Alhaji Khaleelullah kallon Kaka kawai yakeyi hango irin kamar da takeyi da Mahaifiyar shi sai dai ita jikin tsufa da kuma wahalar rayuwa da ta maida kaka haka, sannan ba kowa zai iya gane kamar da sukeyi da Hassenat ba sai makusancin ta kuma wanda ya san ɗaya daga cikin su sosai, ƙarisawa yayi sai ya samu kanshi da duƙawa har ƙasa yana gaida kaka, cikin dauriya da kuma jin wani faɗuwar gaba da sarawa da kan ta yakeyi kaka ta amsa da kyar, yayi mata ya jiki ta ce da sauki, ɗagowa yayi ya zubama Mubasshir da yake tsugunne a ƙasa yana gaisheshi ido, ƙarisowa yayi ya ɗago shi ya rungumeshi a jikin shi ya ce ma kaka, "kaka wannan yaro naki yayi matuƙar kama da ni da kuma wani yarona wanda shine Babban ɗana, tun da na ɗora idona a kan shi naji ina matuƙar ƙaunar yaron a raina don Allah kaka ko zaku iya bani labarin ku a taƙaice.?
Alhaji Khaleelullah ya ƙarisa maganar yana mai ƙure kaka da ido, a zahiri kallon kaka yakeyi amma a baɗini kallon Mommah yakeyi a cikin fuskan kaka, Mubasshir ne yayi saurin faɗin, "mai zai hana mu baka labarin mu," ya faɗi haka ganin kaka taki cewa komai, da sauri duk suka waiga suna kallon Mubasshir Alhaji ya kalli mutanen da suke tare ya ce su fita su basu guri, bayan fitarsu ne ya kalli Mubasshir ya ce, "ɗana ina jin ka."
Kwashe labarin su tsaf yayi ya faɗa ma Alhaji iya abun da Kaka ta faɗa mai, sosai kaka take kuka ita kaɗai tasan kukan da takeyi, matsawa kusa da ita yayi ya ce ma kaka, "Kaka kiyi haƙuri insha Allah wahalar ku ta zo ƙarshe zan baku gurin zama sannan zan ƙara ma yaron ki albashi akan yadda ake biyan shi kuma nayi alƙawarin na ɗauki nauyin karatun shi har ya kammala."
Sosai Kaka tayi farin ciki sai gashi ta sauko har ƙasa zata duƙa da sauri Alhaji Khaleelullah ya ɗagota, nan ya ce a nemomai likitocin asibitin ana suna zuwa ya nemi sallama aka sallamesu yaje ya siyamusu magunguna suka hau mota ya nufi wani unguwa ce na marasa karfi sosai gidane ɗan dai dai mai kyau ya tsaya suma motocin securityn shi ma suka tsaya suka firfito dama kafin su iso ya tura wasu daga cikin securityn shi akan suje kasuwa su siyo duk abun da za'a buƙata, suna shiga cikin gidan ba jimawa wanda Alhaji ya aika suka dawo suna zuwa aka fara shirya gidan nan da na komai yayi tsaf ga kayan abinci da Alhaji ya jibge musu, sosai sukayi godiya, bayan tafiyar su Kaka ta shige ɗaki ta faɗa duniyar tunani.
*************************
ƘASAR CAMEROON
Babban birnin Yawundi, wani Mahaukaci ne yake zaune a gefen wata magudanar ruwa, can kamar an tsikareshi ya tashi ya ɗauko wani gwangwani ya ɗibi ruwar kwatar nan ya sha bayan ya gama sha ne ya shimfiɗa wani tsumma ya kwanta, duk in da ka kalli wannan mahaukaci sai ka tausayamai ga tsufa ga hauka, can ya tashi ya zauna ya fara jera hamma alamu yana jin yunwa, wata yarinya ce ba zata wuce shekara bakwai ba take tafiya tana waige-waige jikin ta sanye da unifoam ɗin makaranta riƙe take da Lunch basket na makaranta da yake ɗauke da kulan abinci da plask na silba na ruwan zafi, can ta hango mahaukacin zaune ya zabga tagumi cike da farin ciki ta nufeshi tana zuwa mahaukacin ya fara farin ciki yana murna da ganin ta, ta shi yayi ya fara karkaɗe gurin ya koma ya zauna ita ma ta zauna a gefen shi ta buɗe abincin ta debo ta fara bashi a baki ta tsiiyaya tea ɗin a murfin plask ɗin ta tana bashi yana karɓa yana cinyewa da sauri da sauri sai dariya take mai shiko yana ta wasa da beat ɗin kitson da ke kan yarinyar a haka har ya gama cin abincin ta curo ruwa a jakar ta ta bashi ya sha nan suka fara wasa, ɗauko text book ɗin ta tayi ta fara yin Home work ɗin da aka basu, tayi tayi tayi wani math ta kasa shiko mahaukacin na ta wasa abun shi, can ta ɗago ta miƙa mai book ɗin ta ce, "na kasa yi Didi yi mun."
Karɓan littafin yayi da pensil ɗin ya fara yi mata, abun gwanin mamaki kuma irin rubutun yarinyar yayi, ya miƙa mata murna tayi ta rungumeshi, dai dai isowar wasu mutane biyu gurin a mota suna faɗin, "kai gatanan fa a gurin wannan shegen tsohon mahaukacin nan faɗin driver motar, da sauri Suka fito baki ɗayan su suka nufo gurin da suke, mahaifiyar Amal na zuwa ta nufi gurin su ta fizgo Amal a jikin wannan mahaukaci ta ɗauketa da wata gigitacciyan Mari, hakan yasa Amal ta kwalla wani ƙara, take jikin mahaukacin nan na rawa ya miƙe ya rufe maman Amal da duka gabaɗaya mutanen gurin sun ƙasa kwatan ta, Amal ne ta zo ta ruƙe shi ta ce da ƙarfi, "Didi ka bari haka momy ne fa.!
Da sauri ya saki matar ya koma bayan Amal ya tsaya yana zazzare ido, sosai Maman Amal take tsine ma wannan mahaukacin ta ce sai ta kwaso mai ƴan sanda, tuni mutane suka taru a gurin kowa na faɗan albarkacin bakin shi, haka dai su Amal suka shige mota sukayi na gida an bar Momyn Amal da tsamin jiki sai da ta sha magani.
A daren ranar mahaukacin nan na barcin shi aka zo akai mai dukan kawo wuƙa an wayi garine aka ganshi jina jina mutanen gurin sukayi karo karo aka tafi da shi Asibiti.
A can gida kuwa Momyn Amal ne ta ja ma Amal kunne ta ce duk ranar da ta ƙara zuwa gurin mahaukacin nan sai ta yanke mata ƙafa, sosa Amal ke kuka tamkar zata shiɗe, tana fita ta ce ma driver ya kira mata daddyn ta da rawar jiki kuwa ya kirashi yana ɗauka Amal ta fashe da kuka.
"************************
NIGERIA KADUNA
Mugune ya kalli matar da take zaune a gefen gado ya ce mata, "Hajiya yanzu ya kike jin gefen cikin na ki, saboda yau likita zai zo ya warware miki ɗinkin na ki."
Yana gama maganar ya fice yaja ƙofar ya rufe da makulli, girgiza kai matar tayi ta koma ta kwanta.
Barrister Khasheefat ne take tafe a motar ta tana amsa waya take faɗin, "ina so ka bibiyan mun duk wani motsin shi da kiran da zaiyi, saboda akwai zargin da nakeyi a kan shi yanzu haka ina hanya zani gidan driver Hajiya Hindu ne."
Tana kammala wayar wani kiran ya ƙara shigowa wayarta, dauka tayi tana sauraren maganar da wanda yake kirata yake faɗa mata, "Barrister Hasashen ki ya zama gaskiya domin yanzu haka muna maƙabartan kuma mun tabbatar da hakan."
"Good Zainuddin amma kun tabbatar nan ɗin ne bakuyi missing ba.?
"Sosai ma kuwa Barrister karki manta da ni fa akayi jana'izan ta."
"Ok to shikenan ba damuwa in na dawo zan biyo in karɓi evidence ɗin da sauran abun da ya kamata mu tattauna domin yanzu haka ina hanyar zuwa Hayin ɗanmani ne, ok tom sai ka ji ni nagode sosai."
Murmushi Barrister Khasheeefa tayi, "tabbass tunanina da lissafina zai zo dai dai."
*************************
DUBAI
Yau an ci sa'a su Ayrah sun fito daga kulle kansu da sukayi, sai dai sun ƙi kula kowa.
Shigowar Baffah ya yi dai dai da fitowar Ummi daga kichin hannun ta riƙe da yankakkun fruit da sauri ta ƙariso ta ce ma Baffah, "well come Noorey, ɗan rungumarta Baffah yayi ya sumbaceta a goshi ya ce, "yauwa hayateey ya gidan ya yaran fatan duk kuna lafiya."
"Muna lafiya," kamo Baffah tayi ta zaunar da shi, taje ta ɗauko ruwa mai sanyi ta zuba mai a kofi sannan ta rage mai falmaran ɗin jikin shi da takalmi, sannan ta tashi taje ta haɗamai ruwan wanka ta dawo suka shige domin yin wanka.
Zaune suke da Kaka suna cin Abinci kwano ɗaya, can Mubasshir ya ɗago kai ya kalli kaka ya ce mata, "kaka ko hoton iyayena baki da shi to.?
CAMEROON
"Daddy Momy ne ta zaneni, kuma ta hanani zuwa gurin Didi na," ta ƙarisa maganar tana fashewa da kuka.
"Oh Amal rigima kiyi shiru ba wan da ya isa ya rabaki da Didin ki yau zan dawo insha Allah, ki share hawayenki kije makaranta in kin tashi ki je gurin Didi inna dawo ma da kaina zanje in ɗauko shi in dawo da shi gidan mu, kina so ai ko."?
"Eh daddy ina so mana sosai ma kuwa."
Miƙa ma driver wayar shi ta yi tana tsallen murna ta shige mota suka nufi makaranta, ana ta shi wurin Didi ta wuce yau bata ganshi ba sai tarkacen kayan haukan shi, sosai ta dunga neman shi har da kukan ta ita dai ta san Didi bai zuwa ko ina, amma yau gashi baya gurin, a cikin mutanen da ke gurin ne wani ya taso ya zo in da take zaune saboda gaba ɗaya ƴan gurin sun san Amal saboda zuwa gurin Didi da irin shakuwar da sukayi ya ce mata, "yarinya gara ma ki tashi ki tafi domin kuwa wanda kika zo nema ya Mutu jiya wasu suka zo suka mai dukan tsiya da daddare bayan mun kai shi Asibiti rai yayi halin sa, zaro ido Amal tayi ta kalli mutumin cikin kwaɓa fuska irin na sangartattun ƴaƴa ta ce mai, "kenan Didi ya tafi in da ba'a dawo kamar in da ƙanwata ta tafi, shikenan fa ba zan ƙara ganin shi ba kake nufi.?
"Sosai ma kuwa gara ki tashi ki tafi."
Bai gama rufe baki ba suka ga yarinya ta sulale a gurin ta faɗi tamkar matacciya.
*************************
DUBAI
"Mubasshiru kayi haƙuri akwai abun da nake jira zan baka labarin ko mu waye kuma har iyayen ka ma zan nuna maka ba wai hoton su ba, insha Allah."
"Shikenan kaka Allah ya nuna mana lokacin."
'Ameeen ɗan albarka."
"Hayateey yau na ga abun mamaki, wani yaro na gani ba zai wuce sa'an Ayrah ba ko zai girmeta bai fi da watanni ba, suna bala'in kama da Ameeenullah kama sosai na ƴan uwan ta ka, kuma tun da naga yaron nan naji wani irin ƙaunar yaron ya shiga raina tamkar jinina, kuma kin san asalin su daga ina suke,? to daga Nigeria suke, hakan yasa na fara tunanin anya ban da alaƙa na jini da yaron nan.?
"Hayateeey kenan kai har yanzu kana nan akan bakanka na cewa sai ka nemo dangin ku kai da Mommah Alhalin gamu mun isheku rayuwar duniya mahaifiina ya ɗaukeku tamkar dangi ɗaya, in har su ƴan uwan na ku na son ku zasu kawo hakane basu neme ku ba, karfa damuwar son ganin dangin ka yasa kaje ka ɗauko wanda zasu wargaza mana farin ciki mussaman ƴan Nigeria ba wanda ya kai su rashin gaskiya da cin amana.
"Ya isa haka! kin san dai ko ya suke kasata ce, kuma ina son ta kuma ina kishinta duk da ban taɓa zuwa ba har yau duk kasuwancina da tafiye tafiye ɗina, don dangin mu basu nememu ba hakan ba shi zai sa ni in ki nemansu ba, kuma insha Allah zamu haɗu da su a lokacin da ya dace domin ni ina ji a jikina, ba'a son ransu suka rasamu ba."
Baffah na gama maganar shi ya tashi ya fice ya bar Ummi zaune tana cika tana batsewa, saboda ita in da abun da ta tsana a duniya ta ji mijin ta na zancen dangin shi ko Nigeria tafi so suyi ta rayuwar su a haka.
Washegari Ayrah ce ta fito riƙe da jaka a hannun ta ranar ta riga kowa shiryawa saboda zasuje gidan su Mubasshir, hakan ba ƙaramin ba ƴan gidan mamaki yayi ba har Akheee Abdallah yake tsokanar ta, "to fa yau za'ayi ruwa da ƙanƙara, wai yau Ayrah ce ta riga kowa shiryawa, Anwar zo ka ga mutumiyar ka yau kamar tayi makuwa."
Abdallah ta ƙarisa maganar ya dariya ƙasa-ƙasa, kuka ta fara tana bubbuga ƙafar ta a ƙa sani tana faɗin, "Ummi kinga su Akheee suna zolayata ko."
"Ba dole su zolaye ki ba yau munga abun mamaki ne wanda bamu saba gani ba."
"Kai Hajjah har da ke a tsokanar mun Auta ko."
Cewar Baffah da shigowar shi falon kenan, Pappah ne shima ya sauko daga sama daga nan aka fara gaisuwa cikin farin ciki da ƙaunar juna kasancewar su family masu tsananin son junan su, haka suka dunguma zuwa teburin cin abinci kowa ya zauna, sai da sukayi addu'a sannan suka fara ci, bayan sun kammala ne kowa ya nufi hanyar makaranta yayin da Baffah da Ameeenullah suka nufi gurin aiki, kowa ya fita cikin farin ciki.
Mubasshir ne zaune a sit ɗin shi yana duba Assignment ɗin da aka bada da bai zo ba, shigowar ta aji kenan shi ta fara hangowa gurin shi ta nufa cike da fara'ar ta hannun ta riƙe niƙi-niƙi da kayayyaki ta ce mai, "nayi kewarka kwana biyu, ya mai jikin i hope taji sauki."
Ta ƙarisa maganar tana zama kusa da Mubasshir, matsawa yayi da sauri ya ƙara ɗaure fuska, cike da miskilanci ya ce mata, "ke tashi a nan gurin, sannan kina da matsala da mai jikin ne da zaki dunga tanbayata.!
Ya ƙarisa maganar cikin kauda kai tamkar wanda aka sa yayi maganar dole, kuma ba zaka ce shi ya yi maganar ba, ɓata fuska tayi cike da shagwaɓa ta ce mai, "Allah ya baka haƙuri, dama in ji ya ta ƙara ji ne fa, sannan ga wannan a kai mata, kallon da ya watsa mata ne sai da ƴan hanjin ta suka juya jikin ta na rawa ta tashi nan da nan idon ta ya kawo kwalla, domin duk surutun Ayrah tana da bala'in tsoro ga saurin kuka, juyawa tayi zata tafi da kayan ba zato taji ya ce mata ajiye an gode da sauri ta juyo taga bama ita yake kallo ba tamkar ba shi yayi maganar ba, haka ta ƙariso ta zo ta ajiye kayan jikin ta a sanyaye ta miƙa zata bar gurin ta ji ya ƙara ce mata i am sorry, da sauri ta ƙara waigowa ganin shi tayi yana rubutu kan shi a duƙe tamkar ba shi yayi maganar ba don dai kawai ta riga ta riƙe muryan shi ne a kwakkwalwar kan ta da zata ce ba shi yayi ba, tunanin yake yi meyasa yake yi ma yarinyar nan haka duk da yana jin ta tamkar ƴar uwar shi ta jini, tsaki ya ja to shi meye ma haɗin shi da ita, shi ya tsane mutum wanda ya cika shegen surutun tsiya, wata zuciyar kuma ta ce ai tana da kirki gashi tana kama da Kaka, kai haba ta ina ma taga kyan kaka, haka ya dunga tunani har malami ya shigo ajin na su.
Bayan tashi makaranta yau Abdallah ya zo ɗaukar ta saboda Anwar sun tafi wani Excussion, "yauwa Akheee kaga wanda ya shiga taxi ɗin can don Allah mu bishi kagani in nuna ma wani abu."
"Ayrah kina da matsala wallahi."
"Please Akheee."
Ta ƙarasa maganar tana dunkula hannu alamar roƙonshi.
*************************
NIGERIA KADUNA
Likita ne tsaye a kan matar yana goge mata gurin ciwon da ke gefen cikin ta in da da ka kalli gurin zaka san ɗin ki akayi, bayan ya gama kwance ɗinki ne ya fara dressing ɗin gurin har ya kammala ya basu magungunar da ya kamata ta sha ya musu bayani ya fice wata dake tsaye kusa da Namiji ta fita sai gata ɗauke da tray ɗin abinci da ruwa ta ajiye a gaban matar suka fice suka kulle kofar, girgiza kai matar ta yi ta ɗauki abincin ta fara ci.
"Barrister Zainab tafiya zuwa Taraba ya kamani yanzu haka ina hanya ina so zan je in ga yarinyar Hajiya Saudat domin akwai tanbayoyin da zan mata, shiyasa na kiraki in faɗa miki ki kulamun da office ɗina insha Allah jibi zan dawo."
"Ok karki damu ƙawata sai kin dawo."
Suna gama wayar Barrister Zainab ta tashi da sauri ta buɗe wani drawer ta ɗauko number waya ta fara sawa a wayar ta da sauri da sauri, bugu ɗaya yayi aka ɗauka, "hello eh ni ce Barrister Zainab ƙawar Barrister Khasheefat, eh yanzu haka ta kama hanyar zuwa Taraba don yanzu mukayi magana da ita, saboda haka kusan duk yadda zakuyi ku hana ta zuwa, don akwai matsala sosai in har ta isa zata iya fahimtar wani abu daga gurin yarinyar nan, domin ita ɗin gwanace a gurin bincike, ok tom ba damuwa sai na jika rankaya dade.
*************************
"Umma ina buƙatar addu'ar ki agareni domin addu'ar ki shi ke sa nake ƙara samun nasarori a rayuwata, insha Allah yau na ke son zan tafi Taraba yin wani bincike amma jirgin karfe huɗu zan bi shiyasa na ce bari in zo in faɗa miki, ki mun addu'an da kika saba domin addu'an uwa karɓaɓɓene ga ƴaƴan ta."
Murmushi ƴar farar tsohuwar tayi ta ƙara gyara zaman farin medical glass ɗin da ke idon ta ta ce, "Khasheeefat ba zan taɓa gajiyawa da miki addu'a ba domin ke ɗin ɗiya ce tamkar da dubu a ko ina zan bigi ƙirji in nu naki a matsayin ƴata da na ke alfahari da ke a duniya, wacce na san ko bayan rai na na bar baya mai matuƙar anfani, duk da ba'a shedan yaran yanzu amma nikam ina shaidar ƴa ta na bata tarbiya na koyar da ita gaskiya da ruƙon amana na bata ilimin addini da na zamani, na haneki da cin hanci da rashawa ko cin haram duk ƙanƙantanshi, domin har na gama aikin gwammnati na a matsayin shugaban lauyoyi ban taɓa karɓan cin hanci ba, ina fatan ƴata ma zata kasance haka, Allah ya miki albarka ya kareki a duk in da kike ya baki miji nagari wanda zai riƙemun ke da amana domin duk duniya kece dangina, ban da kowa sai ke sai Allah."
Umma ta ƙarisa maganar tana mai zubar da kwalla, ta ke jikin Khasheefa yayi sanyi, ta rungume Umma tana mai share mata hawaye, "kiyi haƙuri Umma komai na duniya mai wucewa ce ya ci a ce kin cire wannan damuwar a ran ki."
Bayan wasu awanni Khasheefat ne ta fito riƙe akwatin ta tayi ma Umma sallama ta kama hanyar Airport, tana zuwa minti biyar jirgin su ya ɗaga sai Taraba.
*************************
CAMEROON
Sosai Daddyn Amal yake kallon Didi shi dai yasan fuskar nan, amma ya rasa ina ya san shi bayan Didi ya farfaɗo ya ga Amal, da sauri ya miƙe ya cire ƙarin ruwan jikin shi ya ɗauki Amal yana ta cillata sama yana dariya, ita ma dariyan ta ke yi, can ya sauke ta ƙasa suka fara rawa da fareti sosai Daddyn Amal da Nurses suke kallon su cike da burgewa da mamakin irin wannan shaƙuwa na su, doctor ne ya kalli daddyn Amal yace, "tun da ma mara lfiya ya ji sauki kawai za'a sallameshi, ga takardar magungunan shi kuje ku siya sannan wannan takarda biyan kuɗin gado ne kuje ku biya shikenan sai ku zo office a baku takardan sallama, da sauran wasu shawarwarin da ya kamata a dunga kiyayewa domin sanyi ya fara kamashi."
"Ok Doctor bari in je in biya in dawo, baby Amal zo muje a siyomai magani mu dawo."
"A'a Daddy ni ba zan tafi ba Didi ya ƙara guduwa ya barni ka je ka dawo sai mu ɗaukeshi mu tafi da shi gidan mu."
Girgiza kai Daddyn Amal yayi ya fita yana mamakin irin wannan shaƙuwa tsakanin Amal da wannan mahaukaci da basu haɗa komai da shi ba.
*************************
DUBAI
Da gudu Mubasshir ya ƙariso ya tare kaka da take shirin faɗuwa, tuni jikin Ayrah ya fara rawa duk ta ruɗe, ajiye kaka Mubasshir yayi a kan kujera ran shi a ɓace ya nufo Ayrah gadan gadan da gudu ta juya ta nufi mota tana zuwa ta ce ma Akheee Abdallah "mu tafi akheee da sauri kar wancan ya ƙariso, da sauri Abdallah yaja motar yana kallon fuskar ƙanwan ta shi da take firgice, kallon ta yake cike da tuhuma, "Ayrah mai kika je kika aikata.?
"Akheee kayi shiru."
Ta ƙarasa maganar tamkar wacce zata fashe da kuka, girgiza kai kawai yayi ya cigaba da tuƙin shi kasancewar shi mai sauƙin ƙai bai cika shiga abun da bai shafeshi ba ko aka nuna ba'a son ya sani.
Cikin huci Mubasshir ya koma yana mai yayyafa ma kaka ruwa wani irin ajiyar zuciya ta saki ta ɗaga ido tana kallon Mubasshir sai taji gaba ɗaya ya bata tausayi kwana biyun nan gaba ɗaya ta kasa kwantar da hankalin ta balle na shi ya kwanta, ta kai ta kawo yanzu har gizo ƴar uwar ta Hasseenat ta ke mata, wanda rabon ta da ita shekara arba'in kenan.
"Kaka mene yarimyar nan ta miki ne, ki faɗamun wallahi sai na hukuntata."
"Mubasshir da gaske dama wata yarinya ta zo gidan nan ba gizo take mun ba."
Zaro ido yayi yana kallon Kakar ta shi cike da mamakin abun da ta faɗa, "dama kaka kin san ta ne.?
"A'a b,a,n san ta ba."
Kaka ta ƙarisa maganar tata a rarraɓe tana zare ido.
Suna shiga haraban gidan Ayrah ta buɗe mota ta fice ko jakar makaranta bata ɗauka ba ta shige direct sai ɗakin Mommah tana zuwa ta faɗa jikin Mommah ta saka ihu, sosai hankalin Mommah ya tashi ta rungumeta tana tanbayarta da ido sai da Ayrah tayi kuka mai isar ta sannan ta dago ta ce ma Mommah, "ki zo mu je kiga wata Mommah irin ku ɗaya sai dai ita baƙar fata ce kin fita haske da ƙiba, zaki je in ce Akheee Abdallah ya kaimu.?
Ɗaga kai Mommah tayi, tsalle Ayrah ta yi ta fita da gudu taje ta dunga roƙon Abdallah ya ce ma ta kin san dai ba in da ake fita da Mommah sai dai Asibiti in su Ummi da Hajjah suka dawo basu gammu ba fa,? "ba abun da zai faru Akheee insha Allah zamu dawo kafun su dawo."
Fitowa sukayi suka tabbatar ba wanda ya gansu suka sa Mommah a mota suka fice daga gidan na su, suna fita su Hajjah na dawowa.
*************************
NIGERIA TARABA
Bayan Barrister ta sauka a hotel ta yi sallolin da ake bin ta ta zauna tana azkar kasancewar dare yayi sosai lokacin tea kawai ta sha ta haye gado tana addu'a sai barci.
Zaune take tana duba wasu takardun can ta kirata wata vedio call ta ce mata, "Mary ya ake ciki ne, nifa gaba ɗaya ina ji a jikina Momy tana nan da rai bata mutu ba, shiyasa gaba ɗaya hankalina ya ƙi kwanciya, amma ina so in zo Kadunan gobe ko jibi ina ta dai shirya plan ɗin yadda zan baro wannan ƙaddararren garin aikin banza an zo a ajiye mutum ana takura mai.!
Ta ƙarasa maganar tana jan zakii, can ta tashi ta gama haɗa kayan ta tass a wani ɗan trooley ta kwanta da shirin gobe da safe sai kaduna saboda ta riga tayi booking jirgin karfe shida na safe.
*************************
KADUNA
"To wai ke Marry garin yaya aka samu akasi haka kin san an ce awa 48 zata dawo cikin hayyacin ta kuma an riga an gama tsara komai akan lokacin na cika zakuje ku tono ta ya akayu kuka bari wasu suka tone ta, ga shi ita matar nan da muke zargin da sa hannun ta har yanzu taki faɗin komai."
"Wallahi oga ni kaina na ji mamaki yadda akayi har wani ya gano plan ɗim mu, amma zamu binciko duk yadda aka haihu a ragaya."
"Amma na ji mamaki wallahi da ka ce mun ba tabi mota ba, kuma ni a motar ta ta ce zata tafi fa, kasan wannan shegiyar matar akwai bala'in wayau amma ka bari zan ƙara dukan ruwan cikin ta mujji in jirgi zata biyo ta dawo sai a san yadda za'ayi, ok nagode yallaɓai.
Hajiya Hindu ne zaune a cell ɗin a raɓe a gefe ga jikin ta duk tabon duka, ga rashin barci gaba ɗaya ta lalace ga dangin ta gaba ɗaya ba mai zuwa in da take balle a kawo mata abinci, gashi an haɗata da tatattun mata irin ƴan duniyan nan, ranar tana ji tana gani su ka banƙareta suka biya buƙatar su da ita bayan haka suka lakaɗa mata duka, haka suke mata duk daren Allah, su biyar ne ita na shida duka sai sun biya buƙatar su da ita sannan su daka, hakan yasa har fargaban dare take ya zo, kullum cikin nadama take saboda abin da bata taɓa aikatawa ba tun da ƙuricciyar ta wai ta nemi mace ƴar uwar ta sai gashi wai tana ji tana gani ƴaƴan cikin ta suna aikata mata hakan tayi magana ta ci duka, ta kai ƙara gurin ƴan sanda ko bi takanta basuyi ba kasancewar tana gani wani a cikin su zai zo ya ɗauki wata a cikin ƴan matan su rage dare wataran ma sai asuba ake maidosu da abincin su mai rai da lafiya, yayin da tana gani suna ci ko loma ba zasu bata ba.
*************************
NIGERIA TARABA
Fitowa Aneesa tayi riƙe da trolley ƙarami a hannun ta tana ja dai dai fitowar Momy Hafsat, tsayawa tayi tana kallon ta fuskar ta ɗauke da mamaki, "My baby ina zaki haka da sassafe riƙe da travelling bag.?
Jikin Aneeesa ne ya fara rawa sai kuma zuciyar ta ta fara gargaɗin ta tana faɗin ki natsu Aneesa karki sa ta zargi wani abu a gareki, marairaice fuska tayi tana faɗin, "Momy ina son zanje kaduna ne ance exam ɗin mu ya fito, sannan kuma ina kewar can don Allah kar ki ce zaki dakatar da ni na roƙeƙi Aunty ta," ta ƙarisa maganar haɗe da yin fuskar tausayi idanuwan ta na cikowa da kwallah, girgiza kai Aunty tayi cike da tausayin yarinyar ƴar uwar tata, domin kullum ƙara tausayin Aneesa takeyi musamman ganin in da kullum take ramewa ta ke lalacewa, ga shi har yau taki sakin jikin ta, "shikenan Aneesa kije Allah ya tsare amma ki tabbatar kina sauka kin kirani."
Da sauri ta rungume Momy Hafsat tana faɗin, "thank you Momy, sai na dawo."
Sosai Momy Hafsat ta ji daɗi ganin yau Aneesa tayi farin ciki tun bayan rasuwar Mahaifiyar ta, da kallo ta bita har ta fice ta bita da sauri ta ce bari driver ya kaita Airpot.
Ta tafi da awa biyu sai ga Barrisster Khasheefat ta iso gidan kasancewar ta samu address ɗin gidan tun daga kaduna, tarba ta musamman Momy Hafsat tayi ma Barrister kasancewar Momy Hafsat akwai kirki sosai, bayan ta kammala ne ta gabatar da kan ta ga Momy Hafsat da kuma abun da ya kawota cewan tana so ta tattauna da Aneesa zata mata wasu tanbayoyi.
"Ayyah Barrister gashi kun sha bam-bam domin yau Aneesa ta tafi kaduna."
"What kaduna kuma amma Hajiya me taje yi kaduna,? "eh to ta ce mun dai wai jarabawar su ya fito sannan tana kewar kaduna tana so ta je ta ɗan ɗebe kewa."
Girgiza kai Barister Khasheeefat tayi ta ce, "tabbass hasashe na yana son zama gaskiya Hajiya, amma don Allah zan iya miki wasu tanbayoyi.?
"Sosai ma kuwa Barrisster mai zai hana ina sauraran ki."
"Yau kimanin sati biyu kenan da rasuwar marigayiya, shin zaki iya faɗamin alaƙar ki da ita,? "marigayiya dai ƴar uwa ta ce uwar mu ɗaya uban mu ɗaya da ita, ita ce autar mu."
"Masha Allah, amma daga lokacin da ƴar uwar ki ta haifi ƴar ta Aneesa har zuwa yau baki taɓa lura cewa ƴar batayi kama da kowa ba kaf cikin zuri'ar ku har zuwa dangin mahaifin ta, sannan a ɗan zaman nan da kukayi da ita baki fuskanci wasu halaye a tattare da yarinyar ba.?
"In ban da abinki Barrisater so nawa akan yi haka, kiga mutum ya haifi ɗa bai yi kama da shi ba, balle wani a cikin dangi, kawai dai mu abin da muka ɗauka daga Allah ne, sannan kuma gaskiya ɗan zama na da Aneesa banga wani abun aibu ba game da ita, yarinya ce dai mai son shiru shiru bata da hayaniya."
"Ok Hajiya ko zan iya ganin ɗakin da take,? "ba damuwa zo muje."
Tashi Barister tayi ta bi Hajiya zuwa ɗakin da Aneesa take zaune, kallon ɗakin Barrister takeyi ko ina da ina can ta nufi drawer da ke ɗakin, ta buɗe wayam suka gani ba komai a cikin drawer zaro ido sukayi a tare Barrister ta waigo tana kallon Momy, ƙarisowa Momy tayi ita ma tana kallon drawer cike da mamaki, "Hajiya dama Aneesa ba zata dawo bane naga ta kwashe kayanta gaba ɗaya, me hakan ke nufi.?
"Ni kaina mamakin da nakeyi kenan, me hakan ke nufi, kuma ni ƙaramin jaka naga ta fita da shi fa amma abun da mamaki.!
"Shikenan Hajiya nagode ni zan koma, ba damuwa."
"Tom Barrisster Allah ya tsare ya kiyaye hanya ya bada sa'a."
Momy ta ƙarisa maganar jikin ta sanyaye ta biyo bayan Barrister suka fito.
*************************
KADUNA
Saukan Aneesa Airport yayi dai dai da isowar Su Marry da jerry, dukan su basufi sa'oin Aneesa ba yarane ƙanana ƙarisowa Aneesa tayi gurinsu fuskarta ɗauke da murmushi, "hi freand," "well come freand."
Cewar Jerry yana miƙa mata hannu suka gaisa, ƙarisawa jikin motar da suka zo da shi sukayi shiga sukayi suka fice daga Airpot ɗin.
*************************
Wata matashiyar budurwace wacce ba zata wuce shekara talatin ba ta turo kofa ta shigo, bakin ta ɗauke da sallama, ɗago kai matar da take zaune a kan sallaya tayi tare da amsa mata sallamar.
"Hajiya sannu da hutawa, ya ƙarfin jikin kuma.?
"da sauki ƴan mata, dama ina so in tanbayeki ne, wai ya akayi na zo nan sannan me ya sameni a gefen cikina kamar yankar wuƙa.?
Murmushi budurwan nan tayi sanan ta gyara zama, "Hajiya labari ne mai tsawo zan faɗa miki amma ba yanzu ba."
"Amma meyasa ba zaki faɗamun yanzu ba, sannan meyasa kullum kuke kulleni a ɗaki kunki barina in tafi ko in san a ina nake, kun ki bani waya in kira kowa nawa, ina so in ji halin da ƴata take ciki, ban kuma san tsawon kwana nawa na ɗauka a hannun ku ba, in kuɗi kuke so ko wani abu ku faɗamun mana."
Murmushi budurwan ta ƙarayi, "hajiya karki damu lokaci kaɗan ya rage, ƴar ki kuma tana cikin ƙoshin lafiya yanzu haka yau ta sauka a kaduna daga Taraba gurin ƴar uwar ki, na barki lafiya."
Da kallo matar ta bi yarinyar kafin ta miƙe ta nannaɗe daddumar ta koma bakin gado ta zauna ta rafka tagumi.
*************************
Zaune suke su biyar Aneesa ta haɗa rai tana ta masifa, kowan su ya yi shiru, shigowar wani mutum ne babban mutum kuma yasa dukan su suka miƙe kallon shi Aneesa tayi ta ce mai, "especter ya ake ciki akwai wani imformation ne.?
"Eh to yanzu haka Barrister Khasheefat ta je Taraba, tun shekaranjiya na so in faɗamiki na dunga kiran wayar ki bai zuwa, to ashe ma kin baro can ɗin, bana so ku haɗu da ita kwata-kwata don ita ɗin akwai basira da kwarewa in har kai ka kasance mara gaskiya in dai kuka haɗu saai ta gano ka, gashi yau saura kwana biyar a shiga kotu."
"Espector kenan kar ka wani ji ka damu ko mu haɗu da ita ko kar mu haɗu duk ɗaya saboda duk wayanta bata isa ta gane waye Aneesa ba domin ni na fi dila wayau ma, yanzu ya batun maigadin gida kunyi waya da shi kuwa, fatan ba damuwa.?
"Eh to munyi waya da shi ya faɗamun Barrister fa ta je gurin shi amma dai bai yarda ya ce komai ba."
"Shikenan yanzu muje in ga matar nan sai mu san wani mataki ya da ce in ɗauka a kan ta.
Duka suka dunguma suka nufi ɗakin da aka kulle matan.
*************************
DUBAI
Papa ne ya ce ma Hajja, "wancan kamar su Mommah yara ita da su Abdallah ina zasu.?
Papa ya faɗa cike da ruɗewa ya juya kan motar ya bisu da gudu ya sha gaban motar na su suka taka wani birki saura kaɗan suyi karo, a firgice suka fito daga motar Ayrah na riƙe da hannun Mommah, Papa ya buɗe ran shi ɓace yana isowa ya tsinke Abdallah da mari ya ɗaga hannu zai ƙara mai Hajja ta riƙe shi, "haba Papa ka tsaya ka tanbayi ina zasu mai ya fito da su mana.
"Yaron nan bai da hankali, yana sane ba lafiya ce da ita ba ina zai ɗauketa ya kaita, in ita da Ayrah basu da hankali shima bai da hankali ne, zaku wuce muje gida kokuwa"
Dafe da kumatu Abdallah yake yana wassafa irin dukan da zai ma Ayrah don ita ta ja mishi, ita ko Ayrah ba in da jikin ta bai rawa ta rungume Mommah sosai, tana jin tsoron kar ta samu nata rabon.
Bayan kwana biyu abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa har da marin da Mubasshir yayi wa Ayrah da warning sosai akan karta ƙara shiga harkan shi, kuma hakan bai sa tayi zuciya da shi ba kullum cikin ƙara burgeta yakeyi.
In da gefe guda kuma komai ya koma dai dai tsakanin kaka da Mubasshir suna zaune cikin walwala kaka ta sauke duk wata damuwa saboda wanzuwar farin cikin Mubasshir in da in ta koma ɗaki gefe guda zata ci kukan ta ta share hawaye.
************************
CAMEEROON
Daddyn Amal ne ya yi parking motan shi a haraban gidan su in da Amal da Didi suka fito daga motar suka nufi wani ɓarayi na daban a gidan dama kafin su dawo ya riga yayi waya cewa a gyara mai shashin boys queters nan ya kai Didi da kan shi ya taimaka ma Didi yayi wanka ya bashi wasu kaya ya sa ya watsar da yagaggun da ya cire ya kawo abinci ya bashi kin ci yayi sai da Amal ta sa hannu sannan shima ya sa ya fara ci, sosai Daddyn Amal yake jin tausayin Didi ya kuma yi alƙawari zai taimake shi insha Allah da iya ƙarfin shi, bayan ya kammala ya kamo hannun Amal zasu fita da sauri Didi ya taso ya biyosu, da kyar da ya lallaɓa Didi da Amal suka rabu zasu fita kenan sai ga Momyn Amal ta shigo ta dawo daga gurin aiki, ai zabura tayi ta koma bayan daddyn Amal ganin Didi ya na zazzare ido nuna shi ta farayi da hannu tana faɗin, "daddyn Amal mai ya kawo mahaukaci gidan mu ka fara jajibe-jajiben naka ko kai da ƴar ka, wallahi ba zan zauna gida ɗaya da mahaukaci ba ya je ya naƙasani sai dai ku zaɓa ko ni ko shi.
*************************
NIGERIA KADUNA
Yau ta kama monday 20/6/2022 misalin ƙarfe takwas da rabi na safe, yau ne ake gabatar da shari'a akan mutuwar Hajiya Saudat Mubasshir mailafiya a babban kotun da ke cikin garin Kaduna, kotu ta cika makil har waje jama'a ne in bakajin ƙarar komai sai na fankoki da yake aiki, in da mgatakarda ya miƙe ya fara magana kamar haka, "yau ne kotu zata saurari ƙarar Aneesa Mubasshir Mailafiya in da take ƙarar Mahaifiyar Baban ta wato Hajiya Hindu Usman mailafiya akan zargin ta da ta keyi gurin kashe mata mahaifiya nagode."
Magatakarda ya ƙarisa magana yana miƙama Alƙali takardun hannun shi sannan ya duka alaman girmamawa sannan ya zauna, in da alkali ya umarci lauyoyi su tashi su gabatar da kan su, Barrister Mansur ne ya miƙe, "sunana Barrister Mansur iliya nine lauyan wacce take ƙara nagode."
Shiru kotu tayi na ɗan wasu daƙiƙu, Alkali ya ɗago kai ya ce, "ina lauyan wacce ake ƙara.?
"Bata iso ba ya mai girma mai shari'a.
Cewar Barrister Mansur yana wani sake murmushi mai ɗauke da ma'anoni.
*************************
Sosai take gudu a motar tata tamkar zata tashi sama saboda lura da tayi cewa tamkar wasu na binta duk basajar da tayi na fitowa da motar mahaifiyar ta saboda irin haka amma sai da aka samu matsalan da ta guda canza hanya tayi ta nufi hanyar Murtala squre madadin ta bi Ahmadu Bello way sosai take gudu yankewa ta kuma yi ta bi ta Sultan road tana hawa titin sultan road kasancewar safiya ce ba cunkuson mutane hakan ya sa suka cimmata suka sha gaban ta kaɗan ya rage su bugi juna ta taka birki da sauri futuwa sukayi suka zagaye motar, fitowa ita ma tayi tana binsu da kallo, "lafiya kuke ta bina tun ɗazu.?
"Oh baki ma san meyasa muke binki ba ko? kawo takardun da kike ƙoƙarin zuwa kotu ki gabatar da shi a matsayin shaidu."
Murmushi Barrister Khasheefat tayi cike da rashin tsoro ta ce, "ba zan bada ba ɗin.
Bata gama rufe baki ba ɗayan dake ta bayan ta ya kwaɗa mata ƙarfen da ke hannun shi tuni ta faɗi ta sume a gurin da sauri suka nufi motar tata suka fara bincikewa sai da suka kwashe duk wasu takardu da ke cikin motar suka dawo suka ɗauki wayar ta da ke yashe a ƙasa sannan suka juya suka fita suka haye motar su, suna barin gurin Barrister Zainab ta ƙariso gurin da gudu a ruɗe ta fara girgizata, da sauri ta kinkimeta ta ɗora ta akan mota ta ja ta nufi asibitin da suka fi kusa wato Garden City hospital.
*************************
KOTU
Bayan shafe wasu mintoci da Alkali yayi ba tare da ya tanka ba, sai can ya ɗago ya fara magana cewa, "shin wacce ake ƙara tana da wani uzuri da zata gamsar da kotu game da rashin isowar lauyan ta har tsawon wannan lokaci.?
Alkali ya ƙarisa maganar shi yana kallon Hajiya Hindu da ta koɗe ta ƙanjame tamkar mai ciwon ƙanjamau, dukar da kan ta tayi ta ce "ya maigirma mai shari'a ina rokon wannan kotu mai albarka da ta taimaka a ɗaga shari'an nan har zuwa wani ɗan lokaci domin sanin mai ya hana lauya ta zuwa, duk da nasan cewa akwai kwakkwaran dalili domin ita ɗin jajirtacciyace hakanan ba zata ƙi zuwa ba dalili ba."
"Ba zai taɓa yuwuwa ba takan rashin zuwan lauyan ki da tayi da gangan ba wani dalili a ce a ɗaga mana shari'a hakan ya nuna cewa baku da gaskiya kenan daga ke har lauyan ta ki.!
Barrister Mansur ya faɗa haka cike da kumfar baki, nan da nan kotu ta kaure da hayaniya kowa na faɗin albarkacin bakin shi in da da yawa daga cikin mutane zagin Hajiya Hindu akeyi, ita ko sosai a gurin ta ke ƙara jin wani tarin nadama na ƙara shigarta Nadaman da baida amfani agareta, Alƙali na ya buga gudumar shi alamun ayi shiru nan da nan kotu tayi tsit, Alƙali ya fara magana cewa "wannan kotu mai adalci ta ɗaga wannan shari'ar zuwa nan da 24/6/2022 bisa roƙar alfarma da wacce ake ƙara tayi, sannan kai kuma Barrisster Mansur ka kiyaye harshenka gurin yi ma kotu katsalandan a cikin abun da bai shafeka ba don gaba ka ƙara irin haka kotu zata cika tara haɗa da ɗauri."
Alƙali na gama magana ya buga guduman shi gabaɗaya kowa ya miƙe, nan mutane suka fara firfita bayan alƙali ya fita kowa da abun da yake faɗi, yayin da ƴan sanda suka tasa ƙeyar Hajiya Hindu suka tafi da ita.
*************************
0 comments:
Post a Comment