鈥淲allahi kuwa鈥�
Ma'u da rufe baki tana zaro ido.
鈥淜uma Wallahi da gaske koko na sa da safen nan, Fulani da gaske kin iya鈥�
Wani kalar dadi ya kara rufe Fadime jin ta canki abun da Ma'u ta karya da shi yau, bayan ta gama fada mata ita tana da aljannu kuma suna sa ta gane komai na mutum.
鈥淵anzu kenan za ki iya fadawa mutum abun da zai same shi鈥�
鈥淓h amman sai na yi bachi, amman dan Allah Ma'u karki fadawa ko sai wanda kika yarda da shi, idan Bappa ya ji zai min fada ko ya doke ni ma鈥�
鈥淏a zan fada ba鈥�
Fadime ta yi dariya.
鈥淚nna tace masu irin wannan abun kudi ake ba su, idan kina ga wani na son a masa ya bada kudi ki kawo shi zan masa amman a boye鈥�
鈥淎iko zan ta kawo miki mutane Wallahi, sai ki sammin wani abu ni ma鈥�
Sai da hantsi ya bude sosai sannan Fadime ta bar kofar gidansu Ma'u ta dawo gida. Kai tsaye ta nufi bukkatarta ta dauko biro da littafinta ta fara rubuta hau Amo tace zata kawo mata miji, kuma ta fadawa kawarta Ma'u cewar tana dubi.
Gaba daya wunin ranar wuni tai cikin farinciki da jindadi kana ganinta kasan dadi take ji tana murna wai Amo ta mata miji kuma a bunni.
Amo dai sai kallonta take a ranta tana fadin
鈥榋aka si ubanka idan ka aureshi mutuwa za kai, idan ka gagaran ci ai ba ka gagari wani ba鈥�
Ta fada tana dan murmushi sai da Fadime ta mike tsaye tana kora shanu zuwa daji Amo ta lura yau wutar nan bata biye da ita, a razane ta mike tsaye tana bin bayanta da kallo.
Inna ma ta mike tsaye daga can cikin bukkar da take zaune tana kallon Amo, wacce razanar ta bayyana, Inna daman can ta dade tana zargin Amo da maita ba tun yau ba, tun daga lokacin da ta bata labarin cewar suna da maitar gado wacce ake bawa yara tun suna kanana amman ita Allah ya tsareta ba a bata ba, ga yayan wabin da Inna tai ta yi a duk inda take neman magani sai ace manya ce take cinye mata yaya, wani cikin ma tun kan ya zo duniya zata yi barinsa, Fadime ce kawai ta rayu ita ma daker dan babu kalar ciwon da ba tai ba, Allah ne dai ya rata ta da kuma addu'oin da take yawan yi mata, Bappa ma yana mata sosai har rubutu yake mata ya bata ta sha, tun a wacan lokacin idan Inna ta fada masa tana zargin Amo sai ya karyarta yace baya son tashin hankalin, har yake ganin kamar kamar Inna tana haka ne saboda Amo kishi, bayan kuma ita ta zo ta tararda Amo.
Sunsunsun Amo ta shige bukkarta da mugun mamaki, ta sani wani sa'in ana samun akasin abun da tai mata, sai dai ba ko yaushe ba, domin Fadime babu ruwanta da addu'a sai dai idan yi mata akai, kuma wannan wutar ta dade da saka mata ita tun Fadime na karama, taya yau rana daya za a wayi gari babu ta? Ko dai Inna ta karbo mata wani maganin ne? Idan ba haka ba gaya wutar ta bar binta? Adakin ta kasa zaune ta kasa tsaye sai safa da marwa take gaba daya hankalinta ya kasa kwanciya.
A kullum idan Fadime zata je kiwo sai ta saka shanun gaba tana binsu a baya, ban da kwana biyun nan da take son sake ganin Wasim, kullum baya take baro shanun sai idan sun kawo kansu. Tana isa ta haye saman dutsen ta fara kiransa.
鈥淢ai busa鈥�
Haka take kiransa a duk lokacin da ta iso gaban dutsen, duk kiran da zata masa kuma ba zata ganshi ba, ba zata ji busar ba, bata kuma fasa kiran ba. Sai dai shi yana saukowa kasa ne ya boya jikin dutsen yana kallonta har tai abunda za tai ta gama.
Sai da ta sauko saman dutsin sannan ta ganshi kasa tsaye ta inda zata ganshi yana kallonta fuskarsa da murmushi, dan tsoro ta ji.
鈥淜enan shi aljanin dutse ne?鈥�
Ta raya a ranta, a fili kuma sai ya kara hayewa saman dutson alamar ba zata sauko ba. Ganin hakan yasa ya fara haurowa saman dutsen still yana mata murmushi.
鈥淜a yi hakuri ni ba dan wani abu na kira ka ba鈥�
Ta fada tana kokarin sauka ta dayan bangaren, ganin hakan yasa shi ma ya juya ya sauka. Sai suka koma kallo kallo ita da shi, ta kira shi ne kawai ba dan tana da abun cewa ba, kuma bata san zai ji ta ba, tun da ta saba kiransa kwana biyu bata ji shi ba. Da hannu yai mata alama da ta zo sai ta kanne kafada alamar ba zata zo ba, ta girgiza masa kai. Zaunawa yai a gurin ta dauke kai daga barin kallonta. Hakan yasa zuciyarta ta raya mata cewar ko aljani ne shi ba zai cutar da ita ba tun da har mafarkinsa take. A da idan Inna tace mata tai addu'a sai tace mata wuya take ji, amman a yau da take son zuwa kusa da shi sai da ta tsaya ta karanta addu'oin data iya sannan ta tunkareshi tana takawa kadankadan kamar mai tsoron ya ji takunta, kansa na kasa har ta kawo kusa da shi ta risina ta leki fuskarsa, sai ya sakar mata murmushi ita kuma tai masa dariya irin dariyar nan ta dole kuma ta tsoro wacce mutum ke yi a rikice.
鈥淜ai aljani ne?鈥�
鈥淎a鈥�
Ya amsa mata yana dagowa ya kalleta da kyau.
鈥淭o miyasa na ke mafarkinka?鈥�
Kallonta kawai yake irin kallon nan na son tantace gaskiyarta. Kamar tasan irin kallon da yake mata sai tace.
鈥淲allahi ba karya na ke ba, ina mafarkin, da wani mutum kuma da wani kana rike da wannan abun busar kana busa amman kullum baya kake bani, shiyasa lokacin da na ji busarka na zo har nan dan gani idan da gaske ne, kuma busar iri daya ce鈥�
鈥淣i ba aljani ne bane鈥�
Ya fada cike da mamakin mafarkinsa da tace tana yi.
鈥淜uma tun lokacin nan nagge bata sake mutuwa ba, miyasa kake saka wannan abun鈥�
Ta nuna warkin dake kugunsa, sai yai murmushi.
鈥淗aka muke, kayan garin mu鈥�
鈥淚na ne garin ku?鈥�
鈥淕aruk鈥�
Ta gwala ido tana matsowa kusa da shi, sai a lokacin ta tuna da taba jin labarin garin ance mutanen ciki basa saka tufafi kuma matsafa ne.
Ta zauna a kasa tana kara kallonsa.
鈥淜ai kake min tsafi nake mafarkinka kenan?鈥�
鈥淎a鈥�
鈥淵a za'ayi na tabbatar da kai mutum ne?鈥�
鈥淚dan kika taba jikina za ki ji shi kamar na ki, idan na aljanine za ki jishi da sanyi ko taushi ko gashi ko kiji kamar ba hannun mutum ba鈥�
Dan matsawa tai kusa da shi, sai ya miko mata hannunsa ta taba sannan ta taba nata, sai ta ji shi normal kamar ita. Amman hakan be sa ta gansu ba.
鈥淜a yanke kanka na ga jini sai na yarda鈥�
Wannan karon dariya yake, a ransa yana mamakin wauta irin nata taya zata ce ya yanka jikinsa.
鈥淪amo min kare ko dutse mai tsine鈥�
Ba musu ta tashi taje ta samo masa, ta kawo ta zauna kusa da dan tabbatarwa idan da gaske yankawan zai yi ko a'a.
鈥淢iye sunanki?鈥�
鈥淔adime鈥�
Ta amsa mashi tana kallonsa da manyan idonta masu haske da daukar hankali. Murmushi yai ya mike hannun na dama ya saka hannunsa na hadu ya karkari hannunsa na dama kadan jini ya dan fito. Da sauri ta rufe ido tsigar jikinta na tashi.
鈥淚nnalillahi, da gaske ka yanka ni wasa nake maka fa鈥�
鈥淏a hakan zai sa ki yarda da ni ba鈥�
Ya fada yana kallon gashin kanta.
鈥淣a yarda鈥�
Ta fada bayan ta bude idon.
鈥淢iye sunanka?鈥�
鈥淲asim鈥�
Haka ta fara masa tambayoyi kala kala yana bata amsa, duk abun da ta tambaya sai ya bata amsa, tun tana da sauran tsoron har ta sake jiki da shi.
Har da karbar sarewarsa ta busa, sai nata busar bata fita saboda bata iya ba. Har sai da ya karba da kansa ya fara busar tana ta kallonsa cike da burgewa.
鈥淲aya koya maka?鈥�
鈥淲ani tsoho鈥�
鈥淎 ina yake?鈥�
鈥淕arinmu鈥�
Ya amsa yana kallonta, mugun burgeshi take, ko wane motsi nata the way da take tambayarsa yadda take sake jiki da shi far'arta kyauta and everything. Ta gyada kai tana murmushi, da yamma lis ta koro shannun ta sako su a gaba ta jeru ita ta shi suna tafiya, sai ya rakota har kusa da hanyar gidansu sannan ya tsaya ita kuma ta daga masa hannu, shi ma ya dago mata sai ta juya ta cigaba da tafiya sai kwasar dariya take.
Daman tun dazun take jin dariyar take son ta yi ta kasa, wai basa saka rika kuma basa son shiga cikin mutanen da na nasu ba, gaba daya kallon mahaukata take musu.
Sai ta kai shannun gida ta shigarda da su gurin da aka saba ajesu, sannan ta sunsuda ta fita, sai da ta kama hanya sannan ta hango Bappa tafe tare da wani makocinsu, da sauri ta boya bayan wata bishiyar dogon yaro. Kasancewar bishiyar katuwa yasa Bappa da mutunen ba su lura da ita ba, domin gaba daya hankalinsu baya gurin yana kan abunda suke tattaunawa ne.
鈥淕askiya ina baka shawarar ka kara aure kawai鈥�
Shine kawai abun da ta ji, duk da bata san abunda ake tattaunawa akai ba, amman tabbas ta ji Bappa na ce masa ya kara aure, a gurin tai ta tsayi har sai da suka karyar kwana sannan ta fito yana girgiza kai tana dariya.
Juyawa tai ta canja hanya zuwa gidansu Ma'u, ko da ta shiga ta samu Ma'u na alwala sallah magariba, sai ta risino kusa da ita.
鈥淢a'u nan da kwana biyu mijin Ande Hanne zai fara maganar aure ce ni na fada miki鈥�
Ma'u ta kalleta da sauri.
鈥淎ljanin ne ya fada miki?鈥�
鈥淓h, yau da naje kiwo ma a fili ya ganshi yace zan rika ba da magani zan rika fadawa mutane komai鈥�
Ma'u ta kara zaro ido gaba daya ma sai ta ji tsoron Fadime ya fara kamata.
鈥淒a gaske?鈥�
鈥淎llah amman karki fadawa kowa鈥�
鈥淏a zan fada ba鈥�
Gaba daya tsoro ya gama kama Ma'u, Fadime ma ta lura da hakan kuma ta jidadi, ita gaba daya tun da Inna ta fada mata masu magani kudi ake ba su su fadawa mutum matsalarsa ta ji tana sha'awar abun. Haka ta kwana da tunani kala kala na irin karyar da za ta yi ma Inna ta yarda ta fara bada maganin.
Sai da Fadime ta gama karyawa da fura mai tsami sannan ta zauna saman tabarmar da Inna ke zaune tana gyaran gida.
鈥淚nna na sake mafarkin aljanun nan sun ce zan bada magani fa鈥�
Inna ta daka mata tsawa.
鈥淔ulani kar na sakd jin maganar nan a bakin ki, da kin sake maganar nan sai na fadawa Malam鈥�
Da sauri tace.
鈥淣a bari鈥�
鈥淕ashi kije ki debo ruwa鈥�
Ta tashi da sauri ta nufi inda tulun daukar ruwan yake ta dauka ta fice da sauri ta nufi gurin deban ruwa, tasan Bappa sarai be son irin abubuwan nan. Tana tafe tana wakewaken har ta isa, sai da ta duka ta fara cikon ruwa sai ta ji a na kirata.
鈥淔adime鈥�
Da sauri ta juyo suna hada ido ta sakar masa murmushi kamar yadda shi ma yake mata murmushi. Tsaye yake nesa da ita.
鈥淎she kana zuwa nan da safe鈥�
Ya gyada mata kai yana karasowa kusa da ita, har yanzu bata daina jin tsoro ba sai dai ba kamar na da ba.
鈥淩uwa kike deba?鈥�
鈥淓h鈥�
Ta fada tana dariya sannan ta duka ta cigaba da cikon, sai kuma ta juyo ta kalleshi.
鈥淒an Allah ka taimaka min ka min wani abu鈥�
鈥淢inene鈥�
鈥淪o na ke idan na cika tulun nan, ka masa tsafi tun da ku matsafa ne ai zaka iya ko?鈥�
鈥淪aboda me?鈥�
鈥淪aboda Inna ta yarda cewar ina mafarkin aljanun, so na ke ka masa tsafi sai na je gida na aje tulun sai ruwan su zama maciji鈥�
鈥淏a ki jin tsoro?鈥�
鈥淎i ba anan ba sai na je gida, amman ka min alkawarin ba za ka cutar da ni ba鈥�
鈥淜o wani ba zan bari ya cutar da ke ba鈥�
鈥淭o ka min ka ji鈥�
Ya daga mata kai. Sai da ta cika tulun dam sannan ta matsa tace yai mata ita dai burinta kar Inna ta karyartata, burinta Inna ta bata hadin kai ba sai Bappa yaji ba. Matsawa yai kusa da tulun ya saka hannunta yana ta kallonta be wani dade ba ya cire sai ta zaro ido.
鈥淵anzu shikenan da naje gida zan ga ruwan ya zama maciji?鈥�
Ya daga mata kai alamar Eh yana ta kallonta, sannan ya tallaba tulun ya dora mata saman kai, tsakanin dora mata tulun da fara jin motsin abu mai rai a cikin tulun be yi minti 1 ba.
Yana kallonta sai ta fashe da kuka.
鈥淏a yanzu na ce ba, Wayyo Bappa wayyo Bappa wayyo Bapppa鈥�
Sai fitsari, ta fara kukan da gaske gasken hawaye kamar ruwa.
鈥淚dan kika sauke tulun macijin ciki zai cijeki, karki sauke sai kin isa gida鈥�
Ya fada yana dariya. Gaba daya jikin Fadime rawa yake kafafuwanta sai lankwashewa suke kamar zata fadi, numfashinta ya fara sama sama, faduwa tai kasa ta fara rarrafe dan bata ma iya tafiya, haka nan ta isa gari duk da bata zanenta da zawo sai kuka take tana kiran Bapppaa, ga tulun saman kanta. Duk wanda ya kalleta sai ya ganta da tulu saman kai ga kan maciji ya leko, mutane sai gudu suke, kamin ta isa gida har ta canja kammani.
鈥淏appppa wayyo Inna na bani na taro aljalina鈥�
Ta kasa tashi tsaye gani ba take idan ta mike macijin zai iya saukowa, mutane aka fara taruwa ana kallonta tai zaure a kasa sai rusar kuka take fuska duk da bace da majina da hawaye zuciya kuma kamar ta fashe dan tsoro, ita gaba daya bata dauka ma da gaske yana iya yin tsafi ba sai yanzu.
鈥淢ike tsaye ki zafar da tulun鈥�
Kowa abun da yake fada kenan, ita kuma babu kuzarin mikewar tsaye gashi yace mata idan bata isa gida bata sauke zai cijeta.
鈥淵ace sai na kai shi gida, ku dauke ni ku kai ni gida, wayyo Bapppaa na wayyo Bapppaa鈥�
Ta fada tana ta yarfe hannu, idonta har ya kumbura saboda kuka.
FALMATA POV.
Da tunani kala biyu Falmata ta isa gida, tunanin saukin kai da jindadin kadeta da M2 yai ga kuma kiranta da Ammy tai ta mata tambayoyi, ko miyasa tai mata haka oho. Sosai ta so ta biya ta gidansu kawarta Khadija ta labarta mata yadda ta ga M2 sai ta tuna da Baba ya mata iyaka da gidan. Hakan yasa tai hanzarin cira kafa ta isa gida, da zimmar ta gama aikinta dan ta samu isa Islamiya da wuri ta labarta musu. Ko da ta isa gida har Gambo ta sanar da sakon Ammy ta bar gidan dan ita abun hawa ta hau ba kamar Falmata ba da take tafiya a kafa.
Falmata na isa ta manta da wani kunci da tsoron fada ko wani abu, ta hau bawa Naja labarin yadda ta ga M2.
鈥淒an Allah matsa can mahaukaciya, hala M2 ne banza da zaki ganshi a bagas, sannu kakar farin jini, dan kin ji ana cewa kina da farinjini shine kike wani karya kin ga M2 mahaukaciya鈥�
Ko kadan bata ji abun da Naja ta fada ba, amman a yanayin yadda take harararta take jan tsaki tasan karyarta tayi, hakan yasa Falmata ta kara boye hular da ya bata a cikin jikinta ta mike tsaye cikin rashin jindadi ta nufi dakinsu. Tumba dake zaune bakin kofar dakinta ta bushe da dariya.
鈥淲allahi yarinyar can ta fara haukacewa, mugun son M2 da take ne yasa ta fara ganin mutane na zame mata haka鈥�
Naja ta ja tsaki.
鈥淜o mai wankewa M2 takalmi ta isa ta gani balle M2, ita fa yadda ake fadar tana da farin jinin nan wani jin kanta take鈥�
鈥淜ira min ita鈥�
Tumba ta fada tana dariya, daga inda Naja take zaune ta kwala mata kira.
鈥淜e kurma zo ana kiranki鈥�
Falmata har cikin ranta ta ji sunan, wani abu na rashin jindadi ya ratsa zuciyarta, ta saka hular M2 can ciki bakkon kayanta sannan ta fito ta tsaya bakin kofa jiki ba gwari tun da babu wani abincin kirki a ciki.
鈥淜e yar kurma, dazun Gambo ta zo tace zaki rika wuni can kina rainon yara鈥�
Tumba ta fada mata tana mata alama irin na kurame. Naja ta saka dariya.
鈥淏an cin kurmanta har da hauka na son kamaki, kin fara ganin mutane kina ce musu M2 ko?鈥�
A nan ma Tumba ta saka mata dariya, a gurin Falmata ta duka ta fashe da kuka, ba karyatata da suke take ji ma ciwo ba, kiran da kurma da suke a yanzu.
鈥淛i munafuka salon a shigo ace wani abu Umma tai miki kike kuka mu kuke dariya ko? Da shegen baki kamar zunubi鈥�
Naja ta fada cikin tsawa, sai Falmata ta mike tsaye ta shige dakinsu ta cigaba da kuka tana rufe bakinta dan kar sautin kukanta ya fito.
Sai da tai mai isarta sannan ta fito ta zuba surfe ta fara, sai da ta surfe tiya da rabi sannan ta shiga tai wanka ta saka uniform dinta na Islamiya ta dauko qur'ane ta da littafai ta fice.
Kusan kullum cikin rashin jindadi taje zuwa makaranta, saboda rashin jin da take a yanzu, idan akai karatu sai Khadija ko wata ta rada mata abun da Malam ya fada a kunne sannan ta ji, sai kuma idan Malamin yayi da karfi, Falmata ba yarinya ce mai yawan surutu ba, amman hakan be hanata fadawa yan ajin su cewar ta hadu da M2 ba, most of them sun karyatata wasu na fadin dan dai tana son shi sosai ne yasa ta ga mai kama da shi.
Haka dai ta bar Islamiya cikin rashin jindadin yadda suka karyarta daman ta san ba za su yarda ba, ita ma dai a lokacin ta fara kwankwanto da gaske M2 ta gani ko mai kama da shi?
Ko da ta iso gida sai ta tararda wani tashin hankali, yaron da aka aiko yana tsaye yana jiran dawowarta Tumba kuma ta yi wani shegen zama tana rawa da kafa. Ta shigo da sallama Tumba ta hau ta da matsifa.
鈥淎she Falmata zuwa kike kina cin bashin garin kwaki a shago da sunana?鈥�
Dakan shida-shida gabana yai, ta sani yau asirinta ya tonu, tabbas tana zuwa karba kuma idan ta je Tumba take cewa saboda tana jin kunyar tace ita zai bawa bashin gari.
鈥淪aboda asan ba a baki abinci ko kuma dan ki bata min suna ni da ubanki? To ya aiko yace a bashi kudinshi bari ubanki ya dawo sai kin fadi dalilinki na bata min suna鈥�
Kamar an tureta haka ta fadi gaban Tumba kamar mai neman gafara hawaye sai sallama suke a fuskarta.
鈥淒an Allah dan darajar Annabi karki fadawa Baba Umma, ki rufa min asiri, zan samu kudinsa yanzu na bashi, ki yi hakuri Umma ba zan, idan na sake ki kashe ni, Umma wallahi yunwa take damuna shiyasa na ci bashin amman daga yanzu ko zan mutu ba zan sake ba, na rantse da Allah Umma, dan manzon Rahama ki rufa min asiri Umma ba zan sake ba har abada鈥�
Tumba ta fisge kafarta tana kallon.
鈥淭afi idan Babanta ya dawo za a fada masa鈥�
Yaron ya juya ya fice, sai Falmata ta mike tsaye da sauri.
鈥淣a bani na lalace na shiga uku wayyo ni Allah na Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un鈥�
Ta furta ta karfi kuka na subuce mata, sai ta saka hannunta da sauri ta rufe bakinta, da gudu ta shiga dakinsu ta fada kan shimfidar da take kwana.
鈥淲ayyo ni Allah na yau asiri na ya bonu, wayyo Mama Mama ina ma ni na mutu ba ke ba, Allah ka karbi raina kamin Baba ya dawo Allah na shiga uku鈥�
Ta fada tana yarfe hannunta hawaye sai zubo mata suke kamar ba gobe.
ZAINAB POV.
Ta dan yi shiru sannan tace.
鈥淣a ce mishi ya bari har na dawo daga tafiyar da zan yi鈥�
Ammy ta kalleta.
鈥淣i fa ina tsoron lafiyar nan Zainab, kin san kasar ba wani tsoro kuma ki ce za ki je garin cikin mutanen da ake fadar basa saka tufafi? Kina ganin ma za su aminta ki dauke su hoto ne?鈥�
鈥淣o ba wai kai tsaye zanje can ba, zan sauka garin dake kusa da su ne, nai magana da mutanen tukuna sai na isa garin, kuma ko ban samu zuwa can ba ai ance akwai manyan duwatsu a kusa da su da ruwa, kuma ance akwai Fulani irin masu yin bukka da gidan zana su zauna a kusa da su, ko da ban samu isa can ba na san ba zan sara abun dauka ba鈥�
鈥淭o Allah dai ya tsare鈥�
鈥淎min, Ammy dan Allah ki mata magana, ban zan abun da mutunen nan yai mata ba, ta ki ta saurare ni, ni kuma ina son shi, shi yanzu yace yana son ya turo kuma ya sanar a gidansu amman sai ya samu tabbaci daga gareni鈥�
Ammy ta yi murmushi.
鈥淜arki samu damuwa, zan yi magana da ita, idan ta aminta sai a sanarwa yan'uwan mahaifinki鈥�
鈥淣a gode Ammy鈥�
Mikewa tai tsaye tana sanye da riga da wando English wears, kanta sanye da dankwalin nan da ake yayi blue.
鈥淏ari na duba dakinta idan tana nan sai na turo miki ita鈥�
Kai kawai Ammy ta daga mata, ta maida dubanta gurin tv dake dakinta, kallon kawai take amman hankalinta baya can, bata da damuwar da ta wuce ta Mai Martaba a yanzu, a iya tunaninta ta rasa gane abun da yake damunsa, gashi idan an gwada yi masa na hausa sai abu ya karu a maimakon raguwa. Kiran wayarta nd ya katse mata tunanin da take, sai ta mika hannu ta dauka.
鈥淎ssalamu Alaikum鈥�
Ra'ees ya amsa daga dayan bangaren.
鈥淲a'alaiki-Assalam, Ammy barka da yamma鈥�
鈥淵auwa Ra'ees ya gida鈥�
Ta fada cike da kasaitar da ta zame mata jiki.
鈥淎l-hamdulillah Ammy an samu wata, amman dai ba mu je, sai dai marikiyar yarinyar tace zata iya aura masa ita鈥�
鈥淜a fada mata matsalar sa ne?鈥�
鈥淓h ta ji komai, firar ma ta ji muna yi shine tace tana da 拼a zata ba shi, amman dai ba mu je ba tukuna鈥�
鈥淭o yayi kyau, amman fa ba sai kun bayyana dan wane ba, kuma ka yi duk abun da ya dace, karka bari Shattima ya ji komai, sai an kammala yadda ba zai iya ce mana aa ba鈥�
鈥淚n-Sha-Allah Ammy鈥�
鈥淣a gode Allah ya maka albarka鈥�
鈥淎meen鈥�
Tana kokarin aje wayar aka kwankwaso kofar dakin kamin a turo a shigo. Hajiya Balki ce Nana na biye da ita a baya, a baki kofa ta tsaya tana kallon Ammy sai cika take tana batsewa.
鈥淵anzu an kyauta kenan? Sai a dauke yarinya akaita gurin Waziri bayan kin san ita da Waziri ba jituwa suke ba?鈥�
Ammy ta kalleta da mamaki kamar ba zata ce komai ba.
鈥淎n kaita gidan Waziri kamar wacce aka kai gidan yari? Kanen ubanta ne fa鈥�
鈥淣a san kanen ubanta ne ai, amman tun da bata son zuwa ai sai a kyaleta鈥�
Ammy ta dauke kai bata sake ce mata komai ba. Ganin hakan yasa ta juya ta fita N
0 comments:
Post a Comment