Babu abunda ta fasa daga cikin aikin gidan da ta saba, ta sani sarai idan ta saka kuiya ko tace ba zata iya ba wani karin wahalar ne. Tana aikin tana kukan zuci har ta yi ta gama, ta dawo dakinsu ta zauna ta gefe daya dan bata iya zama daidai.
Tumba ce ta shigo dakin tana kare mata kallo.
鈥淏a za ki tashi ki je gurin aikin ba?鈥�
Kallon Tumba tai kamar zata fasa kuka, bata jin abunda ta ce sai dai tana ganin bakinta na motsi.
鈥淏an ji komai ba Umma鈥�
Ta fada muryarta na rawa kamar yadda jikinta ma yake rawa dan ganin take kamar dukanta Tumba za tai ko ta sake mata wani mugun sherin. Wani kallo Tumba tai mata.
鈥淣i za ki fara yi wani sabon siyasa?鈥�
Ganin Tumba ta nuna kanta da yatsa yasa ta nemi duk inda wani kuzari yake ta tattaro shi ta saka a jikinta ta mike tsaye ta karasa kusa da Tumba dan jin abunda take fada.
鈥淲allahi ban ji me kika ce ba Umma bana ji sosai鈥�
Ta fada kamar zata fasa kuka, Tumba ta san Falmata ba zata mata karya ba, ba zata mata haka da gangan ba, yanayinta kadai ya isa ya sanar da gaskiyarta.
Tumba ta dan tabe baki, sai a lokacin ne take girmama marin domin ba marin wasa Baba yai ma Falmata ta ba, gashi fuskarta har ya kumbura.
鈥淐ewar nai ki tashi ki tafi aikin鈥�
Tumba ta fada cikin daga murya ta maimaita mata ta yadda za ta ji. A take Falmata ta fara murza yatsun hannunta so take ta sake tuna mata cewar sun koreta amman sanin waye Tumba yasa dole tai shiru ta sauke kanta kasa.
鈥淏a za ki je, ki ba su hakuri ba?鈥�
Wannan karon ta ji domin Tumba da karfi tai maganar.
鈥淭o鈥�
Amsa tana motsa jikinta daker domin ba karamin tsami yai mata ba. Tumba ta juya ta fice daga dakin. Falmata ta nufi gurin da Hijabinta yake ta dauka ta saka ta fito. Da gangan Tumba ta kira ta karbi dumamenta ganin Baba na tsaye yana shirin tafiya.
Falmata ta nufi inda Tumba take da zimmar karba ba dan ta ji abunda tace ba sai dan ganin tana miko mata kwanonta. Ba dan tana jin yunwa ba domin komai ya fitar mata a rai, kan ta karasa Baba ya daka mata tsawa.
鈥淜ar ki karbi abincin nan, ba za ki sake cin abincin gidana ba, tun da kika zabi iskanci....鈥�
Cak Falmata ta tsaya ta kasa karasawa gurin da Tumba take zaune taka miko mata dumamen, ta ji abunda Baba yace saboda yanayin muryarsa irin mazajen nan da idan suna magana daga murya suke, balle kuma ita da baya iya yi mata magana a hankali.
鈥淗aba Malam ba a horo da yunwa, na san Falmata ta yi laifi amman ka dubi girman Allah ka yi hakuri, ba a biye ta yaro鈥�
鈥淣i dai na fada miki ban yafe a bata abincin gidana ba, ba zan ciyar da karuwa ba鈥�
Ya fada kai tsaye sannan ya nufi kofar fita ko inda Falmata take be kalla ba. Baki sake Falmata ta bishi da kallo hawaye na sauko mata zuciyarta na mugun kuna, kamin ta kalli Tumba wacce ke kukan karya.
鈥淲allahi da na san haka abun zai zama da ban fada maka ba, wannan abu be min dadi ba ni Ramatu鈥�
Bata iya ji yo komai amman tana gani ganin yadda bakinta ke motsi ta san da kuma kukan murnafurcin da take, ta san ta shirya komai ne. Daker Falmata ta hade abun da ya tsaya mata a wuya sannan ta nufi kofar fita tana jin kamar ta mutu a yau ta huta, taya zata rayu a idan ubanta kuma ace ba zata ci abincin gidan ba? Miyasa Tumba zata mata haka? Me tai mata? Saboda ta fadi gaskiya? Mi ya kaita fada mata gaskiyar? Miyasa ma yasa ta aikata tun farko? Tana tafiya tana tambayar kanta tambayar da bata da amsa hawaye sai aikinsu suke a fuskarta.
Gidansu kawarta Khadija ta nufa, sa same a tsakar gidan tana wanki kasancewar yau assabar babu school, Khadija na ganin Falmata hankalinta yai mugun tashin.
鈥淚nnalillahi ke lafiya me ya same ki?鈥�
Bata ji abunda Khadija tace ba amman tabbas ta ga bakinta na motsi. Hakan yasa Falmata ta fashe da kuka, ta sani an nakasata kenan.
鈥淜hadija Umma ta min shari ta ce Baba ta ga namiji yana taba ni, Baba ya min mari biyu kuma ya doke ni, ya ce kar a sake bani abincinsa, Khadija bana iya ji yanzu sai an yi magana da karfi na shiga uku鈥�
Wani irin rirrike Khadijar take tana fadin kukan kan ya samu hanyarsa, a take Khadija ita ma ta fashe da kuka ita da kawarta aka rasa nai rarrashi wani. Mahaifiyar Khadija ta saki tsintsiyar hannunta tana hawaye.
鈥淲ai me kika tarewa matar nan ne? Wani irin zallumci ne wannan?鈥�
鈥淎llah ya isar miki Falmata Allah ya saka miki鈥�
Khadija ta fada cikin kuka, kamin ta kama kawar tata su nufi baranda su zauna. A gidan Falmata tai wuni Maman Khadija da Khadija suka kitsa mata idan ta koma ta ce wa Falmata taje gurin aikin ta ba su hakuri sun maida ta.
鈥淜ullun idan ta tura ki aiki ki dawo nan ki zauna sai lokacin komawarki gida yayi sannan ki koma, abinci kuma ki zo nan ki rika ci kullum鈥�
Maman Khadija ta fada mata a kunne cike da tausayawa, domin idan bata mata rada ba ba zata ji abunda tace ba. Falmata ta gyada kai.
鈥淣a gode鈥�
鈥淏abu komai ai yiwa kaine, wannan rashin imani na Tumba yayi yawa, ko dan tana ganin bata haifa ba ne take haka? Wannan wace irin zuciyata ce?鈥�
鈥淎llah zai saka mata In-Sha-Allah鈥�
Khadija ta fada tana sharewa Falmata hawayenta. Sai da Falmata ta auna lokacin komawarta sannan ta fita daga gidansu Khadija ta kama hanyar gida tana ta jin tsoro domin gani take kamar asirinta zai tonu Umma ta gano bata je aikin ba.
AA POV.
Tun shekaranjiya da yai hadari da Nana be sake fita aiki ba, ba dan kuma baya iya fitar ba, sai yai amfanin da accident din da yai yace musu ba shi da lafiya zai dauki sati yana jinya, tsoro ya cika masa ciki yana ganin kamar idan yaje zai iya haduwa da Nana ta kira wani tace gashi nan a kama shi wata kila ma Babanta Soja ne ko Alkali a masa daurin goro. Anti Rabi kam ba a magana domin ko kofar gidan aka taba sai ta ji kamar zuwa za ayi a tafi da ita da AA.
鈥淏abu irin gargadin da ban maka ba, amman baka ji ba, gashi nan ka je ka kwaso mana abu kai baka cikin natsuwa ni bana ciki鈥�
Kallon Anty Rabi yai yana murmushi, duk irin tsoro da fargabar da yake idan ya tuna Nana da yadda take wasu dabi'un sai ya samu kansa da annashuwa, ba laifi tana da wauta and he likes that ko dan kudin da take sake masa.
鈥淏abu fa wani abu Anti, da za su kamamu ai da ba za su kai yanzu ba a nemo inda nake ba, ina tunanin bata fada ba ne saboda ita ma bata da gaskiya ai鈥�
鈥淗mm ka sani ko ana can ana nemanka?鈥�
鈥淚dan nemana ake ai ta san gidan nan, kuma ta san inda na ke aiki鈥�
Ya fada har lokacin murmushi yake.
鈥淢aybe yar farin ce tana da wauta sosai鈥�
Ya fada a fili sannan ya mike tsaye, da gaske he miss her, Allah ka dai ya san irin karyar da tai, da kuma irin sakin da za tayi, no wait ta ma isa gida? What if inda ya barta wani abun ya same ta? Ko ta bi wani kamar yadda ta bishi, ai ba kowa ne na gari ba right? Idan ta nunawa wani kudi zai ma iya kidnapped dinta. A take hankalinsa yai mugun tashi wayarsa dake aljihunsa ya ciro ya chiga contacts sai a lokacin ya tuna ai shi ya bata number sa kuma bata kira shi ba.
Gaba daya sai ya ji ba shi da natsuwa tunaninsa be kawo masa haka ba sai yanzu, and if wani abu ya same ta shi ne sanadi, domin shi ya barta a gurin kuma ya san abunda yai be kyauta ba. Gaba daya sai ya ji hankalinsa yai mugun tashi, be bari Anti Rabi ta fahimci komai ba ya shiga dakinsa ya cire vest din jikinsa ya dauki wata bakar t shirt ya saka ya fito.
鈥淎nti bari na leka nan waje鈥�
鈥淭o Allah dai ya tsare idan ka ji baka natsu ba ka dawo gida dan Allah鈥�
鈥淥kay In-Sha-Allah鈥�
Sai da yai addu'ar fita daga gida sannan ya fita gidan. Kai tsaye gurin aikinsa ya nufa duk da ya san ba lallai ne ya ganta ba, sai dai sanin cewa tana yawan zuwa gurin wata kila ma an zo nemansa.
SHATTIMA POV.
Ya saba every end of the week yana ziyartar dakin motsa jiki, but wannan karon sati biyu be je ba saboda be samu zama ba. Hakan yasa yake jin jikin kamar ba nasa ba, tafiya yake a hankali kamar wanda baya son taka kasa da daidaiya yake bin ko'ina da kallo har ya shigo bangaren mahaifiyarsa.
A falo ya tararda yaransa, Iya na zaune kusa da su tana musu wasa sai dai gaba dayansu wani laye suke kamar basu jin bachi.
鈥淏abban Mutum an shigo?鈥�
Iya ta fada baki har kunne.
鈥淓h Iya ya gidan?鈥�
Ya amsa mata yana leka yaransa.
鈥淕ashi nan fa sun sha ado, yanzu na gama gyara dakinsu鈥�
Da mamaki ya kalleta.
鈥淢ai gyaran bata zo ba ne?鈥�
Iya ta tabe baki tana mikewa tsaye.
鈥淲annan yarinyar, bata zo ba, wata kila sai gobe ko jibi鈥�
Shattima be ce komai ba, but maybe dan ta kamata tana yi ma yaransa addu'a ne yasa ta ji tsoro ta ki dawowa.
鈥淜arka damu ba dole sai an kawo wata ba, ni kaina zan iya kula da su da dakinsu鈥�
Dan murmushi yai.
鈥淗aba Iya ai ba girmanki ba ne, idan bata dawo ba dai za mu samu wata鈥�
Iya ta yi murmushi tana kallonsa.
鈥淗aka ne Allah ya taimaka, bari na maida su dakinsu鈥�
鈥淎mman a samo wacce zata tsaya da su bana son a na barinsu su kadai鈥�
鈥淎n gama Babban Mutum鈥�
Ta amsa masa har da dan risinawa, shi kuma ya wuce dakin mahaifiyarsa. Kwance ya same ta waya a hannunta tana latsawa, sai da ya zauna sannan ya mika mata gaisuwa. Sai ta dago ta kalleshi.
鈥淟afiya Kalau Shattima鈥�
鈥淎mmy ina tunanin gobe zan koma鈥�
Bata ce masa komai a har na tsawon minti uku. Hakan yasa ya sake cewa.
鈥淎mman ba zan yi dadewar wacan lokacin ba zan dawo鈥�
鈥淵a dai kamata ka nemi transfer gaskiya, ka fi kowa sanin halin da mahaifinka yake ciki鈥�
Kwankwaso kofar dakin da akai ne ya hana shi cewa komai, be kuma dago ta kalli kofar ba, sanin wanda ya shigo dakin ba bayan Ammy ta ba shi umarni, kamshin turaren kadai ya isa ya sanar nasa cewer Sirleem ne domin ya san kalar turarensa kamar yadda Sirleem din ma ya san na Shattima. A kasa ya zauna yana mikawa Ammy gaisuwa sai ta amsa masa da murmushi tana kokarin tashi daga kwancen da take.
鈥淵a gida ya aiki?鈥�
鈥淎lhamdulillah, dazu Hajiya ke Fada min Nana ta samu accident鈥�
鈥淓h amman da sauki sosai鈥�
鈥淎llah ya tsare gaba鈥�
鈥淎min鈥�
After some minutes ya mike tsaye yana mata sallama.
鈥淪hattima ba ku gaisa ba鈥�
Daga shi har Shattiman ba su dadin maganar Hajiya ba. Domin kowa jin kansa yake ba ma kamar Shattima, ko da wasa Shattima be dago ya kalli Hajiya ba gudun kar ta masa umarni da ido cewar ya gaisa da Sirleem domin shi ya cancanci Sirleem ya gaushe shi ko dan neman auren kanwarsa da yake. Sirleem ya kasara inda Shattima yake zaune ya mika masa hannu sanin cewar idan za a shekara dari a haka Shattima ba zai ce masa uffan ba.
鈥淪hattiman ai ban kura da kai ba sai yanzu鈥�
Sirleem ya fada yana mika masa hannu. Hannun kawai Shattima ya mika masa suka gaisa ba tare da ya kalli Sirleem ba balle har wata kalma ta fito daga bakin Shattima. Sai da Sirleem ya nufi kofa sannan Shattima ya daga kai ya kalleshi, sai kuma ya dauke kai ya kalli mahaifiyarsa wace ke kallonsa tun lokacin da Sirleem ya mika masa hannun.
Sam Sirleem be jidadin abunda Shattima yai masa ba, ya sani ba tun yau Shattima ya saba nuna masa cewar shi ne dan masu gida shi kuma agola, ba shi kadai ba har Zainab wacce kusan matsayinsu daya da shi haka take nuna masa isa tana takama.
Kamin ya karasa fita falon Nana ta kira shi.
鈥淵a Sirleem鈥�
Juyowa yai ya kalleta be ce komai ba, sai da ta kalli kofar corridor dakin Ammy sannan ta karaso inda yake.
鈥淵a jikin na ki?鈥�
鈥淣a ji sauki, Ya Sirleem ban karya ba鈥�
鈥淲hy?鈥�
Ya tambaya cike da mamaki ganin har 5pm ta kusa ace bata karya ba. Sai da ta sake kallon corridor sannan ta ce.
鈥淒an Allah zaka kai ni restaurant na ci abinci? Amman karka tambayi Ammy?鈥�
Ya kalli inda take kallo sai kuma ya kalleta kamar ya musa mata sai kuma wata zuciyar ta hana shi.
鈥淎lright muje鈥�
鈥淜aje can bangarenku ka jira ni, bari na dauko mayafina鈥�
Har ta juya sai ya kira ta ta juyo.
鈥淣ana... An hana ki fita da ni ne ko me?鈥�
鈥淶an fada maka a mota kaje can ka jira ni鈥�
Bata tsaya jiran abunda zai ce ba ta koma dakin ta dauko kudin da Hajiya ta bata 20k ta saka a cikin skirt dinta sannan ta saka wani karamin veil ta fito da gudu kamar ba ita ce ke ciwon kafa ba. Kamar wacce tai wani kaifi take tsoron a ji haka ta sauka stairs din ta nufi bangarensu Hajiya gabanta sai faduwa yake kar tai arba da Shattima ko Zainab ko wani wanda zai fadawa Ammy ta fita tare da Sirleem.
Can bangaren Hajiya ta nufa sai dai bata shiga ciki ba ta nufi gurin da motocin gidan suke, tun kan ta karasa ya bude mata front seat tana shiga ta rufe motar da sauri.
鈥淴&Y restaurant za mu je, kuma ba fita za ka yi ba, ni zanje nai mana takeaway Please鈥�
Jinginar da kansa yai jikin motar yana kallonta. Can kuma ya tashi motar suka fara tafiya.
鈥淲aya hana ki fita da ni hala?鈥�
鈥淏abu鈥�
Da bashi amsa tana taba kudin da ta boye jikinta dan ta tabbatar idan suna nan.
03/12/2021, 08:22 - 馃馃馃馃: *馃悇馃悇 FULANI 馃悇馃悇*
By Khadeeja Candy
*10*
FALMATA POV.
Haka ta kwana da ragowar yunwa a cikinta, washe gari tun da asubar fari Tumba ta fito ta fara kunna wuta a lokacin Falmata na waje tana alwala sallah asuba, baya ta gama ta shiga daki ta dauki hijabinta zata saka tai sallah sai ta ji an rikota sakamakon kiran da ta yi ta mata bata ji ba.
鈥淜arki sallah bari ki yi wanka鈥�
Ta rada mata a kunne, ba ta isa tace mata bari na gama sallah ba, dan haka ta aje Hijabin ta fito bakin kofar dakin ta zauna tana ta kallon wutar da Tumba ke ta aikin fetawa tana tura ledodi, nan da nan ruwan sukai zafi sai ta dauko wani garin magani ta zuba a cikin ruwa ta juya shi sannan ta sauke ta tsirka mata da ruwan sanyi.
鈥淶o dauki ga shi nan ki yi wanka maganin tsari ne鈥�
Tana maganar tana mata alama da abunda take nufi irin yadda ake ma kurame. Falmata ta tashi daga inda take zaune ta dauki ruwan maganin ta shiga bandaki ta cire kayan jikinta ta watsa ruwan ta fito. Da hannu tai mata a alama da ta zo, sai Falmata ta aje bokitin hannunta ta karasa inda take tsaye, duba ta tai dan ta tabbatar idan ta yi wanka, ga kuma shaida ta gani maganin ko'ina a jikinta.
鈥淭o je ki yi sallah ma鈥�
Nan ma alamar kurame tai mata, sai Falmata ta juya ta shige cikin dakin ta dauki wasu tufafin ta saka ta saka hijabinta ta fara sallah.
Bayan ta gama tai addu'ointa kamar yadda ta saba sannan ta fito ta gyara ko'ina na gidan tai wanke wanke, ba ta ko tsaya tambayar abincinta ba ta fice da zimmar zuwa gurin aikin karya.
Tana tafe tana nemawa kanta mafita, ta sake komawa gidansu Khadija ko kuma dai ta koma gurin aikin ta sake ba su hakuri? Domin idan wata yayi Tumba zata tambayi kudinta na albashi to me za ta ce mata? To idan ma ta koma za su karbe ta ne? Sai ta rasa wanda za tai, daga karshe dai ta yanke shawarar zuwa gidansu Khadija domin har ga Allah ita yanzu tsoron zuwa gidan can take, abun da bata sani ba Naja na biye da ita a baya tana lekenta kamar yadda Tumba ta saka ta. Sai dai ita bata lura ba har ta shige cikin gidansu Khadija. Yau kan bata samu Khadija a gidan ba dan ta tafi islamiyar safe kasancewar yau Sunday, Maman Khadija bata tsaya komai ba ta zubo mata abinci, Falmata ta zauna ta ci sai da ta koshi sannan ta nemi guri ta kwanta tai ta bachinta. Sai kusan azahar sannan Khadija ta tashe ta, firgigit ta mike tsaye dan lokacin komawarta gida yayi har ma ya dan gota.
Duk yadda Maman Khadija da ita Khadijar kanta suka so Falmata ta tsaya ta ci abinci sai ta ki gaba daya hankalinta ya tashi kar ta koma late Tumba ta doketa.
鈥淜o na zuba miki a leda?鈥�
鈥淚dan ta gani zata iya min fada鈥�
Duk da rada Khadija take mata maganar. Bata jira abunda Khadija zata sake cewa ba ta fice daga gidan hankalinta a tashe, da sallama ta shiga gidan Naja ta amsa mata tana tabe baki.
鈥淎she idan an tura ki aiki gidansu Khadija kike zuwa kina zaunawa ko? Ai na biki dazun na gani鈥�
Naja ta fada cikin daga murya ta yadda Falmata zata iya jinta. Wani irin bugawa gabanta yai da karfi, da zaro ido tana kallon kofar dakin Tumba sai ta nufo gurin Naja ta riketa.
鈥淒an Allah Naja karki fada, dan Allah ki rufa min asiri鈥�
Tana rufe baki Tumba na fitowa daga dakinta ta tsaya bakin kofa rike da kunkuru tana hararar Falmata, da sauri Falmata ta mike tsaye ta fashe da kuka, a take tsoro ya kamata ta rika ganin kamar Tumba dukanta za tai sai ta fara ja da baya baya tana ganin Tumba ta motsa ta fice daga gidan da sauri. Komawa tai gidansu Khadija ta zauna, a can ta wuni har dare ba ta fada musu abun da yasa ta gudo ba, sai dai suna ganin yadda hankalinta ya tashi sun ssn ba lafiya ba. Sai bayan sallah isha'i Naja ta zo kiranta, cikin rashin kuzari ta tashi suka fita daga gidan tare tun kan su karasa gida ta fara kuka.
Suna shiga cikin gidan fara rabawa jikin gina tana kallon mahaifinta dake watso mata harara.
鈥淕ata nan ashe idan an turata aiki gidansu Khadija take shiga, yau aikin komai ba tai ba can ta wuni, ni dai dan Allah ka yi mata tsakani da yarinyar ba ma yarinyar kirki bace Wallahi鈥�
Tumba ta fada tana narke murya kamar gaske.
鈥淲ato Falmata duk abun da za a fada miki ba kya ji ko? Kullum sai kin tsiro wani bakin hali ko?鈥�
Bata ji abunda Tumba ta fada ba amman ta ji abunda mahaifinta yace shi da yake da tsawa yake mata magana.
鈥淶o nan....鈥�
鈥淏aba dan Allah ka yi hakuri sun kore ni kuma ina tsoron komawa gidan da? Allah kai hakuri gobe zan je鈥�
Ta fada cikin kuka.
鈥淶o na ce....鈥�
Ta fara tafiya tana kuka tana kallon Tumba tana jin kamar ta taso ta zo ta cece ta, irin yadda mahaifiyarta take mata idan za a doke ta, gabansa taje ta tsaya ta rika hannunta ya murde iya kar karfinsa sai da ta fasa wani irin ihun ta fadi kasa.
鈥淲ayyo Baba Wayyo Baba dan Allah kayi hakuri, ka yafe min Baba karka kashe ni dan Allah鈥�
Sakin hannun nata yai ya rika hijabinta yaja ta daga inda take kwance har gurin da tumakinsu suke daure, ya kwance igiya daya ya daure mata kafa tamau, zai juya ta riko kafarsa.
鈥淒an Allah Baba ka yi hakuri, karka ba ni na kwana a cikin tumaki dan Allah Baba鈥�
Kasa juyowa yai kuma ya kasa tafiya har cikin ransa yake jin kukan yarsa idonsa suka cika da hawaye, amman sai ya ji ba zai iya mata komai ba bayan haka, fisge kafarsa yai ya fice daga gurin ya barta tana ta kuka. Tun tana kukan tana kiran sunansa tana bashi hakuri har koma kiran Tumba tana bata hakuri daga kashe sai ta hakura ta kwanta a gurin tana ta hawaye, ba hawayen kwana a gurin kadai ba har da hannunta da take jin kamar ya karye saboda mugun rikon da Baba yai ma hannun nata, ga kafarta da ya daure da karfen rodi ya tsuke mata kafar sosai.
Ba tai wani bachi kirki ba saboda kuka da ciwon hannu da kafa da kuma warin fitsarin dabbobin dake gurin, sai da rana ta fara fitowa sannan Tumba ta zo ta kwance ta.
鈥淣a gode鈥�
Falmata ta fada tana kallon Tumba da idanuwanta da suka kankance tsabar kuka da wahala, ba ta yi zaton za ta kwance ta wuri haka ba ya dauka ko sai ta kwana biyu ko fiye ma.
鈥淭ashi kije ki shirya ki tafi gurin aikin鈥�
鈥淭o鈥�
Ta fada jikinta na ta rawa wani irin sanyi take ji yana ratsata kamar zazzabi na son rufe ta. Duk yadda ta so tai wanka kamin ta fara yin sallah sai ta kasa saboda hannunta bata iya komai da shi ga kafarta ma dingishi take, haka nan dai ta wanke jikinta sannan tai alwala ta shiga dakinsu ta saka wasu tufafin tai sallah ta fito tana jin jiri na dibarta ta durkusa a wahale ta gaishe da mahaifinta.
鈥淏aba ina kwana?鈥�
Be amsa ba daman yana tsaye ne yana sauraren abunda Tumba take fada masa akan Khadija cikin tsawa ya ce.
鈥淏abu ke babu Khadija daga yau, balle har ki je gidansu, na miki tsakani da ita鈥�
鈥淭o Baba鈥�
Ta amsa masa tana jin kamar ba zata iya numfashi ba, ga idonta sai ciwo yake, mikewa tai tsaye bayan ta gaishe da Tumba ta nufi kofar fita kamar wata musaka ta fice daga gidan. Da kallo Baba ya fita har ta fice sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali ta yadda Tumba ba zata ji ya juya ya koma cikin dakinta.
Kai tsaye Masarautar Falmata ta nufa a ranta tana ta addu'ar Allah yasa su karbe ba, domin idan ba su karbe ta ba bata san yadda zata yi ba, kamar yadda ta saba sai ta gaishe da kowa take shiga ciki, sai dai bata tsaya jiran su amsa tun da ko sun amsa idan ba su kwarai ba ba ji za tai ba. Sai da ta kawo gate din da zai sadata da bangren Ammy cikin rashin
0 comments:
Post a Comment