DAGA TAIMAKO Page 16-20
.
Ayuba tashi yayi ya zauna ya duba agogon wayansa yaga k'arfe hud'u saura shima jikinsa ne ya fara rawa tsoro ya rufeshi yana tunanin Wanda ke kwankwasa k'ofa uwar haka,Kallon Surayya yayi da ta jike da gumi sabida tsananin tsoro yace ta d'aga shi yaje ya duba Wanda ke kwankwasa k'ofar,kankameshi tayi tace kar yaje ko ina yasani ko aljanar ce take kwankwasa musu k'ofa,ce mata yayi ba bud'ewa zai yi ba zai lek'a ta ramin k'ofar ne yaga waye, Surayya kin cika shi tayi,suka mik'e tare Ayuba ya bud'e k'ofa ahankali suka fito suna dab da isa k'ofar suka jiyo guje gujen maguna asaman kwanu, taku biyu Surayya tayi ta shige d'aki,Ayuba ya rufa mata baya,karkashin gado Surayya tafara shirin shigewa,Ayuba ya rufe k'ofar har da Dan tusar sa.
.
Abdulmajeed dake kwance a kasa a sume,ji yayi an yayyafa mishi ruwa ahankali ya bud'e idonsa,ganin bai ga kowa bane yasa ya mik'e aguje yana bubbuga gidan Ayuba,Surayya da Ayuba da jikinsu tun a lokacin bai bar rawa ba,suna dunkulle awaje d'aya,jin da suka yi an k'ara bubbuga gidan ne yasa suka wage baki suna adduoi Ayuba na karanta Laqadjaakum,Surayya na karanta Fatiha Dan ba k'aramin tsorata suka yi ba Dan har a lokacin suna jin guje guje asaman kwanu,Abdulmajeed da shima a mugun firgice yake ganin babu alamar za a bud'e k'ofar ne yasa ya hau k'wallawa Ayuba kira yana yazo ya bud'e masa shine Abdulmajeed,cak Ayuba ya tsaya da karatun da yake,ya kasa kunne Dan kamar sunansa yaji ana kira,muryar Abdulmajeed ya jiyo yana Kiran sunansa,da sauri ya raba jikinsa Dana Surayya ya mik'e yayi waje Surayya sai kiranshi take ya dawo,Abdulmajeed
kuwa waige waige kawai yake yana kiran sunan Ayuba ga tsanin tsoro ga wani gudawar da yake ji,Ayuba na bud'e gidan ya shige da gudu,Ayuba kuwa yayi sauri ya rufe gidan,a tsakar gida ya sameshi yana kai da kawowa, " Abdulmajeed Lafiya kuwa daddaren nan waye ya koro ka"? Ayuba yace yana kallon gajeran wandansa dake Neman sub'alewa daga jikinsa "Ayuba bani touchlight na Shiga band'aki tukuna kashi nake ji" Ayuba d'akinsa ya shige ya tarar da Surayya a zaune akan gado duk ta had'a zufa sai ajiyar zuciya take Dan sai da ta jiyo muryar Abdulmajeed hankalinta ya kwanta,Touch light d'in dake gaban mudubi ya d'auka yayi waje da sauri Abdulmajeed ya k'arbi touch light d'in daga hanun Ayuba ya shige band'akin Dan ginin Gidansu iri d'aya ne kasancewar haya duk saka kama,yana hawa kan Masan yafara sukurkuta gudawan,Ayuba ciki ya koma ya zauna a gefen Surayya aikuwa suka jiyo karar sauk'ar gudawan Abdulmajeed ji kake "buut bubut" Surayya mai zata yi in ba dariya ba har da rik'e ciki,Ayuba shima duk yanda yaso ya gintse dariyar da ta taho masa kasawa yayi sai da ya saki dariyan,Surayya kasa tayi da murya tafara maganar " Ayuba duk yanda akayi Aljanar nan ce ta tsorata Abdulmajeed shi yasa kaganshi daddaren nan gashi sabida tsorata da yayi bar da su gudawa Ashe Muhibba ma ta fishi jarumtaka"Surayya tace tana k'ara kyalkyalewa da dariya,Ayuba shima kasa yayi da murya yace " aikuwa inaga aljanar ce ta koro shi Dan babu Riga a jikinsa da gashi sai gajeran wando" Abdulmajeed Sai da yayi minti goma sha Biyar a band'akin kafin ya fito,yana sauke ajiyar zuciya,Ayuba mik'ewa yayi, ya yi hanyar waje,palo ya bud'e yace wa Abdulmajeed bismillah,tare suka shiga palon, Abdulmajeed ya ajiye touch light d'in hanunsa yacewa ya Ayuba taimaka masa da Riga ya sa,Ayuba d'akinsa ya koma ya d'auko masa doguwar Riga Surayya kuwa ta biyoshi Dan tace bazata iya zama ita kadai ba,zura rigar yayi ya zauna,Ayuba yace "Abdulmajeed ina jinka mai ya faru,"
.
" Ayuba Allah ne yayi ina da sauran numfashi agaba da tuni kaji labarin na mutu tun k'arfe 11 Aljana ta sako ni agaba ina zaman zama na Muhibba ta janyo min" ba irin gargadin da ban mata ba akan tasan irin wayanda Zata na taimakawa tana Sanin irin wayanda zasu na na shigar min gida Sai gashi ta janyo min masifa daga taimako,"Subhanallahi kace abinda ya faru kenan,Allah ya tsare mu da tsarewarsa ya kare mu daga sharrinta" " Ameen kai dai ai naga masifa wlh har k'ofar gidanan ta biyoni Allah Ayuba ba Dan ina da dauriya ba da tuni na mutu," "innalillahi wa inna ilaihi rajiun Allah ya tsare mu kace ba k'aramin tashin hankali Muhibba tagani ba" Ayuba yace yana girgiza kai,"yanzu ya zaka yi Abdulmajeed? "Ai Ayuba barin gidanan ya kamani ana iddar da sallahr asuba zanje gidanmu in fad'awa Mahafina bazan iya zama agidanan ba gaskiya"Katse shi Ayuba yayi yace " aa ba haka zaayi ba dudu watanku biyar a gidanan Sauk'ar Qur'ani za'ayi a gidan insha Allahu aljanar zata bar gidan," "hmm Ayuba kenan Dan ba Kai ne kaga aljanar ba da wallahi kai ma barin gidan zaka yi.
.
Ana idar da sallar asuba Abdumajeed ya k'arbi kud'i awajen Ayuba Dan yace babu abinda zai sa ya k'ara shiga gidansa babu yanda Ayuba bai yi ba akan ya Shiga gidan zai raka shi ya d'auko machine d'insa ya hau bai kamata ace yana da machine yaje ya hau adaidata sahu ba,fir Abdulmajeed yak'i da gashi sai doguwar rigar da Ayuba ya bashi da Dari biyar d'in da ya k'arba awajen Ayuba ya dau hanyar bakin titi,sai da ya samu awa d'aya abakin titi bai samu abun hawa ba,Dan gari bai gama waye ba,wani adaidaita Sahu ya hango daga nesa ya taho ta inda yake,hannu biyu ya d'aga yana "wait wait ",adaidaita sahun sai da ya d'an wuce shi Kafin ya tsaya ,da sauri ya k'arasa inda adaidaita sahun yake yahau yacewa mai adaidaita Sahun " kofar nassarawa zaka kaini,"mai adaidata sahun bai ce komai ba ya ja suka tafi,juyawa yayi ahankali ya kalli gefensa,wata matashiyar buduruwa ce a zaune agafensa faraa ce tas Dan farinta har d'aukan ido yake,bak'ak'en kaya ne ajikinta,babu abinda kake gani sai hannyenta Dan kanta ma anad'e yake, ta kau da kanta tana kallon gefe, ,Abdulmajeed gabansa ne yayi wani irin fad'uwa tsoro ya rufeshi yana tunani ko aljanar ce ta biyoshi,matsawa yayi nesa sosai da ita gabansa na fad'uwa ahankali ya lek'a k'afarta yaga shima arufe,har a lokacin tana kallon gefe bata juyo ba,Abdulmajeed madubin adaidaita sahun ya kalla dake , saitin ta, Aljanar nan ya hango ta mudubi ta sakar mishi murmushi hakoranta amadadin jajjaye bak'ak'e ne ma su tsini Kamar allura,"wait wait anan zan sauk'a," Abdulmajeed yace agigice adaidaita sahun bai gama tsayawa ba ya duro daga adaidaita sahun ya sa gudu,mai adaidata sahun aguje shima ya bishi ya rik'e mishi Riga yana "ya zaka gudu kabani iya kud'in Dana kawo ka nan"Abdulmajeed doke hanunsa yayi yace " cikani Dan ubanka aljana ce acikin adaidaita sahun ka""Al me"? "Aljana" Abdulmajeed yace yana k'ara dibawa aguje,abin mamaki Mai adaidaita sahu ne gaban Abdulmajeed yana ta zuba gudu,duk Wanda ya tambayesu akan mai suke gudu,suna cewa aljana ce shima zai diba aguje
.
Wani dake zaune a can gefe da duk abinda yake faruwa yana gani adai daita sahun ya fara lek'awa Dan yaga ko wani abun ne aciki shi yasa suke gudu, babu abinda ya gani acikin adaidaita sahun ,da gudu ya bi su Abdulmajeed,ya kamo Mai daidaita sahun da tsabar gudu kamar ya tuntsira,Mai adaidaita sahun juyowa yayi afirgice, mutumin ya tambayeshi mai ya faru suke gudu,da sauri mai adaidaita sahun ya gaya mishi yana Neman kwace rigarsa daga hanun mutumin Dan tunda ga lokacin da ya tab'a mak'ala earpiece a kunensa ya shiga band'aki yana jin waka,yaji an sharara masa mari,yake tsoron aljanu ko sunansu yaji sai ya tsorata,mutumin kwantar masa da hankali yayi yace ya kwantar da hankalinsa ya lek'a adaidaita sahu babu komai,mai adaidaita sahun mukulin adaidaita sahun ya bashi yace masa Dan Allah ya taimaka masa ya d'auko mishi adaidaita sahun shi dai tsoro yake ji.
.
Abdulmajeed sai da yayi nisa sosai ya tsaya gabad'aya ya gama tsorata,bus ya Tara ya hau Dan bazai iya kuma hawa adaidaita sahu ba,hankalinsa ne ya kwanta da yaga bus d'in acike,ajiyar zuciya ya ringa saukewa yana bin mutanen cikin bus d'in da kallo in banda zare ido babu abinda yake yi.
,
Muhibba kuwa aranar barci bai ga idonta ba dan kasa barci tayi,tunda tayi aure bata tab'a raba shimfid'a da Abdulmajeed ba,gashi yau sabida tashin hankalin da masifa da Aljanar da ta taimakawa ta sata yasa ta zo cikin kanenta ta kwanta,kewar Abdulmajeed ne yabi ya dameta tana tunanin yau ko mai yaci,tasan tunda bai zo ba,bai kuma kira awaya ba tasan bak'aramin fushi yake da ita ba,dan ya d'auka karya take yi babu wata aljanar da take tsorata ta, agogo ta duba taga k'arfe biyun dare,wayar Nafeesa ta d'auko ta kuna, tayi dailing number Abdulmajeed,ji tayi yanata ringing bai d'auka ba,ahaka ta cigaba da kiransa,sai da ta gaji Dan kan ta ta ajiye wayar,kuka ta fashe dashi tana tunanin yana ganin kiran kin d'auka yayi,sabida Fushin da yake yi da ita,Dan tasan halin Abdulmajeed ya tsani yaga ya bata umarni ta tsallake,to ya zata yi, zuwa gidan shine mafita agareta Dan in ta cigaba da zama agidan aljanar Zata iya zautar da ita, ga Abdulmajeed yaki yarda da ita, dana sani ta ringa yi na Taimaka aljanar da tayi,yanzu Surayya da ta rufe k'ofarta bata bari aljanar ta shigar mata gida ba tana can hankalinta kwance babu abinda ya raba ta da mijinta,ahaka Muhibba ta zauna tana kuka tana tunani,sai da aka fara kiraye kirayen sallah ta mik'e ta nufi band'aki Dan tayi alwala.
.
Abdulmajeed kuwa ana sauke shi ko canji bai tsaya k'arba ba ya nufi gidansu da sauri,a tsakar gida ya tarar da mahaifinsa mallam Isah yana shan koko da kosai,mahaifiyarsa kuma tana kitchen,Mallam Isah mik'ewa yayi da sauri da ya ga yanda Abdulmajeed ya shigo yace "Subhanallahi Abdul lafiya daga ina"? Abdulmajeed zubewa yayi a kasa yana sauke numfashi kamar Wanda yayi gudu,Hafsat Mahaifiyarsa itama lek'owa tayi tana kallonsa,Abdulmajeed bai ce komai ba ya cigaba da sauk'e ajiyar zuciya,Hafsa fitowa tayi daga kitchen d'in tace "Abdul ba tambayarka ake ba daga ina kake da sassafe nan?,ina Muhibbar? Mallam anya lafiya kuwa ka ganshi fa duk a firgice kamar Wanda aka koro" Hafsat tace tana k'ara kallan Abdulmajeed,"kai bana San Shashanci ana tambayarka lafiya kazo mana gida da sasafe ina ka baro iyalin naka?" Mallam isah yace atsawace.
.
" Abba aljana ce ta sako in agaba ta hanani sakat,wlh jiya ban runtsa ba,yanzu ma Dana taho sai da ta biyoni,watak'ila ma yanzu ta biyoni gidanan"
.
Mallam Isah da hafsa had'a baki suka yi wajen rafka sallati Mallam isah yace, "Aljana kuma bangane ba kayi min bayani sosai mai ya had'a ka da Aljana ina Muhibbar?share zufa yayi,ya fara basu labari,tundaga lokacin da Muhibba ta taimakawa Aljana ta shigar musu band'aki,zuwa lokacin da Muhibba ta tafi gidansu sabida tsorata ta da aljanar take yi,da yanda shima aljanar ta ringa tsorata shi har a adaidaita sahu,ya k'ara da "gaskiya Abba bazan iya cigaba da zaman gidanan ba Dan aljanar tana gidan,tashi zanyi daga gidan,wlh badan na ga aljanar da idona ba,na d'auka karya Muhibba take yi,Umma wlh baki ga aljanar ba, sallati Hafsa tayi tana tafa hannu tace "Ikon Allah daga taimako kun janyowa kanku masifa,ni Muhibbar ma nafi tausayawa abinda zai firgita namiji kamar Abdulmajeed sabida tsanin firgita da yayi rigar ma abaibai ya sako ta,lailai tashin hankalin da Muhibba tagani ba kadan bane," Mallam Isah cewa yayi "Hafsa ba dole Aljanu su ringa bibiyarsu ba,kin San irin sakacin Abdulmajeed tun Kafin yayi aure, babu irin fad'an da bana mishi,shine wasa da sallah,baya azkar yanda yaga kanensa nayi,kai tsaye zai shiga band'aki batare da yayi add'ua ba,ballantana azo gasu karatun Qurani ,yanzu da zaki tambayeshi yaushe Rabin da ya d'auko Qurani ya karanta wlh bazai iya gaya miki ba,
Abdulmajeed ne zai ga abinda ya tsorata shi amadadin yayi addua sai dai ya kurma ihu,
nan massallaci yaje bazai je ba,sai dai yayi sallar agida,ki gayamin ya aljanu baza su sako shi agaba ,duk wani Abu dazai kareshi daga sharrin aljanu ba yi yake ba,ko karya ne"? Mallam Isah yace yana kallon Abdulmajeed da ya sunkuyar da kai,Dan yasan tabbas duk maganar da mahaifinsa ya fad'a gaskiya ne,Dan Muhibba ma bata fiye sa dankwalli ba kullum gashinta a bud'e yake, tunani ya hau yi, yanzu akan wanan d'an k'aramin dalilin sai Aljana ta sako su agaba,maganar mahaifinsa ne ya katse masa tunanin da yake,Dan haka in zaka gyara halinka ka gyara,matarka ma naji ance zama take babu dankwalli Nura da yaje gidan kwanaki naji yana fad'awa mamanku,duk wata k'ofa abud'e take da aljanu zasa dame ku,da kake cewa zaka tashi kabar gidan kana da kud'in kama wani gidan ne, Dan in kana tunanin ni zan kama maka Nima nan bani da kud'i,gwara ma ka hak'ura da zancen tashi,zan sa mallamai suje suyi sauk'a agidan,kuma sai Ku daina sakaci da addua,insha Allahu zata daina tsorata Ku,gidan ya daina rabo da karatun Qurani,in bazaku iya karantawa ba kuringa kunawa, awaya,"nasiha Mallam Isah yayi mishi sosai ya bashi addu'oi,godiya yayi wa Mahaifinsa ya mik'e ya nufi d'akinsu da samarin gidan ke kwana Dan barcine a idonsa yana kwanciya ya hau tunanin babu yanda zaayi ya cigaba da zama agidan zai nemi kud'i ya kama wani gidan,da wanan tunanin barci yayi awon gaba dashi.
.
K'arfe hud'u na yamma ya shirya ya nufi gidansu Muhibba a machine d'in kaninsa,yana isa gidan ya samu Mallam Hashimu a k'ofar gida yana zaune shi da wani makocinsu,parking yayi ya tsuguna har kasa ya gaishe su,suka amsa,Mallam Hashimu tambayarsa ya hau yi lafiya suke ta gwada wayarsa yana ringing bai d'auka ba,sai a lokacin ya tuna wayar na gida,karya ya mishi da wayarsa fad'uwa tayi shima yana kira ba a d'aga ba,Malam Hashimu ce masa yayi jiya Muhibba tazo ta fad'a musu abinda ke faruwa dama shi yasa yake neman shi ,anan yake fad'a masa yasa ayi musu sauk'ar Qur'ani a gidan,insha Allahu aljanu zasu daina damunsu,godiya Abdulmajeed yayi mishi,Mallam Hashimu yace ya shiga ciki bari yah kira masa Muhibba,d'akin da suke zance da Muhibba kafin suyi aure ya shiga ya zauna,Muhibba da bata Dade da fitowa daga wanka ba tana zaune agaban mudubi tana so ta shafa mai Abdulmajeed ne ya fado mata arai ta kasa shafa man,tana cikin Tunanin Abdulmajeed Mallam Hashimu ya d'aga labulen d'akin yace mata taje Abdulmajeed na kiranta yana d'akin yayanta,wani irin farinciki ne ya rufe ta,ta mik'e da sauri ta zura doguwar Riga ta fesa turaren Nafeesa tayi waje,tana zuwa k'ofar d'akin gabanta ya hau fad'uwa Dan bata san ya zasu kwashe da Abdulmajeed,sallama tayi ta shiga ahankali,Abdulmajeed kuwa Dama yana Shiga ya had'e rai,Muhibba sunkuyar da kanta tayi sakamakon kallon da yake jifanta dashi,"sannu da zuwa " Muhibba race tana k'ara sunkuyar dakai,Abdulmajeed wani mugun kallo ya mata yace " Muhibba Ashe baki da hankali ni zaki yiwa karya kice min tsohuwa ce tayi bara kika bata abinci Ashe aljana kika bud'ewa k'ofa ta shigar min band'aki,"Muhibba jikinta ne yafara rawa Dan bata tab'a ganin b'acin ran Abdulmajeed haka ba,cikin rawar murya tafara magana " Dan Allah kayi hakuri nayi kuskure wlh bansan aljana na bud'ewa k'ofa ba," Dalla rufemin baki wane irin gargadi ne ban miki ba akan kwashe kwashe ai gashi nan kin janyo wa kanki daga taimako,Dan babu abinda ya shafeni,haka zamu koma gidan ayau duk abinda tayi miki ke kika janyowa kanki,Dan da baki bud'e mata k'ofa ba babu yanda zata shigo gidan,Surayya da ta ganta ta kulle k'ofarta kinga tana can hankalinta kwance,tunda ya fara magana hawaye ke zubo mata,"Abdul wlh bazan iya kwana agidanan ba ni nasan mai nake gani," Abdulmajeed d'aga mata hannu yayi yace " wa ya janyo?
.
babu abinda ya dameni jiya barcina nasha lafiya lau babu komai a gidana ke da kike bud'e mata k'ofa ke kike ganinta dan haka" shiru yayi sakamakon ganin aljanar nan daya yi abayan Muhibba ayanayi na ban tsoro ta gwalalo idonta gabad'aya tana kallonsa,jikinsa ne ya hau rawa ,cikinsa yayi wani irin murd'awa ya saki tusa mai shegen d'oyi ihu ya saki yana " kiyi min rai wlh karya nake jiya ban runtsa ba wayyo Allahna" Muhibba ido ta gwalo tana kallonsa cikin tsananin mamaki Dan ta waiga bata ga komai ba,Abdulmajeed ganin Ajanar ta nufoshi yasa yayi waje dagudu,sabida gigicewar da yayi d'akinsu Muhibba ya shige ya kullo k'ofar.
0 comments:
Post a Comment