Zaune Aneesa take a ɗakin da aka sauke ta tana ta uban duba wayarta duk bayan minti biyar, can kirane ya shigo mata da sauri ta ɗauki kiran ta kara a kunnen ta ta ce, "Hello ya ake ciki ne tun ɗazu fa nake jiran kiranki amma na jiki shiru da fatan an kammala wancan aikin ko, ok tom kar dai ki bari a samu matsala kinji ko, yau nagode sosai sai na ƙara jin ki."
Wayar ce ta suɓuce a hannun ta ta faɗi kasancewar ganin ƙanwar momy tana binta da kallon tuhuma.
DUBAI
"Amma don Allah kasan gidan su in an tashi ka rakani.?
"Eh na sani."
Komawa sit ɗin ta tayi ta zauna tana ta tunanin Mubasshir, duk da har yau bai taɓa kulata ba ko ya mata magana amma har yau bata fasa yi mai magana ba, kasancewar shi Mubasshir in ya shigo aji ya zauna bai kula kowa sai abokin shi guda ɗaya shima in har ba maganar karatu ba ne ko suna discussion to ba zakaji hirar su ba, sai dai Allah ya zubama Mubasshir kyau domin farin shi irin tar tar ɗin nan ne ga suman shi tamkar na ƴan kasar amma shi kwata-kwata bai magana irin miskilin nanne na karshe ko dariya ba yayi in har ba yana gaban Kakar shi ba wacce take riƙeshi da sh, wacce ita kaɗai ya sani a rayuwar shi, ita ce uwar shi ita ce Uban shi, domin tun yana jariri ta zo da shi ƙasar Dubai tana aiki a wani gidan ƴan Nigeria sannan tana ɗan sana'oin ta na yau da kullum da haka take biyan ma Mubasshir kuɗin makaranta take mai duk wani hidima hakan ya sa gabaɗaya rayuwar Mubasshir ya dogara ne aka Kakar shi wacce duk duniya ba wacce yake so kamar ita, hakan ta kasance gareta ita ma duk duniya ba wanda ta keso ta kalla tayi farin ciki irin Mubasshir wataran kuma tayi kuka, in ta tuna irin ɗumbin dukiyar da Mahaifin shi yake da shi, amma ga irin rayuwar da ya taso na cikin wahala da bauta, domin tun da ya taso yayi wayau, bai taɓa yarda ya bar kaka ta yi aiki ita kaɗai ba kama daga girki, wanke-wanke da sauransu komai tare sukeyi tun tana hanashi har ta kyaleshi, haka suke rayuwa da daɗi ba daɗi duk da yaran gidan suna da wulaƙanci, don ma suna shakkan Mubasshir tun ranar da Salma ta watsama Kaka abinci a jiki dai dai lokacin Mubasshir na fitowa daga kichin riƙe da kulan Abinci zai jera a dining ai bai san lokacin da ya saki kular ya ƙariso ya tsinka mata mari zafafa guda biyu, haɗe da warning kuma ya sa ta duƙa ta kwashe abincin tun daga ranar suke shakkan taɓa Kaka, tun daga ranar kuma Salma take shisshigema Mubasshir tana bashi haƙuri, shiko ko ta kanta baiyi.
Mubasshir ne zaune ya tasa Kaka a gaba yana kuka fuskar shi tai jajir, jijiyoyin kanshi sunyu ruɗu-ruɗu da kyar ya buɗe baki ya ce, "kaka ya kamata ki faɗamun meye tsakanin ki da matar da aka nuno a TV ta mutu a Nigeria kika kama ciwo, bayan kin ce bamu da sauran dangi a Nigeria duk sun mutu a sanadin boom."
"Mubasshiru na yau shekarar mu goma sha huɗu da ƴan watanni a ƙasar nan, kullum ina rayuwa ce cikin tausayin ka da ƙuncin da neman mafita ya zan inganta rayuwarka."
Wayar Mubasshir ne tayi ƙara yayi sauri ya fito da shi daga aljihun wandon shi, da sauri ya miƙe yana faɗin, "Kaka na shiga uku na kodai shugaban Company ya zo yau ne domin duk ranar juma'a yake zuwa ziyara yaji matsalolin ma'aikata, sai dai in har baka zo aiki bai saurara ma mutum, ina ga shine ya zo."
"Ka ɗauka insha Allah Alheri ne."
"Hello eh nine Mubasshir Mubasshir, wallahi Kaka ta ce ba lafiya yanzu haka muna asibiti, eh ranka ya daɗe tom nagode Allah ya saka da alheri."
"Kaka albishirinki yau zamu warke kin ga dama na kasa siyan maganin da aka rubuta miki duka amma nasan in ya zo tabbas zai taimake mu don an ce shi mutum ne mai matuƙar tausayi da taimako."
"To Mubasshiru Allah yasa mu da ce, ni yanzu tunanina in da zamu koma, tun da kaga can gidan sun sallamemu daga aiki, ga rashin madafa ni komai ya fita mun a rai ya kamata a ce yanzu mun haƙura da aikin ina tunanin ya zamuyi mu koma Nigeria, don kaga daga lokacin da na zo ƙasar nan har zuwa yanxu na yi aiki a gidaje yayi goma, wasu hawaye ne suka zubo ma kaka da sauri Mubasshir yasa hannu ya goge ma kaka Hawayen ya ce mata, "Kaka ni ina ji ban son Nigeria ɗin nan na tsane ko sunan shi in ji, zanyi iya ƙoƙarina in samo mana kuɗi mu kama ko da haya ne, kinji Kaka don Allah na roƙeƙi ki bar maganar Nigeria ɗin nan."
Yana gama faɗin haka ya tashi ya fice daga ɗakin da kaka take kwance ya bugomata kofar da karfi, sosai hankalin kaka ya tashi meyasa a duk lokacin da taima Mubasshiru maganar Nigeria sai yayi fushi mai tsanani har abinci ma bai ci, ta ina zata bullomai domin ita yanzu gabaɗaya tunaninta ya karkata ne gurin yadda zata maida Mubasshir ga ahalin shi, to amma taya tana tsoron ta maidashi a kara cutar da shi balle yanzu da ya zama maraya ba uwa ba uba, a haka Kaka ta dunga tunani har barci ya ɗauketa.
*************************
"Kin san wani Abu Mommah wallahi akwai wani mai kama da Akhee babba na gidan nan irin su ɗaya sai dai shi bai kai girma Akheee ba ajinmu ɗaya da shi, komai na su iri ɗaya har da Baffa kama sukeyi tamkar shi ya haifesu, harfa dimple ɗin gefen fuskan Akhee babba shima yana da shi, har miskilancin su, da ƙin kula mutane, da hasken fatar su da kin yin dariya fa, kai wallahi ina baku labari da girmansu ɗaya da Akhee babba zance ƴan biyu Ummi ta haifa aka ɗauke ɗaya."
Tun da Airah take zubanta Mommah ta zuba mata ido sai murmushi takeyi, yayin da Anwar yake gefe yana yin Assignment a cikin system ɗin shi, shiko Abdallah sai dariya yakeyi ƙasa-ƙasa don tun da Airah ta fara gulmanta Aminullah na gurin yana jin ta ya ƙara kicin kicin da rai, basuji ƙarasowar shi ba ita da Mommah sai ji sukayi ya sakar ma Airah rankwashi a kai, wani ihu da ta saka gaba ɗaya mutanen gidan sai da suka hallara, Mommah ma wani miƙewa ta ta wurga ma Aminullah filon dake kusa da ita cikin jin haushin abun da ya ma Airah ta ja hannun ta suka shige ɗaki suka kullo kofa, nan aka fara kallon-kallo domin sun san yau Aminullah ya kiramusu masifa a gidan don yau yini zasuyi a ɗaki ba zasu taɓa buɗe kofar ba, ko abinci sun bar ci ba mai sasu su buɗe kofar daga Baffa sa Pappa ga Pappah ma bashi ƙasar yana India, shi kuma Baffa ba zai dawo da wuri ba saboda yau yana da ziyara da yawa na companonin shi da shagunan shi, sosai Ummi ta fara ma Ameenullah magana cike da ɓacin rai nan suka rufeshi da faɗa ita da Hajjah.
"Haba Ummi sai yarinyar nan ta dunga rashin kunyarta a gidan nan ku hana ai mata hukunci saboda kar Mommah tai fushi, to wallahi suyi ta zama a ɗakin kar su fito ɗin badai abincin ne ba za su ci ba kar su ci ɗin cikin su, ita kuma Mommah dama kiris take jira ta samu abin fakewa don kar ta sha magani."
Yana gama maganar shi yayi ficewar su ya barsu a nan sunyi jugum-jugum.
ASIBITI
Shigowar Alhaji Khaleelullah Majeeed Asibiti ya jawo hankalin mutane da yawa, kasancewar Asibitine ƙarami na marasa karfi ko gate babu, yana shigowa ya ce a kira mai Mubasshir, shi kuma Mubasshir yana zauna a bakin kofar da Kaka take kwance, yaji kira da sauri ya ɗauki wayar yana faɗin "eh room 4 gashinan ma na hangoku.
Da sauri ya ƙarisa gurin su tun daga nesa Alhaji Khaleelullah ya ƙure Mubasshir da kallo yana jin gaban shi na matuƙar faɗuwa ga wani tsantsan kama da yakeyi da Ameeenullah, haka mutanen da ke tare da shi suka ƙure Mubasshir da kallo suna mamakin girma da buwaya na ubangiji da yake hallita iri ɗaya, haka suka ƙarisa suka shiga cikin ɗakin da kaka take dai da ta farka daga barcin da takeyi wani irin Zabura tayi tamkar zata faɗo ganin Alhaji Khaleelullah, ido waje ta ke kallon shi tuni wani zufa ya fara karyo mata.
*************************
NIGERIA KADUNA
"Sunana Barister Mansir Khaleed nine lauyar Aneesa ni ce wanda zamu kara da ke game da shari'ar."
Murmushi Barister Khasheeefa tayi ta ce mai, "sunana Barister Khasheefa Mudassir ni ce lauyar mai kare wacce ake zargi."
"Nice to meet you."
"Thank you."
Barister Khasheefa ce take tsaye bakin kofar wani gida daga ganin gidan kasan gidane irin na yaku bayi, can sai ga wani yaro ya fito yana ce mata, "wai an ce ya ɗan fita amma yanzu zai dawo ki shigo ki jirashi."
"Ok to nagode ko ƙanina, riƙe wannan ka siyi alewa."
Barister ta ƙarisa maganar ta tana miƙama yaron ɗari biyu ta kutsa kai ta shiga gidan ɗauke da sallama, sannu da zuwa matar gidan tayi mata ta shimfiɗa mata tabarma ta zauna suna gaisawa, zaman ta ba daɗewa sai ga Idi maigadi ya shigo ɗauke da buhun gari alamu sun nuna niƙar tuwo yaje kaiwa.
"Ikon Allah Rahane baƙuwa mukayi a gidan namu,? ya faɗa yana washe baki domin shi Idi Allah yayi shi mutum ne mai masifar son kuɗi, akan kuɗi zai iya yin koma, hararar shi matar tayi ta ce, "gatanan ai gurin ka ta zo," tana gama faɗamai haka ta ɗauki buhun niƙar ta tayi ɗan kicin ɗin na su da aka kewaye da fale-fale, zama yayi yana gaida Barister, ta amsa mai cikin sakin fuska, "sunana Barrister Khasheefat na zo ne don in ɗan ma tambayoyi game da kisan da akayi a gidan Alhaji Mubasshir mailafiya."
Wani zabura Idi yayi nan da nan zufa ta fara keto mai jikin shi ya fara rawa yana faɗi, "wallahi ni ban san komai ba game da Mutuwar Hajiya ba."
Da kallo kawai Barrister ta bishi, kallo mai cike da ma'anoni daga nan bata ƙara magana ba ta ɗauki jakar ta ta mai sallama ta kama hanya ya biyota har kofar gida yana cewa, "ki gaida gida nagode Allah dai yaji ƙan Hajiya baiwar Allah."
Haka dai ya dunga ƴan kame kamen shi har Barrister ta hau motar ta ta tafi.
*************************
TARABA
"Ƴata da wa kike waya cikin wannan dare da ya kamata a ce kina barci ko kina sallah kina roƙama mahaifiyar ki gafara.?
"Momy ina waya da lauyer da na ɗauka ne take faɗa mun rana ashirin da uku ga watan gobe za'a fara shiga kotu."
"Allah sarki Aneeesa don dai kin matsane akan cewa sai anyi shari'ar nan Amma ita kanta Daddah ta ce ta yafe a kyale Hindu duniya zata koyamata darasi, amma shikenan ki kwanta kiyi barci kin ji sai da safe."
Momy Hafsat na gama magana ta fita ta jama Aneesa kofa, wani irin ajiyar zuciya tare da hamdala Aneeeaasa tayi ta ɗauko wayarta da ta faɗi ƙasa, juyawa tayi ta buɗe draweer ta fito da wata jaka cikin jakar wata jaka ce a ciki tana buɗewa sai ga kalolin kayan maye nan kala-kala wani ta ɗauko kamar kwaya ta buɗe frige ta ɗauko ruwa ta shanye sannan ta ɗauko syrup ta fara korawa tana gamawa ta harhaɗa kayan ta ta mayar ta koma ta kwanta in da ta fara jin ta tana yawo a gajimare.✍️✍️✍️✍️
Kafin safe Aneeesa ta ware daga kayan mayen da ta sha, domin ita duk iskancin ta ba ta shan kayan maye da rana ko safe sai da daddare in taje kwanciya zata sha, saboda ta ce hakan yafi rufin asiri gashi mutum na samun chaji iya chaji kayi barci cikin nishaɗi tamkar tana yawo a gajimare haka take jin ta, bayan ta ta shi tayi sallah ne ta ɗauko wayarta lokacin karfe takwass na safe, latsa wasu Numbobi tayi ta danna gurin kira, "Hello ƙawata ya ake ciki ne, da fatan kina kula da kyau, fatan ba ai mata wani illah ba,? to tana cin Abinci kuwa, nifa ban so kuna barin ta da yunwa please, har yanzu ba tayi wani magana,? ok shikenan bata shirya tsira da rayuwarta bane tabbass ku cigaba da binciken ta har sai tayi magana, sai kin jini, sannan ina ƙara gargaɗinki karki sake ku kirani in ba ni na kiraku ba."
Kashe wayar tayi ta na mai murmushi mai cike da ma'anoni, "Tabbass baki san waye Aneesa ba domin makircina ya fi na Mace mai shekara tamanin a duniya kallon ku kawai na keyi, karki maganar da rabon zan gwadamiki rashin imanina ne."
Tana gama wannan maganar ta fashe da kuka tana faɗin, Allah sarki Momy da Daddy nayi rashin iyayena yanzu na zama marainiya ba uwa ba uba, tabbass kaka ba zan taɓa yafe miki ba sai na ɗau fansar jinin mahaifiyata, na san da Momy na nan da yanzu ta rungumeni ta bani abinci ta yi mun nasiha." Ƙara fashewa tayi da kuka mai tsuma zuciya, gunin ban tausayi haka Momy Hafaat ta zo ta sameta, da sauri ta ƙariso gareta ta rungumota a jikin ta tana shafa bayan ta, "kiyi haƙuri Aneeesa mutuwar uwa an san akwai ciwo, amma haƙuri akeyi duk wanda ya mutu ya mutu, ki ɗaukeni tamkar mahaifiyarki duk abun da kikeso ki mun magana ki saki jikin ki nan tamkar gidan ku ne kinji ƴata."
Haka momy hafsat ta dunga kwantar ma da Aneesa hankali har tayi shiru, momy hafsat ta shiga toilet ta haɗa mata ruwan wanka ta kamata ta kaita ta ce mata tayi wanka ita kuma momy hafsat ta fito toilet ta rufo mata kofar taje drawer ta ɗauko mata kayan sawa ta ajiye mata akan gado ta fice, ba ta daɗe da fita ba ta dawo ɗauke da tray cike da abin karyawa, zama tayi a bakin gado tana jiran fitowar Aneeesa, fitowar Aneesa kenan daga wanka tana goge jikin ta da wani towel taje gaban mirrow ta fara shafa bayan ta gama ta sanya kayan ta ta ƙariso kusa da Momy Hafsat ta zauna ta jingina jikin ta a jikin Momy Hafsat ta buɗe baki da kyar ta ce, "momy ina jin yunwa."
Ta faɗa a shagwaɓe, riko hannun ta Momy tayi ta zaunar da ita a lallausan kafet ɗin da ke gefen gadon ita ma ta zauna ta jawo farantin abinci ta haɗa tea ta fara bata.
*************************
KADUNA
"Barrister Zainab ni ban taɓa ganin shari'a irin wannan ba a rayuwa ta, ni kin san ma mai yafi ban mamaki da zargi ni ina tunanin kamar fa Matar nan bata mutu ba, don ina zargin wani abu."
"What Barrister Khasheefa kin san me kike faɗa kuwa,? kin taɓa jin wanda ya mutu ya dawo, kin san hakan ba zai taɓa yuwuwa."
"Barrister Zainab kenan ni dai taimako ɗaya zaki mun game da shari'ar nan, kawo kunnenki ki ji, matsowa Barrister zainab tayi ta raɗa mata wani abu a kunne sannan ta miƙe ta ɗauki jakarta tayi mata sallama ta ce, "ƙawata bari in koma office akwai binciken da nake so in ƙarasa."
"Ok ƙawata sai mun haɗun kawai, karki samu damuwa zan baki haɗin kai ɗari bisa ɗari."
*************************
0 comments:
Post a Comment