tafiyarsa kaduna da hafsat tayi tutsun ba zata je ba.
Ran hajiyan ya dan tabu,tun ba yau ba tasan matsalar dake cikin gidanshi,ba yau ta fara gani da fuskanta ba,saidai batason shiga lamuran gidansa sam,hakanan a matsayinta na uwa bata da abinda zata masa illa addu'a da kuma bashi shawara na gari
"Kayi haquri ka tafin,kada ka matsa mata,duk sanda ka samu sarari ka dinga zuwa kana ganinsu,ta wani fannin tana da hanzarinta daya kamata a duba,ko don karatun mariya(mimi) da yanzu ta farashi kada ya samu tangarda,zama da iyali dan haquri ne,mahaifanku dukka haquri sukayi damu har zuwa sanda Allah ya rabamu,komai yayi farko kuma yana da qarshe" ajiyar zuciya ya saki,maganganun hajiyan sai suka sake kwantar masa da hankali da sanya masa nutsuwa,kalmominta masu tsada ne da baiwa zuciya da kuma ruhi nutsuwa,take yaji gaba daya dukka wani kwadayinsa na tafiya kaduna da hafsat din yakau a take
"Na gode hajiya" ya fada yana bude abincin data saka aka kawo masa,ya fara ci a hankali suna hira da hajiya,hirar da ako yaushe ita ke debe masa damuwa.
Basu jima suna hirar ba babban yayansa ya shigo,wannan yaja hirar tasu,har yakai qarfe tara na dare,sai da zai tafi yace ya saukeshi a hanya,ya ajjiyeshin sannan ya wuce gida shima.
Tun k'arfe takwas da rabi duka yaran sukayi bacci,ta kwashesu ta kaisu dakinsu ta kwantar dasu,ranta a jagule,kishi fal ranta,zuciya nata mata saqe kala daban daban kan inda ya tsaya din,don ba kasafai yake kaiwa dare haka a waje ba,koda zaikai din yana kiranta ya gaya mata zai kai dare din,tunda babu ta yadda aikinsu baya kamawa.
Dakinta ta wuce bayan ta rage hasken falon,tanaso qwarai tayi wanka amma kuma tana gandar zuba ruwa a jikinta,saita zarme da zama gefan gadonta kawai taja wayarta ta fara chart.
Batasan lokaci ya ja haka ba sai data ji qarar shigowar motarsa,ta sauke wayar tana duba lokaci,sai taci gaba da chart dinta,don tasan yawanci bai fiya dawowa shi kadai ba,kuma idan hakan ta kasance sai ya sallamesu kafin ya shigo cikin gidan.
Duk da yasan babu lallai ya samu kowa a falon amma bai fasa yin sallama ba,ya dan bi falon da kallo,babu laifi,bai wani kacame can da yawa ba,duk da bai masa tsari yadda rai da zuciyarsa sukeso ba,kai tsaye dakin yaran ya wuce,ya tura qofa ya shiga,wutar dakin tana kunne,yabi yaran da kallo,ba alamun an musu wanka da zasu kwanta bare ayi maganar brush,kowanne cikinsu yana da kayan bacci qasa da kala goma goma,amma bazaice ya gansu dasu sau biyar ba,baima san inda take kaisu ba.
Yadan jima a kansu yana musu addu'ar daya tabbatar bata musu ba,ya shafesu da ita,ya sake gyara musu kwanciyar ya lullubesu sannan ya kashe wutar dakin ya fito yaja musu qofar.
Yana fitowa tana fitowa a nata dakin,kallon kallo sukayi a tsakaninsu,tanason ta karanci har yanzu ranshi na abace ne ko ya haqura?,duk da ba yau suka saba irin wannan ba,yayin da shi kuma yake kallon dressing din jikinta,kayan daya fita ya barta ne dasu,wanda tun safe suke jikinta,duk da yalwar suturu da take dasu masu tsada da kyan gaske,to amma fa idan ka gansu a jikinta wani babban sha'ani ya tashi da zata shiga dangi ko qawaye tayi bajinta
"Sannu da zuwa" ta fada tana dan basarwa"
"Yauwa,ya gida ya yaran?"
"Alhmdlh" ta amsa masa tana mamaki,a yadda ya fita bata taba kawo saukarsa a nan kusa ba,amma sai taga kamar babu abinda ya faru
"Anan zaka ci abincin naka?" Ta tambayeshi sanda taga yana takawa yana barin wajen
"Zan danyi wanka,kamar nan da minti goma ki kawomin sashena" dan yatsina fuska tayi can qasan ranta tana mita,bayan wahalar girkin da tasha kuma sai ya sanyata wahalar diban cooler din abinci ta bishi dasu?,me yasa bazai zauna a nan yaci ba?,bata amsa masa ba har ya fice,sai ta juya ta koma daki abinta taci gaba da charting dinta.
Da sauri ta miqe sanda taji agogi ya buga,minti goma sai data ninkasu wajen sau hudu,ta qara ya zama minti arba'in da kusan biyar ba tare data ankara ba,ta jefa wayar gefe ta miqe tana gyara daurin dankwalin atamfar dake kanta sannan ta fito tana gyara daurin zaninta daya dangale tana qoqarin daidaita tsahonsa.
Har ya gama shirinsa tsaf ba ita ba alamunta,ba wani yunwa yake ji ba ya riga da ya take cikinsa wajen hajiyarsa,don haka bai wani damu ba can,dama kuma idan da sabo ya riga ya saba,sai ya dauko luggage dinsa ya fara shirya kayan da zai tafi kaduna dasu.
Ya gama hadasu tsaf ya debo wasu takardu nasa yana dubawa,sai ya koma kan sofa dake dakin ya zauna yana dubawa cikin nutsuwar nan tasa.
*_RIGIJI GABJI!_*π₯π₯
*_WANI KAYA SAI AMALE_*π₯π₯π₯
*FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*π₯π₯
*JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA*
*_'YAN BIYAR DIN NAN NE FA_*
*_SARAKAN LABARUN_*
*NISHADI*
*CAKWAKIYA*
*GWAGWARMAYA*
*BARKWANCI*
*TSANTSAR DARASIN RAYUWA*
*TARE DA*
*ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI*
*SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!*
*KIN SHIRYA MADAM?*
*MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*
*DAUD'AR GORA* Billynabdul
*KI KULANI* Missxoxo
*IDON NERA* Mamuhghee
*RUMBUN K'AYA* hafsat rano
*A RUBUCE TAKE* Huguma
*ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number
09033181070
*MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*
09166221261
*Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*ππΎππΎ
*Arewabooks:huguma*
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 15
Qwayar idanunsa ya daga kan takardun yana dubanta sanda take shigowa dauke da kwanukan,ya sauke boyayyar ajiyar zuciya yana qarewa dressing dinta kallo,baisan sai Yaushe hafsat zata canza ba,baisan me zaiyi da zai canza ta ba,duka wani burinsa a kanta ya dade da tarwatsewa,wani lokaci sai ya dinga gani kamar ba hafsat dinsa ba.
A gabansa ta ajjiye abincin sannan ta koma gefansa ta zauna tana maida idanunta ga takardun da yake dubawar shima
"Ga abincin" ya daga takarda daya yana juya bayanta ba tare da ya kalleta ba
"Shi zai zubamin kansa da kansa?" Jim ta danyi sannan ta tabe baki,wani lokaci ya fiya jin kai da izza,hutsu ne na gaske,sai yayi kamar ya sauko ko ya canza sai kuma ya sake hargitse mata,ita kanta tana sarawa kanta yanda take haqurin zama dashi,sai ta sauka tana zuba masa ta ajiiye gabansa tana komawa mazauninta.
Sai daya qara minti kusan biyar sannan ya ajjiye takardun ya sauko,tana ta satar kallonsa,tana son masa maganar motarta data fara bata matsala tana shakka,dazun sun rabu ba ta dadi ba,yanzun kuma taga yana hada kaya,ta tabbatar kayan tafiya KD ne,wala'alla ya haqura ne ya janye qudurinsa?,idan hakanne ita tafi mata nono fari,saidai tafi kowa sani,shurunsa bashi da sauqi,mataki ne zai dauka daga baya ta ruwan sanyi,koma dai yaya ne idan har ya janye din shikenan its buqatarta ta biya,a hakan ta daure dai tayi gyaran murya kadan.
Ya jita sarai yayi kamar baiji ba,sai data gaji da gyaran muryarta sannan ta magantu
"Wai kayan tafiyar kake hadawa?"
"sune" ya bata amsa a taqaice
"Allah yasa a koma a sa'a,mudin ko weekend ma dinga zuwar maka,kaga bazai shafi karatun mimi ba" ta fada har qasan ranta tana jin ta fada ne kawai don ta wanke kanta,bawai don zata iya wannan jigilar ba
"Yayi" ya amsa mata a taqaice kawai,don baison doguwar magana.
Shuru ya sake ratsa tsakani,tana ta tauna yadda zata gaya masa zancan motar,don so take kafin bikin qawarta din nan ya sauya mata,taje a hajiyar ta da sabuwar mota,ba wannan qaramar motar da kowa ya sanya da ita ba
"Nace ba" ta fada a darare
"Uhmmm,kikace me?"
"don Allah ba.....abban mimi motata...wallahi matsala take ta bani,sannan ma tayi tsufa da yawa,kada kunya na dinga shigarta bayan mutane sunsan matsayinka" shuru kamar bazai amsata ba,yaci gaba da cin abincinsa,yayin data kasa ta tsare ta kafeshi da idanu tana jiran ta cewarsa,har sai data gaji da jiran amsa ta sake magantuwa
"Bakace komai ba abban mimi" plate din hannunsa ya ajjiye,ya waiwayo ya dubeta
"Bani da kudi a yanzu" fuska ta dan bata
"Abban mimi baka da kudi fa kake fada?,ko allowance dinka ya isa ka canza min babbar mota bama qarama bafa"
"Kudina a yanzun bana canza mota bane,ina da abu me muhimmanci da ya fishi" daga haka ya miqe yaci gaba da aikinsa hankali kwance,cikin bacin rai taci gaba da zama wajen,tana ta baqin rai ita kadai,zantukan yayarta take tunawa
"Kada fa kiga mijina ya canzamin mota ki dauka kema wannan mijin naki me ra'ayin riqau zai canza miki mota ta sauqi,mafi kyau ki haqura da maganar zancan mota yanzun,nasan halinsa sarai ba canza mikin zaiyi ba" a sannan baki ta tabe tana dan kada qafarta
"Kiyi haquri umman walida,amma banjin yadda abbas ke kashemin kudi da yadda yakeji dani kina samun haka wajen baban walida....."
"Ke kinga dakata,karki gayamin baqa mana" ta dakatar da ita,duk da cikin wasa suke maganar
"Kowa ya san abbas yana jiqaki,amma kuma duk cikinmu babu wadda juya miji ke mata wahala irinki koba haka bane?" Ta fada tana duban sauran sisters dinta dake wajen,dariya suka danyi suna gasgata maganar maman walida din da suke kira da anty balaraba,wannan ya hasalata,ta kuma ci musu alwashin kawo sabuwar mota don ta nuna musu ta isa da mijinta kamar kowacce mace.
Har yaci qarfin aikinsa tana zaune a wajen bata sake tofa tata ba,ta tattara fushin duniya ta azama ranta,me yasa koda yaushe abbas din sai ya kunyatata yakejin dadi?,kafin ya kammala aikin ta tattare tabar masa wajen,sai kawai tayi komawarta sashenta,tayi kwanciyarta acan.
Shima daya gama komai kwanciyarsa yayi,bai wani tsaya bi ta kanta ba,bayason rainin wayo da kuma rashin hankali,ta kuma fi kowa sani abinda baya tolerating kenan.
Washegari haka tayita kumbure kumburenta,sai ya nuna baisan ma abinda takeyi ba,ayi masa laifi kuma a fishi fushi?,yayita hidimarsa da yaransa,yana kuma yin breakfast ya shirya zai fita,mimi ta maqale masa sai ta bishi,ya kaita gidan hajiya,hafsat din nata danqara masa mata harara amma yarinyar batasan tana yi ba,ya shiga dakinsu ya shiryata da kyau cikin sabbin kayanta dake danqare a cupboard ba'a sanya musu,baisan uban me takeyi da kayan ba,yasan dai wani lokaci takan diba ta rabar,duk cikin fariya da alfaharin shi din wuyansa ya isa yankan da yake danqaro musu suttura ya ajjiye.
Yana fita ta bishi da tsaki ta kuma miqe abinta saman doguwar kujera tana gunaguni,duk yadda take sonshi yana sanyawa yana fita a ranta gaba daya,bata isa ta sashi yayi abu ba sai abinda yayi niyya ya kuma tsarama kansa,kallo ta kunna abinta tana daga kwance,nawwara da yau suka samu albarkar wanka tun safe tana ta kaikawo tana wasanta qasan carfet,har bacci ya dauketa ta bingire a nan.
Har biyu ta buga tana kwance tana kallo bata da niyyar tashi ta kintsa gidan,sai da taji sallama daga qofar falo sannan ta miqe tana sauke qafafunta qasa.
"Anty ummee,ni banma dauki murya ba wallahi"
"Ina zaki dauka kin tasa tv a gaba" ta fadi tana duqawa ta dauke nawwara daga qasa ta maidata saman kujera sannan ta zauna daga gefanta tana cewa
"Yanzun da banzo ba a qasa zaki barta har tayi barcinta ta tashi" baki ta tabe,bacin ranta da ya dan lafa yana motsa mata
"Hmmm,a qufule nake anty ummee,ubanta yaja mata,shi ya qunsan takaici"
"Ke kam damuwarki da abbas bata qarewa,gashi dai baki rasa komai ba amma ko yaushe cikin complain?"
"Na rasa ya zanyi dashi anty ummee,dan bada umarnin nan da mata kewa miji ni bansanshi ba" baki ta tabe tana jingina sosai da kujera
"Ke kikaso hafsa" bata motsa daga wajen ba ta zayyanewa anty ummee din komai,itace wadda take bi a dakinsu,uwarsu daya ubansu daya,sai data gama tas sannan ta dubeta
"A cikin banza ma ke banza ce wallahi hafsat,ke ko asiri kike fa saikin hada da kissa da kisisina yake ci maka yadda kakeso,ke dan makircin nan na mata ma ace baki iya ba?,ko da yake ko an doraki ma sauka kike" ta qarashe maganar tana yaada kanta gefe cike da takaicin 'yar uwartata.
Matsowa tayi sosai kusa da ita
"Zanyi wallahi anty ummeee" sai data qare mata kallo sannan ta zauna sosai tace da ita
"Ki tattara kayanki ki bishi kaduna kamar yadda yakeso,yaran idan ta kama ko gida ko hannun hajiyarsa basai ki barsu ba?,bama mimi bace ita kadai?,idan kuka tafi can daga ke saishi,ba 'yan uwansa akusa ba 'yan sanya idanu,Allah ne kadai yasan nawa zaki tatsa daga jikinsa,masu aikin damarar nan fa ba qaramin iya soyayya sukayi ba,amma ke gaba daya komai naki a rikice?ki bishi ki kwantar da kai,dadin yadda kika faranta masa ma wallahi baisan sanda zai sauya miki motar ba babu wanda yaji ba wanda ya gani" Fuska ta bata,don ta dauka wata mafitar zata bata ba wannan ba,sai itama anty ummee din ta zuba mata idanu tana dubanta
"Ba zakije ba kenan?" Cikin tsuke fuska tace
"Ni anty ummee,kaduna fa wa na sani wa ya sanni?"
"To ai shikenan saikiyita zama bauchi ki tsanana uwar da zaki tsinana" ta fada tana buga cinya. Shuru tayi na wasu sakanni tana nazari,yayin da anty ummee ke qarewa qawataccen falon nata kallo yadda ta barshi komai a zaune da duwawunsa,babu tsari bare kintsi
"Shikenan anty ummee,an gwada aiki da shawarar taki,zanje"
"Yadaifi miki" ta bata amsa sannan ta maido dubanta kanta
"Yanzu kika tashi a barci ne wai?" Kai ta girgiza tana dubanta
"A'ah,me kike gani?"
"Bakiji bashi bashin da jikinki yakeyi ba?,sannan wannan uwar bolar da kika barwa falonki ta mece?" Shinshina jikinta ta soma yi,sannan ta bata fuska,don ita bataji komai ba
"Ni ba abinda jikina yakeyi,hancinki ne dai,falo kuma wallahi yara ne suka bata su da ubansu kafin su fita,don jiya da daddare fes na shareshi kafin na kwanta,yanzu kuma ina shirin tashi na sake gyarawa kika shigo"
"Allah ya sawwaqe" kawai tace da ita,tasan halinta ba yau ba ba jiya ba,koda ta tsaya gaya mata qarancin tsaftarta ma uzurin yara zata yita kawo mata,kamar ita tafi kowa haihuwa a duniya.
Suna taba hira tana gyara falon har ta gama,ta shiga kitchen tana tunanin me zata dafa harda abbas din,don ba zata iya girki biyu ba,tayi yanzu tazo tayi musu na dare?,sai kawai ta dora.taliya da miya,suka wuce uwar dakan hafsat din anty ummee na sake jaddada mata muhimmancin binsa kadunan,tare da dabaru na kissa na yadda zata samu yadda takeso.
Ita ta tayata suka hada kayanta dana yara,don tasan iya wannan sai ya zame mata aikin gabas,cikin kayan nata taga wasu night gown,tasan kudinsu saboda ta gansu wajen wata qawarta kwanaki da tayo order dinsu
"Kai....wadannan nighty din fa?"
"Sunyi kyau ne?" Ta amsata tana zuge qaramar jakar data zuba undies dinsu
"Sosaima,ke bakisan kudinsu ba?" Baki ta tabe
"Bana ce ba gaskiya,shi ya siyomin su kwanaki,ni kuma Allah ya gani bazan iya sanyasu ba,kamar waga kafira,shi yayita wani aiki kamar dan iska dan iska,ko kunyar yaranshi biyu baya ji" galala anty ummee ke kallon hafsat din,idan tayi wani abun kamar batayi karatu ba,ita yanzun just shekara ashirin da takwas zuwa da tara har tayi tsufan da bazatayi gyara ba?, Amma da yake itama kayan takeso sai bata bata shawarar komai ba,ta ninke abinta ta sanya a jaka,ita tasan darajarsu.
Da ta tashi tafiya ta sake tambayar wasu designers turare da ya siyo mata,guda uku ne,guda biyu dubu ashirin da bibbiyu ya siyosu,guda daya dubu talatin,hakanan yake,mayen qamshi ne,shi yasa baya siyan banzan turare,ko su mimi zai siyawa turare baya siya musu na qaramin kudi,bata damu da su ba shi yasa.batasan daraja ko tsadarsu ba,tace ta dauka wanda takeso,ta kuwa dauke dan dubu talatin dana ashirin da biyun guda daya tayi tafiyarta,dama yawa yawan zuwanta gidan abinda ke kawota kenan,don ta qaru da 'yar uwarta,duk da tana bata shawarwari na gaskiya a wasu lokuttan,rashin daukan shawara ke damun hafsat din,data fara saita tattara ta zubar,tafi ganewa yawan qorafi da kai k'ara.
*_RIGIJI GABJI!_*π₯π₯
*_WANI KAYA SAI AMALE_*π₯π₯π₯
*FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*π₯π₯
*JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA*
*_'YAN BIYAR DIN NAN NE FA_*
*_SARAKAN LABARUN_*
*NISHADI*
*CAKWAKIYA*
*GWAGWARMAYA*
*BARKWANCI*
*TSANTSAR DARASIN RAYUWA*
*TARE DA*
*ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI*
*SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!*
*KIN SHIRYA MADAM?*
*MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*
*DAUD'AR GORA* Billynabdul
*KI KULANI* Missxoxo
*IDON NERA* Mamuhghee
*RUMBUN K'AYA* hafsat rano
*A RUBUCE TAKE* Huguma
*ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number
09033181070
*MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*
09166221261
*Yan NIJER π³πͺπ³πͺzaku tuntubi wannan number*
+227 90 16 59 91
*Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*ππΎππΎ
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: huguma*
Page 16
Tunda ya fita yaso miqa mimi wajen hajiya sai ya wuce,idan ya dawo ya dauketa su wuce gida,amma tun baiyi nisa ba ogansa yayi kiransa,yayi shigowar ba zata yankinsu,don haka ya wuce da ita,sai ya ajjiyeta wajen rose abokiyar aikinsu ce,babbar macace haka,tana da matuqar kirki da son yara,sai yamma sosai sannan suka gama,ya dauketa suka yo gidan hajiyan.
A qofar gida yayi parking,ya buda murfin motar ya fita ya zagaya ya fiddo mimi,yana riqe da hannunta suna shiga cikin gidan,tana basu labarin rose da irin abubuwan data siya mata,yana saurarenta yana murmushi,yaransa sune ke debe masa mafi yawa daga damuwae hafsat.
Dai dai lokacin da widad ke daura alwala bakin famfon dake farfajiyar gidan,ta gama wanke qafafuwanta kenan tana gyara daurin dankwalinta gizo gizo ya taho,fallatsin ruwa yasa ya qara gudu,take ta rude,sai taga kamar kanta zaiyo,wannan yasa ta saki qara sannan kuma ta buga tsalle tana komawa gefe,bata dora ko ina ba sai a gabansa ba tare data lura da waye ke tsaye a wajen ba,saboda hankalinta gaba daya yana kan gizo gizon.
Baya yaja yana bata fuska gami da dubanta,baya iya ganin fuskarta,sai sassalkar sumarta data yiwa kanta rumfa,sanadin dankwalinta da ya zame yake kuma riqe a hannunta tana ci gaba da kallon gizo gizon
"Allah yasa bai tabani ba" yaji ta fadi tana ci gaba da maida daurin dankwalinta,wannan ya alamta masa ma batasan me tayi ba,sai ya kama hannun mimi suka shige cikin falo.
"Yau kice a gidan kishiyata,ko batan kai kikayi?" Hajiya ta fada cikin dariya,yayin da su nujood dake falon suka fara gaidashi,yana amsa musu wayarsa ta dauki tsuwwa,sai ya fidda wayar yana dubawa,kawun sa ne,wanda shima gidansa ke jikin gidan kawu hassan,gida daya ne daa gaba daya,bayan rasuwar mahaifinsu aka raba gado aka fitarwa da kowa shiyyarsa ya gyara ya maidata gida me zaman kansa.
Hajiya dake faman tsokanar mimi ya kalla
"Hajiya bari naje,kawu imrana ke nemana,yace yaga motata a waje"
"To ba laifi saika dawo" sai ya juya ya fice.
A harabar gidan ya hangeta waje daya ta shimfida dankwalinta tana sallah,ya dauke kansa a hankali ya doshi gate din,ina hajiya ta samo wannan?,duka sauran yaran muhsin ne ya sani,amma wannan mai tsalle tsallen fa?. Dan tsaki yaja yana ture tunanin gefe guda ya doshi qofar gidan kawu imrana.
Koda ta gama sallarta tattarawa tayi ta shige ciki,don ita ko sau daya ba wanda ta gani,tun daga shigowar tasa har fitarsa ta yanzun,bata jima da shiga ba hajjaa ta iso ta hada kansu suka wuce gida tana sake yima hajiya godiya da ban gajiya.
Sai bayan magariba ya dawo,yaci abincinsa sukayi hira da hajiyan,sanda ya tasamma tafiya mimi tayi bacci,don haka ya barta a gidan
"Babu matsala abbas kuwa idan ka barta?" Hajiyan ta tambaya a fakaice,saboda tasan halin hafsat,tana da tsananin nuna son 'ya'ya,bata iya boyewa gaban kowa,idan ka gansu sun kwana wani guri to tare da ita ne.
Wani abu yaji ya tsaya mas a wuya,jikinsa yayi sanyi,mahaifiyarsa ke shakku da kokwanton kwanan diyar da shi ua haifeta a hannunta?,tabbas da saake,akwai kuma gyara
"Ba komai hajiya,idanma kina buqatar wasu qarin kwanakin sai na debo miki kayanta" murmushi ta saki tana shafa kan mimin
"A'ah,kwana dayan ma yayi alhmdlh" boyayyar ajiyar zuciya ya sauke,sukayi sallama ya fita.
Yana tuqi a hanya amma tunani ne fal kwanyarsa,qarar wayarsa ce ta taimaka masa ta katse masa tunanin,ya duba mai kiran,sai ya dan saki miskilin murmushin nan nasa,ya miqa hannu ya daga
"Allah ya taimakeka ranka ya dade,tuba nake,kwana biyu an zubda ni,naji tsoron kada hakan ya zama silar watsewar zumunci nace bari na kiraka"
"Wallahi ko yau naso shiga na gaida umma,kawu ma'aruf ne ya tsaidani,sai kuma na sha'afa,ta yaya zan manta da kai,ayyuka ne suka taru sukayimin yawa,that's why na ajjiyema governor ADC dinsa saboda na ragewa kaina wasun sabgogin,so kuma maimakon su barni na huta,wallahi kaga sun sake cillani KD"
"Naji labari,ina nan ina tunanin me yasa ka ajjiye appointment din?,bayan kana da sauran lokaci?" Kansa ya shafa da hannunsa
"Mu hadu kawai gobe idan kana gari"
"Ina nan,babu damuwa zan sameka gida"
"To sai na ganka" sukayi sallama ya ajjiye wayar yana furzar da iska me zafi daga bakinsa,hadi da sanya idanunsa kan hanya yana duba shagon dake masa aski,ya samu suna nan don haka ya gangara yayi parking ya kashe motar ya fito.
Babban kanti ne na matasa masu aji,masu j da jini a jika wadanda duniyar ke garawa,suna qaruwa ga jikinsa sosai,sun kuma san matsayinsa,don haka tarbar musamman sukayi masa,ya zauna yana duba jaridar da suke ajewa kafin a gamawa wanda ka samu.
Goma na dare ya baro wajen,ya tsaya ya siya fruit ya wuce gida,don yaga kaman nasun ya qare,to amma babu lallai ta gaya masa babu ya sanya a kawo kamar yadda aka saba,qila sai ya tashi amfani dashi sannan tace masa babun.
Kulle ko ina yayi sannan ya wuce sashenta don ya duba lafiyarsu kamar yadda ya saba,ko me sukayi da ita baya fasa wannan,ko bai shiga don ita ba zai shiga don yaransa.
Abun mamaki yau zaune ya sameta a falon,saidai fuskarta gana daya babu annuri,yau din ba laifi,wani lace ne a jikinta peach color dinkin riga da zani,fuskarta tas babu digon komai,sai daurin ture kaga tsiya da tayi.
Tana daga zaunen tayi masa sannu da zuwa,ya amsa mata yana wucewa dakinsu mimi,yaga nawwara sannan ya fito,sai ta miqe tana cewa
"Ina kaje wai?,sanda ka shigo gidan nan fa goma ta wuce" hannayensa zube a aljihun wandonsa ya waiwayo ya zube mata manyan idanunsa yana kallonta,a nutse ya buda baki
"Ina wajen hajiya,daga nan na wuce aski" ya bata amsa yana kafeta da kallo me alamta sai kuma me?,kasa jurar idanuwan nasa tayi,sai ta kauda kanta,cikin salo na mita tace
"Amma yanzu dai tsakani da Allah duk inda kaga dama kake zuwa,kama daina gayamin kana waje kaza" hannunsa ya fidda daga aljihunsa ya juya kawai yaci gaba da tafiya ba tare daya tanka mata ba
"Ina mimi?" Ta fada tans leqe leqe,don sai a sannan hankalinta ya bata ba tare suka shigo ba
"Tana wajen hajiya,zata kwana can" wani abune yayi mata tsaye a maqoshi,har ta bude baki zatayi magana sai kuma ta hadiye data tuna da maganganun anty ummee,ranta a bace amma tayi qoqarin rage kaifin bacin ran nata daga samsn fuskarta ta sake cewa dashi
"Ga abincinka" ya riga ya qoshi sosai,amma yana cewa bazaici din ba sabuwar magana zata balle da ita,abinda bai buqata
"Me kika dafa?"
"Tuwon shinkafa ne" kai ya jinjina,ba kasafai tuwon shinkafarta ke shiga ba,koda bata jima da gamashi ba kana gutsura yana wargajewa,ga uban gaari da zaka yita cin karo dashi a ciki wanda ta d'aure tuwon
"Babu wani abun sai shi?" Sai a sannan ta tuna ta yiwa anty ummee dafadukan taliya,wadda har shi ta dafa amma anty ummee din tace ta daure ta canza masa abincin da tasan yafi so,hakan zai sake sassauto dashi
"Sai jallop din taliya" kai ya jinjina,duka babu wanda zai iya ci,sai yace da ita
"Hadomin black tea kawai,ki saka kayan qamshi please sosai a ciki"
"Tom" ta amsa takaici na cikata,baisan tana yi ba ya sanya kai ya fice,saita daga kai tana kallon agogo,takaici goma da shirin,ta zauna ta wahala tayi masa tuwon amma ya watsa mata qasa a ido,ita anty ummee idan tana bata wasu shawarwarin rashun sanin halin abbas dinne yasa take gaya matan,sannan yanzun qarfe goma harda kusan rabi a sanya mutum wani shig kitchen,ko uwarta bata taba bata wannan aikin ba,tana qananun motoci haka ta shige kitchen din,rabi da rabin hankalinta yana kan mimi dake wajen hajiyar,taja tsaki yafi a qirga,wai duka duka nawa mimin take da tsohuwar zata nace sai ta kwana wajenta(ni kuwa nace uhmmm,sai kace ke din wata uwar kike iya musu).
Saman tray ta kammala komai ta wuce sassanshi dashi,sanda ta shiga bedroom din taji motsin ruwa a toilet,da alama wanka yakeyi kenan,sai ta dora masa saman madubi tana tabe baki,shi mutum Allahn da yayishi bashi da wani aiki saina wanka kamar kwado?,da wannan tunanin ta koma nata sassan don ta kashe wutar ta kuma dauko nawwara,don a nan yau tayi niyyar kwana.
Nawwaran kawai ta dauko,wata zuciyar na cewa ta dauko turare da night gown amma taji ba zata iya ba,ta rufe sassan ta koma nashi. Har sanda ta koma din bai fito ba,sai ta kwantar da yarinyar saman gadon,ta zauna saman sofa bed tana danna wayar ta.
Ringing wayarsa dake saman madubi ta fara,saita miqe da hanzari kai kace ita ake kira,haka dabi'arta take,duk wanda zai kira saita duba waye idan baya kusa da wayar,idan kuwa yana kusa kunnuwanta gaba daya tafiya suke ga wayar,sai ta tantance me yakeyi kafin taci gaba da harkarta,ta nufi wayar tana duba me kiran kamar yadda ta saba,sai taga sunan rose.
*RUMBUN K'AYA*π₯
*DAUDAR GORA*π₯
*IDON NERA*π₯
*A RUBUCE TAKE*π₯
*KI KULANI*π₯
*_uhmmmm_*ππππππππππ
*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*
*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*
*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️
*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*
*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*
*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*π₯π₯π₯π₯π₯
0022419171
Maryam sani
Access bank.
Shaidar biya tananππ»
09033181070
*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*
09166221261
π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+227 90 16 59 91
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*Thanks for choosing us*π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 17
____________________________
*_KAMSHI!_* *_KAMSHI_* *_KAMSHI_*
*TABBAS K'AMSHI RAHAMA NE. INA MASU NEMAN INDA ZASU SAYI TURARUKAN WUTA MASU KAMA GIDAH! DA TURAREN KAYA, TURAREN TSGUNNO, TURAREN WANKA DANA WANKI DA JIKI?*
_KAI BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA TURAREN KHUMRAH KALA KALA DA KULACCAMS NA KECE RAINI._
_AROOS_SCENTS_
_AROOS_SCENTS_
_AROOS_SCENTS_
_KUNJI SUNAN KO? *AROOS_SCENTS*_
_*AROOS SCENTS* SUNA GARIN *KADUNA* SUNA KUMA TURA KAYAN SU A FADIN NAJERIYA DA KETARE_
_LAMBAR WHATSAPP DIN SU :07067786384_
_INSTAGRAM : aroos _scents_
_SCENT HEAVENπSMELL RICH! LEAVE DEM WONDER WHAT YIU USED…πA SCENT LIKE NO OTHER. SCENT THAT WARDS AWAY SMELLS_
_KYAU! INGANCHI DA KAMSHI MAI SANYAYA ZUCIYA SAI KAYAN TURAREN_ *aroos scents*
____________________________
"Rose?" Ta maimaita sunan da qarfi tana fidda idanu,abu na farko da zuciyarta ta sawwara mata ire iren sunayen soyayya ne da namiji ke sanyawa masoyiyarsa mace,take duk wani jini dake jikinta ya fara tafasa,ta fara fidda huci daga bakinta,mugun kishinta nan ya motsa,ta warfci wayar ta daga ta kara a kunnenta.
Sallamar da akayi da kuma muryar mace ya tunzurata,bata jira komai ba ta fara zunduma mata ashar da zagi
"Shegiya karuwa,riqeshin da kikayi yau duka bai isheki ba,saikin biyoshi da kira yana cikin iyalinsa?,to wallahi billahillazi abbas yafi qarfinki,nawa ne ni kadai,ba wata mace data isa ta rabeshi na bart......."
Bata qarasa ba taji an warce wayar daga hannunta,tabi inda taji an fusge wayar da kallo bala'i yana cinta,don bata gama fadar tarin tulin qazaman miyagun kalmomin dake bakinta ba,sai taga abbas ne,daure da towel yana duba wanda yayi kiran nasa,tun yana bandaki ya fara juyo sautin muryarta,baisan da waye take wannan hayagagar ba gashi dare ya fara yi,sai daya fito ya fuskanci a waya ne,wayarma kuma tasa.
Already an katse kiran daga can,sai yabi kiran yana sake kara wayar a kunnensa,idanuwansa da suka hautsine saboda baqinciki suna kan fuskar hafsat dake huci,jin alamun yabi kiran sai ta fara matsowa
"Kiranta ma ka sakeyi,kuma a gabana?,wal......" Mugun kallon da ya watsa mata yasa ta danyi laqwas tana dubansa shaidan na sake ingizata.
Murya a sanyaye rose tayi sallama kafin yace komai ta rigashi
"Sorry sir,na kiraka da dare ko?,a baiwa madam haquri"
"No,kada ki damu,wani abunne ya faru?" Cikin gurbatacciyar hausarta ta fara masa bayani
"Eh....dazun da kuna meeting mimi tayi bacci a office ta yar da dan kunnenta ne,dana duba kuma naga kaman gold ne,so don kada ayita nema hankali ya tashi shi yasa nace bari nayi maka magana" ajiyar zuciya ya sauke yana qoqarin cooling temper dinsa
"Is okay,ba damuwa,ki aje wajenki,idan na shigo gobe zan karba,idan ban shigo ba zansa ko samuel ki bawa sai ya kawo"
"Okay sir"
"Sorry rose,am sorry"
"No sir,babu komai fa,nasan bata ganeni bane"
"Good night" ya fada yana datse wayar,ya cillata saman gadonsa,sannan ya waiwayo gareta.
Bacin ran data gani cikin idanunsa ya sake sanya jikinta yin laushi,bayan ta gane wace rose din
"Indai rashin hankali da rashin nutsuwa zaki saka a gaban hankalinki zakita aikata abinda zai kaiki ga nadama mara amfani,tsabar banzan kishinki yasa idanunki sun rufe ki kasa gane wace tayi kiran,rose dince baki sani ba?,kiyi a hankali dani ki fita idanuna hafsat,idan kika kaini bango zan baki mamaki wallahi" can qasan ranta taja tsaki,ya jima yana fadin zai bata mamaki,wanne mamaki kenan,amma a saman fuskarta saita yamutsa fuska tana nuna rashin jin dadi
"Ai kasan bansan ita bace,inda na sani ai bazanyi mata haka ba,kuma itama ta yaya zata kira.mutum da aurensa a irin wannan lokaci?"
"Bakiji dalilin da yasa ta kira bane?" Ya fada a tsawace ransa na sake baci,har abada kenan ita ba zata gane tayi laifi ba saita kawo nata uzurin?
"Ina jaddada miki ki shiga hankalinki,bani da lokacin kule kulen mata,amma idan naso ke baki isa ki hanani ko ki tsaidani ba" ya fada yana nunata da yatsa.
Maganar ta doketa itama,to me yake nufi?,taso hasala amma sai ta bagarar,tasan ya fada ne kawai don ya tunzurata ya bata haushi itama,tafi kowa sanin waye abbas din,bata da wannan damuwar don ya fada.
Yadda ya banzatar da ita yana shiryawa taji duk ta takura,saita taka a hankali ta isa inda yake tsaye,ta rungume faffadan bayansa da yake shirin lullubewa da riga
"Kayi haquri don Allah,kuma na shirya zan bika kadunan" maganar tata tazo masa a bazata,wannan yayi nasarar saukar da fushinsa cikin qasa da second biyar,ya ajjiye rigar hannun nasa,ya waiwayo ya kama hannyenta ya zaunar da ita gefan gadon sannan shima ya zauna.
Cikin qwayar idanunta ya sanya nashi sannan ya fara mata magana a tausashe
"Bansan me yasa kika kasa fahimatata ba har yanzu,tsahon shekara biyar cikin ta shida,bani da burin da ya wuce naga gidana da iyalina cikin walwala fahimta da kuma qaunar juna,wannan rayuwar ba itace mafarkina ba a rayuwar aure na,inason gidana ya zama very romantic place,matata ta zama tafi kowacce mace iya soyayya tsafta tattali da iya kula dani,wannan shine nawa qarfin gwiwar da zai bani damar tafi da ayyukana yadda ya dace,ya kuma qara kusancinmu,ban takuraki zuwa kaduna saboda radin kaina ba,nayi hakanne saboda na jawo kusanci a tsakaninmu,kusancin da zai sake haifar da sabuwar soyayya da shaquwa tsakanina dake,ni abbas babu wata mace a gaba a yanzu,duk sanda kuma kikaga wata mace ta shiga rayuwata ba shakka gazawarki ne,daga gareki ne,na baki wannan satar amsar,ruwanki ki tare ko ina kiyi gadin qofar,ruwanki ki bada dama a shiga,amma kiyi qoqari mu zauna lafiya" a daren dai anyi abun arziqi,duk da daurewa kawai takeyi,abubuwa biyu ne sukayi mata tsaye a rai,maganarsa ta qarshe da kuma taraddadin barin bauchi ta koma rayuwar kaduna.
A dukka hasashenta bata ga wata qofa da ta baiwa wata mace ta shiga rayuwarsa ba,tana kishinsa irin kishin dake matsewa kowacce mace qofar shiga rayuwar mijin wata,tana kaffa kaffa da shigarsa da fitarsa,a gida gwagwadon abinda zata iya tana masa,saidai shi da baya gani ma,amma tana takura a abubuwa da yawa duk don sabodashi,batasan kuma me ya rage ba,me yakeso kuma?.
_wannan kenan_
Kwanaki biyu suka qara suka gama shirinsu,har zuwa lokacin yana mamakin abinda ya sauya mata ra'ayin binsa kadunan,saidai bai matsa da sai ya sani ba,tunda zurfafa binciken a wadansu lokuttan ba alkhairi yake haifarwa ba.
Ana gobe zasu tafi ya sanyata ta shirya don suje su yiwa hajiya sallama,daga nan kuma ya sauketa a gidansu,tana ta qoqarin danne zuciyarta ne,da kuma bin dukka abinda yakeso,saboda bataso ta bata hanyar data fara sharewa kanta,don antyn ummee tana ta jan kunnenta kan sai tayi juriya,kuma saita kula,don haka ta shirya ta bishi.
Hannu bibbiyu hajiyan ta karbeta kamar yadda ta saba,cikin kirki da karamcin nan nata,ba laifi hafsat din kadaran kadaham itama,har suka gama gaisawar suka taba hira sama sama,saita miqe tana duba agogo gami da kallonsa
"Inaga ya kamata ka saukeni a gidan,lokacin yana tafiya" kansa ya dauke daga kan jaridar da yake dubawa ya kalleta,har ya buda baki zaiyi magana hajiyan ta rigashi
"Gaskiya kam,kuma sallama zakuyi ya kamata ace kinje da wuri don ki samu isashen lokaci,tashi ka sauketa abbas" baice uffan ba,saboda maganar hajiya gaba take da maganar kowa a fadin duniya,banda haka xamanta a gidan yayi kadan sosai,duka duka ko awa guda bata rufa ba,sai ya ajjiye jaridar ya miqe yana daukan key din motar sa ya fice,ta yiwa hajiya sallama,ita kuma tasa muneera ta bita da kayan amfanin kitchen data tanadar musu,kamar su kuka kubewa daddawa kanwa da yaji da sauransu,saboda tasan abbas din ma'abocin son tuwo ne,a halayya kuma irin ta hafsat din babu lallai ta tsaya tunanin tanadarsu,ta bisu da addu'a suka lafiya,qwaqwalwarta fal mamakin yadda hafsat din ta sauya ra'ayi,duk da bata tsaya tambayar abbas din ba.
***********
Gab da sallar magariba hajjaa ta iso gidan hajiyan,cike da gajiya da kuma farincikin gama cooking classe din da sukayi na kwanaki biyar,wanda dai dai yake da na kwanaki sittin a wata makarantar,ita kanta tasan ta qaru over da abubuwa masu yawa.
Tana shiga ta miqawa nujood jakarta ta daura alwala kawai sannan ta shige falon hajiyan,ta zauna suka gaisa hajiyan tayi mata sannu,sannan ta kira muneera kan ta zubo abincin dare suci kafin su wuce
"Hajiya da kin barsu,yauma kafin na fito sai da nayi girki"
"Me yasa kike nuna wa gidan nan kamar ba gidanku bane hadiyya?,kinga muneera zubo,idan ba zata ci ba yaran zasu ci,xakuci ai ko widad?" Tayi tambayar tana kallon widad,wadda keta faman hada kayansu a jaka tana kammalewa.
Murmushi ta saki tana sadda kanta qasa,ba tare data amsawa hajiyan ba
"Au,babarki zaki goyawa baya kenan,sai faman hada kaya kike,kamar dama kin gaji da zuwa gidanmu " wannan karon har sai da haqoranta suka fito tana dariya cike da kunya
"Ba haka bane hajiya,muna ta saki aiki fa kwama biyar din nan,kema zaki huta" maganar yarinyar saita burgeta,ta kuma sake saka mata qaunarta a zuciyarta,haka kawai cikin kwanakin taji yarinyar ta kwanta mata,tana kuma burgeta,saboda taga bambancin dabi'a tsakaninta da sauran yara,sau tari takan zauna nan kusa da hajiyan suyita hira abinsu,widad din najin hajiya kamar ummunta,idan tana tare da ita sai taji kamar ummu,tana debe mata kewarta sosai.
"Ni ai ban gaji da ganinku ba widad"
"To mu zauna hajiya?" Ta tambayeta cike da quruciya,murmushi hajiyan ta sake,ta waiwaya tana duban hajjaa dai dai sanda ta sallame daga sallar
"nikam da zaku bani widad da nayi murna na kuma gode muku" dariya hajjaa ta saki,ba tare daga fahimci abinda hajiya ke nufi ba,ta zare hijabinta tana cewa
"Widad hajiya?,wannan mara sabo din da rashin sakewa da mutane?,idan muka baki widad ai mun gayyatowa kanmu ummu,takanas zata tahi bauchi ta dauke kayarta,dama 'yar aro ce" kai hajiya ta kada
"Ni ba aro nakeso a bani ita ba,inaso a bani ita na baiwa abbas dina,kinga shikenan ta zama diyata babu zancan aro kuma" a yadda hajiyan tayi maganar yasa hajjaa maido hankalinta jikinta,ta kalli fuskar hajiyan da kyau,sai taga gaskiya baro baro kwance saman fuskarta,kalamanta sunyi kama da kalaman da suke fita daga can qasan zuciya,babu alamun wasa ko kakaci a ciki.
Daurewa hajjaa tayi tayi murmushi,don zancan gaba daya sanyayar mata da jiki yayi,abbas hajiya ke magana,dan gayun matashin nan, mahaukacin damarar nan da kwanan nan aka qara masa rank?,abbas din dake da mata da yara biyu?,,abbas fa
"To ai hajiya idan kinaso sai a bakin ai"
"So kai,saboda inaso dinne ma na sako zancan,amma dai zan sake tuntubarki,ki shaidawa muhsin din"
"To hajiya ba matsala" ta fada tana murmushi,zuciyarta na bata da wasa hajiyan tayi maganar,saita maida dubanta ga widad wadda tuni ta matsa gaba suna magana da nujood,don haka batasan ma wainar da ake toyawa ba.
Sanda suka tashi tafiyar kayan ciye ciye ta hada musu da yawa a leda,hajiyan 'yar gatan tsohuwa ce,babu abinda ta rasa a gidanta,wannan ya sanya babu abinda zakaje baka samu ba a gidan.
*BAYAN SATI DAYA*
Tsaye take hadiyya take cikin kitchen din tana hadawa uncle muhsin abincinsa,gefe daya yaranne gaba daya sun cika mata kunne,hayaniya suketa yi suna tsokanar widad,wadda gaba daya cikin satin ta fara birkice musu,tunda tayi waya da ummun ta gaba daya hankalinta ya karkata zuwa komawa gida
"Ya isa don Allah kuyi mana shuru" waiwaya tayi ga widad
"Zan gayawa uncle dinki kada ki damu,zai kaiki kiga ummun da kansa indai free yake bashi da aiki" kai ta gyada tana danjin relief a ranta,a kwanakin nan ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta gaban ummun,bata taba zaton akwai abinda zai kawo rabuwarsu haka na tsahon lokaci ba,tama yi qoqari,don ko kwana guda batayi gidan kowa indai ba tare da ita ba,sai gashi yau ta doshi wata kusan guda cur.
Sanda hajjaa ta isa yana amsa waya ne,saita zuba masa komai ta kuma jera a gabansa,tana niyyar tashi don ta koma kitchen din ta sallami yaran yayi mata nuni da hannu kan ta zauna,saita koma ta zauna din,ya kammala wayarsa ya kashe yana dubanta
"Wanne saqo hajiyan abbas ya baki baki gayamin ba?" Cikin mamaki don ita sam ta ajjiye wannan batun tace
"Saqo kuma?,anya kuwa?"
"Gashi yanzun ta kirani tana tambayata,tace idan kin kammala gayamin din zata sake kirana" sai a sannan hankalinta yakai,tadan dafe kanta tana fadin
"Ya salam,wallahi sai da kazo da maganar na tuna" kansa ya girgiza
"Bai kuma.kamata ba,hajiya kamar uwa take a wajenmu gaba daya"
"Ba haka bane abba,zancan ne naji kamar zolaya take yi,hankali na bai kama ba" ta fada tana kada kai
"Wanne irin zance ne haka?" Uncle muhsin da ya fara cin abincinsa ya fada yana kallonta
"Widad takeso a basu ta baiwa abbas aurenta"
*_AREWABOOKS: Huguma_*
*RUMBUN K'AYA*π₯
*DAUDAR GORA*π₯
*IDON NERA*π₯
*A RUBUCE TAKE*π₯
*KI KULANI*π₯
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*π₯π₯π₯π₯π₯
0022419171
Maryam sani
Access bank.
Shaidar biya tananππ»
09033181070
*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*
09166221261
π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+227 90 16 59 91
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*Thanks for choosing us*π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:huguma*
Page 18
Shi kansa zancan yazo masa a bazata,sai ya ajjiye spoon din hannunsa yana duban hajjaa
"Abbas....abbas nawa fa" kai ta gyada
"Eh shi" kamar me jiran hajjaa ta tabbatar masa da batun sai ga kiran hajiya ya sake shigowa wayarsa,ya kalli wayar na wasu sakanni zuciyarsa na gaya masa da gaske hajiyan take,tunda har ta kasa sakat saita samu tabbacin isar saqon kunnensa,ya dauka wayar a nutse ya kara a kunnensa
"Ina fata saqon nawa ya riskeka?" Kai ya gyada kamar tana gabansa
"Eh hajiya,yanzun take isarmin dashi"
"To alhamdulillah" ta fadi tana sauraren ji daga gareshi
"Amma hajiya....wani hanzari ba gudu ba,kina ganin babu matsala daga wajen shi abbas din?" Yayi tambayar saboda sanin halin abokin nasa,sun jima a tare tun zuwanshi bauchi,duk da cewa ya girmewa abbas din,amma suna tare dashi,don itama dama abota ba sai da sa'anka ba,takan iya zuwa ta kowacce fuska,Itama hajiyan kai ta kada kamar yana wajen
"Bani da haufi akan abbas ko kadan,bamu ita din shine mai wuyar" sosai hajiyan ta aza masa nauyin da bazai iya kufcewa ba,tana masa kallon mazaunin uba a wajen widad,tasan kuma ya isa ya zartar da hukunci a kanta shi yasa ta nemeshi kai tsaye,uwa uba kuma abbas din wani irin mutum ne mai kima da daraja a wajensa,yafi kowa sanin irin qaunar da yakema mahaifiyarsa,kamar yadda ta dauki shi shima a mazaunin d'a,bai kyautu ya dubi tsabar qwayar idanunta yace mata bazasu bada auren widad ga abbas din da yana sahun farko farko na wadanda zasu bada shaidar kyawun hali da nagartarsa,bayan gajeran nazarin da bai wuce shurun sauraren hajiyar ba ya amsa mata
"Hajiya ai abbas nawa ne,babu damuwa,an bashi widad,zan kuma sanar da can gida in sha Allah". Irin addu'ar da yaji hajiyan tana kwararo masa sai da abin ya bashi mamaki,wanne irin so take mata haka?,lallai da bai amsa ba Allah ne kadai yasan rashin dadin da zataji,duk da ba zata nuna masa ba.
Wayar ya ajjiye gefe,ya daga kai yana duban hajjaa data tsareshi da idanu,kafin yace komai ta rigashi
"Abbaa,aure fa kake bayarwa,auren widad din da ummu ta baka aronta?,ba tare da sahalewar ummu ko yaaya mahmud ba?" Dan gajeran murmushi ya saki
"Yadda zan bada auren nujood kai tsaye babu haufi haka zan bada na widad,ina da wannan license din"
"Amma kana ganin aurenta da abbas yayi dai dai?" Ta sake tambayarsa cikin jin d'ar d'ar da fargaba
"Yana da wani aibune da musulunci yace idan namiji yana dashi bai cancanci ku bashi auren diyarku ba?" Kai ta girgiza da sauri
"Ko kadan,abbas nagartaccen mutum ne mai kyawawan dabi'u abun kwaikwayo,amma abba kada fa ka manta yana da mata,sannan matarsa din nan ko kwanaki na danji ana kuka da ita,bata da kirki abba,zamansu da widad mai qananun shekaru a mazaunin kishiya zai yiwu?"
"Duka ba wannan bane abun dubawar ba,tunda ba ita zata zauna da ita ba,indai ya cancanta magana ta qare" sai ya dauki spoon dinsa yaci gaba da cin abincinsa,dama tasan haka zaya fada,su maza nasu hangen daban dana mata,gaba daya hanakalin hajjan bai kwanta ba,bawai don abbas bai cancanta bane,aah,tana duba wani abu na dabanne,don haka ta gaza barin maganar
"Gaskiya abba bazan tayaka gayawa ummu wannan maganar ba wallahi,kada ka sani a ciki" dariya yadan saki
"Matsoraciya,yo waye ya sanya dama dake?"
"Amma zataga a gidana aka shirya fa,gashi widad dinma ta matsu tana son zuwa gida,ya za'a yi kenan?"
"Dama ina tunanin next week qarshensa taje taga ummu din,saboda ita kanta ummu kwanan nan maganar na dawo mata da yarinya taketa yi" shuru ya ratsa tsakaninsu,har uncle muhsin din ya fuskanci kamar ta shiga damuwa ne,don haka yayi gyaran murya
"Ni banji komai game da haka ba hadiyya,abbas yana da nagartar da ko nujood yace yana so zan bashi,zai riqe mana widad da amana, sa'annan kuma ina da tabbaci hundred percent karatunta bazai yanke ba,zataci gaba da karatu har zuwa inda takeso,so kinga babu wannan haufin"
"Gaskiya kam" ta amsa masa tana dan jin nutsuwa kadan,to amma batun zama da kishiya tasan ba abu bane mai sauqi,koda ga babbar macace bare yarinya irin widad,GOYON KAKA.
**********
Tunda hajiya ta samu tabbacin samun widad daga wajen uncle muhsin wata nutsuwa da farinciki ta dinga saukar mata,haka kawai ta dinga jin nutsuwa da gamsuwa da al'amarin,ta dinga ji kamar ta daga waya tace yazo tana son ganinsa,to amma tasan zuwa qarshen wata zai zo ganinta,babu buqatar ta daga masa hankali ta sanyashi biyo hanya,sai tayi amfani da wannan damar ta yawaita addu'a kan Allah ya sanya dukkan alkhairinsa akan lamarin,yasa ayi a sa'a,ya kade dukkan fitina.
************
Dukka shirin da yakeyi tana zaune gefan gado tana kallonsa,a yanzun da zai tafi bauchi tana jin inama yace ta shirya ta bishi,zaman garin ya gama kai mata ko ina,daurewa kawai take tana cijewa,ita kam duk inda zama zai kaita indai ba cikin garinta ba bataso.
Bugu da qari taga sabon key din mota garin bincike bincikenta,tana sake dauriya akan dauriya ne cike da fatan wannan motar ta zamana tata ce kamar yadda anty ummee data baiwa labari tayi mata hasashe.
Tsaf ya shirya cikin yadin kufta,wanda yayi matuqar masa kyau,ya fidda kwarjininsa da kuma kyan zubi da Allah ya bashi,saita sake karkata kai tana qare masa kallo,sau tari ita kanta takan gayawa kanta tabbas abbas wani rabo ne nata da Allah ya tsaga mata sai ta sameshi,amma ita kanta idan ta tsaya ta kalli kanta tana gano tarjn banbance banbance tsakaninta dashi,shi yasa take qara matsa qaimi wajen kishinsa,saboda tana tsoro.....tana tsoron kada idanun wata ya fada kansa,ta kuma sani wasu 'yammatan indai suka baza komarsu sai sun samu,bata fiya damuwa dashi ba,tasan sam mata basu a lissafinsa,amma shi din yana cikin lissafin gomayyar mata da suke kwana su kuma tashi da soyayyarsa,koda cikin danginsa kuwa tana da wannan information din akansa.
Hure mata idanu yayi da sassanyar iskar bakinsa,abinda ya sanyata ja da baya da sauri,sai kuma ta saki murmushi
"Har ka bani tsoro" ta fada tana dan harararsa
"Ni kika bawa tsoro,wannan kallon kamar zaki cinyeni?" Murmushi ta saki
"Da da hali cinyekan zanyi,don banason kowacce mace ta kalleka kota rabeka,ni kaina bansan adadin kishinka da nake ba" daga kai yayi ya kalleta daga daura agogon da yakeyi,har launin fuskarta ya sauya,sai ya maida kai yaci gaba da daura agogonsa ba tare da yace da ita komai ba.
Ya rasa wanne irin dan banzan kishi take dashi,wanda kullum baya raguwa saima daduwa da yakeyi,abun takaicin har yau batasan yadda zata tsare masa komai ba,inda yadda take kishinsa haka ta tsaya masa wajen komai da lallai ya gama yin sa'a.
Ganin bai bata amsa ba tasan bazai ce komai ba,don haka ta sauya akalar maganarta
"Nidai da zaka barni Allah wannan watan zan bika,kamar na shekara banje gida ba haka nakeji"
"Sai next month kamar yadda nace" ranta tadan bata kadan,har ya gama shirinsa ya fito bata sake magana ba.
"Rakiyar ta isa daga nan" ya fada yana dakatar da ita daga qofar falon,saboda akwai driver daga waje da zasuyi tafiyar tare,mutum ne shi mai tsananin kishin iyalinsa,yakai bakinsa saman goshinta yayi kissing dinsa yana fadin
"Sai na dawo,ki kula da gida da yaran"
"A dawo lafiya" ta fada a taqaice tana dubansa har ya fice,tana tsaye ta window tana leqensa har motarsu ta fice,taja da baya ta zauna saman kujera tana jan tsaki
"Babu biki ba suna ba barka,an takure a baqon muhalli" ta sake fadi a fili,sai kuma ta miqe ta nufi dakinsa,ta buda ta shiga ta isa inda taga key din motar,ta jawo da zummar sake duba motar wacce ce?.
Wayam taga wajen babu muqullin,ta shiga birkitawa kamar wadda ta bashi ajiya,saidai babu shi ba alamarsa,da alamu ya dauka kenan,to amma me zaiyi dashi?,ta tambayi kanta tana zurfafa tunaninta,to ba tata bace kenan?,amma kuma motar da suka fita cikinta ai tasan motar,ba sabuwa bace,gaba daya sai ranta ya baci,ta jawo waya kamar zata kirashi ta tambayeshi sai wata zuciyar ta hanata,ta shawarceta ta bari ya isa gida tukunna.
*_RUMBUN K'AYA_*
*_IDON NERA_*
*_DAUDAR GORA_*
*_KI KULANI_*
*_A RUBUCE TAKE_*
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*π₯π₯π₯π₯π₯
0022419171
Maryam sani
Access bank.
Shaidar biya tananππ»
09033181070
*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*
09166221261
π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+227 90 16 59 91
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*Thanks for choosing us*π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*
Page 19
Kafin ya iso tuni hajiyan ta sanya an tanadar masa abincin da yafiso har kala biyu,irin abincin da tasan zaiyi wuya ya samu a gidansa,duk da qaunar da yake masa,ta kuma hada masa lemo shima kala biyu,zobo da kuma ginger drink da aka dan matsa lemon tsami kadan a ciki qamshinsa ya fito.
Da yake tun karfe tara na safiya ya taso,ana azahar yana shiga layinsu,jakarsa kawai ya bayar aka shiga dasu shi da drivern nashi da yake usulmi ne suka wuce masallaci.
Ana idar da sallah yace masa zai juya ya koma kaduna,yasan akwai aikin da ya baro,saboda haka bai matsashi ba,yadai karba abincin wajen hajiyar ya hadashi dashi,yace yaci a mota,ya kuma fidda kudi masu dan nauyi yayi masa ihsani,wannan yana daya daga cikin abinda yasa abbas din ke samun biyayya da qauna gami da daukaka a wajen aikinsu,duk da biyayya dole ce a tsarin aikunsu,amma suna masa soyayya ne ta har cikin ransu saboda kyawawan dabi'unsa.
Cikin nutsuwa ya shiga gidan nasu,yana jin farincikin ganin hajiyar tasa,jtama tana falo a zaune tana ta dakon shigowarsa,ta amsa sallamarsa ya sanyo kai falon fuskokinsu dukka dauke da murmushi.
Kamar kullum ya duqa a qabanta ya gaidata,ta amsa masa cikin kulawa addu'a gami da tambayar lafiyarsa data iyalinsa,ya tabbatar mata da komai lafiya lau,ya kuma isar mata da saqon gaisuwa daga hafsa din,wanda a zahiri bata samu hakan ba,shi ya qirqira abinsa saboda sama mata soyayya da kuma kare martabarta a idanun mahaifiyarsa.
Da kanta tayi serving nashi,yana cin abincin suna hira,wanda kusan abubuwane da suka dan faffaru da baya nan,ciki harda ciwon da diyar babbar yayarsu tayi
"Zanyi qoqari na shiga in sha Allah"
"Ya kamata,don ka kwana biyu bakaje mata ba,tana ta min qorafi rannan"
"In sha Allah".
Sai da aka kira la'asar sannan ya fita a falon,yace ma hajiyan zaije wajen Suraj,amma bayan magariba zai dawo
"To Allah ya tsare,akwai maganar dama da nakeson nayi dakai"
"To bari na zauna mu gama sai na wuce"
"A'ah,jeka abunka,idan ka dawo mayi maganar,Allah ya tsare".
Tsahon lokaci suka dauka shi da suraj din,saboda kwana biyu basu hadu ba,yanayin ayyuka da canjin muqamai da abbas din ke samu a kufi a kufi,anan suraj din ya samu damar masa qorafin
"Naji mamaki sanda naji ka ajjiye appointment dinka,dama cefa da 'yan sanda da yawa suke jira" kansa ya shafo kadan yana duban suraj din
"Nafi nutsuwa da hakanne suraj"
"To kuma gashi sun biyoka da asp ba"
"Gwara wannan kam,qarin matsayi ne,a tayamu da addu'a Allah ya bamu wuyan dauka da saukewa"
"Ameen ya rahman".
Bayan sun idar da magariba suka sake fita da suraj din a mota ya rakashi wani waje,a hanya ya tsaya qofan wani suya spot yana kashe motar
"Kadan rakani ciki na yima hajiya siyayya mana"
"Ba damuwa muje mana",tare suka jera xuwa cikin,suna tafe suna hira har suka isa,suka wuce kai tsaye inda zasu bada order din abinda sukazo siya din.
Sun samu 'yammata biyu tsaye gaban kantar,wanna yasa abbas din ya bada taqi a tsakaninsu,ya tsaya daga baya baya suna ci gaba da magana da suraj din,irin hirar da ta shafesu.
Tunda suka tsaya din gaba daya hankalinta ya karkata a kansa,ba qaramun daukan hankalinta abbas din yayi ba,shigar qananun kayan dake jikinsa sun taimaka wajen fidda surarshi ta qaqqarfan namiji,har suka gama biyan abinda zasu siya din,saita bude da duba wayarta tadan matsa gefe kadan tana cewa qawarta
"Ina zuwa".
Hankalinsa nakan suraj yana saurarensa yana saka order din abinda yakeso,har yaso yayi mistake ma saida waiter din yayi masa magana,aka hada masa komai ya irga kudin cikin wallet dinsa ya aje musu,saidai garin daukan ledan bai ankara ba ya dauki tata ledar,tana sane ta barshi har sai da isa gaban motarsa sannan yaji ana fadi cikin siririyar muryarta dake nuna zallar yauqi da gwalli
"Hi.....hi,ranka ya dade" cak ya tsaya,don har ya bude murfin motar,ya waiwayo don ganin ko dashi ake.
Da murmushi ta dinga jifansa har ta iso,cikin tausasa muryarta tace
"Yallabai ledata ka dauke" ledar hannun nasa ya daga ya kalla,sai sannan ya lura,ya sauketa gami da miqa mata yana cewa
"Sorry"
"Ba laifi ai,hakan yayimun,kaga ko babu komai leda zata qulla mana zumunci" bai amsa mata ba illa amsar tasa ledar da yayi
"Sunana rafi'ah" tayi saurin fada ganin yana shirin shigewa motarsa
"Good,thank you ko" matsowa ta sakeyi don fa fuskanci rufewa zaiyi
"Ko zan samu digits naka?"
"Am sorry to say no" ya fada yana maida murfin motar a hankali ya rufe,sannan ya tashi motar yayi reverse suka fice daga wajen.
"Har yanxu kana lokaci mutumina,bansan me yake fusgar hankalinsu ba haka,adan bani sirrin mana" ya fuskanci sarai abinda suraj yake fada,fuskarsa kadaram kadaham ya waiwayo kadan ya dubeshi sannan ya maida kansa ga titi
"Kai har yanzu baka girma na suraj,ana ta neman na abincin da za'a kaiwa iyali kuma wa yake ta wannan" ya fada yana shafar habarsa dake zagaye da gemun daya samu wadataccen tsafta da gyara
"Banga alama ba,don duk sanda muka fito irin haka sai wata ta taya"
"To ai sai suyita yi,ta gidanma ya ka cika da ita bare ka sake daukan wata,kayita hadama kanka rigima da zafi,bazan iya daukan wannan ba"
"Fada dai kake,bari ayi katari da wadda zata sace maka zuciya"
"Haka kake gani" abbas ya maida masa amsa,hankali da idanunsa naga titi.
Dariya kawai Suraj yayi,bai sake cewa komai ba suka shiga wata hirar.
Sai daya fara sauke suraj a gida bayan ya hadashi da tashi ledar sannan ya koma gidan hajiyan.
Bayan isha'i ya zauna sukaci abinci,kusan tare da hajiyan,saidai kowa kwanonsa daban,bayan sun kammala ya dauke kwanukan da kansa ya tattare wajen sannan ya dawo ya zauna yana fuskantar hajiyan
"Hajiya kince zamuyi magana ko?" Gyara zamanta tayi sosai
"Eh tabbas"
"To ina jinki,Allah yasa ba wani laifi nayi ba" murmushi ta sake
"Laifi abbas?,a'ah ko kadan,wani alkhairi na hango maka,na kumayi karambanin zartar maka dashi ba tare dana tuntube ka ba" qaramin murmushi ya saki
"Hajiya...ai kinfi qarfin ki yiwa rayuwata karambani,kome kika ga dama ki zartar dashi kanki tsaye kawai" kai ta dan jinjina sannan tace
"Aure na nema maka,'yar uwa ko 'yar muhsin" sosai gabansa ya fadi,abinda ya jima baiji irinsa ba tsahon rayuwarsa
"Hajiya nujood?" Ya fada cikin fargaba,don ko da ya kasance itace bazai iya musawa hajiyan ba,haka zai auretan,yarinyar dake kallonsa a mazaunin ubanta
"A'ah,widad" ajiyar zuciya ya sauke,sai yaji tashin hankalin da yake ciki din ya ragu,ya samu 'yar nutsuwa,duk da fahimci wa take nufi din ba,amma dai ya fahimci wata ce daban ba nujood ba
"Inason kaje ka ganta,duk da ina zaton zuwansu gidan nan kamar ka taba ganinta,amma wannan zuwa ne na musamman,kaje ka gabatar mata da kanka" kai yadan sunkui qasa
"In sha Allah hajiya zan saka rana sai na sanarwa muhsin din sai naje" har cikin ranta ta sake qaunar abbas din,tasan dama bashi da matsala kome kuwa tace yayi,saidai ta dauka zaiyi jayayya ko ya qalubalanci wannan danyan hukuncin nata.
Duk yadda yaso ya fidda damuwa ya zauna suyi hira sosai amma ya kasa,jiki da zuciyarsa dukka a takure suke,dole bayan qarfe tara ya yiwa hajiyan sallama ya wuce gidansa.
A kan hanya yana tuqi amma tunani ne fal kwanyarsa,aure?,wacece widad din ma?,oho shi bai ganeta ba,amma me hajiya ta hango masa?,sai Allah,bazai iya mata wannan tambayar titsiyen ba,da wannan damuwar da kuma tunanin ya isa gida.
Bashi da hadi da sassan hafsa,don haka sassansa ya wuce,yabude ya shiga yana tsaye tsakar falon kamar maison tuna abinda ya kamata yayi wayarsa ta dauki sassanyan busar sarewar dake a mazaunin ringtone dinsa,don bayason ringtone mai hayaniya da yawa,mafi yawan lokutta ma yafi barin wayar tasa a vibration.
Cikin wata kasala da gajiya da maganar hajiya ta saukar masa ya zaro wayar yana duba me kiran,hafsat dince,sai ya daga kiran yana neman kujera daya cikin falon ya zauna
"Ina ka shiga ne inata kira baka daga ba" ta fada muryarta a tsaye carrr,alamun qagauta da son samun mutum,shuru yayi yana nazartar muryarta
"Lafiya?" Ya fada da nutsatsiyar muryarsa mai nauyi,wadda ta dawo da hafsat din cikin nutsuwarta kadan,ta kuma fuskanci yanayin data masa magana baiyi dai dai ba,kishi ne keta cin ranta,har idanunta suka so rufewa,gani take kamar yana tare da wata ne shi yasa yaqi daga wayarta,
"Ah....uhmm lafiya qalau,kawai hankalina ya dan tashi da naga inata kira baka daga ba"
"Oh.....am fine,kufa?"
"Lafiya qalau muke,yara gaba daya sunyi kewarka"
"That's my babies.....kefa?" Ya fada yana danne damuwarsa,murmushi ta saki wanda ya jiyo sautinsa
"To nima nayi" ta fada tana danjin nauyi,idanunsa ya lumshe yana kuma budesu,she's not romantic woman at all,ya rasa yadda zai canzata,kamar irin matan da soyayya bata damesu ba sam,dai dai da greetings cards da yake siya mata time to time,musamman idan yayi tafiya ya dawo bata wani daukar abun da muhimmanci,wani lokaci ma idan ya kawo cards din bata ko budesu bare ta karanta,karba take ta ajjiye bayan ta bishi da SANNU.
"I miss you more than you can imagine" ya fada with softness,wanda har sai data ji tsigar jikinta ta tashi,wani abu ya tsarga mata,amma sai tace
"Allah ya qara zumunci"
"Zumunci dai?" Ya maimaita a ransa,even kalmomin da zatayi appreciating nasa bata dasu,har ya fara sabawa.
Shurun da ya gilma tayi amfani da wannan daqiqun
"Magana da zamuyi ko ince tambaya zanyi"
"Am sorry ranki ya dade,yanzun nan na shigo gida,bari na gama shiryawa saina kiraki,inaso yau ayimin hira sosai,na gaji da yawa"
"Kai da kaje hutu?,me kayi daya gaji da kai?" Ta fadi da salon tambaya,ita sam hankalinta bai kwanciya idan basa tare
"Yawo" ya amsa mata a taqaice,sai ranta ya sosu,anya ba abinda take zato bane
"Yawo kuma abban mimi?,don Allah ka daina banso wallahi"
"It's okay" ya fada fuskarsa na fidda miskilin murmushin da bai shiryawa ba,yasan meke damunta
"Ka kira da wuri,don bacci nakeji inason na kwanta"
"Okay" yace da ita yana katse wayar gami da ajjiye ta gefe
"Hafsat hafsat,ko sai yaushe zata canza?" Yayi maganar shi da zuciyarsa,sai ya miqe yana wucewa bedroom.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so,zasu fara fita a gobe da izinin mai duka_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 90 16 59 91
*Zafafa biyar kadai keda sinqin nau'ikan kalar labarun da kukafiso jimilla a lokaci guda*π€π
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*
Page 20
Sai daya gama duk abinda yakeyi ya kwanta yaja bargonsa zuwa qugu bayan ya rage hasken dakin sannan ya kirata.
Har tayi ringing ta gama bata dauka ba,ya sake kira karo na biyu sannan ta miqe daga kwanciyar da tayi,ta jawo wayar tana sakin hamma,dan qaramin tsaki taja,banda maganar da takeso suyi nada muhimmanci da bazata daga ba,batason zancan motar yayi nisa kada taje ta zama rabon wasu,abinda kawai bataso yanzun zaice saita tsaya sunyi hirar soyayya,batasan me dame zata ce masa ba,daga qarshe kuma ya tada mata feelings ko ya isheta da fitina idan ya dawo.
Cikin qaramin sauti tayi masa sallamar wanda baccin data fara ji ya jawo hakan,saidai shi din abun ya tabashi,har ya tada masa tsigar jikinsa,ya rufe idanunsa yana amsa mata
"Am sorry,na tasheki halan?"
"Ummm,babu komai"
"Thanks" da hanzarinta ta katsi numfashinsa
"Abban mimi ina cikin maka gyara ne shekaran jiya naga key din sabuwar mota,to yau kuma mimi ta tabo wajen ta zubda kaya,da na maida kayan banga key din ba,nace Allah yasa ba wani wajen ta jefa maka ba"
"Noo,ni na tafi dashi,motar dama ta hajiya ce,so sai na baiwa samuel nace gobe ya biyoni da ita a kawo mata,kinsan motar da ake fita da ita ta samu matsala" idan tace ga irin bacin ran da taji ya saukar mata ma ta yiwa kanta qarya,abinda taketa hasashe kenan,take kuma gudu,yanzun motar ya dauka ya baiwa hajiyan bayan yasan tana da buqata,tana ta kuma gaya masa ya canza matan bai canza ba?,ta yaya zata nuna masa ma zallar bacin ranta?
"Abban mimi amma dai kasan ina da buqatar motar nan ko?,sati nawa ina maka naci ka hanani?,amma a gabana ka siya......"
"Hafsatu" ya kirata da sunan da mafi yawa jama'a ke kiranta ba tare da ya bari ta idar da maganarta ba,kiran kuwa ya ratsa mata ko ina,yana da wata murya dake da kwarjini
"Baki gane wacce na siyawa motat bane?,hajiyata mahaifiya ta nake magana" boyayyar ajiyar zuciya ta sauke,tana kuma qoqarin sassauta harshenta
"Bance bakayi dai dai ba ai,amma nafi buqatar motar,da sai ka karba ta wajena ayi mata gyara ka bata,tunda hajiya bako yaushe ta fiya fita ba,sai ta dade a gida bata fita ba,zata iya manage da ita"
"Hajiyan tawa za'a bawa ragowar motarki tayi manage?" Cikin zallar mamaki ya jefa mata tambayar, jikinta daga can yayi sanyi,saidai bacin ran da takeji a zuciyarta ya hanata gayawa kanta tana fadin abinda bai kamata bane
"To menene a ciki?"
"A wajena wani abunne,idan bakisan darajarta ba ni nasan darajarta,tafi qarfin cin ragowar kowa a duniya bare taki ragowar,karki kuskura ki kaini bango da banzayen maganganunki,idan ba haka ba zaki gane kuskurenki,ki adana maganganunki basu da wani amfani a wajena,kudi dai nawa ne,zan kuma wahaltawa mahaifiya ta a duk sanda naso ba tare da shawara ko yardarki ba"
"Amma dai kasan nima ina da hakki ai a kanka ko?,tunda nima matark......"
"You are very stupid" ya fada da zafi yana datse kiran,bayason yaci gaba da saurarenta kada ta tunzarashi,idan ya tunzura baisan me zai biyo baya ba,yana kallonta tanata kiransa amma yaqi dagawa,sai ma ya maida wayar silent ya maida kansa ya kwanta yana ta furzar da iska a bakinsa ko zai samu zuciyarsa ta rage zafin da take masa.
Bayan kiran ya tsagaita da shigowa sai kuma wani haske yayi blinking,alamun shigowar tex,wayar ya jawo da niyyar kasheta gaba daya,saidai saqon ya fito saman screen din
_Tunda ni bankai wani bigire na abu mai muhimmanci a tare da kai ba,nima bazan zauna ina aikin da ba'a gani ba,zan dawo garinmu inda akasan darajata_
"Mtsweew,shirme kawai" ya fada qasa qasa,ya danne switch button ya kashe wayar gaba daya ya dorata saman bedside drawer,ya sake jan duvet yana rintse idanu,saidai gaba daya baccin yaqi daukarsa,muraja'a kwanyarsa ta shiga yi masa kan halaye da dabi'un hafsat,tun daga kan aurensu kawo yau,tun kafin aurensu ya fahimci wasu baqin halaye daga gareta,banbancin ra'ayi da kuma wasu abubuwa masu yawa,ya dauka idan sukayi aure zai iya canzata,ashe yayi kuskure,babu wani sauran canji,saima abubuwa da suke ta'azzara kullum.
Gefe daya kuma tunaninsa ya cilla kan maganarsu da hajiya,sai ya sauke ajiyar zuciya yana ambaton sunan Allah ya kawo masa agaji.
********Washegari bai tashi da wuri ba,saboda ya sanyama ransa babu inda zai fita yau din,sai wajen sha daya da rabi sannan ya shiga kitchen ya dafa irin tea dinsa ya soya qwai hudu ya dauki slice of bread ya hada dashi ya dawo falonsa ya zauna yaci,bayan ya gama ya kalli labarai kadan kafin ya canza wani program da akace masa jiya anyi da senior dinsu bai samu gani ba,bayan ya gama ya buda qofa ya karbi news paper wajen yaron dake kawo masa ya karanta,sai yayi wanka ya sanya wata jallabiya mai sulbi,wadda ta karbeshi sosai,ya daura alwala ya wuce masallacin dake gaban unguwarsu wanda suke sallah qarfe daya na rana,a qa'ida idan zai hau abun hawa zuwa masallacin zai biya 30naira amma ya zabi takawa a qafa,don tafiyar qafa ba baqon abu bane a wajensu.
Bai dawo gidan ba sai qarfe biyu da rabi na rana,don yadan tsaya da mutane,yaron dake masa aike aike ya aika ya samo masa masa me kyau ko tuwo,sai daya buda fridge yasha ruwa mai matsakaicin sanyi sannan ya samu waje ya zauna yana qoqarin kunna wayarsa.
Saqonni ne suka soma shigowa,kamar bazai bude ba don yana tsammanin hafsa ce,kada ya karanta abinda zai bata masa rai,sai kuma ya buda din,ba ita bace,ire iren 'yammatan dake crushing a kansa ne,yana mamakin ta inda suke samun numbers dinsa,bai ma batawa kansa lokaci ya karanta din ba ya goge saqon,yana tuna sanda yake barinsu ga wayarshi,irin tashin hankalin da sukeyi da hafsa din a kansu a lokacin,shi kuma rashin muhimmancinsu da rashin damuwa da masu saqon yasa yake mantawa ma dasu cikin wayar bare ya share kada ta gani din,yayin da kishi ke sanyata taga kamar yana sane ya barsu.
Number hajiya ya nema ya kira,suka gaisa,ya shaida mata yau bazai fito ba yana gida kada taji shuru,fatan alkhairi tayi masa sukayi sallama,kamar ya ajjiye wayar sai yaga akwai kuma wani haqqin bisa wuyansa,don haka ya nema number hafsa din ya kira.
Tsaf ta qaraci ringing dinta ta katse ba'a daga ba,sai ya sake kira amma sai aka gaya masa a kashe take,yayita qoqarin kira ana maimaita masa a kashe take,sai ya ajjiye wayar ya haqura,dai dai lokacin yaron da ya aikata din ya dawo ya karba saqon ya sallameshi.
Sai da yaci abinci ya nutsa sannan ya kira suraj,suka gaisa suka taba hirarsu sannan ya buqaci ganinsa
"Yau bana gari,na danyi balaguro azare,amma yau din zan dawo,zan sameka gida gobe"
"Yayi,babu damuwa,saina jika" sukayi sallama.
Wunin ranar a gida yayita shi kadai,yanata juya maganar auren da hajiyan ta nema masa,saida yamma ne ya fita farfajiyar gidan ya motsa jikinsa,ya danyi strolling cikin layinsu zuwa baya sannan ya dawo ciki.
A farfajiyar gidan ya sanya musu kujeru shi da suraj,sannan ya dafo musu black tea wanda yasha kayan qamshi da ganyayyaki masu dadi,ya zubo musu a wata buta me hade da wasu irin cups ya zuba ya miqawa suraj,sannan yaja kujera yana zama
"Kai....abbas badai iya dafa tea ba wallahi"
"Zaka fara ko?" Kai ya girgiza yana dariya
"Kasan Allah?,sai an tara mata da yawa basu iya dafa tea kamar haka ba" baice komai ba illa kai nasa cup din baki da yayi,saboda yasan haka dinne,koda a cikin gidansa ma,don yawancin lokutta ya gwammaci ya tashi ya dafa tea dinsa da kansa akan yasa hafsat ta dafa masa,indai kaga ya sha nata to lalura ce babu yadda zaiyi.
Suna shan tea din suna taba hirar da bata qarewa tsakaninsu,suraj din aboki ne na tun lokacin quruciya har zuwa girma,kuma har yanzun kusan shine babban abokinsa sannan muhsin ya biyo baya.
"Kace kana son ganina,me ya faru?" Cup din abbas ya ajjiye,yana hade yatsun hannunsa guri guda,sannan yayi crossing qafafuwansa suma yana duban suraj din,sai kuma yadan shafi goshinsa kadan sannan ya fara magana
"Bansan ta ina ma zan fara maka bayani ba suraj,hajiya ce ta nema min auren 'yar yayan muhsin"
"Ummm,kaga dan gata...kai yanzun ma auren sai an nema maka,bana fari ba ba komai ba?"
"Akwai matsala suraj" da dan mamaki saman fuskarsa yake dubansa
"Matsala ta meye?,matar ce bata yi maka ba ko kuwa?" Kai ya girgiza
"Ba wannan maganar ake ba,don ko fuskarta ban sani ba,suraj cikin gidana akwai matsala sosai,ban kuma gama solving matsalar ba ta yaya zan qara aure suraj? Da shegen kishin hafsa zanji ko kuma da sabon auren da nayi?,beside ma kwata kwata banajin ina da cikakken lokacin fuskantar matsalolin mata bayan wadda nake ciki" Murmushi suraj din yayi cikin kwanciyar hankali,ya kuma gyara zamansa da kyau,shi kam kamar hajiya ta shiga tunaninsa ne,wannan abun da tayin shawarar da ya dade yana son bawa abbas din,amma kasancewarsa ba mai magana ba,ba kuma me fadan sirrinsa ba yasa ya qyaleshi ya zuba masa idanu,duk da cewa mutumin da yake da matsayi a wajensa kamar suraj dake shiga gidansa lokaci bayan lokaci zai fuskanci akwai damuwa a gidan,daga fannin tsafta kawai zakasan akwai nakasu,tunda tsafta da qazanta basa boyuwa
"To ai kai abinda baka sani ba,wannan auren shine hanyar gyaruwar duk wata matsala taka da damuwa"
"Kamar yaya?" Ya tambayeshi yana dan yamutsa girarsa
"Bari nayi maka gwari gwari,yawancin mata suna qoqarin ganin sun gyara tsakaninsu da mazajensu ne a sanda suka qara aure,gudun kada kishiyar data shigo taga gazawarsu,ko ta qwace musu miji ka fahimta?,to sai kaga itama ta zage damtse don kar a barta a baya,gefe guda kuma ga kulawa daga amarya kana samu,kowacce qoqari take taga itace star a wajenka" shuru abbas yayi kawai yana jin suraj,mai daki shi yasan inda yake masa yoyo,baya tunanin qarin aurensa zai zama gyara ga hafsat,amma bai san ikon Allah ba,kawai abu daya ya sani,ko ransa hajiya tace ya cire ya bayar zai iya,bare wannan buqatar da bata fi qarfin ikonsa ba,ya sauke ajiyar zuciya yana zama sosai cikin kujera manyan idanun san nan akan suraj
"Hajiya tafi qarfin komai a wajena suraj,batun rashin karba ma bai taso min ba,kawai inason jin yadda za'ayi" dariya yayi ya koma ya jingina da kujera
"Ya kuwa za'a yi,kawai ka shirya kaje kuga juna kai da ita,sai mu fara shirin biki".
*********Tunda hajjaa ta gaya mata saura kwanaki biyar ta tafi kano take murna da zumudi,kullum cikin shirya kaya take,ko ta shirya sai ta fiddasu ta sake shiryawa,kowa a gidan dariya yake mata yana tsonakarta,ranar da nujood ta tsokaneta da cewar
"Dama abba yace an fasa" fada suka kusa yi,taqi kula nujood din wunin ranar,saida hajjaa ta shiga batun ta musu sasanci.
Saura kwanaki uku ta tafi da yamma suna kitchen suna ma hajjaa yanke yanken kayan miya,da yake tun zuwansu hajjan ke hadasu su shiga kitchen tare,ko daya widad din bata da son jiki,kuma tana sha'awar yin girkin dama,ummu ke hanata tana ganin kamar zata qone ko kuma wani abun zai sameta.
Uncle muhsin ne ya shigo,dawowarsa kenan daga aiki,kai tsaye ya wuto kitchen din ya tsaya bakin qofa ya leqo yana tsokanarsu
"Manyan 'yammata ne ke girki yau kenan" murmushi hajjaa tayi
"Aiko dai yau su abba za'a ci dadi"
"To Allah ya taimaka,dan zo mana minti uku"
"To abba" ta fada tana tsame hannunta daga abinda take tabi bayansa.
Sai da suka shiga bedroom dinsa,ta tayashi ya rage kayan jikinsa sannan yace mata
"Widad fa gobe zatayi baqo,hajiya da kanta ta kirani ta gayamin gobe abbas zaizo suga juna" baki hajjaa ta kama tana murmushi
"Ikon Allah,abu kamar wasa yana shirin zama gaske,to Allah dai ya doramu akan 'yar rigimar hajiyan,tunda dai abbas ba shine na farko ba"
"Ba komai in sha Allah,idan sun gama girkin ki turon ita nayi mata magana da kaina"
"Yafi dai abba" sai yayi dariya
"Na fuskanci tsoro dai kike"
"Wallahi abba,Allah dai ya tabbatar da alkhairi,ya kauda fitina"
"Ameen ya rahman" ya amsa mata yana nufar bandaki,ita kuma ta baro dakin da zummar zuwa ta kawo masa abun sha kafin girkin ya kammala.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 90 16 59 91
*Zafafa biyar kadai keda sinqin nau'ikan kalar labarun da kukafiso jimilla a lokaci guda*π€π
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 21
Sai da suka gama cin abincin ma sannan uncle muhsin ya shigo,ya zauna suka gaisheshi,widad ta miqe zata tattara kwanukan uncle muhsin yace
"Dawo widad muyi magana,nujood debe kwanukan ke da musaddiq" da zumudinta ta dawo ta zauna,tana tunanin labarin tafiya gida zaiyi mata
"Widadun ummu" uncle muhsin ya fada yana murmushi
"Na'am uncle" ta amsa masa itama ta amsa masa murmushin,tun da tana son uncle muhsin sosai,kasancewar yana saya daga cikin jama'ar da suke nuna mata qauna da kulawa
"Akwai wani abokina,sunanshi abbas,yacemin yana son yarinya mai hankali da nutsuwa zai aura,nasan widad dina nada hankali da nutsuwa,ina kuma alfahari da ita,wannan yasa nace masa yazo ya ganki kema ki ganshi" gabanta ne yadan fadi,saita dan rage fara'a kadan,uncle muhsin din ya karanci haka,don haka yayi murmushi
"Kada ki damu,indai kika ganshi baiyi miki ba shikenan,babu wanda zai takura miki kinji ko?" Kai ta gyada
"To uncle"
"Yauwa,Allah yayi albarka widad"
"Ameen uncle" ta amsa masa tana miqewa,jikinta yayi wani irin mutuwa,kamar zata daki sai kuma ta fasa tabi bayan nujood data tsaya a kitchen.
Wanke wanke ta samu tana shirin yi,saita tsaya gefenta nujood din ta waiwayo
"Menene?,na dauka zan ganki kina tsalle zaki gida,ko abban cewa yayi an fasa tafiyar?" Kanta ta girgiza
"Wai wani abokinsa ne zaizo gobe ya ganni yanason yayi aure" murmushi nujood tayi
"Ke wanne irin farinjini ne dake,amma abokin abba?,na sassan abokansa,wa yace miki?" Idanunta tadan juya alamar tunani na wasu sakanni sannan da sauri tace
"Wai abbas"
"What?" Nujood ta fada tana ajjiye plate din hannunta
"Wai uncle abbas abba yake nufi?"
"Oho,inajin shi dinne ko?" Ruqunqume widad nujood tayi,tana dan ihun murna
"Wayyo widad,don Allah kada kice baki sonshi, uncle abbas yayi mugun haduwa,saima idan yasa uniform din nan nasa,ga miskilanci ga tsafta ga gayu,idan yazo gidan nan har ya tafi qamshin turarensa yana nan,don Allah kice kin yarda" ture nujood widad tayi tana tura baki
"Dalla malama,ni ba wani nan,na barmiki ke ki cewa uncle kina so" dariya sosai nujood ta qyalqyale da shi tana cewa
"Ni ai babana ne,banda haka ni abba zai bawa,tunda kika ga bai bashi ba kuwa babana ne din" ita dai widad bata sake cewa komai ba,sai ta hau saman kantan kitchen din ta zauna,tana sauraren nujood nata bata labarin uncle abbas din.
Musaddiq ne ya shigo yayi kiran widad bayan kaman awa daya,yace tazo hajjaa nason magana da ita,ta sauko.tabi bayansa.
A bedroom dinta ta sameta tana daga wasu kaya
"Shigo mana widad" hajjaa ta fada ganin widad din ta dan rab'e,qarasa shigowar tayi,hajjan ta dan tsokanarta kan kayan tafiya kano take hada mata,don ta samu ta sake sosai tayi maganar da ta sanya aka kirata din dominta,ganin ta sake din sai tace da ita
"Kinji abinda abbanku ya fada ko?" Kai ta gyada mata ba tare da ta amsa mata ba
"Karki damu,abbas nada matuqar kirki,sannan shi din dan hajiya ne,hajiya dai wadda kuka zauna gidanta wancan satin" maganar data fada na cewa dan hajiyan ne ya sanyata sakin jikinta sosai,cikin dabara hajjaa keta janta da zance har ta saki jikinta,sai a sannan ta sallameta.
Da yamma lis ta kama widad din duk rashin son kitso irin nata ta sake wanke mata kai,tana ta qi tana turjewa,sai data sanya su musaddiq suka dinga yi mata dariya ,tare da waqar me kukan kitso sannan ta nutsu,ta raba kanta tayi mata manyan kalaba da suka jelarsu masu tsaho zubo gefe da gefan fuskarta,saura kuma suka sauka a bayanta,kasancewar ba kasafai ta fiya kitso ba saboda qin da take masa,sai kalbar ta haska fuskarta tayi mata kyau sosai,hajjaa ta qawata qarshen kowacce jela da duwatsun kitso masu yawa da suka qarawa kalbar kyau suka taimaka kuma ta kwanta mata sosai a fuskar da bayanta.
Itakam widad gaba daya murnar tafiya gida ya sanya ma bata damu ko ya dauki batun zuwan abbas da muhimmanci ba,siyayyar da uncle muhsin yayi mata taketa shiryawa abinta,tana ta zancensu Aafiya da sauran 'yan uwanta,da wannan batun ta kwanta bacci.
************Washegari a gida yayi breakfast wajen hajiya,ya kuma shaida mata yau din suraj zai rakashi gidan muhsin din.
Har cikin zuciya da ruhinta take jin farinciki,tayi addu'a sosai tare da fatan samun dacewa da albarka mai yawa cikin lamarin.
Sai Azhar ya wuce gida bayan yayi salla a nan,yana komawa bacci ya kwanta,bai farka ba sai gab da la'asar,tun bai tashi daga kan gadonsa ba ya janyo waya yana sake lalubar number hafsa,saidai yau din ma har tayi ringing ta gama bata dauka ba,a qa'ida idan yayima mutun kira daya baya qarawa,amma wannan karon ita din sai daya kira sau uku bata dauka ba,sai ya maida wayar ya ajjiye ransa yana baci,ya miqe ya shiga toilet ya daura alwala ya wuce masallaci.
Yana dawowa dakin kira na shigowa wayar tasa,suraj ne yana dagawa ya soma zolayarsa
"Sabon ango,Allah dai yasa ka shirya" ido ya lumshe yadan saki murmushi,surja badai zolaya ba
"Haba duk zumudin na meye?,bayan la'asar fa mukayi dakai,kuma yanzun nan ma aka gama sallar" dariya suraj din yayi
"Na qagu ne naga wacce mai sa'ar ce zata sake samunka,bama ni kadai ba,kaga zainab a nan ita kanta so take naje na dawo na gaya mata wacece"
"Ita da hafsat kuwa"
"To sai me?,kayi qoqari ka shirya,gani nan fitowa,abinci kawai zanci"
"Saika qaraso" ya fada yana katse wayar,dole ya fidda hular da ya sanya ya aje,ya shiga bandaki ya don yin wanka.
Yana tsaye yana tsane ruwan da yayi lumm cikin gargasar jikinsa yana duban madubi,karo na barkatai ya sake kallon wayarsa yana tuna adadin wayar da ya yiwa hafsat din bata dauka ba,sai ya jinjina kai yana qiyasta yadda zai fita daga bauchi jibi da sassafe zuwa kaduna.
Ya gama shirinsa tsaf yana gaban mudubi yana kallon kansa,hannunsa riqe da hularsa yana karyata,yana jin wani banbarakwai,wai yau shine a karo na biyu zashi zance,zancen ma wajen wadda baisan wacece ba,ya dora hularsa sannan ya dauki sassanyan turarensa dake fallasashi a duk inda ya shiga ya feshe jikinsa dashi.
Kiran suraj da ya shigo ya shaida masa isowarshi,saiya kara wayar a kunne ya tallafeta da kafadarsa saboda takalman da yake sanyawa a qafarsa bayan ya zauna kan dressing chair yana fadin
"Ka qaraso ciki mana"
"A'ah,ina cikin mota fito kawai" bai musa masa ba,ya zame wayar ya qarasa sanya wasu rufaffun takalma masu kyau da asalin tsada da wasu sake fidda shigarsa,ya dauki wayar ya mayar aljihu ya dauki keys din gidan suma ya saka sannan ya fito.
"Kai mutumina,kamar yau ne zan rakaka wajen maman mimi?" Harara ya watsa masa bayan ya rufo murfin motar sannan yace
"Kunna mota mu wuce,so nake muyi mu dawo,ina da wani uzuri"
"Yanzu kuwa yallabai" ya fadi yana dariya,sai ya tada motar suka wuce.
Suraj nata jansa da hira amma shi hankalinsa ya rabu kashi kashi,dubansa yayi sanda yaga yana qoqarin parking qofar wani qaramin mall
"Bari mudan samo abinda za'a kai mata,ai bama shiga hannu rabbana ba"
"Share kawai suraj mu tafi please"
"A'ah,nikam ba za'ayi haka dani ba,ko banza fa ta zama matarka,tunda an riga an tambaya an kuma baka" maganar sai yaji tayi masa nauyi,bace komai ba har suraj din ya fice,bai kuma dade ba ya dawo da tarin alawoyi da chocolates masu tsada da dadi,ya ajjiye ledar ya kunna motar sukaci gaba da tafiya.
~~~~~
"Kai,tubarkalla ma sha Allah,diyata din nan badai kyau ba" hajjaa ta fada bayan ta gama shirya widad,cikin wata sabuwar dark blue din super vilisco,dinkin doguwar riga,ta fidda jelar kalbarta tayi ta fito ta qasan daurin dankwalin data yi mata,ya zauna das a kanta,sannan ta bata siririn mayafi da ya dace da atamfar.
Murmushi widad kawai keyi tana kallon kanta a cikin mudubin,badan badan ba da sai tace bata taba ganin tayi kyau haka ba,ummu ta tabo daa,bata iya zama tayi mata wadan nan qyale qyalen,saidai ko yaushe zaka samu widad din fes cikin tsananin tsafta da kuma sutturu masu tsada,saidai ita da kanta take zama tayi kwalliyarta wansa a wajensu Aafiya da yayyansu su ramziyya take kwaikwaya,ko latifa da take mutuniyarta ita dinma bawai ta yanzu bace,ba wani iyawa tayi sosai ba,amma da yake hajjaan gwanar ado ce,a yau din ta qawata widad din sosai,har abun yayi mata dadi ya kuma burgeta ita kanta,farincikin yadda taga tayi kyau yasa bata jin wani fargaba ko bacin ran zuwan baqon,Allah Allah ma take yazo ya tafi tazo hajjaa tayi mata hotuna masu kyau ta turawa daya daga cikin 'yan gidansu su nunawa ummunta kafin ta isa gida.
0 comments:
Post a Comment