"Bude musu setting room,ka kunna ac kadan kada tayi yawa,sai kazo kakai musu ruwa" da to ya amsa ya juya yana ficewa.
Sai da hajjaa ta tabbatar an kai komai sannan taja hannun widad ta zaunar da ita
"Na sanki da hankali da nutsuwa,to ki qaro wata a kai,idan kin shiga ki gaishesu kinji?"
"Tom" ta fada tana gyada kai,sai hajjaa ta kira nujood,ta sanyata ta saka hijab tace ta raka widad,har sun fita ta kirayeta
"Karki ce zaki zauna,nasan halinku da shirme,kina rakata kuna gaisawa ki dawo ciki"
"To" tace tana ficewa,suka rankaya kuwa ita da widad din zuwa setting room.
Setting room din yabi da kallo,duk da ba baqonsa bane,don yawanci idan yazo a nan suke zama da muhsin din,kamar bazai zauna ba,haka kawai ya samu kansa da qaguwa na ganin wacece,wayarsa da aka kira ya duba kuma yaga ogansa ne ya sanyashi zama dole,don suna da wani irin respect na ga gaba dasu,ya fara amsa wayar cikin nutsuwa da kuma girmamawa.
Suna cikin yin sallama da ogan nasa yaji suraj ya dan taboshi,sai ya maida dubansa ga suraj din don,signal yayi masa da ido yana masa nuni da hanyar shigowa setting room din,ya qarqare wayar yana ajjiyeta gefansa,sannan ya maida dubansa ga inda suraj din ke masa nuni.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 22
Nujood da widad dake tahowa yake nuna masa,baiji abinda yace ba,yadai ci gaba da kallonsu,suna sarqafe da hannun juna,widad din tana jin gabanta na faduwa ne gami da sanyin jiki haka kawai,yayin da nujood ke tsokanarta,har ta daga qafa zata dan bi nujood din da gudu sai kuma ta tuna taga qofar setting room din a bude,wannan yasa takai idanunta ciki,bata hango wadanda ke ciki tar,saidai ta tabbatar suna iya kallonsu.
Da sallama suka shigo,suraj ne ya amsa musu fuskarsa da murmushi,nujood din na riqe da hannun widad suka qarasa cikin falon.
Nujood dince ta fara gaida abbas,fuskarsa kadaram kadaham ya amsa,already ta san halinsa,bai fiya fara'a ba don haka bata damu ba,ta maida akalar gaisuwar ta ga suraj
"Lafiya lau,ya karatu?" Ya amsa mata cikin fara'a da murmushi
"Alhmdlh" tuna abinda hajjaa tace da ita ya sanyata miqewa
"Saikin shigo" ta fada tana duban widad cikin salo na tsokana,wanda iya ita da ita ne kawai zasu fahimta.
Maganar nujood din taja hankalin abbas harma da suraj,tunani iri daya ya darsu a ransu lokaci guda,kowanne dubanta yake,abinda ya sanyata taji kamar an aza mata wani nauyi,gaba daya ta jita kamar a daure,kallon da suke mata yana neman daburtata,tana takure a gefe tsakanin kujeru tana wasa da gefan mayafinta,saita nannadeshi ta wareshi,suraj ya fuskanci hakan,don haka yayi gyaran murya,cikin murmushi kuma yace
"Barka da fitowa 'yammata" muryar suraj din saita ankarar da ita mantuwar da tayi bata gaidasu ba,don haka ta daga kai in ta fara gaida suraj din,cikin sakewa da fara'a da kuma kulawa ya amsa mata,sa'annan ta koma ga abbas,idanu saika hada,take taji ya fiya kwarjini da yawa,tunda suka shigo kuma ta karanci fuskarsa bashi da yawan fara'a,sannan koda bata dade a wajen ba alamu su nuna yana da yawan shuru shuru,don ko daya bataji muryarsa ba tun bayan daya amsa gaisuwar nujood
"Ina yini" ta fada tana kaida kanta,sai daya lumshe idanunsa ya bude sannan ya amsa mata,'yammatan daya fada sai abbas yaji kamar gatse ne yake masa,zaqin muryarta kuma me cike da zallar quruciya na zaga kwanyarsa
"Kada dai ya kasance ita hajiya ta zaba masa?,anya kuwa?" Kamar suraj yasan tambayar dake yawo a ransa kenan,sai ya tsinceshi yana cewa
"Allah yasa kece wadda hajiya tace muzo mu gani?" Kanta a qasa kawai ta gyada kanta,amsar data tilastawa abbas maida bayansa jikin kujera ya jinginar kawai idanunsa a lumshe.
Yana iya jin yadda suraj keta janta da hira,tana amsa masa da qyar,muryarta cakude da kunya da kuma tsoro hadi da rashin sabo,tunda suraj din ya kalleshi ya karanci yanayinsa,wannan yasa ya karbe hirar abinsa ba tare daya sanyoshi ba,kamar ma shi abbas din ya yiwa rakiya.
Jinnta take a takure kota ina,musaman idan ta waiwaya inda abbas din ke zaune abinsa ya sanya musu kunne
"Wannan abokin nasa,ko me yasa yazo dashi?" Abinda tayita fada kenan a ranta
"To widad mu zamu wuce,sai kuma wani jiqon?" Suraj ya fada yana duba agogonsa,maganar data yiwa widad din mugun dadi,don kafin ma ya miqe ita ta miqe tana cewa
"Ku gaida gida" saita kada kai abinta tayi hanyar ficewa,a lokacinne abbas ya bude manyan idanunsa yana binta da kallo
"Minti daya mana malama widad" suraj ya fada yana miqewa da ledar siyayyarsa a hannu yana yiwa abbas sign din ya tashi mana,sai ya kauda kai kamar bai gani ba,don haka ya taka ya isa inda take tsaye ya miqa mata ledar,cikin ransa yana fadin siyayyar kuwa ta dace da ita
"Ga wannan ko babu yawa" sai data dora idanunta kan abbas dake zaune daga bayan suraj din taga ita yake kalla sannan ta saka hannu ta karba gabanta na faduwa
"Na gode" ta fada tana ficewa a dakin da hanzari gabanta na wani irin faduwa.
Da baya suraj ya dawo a hankali yana hararar abbas
"Duk alamar da nake maka ka tashi ka miqa mata don ta fuskanci ma waye abbas din a cikinmu amma kayi banza dani?"
"Wai kanason kacemin wajenta mukazo zancan?" Abbas din yayi tambayar hankalinsa kwance,sai haushi ya kama suraj,ya watsa masa harara
"Ban sani ba,next time dama idan zaka zo kada ka sake ka kirani,idan kazo kai kadai zaka gane wajen wa kazo din,tashi mu tafi,ka barni ni kadai sai zuba nake".
Cikin mota gaba daya kansa ya kwance,me yasa hajiya ta dauko masa wannan?,ta yaya zai samu sauqi ko kulawa daga wajenta,kansa kada,gaskiya bazai iya sake zuwa zance ba,yaje yace mata me?.
Yana jin suraj yana ta hirarsa amma bai saka baki ba,saboda gaba daya tunaninsa na ata wani waje,suffarta da kamanninta yaketa qoqarin maidowa idanunsa ya hadasu waje daya,babu qarya.....tana da kyau,ita din kyakkyawace ta gasken gaske,to ko kyawun hajiya ta gani?,sai ya sake girgiza kansa,yasan hajiyan,tasan abun qwarai sarai,bai gano me ta hango masa ba,amma ya tabbatar akwai abinda ta hanga din.
Saida suraj ya ajjiyeshi a gida sannan shima ya wuce,abbas din ya masa ban gajiya da godiya
"Ai babu wannan tsakaninmu,kawai dai next time ka tafi kai kadai,saboda ka samu ku fahimci juna sosai, she's too young,dole sai kana janta a jiki da dabaru sannan zata saki jiki da kai,amma kuma ina me tabbatar maka indai aka samu shaquwa sabo da kusanci tsakaninka da ita,ina me tabbatar maka.....ina sake fadi ina mai tabbatar maka anan zaka fahimci komai basai an gaya maka ba" abinda suraj ya gaya masa kenan,wanda ya tsaya masa a rai,ya kasa fahimta kuma,da wannan maganar ya kwanta.
Ita kuwa widad tana fitowa ta qara da dan gudu gudu,wani irin tsoro takeji da faduwar gaba sosai,don sai data tsaya a hanya tadan saisaita numfashinta tana dafe qirjinta da hannu,batasan me yasa batason wancan abokin nasa yana kallonta ba,to amma itafa wallahi mai wanna zubar maganar indai shine wanda uncle muhsin ya turo mata baiyi mata ba sam,saita tabe baki tana buda ledar daya bata,murmushi ya subuce mata da taga masoyiyar wato chocolate,saita zabura tayi cikin gidan tana qwalawa nujood kira.
"Iyyeee,yammatan ummu,da alama ciniki ya fada tunda naga kin dade da yawa" hajjaa ta fada cikin salon tsokana tana murmushi,baki ta tura gaba tana ajjiyewa hajjaa ledar,kanta tsaye cike da zallar wautar quruciya tace
"Ni gaskiya indai wannan mai surutun ne bana sonsa" dariya nujood ta sheqe da ita,kafin tace komai hajjaan da uncle muhsin ya bata aikin tuntubar widad din idan ta dawo aji ta bakinta tace da ita cikin tattara hankalinta
"Saboda me?"
"Ya cika siranta,kuma ya fiya magana" wannan karon nujood dariya harda fadowa
"Bafa uncle abbas take fada ba,uncle suraj ne wallahi take nufi" sai hajjan itama ta saki dariya,tasan suraj din,duk da ba sosai ba,amma sai da nujood ta fada sannan ta tuna tabbas yana da kirki yana kuma da hira
"To alhamdulillah,indai hakane uncle abbas yayi kenan?" Ta fada tana kallon widad,yadda suka tsareta suna jiran amsarta ya bata kunya,saita dauki filo ta cusa fuskarta a ciki tana dariya cike da jin kunya
"Allah nidai hajjaa...."kunya ta sanyata tashi da gudu tayi dakinsu,sai suka bita da dariya,hajjaa taja chocolate din ta ajjiye da nufin idan uncle muhsin ya dawo ta nuna masa kafin su taba,ta kuma hada da gaya masa yadda sukayi da widad din.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 23
Duka dai yanata juya yadda abubuwan zasu kasance har ya gama abinda yakeyi yazo kwanciya,sai ya kauda wanann tunanin ya sake maimaita kiran hafsat amma kamar dai ko yaushe,sai abun ya shiga daure masa kai da kuma bashi tsoro,don haka ya sauya akalar kiran zuwa ga wani constable dake area din nasu,ya aikashi yaje gidansa ya duba masa lafiyarsu,cike da girmamawa ya amsa masa ya kashe wayar ya zauna yana jiran feedback.
Bai haura minti biyar ba yayi kiransa
"They're fine sir"
"Are you sure?"
"Yes sir" ya sake tabbatar masa,sai yaji ransa ya baci,ya kashe wayar ya ajjiye yana gyara kwanciyarsa gami da lumshe idanunsa yana furzar da iska daga bakinsa
"Dole ya dauki mataki akan hafsat din,abun nata qara gaba yake,wannan zallar raini ne" ya fada a ransa.
Washegari daga strolling ya wuce gidan hajiya a qasa,duk da 'yar tazarar dake tsakaninsu sai gashi yaje,saidai ya hada gumi sharkaf kafin ya isa din,hajiya nata masa sannu da fadan bai ganin nisa yayo wannan tafiyar a qafa?, qaramin murmushi ya saki
"Hajiya kin manta aikina ne?,tafiya tsaiwa wahala da yunwa duka an koyamana juriyarsu"kai ta jinjina kawai
"To Allah ya bamu dacewa" muneera ce ta hado masa breakfast kamar ko yaushe,yau din hajiya bata iya bari ya gama cin abincin ba ta jeho masa tambayar
"ya ake ciki?,kaje kuwa?" Kai ya jinjina
"Naje hajiya"
"Ina fatan komai yayi?" Me zai iya cewa hajiya,bashi da wata amsa data wuce cewa
"Alhamdulillahi" ya amsata yana kurbar tea dinsa,sai ta saki murmushi tana jin dadi har cikin ranta,ta sauke ajiyar zuciya
"Inaso ayin auren nan a nan kurkusa abbas indai zai yiwu" da qyar ya hadiye bread din dake bakinsa,sannan ya daga idanunsa yana duban hajiyan
"Kamar nan da yaushe kike so hajiya?"
"Zuwa yaushe zaka shirya dai?" Shuru ya danyi,tunda ta magantu lallai da gaske tanaso ayi a kusa din,koda yaushe babban burinsa shine ya cika umarninta
"Kada ka damu,kayi tunani a hankali,ko bayan ka koma ne sai ka fadi zuwa lokacin da kake ganin ka gama shiryawa"
"To hajiya" ya fada cikin girmamawa,saidai tuni kwanyarsa tayi nisa wajen tunanin yadda abubuwa suke ta sauyawa suna zuwa masa a bazata.
~~~~~~~~
Sai la'asar ya koma gida,kai tsaye ya shiga bandaki yayi wanka,bayan ya fito ya fito zuwa sassanta don ya samu Black tea,cikin mintuna ya hada ya dawo falon da zummar zama,amma sai ya dinga jin kamar hayaniya hayaniya daga qofar gidan,sai ya miqe ya yaye laluben window din da ya bulla har harabar gidan,harabar gidan fes babu kowa hakanan babu komai,amma qoramar qofar gate din gidan a bude take,ya kuma tabbatar hayaniyar a qofar gidan sosai take tashi,don haka ya ajjiye cup din ya zura slipper dinsa da ya cire ya doshi qofar fita.
Tun kafin ya qarasa ya dinga ji kamar muryar hafsa,amma sai ya qaryata kunnuwansa,tunda yasan bata nan,saidai yana dosar waje kunnuwansa na sake ji masa muryar tata.
A hankali ya buda qofar ya fita,take idanuwansa suka gasgata masa abinda kunnuwansa suka ji,zallar mamaki ya kusa kasheshi a wajen
"Hafsa a bauchi?" Ya yiwa kansa tambayar da bai san amsarta ba,yana sake zubawa hafsa din idanu,wadda bata ma fahimci ya fito ba,ta taqarqare sunata sa'insa ita da wani,nawwara na hannunta,mimi na tsaye gefanta tana riqe da hannunta,maqotansa biyu keta bada baki,yayin da wasu matasa dake sana'ar business center a wani dan container irin na mtn gaban gidan kadan suma suka iso wajen.
Yana fitowa daya daga cikin maqotan nasa ya ganshi,da sauri yace
"Yauwa alhmdlh,ga mai gidanta nan ma ya fito,mun dauka ai baka nan shi yasa tun dazu bamu yimaka magana ba" dukka idanu suka waiwayo suka zuba masa,take yaji ya muzanta,ya aro jarumta da juriya ya qaraso wajen yana riqe da hannun mimi,wadda tunda ta ganshi ta sheqo da gudu ta maqale ubanta.
Qarawa yayi ya miqa hafsa din ita yana cewa
"Wuce gida" saboda ganinta cikin mazan ba qaramin quntata masa rai yayi ba,ga kuma baqincikin tahowar da tayi babu izini ko shawara dashi.
"Alhaji kayi haquri,amma babu inda zata saita cikamin kudina,zata gane ni din matsiyaci ne na ainihi" fuska a daure abbas ya juya yana dubansa
"Kaga,barta ta tafi,za'a biyaka koma nawa ne"
"To shikenan alhaji" sai daya tabbatar ta shiga gida ita da kayanta sannan ya juyo ga mutumin
"Me ya faru?" Gyara tsaiwarsa yayi yana sake riqe qugunsa
"Tun daga tashar kawo na daukota alhaji ita kadai qwallin qwal da sunan shata tayi,mukayi ciniki ita akan dubu sha biyar,sai da mukazo nann sannann zata hadani da dubu goma,wai nayi haquri bata da kudi,kudinta basu kai ba" cikin matuqar bacin rai ya fara laluba aljihunsa
"nawa ne cikon kudin naka?"
"Dubu biyar ne ranka ya dade" mai motar ya fada cikin matuqar jin dadi ganin hakkinsa zai fiti,sai ya irga ya miqa masa,yasa hannu ya amshe yana godiya,ya juya yana komawa motarsa
"Lamarin mata sai haquri,tun dazu muketa qoqarin raba rigimar mu bashi kudin amma taqi saurararmu,Allah dai ya kyauta" maqotan nashi suka fada,gaba daga kunya ta gama baibayeshi,kamar shi matarsa tana fada dame mota akan cikon dubu biyar,bayason tsaiwa bare suja wata doguwar magana,duk da sunyi qoqari kuma alkhairi sukayi masa,sai ya basu hannu sukayi musabaha yana musu godiya,ya juya ya shige cikin gidan,xuciyarsa da rayuwarsa na wani irin quntata,wannan wanne irin kwance zani ne a kasuwa tayi masa?,me ma takeyi a bauchi?,wa ya bata ikon tahowa?,da wadan nan tambayoyin ya saka kai cikin gidan,kai tsaye ya zarce sassanta.
Yana sallama cikin falon su mimi suka taho da gudu suka rungume qafafunsa,ya duqa ya daukesu gaba dayansu yana musu oyoyo,ba tare da ya zauna ba yake qarewa falon kallo,bata a ciki,saidai kayansu da suka taho dasu watse a falon,yawan kayan ya tabbatar masa gaba daya kayansu ta debo daga can,ya jinjina kai ya sauke yaran yana kunna musu tv
"Ku kalli cartoon ina zuwa" ya fadi yana shafa kansu,mimi dake da wayo ta gyada kai ya wuce ciki.
Daya shiga tana toilet,don yaji motsin ruwa,sai ya harde hannayensa a qirji ya jingina da jikin madubinta yana qarewa dakin kallo,a hargitse dakin yake,babu kintsi kwata kwata,da alama tun sanda zasu tafi kadunan haka ta barshi.
Tana motsa qofar ya mayar da dubansa kai,sai gata ta fito da alama alwala ta daura,ko sallar la'asar dinma bata samu yi ba kenan,suna hada idanu ta daure fuskarta da kyau,batason ta karaya ko yayi mata kwarjinin da zata kasa fadin maganganun dake cikinta,ta dauke kai kamar bata ganshi ba tana nufar inda abun sallarta yake a watse a qasa zata dauka
"Yaushe kika nemi izinina da har kika baro kaduna kika taho bauchi?" Dagowa tayi,tanason dubansa kai tsaye amma tasan tayi qarya,a kaikaice take duban gefansa
"Saina nema izininka?,tunda bani da amfani ai ya kamata na shaida hakan,na baka waje,mutumin da bashi da kimar da za'a bashi sabuwar mota kaga wacce daraja gareshi?" Idanunsa ya lumshe yana ambatar sunan Allah,wani abu ya tsaye masa a wuya,tabbas inda shi madokin mata ne yau din nan sai ya tsitsinkawa hafsa mari,banda tsabar hauka a yanayin da ake ciki na matsalar tsaro da aka fara fuskanta tana matar ASP zata debo yara har guda biyu su kamo hanya ita kadai?,sannan duka ba tare da wata hujja mai qarfi ba illa dai kawai yaqi canza mata mota?.
"Kinsan abinda kikeyi kuwa?" Ya fada bayan ya bude idanunsa yana dubanta
"Na sani mana" ta amsa shi kanta tsaye,sannan ta dora
"Ai babu dole,yadda ban maka dole ba nima bazakamin ba,kowa yayi abinda ransa yakeso,Kaduna ne bazan zauna ba,ka nemo wadda zata zauna da kai cikin wadanda kake baiwa kyautar" sosai maganar ta dakeshi,wani bacin rai ya lullubeshi,ya bude bakinsa a zafafe mimi ta turo qofar riqe da.hannun nawwara,dole ya hadiye abinda ke taso masan,sannan yabar jikin madubin yana dosar qofa
"Hakane,kiyi abinda ranki yakeso,nima zanyi abinda raina yakeso,zan baki mamaki tabbas wannan karon hafsa kamar yadda nasha fada,zan kuma nemo mai zama dani din" daga haka ya fice ba tare da yaja mata qofar ba.
Da kallo ta bishi,haka kawai cikin jikinta taji jikinta yayi sanyi,yadda yayi maganar kamar he's serious,amma kuma data tuna ya saba fada dama sai ta tabe baki kawai,tasan ya fada ne kawai saboda yayi mata barazana,don haka ta karkade abun sallarta ta shimfida tana cewa
"Mu bawa juna mamaki dai" ta sanya hijabinta ta tayar da sallar.
Sanda ta idar yaran nata mata rigimar yunwa
"Ba uban da zai sakani wani shiga kitchen na kwaso gajiya" saita laluba jakarta ta fito da biscuit da lemon roba guda daya ta miqa musu,maimakin ta tashi ta gyara koda dakin nata ne daya cika da shara da qura,sai ta koma saman gadonta ta miqe abinta,ta dauki wayarta ta fara chart.
Hankalinta kwance take chart dinta,yaran nata basu qoshi bama babu wanda ta kula,ba jimawa kira ya shigo wayarta,data duba sai taga yayarta ce,ta gyara kwanciyarta tana saka wayar a kunnenta.
Bayan sun gaisa take ce mata
"Ana hada gudunmawar bikin nafisatu ne,nace bari nayi miki magana,don an kusa gama hadawa" take ranta ya baci fara'arta ta janye,bata qaunar abinda zai sanyata fidda kudi,itafa abu indai ba abbas bane zaiyi mata shi to ta gwammace ta haqura da yinsa koda ita zata amfana,a yanzun kuwa da suketa uwaka ubaka dashi ba zata ma dosheshi da wata buqata ba,da sai ta lallaba ta karba wajensa,ta zabge rabi ta basu rabi
"Nifa gaskiya anty shamsiyya bani da kudi" takaici da haushi ya kamata,suna ganin yanzun mijin hafsatun ya fara danshi danshi amma ko daya yarinyar bata banbaruwa
"Ke dama kullum cikin babu kike,to ba kyauta nace ki bani ba,contribution ne na biki,idan zaki bayar ki bayar,idan baki bayarwa ki fada ki daina batan lokaci" murya a cunkushe tace
"Nawa ne kudin?"
"Dubu goma goma ce ba wani kayan gabas ba,kuma ko atika da bata da wani qarfi tuni ta bada nata"
"Shikenan zanyi shawara,zan kiraki idan sun samu" bata amsa mata ba ta kashe kiran,hafsa taja tsaki tana gyara kwanciyarta,gaba daya sunbi sun dameta ba gaira ba dalili.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 24
Kai kawo ya dinga yi cikin dakin,ransa na masa suya,me zaiyi ya huce takaicin hafsa?,yasan dai tabbas bazai qyaleta ba,anzo gabar da dole ya koya mata lesson kamar yadda yasha fada.
Idanunsa suka sauka akan wayarsa,sai ya jawota da hanzari ya fara kiran layin hajiya,bugu biyu ta daga
"Abbas ya akayi?" Ta tambayeshi da mamaki,ganin bai wani jima da barin gidan ba,qoqarin dai daita muryarsa yayi,don bayason ta fuskanci akwai wata matsala ne ta tashi hankalinta
"Lafiya lau hajiya,cewa nayi zai yiwu a gabatar da neman auren cikin satin nan?" Kai ta jinjina cike da mamaki,anya babu walakin goro a miya?
"Eh to,saidai na nema kawunnanka naji"
"Idan zaiyuwu hajiya kawai ayi,na shirya" tana saurin gano damuwa da kuma fushinsa,yadda yayi maganar a jikinta taji akwai damuwa,amma zata tambayeshi a hankali
"Shikenan,zanyi magana dasu,duk yadda ake ciki zaka ji"
"To hajiya na gode,gobe da yamma zan wuce,zan shigo ta nan kafin na wuce din in sha Allah"
"To ba damuwa,Allah yakai mana rai" daga haka sukayi sallama.
Cikin mamaki take sauke wayar,saidai kuma ta samu kanta da sakin murmushi tare da fadin
"Alhamdulillah" zuciyarta na gaya mata wataqila akwai alkhairi mai tarin yawa a abun,shi yasa Allah ya kawo komai a kurkusa haka ya sauqaqe matsala da damuwa.
"Tofa,ta samu kenan hajiya?" Faccalarta da suke tare a falon,ita da yayar abbas din mai suna mabruka suna hira ta fadi,wayar ta ajjiye gefe tana cewa
"Aure ne ya tasowa danki" da mamaki ta kalleta
"D'ana,wa kenan?"
"Abbas mana" kallonta sukayi gaba daya cike da mamaki,abbas din da kowa yasan dabi'arsa,mutumin da ko auren hafsa dinma kamar bazaiyi ba saboda tsabar I don't care manner irin nashi da rashin baiwa lamarin soyayya muhimmanci?
"Abbas din yaushe har yaga wata yanaso?" Faccalar tata da yara ke kira da gwaggwo fanteka ta fada
"Tayani tambaya gwaggwo,na dauka ma bashir ko yaya sa'id zata ce,ko kuma Sunusi" kai ta girgiza tana murmushi
"Abbas ne" kai suka jinjina su duka,mabruka tace
"Ya cancanci ya qara aure dama tuni,wannan rayuwar da akeyi a gidansa bata da ma'ana sam,naga qoqarinsa ma,ganin baida wannan ra'ayin yasa ban taba tuntubarshi da maganar ba,ga 'yammata nan cike a dangi,ya zabi wata ya qara ko zai samu sassauci,haba abun na hafsa yayi yawa" kai gwaggwo ta gyada itama
"Gaskiya dai,yammata kyawawa fa gasunan masu hankali,ita wannan din a ina ya samota?,cikin yan uwansa ne?,amma banji batun ba sai yanzu?" Gwaggwo ta fada cike da son jin wace?,tana fata ya zamana cikin yaranta ne,duk da tasan zaiyi wuya,don inda cikin nasu ne da tuni ta fahimta,amma rabonta da abbas a gidan tun sanda tayi wata rashin lafiya ya shiga ya dubata
"Ba cikin dangi bane,wata yarinya ce diya take a wajen muhsin abokinsa,dukkanku ai nasan kunsan muhsin?" Ta fada tana kallon fuskokinsu, gwaggwo da tuni fuskarta ta sauya tace
"Qwarai kuwa" sai hajiya ta dora
"Yarinya ce ma,amma nutsuwarta da hankalinta ya bani abbas din xai samu nutsuwa a gidansa,zai kuma ce ayi ayi,a bari a bari"
"Turqashi" gwaggo fanteka ta fada ba tare da tasan kalmar ta fita a bakinta ba,wani bacin rau na motsa mata,yaron da dukkan alamu suke nuna zaiyi arziqi cikin dangin nasu,taketa qulafucin ganin ta samu ta jogana diyarta,lokaci daya hajiyan ta wargaza fatanta da burinta ta dauko wata bare ta maqala masa?.
"Banda abun hajiya ruqayya,gida bata qoshi ba za'a baiwa dawa?,gamu da yaran yammata duka sun tasa saiki dauko bare ki bashi?,duk da itama hafsan akwai alaqa amma ai baiyi alaqar sa da yaran kawunnansa ba ko?" Gwaggo fanteka ta fada tana dora murmushin yaqe kan fuskarta
"Gaskiya nima wannan tunanin yazo min" mabruka ta fada tana gyada kai, murmushi hajiya tayi
"Auren dangantakar ai bai amfana komai ba gwaggwo,gwara a gwada baren ko a nan za'a dace ko?" Kai ta kawar tana tabe baki,bacin rai iya bacin rai yana cikata,wanann babbar dama haka za'ayi asararta?,suna ji suna gani
"Da dai kin sake tunani gaskiya,duk yadda bare yake da dadi ai baikai dadin dan uwa ba"
"Hakane" ta amsa mata a taqaice,tasan halin gwaggwon da mita,ita kuma dama can bamaison dogon magana bace,gwggwon na daya daga cikin masu kushe aikin dan sanda a sanda abbas ya samu aikin
"Dan sanda?,me na sama yaci ballantana ya baiwa na qasa?,kayan cin hanci da rashawa" wannan shine abinda taji tana fada sanda hajiyan taje gidan da kanta tana shaidawa kawunsa mijin gwaggwon cewa ya samu aikin,tun daga matakin constable saai yanzun da daukaka ta fara zuwa masa ake kwadayin hada zuri'a da ita?,duk haqurinta da kawaicinta ita din ba mahaukaciya bace.
Hirar duka saita fita akan gwaggwo fanteka ta zama mara dadi,don haka bata jima ba ta miqe ta yiwa hajiyan sallama ta fice.
*WIDAD*
Sanda ta bude ido ta ganta qofar gidansu sai taga kamar wasa,kasa jira tayi drivern da uncle muhsin ya daukar mata shata har qofar gida ya fidda mata kayanta,ta sauka daga nan ta nufi gate din da gudu gudunta,ji take kamar zata bude ido ta ganta ta koma bauchi.
Cikin sa'a kuwa tana buda gate din ummun ta hanga tsaye a farfajiyar gidan ita da kawunnanta,sanye da atamfa da kuma hijabi,hannunta riqe da carbi,da alama salla ta idar suka tasota,akwai zancan da sukeyi.
"Ummunaaa" ta fada da qarfi sannan ta kwasa da gudunta,ta isa gabanta ta fada jikinta tana ruqungumeta.
Sai da ummun tayi taga taga zata fadi kawu ya tareta
"Ashsha,ashsha,zata kada mana uwa" sai ta saki dariya tana sakin ummun suka miqe tsaye dai dai ummun itama tana dariya idanunta akan fuskar widad din,kamar fa shekara bata ganta ba.
"Ke dawa?,yanzu kike tafe?" Ummu ta fadi tana dubanta
"Ni kadai yanzu yanzu na qaraso"
"Iyeee,muhsin din barmin ke yayi ke kadai kika kamo hanya?,tabdijan ,zamu hadu dashi kuwa"kafin ta qarashe drivern uncle muhsin din ya shigo da jakankunanta,suka gaisa yace zai koma,ummu tace a'ah sai yaci abinci,suka wuce ciki ita da widad tace taje ta kawo masa abincin,su kawu kuma suka fice bayan an bashi wajen zama anan farfajiyar gidan.
Zuwa wani lokaci sai ga sassan ummu ya dan cika da sauran yaran gidan,su Aafiya rafi'ah fareesa da sauran wadanda suke shekaru kusan daya,sun baibayeta tana ta basu labarin bauchi.
"Kano fa tafi dadi Allah" ta fada daga qarshe tana yamutsa fuska,dariya sukayi mata
"Daga baya kenan,bayan kin gama kwanakinki" dariya tayi tana cewa
"Da gaske nake muku,bari kuga" sai ta wuce daki ta janyo jakarta,ta fidda jakar ledar kayan makeup din da hajjaa ta damqa mata tace inji abbas,tunda ta taho kayan suke daukan hankalinta,komai na ciki ya burgeta ya kuma yi mata kyau,harda takalmi me tsini irin nasu basma da aka sako musu a lefe,tayita maitar takalmin sai basman ta jefa mata harara
"Ba baki zanyi bafa,kiyi addu'a kema Allah ya kawo me siya miki" fushi tayi tana tura baki tabar gurin,sai gashi ta sameshi sama ta ka,bayan shi harda mayafi da hand bag qarama mai matuqar kyau,a nan ta zazzage musu kayan,suka dinga santinsu,daga baya ta daukarwa kowa wani abun daga cikin kayan kwalliyar.
*************
Kwana biyu a tsakani tana kitchen tana cin abinci suna hira da latifa,ta ajjiye warmer din data zuba abincin alhaji a ciki tana cewa
"Ashe dan bauchi kika samo mana kuma" kallonta tayi tana ci gaba da cin abincinta,don ita har ga Alla ma ta manta da wani batu
"Dan bauchi?"
"Eh mana,naji abba mahmudu yazo suna zancan da alhaji ai"
"Auho,wai abokin uncle muhsin"
"Shifa" sai widad din tayi shuru kawai,don batasan me zatace ba,itadai ba sanin soyayya tayi ba bare ta tantance tana sonsa ko bata sonshi,kawai dai taji bata damu ba bata takura ba kamar sands ake zancan mahfood da ma'aruf.
Sosai ummu ta dinga juya zancan bayan da mahaifin widad ya zartar da cewa an bawa abbas widad don,amma bata taba kawo cewa zasu nema aurenta a nan kusa ba haka,taji abun sosai a ranta,a yadda ta lura kuma shi mahmudu din a shirye yake da auren diyarsa,tasan watarana komai tsahon zaman da zatayi da qaunar da takewa widad su rabu dole ta aurar da ita,so a yanzun bataga nata hurumin da zata hanashi bada auren 'yarsa ba,tunda dukkan bincike da shaidu sun tabbatar da nagartar me neman auren kamar yadda musulunci yayi umarni.
Amma babban abun shine,kishiya daya tabbata widad din nada ita,ta yaya yarinya kamar widad din zata iya fuskantar abu me wahala da zafi kamar kishi?,bata sani ba,saidai tana fatan ko mai zaizo da sauqi fiye da yadda suke zata.
Kwanan widad din biyu da dawowa maneman auren abbas din suka iso kano qarqashin jagorancin uncle muhsin,sunga karamci irin na kanawa,duk da cewa su din ba kanawa bane usul,amma tunda an haifi 'ya'ya da jikokinta suna amsa wannan sunan.
Cikin girma da mutunci gami da karamci suka gabatar da neman auren abbas ga widad din,aka sake jaddada basu,suka nema alfarmar karbar kudin aurensu harda sadaki,take alhaji yasa aka karba komai,suka karbi roqonsu na daurin auren sati mai zuwa.
A ranar zancan auren widad ya fara yawo a dangi,abinka da family house,kowa idan yaji zai gayawa na kusa dashi,bugu da qari widad din 'yar gatan ummu,mai masoya da kuma tarin abokan adawa.
"Uhmmm,sunje sun zaba mata miji ba,ai dama wannan yadda akaci buri a kanta nasan sai me abun hannu zasu bata" wannan shine abinda wasu suka dinga fada,musamman da suka samu labarin muqamin da ya riqe a gwamnatin bauchin,da kuma wanda yake kai yanzu,gani sukeyi uncle muhsin ya dauketa ne dama kawai don ya aikata hakan.
Ita kuwa sam batasan ma me akeyi ba,don har ta koma islamiyya,wadda tun tafiyarta qaunar makarantar bata bar ranta ba,sanda ta koma din sai ta samu basu wani tsere mata ba,tunda ta dora daga inda ta tsaya a bauchin.
**********Karfe shida saura na yamma suka iso gidan ita da Aafiya rafi'ah da widad din,bayan tasowarsu daga islamiyyar,gab da zasu shiga gate din gidan Aafiya ta kalleta
"Nifa zancan bikinki naji ummanmu tana yi,wai nan da sati daya"
"Nifa abinda yake hadani dake tsokanarki" widad ta fada tana watsa ragowar alawar data siya cikin jakarta
"Wallahi nima haka naji,don kafin mu tafi islamiyya naji umma tana waya a karbo atamfofi akai mana wajen mai dinki"
"Mahaukata,sai kuyi ai" widad din ta fada tana yin gaba abinta tana dan waqenta.
Bata ma tsayasu ba ta zarce sassan ummu abinta,tana sallama a falon ta soma zare hijabinta daya dameta,gashinta mai santsi ya ware,don dama ita din ba ma'abociyar saka dankwali bace,tafi sanya hula,itama ba ko da yaushe ba,sai ummu tayita fama da ita.
Ummu da anty halima ne a falon
"Anty halima ina nabiha?,kikace idan zaki sake zuwa tare zaku zo?" Widad ta fada tana barewa alewan ta tura bakin yaron anty halima dake kan cinyarta.
Da kallo anty halima ta bita,tana dan jin tausayin widad din
"Oh ni sadiya?,wannan wacce irin amarya ce ummu?" Dan murmushi ummun tayi,ita kanta tausayin widad din takeji,har yanzu ma bata zauna tayi magana cikakkiya da ita ba kan auren da tasan widad din batasan meye shi ba,bata kuma da labari cikakke akan yinsa.
"Au ina yini?" Ta fada tana dariya bayan ta tuna nata gaidata ba,ba kuma tare data maida hankali ga maganarta ta farko ba
"Lafiya lau widad,nabiha zasuzo,sai satin biki in sha Allah"
"Allah ya kaimu" ta fada tana gyada kai hankalinta kwance,saita dubi ummu a shagwabe
"Yunwa wlh nakeji ummu,dazu banci abinci ba Aafiya ta matsamin na taho mu tafi"
"ki wuce latifa tana kitchen ki karba"
"Tom" ta fadi tana wurga jakarta ta zarce kitchen din,yayin da dukka su biyun suka bita da kallo.
Ummu ce ta fara dauke idanunta tana sakin ajiyar zuciya,anty halima tace tana dariya
"Wai,wa yaga widad amarya" kai ummu ta kada
"Tausayinta nakeji halima,ban taba kawo rabuwarmu a nan kusa ba" tabe baki anty haliman tayi
"Kaji ummu,to mu da aka rabu damu din tun bamu kai haka ba me ya samemu?,gamu ragal damu?,itama zata ware ne kamar kowacce mace" kai ummu ta girgiza
"Ba zaki gane ba halima,dukkanku kunfi widad wayo sanda aka muku aure,kawai don lokaci yayi ne ba yadda zanyi,amma ban shirya kaita wani uwa duniya ba"
"Tunda dai babanta ya bada ita,alhaji kuma ya goyi baya dole saidai ayi haquri,yanzu kawai yadda za'a tattarata akaita bata iya komai ba,kunbi duk kun shagwabata,bata iya komai ba,komai yi mata akeyi" anty halima ta fada tana mele baki,ta rasa wanne irin so ummun takewa widad?,tamkar ma ba mahaifin widad din ta haifa ba,ita ta haifa,ko ita diyarta ta cikinta bata jin tana mata son da takewa widad din.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 25
Murmushi kadan ummu tayi,qarara ta hango kishin widad a idanun halima,ta rasa me yasa haliman ta kasa sabawa da hakan,sai ta gyara zama
"Mu dinma uwayenku da sanda aka aurar damu banajin munkai ya widad din,a gidan muka iya abubuwa,tun mun kwamacala har muka qware,yanzu gashi ba'a ce mune muka haifeku ba" kauda kanta anty halima tayi,tasan dama duk yadda takai bakai isa ka fadi wallen widad ko ka kusheta ga ummun ba.
Yau din tun qarfe takwas ta qudunduna a bargo cikin dakin ummu,bayan ta gama qarewa kayan data gani jibge a dakin ummun kallo,tun shekaran jiya taga ummun nata jibge kaya a dakin nata,itadai bata ce ga dalili ba,ta dan tura baki taja bargo abinta,bacci yau takeji da gaske,don ko sassan anty madina da aka cika ana hira yadda aka saba taqi zama,bugu da qari kuma yadda suketa faman kiranta da sunan amarya,wanda ta dauka duka tsokana ce irin tasu yau ta sauka a kanta suka tasota gaba,ita kuma bataso.
Fakare tayi tana jiran bacci ya iso,gefe daya tsoro tsoro takeji saboda ummun tana wajen dattijon mijinta,buda qofar dakin akayi a hankali,sai ta tada idonta tana kallon me shigowar ba tare data tashi ba,ummun ce,hannunta dauke da babbar baqar leda
"Yauwwa,gwara ma da bakiyi baccin ba,tashi" kai tsaye ta miqe din,don itama tanason yiwa.ummu tambayar
"Ummu...wai wannan kayan,na wanene duk sun cika miki daki?"
"Kayan aurenki ne" ta amsa mata gaba gadi tana kallon fuskar widad din,cike da fargabar yadda zata kalli zancan,kada ta watsa musu qasa a ido.
Idanun ta fitar,fuskarta babu wani emotion saina mamakin
"Aurena ummu?,duka wadan nan kayan?" Kai ta gyada mata
"Eh,harda wasu ma" ta fada tana bude mata ledar
"Wannan babanku yace ki zaba iya wadanda kikeso za'a dinka miki" da mamaki ta sake duban ummu
"Wai duka nawa ne?"
"Kadanma kika gani shalele ta,za'a kawo lefe a kawatuna duka naki" murmushi ya subucewa widad,kawai taji farincikin na kamata
"Harda kayan kwalliya ma irin nasu anty ramziyya?"
"Sosai,inajinma yafi nasu" ta fada tana murmushi ganin bata dauki zancan da zafi yadda ta saba ba,da wannan hirar ummun ta dinga hilatarta tana jaddada mata zancan auren,quruciya ta sanya widad din bata wani damu ba,saima cika da tayi da zumudin zuwan ranar da za'a kawo mata kayanta,wanda ummun tace mata sai ranar daurin aurenta.
********Wasa gaske saiga shirin biki nata kankama daga bangarensu widad,sam bata wani damu ko daga hankalinta ba,abinda ya baiwa kowa mamaki,yayin da wasu kuma hankalinsu ya kwanta ganin bata qi yadda ta saba ba,'yan adawa kuma fadi suke
"Shegiya dama da guntun wayonta,gashi tayi luff kamar ba ita taqi 'yan uwanta har mutum biyu ba" oho,ita dai sabgar gabanta takeyi kawai,tana lissafin ranar da za'a kawo mata kayan kwalliya.
Daga bangaren su abbas kuwa maganar ta fara yawo,da yawa daga cikin dangi wadanda sukaci burin zuwan wannan rana,ranar da abbas zai qara aure labarin baije musu a dadi ba,wadanda suka jima suna addu'ar hajiyan ta sanyashi qara aure saboda halayen hafsa,duk sai gwiwarsu tayi sanyi,hajiyan ta musu ba zata,irin abbas din shi kowa ke kwadayin samu,saboda alamun wadata da aziqi dukka sun fara bayyana a tattare dashi.
Tabbas hajiyan tasan da wannan,shi yasa tayi musu wannan ba zatar,ta kuma zartar da wannan hukuncin,fatanta daya abbas din ya samu inuwar da zai huta,ya kuma samu sanyin idaniyarsa.
Har a sannan hafsat din bata da labari,gidanta ba gidan zuwan 'yan uwan abbas bane,bama su kadai ba,hatta da nata dangin,saboda wata iriyar jarrababbiyar rowa da take da ita,muguwar sa'a ka taka idan kaje gidan ka samu tarbar pure water bare abinci,kusan anty ummee ce kawai ke samun wannan daga gareta,shi kuwa abbas,bayan ya ajjiye wa hajiya dukkan wani abu da yasan zata iya nema daga gareshi,komawa yayi kaduna,amma yace mata cikin satin daurin auren zaiyi qoqarin zuwa da wuri,da fatan alkhairi ta bishi,domin kuwa ita ya gama mata komai,sai fatan dacewa bisa niyyar alkhairin data nufaci rayuwarsa dashi.
************
Daga can tsakiyar 'yan jaridar dake dauke da nau'ikan kayan aiki daban daban,ASP ABBAS SARKI ne tsaye,sanye da uniform din 'yan sanda daga dace da structure na jikinsa,ya kuma yi masa kyau ainun,iya yadda yake tsayen kadai ya isa ya gaya maka cewa jajirtaccen police ne,wanda ya qware a aikinsa
"Wannan shine abinda ya faru a taqaice,we will let you know when the investigation is completed". Sai ya zare hannunsa daga aljihu yana shirin wucewa,amma suka sake yunquro masa da tarin tulin tambayoyinsu,rasa wacce zai amsa yayi,saidai akwai wani cikinsu da yafi kowa matsa masa da tambayar
"Amma yallabai,labari ya iskemu cewa kai da kanka ka gudanar da wannan aikin,kuma kaine ka samu nasara cafko su,shin meye gaskiyar wannan al'amari?,don dama jama'a sun dade da saninka da kuma ficenka wajen gudanar da aiki?"
Wani miskilin murmushi yayi wanda yake cike da tarin gajiya,murmushin da har yau hafsa ta gaza gane irinsa har sai ya buda baki ya magantu,yasa hannu ya cire hular police din dake kansa mai zubin P-cap,cikin muryarsa mai zurfi da kwarjini ya fara amsa tambayar tasa,bayan tarin jama'ar dake wajen sunyi shuru suna jiran amsa
"Ko ni nayi wannan aiki,ko bani nayi ba nasara ce,nasarata kuwa nasarar dukka jami'an tsaro musamman na 'yan sanda dake wannan qasar ne,muhimmin abu aci gaba da yi mana addu'a,fatan nasara" ya fada yana saluting nasu,sannan ya juya sa sassarfa ya shige ciki gudun kada su sake tsaidashi,sai wajen ya rude da muryoyinsu cikin farinciki kowanne na bawa kafar yada labaran nashi cikakken jawabi.
Tsaye yayi gaban table din office dinsa bayan ya ajjiye hular hannunsa a kai,saiya zare agogonsa ma ya dorashi saman hular,ya furzar da iska yana duba lokaci,ya riga yayi alqawarin barin Kaduna a yau zuwa bauchi,lokaci yanata quracewa ba tare da ya shaidawa hafsa komai ba,yanason ta fara ji daga bakinsa shi yasa ya hana kowa ya gaya masa,duk haukar da zatayi ta yita ta gama,yasan tabbas akwai case babba
Uwa uba kuma mai girma gwamnan bauchin yanason ganinsa,ya bashi appointment gobe da yammaci,zai sameshi gidan gonarsa,to dole tafiya ta kamashi a yau,saidai yana jin komai ma zaizo masa da sauqi da yardar Allah,tunda aikin da yake kwana ya kuma tashi dashi ya kammalashi,duka suspect dinsu suna hannu.
Wayarsa ya ciro da sirritaccen layinsa da ba kowa ya sanshi ba,ya kira wata number yayi confirming samun flight daga kaduna zuwa bauchi sannan ya aje wayar,ba kasafai ya fiya zirga zirga a jirgi ba,yafi ganewa yayi driving da kansa wani lokaci,yana tafe yana karantar hanya da inda tsaro yayi qaranci ko kuma inda komai yake tafiya dai dai,amma a yau din bashi da zabi illa yabi jirgin.
Taku biyu ya qara kamar zai fita,sai kuma ya fasa,ya sake daukar wayar yayi kira na sakanni ya ajjiye,ya shiga toilet ya kama ruwa sannan ya fito,ya duba dukka wani abu da yake da buqata cikin office din ya hada waje guda,bayan yayi wasu rubuce rubuce a wasu files sannan ya fito.
Daya daga cikin juniors dinsa ne yake driving nasa zuwa gida,yana a motar ya kira hafsat din don ya shaida mata tahowarsa,mimi ce ta fara daga wayar,sai data gama shirmenta sannan uwar ta karba wayar
"Kuna lafiya keda yaran?" Ya fadi don yasan zaiyi wuya ta fara tambayarsa lafiyarsa kota gaisheshi
"Lafiya qalau muke" ta amsa masa cikin ranta tana mamakin yadda ya sauko daga laifin data masa haka da wurwuri,duk da dama shi din bai cika riqo ba,amma a yadda taga ransa ya baci jikinta yayi sanyi,ta kuma aza zai mata hukunci mafi tsauri ne
"Am on my way to bauchi in sha Allah,two to three hours"
"Tooo....basai Friday ko Saturday ba?" Goshinsa ya murza kadan,ya salam,a nashi zaton tayi murna da yace zai dawo din ko?,amma saita buge da tuna masa ranar dawowarsa batayi ba?
"Na sani,inda muhimmin abu ne da zanyi a nan"
"Okay to,a taho mana da tsaraba"
"Yayi.....me zan samu?" Ta fahimci sarai me yake nufi,amma sai tayi kamar bata gane din ba
"Kamar me kenan?" Ta fada tana dan bata fuska,duk da ba ganinta yakeyi ba,zai dawo yanzu zai fara damunta da tsarabe tsarabensa.
"In so samu ne tuwo nakeso" tanason musa masa amma kuma batason bata saukowa da yayi daga fushin da yayi da ita ba tare data bashi haquri ba
"Xan qoqarta" ta fada cikin ranta tana jin ba zata iya yi ba
"Alright,saina qaraso" ya amsa ta ba tare da yaja doguwar hira da ita ba.
Bai wuce hutun awa yayi cikin gidan nasa ba,ya shirya ya wuce airport,gab da sallar isha'i cikin gidansa tayi masa, samuel ne yaje ya daukoshi ya ajeshi,ya shiga gidan nasa dauke da jakarsa,wata a hannu wata a kafada,sabida baya barin kowa da kowa ya shiga masa gida.
Yana shiga falon yanayinsa ya canza gaba daya,saboda qarancin tsafta da falon yake da,babu wani alamun qamshi ko qanqani da zaka iya ji daga falon,wala'alla ma idan ka taki mummunar sa'a hancinka ya iya shaqo maka qauri mara dadi dake ratsowa tun daga kitchen din dake falon zuwa hancinka.
Wannan ba baqon abu bane a wajensa,yayi fada yayi nasiha amma jiya iyau babu wani ci gaba,saidai yaci gaba da haquri kau da kai da nusashe ta,duk da hakan tana ganin kamar gazawarta yake gani,tunda dai tana iya nata bakin qoqarin a ganinta.
Yaran da suka garzayo suna masa oyoyo ya daure ya duqa ya rungumesu cikin jikinsa,ko daya babu wani kyakkyawan yanayi a tattare dasu suma,ita kuwa saita aje wayar hannunta tana dan sosa kai irin na marasa gaskiya,tare da qoqarin yi masa sannu da zuwa.
Amsawa yayi yana kallonta,wani hargitsatsen kaya ne a jikinta,atamfar dake jikinta ya soma gajiya da ganinta,idan zai iya tunawa da ita tazo gidan,kuma har yau ta gaza bada ita kyauta saboda tsabar baqar rowa,sau tari yakan tambayi kansa menene amfanin karatun da hafsa tayi?,tabbas da yasan haka zata ci gaba da kasancewa,baiga abinda zai sanya ya barta ci gaba da karatun ba,don wadan nan dabi'un nata babu wanda zai gani ya dauka yasan bihim a boko.
"Muje ku rakani na shirya" ya fada yana kada kan yaransa,saita bi bayansu da harara
"Agwagwa sarkin wanka" tafada,don tasan zuwa zaiyi ya hada ruwa ya musu wanka,ita duka ba wannan bane ya dameta,yadda dafa dukan shinkafar da tayi masa ta kama ta kuma yi qauri da kyau,ta yadda zata masa bayani take tunani,tasan halinsa,sarai baya wasa da cikinsa,ya baiwa abincinsa muhimmanci sosai.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 26
Koda ya shiga sassansa sai yaji dama dama,duk da cewa akwai qura data dan shishshigo masa amma kuma babu wannan dattin da annakiyar ta sassan hafsat,bai gaji sosai ba kasancewar tafiyar jirgi ta banbanta data mota,don haka ya ajjiye yaran saman kujera sunata masa hira,yahau kakkabe sashen nasa da goge goge,sai da yaga komai ya dauki haske,sannan ya hada ruwa yayi musu wanka da kyau,yana wasafa yadda zai samu lokaci yakai mimi a wanke mata gashinta.
Sai da ya gama shiryasu sannan yayi nasa wankan,ya shirya cikin kayan barci saboda tara ta gota a sannan,kamar ya kirata yace ta kawo masa abincin nan amma sai ya fasa,ya tasa yaran a gaba suka koma can.
Tana kitchen tana ta kaca kacar yadda zata hada masa koda coleslaw ne mimi ta shigo tace tazo inji daddy, saita maida.kayan hadin data debo din kawai,ta kwashi warmer da plate din ta biyo bayan yarinyar,tana dan hade ranta,wai koda hakan zai sanya yaji shakkar mata magana ko fada.
Saidai kuma ya bata mamaki,saboda yadda yakecin abincin yana yiwa yaransa hira ba tare da yace da ita komai ba,can qasan ransa yana ji ne kamar ya furzar da abincin daga bakinsa,duka dai yana daurewa ne saboda muhimmiyar maganar da zaiyi mata.
Koda ya gama cin abincin bai tashi a wajen ba,sunta hira da yaransa yana biyewa shirmensu,duk da hirar babu wani armashi,ita kuwa gogar tana zaune a gefa tana danna waya,abinda tafi kauri kenan,bata wani damu da hira da miji ba sam,lokaci lokaci takan dan sanya musu baki a hirar,a haka har nawwara dake saman cinyarsa tayi bacci,jimawa kadan mimi ma ta soma gyangyadi
"Gwara ki kaisu daki ko?" Yace da ita yana dubanta,saita aje wayarta tana dan bata rai
"Sai da nace ma mimi ta wuce daki idan ta fara jin bacci fa"
"She's too young da zata gane hakan ai" qarasowa tayi ta soma tashinta cikin hararrami,ya dakatar da ita cikin dabara ya daga yarinyar,ta kama hannunta suka wuce daki.
Ba jimawa ya miqe,ya nufi kitchen don dafa tea,saboda ba wani sakin ciki yayi yaci abincin ba.
Da kallo yabi kitchen din saboda uban wanke wanke da ya fara cin karo dashi,kana gani kasan ba iya kwanukan yau bane,saboda wasu ma sun fara bushewa wasu kuma sauran abincin ciki ya fara rubewa,kai ya girgiza takaicin na cinsa,ya matsa ya duba ma'ajiyar tukwanenta,cikin taimakon Allah ya samu wata wankakkiya,ya hada komai da komai ya tsaya ya jira ya tafasa ya juye ya dawo falon ya zauna ya fara kurba a hankali yana kallon labarai da ake haskowa a tashar alhadath,saidai sam ba ta nan hankalinsa yake ba,yana jiran jin fitowar hafsa ne,amma har ya gama babu ita ba dalilinta,wannan yasa ya miqe ya nufi dakin kansa tsaye.
Yana tura qofar suka hada ido,tana kwance tsakiyar yaran,ya qarasa shiga ciki a hankali hannayensa zube a aljihun wandonsa yana nazarin dakin a fakaice,komai babu kintsi,ko ina ba'a gyare yake ba,sai ya kauda kai ya maida gareta
"Zan wuce daki,wa zan daukar miki a cikinsu,coz na fara jin bacci,inason kuma muyi magana dake" fuska tadan yamutsa kadan
"Kawai ka kwanta a nan mana,ni bansan me yasa bakason kwana a dakina ba,saidai ni kullum ina yawon binka?" Ta fada yau dai tana dan karya murya,jingina yayi da madubin dakin yana qoqarin controlling kanta,gaba daya dakin its not well organized,komai a birkice yake ba bisa tsari ba,duk sanda zai kwana a dakin komai sai ya nemi inda aka wulla masa,wannan dalilin ya sanya zaiyi wuya kaga wani abu nasa mai muhimmanci a dakin.
Kafada ya dage
"Well,zanje na shirya"
"Yauwa,thank you"tafada tana dan jin dadi,saiya juya a hankali ya fice a dakin.
Sai da yayi shafa'i da wutirinsa,ya kuma dauka duk abinda yasan zai iya buqata sannan ya rufe sashen ya koma,ya isa dakin ya dora kayansa saman madubinta yana fadin
"didn't you sleep?" Saita motsa kadan tana cewa
"Uhmm"
"Okay,tashi,dama muyi magana dake" dan muskutawa tayi kadan,sai kuma ta miqe a hankali ta zauna tana dan murza idanu,zuciyarta na bada Allah yasa samuwa ce tazo.
Kujerar gaban madubi yaja ya zauna dab da ita,har gwiwoyinsu na gogar na juna,ya goye hannayensa a qirji yana duban fuskarta da manyan idanun nan nasa da suke saurin kassarata,tsahon wasu mintuna baice komai ba,har sai data qosa tace masa
"Wannan kallon fa?,kana azamin nauyi fa,ka tasheni bakacemin komai ba" kai ya gyada siririn murmushi yana kufce masa,saiya saki hannayen nasa ya hade yatsunsa waje guda
"Har yanzu motar da kikace min kinaso ita dince baki canza ra'ayi ba?" Wani madaukakin murmushi ya kubcewa hafsat din,abunda bata taba kawowa shi xai mata maganarsa ba,duk da dama abbas din ya iya bazata,ba daga nan ba
"Eh itace" ta fada cike da zallar zumudi
"Shikenan,nan da two to three weeks zata iso.....sannan kuma.....inaso ki duba kayan dakin da kikeson canzawa,ki turonsu ta watsapp,amma kada su d'ara 1mil,sai nasu mimi su kuma kada su wuce 50000k" wani irin mamaki da farinciki suka cikata,cikin muryar zumudi tace
"Da gask kake abban mimi?" ta fada idanunta a waje tanason ta samu tabbaci.
Kai ya jinjina mata yana sakin qaramin murmushi cikin bata tabbaci,hannunsa ta kama ya riqe da kyau tana dariyar farinciki gami da yi masa godiya.
Hannayen nasu yabi da kallo,yadda ta riqe masa.hannun dama bata aikata hakan idan ba wani abun farinciki ya sameta ba,idan bai manta ba rabon data riqe masa hannun haka tun lokacin da ya shaida mata ya biya mata hajji,sai ya zame hannun a hankali yana cewa
"Yauwa,dama nace zamuyi magana ko?"
"Ai mun gama magana,irin wannan manya manyan albishir haka?" Ta fada tana washe baki,sai ya kada kai
"Saura abu daya"
"To ina saurarenka" ta fadi ba tare data bada wani muhimmin ba
"Hafsa" ya kira sunanta,sai ta amsa tana murmushi
"Komai muqaddari ne daga Allah ko?,hakanan rayuwarmu da dukka qaddarorinmu suna hannunsa,yadda ya tsara haka bawa zaibi,hakanan fadarsa ne daga qur'ani ku auri abinda yayi muku dadi daga mata bibbiyu uku uku da hurhudu....." Statement dinsa na qarshe yasa fara'ar fuskarta taja baya,wani tunani kuma ya gilma mata,saita zuba masa idanu gabanta na wani irin faduwa,zuciyarta kamar zata fasa qirjinta ta fito
"Hafsat,Allah ya nufeni da qara aure,wanda za'a daura shi cikin sati mai zuwa"
"Meeee!!!" Ya fada da wata irin shaqaqqiyar murya,wadda tuquqin bala'i yasa ta gaza fita da kyau yadda ya kamata
"Relax,calm down please,hakan ba yana nufin matsayinki ya canza daga yadda kike a zuciyata ba....."
"Wallahi qarya ne!......qarya ne abbas......qarya ne wannan" ta fada ya qaaraaji tana nunashi kamar wata mahaukaciya sabon kamu
"Shine ka zaunar dani kana yimin wadan nan kyaututtukan?,to banaso,ka riqe kyaututtukan ka!,wallahi baka isa kuma ka qara aure ba!,ni kadai ce matarka!,ni kadai zaka zauna da ita duniya da lahira!!" Ta fadi da wani qaaraajin tana dubansa da idanunta da sukayi jazur suka kuma firfito kamar wadda aka shaqawa borkono.
"Cool down,karki bari ranki ya baci kinji......zauna muyi magana ta fahimta dake" ya fada with softness yana yunqurin kamota ganin tana shirin miqewa,fusgewa tayi tana jifansa da wani mahaukacin kallo,ta bude bakinta cikin madaukakin sauti ta fara gaya masa dukkan maganganun da suka zo bakinta,miyagun kalamai na aibatawa da kuma tunzuri,sai ya koma kawai ya zauna,ya harde hannayensa a qirji yana kallonta a nutse.
Ya sani ita aka tabo,kasancewa batun lamari na kishiya a wajen mace babban al'amari ne da ba kasafai suke iya daukan wannan mummunan labarin ba,wannan dalili ya sanya ya bata dama taketa fadin dukkan abinda taga dama ba tare da yayi yunqurin dakatar da ita ba,duk da kalamanta akwai wuce gona da iri da kuma zaqewa da yawa,amma yayi haquri ne ya jura saboda yasan wani ciwo ne da radadi daga zuciyarta,wanda shine ya dasa mata shi yanzu yanzu.
"Shine ka zauna kana kallona?, wallahi abbas baka isa ba,wallahi nace bazaiyiwu ba" sai tayo kanshi,tana rarumo kwalaben turaren dake saman madubinta ya soma qoqarin jifansa dasu.
Cikin qwarewa ya dinga sanya hannu yana cafe duk wadda ta jefo,ganin ko daya bata sameshi ba sai tayi kukan kura ta jawo bed lamp ta wurgota.
Bai samu tareta ba,amma ta dakar masa hannaye,glass din jiki kuma ya yankeshi ba tare daya lura ba,saita tsugunna inda take ajjiye takalmanta ta fara daukansu suma daya bayan daya tana masa ruwansu.
Miqewa yayi cikin zafin nama da mazantaka ya isa gareta,ya kama dukka hannayenta ya hade cikin hannunsa guda yana kallon fuskarta,ransa ya soma baci,ya dubi sashen dasu mimi ke a kwance,Allah yasa babu daya cikin abinda take wurgowa daya samesu
"Ki nutsu hafsat!,ki nutsu!"ya fada shima da murya sa mai kaifi da zurfi,saita dakata din ta kece da wani irin kuka
"Macuci azzalumi,Allah ya isa tsakanina da kai,kuma wallahi wallahi baka isa kayi wannan auren ba,idan ba haka ba sai na baka mamaki nima dakai da munafukar da zaka auro,ka fita ka barmin dakina,ka fita bana son ganinka!" Ta fada da mugun qarfi,saiya sakar mata hannaye,ya kuma taka a hankali zai fice,sautin amon muryarta ya dakatar dashi
"Kazo ka kwashesu,suma bana son ganinsu,ka debesu daga gabana!" Dawowa yayi a nutse yadan tsaya gabanta yana kallon yadda ta birkice gaba daya,jikinta banda tsuma babu abinda yakeyi,yasa hannu ya kwashe dukkan yaran ya fita dasu.
Ya jima yana mamakin baqin kishi it n na hafsat din,ashe abun ya wuce yadda take tsammani?,wanne irin hauka ne wannan?.
Bai lura da hannunsa dake zubar jini ba sai daya kwantar da yaran saman gadonsa yaga stains na jinin a jikin blue bedsheet din nasa
"Ya salam" ya fada sanda yake duba wajen,sai yaga ya yanke sosai,don haka ya koma dakin yaran dake sassanta don ya dauko first aid kit.
Tun daga falonta yana iya jiyo gunjin kukanta,irin kukan da mutum yake zama dirshan ya bude dukka muryarsa yayishi,tausayinta sosai ya saukar masa a rai,sai ya kasa wucewa ya sake komawa ta dakin,sai biyu yana murda handle din yana jinsa a riqe da alama ta kulle ne daga ciki,ya sassauta murya yana kiran sunanta
"Open the door please, don't hurt yourself fa"
"Ka tafi ka bani waje abbas,na tsaneka,banason kallon fuskarta,ka tafi nace tun ban bude na lahantaka ba!!" Duk yadda yaso ta bude din taqi,sai ma wasu miyagun kalmomin da zagi da yake antayo masa,hannunsa nata digar jini,dole ya haqura ya dauki kit din ya koma dakinsa ya gyara wajen.
Daren ranar baccinsa ragaggene,haka yayita kai kawo tsakanin dakinsa zuwa sassanta,yasan halinta da muguwar baqar zuciya,yana fargabar kada ta illata kanta ita daya kulle a dakin,saidai duk sanda yaje din zaiji motsinta,wannan ke bashi 'yar nutsuwa kadan.
*Arewabooks: Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 27
Washegari yaran da suka tashi suka gansu wajen babansu sam basu damu ba,murna suka dinga yi abinsu,shi ya dinga tiri tiri dasu,ya shiga kitchen da kansa ya hada musu breakfast mai kyau,da yake ya iya abubuwa masu sauqi hakanan cikin abinci,saboda yanayin karatun da yayi.
Sunci kuwa sosai kamar ba gobe,sai ya zauna yana kallonsu,zuciyarsa na gaya masa basa samun kamarsa,duk da store dinsa cike yake da cima kala kala,wani abun har ya rube ko ya lalace batayi amfani dashi ba bata kuma bayar ba saboda baqar rowa,yayi nasihar yayi nasihar har ya koma fadan amma a banza,mutum ne shi mai bajintar wadata iyali tun samunsa baikai haka ba,tun rank dinsa bai kai haka ba,baya son iyalinsa suga wani abu a wani gidan da babu shi cikin gidansa,to amma kusan duk wannan qoqarin nasa a yawancin lokuta a banza yake tashi.
Ruwan tea kawai ya iya sha bayan ya tabbatar sun qoshi,duk ransa a jagule in yake,saboda har sanann hafsat bata bude qofarta ba,yayi knocking yayi har ya gaji,ya ajjiye mata nata breakfast din bakin qofa amma baiga ta bude ta dauka ba.
Bayan duka sun gama ya maida kwanukan kitchen,ya zage kamar yadda ya saba yawa yawan lokutta ya soma gyaran sassan nasa,yayi masa qal yadda yakeso,ya canza bedsheet da sauransu,ya hada duk abinda ya cire da kayansu mimi da yayi musu wanka cikin laundry basket,ya aje inda mai wankinsu zai dauka,sannan shima ya shirya kansa sannan suka dawo falon hafsat din,koda wai zataji motsinsu ta bude qofar.
Saidai har suka gama zamansu ba ita babu dalilinta,a taqaice dai har zuwa azahar bata fito ba,yanason fita masallaci sallah amma kuma bazaiyiwu yabar yaran su biyu cikin gidan ba,don ita mimi din ma ba wani cikakken hankali ne da ita ba,dole ya hada kansu suka wuce sassansa,acan yayi sallar,sai la'asar daya dawo dora musu abinci yaga babu plate din daya ajema hafsat din,da alama yunwa ta korota,ta bude qofa ta dauka kenan,sai ya saki qaramin murmushi ya wuce kitchen din.
Har dare suka kwanta babu wanda yaga qyallinta,a taqaice dai washegari kusan abinda aka maimaita kenan,don haka a kwana na ukun ya shirya yaran da kayansu ya wuce gidan hajiya dasu.
Kallon farko data masa tasan hatsaniya ke tashi a gidan,ta kuma san bata rasa nasaba da batun aurensa,bata matsa da jin ba'asin kawo yaran ba,saboda tasan shi da zurfin ciki,zaiyi wahala ma ya iya zama yana fadin cikinsa,ta daiyi murna da zuwan nasu,don ba zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ta faru ba.
Ya jima a gidan,sai yammaci sannan ya wuce,a sannan tuni nawwara tayi bacci a jikinta,ta baiwa muneera ta kwantar da ita,sai data dawo ta zauna gefan hajiyan
"Hajiya da alama anty hafsat fa......"
"Na sani muneera" hajiyan ta katseta,saita rausayar da kai
"Shima uncle,ya haqura kawai hajiya suyi zamansu mana,irin wannan babu dadi fa don Allah" kallonta hajiya tayi,batasan ko taji abinda uwayenta ke fada ba,har mamaki suke bata yadda suketa goyon bayan hafsat akan auren nan,wanda tasan tsabar son zuciya ne,amma babu wanda baisan halinta ba da dabi'arta,idan sunce basusan yadda abbas yake samun careless daga wajenta ba wannan kam ba zata musa ba,don babu da wanda yake zancan,amma kuma sauran dabi'unta da abbas din ya dinga yaqi ta gyara fa?,ita hajiyan tasna wasu,saboda takan bashi shawari idan ta fuskanci yana cikin damuwa ne
"Ke yarinya ce,ba zaki fahimta ba,sannan keba namiji bace,nan ma ba zaki gane komai ba" amsar da hajiyan ta bata kenan,sai tace
"K'nnnn,ai shikenan" base on her experience tayi maganar,saboda taga halin da mamanta ta shiga sanda babanta yace zaiyi mata kishiya,a sannan hajiyan ce ta shiga batun(muneera 'yar dan hajiyan ce),duk da.bai fasa ba anyi,amma abubuwan da sauqi,to amma yanzun hajiyan da kanta takeson ayima anty hafsat din?.
Yayi tunanin zata kaishi qara wajen hajiya ko daya daga cikin yayunsa maza kamar yadda ta saba a duk sanda wani rikici data kasa jurewa ya hadasu,amma sai yaji shuru batayi ba,bazai iya tuna rana daya rak da ya kai qarar hafsat din ga danginta ba,duk da tarin matsaloli da laifukanta,shi wanann ba dabi'arsa bace kwata kwata.
Kwanaki biyar hafsat din tana a haka,cikon kwana na biyar din Allah ya jeho qanwar mamanta ita da naty ummee,matar data jima rabonta da gidan,yanzun ma.suna sukazo ta bayan layin,anty ummee ta roqeta su biyo.
Yana farfajiyar gidan shi kadai yana duba jarida,suka gaisa dashi suka wuce ciki,ba jimawa anty ummeee ta dawo
"Don Allah yallabai ka duba mana,hafsatun tana ciki kuwa?" Jaridar ya ajjiye ya miqe tsaye yana gyara shirt din jikinsa,yasan tana ciki,kawai taqi budewa ne tana zaton shine yake bugun,kuma a yau ya yanke zai balle qofar zuwa dare muddin bata bude ba,sai ya gewaye anty ummin yayin cikin gidan,ta bishi da kallo tana jaddada miskilancin sa,har yanzu yana nan dai ba abinda ya sauya.
"Ki bude qofar, ummee ce" ya gaya mata kai tsaye,bai qara minti guda ba sai ga motsinta,ta murza key dun data sawa dakin ta bude.
Wani irin scent ne mara dadi ke fitowa daga dakin,saboda qarancin iska me kyau,duk da akwai ac da fanka ta cikin dakin,amma baya zaton tana kunnasu,jikinta tun kayan daya dawo daga kaduna ya sameta dasu ne,da alama har wanka ta yiwa yajin aiki,ta nan inda yake tsaye yana iya jin sauyawar yanayin jikinta,sai ganshin kanta dake cuccure waje daya da alama bata tajeshi,fuskarta gaba daya ta kumbure,kamanninta sun dan jirkita.
Harara ta watsa masa sannan taja tsaki,tsakin da yakai har kunnen anty uwani dake falonta,tadan kama baki tanason tabbatar daga inda tsakin ya fito.
Ya tsani tsaki a duniya,ta kuma san hakan,shi yasa ta bishi dashi,ko zata samu ta fanshe bacin rai da quntata rayuwarta da yayi kaso daya cikin dubu na abinda takejin yayi mata.
Bacin ransa ya daure,ya juya yana barin wajen,saita biyo bayansa a hankali har ya fita a falon,ita kuma ta qaraso ciki,suna hada idanu ta zube a nan ta saki kuka,ciwon dake danqare a ranta ya motsa mata,don a kwanakin ita daya ke fama da baqincikinta cikin daki,kwata kwata basirar ta gayawa wani bata zo mata ba,hasalima wayar tana kashe tun ranar,saboda abbas din ta kashe,bataso yayi kiranta ma.
"subhanallahi meye haka hafsatu?" Anty uwani ta fada cikin firgici tana dago hafsat din,sai ta dan dauke kanta kadan saboda abinda ke tashi a jikin hafsat din,ta jata ta zaunar kan kujera sannan ta zauna dan nesa kasan da ita
"Lafiyarki kuwa?" Anty ummee itama ta jefa mata tambayar tana kallonta,cikin muryar kuka kamar wadda akace wa'adinta ya qarato ta soma magana
"Na shiga uku na lalace anty ummee,anty uwani wallahi mutuwa zanyi,abbas ne yace zai qara aure" ta qarasa fada tana rushewa da kuka,haushi da takaici ya qume anty uwani,yadda taga hafsat din ta aza hannu aka ta zauna dirshan a wajen tana musu irin wannan kukan na tashin hankali
"Mutuwa fa kike fada hafsatu,kinsan mutuwar kuwa?" Anty uwani ta fada tana harararta
"Sai an bita a hankali ai anty uwani.....sannu yi haquri tashi ki daina kukan" anty ummee ta fada yana dagota daga zamewar da tayi daga kan kujerar.
Da kallon takaici anty uwani ta bisu su duka,ta da jin labarin abinda hafsatun keyi a gidanta,qazanta baqar rowa,ga rashin iya mu'amala da mutane,kuma ko a yanzun ta sake shaida tabbatar qazantarta,saboda yadda jikinta yake tashi ba kowa ne zai juri xama kusa da ita ba,da alama kwana biyar din kenan batayi wanka ba.
Tana jinta sanda take rattabowa ummee labarin yadda komai yake wakana,tasani wanda suka fita ma sun gaya mata ba daukan shawara takeyi ba,ko a yanzun ma tasan idan tace zata gaya matan bata baki ne,don haka sai ta miqe
"Kin gama ko na wuce kya taho?" Dubanta anty ummee tayi
"Aah ki bari mu wuce tare mana"
"Um um,yi zamanki,nikam ina da uzuri,saikin taho,hafsatu sai a qara haquri,ki duba dukka iya kurekurenki da abubuwan da kikasan bayaso ki gyara tun yanzu,Allah ya bada haquri" badon tasan anty uwanin bata da wasa ba,bata kuma daukan wargi da ashar zata maka mata,amma hakanan ta hadiye bacin ranta tace mata ta gaida gida da shaqaqqiyar muryarta data ci uban kuka.
"Yanzu me kika yanke ke?" Anty ummee ta fada bayan ta dawo daga raka anty uwani,ragowar hawayen dake fuskarta ta share,tana jin gaba daya rayuwarta ta juya mata baya cikin kwanakin nan
"Babu wata shawara ko dabara da nake da ita,kawai dai abinda na sani,koda tsiya ko da bala'i wallahi bazan bar wata mace ta rabi abbas ba,bazan iya zura ido ina raye ba abbas ya auro wata mace da sunan matarsa ba" jinjina kai anty ummee tayi
"Amma ina ganin wanann ba dabara bace,kwata kwata ragon azanci ne,kinfi kowa sanin halin mijinki,idan yace yes babu wanda ya isa yasashi yace no,tunda ya niyyata babu wanda zai hanashi....."
"Niko naci alwashin koda ta qarqashin qasa saina hana shi auren nan anty ummee" ta fada idanunta na sake kadawa suna kuma sake cika da hawaye.
Ajiyar zuciya anty ummeen ta sauke,sannan tadan gyara zamanta
"Niko sai nace wannan din ba hanya bace mai bullewa,face hanya mai wahala da kuma sanya kashe kudi,a matsayinki na mace,mai yasa ba zakiyi amfani da KISSARKI ba?" A hagunce hafsat din take kallon anty ummee,saboda bata fahimci me tafi nufi ba gaba daya,mafita kawai take nema,saboda haka tace
"Kamar yaya kenan anty ummee???"
**********Tun daga ranar bata sake kulle kanta ba,saidai kuma sabgarta takeyi kawai ba tare data shiga sha'aninsa ba,bai damu can can ba,don ko sanda suke shirin ma ba wani abu take dauke masa ko takeyi masa ba,kusan ya saba....fiye da rabin hidimominsa shikewa kansa,saidai ya dan samu nutsuwa,tunda aqalla bata sake tada wata fitina ba,har abun yaso ya bashi mamaki sosai.
********Karfe biyar na yamma tana kitchen tana hada abincin dare taji knocking,ta fito a kitchen din tana gyara daurin zaninta daketa kwancewa tun dazu,don bata daurin baya sai daurin gefe,a cewarta yana damunta ne.
Tana bude qofar sukayi arangama da yaron gidan wanda ke musu aike aike,sai ya danja baya kadan cikin jin nauyi saboda ganinta babu mayafi
"Madam oga ne yace a kawo,masu kayan gado ne da furnitures,zasu kwashe wadancan su saka sabbabi,yace muzo dasu suyi aikin" ta zuba masa ido ne taga zaiyin ko bazaiyi ba,duk da zancan kullum yana ranta dashi take kwana take kuma tashi,duk da ranta a bace yake matuqa har komai ma baya burgeta,to amma kuma tana son alqawaruran da yayi mata din.
"Su bani minti goma ina zuwa" ta fada tana juyawa,ya rusuna cikin girmamawa ya amsa mata da to.
Dakinta ta koma ta fara kwashe abubuwanta masu muhimmanci waje daya,aikin nada dan yawa,don sai ta shiga dakinsu nawwara ma ta hada nasu kayan,tanason ta samu dan tayi,to amma tasan a dai dai wannan lokacin koda tayi waya gida babu lallai a samu me zuwa ya tayata,saboda kowa yasan halinta da dna banzan rowa,saidai kayi mata wahala,dole ta koma kitchen ta kashe gas din girkin,dama ba wani girkin arziqi ta aza ba,tafi sati ma basa abincin saidai yayo musu takeaway,ita kuma ta nema wani abun taci.
Sai da ta kusa awa guda sannan ta gama,duk ya hada gumi saboda ba maison aiki bace,sanann ta koma kitchen tana maida numfashi,su kuma suka shiga aikin gyara dakunan.
Ana idar da sallar magariba suka gama kafa kayan gadon,da yake ba mutum daya ko biyu bane,sun kusa su biyar,suna fidda wadancan kayan ta fito
"Su kuma wadan nan za'a kaisu?" Ta tambayi shazali yaran gidan
"Yace a fiddasu compound a ajjiyesu" kai ta kada
"Ka bawa masu kayan gadon idan suna siyan second hand,tunda wadan nan ba wani dadewa sukayi ba,kuyi ciniki su baka kudin ka kawomin" kamar yace ba haka oga yace ayi ba,to amma sai yaga meye nasa?,tunda kayanta ne,kuma matarsa ce?,don haka ya amsa mata da to yana ficewa,ita kuma ta juya ta shige dakunan tana jan tsaki a ranta,kudi takeso ta tara mai yawa daga jikinsa,ko banza ta rage wani radadin.
Sosai dakunan sukayi mata kyau,dukka ya zaba favourite colors dinta ne,dakunan sun canza gwanin sha'awa,duk da ranta a bace yake amma sai data danji ta sauka kadan.
Ba'a rufa awa ba kuwa ya dawo mata da kudin kayan cas,ta karba ta soke abinta taci gaba da sabgarta hankali kwance,ranar baya nan,yaje azare,zai kuma kwana sai washegari zai dawo,don haka hankalinta kwance ta gama tsara abinda zatayi da kudin,koda kuwa ya dawo ya tambayi yadda akayi da kayan,barema tasan halinsa,zaiyi wuya ya tambaya din,don bashi da wannan,amma koda yana da niyyar ma ta shirya abin fada masa.
*Arewabooks:Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*
Page 28
*********Washegari tana dakin yaran tana sauya musu kaya bayan tayi musu wanka taji ana sallama a falon nata,qaramin tsaki taja,ita gaba daya batason baqi a rayuwarta tun asali,bare a yanzu da take cikin wannan yanayin,mimi ta aika ta dubo waye?,sai ta dawo tana ce mata baquwa ce,tadan harari yarinyar,har yanzu taqi tayi wayo irin yadda takeso,irin wayon da zata iyayi mata bayanin duk abinda takeson ji,saita ajjiye kayan nawwara da bata kai ga sanya mata ba,ta miqe tana cewa
"Bari muga wanne munafukinne" tayi waje yaran suna biye da ita.
Tun kafin ta qaraso ta hangi wacece,rabi'atu ce,cousins suke da abbas din,takan jima bataga rabi'atun ba,bama ita kadai ba,danginsa ma yawancinsu ba wani zuwa sukeyi ba,saidai idan an hadu a wani sha'ani idan ta samu zuwa saisu gaisa,suna girmama ta dai dai gwargwado,amma ta dauki hakanne a mazaunin don anga mijinta yana da rufin asiri ne.
Fuskarta kadaram kadaham ta qaraso ta samu kujera daya ta zauna tana dan satar kallon rabi'atun,saboda daga nesa taga yadda take satar kallon falon,zuciyarta kuma ta raya mata gyaran da akayi mata take kallo
"Dangin miji irin jaraba" ta fada a ranta,babu dama suga sakakken abu a gida ko a jikinka sai sun nuna a fuska ko a kalaminsu(nace uhmmm,inama suka hadun ko sukazo gidan bare hakan ta faru?).
Ba yabo ba fallasa suka gaisa da rabi'atun,sai kuma shuru yadan biyo baya,sai ita din da taketa qoqarin yiwa su mimi wasa,wadanda suka qi sakin jiki da ita saboda rashin sabo da basuyi da su ba.
Kai rabi'atun ta dago tana cewa
"Wai nan bayanku nazo suna,kinsan a nan qanwar mijina take aure"
"Uhmmm,Allah sarki" ta fada a taqaice
"Sai nace nari na qaraso mu gaisa,na kuma yi miki murna ko jaje zance,ashe kuma yaa abbas aure kishiya zai miki?,kuma a rasa wadda za'a rakito miki sai 'yar wani garin,kuma ma yarinya qanqanuwa wadda a haife ya kusa haifarta" da fari cin mutunci hafsat ta shirya yuwa rabi'atun,amma jin ta fara bata hint akan abubuwan da batasan dasu ba saita maida wuqarta tana gyara zamanta
"Ya kusa haifarta fa kika ce?"
"Wallahi haka inna ke gayamin,tunda kwata kwata bata wuce shekara sha uku zuwa sha hudu ba" wani abu ne ya tsargawa hafsat,saita nema tashin hankalinta kaso talatin cikin dari taji babu shi,ta aro sakin fuska ta dorawa fuskarta
"Kin ganta ne rabi'ah don Allah?" Kai Rabia ta girgiza
"Ban dai ganta ba,amma inna tacemin ta taba ganinta gidan sau daya,badai 'yar nan bace 'yar kano ce" gabanta yadan fadi kadi jin abinda ta fada daga qarshe,ana wata ga wata,ko zakayi kishi yafi kayi da 'yar garinku,kar tasan kar ne,bawai kayi da bare hayin wani gari ba,garin ma da tasha jin masu kishiyoyi daga wannan nahiyar suna qorafi,to amma 'yar shekara sha uku zuwa sha hudu kishiya ce ko 'yar raino?.
"Ni irin wannan auren banda abin hajiyarsu,mutum na zaune da matarsa ya dauko aure,a kuma tsallake gida a tafi dawa?"
"Da gidan da waje duk dai kishiya ce,ko daga dakinki aka fiddo miki da ita sunanta kishiya" hafsat din ta amsa mata rana dan hade rai,saboda tasan yadda 'yan mata da yawa cikin familyn ke sonshi,kamar shi kadai ne namiji a family din nasu,sai data dinga murje idonta tana yanka musu rashin mutunci ta samu salama.
"Gaskiya dai" rabi'atu ta waske ta hanyar fadin haka,bata jima sosai ba saidai hafsat din tadan samu wani haske akan lamarin,da yadda hajiyansa ke maraba da abun,daga qarshe sukayi sallama,ko pure water rabi'atu bata samu daga wajenta ba,haka tabar gidan tana tsine mata cikin zuciyarta,saidai duk da haka sudai suna adawa da wannan auren,tunda nasu basu samu ba 'yan qannensu da suka zama 'yammata gwara a bata goma daya bata gyaru ba gaba daya.
Rabiah tana fita hafsat ta wuce daki cikin hanzari,ta dauko wayarta ta soma neman number din anty ummeee ta labarta mata labarin data samu,saidai duk saurinta ya zama nawa saboda babu kati a wayar tata,dole ta koma ta mobile app din bankin da take amfani dashi,ta saka card din dari biyu ta kirata.
Sai data kusa tsinkewa anty ummee din ta daga,hafsat na daga tsaye ta gaza zama,sai kai kawo takeyi
"Anty ummee....kina jina?" Ta fada da matuqar zaquwa,har kana iya jiyo haka cikin muryarta
"Ina jinki hafsatu,lafiya?" Guri ta samu saman bedside drawer dinta ta zauna sannan ta soma magana
"Yanzun nan rabi'atu cousin din abban mimi tabar gidan nan,kinsan yarinya qarama yaje ya dauko?,ko shekara sha biyar bata cika ba?" Ta qarashe maganar tana tabe baki,takaici yana cikata.
Dariyar da anty ummee ke qyalqyalawa tayi kasake tana saurara,sai daga bisani tace
"Kai haba?,kice raino ya dauko?,tirqashi,to ke ai ta fadi gasassa,babu kuma wani sauran kishi da tashin hankali daya rage miki"
"Kamar yaya?,haba anty ummee,idan za'a maka kishiya ma ai sai ayi maka isassa,wadda zaku goga da ita,ba wata can qasan qasanka ba"
"Tabdijan" anty ummee ta fada sannan ta dora da cewa
"Amma bansan baki da hankali ba sai yau,ke!,kishiyar da zata shigo ta goga da ke ai masifa ce,me yayi miki zafi?,to idan baki sani ba bari na gaya miki,Allah sonki yake shi yasa ya hadashi da qwaila,a yanzun ne za'a fara wasan ma da kyau,dama dukka tana hannunki,idan kika dauki.maganganun da mukayi dake rannan kikayi amfani dasu da kyau to ina me tabbatar miki yadda zaki bawa su mimi da nawwara umarni itama haka ne,ba boka ba malam,komai zaizo miki da sauqi,kina daga kwance kina sarrafa gidan a hannunki,yanxu saurara nayi miki wani sabon karatu......." Gyara zama tayi sosai tana bada hankalinta ga anty ummee din,tana hasashen qamshin gaskiya cikin msganganun anty ummee,sai taji ranta ya fara yin fes
"Ina jinki" ta cewa anty ummeen......
*********Can quryar gadon ummu take kwance abinta,ta duqunqune waje daya,duk kuwa da cewa gidan a cike yake da baqi jikoki da surukan gidan,wanda a baya duk lokaci irin wannan tana tare dasu sunata sabgoginsu,sabanin yau da gaba daya take jinta wani iri,musamman da aketa mata abubuwa daya banbanta dana 'yan uwanta,aka kuma tsameta daga cikinsu.
Tana daga kwancen tana kallon yadda ummu ita da warisha qanwar abbanta suketa hada kaya cikin manyan buhunhuna da kwalaye,wanda gaba daya kayan ummu tace nata ne,gidanta za'a kai mata ayi mata jeranta,itama ta samu nata gidan na qashin kanta,duk sanda ummu ta fadi hakan dadi takeji,amma yau gaba daya jikinta ya sanyaya,gwiwarta ta fara sagewa.
Ana tsaka da wannan latifa tayi sallama ta shigo dakin ummun,ta tsaya daga bakin qofa yana gayawa ummu game gyaran jiki tazo,tunda widad din taji haka ta runtse idanunta tahau baccin qarya,ita kwata kwata batason wannan kwabe kwaben da aketa shafa mata yau wajen sati guda kenan,tana jin sanda ummun ta waiwaya tana qwala mata kira,amma sai ta sake lafewa cikin bargo tayi kamar bacci take,har ta gaji da kira ta juya ga latifa
"Inaga kawai abar aikin nan haka,dama yau da gobe ne kawai ya rage"
"To shikenan,bari na sallameta,yauwa......anty madina tace na gaya miki,kayan miyar ya za'a yi dasu,a markada gaba daya azubasu a freezer baya?"
"Eh hakan yayi,don kada su lalace kafin jibin"
"To shikenan" sai latifan ta juya ya fita,su kuma sukaci gaba da hada kayan,tana labe cikin bargo tana satar kallonsu,tana jin anty warisha na cewa
"Banda abun ummu nawa ma jikin widad din yake,me ya sameshi ma da za'a mata gyara,ita da dama fatarta me kyau ce,a haka ma a karon banza daukan ido takeyi"
"Wallahi madina ta matsa sai anyi mata,to ya na iya,itakam dama ta iya biyewa shirmensu,yanzu haka ta gama tsara musu komai,har kudi tasa muhsin ya karba musu wajen ango wai zasuyi walima" dariya warisha ta sanya
"Kai,Allah mai iko,widad amarya" sai ummun ta murmusa kawai,don dauriya kawai takeyi batason aga rauninta.
Tun tana labe tana kallonsu har baccin gaske ya dauketa,bata farka ba sai dab da la'asar,sanda ta tashi dakin babu kowa,sun gama aikinsu sun fice,bandakin ummun ta shiga ta daura alwala,ta shimfida abun sallar tayi sallarta,saita dan zauna tana jin hayaniyar su nabiha da sauran jikokin gidan,daga bisani ta gaza daurewa ta fito.
Ido kuwa yayi mata caaa,mutane anata kiranta da amarya,saidai ta tura baki tayi gaba abinta,itafa shi yasa tunda aka fara baqin ma batason fitowa,a haka dai ta samu ta wuce sassan anty madina,a canne ta sake sosai abinta,harta manta da komai ma,har sai da anty madina tace lallai gobe za'a tsefe kai ayi kitso,a nan fa suka raba gaari da ita,saboda ta ambato maqiyinta wato kitso.
*RANAR DAURIN AURE*
Cikin jerin gwanon motoci na alfarma suka taso,tun daga garin bauchi zuwa cikin garin kano,qarqashin jagorancin jami'an tsaro da matakai masu tsauri,a ranar tamkar dai wani shugaban qasa,duk yadda ya dauki daurin auren sai ya wuce masa haka,tamkar dai dama ya dade da shiryama hakan,shi kansa cikin sabuwa dal din motarsa yake,yana seat din baya shi da suraj,sanye da wata danyar shadda wadda koda gari aka baka ka canki kudinta ba zaka ajeta nan kusa ba.
Tunda suka taso fuskar hafsat ke masa yawo,tunda zancan ya tsiro bai taba jin tausayinta irin na yau ba,yana hangen yadda fuskarta ta sauya a sanda yake shiga motarsa cikin shigar dake jikinsa a yanzu,saidai zuciyarsa cike take fal da mamakin mene ya sauya hafsat?,me kuma ya kawo wannan sauyin?,yasan halinta ciki da bai,meye ya sanyata zub da makaman yaqinta?,wannan amsar ce har yanzu ya kasa lalubota,sai tarin wasi wasi da yake fama dashi kullum kwanan duniya.
Tun daga titin farko zuwa abinda yakai layin da zao sadaka da ainihin gidan alhj salim mai fata cike yake tanqam da jama'a,idan akace maka jama'a ina nufin jama'a na gaske da zakayi tsammanin daurin auren wata hamshaqiyar budurwar data ci ta qoshi da karatu da wayewa akeyi,gaba daya unguwar a hargitse take sakamakon halartar daurin auren da manyan 'yan siyasa gwamnoni da kuma qusoshin gwamnati da abbas yake hulda dasu sukayi,jama'a dake tsaye a gefe guda suna ci gaba da lissafa gwamnonin da sukaga suna shiga unguwar tasu,sai da suka lissafa shida casss!.
"Bisa dukkan alamu wannan karon babban kamu akayi a gidan nan,lallai yau sun jawo babban kai,kai kaga motocin dake ta gilmawa kamar daurin auren 'yar shugaban qasa?" Ire iren maganganun da matasa 'yan zaman banza a bakin layi keyi kenan,sunayi suna ci gaba da dorawa a lissafin su.
Daga can cikin gidan kuwa a shaqe yake da jama'a,ko ina idan ka kalla hada hada akeyi,zaka tsammaci an dauki shekaru ne ana yiwa bikin tanadi,saidai hausawa suna cewa,kowanne aure da arziqinsa yake zuwa,wanna haka yake,domin kuwa a lokacinne aka baje lefen widad wanda ya iso ne tare da 'yan daurin aure,akwati mai sunan akwati,akwati na alfarma guda goma sha biyar,kowanne maqare da sutturu masu daukan hankali,duk wanda ya daga idanu ya kalla koda baiso magana ba sai bakinsa ya subuce ya furta
"Ma sha Allah"mafi yawan mutane cikin family da wadanda ke cikin gidan dake zuba idon suga wani abun kaico ya bulla sai jikkunansu suka fara yin sanyi,musamman da labarin irin manyan mutanen da suka halarci bikin yajewa kunnuwansu..........
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 29
Qarfe biyu na rana bayan sallar azahar aka daura auren asp abbas da amaryarsa widad mahmud salim akan sadaki naira dubu dari,dubban jama'ar da suka halarci wajen suka haida,labarin kuma ya kai har cikin gida ya fara yawo a tsakanin mata.
Dai dai lokacin widad na zaune tsakiyar anty deena da anty warisha,sai sharban kuka takeyi,duk yadda sukayi da ita tayi shuru bare a samu ayi mata kwalliyar daurin aure taqi,sai suka sakata a gaba kawai suna kallonta.
Anty madina ce tayi sallama ta tana turo qofar dakin,dakin da babu kowa sai su ukun kawai,warisha ta amsa sallamar anty dina dake danna wayarta kai kawai ta daga ta kalli anty madina
"A'ah,na zata zanzo na tarar kun gama,an gama daurin aure fa,angwayen ma yanzun zasu shigo za'ayi hotuna"
"Inafa akayi kwalliya,kin ganta nan ko kayan taqi ta saka ma,ni bansan me yake damunta ba" anty deena ta fada tana ajjiye wayarta a saman madubin dakin.
"Ashsha,haba widad,mene hakan?" Hawayenta taketa qoqarin tsayarwa ta hanyar shareshi da hannuwanta amma hakan ya gagara,wani irin bacin rai tsoro da kuma takura takejin kanta a ciki,wanda ita kanta batasan dalili ba,kawai batason barin gida ne,hakanan shi uncle abbas din ta yaya za'a wani ce shine mijinta tana zaman zamanta?.
Anty madina ce ta cewa su deena din su basu waje minti biyar kacal,nasu musa ba suka miqe,anty deena ta dauki mayafinta mahadin lace din jikinta ta fara yin gaba,don dama ta fara gajiya da zaman lallashin widad din,wadda bata da alamun daina kukan.
Cikin mintuna goma sai ga hawayen ta tsaya tas,anty madina kuma ta shiryata da kanta,hatta da undies ita ta bata ta saka,tana jin kunya tana nonnoqewa,ta shiryata cikin wani lafiyayyen lace fari da ummu ta kashe maqudan kudade wajen siyansa,aka kuma shirya masa nutsatsen dinkin doguwar riga,gashinta da yasha gyara ta tufke mata,sannan ta qawata mata kanta da sarqa ruwan gold da aka sanyawa saman ka,wanda kusan al'adace ta asalin yarensu,hannayenta sun sha warware masu kalolin gold masu asalin tsada,haka yatsun hannunta kowanne zobe ne bibbiyu daga tsakiya.
Fes widad din ta fito,asalin quruciya da qaranci shekarunta na sake bayyana kansu,wanda ya cakuda da qyallin amarcin da akewa kowacce mace feshinsa,komai kyau ko muninta,indai sunan nan na amarya ya hau kanta.
Kiransu anty deena tayi sanda taji hayaniya ta fara cika gidan,muryoyin maza na tashi,alamu dake nuna tawagar angwaye ne suka shigo gaisawa da surukansu,daga inda take sai ta dinga jin kamar an daureta,gabanta ya tsananta faduwa,wani tsoro yana shigarta,kanta a qasa,nutsuwa ta musamman irin wadda duk wanda yasan widad din bai santa da ita ba ta saukar mata.
Shi daya ne cikin motar kwance a seat din gaba,ya dage dukka baqaqen gilasanta,da hular da kuma babbar rigar duka ya ciresu ya jefa seat din baya,ta cikin motar yana iya hagen kai da kawon jama'a,ciki harda gungun abokansa da suka masa karar da ko auren farko bai sameta ba.
Amatsayinsa na jimi'in tsaro,duba daya yayi musu yana daga kwancen ya fahimci shi suke nema,yasan zancan bai wuce ace su shiga cikin gidan,abinda sam bashi a tsarinsa kenan,saboda yana kallon haka a mazaunin keta haddin shari'a,tu dazu ya shigo ya kwanta,ya kuma gargadi Samuel kada ya gayawa kowa yana ciki.
Idanunsa ya janye a hankali daga inda yake kallo sanda yaji ana knocking qofar motar,fuskar suraj yake hangowa wanda yayi wujiga wujiga saboda yawan al'ummar dake wajen,sai yasa hannu a nutse yana daga kwancen ya buda murfin motar,suraj ya sunkuyo yana sako kansa.
Ajiyar zuciya ya sauke
"Gaskiya baka kyauta mana ba,kaifa ake nema tun dazun,zaa shiga gaida iyaye da kakannin amarya,ga masu hotuna suna jira suma zasu wuce" kamar wanda baya son yin magana ya buda bakinsa
"Duk da wannan uban jama'ar zamu kama mu shige musu gida suraj?"
"To ya za'ayi,al'adace" kai ya girgiza
"Ba dani za'ayi wannan aikin ba,idan ya zama dole ka sallamesu su tsaya iya waje,mu shiga koda mu uku ne muhsin yayi mana jagora iya sashen ummu kakarsa mu gaisa mu fito" dan hade rai suraj yayi,sai kuma ya saki dariya
"Kai mutumina,anya ba kishin matarka ka fara ba?" Wani kallo ya watsawa suraj din
"Waikai me yasa baka da girma saina jikinka,yarinyar da idan auren qauye ne na haifi kamarta?"
"Allah yasa motsin gado ce,bar ganin allura,duk qanqantarta qarfe ce,any way.....banga laifinka ba,bari ina zuwa" ya fadi yana maida murfin motar ya rufe.
Sai da yayi settling komai yadda abbas din yakeso sannan ya sanar dashi,hularsa ya dauka ya mayar saman kansa,ya riqe babbar rigar a hannunsa,yana jin ta masa nauyi,saboda rashin sabo da sanyata,tunda gaba daya aikinsa yafi alaqa da qananun kaya.
Kamar jiransa maroqa da masu buga kakaki suke suka fara busarsu suna wasa shi,baisan a inda suka san muqaminsa da kuma muqaman da ya riqe a baya ba,duk da juniors dinsa da suke masa bodyguard hakan bai hanasu binsa da kide kidensu ba
"Ka sallamesu don Allah" yace da suraj,saboda yadda yakejin kidan na haura masa har saman ka,sai da suraj din kuwa ya sallamesu da kudi masu tsoka sannan suka ja suka tsaya daga nan suna ci gaba da yagar rabonsu a hannun duk wamda suka fuskanci dan gaban goshin bikinne.
Babban falon ummun cike yake da jama'a,saidai da yake yana da yalwa babu laifi ba'ayi cushewar da zaka fuskanci yawan jama'ar dake cikinsa ba.
Duk da fargaba da kuma alhinin rabuwa da widad din tata hakan bai hanata qure ado fiye da duk wani bikin jikarta da za'a yi ba,ta cake cikin wani danyen lace purple color daya haska farar fatarta dake dan bayyana yanayin shekaru da suka soma hawa kanta.
Muhsin ne ya gaya mata ga abbas nan zai shigo,don haka ta kira hauwa'u da batulu(matan baban widad) tace su rage mata jama'ar falon.
Duk da jikinsu a mace yake saboda ganin irin hidimar da akeyi amma wannan aikin kam cikin karsashi suka yishi,saboda suma suna buqatar ganin mijin widad din sosai,cikin lokaci qalilan falon ya sake fili,ya zamana sai manya a cikin dangi suka rage,dai dai lokacin sukayi sallama suka shigo cikin falon su uku.
Kamar yadda a tsarin zubi da halitta gami da kwarjini ya fita daban......hakanan adonsa da shaddar jikinsa ta banbanta data kowa,sai ya fito kamar wani wata a cikin taurari,qanwar ummu da sauran jama'ar dake wajen ke marabtarsu,har suka samu waje qasan carfet suka zauna bisa tsari na tarbiyya,sannan aka soma gaisawa.
"Da gani babu tambaya,wannan na tsakiyar shine surukin namu ko?" Batulu da wani malolon abu ya tsaye mata a wuya ta fada,fuskarta kwance sa murmushin yaqe,kusan kowa a wajen sai da yaji banbarakwai,saboda ba ita ya dace tayi tambayar ba,ko banza ya kamata ace akwai kunya tsakaninsu,saboda a yanzun sune kamar copy na mahaifiyar widad.
Murmushi suraj ya danyi,baisan dangantakar ta da widad ba,ya dauka abokiyar wasa ce,tunda suna irin haka,dalilin da yasa ya maida mata kenan cikin salo na wasa
"Aah,nine fa,kingi batan dabo"
"Allah ya sanya alkhairi,yasa anyi kenan,jikanyar tamu qaramar yarinya ce qwarai,sai anyi haquri da halayen quruciya da za'a yita gani,Allah ya bada zuri'a dayyi ba" qanwa ga ummu tayi hanzari katse doguwar maganar da batulu keson taja,falon sai ya game da addu'ar ameen ameen.
Abbas din na shirin miqewa muhsin yashigo yana fadin ina widad din afito da ita,azo ayi musu hoto
"Ya salam" yafada a ransa,me yasa muhsin zai masa haka,bashi da zabi illa yayi jiraye.
Anty madina da anty deena ne suka fito da ita ta can backyard din gidan,basa so kowa ya tsaidasu bare kwalliyar tata ta baci,suna tafe anty madina na jaddada mata kada ta sake tayi kuka,zata bata fuskarta
"Ke maison kwalliya,kinga yadda kikayi kyau kuwa widad,baki taba kyau irin na yau ba" takanji dadi idan akace kwalliya tayi mata kyau,musamman daya zamana ita din mai son kwalliyarce,to amma kuma bata samunta sai lokaci lokaci,yau din da anty madina ke cewa tayi kyau sai bata ji wannan dadin da takanji ba,ta daiyi qoqarin dakewa,tanason farantawa anty madina rai,saboda kirkinta da yadda take sonta.
Sallamarsu cikin falon ya ja hankalin jama'ar dake falon,badawiyya abokiyar wasa ga widad din,wadda shigowarta kenan falon ta saki guda data ratsa falon gaba daya.
"Ma sha Allah.....ma sha Allah,widad Allah yasa anyi a sa'a,Allah yasa mutu ka raba" bakunan masoyanta dake wajen ya cika da addu'a,yayin da kishi hassada da kuma qyashi ya cika zukatan wadanda ke qin jininta hakanan.
Gaban ummu suka so kaita,amma saita musu nuni dasu ajjiyeta gaban abbas din ba tare da tayi magana ba,sun fahimta,saboda haka suka nufi gaban abbas din da ita,ganin haka yasa tun kafin su qaraso suraj da muhammad da suka masa rakiyar suka janye baya,suka basu fili sosai.
A hankali suka tsugunnar da ita a gaban nasa,rabin fuskarta yana rufe,saidai hakan bai hana kayan adon dake jikinta bayyana ba,suka ja da baya,sai falon ya dauki hayaniyar abokan wasa da suketa yiwa juna tsiya tsakaninsu da uncle muhsin,abinda ya dan janye idanun mutane kenan daga kan abbas da widad din.
Tana zama awajen wani irin qamshi ya soma fita daga jikinta,sassanyan qamshi mai fusgar hankali da kwantar da zuciya,irin qamshin dake saurin sakawa zuciya karaya da wani irin sassanyan yanayi,ya daga idanunsa a hankali,fararen hannayenta da suka jan lalle irin na asalin yamalawa su ya fara gani,a hankali yaci gaba da kallonsu kafin ya daga kai zuwa ga fuskarta,dai dai sanda itama ta daga kanta zuwa gareshi don ta gaidashi kamar yadda anty madina ta gaya mata,fuskarta ta fito tarwai da wani irin haske data qara
"Ina yini" ta furta,bugun zuciyarta na bayyana har saman harshenta,ya kuma biyo ta sautin gaisuwarta ya sanya lafazinta fita a rarrabe,amma hakan sai ya qarawa sautinta mai cike da quruciya kyau,sai ya dan lumshe idanunsa kadan yana amsawa
"Lafiya qalau" yana ganin fuskarta a yau ta sake zama ta manya fiye da ranar da ya ganta a gidan muhsin,a yau din ta dan sake zama babba kadan ba kamar ranar ba
"Sir.....me hoton ya gama dauka,saura na tsaye da wanda za'ayi muku da hajiya ummu saboda tarihi ko?"
Sam baima san zaman da tayi wai hoto akeyi ba,muhsin ya cuceshi,yanzun idan baiyi wasa ba kafin la'asar hoton ya riga rana fadawa cikin kafofin internet,ko a haka baisan yadda akayi labarin bikinsa ya karade duniya ba,ko ina ka duba tsakanin whatsapp twitter facebook da instagram zancan da akeyi kenan
"Dagota mana please,yanzu yanzu aka gama baka amanarta fa suna kallonka" suraj ya rada masa,no more option sai bata hannunsa da yayi
"Taso" ya fada yana kallonta,labbansa daya furta taso din take kalla,tsoro da mamaki fal idanunta,dama shima dan iska ne?,abinda take fada kenan a ranta,a gabansu ummun yake bata hannunsa?,bashi da kunya ashe shima?.
Bata gama wannan tunanin ba taji ya kama lallausan tafin hannunta,ba shiri ta miqe ta kuma zame hannunta da sauri hawaye suka fara taruwa a idanunta,lallai saita gayawa ummu abinda yayi mata,so yake ta mutu?,bayan ummu ta hanata tsaiwa kusa da kowa ma?.
_to masu karatu,gafa amarya widad mai cike da tarin wauta quruciya gata kuma goyon kaka,ba'a fara wasan bama,muje zuwa dai_ππ
ππ½
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*
Page 30
Anty deena ta ankara da yadda taketa narai narai da idanu,kadan take jira ta fara sakin ruwan hawayen nata,murya qasa qasa ta yadda ba wanda zaijisu tace
"Haba mana widad,so kike ummu ta gani hankalinta ya tashi?" Kai ta girgiza tana kallon idanun anty deena da golden eyes dinta
"Okay,maza hadiye,hadiye kinji qanwata" kai ta sake gyadawa,sannan aka fara daukan hoto.
Gaba daya ji yayi ya qosa ayi a gama,murya can qasa yace da muhsin
"Please muhsin,am tired wallahi" murmushi yayi,sau tari yana bashi dariya,bai taba ganin dan police wanda bai jure hayaniya ba irinsa
"Okay" ya fada yana dagawa widad hannu,a hankali ta qaraso wajen tana kauda idanunta daga kallon abbas,haka kawai idan ta kalleshi sai taji gabanta ya fadi
"Maza kusa ayi muku ku biyu" wani irin tsoro ya kamata,gabanta ya tsananta faduwa,sai ta narke cike da tsoro tana kallon uncle muhsin,wanda shi sam baima san me takeyi ba
"Matsa widad lokaci na qure musu" anty deena ta fada,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta fara takawa zuwa kusa dashi,nesa kadan dashi ta tsaya,saida mai hoton yayita magana da taimakawar gargadin da anty deena ke mata da idanu ta sake matsawa aka dauka
"Enough please" ya sake fada
"Dama ai an gama" suraj ya amsa wannan karon yana dariya,sallama sukayi dasu ummu,akwai yiwuwar su kwana a kano,duk da babu tabbas, uncle muhsin keson hakan,saboda akwai walima daya shirya musu.
Tun daga wannan lokacin gaba daya ta sake zama sukuku,ita gaba daya komai ya kwance mata,hakanan banbarakwai take kallon komai,daga qarshe dai a daki ta qule ta qarasa yininta,duk kuwa da sabgar da ake cikin gidan.
Da daddare kuwa bata yarda ta kwana da kowa ba sai a bayan ummu,kowa tsiyar ai dole su rabu yake mata,wannan ya sanya zuciyarta karyewa ta kuma soma kuka sosai,da qyar ummu ta rarrasheta.
********Washegari tun da safe anty madina ta aiko kiranta,tana sanye da dogon hijab da ummu ta fidda mata,ganin cewa a yanzun wani nauyi ya hau kanta,kuma gidan akwai 'ya'yan baffaninta maza,ga kuma baqi maza still 'yan biki da basu kai ga tafiya ba.
A kitchen ta taddata tana ta hidimar hada abincin safe,sai ta waiwayo tana kallonta
"A'ah,ya haka?,bakiyi wanka ba dama?" Baki ta turo gaba a shagwabe tace
"Anty madina duka duka yaushe garin ya waye?,kuma Allah an fara sanyi fa" rai anty madina ta bata sosai
"A'ah,daga yau sai yau,kada na sake gani,idan akace mace tana da aure da wuri take wanka ta gyara jikinta kinji ko?,ta fidda kayanta tayi kwalliya sosai" kai ta gyada a sanyaye,ita dai komai sai ace aure aure,duk an takurata da kalmar nan.
"Shiga dakina a hankali kada ki tada min abba,akwai turarenki da kika bari jiya saman mirror,ki dauka ki feshe jikinki sosai,sai kizo zan aikeki" amsawa tayi da to,don ita badai qauna da turare ba,ta wuce dakin anty madinan.
Ba jimawa sai gata ta dawo,tana ta zanga qamshi kuwa,ta nuna mata wani baske tace
"Dauki maza kikai sitting room din kawunnanki" ba tare data kawo komai a ranta ba ta amsa da to,ta dauki kwandon tayi ficewarta,tana tafe tana tsayawa magana da mutanen dake mata magana a hanya,cikin sauran baqi na gidan,har ta isa qofar setting room din.
Jim tayi tana duban baqin half cover din dake qofar setting room din,wanda keta sheqi
"Waye ma to a ciki?" Ta tambayi kanta,bata sani ba don haka ta tabe baki,cikin wannan d'arin d'arin nata da rashin sabo da maza ta saka kai ciki tare da yin sallama.
A lokacin kansa yana duqe a qasa,yanata trying number hafsat ce,wadda tunda ya taho basuyi waya ba,duk kiran da zaiyi sai ace masa is switched off.
A hankali ya daga kansa yana motsa labbansa tare da amsa mata sallamar,idanuwansa suka fada a kanta sanda take takowa kamar mai takatsantsan kada ta taka kwalba,baby face dinta dake tsakiyar blue black din hijab dinta ta fito fes,qananun gashinta masu santsi dake kwance gaban goshinta sun sake qawata fuskar,dan qaramin bakinta me red lips ta dan tsukeshi waje guda,fuskarta sam babu fara'a,sai ya lumshe idanuwansa kana ya maidasu qasa ga hannunsa inda wayarsa ke riqe,shidai baisan me hajiya ta hango ba data zabi ya auri qaramar yarinya har haka,kyau?....ko kuwa me hajiyan ta kalla?,shi kansa bai sani ba.
Tazarar wasu inches ta bayar a tsakaninsu ta ajjiye kwandon,tana daga tsugunne ta gaidashi da siririyar muryarta
"Ina kwana?"
"Kin tashi lafiya?" Ya amsa mata yana sake daga kanshi gareta a karo na biyu,bata amsa masa ba sai miqewa da tayi tsaye ta soma shirin ficewa a setting room din,saboda gaba daya a tsorace take,already ummu tayi mata horon tsoron maza sosai da shan inuwa daya dasu,a yanzun kuma bata gama sanin muhimmancin abbas din ba
Da kallo yabi bayanta,dariya ta taso masa can qasan ransa,ta yaya cikakkiyar budurwa mai shekaru da wayo ta aikata haka?,sai ya gyara zamansa kadan yana lalubo sunanta
"Widad" ya furta a tausashe,tsayawa tayi cak gabanta yana faduwa,dama yasan sunanta wai?,ta tambayi kanta
"Zo mana" ya sake fadi,abinda yasa ta waiwayo kenan,suna hada idanu duk wani kuzarinta yayi nasa waje,sai ta narke fuska
"Ummu zata yimin fada idan na dade" kai ya girgiza yana lumshe idanunsa kamar yadda yake a al'adarsa
"Ba zaki dade din ba,yanzun nan zaki tafi" kallonsa takeyi,sai ya jinjina mata kai alamun tabbatarwa,don haka ta dawo a hankali,ta samu nesa dashi ta zauna.
Tattara dukka hankalinsa yayi ya zuba mata idanu,yanzun ta ina zai fara mata bayani ma?da wanne harshe zai mata magana ta fahimci abinda yake cewa quruciya duk ta baibayeta?,a qa'ida babbar budurwa ce yanzun zaune a gabansa,sai yafi sanin yadda zai dinga handling abubuwa har su saba da juna.
Motsawa tayi kadan tana hade rai saboda yadda yake kallon nata ya sake takurata,ya fahimci haka sai ya aje wayar hannunsa,a bisa tilas ya arawa fuskarsa murmushi sannan ya fara magana
"Ummu ta gaya miki an daura miki aure ko?" Kai ta gyada tana kallonsa
"Good,daga yanzu na zama yayanki,na zama kuma abbanki,zamu tafi dake can zan kaiki gidana,zamu tafi tare,kema gidanki ne duka,zakiyi duk abinda kikeso a ciki,kina so?" Idanunta masu tsananin haske da ratsin gold color ta fara rarrabawa a tsakanin nasa idanun,sai ya kafeta da idanu sosai yana kallon yadda suke juyawa,yadda ta mele baki ta kuma tabe fuska hadi da lumshe idanunta,eye brows dinta masu tsayi suka hade waje guda sannan ta sake bude idanun warrrr a kansa yasa tsigar jikinsa ta zuba
"Bazan dade ba zaka dawo dani wajen ummu?" Ajiyar zuciya mai nauyi ya sake yana dan murmushi kadan
"In sha Allah,nima daga yau na zama yayanki ko?"
"Uncle dina dai ko?,naji nujood na cewa sunanka uncle abb...." Kasa qarasa sunan nashi tayi,tana jin kada tayi abinda bata kyauta ba,murmushi ya subuce masa ba tare da ya shirya ba,har fararen haqoransa suna bayyana,ya fuskanci nauyin kiran sunan nasa take
"Uhnnnn,uncle abbas" sai ta gyada kanta tana hade hannayenta waje guda,yakai duba ga hannun nata,tsararren jan lallen nan nata yana nan tas saman hannunta,ya zuba masa idanu kamar mai karnatar taswirar zane,lallai akwai hikima mai yawa ga masu yin lalle,har da suke iya tsara zane haka ya bada wani kala da nau'i mai kyau.
Rai ta hada sosai ganin yana ta kallon hannun nata, saita zare hannuwan nata zuwa cikin hijabin tana sake qudundunewa waje guda,ya dauke kansa yana maidawa ga dan qaramin leda yar mitsitsiya daya shigo da ita,sai ya dauka ya tura mata
"Wannan waya ce,ki cewa ummu a kunna miki,akwai komai a ciki,zan dinga kiranki,sauran kuma kudi ne,duk abinda kikeson siya ko kike son amfani dashi ki dauka a ciki,kada ki sake tambayar kowa yayi miki wani abu" murna farinciki da kuma mamakin bata waya da akayi ya lullubeta,to amma kuma tana tsoron kaiwa umnu kayan tace wani ne ya bata,duk yadda take zumudin wayar saita noqe
"Wallahi ummu zata dakeni,zatace waye ya bani" murmushin dole ya sake subuce masa
"Kice uncle abbas ne,idan ma bata yarda ba kice a kirani,bazata miki fada ba" sai ta matso kadan,ta dauki ledar tana cewa
"An gode,Allah ya saka da alheri" girma yaji addu'ar tayi masa,sai ya bita sa kallo kawai harta fice,ya maido dubansa cikin falon yana sauke gauron numfashi,tsahon zamansa da hafsa bata taba fadin haka ba,duk girman kyauta idan yayi mata
'An gode' shine iya abinda ta iya fade kenan,bata buqatar cin komai,so yake kawai yaga sun dauki hanyar bauchi,to amma babu dadi su kawo suga baici komai ba,gashi ya baro baqi a masauki,don haka ya fidda qaramin flask din tea dake cikin kayan,ya hada tea.
A gaggauce yake sipping,yana tsaka da kurba uncle muhsin yayi sallama
"Aah ya haka bakaci komai ba?" Ya fada bayan sun gama gaisawa yaga abbas na ajjiye cup din
"Sauri nake ne,ya kamata mu dauki hanya da wuri,saboda kamar gobe nakeson komawa kaduna,akwai gyare gyare da za'a yi acan,a office ma kuma ina da ayyuka da ban gama settling nasu ba bare na dora da nawa,ban taba aiki a kaduna ba sai wannan karon,kaga ina buqatar maida hankali na sauke nauyin al'umma dake kaina" kai muhsin ya jinjina
"Gaskiya ne,to shikenan,muje kayi sallama dasu saimu fita tare,zaka saukeni a al-hamsad tower zan shiga wani shago akwai abinda nakeson dubawa,zuwa azahar an kammala walima in sha Allah saiku wuce kafin la'asar"
Sai data gama nuqu nuqu da fargabar nunawa ummu kayan daya bata,da taga ba zata iya ba saita wuce sassan anty madina,ta sameta ta fito a wanka,don haka ta zauna cikinsu walid dake falo suna kallo harta gama shiryawa ta fito ta sameta
"Widad,har ya tafi baqon?" Kai ta gyada tana miqa mata ledar
"Wannan ya bani,sai da nace bazan karba ba ummu zatamin fada,yace wai ba zata min komai ba" dariya ta subucewa anty madina
"Taso nan" tace da ita bayan ta karba ledar,suka matsa gefe can inda yaran ba zasu jiyosu ba,zama tayi ta zaunar da ita a gefanta
"Shi wannan ai ba baqo bane yanzu,mijinki ne kin gane?,kamar ni da abban walid,kamar ummu da alhaji,kin gane?" Tadai jita,amma bata gane mai take nufi ba,ita kallon abban walid da anty madina takeyi a mazaunin yayanta ne,ummu kuma alhaji babanta ne
"Bari muga me miji ya baiwa matarsa kyautar farko?" Ta fada tana dariya,ta zazzage ledar,kwalin kyakkyawar waya qirar samsung ta fado hade da sabbin kudi a miqe fil dasu
"Lalalala,ah lallai wannan diya tamu da goshi take,tun yanzu?" Dariya ta kubcewa widad,haka kawia taji kunya ta kamata,saita sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta anty madina na tayata dariyar
"Zankadi,bude idonki ki gani" saita bude idon da sauri,ba qarya wayar ta hadu,take taji murnarta ta qaru,qaunar wayar kuma ta shigeta,suna shirin kunnawa momma tayi sallama falon
"Wa'alaikumus salam,qaraso momma,duk sun cika falon" anty madina ta amsa tana qoqarin tattare kudaden waje guda
"Wannan sabbin kudi fa,ko na liqi ne da kikayi canji?,aisai ki adana abunki,bikin da babu ko kidan qwarya bare DJ,kamar wata amaryar buzuzu"
"Uhmmm,momma kenan" anty madina ta fada tana dariyar yaqe
"Albarkar aure ai ake nema,bare widad ma nawa take?,ina qawayen ma bare ace za'a zauna yi mata irin wannan bidi'ar?,ni ban canzo kudin komai bama,angonta ne ya bata hade da wayar?" Sai a sannan idanunta yakai kan wayar
"Kai!" Ta fada cikin ranta,tasan wayar fes,irin wayar da deena tace yallabai(mijinta) ya kawo mata tsarabarta ne daga india a wannan satin daya dawo daga course daga can
"Tofa,da gamo da kasawa,kada fa muna nan mun shanya baki muna kallonta yarinya qarama amma ace har tasan komai,kodai ta bada wani abune aka bata wannan tukuicin haka?" Momma din ta fada tana kama baki, zuciyarta cike fal da qyashi da baqinciki,don ko yanzu data baro sassanta maganar da suka gama kenan da batulu matar babanta da 'yan uwanta da basu tafi ba,duka dai akan widad din,suna ganin komai anyi mata fiye dana 'yan uwanta,ana kuma wuce makadi da rawa a kanta saboda tana da daurin gindin ummu,sun manta kowanne aure da irin nasa nasabin yake zuwa,labarin lefe data samu,manyan mutanen da suka halarci daurin auren da kuma kayan da aketa hadawa za'a tafi jere dasu kawai sukeyi,banbamcin da ake nuna mata akan nasu 'ya'yan yayi yawa.
0 comments:
Post a Comment