GODIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon kafa alƙalamina domin rubuta wannan labari, ya ubangiji ka haneni rubuta ba dai-dai ba, ka bani ikon rubuta abun da al'umma zasu anfana da shi.
SADAUKARWA
GARGADI
Wannan labarin ƙirƙirarren labarine, na yi shi ne dan dan samun takardar Digiri a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ban yarda wani ko wata su juyamun labarina ko su ɗoramun a wata manhaja ba tare da izini na ba ko su siyar mu da labarina ba saboda haƙƙinane basirata ce saboda haka don Allah a kiyaye.
12:00am
Agogo ya buga dai dai lokacin da wata yarinya ƴar kimanin shekara Sha huɗu ta fito daga wani ɗaki ta nufi ɗakin da ke kallon na ta, kallo ɗaya zaka ma yarinyar ka fahimci irin sangartattun yaran nan ne da ba'a kwaɓa musu, kofar ɗakin ta tura tana faɗin, "Momy ina jin yun..." maganar ta ne ta maƙale sakamakon ganin Mahaifiyar ta kwance cikin jini, ga kuma Kakar ta riƙe da wuƙa a hannun ta ya na ɗigar jini, nan da nan jikin Hajiya kaka ya fara rawa ta yar da wuƙar tana faɗin, "wallahi bani na kashe ta ba Aneesa ki yarda da ni.!
Hajiaya Kaka ta ƙarishe maganar cikin tsananin tashin hankali, ta nufa in da Aneesa ta ke tsaye tamkar an dasa ta, ganin Kakar ta nufo ta ne ya sa tayi firgigit ta nufi gawar Mahaifiyar na ta tana sakin wani irin marayan kuka mare sauti, shikenan Kaka kin kashe min mahaifiya kin ji daɗi dama kin dade kina ikrarin sai kin kashe Momy,! to kin kashe ta kaka kin huta, na ce kin huta ta bar miki duniyar, ki tattara dukiyar kiyi yadda kike so, kuma wallahi ki sani yau ba sai gobe ba zan kai ƙarar ki saboda duniya ta san me kika aikata."
Aneeesa na gama faɗin haka ta kama hanya ta fice daga ɗakin, in da take jin zuciyar ta gaba ɗaya ta bushe, kawai ɗaukar fansa ce a ran ta.
Durƙushewa kaka tayi a gurin tana faɗin, "Kaico na ni Hajiya Hindu mai na aikata kenan, yanzu duk duniya ba wanda zai yarda cewa bani na kashe Saudat ba.!
Kuka sosai Hajiya Hindu takeyi tamkar ranta zai fita ga wani irin tsoro da ya dirar mata.
Tafiya take tamkar mahaukaciya kafafun ta ba ko takalmi kanta ba ko ɗankwali burin ta kawai ta isa police station ɗin da ke bayan layin su a zo a kama kaka kafin ita ma ta kashe ta tamkar yadda ta kashe mata mahaifiya, tana isowa kofar get ɗin police station ɗin ta fara bugawa tamkar mahaukaciya, iya ƙarfin ta tana bugawa tana kiran police, da gudu wani ɗan sanda ya futo riƙe da bindiga yana faɗin, "waye yake bugamana get kamar zai karya.?
"Nice nan Aneesa ƴar gidan Commisioner, ƙara na kawo.!
Ta ƙarisa maganar tana ƙara fashewa da kuka, binta da kallo ɗan sandar yayi tamkar yana nazarin wani abu game da ita, sai can ya ce ma ta, "mu shiga ciki ƴan mata, bin shi tayi har zuwa office ɗin ogan su, suna shiga ya sara ma oga ya ce mai, "sir wannan yarinyar ce ta zo mana a ruɗe kuma tana wani magana da ban fahimce ta ba shiyasa na kawota gurin ka domin alamu ya nuna cewa ba a hayyacin ta take ba, ko gama rufe baki bai yi ba Aneesa ta tari numfashin shi tana faɗin, "wallahi ranka ya daɗe ina cikin hayyacina, ƙaran kaka ta na kawo ta kashemun mahaifiya yanzu haka tana can kwance cikin jini, kuma da ido na na gan ta yallaɓai.!
Ta ƙarasa maganar tana mai fashewa da kuka mai tsuma xuciyar mai sauraro.
"What! haba ƴan mata taya za'ayi ki ce kakar ce ta kashe miki mahaifiya, yanzu ina ita kakar ta ki da gawar Mahaifiyar ta ki.?
"Wallahi yallaɓai da gaske nakeyi da idona na ganta, yanzu haka tana gida na kulle gidan don kar ta gudu.
'Officers ku je da ita ku tabbatar kunyi bincike sosai sannan a kamo ita wacce ake tsargi ɗin."
"Haba yallaɓai wani irin zargi in ce ma a idona ta kashe mun mahaifiya ka ce tsargi.
"Karki damu ƴan mata binciken mu shi zai tabbatar da haka ai.
Wane yayi kisan?
Sir ya kamata a rubuta startement akan case ɗin ta don magana ce mai girma, kuma case ce ta cikin gida."
"Eh kofur ka kawo shawara, kuje da ita ku rubuta startement ɗin sai ku ɗibi yara ku tafi."
Ƙamewa yayi ya sara mai haɗi da faɗin cewa, "Ok sir."
Ficewa sukayi da Aneesa sukaje kan Kanta aka rubuta startement sannan baki ɗaya suka dunguma suka shige mota suka saki jiniya sai gidan Commisioner.
*************************
Hajiya Kaka gaba ɗaya ta haɗa zufa jikinta ba in da bai rawa, tayi da na sani yafi a ƙirga tasan tabbass yau asirinta ya tonu kuma tasan in duk duniya zasu taru ba zasu taɓa yardan cewa ba ita tayi kisar nan ba domin Aneesa ta kamata dumu-dumu.
"Wayyo ni Hajiya Hindu na bi shawaran zuciya na biye ma son rai na gashi ina da na sani.!
Bata gama rufe baki ba taji jiniyar ƴan sanda nan da nan taji cikin ta ya juye, domin Hajiya kaka duk bala'in ta akwaita da tsoron ƴan sanda, bata taɓa sanin ƙiyayyar da jikan nata take mata ya kai haka ba sai yau, ba ta gama dawowa duniyar tunanin da takeyi ba taji ana faɗin, "officer gata can ita ta kashemun mahaifiya."
A gigice Hajiya Kaka ta ɗago kai fuskarta shaɓe-shaɓr da hawaye da majinu, hannunta kuma duk jini ta fara faɗin, "wallahi ranka ya daɗe bani na kashe ta ba, zuwa nayi na ganta a cikin wannan halin ni kawai taimakon ta na zo yi in cire wuƙar, ku yarda da ni.!
"Ke tsohuwa ki mana shiru, in mun je can office zaki mana bayani Jenet. ya kira sunan wata police da take daga bakin ƙofa.
"Yes Sir.
"Arest her, in mun je can tayi mana bayani."
"Ok sir"
Jenet ta faɗa tana ƙarasowa gurin Hajiya kaka, fuskar ta a murtuke ta daka ma kaka tsawa tana faɗin, "ban hannunki tsohuwa a haka kamar mutuniyar kirki, ta ƙarasa maganar tana sama kaka ankwa a hannun ta tuni Kaka ta fara sakin fitsari, haka suka tasa kaka aka bar daga Aneesa sai wasu police guda biyu.
Kafin Safe tuni labarin mutuwar Hajiya Saudat matar tsohon Commisioner lafiya na jaha ya karaɗe jihar Kaduna, mutane da yawa sun girgiza da mutuwar Hajiya Saudat, mace mai tausayi da taimakon al'umma, tuni mutane suka fara tsinema kaka da Allah wadai da abun da ta aikata.
*************************
WASHE GARI
Gidan Alhaji Mubashir Mai lafiya ya cika da al'ummar Annabi, in da dangi da ƴan uwa da abokan arziki suka cika gida har da maƙota, in da jimami ya zama biyu ga jimamin mutuwa ga na tsargin Mahaifiyar maigidan da akeyi da kashe matar gidan, mutane da yawa wasu ba gaisuwar ta kawo su ba gulma suka zo yi.
daga dare zuwa safe gaba ɗaya Aneesa ta fita hayyacin ta, tayi kuka har ta ba uku lada, a gaban ta aka ma mahaifiyar ta wanka aka mata sutura, sai da aka jira ƴan uwan Momy suka zo daga Taraba kasancewar ta ƴar can, sunyi kuka haka wata ƙanwar momy ta rungume Aneesa suka cigaba da kuka gunin ban tausayi, haka aka ɗauki gawar Momy bai bar fitar da jini ba, dubban ɗaruruwan mutane ne suka sallaci gawar ta kowa na faɗin halinta nagari ya bita.
1:30pm
POLICE STATION
Cincirindon mutane ne suka taru a bakin police station ɗin suna faɗi, "ba zamu yarda a bamu tsohuwar nan mu kashe ta kawai.! Gefe guda wasu kuma na faɗin we need justice for Hajiya Saudat.
Hajiya Hindatu Mai lafiya ita ɗin mata ce a gurin Alhaji Usman Mailafiya wanda aka fi sani da Alhaji Mailafiya sanannen mutum ne a garin Kaduna in da ya kasance mutum ne mai taimakon talakawa da gajiyayyu da marashi, kuma shi mutum ne mai matuƙar haƙuri da kawaici da kauda kai, sabanin matar shi da ta kasance mace ce mai matuƙar jin kai da ɗagawa gata bata da haƙuri ko na minti guda, gata kwata-kwata bata so ta ga wani ya raɓi mijina hatta ƴan uwan shi ta rabashi da su, duk da kasancewar Auren haɗi akai musu domin da mahaifin shi da mahaifinta wa da ƙani ne, amma hakan bai hata tana wulaƙanta ƴan uwa ba, in har kai ka kasance baka da arziki a cikin dangin to ko ka zo in da take kallon banza ke rabata da kai sosai tayi bakin jini a cikin dangi baki ɗaya ba wanda zakiji ya faɗi alkairita sai sharrinta, ita ko Hajiya Hindu ko a jikinta, saboda duk yawancin zaman su sunfi yi a Abuja kasancewar mijin ta babban mai muƙamine kuma ɗan siyasa ne da ake gogawa da shi a wannan lokacin, hakan ya sa Hajiya Hindu haɗuwa da matan manyan masu faɗa aji a gwamnati nan da na idon ta ya ƙara bushewa, in dai kaga Hajiya Hindu na harka da mutum to kin kasance ke wata ce, duk wani ragama na Alhaji Mailafiya Hajiya Hindu take juyashi, gashi har lokacin Allah bai basu Haihuwa ba kusan shekaran su biyar da Aure hakan yasa Alhaji ya fara tunanin ƙara aure, saboda dangi na ta ƙorafi akan haka ana cewa ya ƙara aure, lokacin da Hajiya Hindu ta ji batun ƙarin Aure hankalinta ya tashi matuƙar gaske haka ta shiga ta fita har sai da aka fasa wannan aure, haka Alhaji ya dunga neman aure amma sai abu ya kankama sai abun ya lalace, kwatsam sai Hajiya Hindu ta tafi wani taro da Matar shugaban ƙasa ta gayyacesu zuwa UK kuma zasu ɗauki tsawon wata uku, bayan tafiyar ta da sati ɗaya Alhaji Mailafiya yayi aure kuma budurwa ya ɗauketa suka tafi Dubai honey moon sosai suka gurci amarcin su ranar da suka dawo ranar Hajiya Hindu ta sauka ƙasar cike da shauƙi da kewar mijin ta kasancewar tana tsananin son mijin nata haka yasa ta kirashi ta faɗa mai cewar gasu sun iso Nigeria tana Abuja amma yanzu zata taso zuwa kaduna, kasancewar tun kafin ta zo tayi booking ɗin jirgi zuwa kaduna, sosai hankali Alhaji ya tashi domin yasan tabbas ba zaman lafiya in har ta san mai ya aikata na yi mata kishiya da yayi ya munafurce ta.
Jirgin su na sauka ta fito tana wara ido ta ina zata ga mijin nata kuma abun ƙaunar ta, can ta hangoshi jingine da mota, gabanta ne ya faɗi ganin irin kyau da wani haske da ya ƙara, da sauri ta ƙariso gurin shi ta rungumeshi tana faɗin, "i miss u hayaty."
"Miss u too wify, ya hanya, gaskiya Uk ɗin nan ya karɓeki kinga in da kika ƙara kyau kuwa."
"Kai Hayaty har na kaika, don bakaga yadda kake kyalli bane tamkar wanda yayi sabon aure."
Gaban shi ne yaji ya faɗi jin abun da ta faɗa, gaba ɗaya sai yaji ya ruɗe, da kyar ya tattaro natsuwar shi tare da zareta daga jikin shi ya buɗe mata mota bayan ta shiga ya rufe, ya zaga ya shiga ya tada motar nan da nan sauran motocin securityn shi suka rufamusu baya, tun da suka iso gida taji gabanta na faɗi, cikin damuwa ta dubi mijin nata ta ce mai, "Minie naji duk jikina yayi sanyi tamkar wata ta raɓeka, ko wani abu ya faru bayan bana nan, duk da zumuɗin da nake in kariso gareka in faɗa maka wani albishir amma sai naji murna na ta koma ciki."
"Haba Wify karki ɓata mana farin ciki mana kin san yadda nake son farin cikin ki kuwa."
Haka dai Alhaji mailafiya ya cika Hajiya Hindu da daɗin baki har suka shiga falon ta, tun daga falo ta fara nuna mai tsantsan kewar shi da tayi, tuni suka fara faranta ma juna rai da soyayya mai tsayawa a ran ma'aurata a haka har suka shige cikin bedroom sosai suka faranta ran juna su na tsawon watannin da basu tare basu suka samu kansu ba sai yamma domin a ɗaki suka ci abinci sukayi sallah sosai ya bata lokacin shi a wannan rana a haka suka kwana suna faranta ran juna in da take faɗa mai tana ɗauke da ciki na tsawon wata uku tun bayan tafiyar ta da kwana biyu ta fahimci haka da taje Asibiti likita ya ƙara tabbatar mata da hakan, sosai Alhaji mailafiya yayi farin ciki take ya shiga mata kyaututtuka na musamman, haka ya ɗauketa suka fita tuni ya mance da zancen wata Amarya ita ko Amarya tana can tana zuba ido ta ga Alhaji ya dawo amma shiru, wasa-wasa sai da akayi sati biyu bata sa Alhaji a ido ba sai a sati na biyu ya shigo sashin ta, "haba darling yau kimanin sati biyu kenan rabon da in saka a idona na kira wayar ka kwata-kwata bai tafiya."
Amarya ta ƙarasa maganar cikin shgwaɓa da bata rai.
"Haba amaryata afuwan wallahi wani tafiya ya taso mun cikin gaggawa na tafi ban faɗa miki ba amma yanzu gani ai na daw..! Maganar ta shi ne ta maƙale lokacin da yayi tozali da Hajiya Hindu a gaban shi tamkar an jefota tana wani irin huci.
Sosai Mutane suka cika police station ɗin, ƴan sanda sai tura mutane suke suna faɗin, "ya isa insha Allah akwai hujjoji da muke tattarawa da zaran mun kammala zamu miƙata kotu alkali ya yanke mata hukunci dai-dai da abun da ta aikata."
Da ƙyar police suka shawo kan mutane suka hakura don wasu ma sunƙi tafiya sai da suka fara watsa musu tiyagas suna harbin bindiga sannan mutane suka fara guduwa.
************************
WASHE GARI
"Hajiya ni ce lawyer ki wacce zan kareki saboda haka nake so ki faɗamun gaskiyar duk abun da ya faru, karki ɓoyemun komai."
Dago ido Hajiya tayi, idon ta yayi luhu luhu ga damuwa ga rashin barci, gaba ɗaya duk masifar hajiya amma tayi sanyi sosai, kamar ba ita ba ce wannan Hajiya ƴar gayu mai isa ga gadara da masifa da dukiya ta taka duk wanda take so, ta sha sawa ana tsare mutum akan laifin da bai taka kara ya karya ba, wai yau ita ce a cikin wannan hali, tabbass rayuwa juyi-juyi ce kwaɗo ya faɗa a ruwan zafi.
"Hajiya kina jina kuwa.?
Cewar Barister Khasheefa, firgigit Hajiya tayi ta fara girgiza kai tana faɗin, "Barister banƙi taki ba amma ki barni kawai a yanke mun hukuncin da ya dace, don in duk jikina bakine ba wanda zai yarda ba ni na kashe Hajiya Saudat ba."
"Hajiya kiyi haƙuri ki faɗamun me ya faru a dare, bai kamata ki sare haka ba, ni na miki alkawarin in dai har baki da hannu a kisar nan zan yi iya ƙoƙarina ganin na kwato miki hakkin ki insha Allah."
"Wallahi Tallahi Barister ba ni na kashe ta ba, duk masifa ta da bala'ina ba zan taba iya kashe mutum ba, ni dai abun da na sani kawai shine ranar da zata mutu da daddare ta zo ɗakina ta sameni in da ta gaidani ni kuma dama tun farko ba son ta nakeyi ba tun da ɗana ya aure ta na ɗauki karan tsana na ɗora mata a kullum tsakanina da ita mugayen furuci ne da hantara, sai dai bata taɓa daga kai da sunan ramawa ba kullum cikin mun biyayya take saboda ita macece mai haƙuri da kawaici ga uwa uba tarbiya, bayan ta gama gaidani duk da ban amsa ba ta nemi guri ta zauna ta ce mun dama ta zo ne muyi wata magana game da rabon gadon Mijin ta da za'ayi gobe akwai wani sirri da ya kamata ta faɗamun duk da Alhaji ya ce ko bayan ba ran shi kar in sake in tona wannan sirrin amma ya zama dole in bayyana hakan ko da Alhaji zai samu salama a cikin ƙabarin shi, har ta gama magana ban tanka mata ba ina rike da wayata ina latsawa haka ta tashi jiki ba kwari ta tafi, bayan tafiyar ta da kamar awa uku na kwanta nayi wani mummunar mafarki wai gashi Saudat na bina da wuƙa hakan yasa na tashi a firgice na nufi ɗakin ta zuwana ɗakin kenan na ga Saudat na juye juye da wuƙa a cikin ta gaba ɗaya na ruɗe kawai sai na riƙe wuƙar na zare dai dai da shigowar Aneesa, kuma yayi dai dai da mutuwar Saudat, wannan shine abun da ya faru ban da shi ban san komai ba game da mutuwar ta."
Kaka ta ƙarisa maganar tana zubar da hawaye tamkar famfo, nisawa Barister tayi ta ce, "karki damu Hajiya insha Allah na miki alkawari sai in da karfina ya ƙare sai an binciko wanda ya aikata kisar nan, na barki lafiya insha Allah in da wasu tanbayoyin ko wani abu da ya kullemun kai zan zo in sameki."
"Insha Allah ni kuma zan faɗa miki gaskiyan abun da na sani."
*************************
KWANA BAKWAI DA MUTUWAR HAJIYA SAUDAT.
Yau akayi addu'an bakwai in da daga ranar da akayi mutuwar zuwa ran da akai bakwai ɗin Aneeesa gaba ɗaya ta zabge ta fita hayyacin ta ko abinci sai ƙannin Momy sun sata a gaba take ci, kullum kuka shine aikin ta, yau ta kama bakwai bayan anyi cincirodan addu'an bakwai daga masalatai zuwa gidajen radio da makarantun islamiyu sai aka taru da ƴan uwan daddy da na momy suka ce to yanzu suna so a basu Aneesa su tafi da ita, su zauna a gurinsu tana ɗebe musu kewar ƴar uwar su, dangi daddy da kyar suka amince, sai maganar raba gado aka ce a bari har sai an ga yadda shari'a ta kaya kura ta lafa sai a raba, kowa ya amince da shawarar da aka yi, a ranar kowa ya watse aka rufe gidan, mutuwa kenan mai yankar ƙauna yau gashi tayi ma Aneesa yankar ƙauna ta raba ta da mahaifan ta, da ta waigo ta kalli gidan sai ta ƙara fashewa da kuka, haka Addah Mariya ta rungumeta a jikin ta tana lallashin ta.
Wani irin kallo take jefa mai, gaba ɗaya ta fita hayyacin ta idon ta sun sauya kala, ji take tamkar zuciyar ta zai faɗo gani take tamkar mafarki takeyi wai yau ita ce Alhaji ya ƙara ma kishiya, kishiyar ma budurwa, aiko yau akwai ƙaramin yaƙi a gidan nan, juyawa tayi ta kalli yarinyar da Alhaji yake kira da Amarya kallon tsaf tai mata tun daga sama har ƙasa, kwata-kwata ma wannan yarinyar batayi kala da matan da zata iya zaman kishi da su ba.
Gefe guda kuma Alhaji Mailafiya ba in da jikin shi bai rawa duk da Ac da ke fallon bai hanashi haɗa zufa ba, da sauri ya ƙarasa kusa da Amaryan shi ya tare tsakanin ta da Hajiya Hindu don yasan tabbas komai zai iya faruwa, wani kallon baka da hankali ta ma Alhaji nan da nan ya ƙara duƙar da kai.
"Ki faɗa mun ko nawa kike so zan baki matuƙar zaki rabu mun da mijina domin mijina wa ni ƙaɗai aka halicce shi, kai kuma sannu ƙasurgumin munafuki maci amana har ni zaka ci amana ko, to wallahi tallahi sai ka san ka ci amanar Hindu, kuma na rantse da Allah sai ka saki matar nan yau ba sai gobe ba, ke kuma na baki zaɓi ko ki rabu mun da miji ta salama ko kuma ki rabu da shi ta tsiya shawara ya rage na ku."
Tana gama maganar ta ta juya hankali tashe ta fita.
"Alhaji dama kasan matar ka ba tasan zakayi aure ba ne ka auro ni,? gaskiya na tsorata da yanayin matar ka, kuma na tabbata zata iya yin komai a kan ka, don Allah ka bar da ni gidan nan kar ta illatani da abun da ke cikina."
Haseena ta ƙarisa maganar tana mai zubar da hawaye, gaba ɗaya sai jikin Alhaji mailafiya yayi sanyi ya rasa ma mai zai ce, fita yayi zuwa garden ɗin da ke cikin gidan ya zauna a cikin wasu kujeru yana jingina kan shi haɗi da lumshe idanun shi.
"Hello Hajiya Jamila kina ji na kuwa,? ina cikin tashin hankali wai tafiyar nan da nayi Alhaji kishiya yaje ya ƙaromin, don Allah in kina da lokaci ki fito kawo ki jirani zan zo in ɗaukeki mu tafi gurin boka zalumu ai ba haka mukayi da shi, ok tom gani nan zuwa, eh yanzun nan ma."
Ajiye wayar tayi ta nufi bedroom ɗin ta drower ta buɗe ta ɗebo kuɗi bandir ɗin ƴan dubu dubu ta zira a jaka ta ɗauko key ɗin mota da mayafi ta fice zuwa haraban gidan.
Tafiyar awa ɗaya sukayi sai gasu a bayan dutsen madarkaci can nesa suka ajiye motar ta su suka fara takawa da kafa har suka isa dai dai wani kogo da ke jikin dutsen da baya da baya suka shiga, wani tsamurarren mutum ne a zaune a kan wani buzu jikin shi ba kaya sai ganye da ya ɗaure a ƙugun shi.
"An gaida la'anannun bil'adama, an gaida wa'inda basu da raban rahman ubangiji, an gaida ɓatattu iyalan shaiɗan, nasan duk abun da ke tafe da ku, tabbass kinyi sake tun da har mijin ki ya riga yayi aure kuma har da rabo a tsakani, domin tana ɗauke da ciki na tsawon sati takwass ɗa namiji ne a cikin, sannan in har kika sake ɗan nan ya zo duniya sai ya fi ɗan da zaki haifa ɗaukaka, gashi mun duba munga dole sai ya zo duniyar, kuma mijin ki ba zai taɓa sakin ta ba, hanya ɗaya ce kawai mafitar ki shine za'a haukata ta tabi duniya, kuma za'a shafe ma kowa tunanin ta har abada, kin amince ko a'a.?
"Eh! eh! boka na amince ni in dai zata fita a rayuwar mijina kome za'ayi ayi kawai taje can takarata ta haifa cikin a yawon haukanta."
"Hahahahahaha tabbass ki cika la'ananniya tabbass aiki anyi an gama ku ta shi ku tafi tanbaɗaɗɗu watsattsu hahhhahah."
Jiki na rawa suka miƙe ta ajiye mai rafar kuɗi a wani ƙoƙon kan mutum suka fara tafiya da baya da baya suna rawa har suka fita daga kogon, suna fita gurin ya koma ya shafe tamkar ba kowa.
*************************
Washegari Haseena tana zaune a falon ta kawai ta ji tamkar ana kiranta haka ta tashi ta fita ba takalmi balle mayafi, lokacin kuma dai dai lokacin salar Azahar ne duk an shiga masallaci har ta fita daga gidan ba wanda ya ganta, tun daga wannan rana kowa ya mance da ita ba wanda ya ƙara tunawa da ita, sosai Hajiya Hindu ta ƙara miƙe ƙafa tana rainan cikin ta yau basu Dubai gobe basu Saudiya jibi suna ingila, haka suka dunga yawo har lokacin Haihuwar ta ya zo, suka tafi ƙasar India a can ta sankato ɗan ta kyakkyawa irin shi ɗaya da mahaifin shi, farin ciki tamkar ya kashe Alhaji Mailafiya washegari suka iso Nigeria kafin ka ce mai gida gabaɗaya ya cika da dangi da abokan arziki, haka Alhaji mailafiya ya dunga kyauta tamkar bai san zafin kuɗi ba.
Ranar suna ta zagayo aka sama yaro suna Mubasshir, tun daga lokacin Hajiya Hindu da Alhaji mailafiya suka ɗauki son duniya suka ɗorama yaronsu.
Shekaru na tafiya rayuwa tana shuɗewa muna ta cin kwanakinmu kwanci ta shi bai da wuya agurin ubangiji har gashi yau shekaran Mubasshir tara a duniya in da duk wani halayen shi na mahaifin shi ya ɗauko kuma shi yana matuƙar san dangin shi hakan yasa suma dangin suke son shi sosai, kuma hakan ba ƙaramin ƙona ma Hajiya Hindu rai yakeyi ba, don ita ba ta so yana hulɗa da dangin su, saboda duk dangin su mijin ta yafi kowa arziki, shiko Mubasshir bai son halin maman na shi ko kaɗan.
Zaune yake a tanƙasheshen falon su yana rubutu, sai ga mai kula da shi ta shigo tana faɗin, "ƙarami Alhaji ga tea ɗin da ka ce in haɗa ma.
Ɗagowar da zai yi kawai ya bige kofi da kanshi gaba ɗaya tea ɗin ya zubo mai a jiki dai dai Hajiya Hindu tana saukowa daga sama, wani salati ta saka haɗi da kwaso gudu.
Rufe ƴar tsohuwar tayi da duka ko ta ko ina tana faɗin cewa, "kashe mun yaro zakiyi da zaki ƙona shi da ruwan zafi.!
"Momy ya isa haka! haba momy wannan tsohuwar a haife ta haifeki amma ki rufe ta da duka, bafa da sanin ta bane, kuma ni na bige kofin nan, kuma tea ɗin ba wani zafi ai ya huce."
Yana ƙarasa maganar ya ƙarisa gurin tsohuwar da take durƙushe a ƙasa ta kasa ɗagowa saboda irin dukan da hajiya Hindu tayi mata ga kuma jikin tsufa, "Kaka ki tashi kinji ki yi haƙuri don Allah laifi na ne."
Ya ƙarisa maganar ya na ruƙo hannun tsohuwar ta miƙe da kyar suka nufi sashin su na masu aiki suna shiga ya ga Saudat tana zaune tana wasan ta hankalin ta kwance da gudu ya saki Kaka ya ƙarisa gurin Saudat ɗin yana faɗin Cutie wasa kikeyi, ki zo muje part ɗin mu muyi wasa da kayan wasa na kin ji.
"A'a ni ba zanje ba inna je momyn ka zata bigeni," yarinyar ta ƙarasa maganar ta cikin gwaranci, tsohuwar ne ta ƙariso ta ce ma Mubashir, "ƙaramin alhaji ka koma sashin ku kar momyn ka tayi ma faɗa, kuma kaga ma rubutu kakeyi ka je ka ƙarisa."
"A'a ni wasa zamuyi nida Cutie."
"Daddah ki barsu suyi wasan su ba'a raba yaro da yaro ai."
"Malam kasan halin uwan yaron nan yanzu sai ta zo tayi mana tijara ta kan hakan."
"Eh duk da haka ki kyalesu suyi wasan su.
************************
Shekaru sun ja rayuwa na daɗa tafiya, yayin da Alhaji mailafiya ya ɗauki Saudat tamkar ƴar shi saboda kawai son da Mubasshir yake mata, hakan yasa har makaranta tare aka sa su, gefe guda kuma hajiya Hindu ta ɗauki karan tsana ta ɗora ma Saudat da iyayen ta wanda asalin su ƴan Taraba ne zamane ya kawo su kaduna har alhaji ya ɗauki Baffan Saudat aiki ita kuma matar shi sai ya ce ta dunga kula da Mubasahir tun da ita hajiya Hindu ba ta cika zama bane ba ta Abuja bata kaduna, yaran Dadda shida ne duk mata ne, kuma suna aure ne a can Taraba dukansu suna auren masu hannu da shuni ne kuma ba abun da suka ragi iyayen su da shi, sai dai shi Baffa mutum ne wanda yake dogara da kan shi, bai jiran wani ya bashi hakan yasa ya ke aiki a gidan Alhaji mailafiya a matsayin driver, duk da ƴaƴan shi kwata kwata ba sa son wannan aikin, Saudat ita ce Auta a gurin su hakan ya sa yayyin ta da iyayen ta suke matuƙar son ta, Autan Baffa suke ce mata.
Kwanci ta shi ba wuya a gurin ubangiji yau gashi Mubasshir ya gama secondry school in da Saudat take aji ukun secondry, sosai soyayya ya shiga tsakanin Saudat da Mubasshir mutane da yawa ana ɗauka ƙanwar shi ce don komai tare sukeyi, hankalin Hajiaya Hindu yayi matuƙar ta shi har gurin boka zalumu ta koma ya tabbatar mata da baza'a taɓa iya raba Saudat da Mubasshir ba in dai aka rabasu tabbas zai iya mutuwa, tun daga lokacin Hajiya Hindu ta ƙara ninka tsanar da take ma Saudat hatta iyayen ta bata kyale ba, tuni ta matsa sai an kai Mubasahir ƙasar waje karatu ita a tunanin ta zata rabasu ta haka, bata san cewar tun bayan gama makaranatr Mubasshir Alhaji mailafiya ya nema mai Auren Saudat a gurin Baffa tuni Baffa ya bashi kuma, auren ya kasance ba wanda ya sani tsakanin Daddah da Hajiaya Hindu iyakan maza da dangin kawai suka sani sai shi Mubasshir ɗin don ko ita Saudat ɗin bata sani ba, sosai ake shirin tafiyan Mubasshir karatu ƙasar India in da zai karanci aikin likita a bangaren mata ranar da ana gobe zai tafi da daddare ya kira Saudat ɗakin shi bayan ta zauna ya fara magana, "cutie ki riƙemun amanar kan ki karki manta duk duniya baki da masoyi sama da ni, ba zan taɓa yafe ma kaina ba matuƙar kika kula wani, domin ke ɗin mallakina ne."
Tuni ta fashe da kuka ta rungume shi tana faɗin "Hamma na zuciyata taka ce mallakin ka ne komai dadewa duk runtsi duk wuya ba zan taɓa dena son ka ba."
"Rungumewar da Saudat tayi ma Mubasshir shine silar komai na kaddarar su, abun ka da lafiyayyen Namiji wanda yake kan gabar tashan balaga a lokacin tuni labari ya canza gaba ɗaya ya ɗauke wuta a tare wani bakon al'amari ya ziyarce su, take ya kasa haƙuri ya fara yawo da hannun shi a sassan jikin ta tuni suka fara aika ma juna sako da salo na irin wanda suka dade suna muradin juna, gaba ɗaya sun kasa control ɗin feelling ɗi da ke tattare da su, gaba ɗaya saudat ta gama narkewa a jikin shi inda tuni tufafin da ke jikin su sukayi ƙaura, haka suka cigaba da aika ma juna da sako mai narkar da zukatan masoya, tuni mai aikuwa ta auku a tsakanin su in da gaba ɗaya Saudat ta fita hayyacin ta tun tana kuka tana kaima Mubasshir doka har ta koma ajiyar zuciya, sai da komai ya lafa ne Mubasshir ya tuna da abun da ya aikata a ruɗe ya ɗauke ta ya nufi banɗaki da ita ba abun da takeyi sai binshi da kallo da kyar ta iya buɗe baki ta ce mai, "Hamma mai yasa ka aikata mun haka, ko a mafarki ban taɓa tunanin zaka iya karɓa abu mafi daraja a tare da ni ba tare da an ɗaura mana aure ba, yanzu fa zunubi muka aikata Allah na fushi da mu, kasan abun da ya mu'allim ya faɗamana lokacin da yake mana karatu ya ce wutan mazinata da banne wayyo Allah na kaicon mu ina tarbiyar da aka daɗee ana bamu."
Tana gama faɗan haka ta fashe da kuka ta fara kai ma Mubasshir duka in da shi kuma ya tsaya ya kasa hanata ko yin mata magana domin ji yakeyi in ya buɗe baki ya ce zaiyi magana kuka zai yi, haka dai ya dage ya mata wanka ya gasata da kyau yasa tayi wankar tsarki shima yayo wanka a daddafe saboda wani zazzaɓi da yake neman rufeshi, haka ya lallaɓa saudat ya rakata zuwa sashin su sai da ya tabbatar ta shiga ɗaki ba wanda ya ganta sannan yayi ajiyar zuciya ya koma bangaren shi, tun da ya kwanta juyi kawai yakeyi ya kasa barci ga zazzaɓi da ya lulluɓeshi da kyar ya tashi ya ɗauko first aid box ɗin shi ya dubo magani ya sha ya koma ya kudundune a kan gado da kyar barci ya ɗaukeshi cike da mafarci ƴar amaryar shi da fara more sadakin shi tun kafin a kai ko ina, gefe guda kuwa Saudat kwana tayi tana kuka da nadamar abun da ta aikata, gani take shikenan yanzu da kyar Hamman ya yarda ya aure ta don ta sha jin ƙawayenta na labari akan cewa in har kika yarda namiji ya sanki kafin aure to ba zai taɓa auren ki, shikenan ita yanzu ta kaɗe in ya ce ba zai aureta ba mai zata ce ma mijin da ta aura game da budurcin ta tana tuna haka sai ta ƙara fashewa da kuka, kafin safe tuni fuskarta ya kunbura yayi jajir abunka da farar fata ga zazzaɓi mai zafi.
WASHE GARI
Karfe shida na safe jirgin su Mubasshir ya daga sai India, in da kafin ya tafi ya shigo har sashin su Saudat tana jin muryan shi sai ta ƙara rufe ido tamkar mai barci haka ya daɗe yana tsaye yana ƙare mata kallo sannan ya ciro wani zoben dimon a aljihun shi ya kama hannunta ya sa mata ya duƙa ya sunbaceta a goshi ya fice da sauri yana share kwallar da ke idon shi, a airpot suka haɗu da momyn shi ta kammala mai komai suna isowa shi da daddyn shi aka fara kiran matafiya tuni jirgin su ya daga sai India.
*************************
BAYAN WATA UKU
Saudat ne take zaune ta zabga tagumi ta faɗa duniyar tunani, yau wata uku da tafiyar Hamman na ta amma bai kirata ba ko sau ɗaya, gashi tun bayan tafiyan shi da kwana biyu take fama da zazzaɓin dare kullum dare bata iya barci ga wani matsanancin felling da take fama da shi ta rasa gane kanta.
Dadda ne ta shigo ɗakin nata riƙe da plate ɗin abinci in da take bin autar na ta da kallon tausayi duk ta rame tayi zuru zuru tamkar wacce tayi shekara tana jinya ƙarisowa tayi ta zauna kusa da ƴar tata wacce tayi nisa cikin duniyar tunani ba ta ma san Daddah ta shigo ba sai da ta taɓe ta tayi firgigit.
"Haba Autan Baffa ki rage tunanin nan addu'a da fatan dawowa lafiya zaki ma yayan naki kinji ki daure ki ci abinci ko ba yawa ki daina zama da yunwa."
Daddah ta ƙarasa maganar tana mai kai ma Saudat abinci bakin ta, tuni saudat taji cikin ta ya wani juya bata son ƙamshin abincin ga wani amai da ya taso mata ai da gudu ta fita xuwa bakin fanfon su ta fara kwara amai tamkar ran ta zai fita.
A ruɗe Dadda ta bi Saudat ta ruƙota sai da ta gama aman gaba ɗaya ta galabaita ta fita hayyacinta, ta taimaka mata ta wanke fuska da baki ta ruƙo ta suka dawo ɗaki, ƙureta da ido Daddah tayi gaban ta na cigaba da faɗi domin ganin wasu canje-canje a tattare da ƴar tata, da kyar ta tattaro natsuwarta ta kalli Saudat ta ce mata, "Saudatun Baffa."
A ruɗe Saudat ta ɗago ta kalli Daddah don tasan babban daliline zaisa Daddah ta ambaci Sunan ta haka, bata gama tunani ba taji Daddah ta jefo mata tanbayar da ya sa gabanta yankewa ya faɗi.
"Yaushe rabon da kiga baƙon ki.?
Cewar Daddah tana kashe ɗiyar tata da ido, gefe guda kuma tana addu'ar kar Allah yasa zargin da take ma ɗiyar tata ya zama gaskiya, dagowa Saudat tayi tana kallon mahaifiyar tata cike da firgici da tsoro ga wani rawa da jikin ta yakeyi take faɗin, "Daddah yau wata uku kenan tun ana gobe Hamma zai tafi da nayi wanka."
Wani irin zabura Daddah tayi haɗi da rafka uban salati tana cakumo wuyar Saudat ta fara bata wasu lafiyayyun tagwayen mari sannan ta rufe ta da duka tana faɗin, "yau ni nashiga uku ni Hafsatu,! Saudat ina tarbiyan da muka baki? uban wa kikaje kika miƙa ma kanki har ya san ki a matsayin ɗiya mace ya ɗirka miki ciki,! yau na bani na lalace kaico na ni wata irin uwace da na gaza gurin kula da ƴata, Saudat zaki faɗa mun wanda ya miki cikin nan ko sai na kashe da duka, da ki haifemun ɗan shege.!
Gaba ɗaya Saudat ta ruɗe ga azaban ciwon da mararta yake mata ga azabar ciwon dukan da Dadda take mata, ga matsananci tashin hankali da ruɗani da ta shiga, taya zata iya kallon idan mahaifiyarta ta faɗa mata cewa wanda sukafi yarda da shi fiye da kowa shi yayi mata ciki, taya zasu yarda mutumin da bai ƙasar ma, wayyo Allah ita kaicon ta tabbass rayuwar ta tana cikin garari wai yau ita ke ɗauke da cikin shege, bata gama tunani ba taji Daddah ta jawota ta haye ruwan cikin ta ta ɗaga muciyar da ke hannunta zata bugamata sai ga Baffa, ai da gudu ya ƙariso ya daka ma Daddah wani uban tsawa da sai da tagigice ta saki muciyar da ma a ruɗe take, yana zuwa ya finciketa daga kan Saudat, in da tuni numfashin Saudat ya tafi na wucin gadi, "baki da hankali ne Daddah yara kashemun ƴa zakiyi,! in rai ya ɓaci ai hankali ke nemoshi komai ta miki ai sai ki bita a hankali ko.!
"Malam kasan abun da ƴar nan tayi kuwa,? ciki gareta fa.!
"Ciki kuma.?
Da sauri ya ƙarisa kusa da Saudat ya ɗagota yana jinginata da jikin shi yana faɗin, "bani ruwa a kofi tafa suma."
Da sauri Daddah ta ɗebo ruwa ta kawo ma Baffa ya shafama ta, tuni ta sauke ajiyar zuciya tana buɗe ido ta kalli Baffa da sauri ta rungume Baffa tana kuka tana faɗin, "Baffa wallahi ba laifina bane laifin Hamma ne."
Wani irin ajiyar zuciya Baffa yayi, saɓanin Daddah da ta zabura tana faɗin, "kina nufin Mubashir.!
Kai ta girgiza alaman eh hakane, kuka Daddah ta saka tana faɗin, "yanzu haka yaron nan zai mana, malam ya naji kayi shiru wallahi ba zan yarda ba ƴata ta haifi shege.!
"Dakata Hafsatu ƴata ba shege zata haifa ba, ɗan sunnah zata haifa domin an daɗe da ɗaura auren Mubasshir da Saudat, rashin haƙuri ne dai irin na yaran zamani yasa har ya kasa haƙura a kaimai ita, amma tun da abun ya zo da haka zanje in samu Alhaji mu san ya za'ayi in za'a turamai matar shi ne a bishi can to."
Gaba ɗaya daga Daddah har Saudat suman zaune sukayi shaye da mamakin jin abun da Baffa ya faɗa, cikin fushi haɗe da ɓacin rai Daddah ta fara magana, "haba malam wannan wani irin ɗanyen hukunci ne ka yanke, kana sanin mahaifiyar yaron nan ba ƙaunar mu takeyi ba, sannan ka ɗauki ƴata ka ba ma yaron ta kaga kenan in kasheta ma zatayi kai baka da asara."
Daddah ta ƙarasa maganar ta tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya, da sauri ta tashi ta fice daga ɗakin, tuni jikin Baffa yayi sanyi ya tashi ya bi bayan Daddah, ita kuma Saudat ta jingina tanajin wani irin a zuciyarta farin ciki zatayi ko baƙin ciki.
*************************
Fitowar Daddah yayi dai dai da juyawar Momy da duk ta gama jin abun da suke cewa, hankali tashe Momy ta koma sashin ta, ko ganin gabanta ba tayi.
Ɗaki Momy ta nufa ta shige can Bedroom ɗin ta, wani zufa ne ya wanke mata jiki duk da sanyin Ac da ke kunne a ɗakin nata, fara kaiwa da dawowa takeyi a cikin ɗakin na ta tamkar wacce ta samu lalurar taɓun hankali, da sauri ta zabura ta nufi gefen gadonta ta ɗauki wayar ta danna na number boka Zalumu bugu ɗaya ana biyu ya ɗauka ya fara faɗin cewa, "kar wani ranki ya ɓaci la'ananniyar Allah sa'a tana tare da mu tabbass an ɗaura auran yaron ki da ita wannan yarinyar, kuma auren su ba zai taɓa mutuwa ba sai dai in har ɗaya ya mutu ya bar ɗaya, sai dai abu ɗaya zan miki shine kawai duk wani ciki da zata samu zamu miƙa ma aljani kundalo jinin shi ya shanye sai dai yabi rariya, shegiya kin amince ko.?
"Eh boka na amince ayi kawai.!
"Hhhhhh angama annamimiya baƙar azzaluma fara mai baƙar zuciya."
Kit ya kashe wayar bin wayar tayi da kallo tayi ƙwafa tana faɗin, "da ni kuke zancen ba dai ni za'a munafunta ba, haka ta fice falon tana maganganu.
*************************
ƘASAR INDIA
Kwance yake a makeken gadon ɗakin shi sai juyi yakeyi, gabaɗaya kewar matar shi yakeyi yana tuna abun da ya faru tsakanin su, lumshe ido yayi ya buɗe saboda jin ƙarar wayar shi da ke gefen filon shi, hannu ya miƙa ya ɗauki wayar zunbur ya miƙe ganin wanda yake kira, "Baffa barka da warhaka."
"Mubasshiru kamin babban laifi kuma kwata-kwata banji daɗin haka ba, meyasa baka faɗamun kana buƙatar matar ka ba kafin ka tafi, to yanzu dai mun gama magana da Mahaifinka za'a san cuku-cukun da za'ayi a turo ma matarka nan ku ƙarata tun da ku yaran yanzu baku da haƙuri, kuma bata da lafiya muna zargin ma mun samu ƙaruwa ne."
Baffa na gama faɗin haka kit ya kashe wayar.
Wani tsalle Mubasshir ya yi ya dira a kan gadon yana faɗin wai Allah ni ɗin ashe jarumine daga buga kwallo ɗaya har ya shiga raga, sai yayi sauri ya rufe idon shi yana jin wani kunya tamkar yana gaban Baffan.
*************************
NIGERIA
"Haba Alhaji a ce ina mahaifiyar Mubasshir ayi mai auren sirri, kamarka ɗan ka ɗaya tilo a rasa wacce zai aura sai ƴar matsiyata to wallahi ba zai yuwu ba sai ya saketa ko kuma nima in aura mai wanda nake so.!
"Kin ga Hindu ki barni ban son hayaniya kai na ciwo yakeyi."
"Eyyema haka ka ce ko to shikenan mu zuba ni da kai.!
Ta ƙarasa maganar tana wani huci ta fice fuuu tamkar zata tashi sama.
BAYAN SATI BIYU
Har anyi ma Saudat Biza, yau zata tafi india ita da Daddy da Baffa, bayan jirgin su ya ɗaga zuwa india a hankali a hankali ta ji kan ta na juyawa, da sauri ta ƙanƙame Baffa saboda jiri da tsoron da suka dirar mata a lokaci guda don wannan shine karon ta na farko da ta hau jirgi.
BAYAN AWA HUƊU DA TASHIN JIRGIN SU.
Tuni Saudat ta fara jin wani azababban ciwon mara tun tana daurewa har ta zo ta kasa daurewa, wani ƙara ta kwalla wanda ya dawo da hankalin ƴan jirgin baki ɗaya, tuni masu bada taimakon gaggawa na cikin jirgin sukayo kan ta, kafin ka ce wani abu tuni jinin ya fara zuba mata,iya taimakon da ya kamata su bata domin ceto rayuwar cikin abun ya ci tura, har suka iso India nan da nan motar Asibiti ta zo aka kinkime Saudat da tuni ta fita hayyacin ta dai dai da lokacin ƙarisowar Mubasshir tuni su Daddy suka shiga motar shi suka bi bayan motar Asibitin.
Washe gari bayan an samu daman ceto ran Saudat bayan matuƙar wahalar da ta sha, sai dai an rasa abun da ke cikinta in da ita da Mubasshir suka zauna suna ta kuka, su Daddy suna lallashin su, a washegarin rana ta biyu Aunty Saudat ta dira ƙasar don kulawa da su, kasancewar ita a lokacin bata da miji mijin ta ya rasu shiyasa baffa ya ce ta zo ta zauna da su.
BAYAN SATI ƊAYA
Su Daddy sun shirya tsaf don komawa amma haka Saudat ta rungume Baffa tana ta kuka tamkar ran ta zai fita gunin ban tausayi da kyar Addah Hafsatu ta riƙeta su Daddy suka shige jirgi jikin su sanyaye Baffa yana jin kamar yayi ma ƴar ta shi kallon ƙarshe ne.
BAYAN SA'O'I HUƊU DA TAFIYAR SU BAFFA.
Su Mubasshir ne suna zaune a ƙayattaccen falon su, yayin da Saudat ta kwanta a cinyar mubasshir suna hira cikin so da ƙauna, remote ya ɗauko ya kunna TV dai dai ana wani sanarwa game da jirgin da ya tashi ƙarfe bakwai da rabi na safe a ƙasar India ya samu hatsari wanda har yanzu an kasa tantance ko akwai wanda basu mutu ba a ciki, gaba ɗayan su miƙewa sukayi a ruɗe yayin da farantin fruit ɗin da ke hannun Addah Hafsatu ya faɗi ya fashe a guje ta ƙariso falon ganin Saudat ta tafi luuuu zata faɗi.
Kafin dare Mubasshir ya gama cuku-cukun yadda za'ayi su tafi gida Nigeria, don dama jirgin yafi kusa da Nigeria shiyasa aka ƙarasa da gawarwakin wa'in da aka samu, wasu ko sam ba'a ga gawarsu ba ma, bayan Mubasshir ya dawo da ƙyar suka samu jirgin da zai tafi gobe da ƙarfe biyu.
*************************
"Don Allah Hindatu kiyi haƙuri komai muƙaddarine daga ubangiji, kuma dole kowa zai mutu."
Cewar wata tsohuwa da take riƙe da momy.
"Guggo baki san in da nake ji bane, kwata-kwata fa ba'a ga gawar Alhaji ba, bamu da tabbacin ya mutu ko yana raye, kuma a wani hali yake ciki, ta ƙarisa maganar cikin rushewa da wani sabon kuka.
Gefe guda Daddah ne ta tasa gawar Baffa wanda ko kwarzane baiyi ba, ban da addu'oi da salati ba abun da takeyi in da tuni ƴaƴan ta da suke Taraba sun iso gabaɗayan su, kowa yana zaune sanye da hijabi da tasbaha a hannun su.
Haka aka gama zaman makoki da komai ba wani labarin Alhaji.
Tun daga lokacin Hajiya ta buɗe wani tashen rashin mutumci in da ta ce ma Daddah su tashi, haka daddah tana ji tana gani ƴaƴan ta suka ɗauketa suka maidata Taraba suka siyamata gida mai kyau madaidaici, sai dai ta tafi tana matuƙar kewan ƴar ta da irin halin da zata shiga a hannun azzaluman uwar mijin ta.
*************************
BAYAN SHEKARA GOMA
Wata hamshaƙiyar mata ce fara tas da ita zaune a wani ƙayataccen falo hannun ta riƙe da littafin hisnul muslim tana karanta addu'oi sai da na mata kallon tsaf na gane Saudat ne wacce yanzu ta zama Hajiya Saudat, bankaɗo kofar falon akayi ba ko Sallama Hajiya Hindatu ne ta shigo ta ƙara gogewa irin na manyan mata masu ji da Naira don tun bayar rasuwar alhaji bata kara aure ba ita ta cigaba da juya dukiyar shi har lokacin da ta mallaka ma Mubasshir wani kaso ya fara gina Asibitoci kasancewar karatun likitanci yayi, har ya zo ya zama Comissional lafiya, in da ya ƙara tara dukiya ninki abun da mahaifiyar shi ta bashi, har yau kuma Hajiya Hindatu ba ta kyale Saudat ta haihu ba, don in dai zata samu ciki matuƙar ta san da shi to sai ta ɓarar, haka ta dunga aura ma Mubasshir mata kala kala suna fita suna barin gidan kuma basu taɓa haihuwar ba kullum Hajiya sai ta zo gidan kasancewar yanzu ba gida ɗaya suke zaune ba, hakan ta kasance yau ma ta shigo ta tsaya ta gama ƙarema falon kallo tana yamutsa fuska, yayin da gefe guda Saudat ta sauka daga kan kujera ta duƙa tana faɗin, "Momy sannu da zuwa ki zauna mana."
Ta ƙarisa maganar tana sunkuyar da kai.
"To annamimiya mai ladabin munafurci, juya wacce ta ƙasa haihuwa sai dai ta ci tai kashi, inna auro mai masu haihuwa kiyi kicin-kicin ki koresu to ki sani wlh nine ajalinki shegiya ƴar matsiyata irin maita.!
Kuka sosai Saudat takeyi in da sabo yaci a ce ta saba da masifar uwar mijin nata amma har yau ta kasa, ta zugunne har Alhaji ya shigo ya ganta a wannan halin tuni ya gane mai ya faru, ajiye jakar hannun shi yayi ya dago matar shi ya rungume ya fara rarrashin ta suka shige ɗaki tuni labari ya sanja a ranar aka samu cikin Aneesa amma ba wanda yasan da haka.
*************************
BAYAN WATA TARA
Nakuɗa sosai ya taso ma Saudat kasancewar Hajiya Hindu bata ƙasar ta tafi wani harkan kasuwanci a Dubai tsawon wata shida, kuma cikin bai bayyana ba sai da ta kusa haihuwa aikuwa sosai Alhaji Mubasshir yayi farin ciki ranar da Saudat zata haihu ranar hajiya ta dira a Nigeria, hankalinta yayi matuƙar tashi jin cewa Saudat zata haihu nan da nan taje ta haɗa baki da Nurses ɗin da kuɗi masu dumbin yawa akan tana so a kashe duk abun da zata haifa, lokacin ita kuma saudat tana can tana fama da nakuɗa in da har ta fita hayyacinta, kasancewar ita da wata mata ce suke naƙudar a tare sai da yadda ta lura matar nan kamar wata ƴar duniya gashi tun da aka kawosu ba wanda taga ta zo kusa da Matar.
Bayan wasu awowi ta haifi sankacecen ɗan ta namiji nan da nan Nurse ta kira hajiya ta shaida mata cewa ta haihu amma namiji amma yanzu haka ta sume, haka ta ce su ɗauki yaron suje su yar da shi can in da ba zai taɓa dawowa garesu ba, in da hali ma a bar ƙasar da shi, tun da tace matar da take kusa da ita itama ta haihu ƴar ta rasu itama ta rasu to a mayarma da Saudat matacciyar ita kuma wancen a nemo gawan wani jaririn a ce nata ne, haka ko akayi Saudat na farkowa ta tarar da wannan jaririya a ƙasa amma tamkar bata da rai wata nurse ce ta shigo ita bata san meke faruwa ba tana zuwa ta ɗaga ƴarinyar taga alamun numfashi a tare da ita nan ta fara bata taimakon gaggawa nan da nan yarinya ta canyara ihu ashe wahala ce yasa tayi tamkar ta mutu, nan da nan aka gyarata aka fito da uwar da ƴar zuwa ɗakin hutu, farinciki gurin Alhaji Mubasshir bai faɗuwa, tun daga asibiti ya fara rabon kuɗi har aka sallamosu, sai dai wani abun mamaki yarinyar kwata-kwata batayi kama da iyayen ba amma su basu ga haka ba ko ƙaɗan sun ɗauki son duniya sun ɗora mata.
Anyi suna na kece raini tamkar ba'a san zafin naira ba in da gefe guda kuma Hajiya Hindu tamkar zata mutu don baƙin ciki, gashi da hannun ta ta ja ɗan ta zai raini ƴar da ba'a san aslinta ba gashi ba daman ta tona tamkar ta tona ma kanta asiri ne.
*************************
BAYAN SHEKAR BIYAR
Aneesa ta ta so akwai izza da isa, gata ba ta jin magana ko kaɗan duk da hajia Saudat tana iya ƙoƙarin ta na gurin bata tarbiyan da ya dace amma duk da haka abun nata gaba gaba yakeyi, gashi ta tsani taga an zo gurin mahaifiyar ta neman taimako ta dunga hararar mutane kenan, gata sangartacciya ce ta ƙarshe ga rashin ƙoƙari a makaranta kullum in taje makaranta sai ta ɗauko magana, tun tana shekara huɗu ta iya ta ɗauki ƙuɗi a ɗakin mahaifiyar ta, kwata-kwata basa shiri da Kaka kasancewar kullum tana ganin kaka tana ma Momyn ta Masifa, ita kuma duk wannan halaya nata bata taɓa yarada a ci zarfin mahaifiyar ta ta kyale hakan yasa in Hajiya tana faɗin ita ce ajalin Saudat, itama sai ta ce in har ta girma sai tayi ajalin hajiya kaka, momyn ta ta sha buge mata baki akan haka tai mata faɗa sosai ta ce kar ta ƙara faɗa, amma bashi zai sa in ta ji Hajiya Hindu ta zo tana masifar ba ita ma ta zo ta yi mata har ta kai Aneeesa tana ƴar shekara biyar Hajiya Hindu ta na shakkar ta.
*************************
BAYAN SHEKARA GOMA SHA UKU
Aneesa ce ta dawo makaranta sanye da Unifom kasancewar ta yarinya mai saurin girma zaka ɗauka ƴar shekara sha takwas ne ita domin komai na alaman budurci ya bayyana a tare da ita, jakar hannun ta ta jefar a kujera hijab ɗin ta ta cire ta wurgar haka takalmin ƙafar ta da safa kujera ta haye ta zauna ta fara kwalama mai aikin su kira, "Harira! Harira!.
Da gudu wacce aka kira Harira ta fito tana amsawa ta zo ta duƙa tana faɗin, "sannu da zuwa Hajiya, bata ida rufe baki ta ɗauke ta da mari tana nuna ta da yatsa, "bance in na dawo in dunga samunki a falo kina jirana ba, da me mutum zaiji da kwalamiki kira ko da yunwar da ya kwaso dallah ki ciremun kaya sannan ki ɗauko min wasu sannan a kawomun abincina, jiki na rawa harira ta fara cire mata kayan makaranta daga ita sai bes da wando gajere iya cinya haka harira ta tattara kayan ta shige ciki ta dawo da wasu kaya a hannun ta ta nufota da shi zata samata, "ke malama dakata maida waɗan nan kayan ba zan sa su ba.
Sai da ta kwaso kaya fin kala takwas tana cewa ta maida sannan ta samu wanda zata sa.
*************************
Kwatsam wani dare suka tashi suka tarar Alhaji ya rasu ba ciwo ba komai Momy da ƴar ta Aneesa sun sha kuka tamkar zasu bishi haka Hajiya Kaka in da gaba ɗaya tayi sanyi ta rasa miji ta rasa ɗan ta mafi soyuwa a ran ta mai tsananin biyayya a gareta.
*************************
BAYAN SHEKARA SHA HUƊU
Idon Aneesa ya ƙara buɗewa in da yanzu take Sss one ta kai bata jin maganar kowa kaka kuwa ta maida ta tamkar kishiyar ta kullum cikin faɗa suke kasancewar yanzu gida ɗaya suke zaune, in da Hajiya Saudat sosai ta zama uwar marayu ita ce gina Masallatai da islamiyu da asibitoci tana cewa ladan ya kai kabarin mijin ta mafi soyuwa a gareta.
Shine kwatsam watarana da daddare ina kwance a ɗaki na ji kamar motsi hakan yasab na fito da sauri, ina zuwa na nufi ɗakin Saudat kasancewar naga kofar ta a buɗe, ina shiga na ganta cikin jini da wuƙa a cikin ta, gaba ɗaya na ruɗe na ƙarisa da sauri ina ƙoƙarin cire mata wuƙar ta cika.
Hajiya Hindu ta ƙarisa maganar cikin matsanancin fashewa da kuka tana faɗin Tabbass alhakin Hassenat ne da ɗana da na hanashi jin daɗin rayuwa har ya koma ga Allah sanadin bugawar da zuciyar shi tayi lokaci guda, ga alhakin Saudat da na rabata da ɗan da ta haifa na sata riƙe shegiya wacce bata da asali."
Sosai Hajiya Hindu ke kuka.
"Barister lokacin ku yayi fa har an ɗan kara muku lokaci."
Nisawa Barister Khaseefa tayi ta miƙe ta ɗauki jakar ta tana mai kallon Hajiya.
"To Hajiya nagode da haɗin kan da kika bani, insha Allah zanyi iya bincike na don gano gaskiyar lamarin, in kuma ina da buƙatar sanin wani abu zaki ganni na dawo."
Sosai Barrister Khasheefa ta shiga tunani mai zurfi, to in ba Hajiya tayi kisan ba waya kashe Hajiya Saudat, dole tana buƙatar tattaunawa da ƴan gidan baki ɗayan su kafin ranar da za'a fara shiga kotu, tana buƙatar ganin yarinyar Hajiyan sannan tana buƙatan gani ƴan aikin gidan baki ɗaya, amma tafi buƙatar ganawa da Aneesat dole gobe zata shirya ta tafi Taraba domin ganawa da ita yarinyar.
*************************
DUBAI
Wata Matace ba zata wuce shekara hamsim ba tana zaune a wani tankasheshen falo, matar fara ce kyakkyawa daga ganin ta tana cikin hutu da kwanciyar hankali zaune take ta rafka uban tagumi ta lula duniyar tunani, a zahiri zaka ɗauka ta san me take tunani amma a baɗini ba tasan komai game da rayuwar duniya ba domin rayuwar tanayi ne kawai ita dai gata nan, can sai ga wata tsohuwa wacce da ka kalleta kasan shekaru sun tafi sai dai irin tsufane na jin daɗi da kwanciyar hankali jikin ta lukui-lukui ƙarisowa tayi cikin falon ta nufi gurin da wacce take zauna tayi tagumi, a hankali ta kai zaune gefenta hannun ta ta ruƙo ta sauke mata tagumin sannan ta miƙa mata maganin da ke hannunta haɗi da tsiyayo ruwa a wani glass cup ta nufi bakinta da shi, karɓan maganin tayi ta tsaya tana kallon maganin tana kallon matar, sai da matar ta girgiza mata kai tukunna sannan ta kai maganin bakin ta ta karɓi ruwan ta sha.
Sosai dattijuwar matan nan take kallon ta, nan da nan ta lula duniyar tunani yau shekara Arba'in da takwas kenan da tsintar wannan baiwar Allah bata taɓa magana ba, gashi sun tsinceta ɗauke da ciki gashi har ta haihu har yaron ya girma sun aura mai ƴar su yanzu yana da yara huɗu uku maza mace ɗaya, yanzu kaf babban birnin ƙasar Dubai ba wanda bai san Alhaji Khaleelullah Majeeed ba, har ma da ƙasashen duniya da suke makwaftaka da su, kasancewar wanda suka tsinci Mahaifiyar shi su ƴan ƙasan Dubai ɗin ne kuma babban ɗan siyasa da kasuwanci sunje Nigeria shida Matar shi harkan wani Business ne suka tsinci Haseeenat, a lokacin ƴarsu ɗaya Hibbatullah shekarar ta biyu a lokacin bayan dawowar su ne Alhaji Majeeed da matarshi Hajiya Majeeda suka yi ma Haseenat katin shaidar zama ƴar ƙasar Dubai suka cigaba da riƙeta tamkar ƙanwa a garesu, sannan sunyi mata iya magani har ta haihu ba wani cigaba akan rashin lafiyar ta, hakan yasa gabaɗaya rainon yaron da ta haifa yana hannun hajiya Majeeda da ƴarta Hibbatullah da ta ɗauki son duniya ta ɗora ma jaririn hakan yasa bayan shekaru masu yawa bayan sun girma akai musu aure duk da Hibbatullah ta girmi Khaleelullah, a haka suke rayuwar su a ƙaton gidan su mai ɗauke da bangarori da yawa, suna rayuwa cikin farin ciki da annashuwa tamkar basu da damuwa, in har yaran su Hibbatullah sun dawo makaranta gaba ɗaya sukan dungumo su shigo sashin kakan nin nasu su sha hira cikin farin ciki da annashuwa, in da suke nuna matuƙar kulawar su ga Mahaifiyar ta Baban su, kowa burin shi yaga tayi farin ciki, itama tana matuƙar son jikokin na ta duk da ba ta magana hakan bai hana ta nuna musu so a zahiri ba Musamman Airah da tafi matuƙar kama da ita gata ita ce kuma auta.
Hakan ce ta kasance yau Aira tana shigowa falon da gudu yayin da Anwar ke biye da ita yana cewa wallahi sai ya bigeta, direct bayan Mommah Haseenat tayi ta rungumeta tana faɗi, "Mommah kin ga Akhee ko, wai don na yar mai da System ba da sanin shi ba. Ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa.
Tsayawa Anwar yayi yana ɓata rai ya ce, "wallahi Mommah da gangar tayi fa.!
Hajiya Majeedat dai tana zaune tana kallon su cikin tsananin ƙaunar jikokin na ta, hararan Anwar Mommah tayi ta ƙara rungume jikar ta ta alamun ba zai taɓata ba, turo baki yayi ya juya yaje ya zauna kusa da Hajiya Majeedat yace, "Hajjah kina ganin Mommah ita kullum bayan Airah take goya a gidan nan shiyasa take ma mutane rashin kunya.
"Ka barsu kawai Anwar kasan daga Airah har Mommah ƴan rigima ne, a taɓasu Baffa da Pappah su zo su hau mu, to ya zamuyi tun da bamu da masu tare mana muma."
Airah ne ta leko ta bayan Mommah tayi ma Anwar gwalo dariya Mommah ta fara, ta miƙe ta kama hannun Aira suka bar falon, Hajja ta jawo Anwar tana shafa mai kai tamkar wani ƙaramin yaro cikin kwantar da murya ta ce mai, "ka rabu da su karka ƙara kulasu."
Washe gari ta kama Monday in da kowa na ta shirin makaranta, ban da Airah da taki tashi zuwan Ummi biyu tana tashin ta sai ta ce ta tashi amma Ummi na fita sai ta koma ta kwanta, sai da kowa ya kammala shiri zasu sashin su Hajjah kasancewar gabaɗaya familyn a nan suke haɗuwa su ci abinci, kowa ya fito ban da Airah Baffa ne ya dubi Ummi ya ce, "wai ina Airah ne,? caraf Anwar ya ce, "Baffah kasan dai ita kasace tana nan tana bacci Ummi tashin ta uku amma taki fitowa kullum sai ta ja min latti, wallahi yau sai dai Akheee Aminullah ya kai ta."
Tun da aka fara maganar bai tanka ba sai da ya ji ɗan uwan na shi ya anbaci sunan shi ya ɗago kai cikin miskilancin da ya saba ya ce "ni dai kun san ban da lokacin wannan ƴar tabarar sai dai ko Abdallah shi ke iya biye ma shirmenta amma ban da ni."
Yana ƙarisa maganar shi yayi gaba abun shi, Baffa ya girgiza kai ya ce, "ni ai sai in kaita tun da ba mai son ƴar lelen Mommahta ni ina son kayata."
Gabadaya falon dariya sukayi dai dai lokacin da Airah ta fito riƙe da jaka a hannu takalmi a hannu sucks ma haka, tana faɗin, "Ummi banga Cap ɗina ba, tun ɗazu nake nema fa."
"Ka gani ko Baffa kullum aka tashi tafiya sai ta ce bata ga kaza ba bataga kaza ba.
Ɓata rai tayi ta ce, "Baffa kana jin shi ko."
"Kyaleshi Shalelena, muje kinji ummin ki zata dubo miki."
Shigowar ta ajin kenan gurin kujerar da yake zama ta fara kallo gani tayi wayam ba shi a gurin cike da damuwa ta ƙarisa kujerar ta ta zauna tayi tagumi, to meke hanashi zuwa makaranta kwana biyu tasan bai fashi kuma bai latti amma lafiya jiya da yau bata ganshi ba, wani abokin shi ne da suke zaune tare a gurin ta gani zaune yayi shiru, ƙarisawa tayi gurin kujeran na su tayi ma abokin sallama ɗagowa yayi ya kalleta ta ce mai, "don Allah kwana biyu mai ya hana Mubasshir Mubasshir zuwa makaranta.?
"Mahaifiyar shi ce bata lafiya suna asibiti tun jiya."
*************************
0 comments:
Post a Comment