A takaice ranar haka aka tashi taron nan batayi rawa ba sbd tsoron kar ya fadawa daddy...haka suka koma hostel itada Billy tanata ciccin magani Billy batabi ta kanta ba ta shiga sabagar gabanta...sai dare da babynta yazo snn ta dan samu nutsuwa dan bai bar hostel dinba saida ya tabbata yayi flushing away wnn damuwan da take ciki.
The next day around 10 suka fita sbd da wuri ake fara lecture din...dress code dinsu na ranan white ne dan basuyi anko ba saidai ance everybody should wear white cloth...itada Billy black straight skirt suka saka da farar shirt sai farin kimono da suka dora akan kayan itama white da digi digon black a jiki suka yafa black veil...ita Billy tasa turban snn tayi veiling da mayafin while hajia indo batasa komai ba sai dan mayafin data yafa akanta...daidai sa bags da suka rike iri daya ne suma duk farare...suna shigowa cikin school kiran Husna ya shigo wayan Billy nan ta dubi Aysha da sauri tace"Lamido ina tunanin su Hamma fasun karaso kinga Husna na kirana"...Aysha tace"to mu karasa parking space muga ko suna can"..daga haka suka wuce zuwa parking lots din...tun daga nesa suka hango motanshi dan haka suka nufi inda take...Hamman nasu ya shiga binsu da kallo yana murmushi yace"lallai ashe gayunku kawai kukeyi a makarantan bamu saniba"..Aysha tace"kai Hamma meya wani gayu a nan"..yana kallon Billy yace"gayu ne mana..dan bakiga yanda kukayi kyau bane"...kafin Aysha tayi mgn Husna tace"Hamma mudai dan Allah mu karasa ciki kar a fara abun arzikin bamu shiga ba..nasan anjima nayi zaka fara cewa azo a tafi daddy yace kar ayi dare"...murmushi kawai yayi gamida girgiza kai snn suka dunguma zuwa hall din...da yake yau kusan kowa yana inviting family ko friends dinshi sai hall din ya cika yayi taf fiyeda sauran ranakun...wuri suka samu suka zazzauna daga gaba gaba yanda za’ayi komai akan idonsu snn suka cigaba da kwasan hira kaman sun shekara basu hadu ba...suna nan zaune gab da za’a fara Sa’eed shima ya shigo tareda lubna aikam suna ganinta suka mike zuwa inda take sukayi hugging dinta..shi kuma Sa’eed ya karas shna gaisawa da Hamma dasu Husna...bayan sun gama rungume rungumensu suka karasa suma suka zauna Lubna nata jadda musu sai sunzo kd bikinta nanda few weeks sukace zasuje inshaAllah...saida kowa ya gama shiga snn Proprietor,Provost da kuma manya manyan doctors da zasu gabatar da lecture suka fara shigowa...duk yawan jama’an dake wurin baisan meyasa idanunshi suka hango mishi ita zaune a tsakiyar wasu maza ba...ranshi yaji ya 6aci sosai yanxun duk space dake cikin hall din nan ta rasa inda zata zauna sai ta shiga cikin maza?..wai wace irin yarinyace ne wnn?..wane irin shegen rashin hankali gareta?..har suka isa high table da aka tanada dominsu suka zauna bai denajin ciwo ba...sai a lokacin Aunty Sumy dasu Miemie suka karaso...Nur ne ya amsa mike daga hannun mc yayi welcoming guests dinsu snn ya gabatar da sunan disease da za’ayi lecture a kanshi Sickle Cell Anaemia wanda akafi sani da Sickler...tafi wurin ya dauka kowa yana ganin dacewar gabatar da lecture akan Sickler sbd yanda masu ciwo irinshi suke facing challenges a rayuwarsu na yau da kullum...bayan hall din ya danyi tsit ya dora da fadin"and before i hand over the mike to our qualified doctor Olusola Bulus...i will like to invite Aisha Ahmad Lamido for a brief introduction of Sickle Cell Anaemia"...fuska daure Bobby ke kallon abokin nashi ko meye ma’anar hakan da yayi oho?..meye amfanin wani kiranta tayi bayani tunda ga doctor zaiyi lecture a barshi ya gabatar da abunshi mana...Aysha da taji sunanta unexpected kasa mikewa tayi daga inda take zaune...Hammanta ne ya sunkuya yayi mata mgn a kunnenta kan idon Bobby da idanunshi ke wurin...a hankali ta mike daga inda ta fito zuwa kan stage...tana isa ya ba ta mike dake hannunshi ta amsa ta fara da gaishe da manyan baqi da colleagues dinta dake wurin snn ta shiga yi musu brief introduction ko ince explanation na Sickle Cell Anaemi kaman yanda aka bukaceta...ta burge mutane da dama a wurin domin tun daga kan yanda take mgn with courage and confidence zaka san ba karamar mai kwanya bace...uwa uba kuma dressing dinta daya sake fito da ainihin kyawunta hatta yanda take mgn ma abun kallo ne...hall din yayi wani irin tsit ko tari babu sai sweek voice dinta dake tashi ta cikin speakers...bata shiga deep ba ta tsaya iya introduction kmr yanda akace tayi snn ta sake miqawa Nur mike din ta sauka daga wurin..tafi sosai aka shiga yi mata hatta doctors dake wurin saida suka jinjina mata dan tayi kokari sosai ba kadan ba...tana karasawa inda take Hammanta ya mika mata hannu suka tafa and again kan idanun Dr.Bobby da yabita da wani hadadden harara data sauka daga stage...kawai haushi yakeji and ya rasa dalili...gaba daya mutanen wurin ma haushinsu yaji yanaji for clapping mata da sukayi ballantana kuma Nur dashine wanda ya haddasa komai...aunty sumy dake zaune daga dan gaba itama kallonshi kawai take tana mamakin abunda aka mashi yake wnn cin kunu haka...ta lura ko noticing zuwansu ma baiyi ba hankalinshi na can wurinda batasan me yake kallo ba...text tayi typing a wayanta"what’s wrong?..why are u frowning ur face?.."ta tura mashi...wayan na aljihunshi yanajin shigowan text bai duba ba..ta sake tura mashi"Bobbyyyy"...zaro wayan yayi cikeda haushin damunshi da akeyi zaisa a flight mode idonshi ya sauka kan sunanshi data kira...sender ya duba yaga itace sai ya bude message din da sauri shi sam ya mance sunyi mgn daxu tace mishi suna hanya...yana gama karantawa ya daga kai yana duban wurin wai ko zai hangota amma bai ganta ba...text ne ya sake shigowa wayan ya duba sai yaga tace"ba ganinmu zakayi ba kawai ka bar frowning face dinka haka kar guest dinka suyi tunanin wani abu"...ajiyar zuciya ya sauke yana sake wurga idonshi still bai gansu ba dan haka yayi typing"ohk na dena"shima ya tura mata...yana gama tafiya ya maida wayan aljihu yana kokarin daidaita face dinshi kmr yanda tace kar guest dinshi suyi tunanin wani abu...doctor Olusola ne ya fara bayani kan yanda Sickler yake..yanda yara ke samu ta hanyar iyayensu and hanyoyin daya kamata abi don ganin sun zauna cikin koshin lafia...saida ya dauki more than one hour yana abu daya kafin ya gama...bayanshi wani doctor Solomon shima yayi bayani stigmatization da suke fuskanta a society da kuma hanyoyin daya kamata abi don kiyaye wnn stigmatization din and lastly doctor Nuruddeen wato Provost yayi bayani kan hanyoyin da za’abi wajen preventing haihuwan yara masu sickler snn idan an haifesun hanyoyin da za’ayi taking proper care of them tun daga neonatal stage zuwa child har zuwa adolescent...daga nan kuma ya sake mika godia wa duk wanda suka halarci taron a matsayinshi na Provost na FCNM tareda fatan komawa gida lafia...daga nan kuma sai aka hau raba drinks da snacks each table aka ajiye musu nasu snn aka faraci...bayan sun gama Provost ya sake amsan mike yace yanaso su zama ready for the Fun Walk don in the next 10 minutes zasu fita...haka kuwa akayi duk mutane suka fara mikewa suna fita daga hall din...Bobby ma ya taso daga inda yake zuwa inda ya hango su aunty sumy zaune...tun kafin ya karasa Ilham ta mike tana rungumoshi..shi kuma yajata suka karasa wurin yana kokarin dora smile kan face dinshi yace"wai yaushe kukazo?..kinsan banga shigownku ba?.."aunty sumy tace"dama ya zaayi kaga shigowanmu hankalinka na wani wajen..wai mema kake kallo ne kam?..and meya 6ata maka rai da kaketa cin magani haka?.."dan shafa kanshi yayi yace"bafa wanda ya 6atamin rai kawai zaman wajen ne ya isheni..kuma zakuyi walk din ne ko bazakuyi ba"..mikewa aunty sumy tayi hannunta rikeda bag dinta tace"rufamin asiri da wnn tafiyar Bobby..komawa gida zamuyi dama lecture mukazo ji kuma an gama so we are going back home"...gyada kanshi yayi cikin jin dadin tafiyar da zasuyi yace"gara ku koma ai dan wnn walk din wahalar banza ne kawai"..aunty sumy ta wuce suka fara tafia tace"wnn karon ma bazakaje ba knn?.."yace"haba!.Allah ya kiyaye ai bazan iya wnn wahalar ba"..murmushi kawai ta sakeyi batace komai ba...saida ya rakasu har mota yaga sun shiga sun fita daga makarantan snn ya juya zuwa office din Nur don yasan da yawa daga guest din da basu tafi ba suna can...snacks ya samu sunaci da drinks dinsu sunata kwasan hira kaman basu ba...daidai lokacin da ya shiga yaji Gabriel na fadin"ni wlh yarinyar nan cema ta burgeni gaba daya tunda na ganta naji na gagara sukuni...yaya ma sunanta kace?.."yayi referring tambayar to Nur dake sauraronshi yana daria yace"kai wnn yarinyar tafi karfink wlh..Lamido matar manya ce ba yara irinku ba"..daria suka saka Gabriel din na cewa kodai shima Nur sonta yake Nuru yace ai babu mamaki ma idan yana son nata...Bobby dake tsaye jikin kofa yana sauraran conversation din nasu kasa karasawa ciki yayi..haka nan yaji wani irin faduwar gaba dajin abunda Nur ya fada..shi sam mgnr Gabriel bai daukeshi da wani abu kaman na Nur ba..da dadewa dama yana zargin Nur sonta yake and now ya tabbatar da zarginsa..dukda ba fitowa fili yayi ya furta yana sonta ba a iya mgnr daya fada ya fahimci da gaske son nata yakeyi...juyawa yayi ya bar office din yana sakin tsaki a fili ya furta"ko uban me Nur zaiyi da wnn yarinyar oho?.."shidai wlh wnn yarinyar yana ganin ko daura masa ita akayi a kafarsa zai kwance ya wurgar don baiga amfanin auren mace mai shegen rawar kai da kula samari ba..jiya ma ya ganta da Abdool and a yanayin da yaga suna mgn yasan da kyar idan shima ba saurayinta bane..daxun ma ya ganta zaune tsakiyar maza su dinma kuma ba abun mamaki bane idan ance samarinta ne shi kam me zaiyi da mace kaman wnn da take daukan maza kaman ‘yan uwanta mata?..a fili ya sake furta"God forbid"..harda tsartar da saliva.😹
Bayan few minutes gaba daya wanda zasuyi walk din suka fita masu police band nata kida haka masu dj sunyi playing music sauran kuma ana tafe ana rawa kowa rikeda banner da akayi rubutu a jiki...dukda tafiyan akwai nisa ba karamin enjoying dinshi sukayi ba don suna tafe suna takawa hadda Aysha data gama dubanta tsaf bataga proprietor a wurin ba...duk inda suka wuce anata kallonsu sbd yawansu haka duk titin da suka hau suke rufeshi gaba daya saidai masu wucewa su nemi wani hanyan...suna tafe sunata daukan pics da videos abundai sai wanda ya gani...haka suka gama zagayensu suka dawo college din a kafa.
Suna shigowa college din can bayan classes dinsu dake nan kmr garden suka wuce kai tsaye suka shimfida manyan carpets a wurin snn suka fiddo abincin da sukazo dashi daga gida suka zazzauna nan sunaci sunata kwasan labari...idan kaga yanda suke hira zakayi zaton duk ‘yan uwan juna ne irin wanda suka shaqu da juna sosai...Lubna da Aysha da Billy sunacin nasu tare..Hamma da Sa’eed suma sunacin nasu sai Husna da Yusra...Billy ce kadai ba ‘yan uwanta kasancewar ita kadai ce mace a gidansu duk sauran siblings dinta maza ne...bayan sun gama ciye ciyen sai suka fara daukan pictures da videos Aysha nata ma Hammanta da bayason daukan hoto daria...a takaice basu suka bar FCNM ba sai after five...suka rakasu har mota suka tafi snn suka dawo ciki ya rage daga Aysha da Billy sai Sa’eed da Lubna...daga nan ya kwashesu zuwa hostel don Lubna cewa tayi ita sai dare zata koma gidan Hajia..hakan kuwa akayi don bai dawo ya dauketa ba sai around 9 na dare..haka suka rabu sunata zullumi kaman bazasu sake haduwa ba bayan ko gobe tace zata dawo kallon sports da zasuyi.
Washegari Friday basu fito daga hostel ba sai wajen 11...lokacin already wanda zasuyi sports suna can field sun fara abunsh...karasawa suma sukayi inda babban sports field din nasu yake...waje suka samu suka zauna suna kallon football da maza keyi...Bobby kam zamanshi yayi a gida sam baiyi niyyar fitaba amma yana tuna zata iya zuwa ta aikata wani abunda ba shikenan ba idan baya nan sai ya mike da sauri sairi ya gama shiryawa ya fita...office din Nur ya tsaya suka tafi field din tare...suna karasawa ciki as usual ya hangota zaune tareda Lubna da Billy sai kallon ball suke suna ihu..muryanta mayafi na kowa tashi a wurin sbd bestynta yana kokari...yana daukan ball zakaji ta fara fadin"yes..yauwa besty na go on..yauwaaa"..Lubna sai daria take mata yayinda Billy tace"ai wlh zaki gaji kuwa indai Lamido ce..haka nan take kallon ball dinta tana ihu idan suna abun arziki knn..idan kuma abun tsiya sukeyi tsit zakijita kaman ba itaba"...Lubna dai dukda haka ta kasa dena daria...Bobby da suka zaune opposite dinsu yana kallonta tana ihu sai kace namiji..ranshi ya 6aci sosai ya rasa wace irin yarinya ce ita...yana kallo da aka tafi half time wnn saurayin da sukayi drama tare yazo inda suke ita kuma ta mike da sauri ta mika mishi dan towel ya goge jikinshi snn ta bashi ruwa yasha sai doka masa murmushi take tanajin kaman ta goyashi sbd farin cikin yana performing...yana gamawa ya maida mata towel da goran ruwan snn ya sake komawa ciki...zuwa yanxu Bobby a kule yake tsaf ji yake kaman ya mika hannu ya kwada mata mari..sbd kazanta har amsan towel daya gama goge guminshi takeyi?..wnn wane irin kazanta ne?..duk kokarinshi na yaga ya manta da abun kasawa yayi dan haka ya mike bayan yacewa Nur yana zuwa ya fita daga wajen...kai tsaye office dinshi ya nufa snn ya zaro wayanshi yayi dialing number dinta da ranar yayi saving as Lamid...wayan na cikin jaka yanata ringing bata gani ba shi kuma bai fasa kiraba sai a karo na uku tayi picking...murya a cushe yace mata"come to my office"...zatayi mgn yace mata"now.."da sauri ta matsar da wayar daga kunnenta sbd ihun da yayi...su Billy ta kalla rai a 6ace tace musu zataje proprietor na nemanta daga haka ta fita daga wurin da sauri tana zullumin ko wani abun ta sakeyi...tana shiga office din ya bita da wnn kallon as always..saida ta karasa gaban table dinshi ta tsaya kafin tayi mgn yace"waye wnn da kike mikawa ruwa daxu?.."da sauri ta dago tana kallonshi sai kuma tayi kasa da ido tace"besty na ne"...da mamaki sosai yake kallonta yace"bestie?.."gyada kai tayi tace"eh.."ranshi ya sake 6aci wato har bude baki ma takeyi tana ce mishi bestynta ne?..a fusace yace"ke yanxu ko kunya bakiji kike kiran wani qato da besty?..are u madd?.."turo baki tayi tana marairaice mishi tace"Allah Sir besty na n..."bata karasaba ya daka mata tsawanda yasata shiga taitayinta sbd firgici...yana huci yacigaba da fadin"wato ke gaba daya bakida aikinda ya wuce kule kulen maza koh?..jiyama na ganki da Abdool shi kuma meye tsakaninki dashi?.."kai tsaye tace"sona yakeyi"..wani irin dumm Bobby yaji gabanshi ya fadi..baisan meyasa duk yaji kalmar wani na sonta sai yaji wnn faduwar gaban ba...bazai manta ba jiya ma haka yaji da Gabriel yace yana sonta..amma why yake jin irin haka?..ganin baida amsan tambayan ya sake daure fuska yana kallonta yace"wato sonki yakeyi?..sbd bakida hankali ke kowanne namiji yace yana sonki saiki biye mashi kuna shashanci koh?..are u even alright?.."turo baki ta sakeyi cike da gajiya da wnn masifan nashi tace"nifa ba sonshi nakeyi ba..kuma ni bana kulashi ko jiyan ma daka ganmu hakuri yake bani ai"..yace"hakuri yake baki shine naga kuna daria?..ni zaki maida mahaukaci?.."kaman zatasa kuka tace"Allah hakuri yake bani kuma na ce mishi inada wanda nakes..."bai bari ta karasaba ya katseda fadin"just stop it okay?..stop it"..tsorata tayi sbd ganin yanda yanayinshi ya sake sauyawa lokaci guda..shi kuma ya dakatar da ita ne ba don komai ba sai don bayason jin wnn faduwar gaban da yakeyi idan yaji ana sonta...yanxun da take kokarin ce mishi tana son wani yasan zai iyajin fiyeda na baya...idanunshi a kanta yana kallon yanda take turo baki kawai sai ya runtse nashi idon don a yanda yakejin zuciyarshi yana iya gaura mata mari sbd zafin da yakeji...kofa kawai ya iya nuna mata ba tareda ya bude idon nashi yace"fita.."kaman jira takeyi ta mike zata fita har takai kofa yace"kuma idan baki maida gashin nan da kika fito dashi waje ba you will see the other side of me"..turo baki tayi ta zake juyawa zata fita yace"ba mgn nayi maki bane?.."dakatawa tayi da tafiyar ta janyo mayafin kanta zuwa inda gashin goshinta ya fito...bai tareda ya sake kallonta ba yace"now leave"..da sauri ta bude kofar ta fita tana fadin"mutum sai shegen baqin hali..ko ina yaji hausa haka maoho?..he speaks kaman hausawa ne suka haifeshi".
Bayan sati hudu...
A cikin four weeks din nan sau biyu suna zuwa gida weekend...karatunsu kuma yanxu ya dauki zafi as suna dab da gama 2nd semester year 2 daga nan kuma sai final year...Sa’eed kuwa shirye shirye sukeyi sosai na Council Exam dinsu daya gabato..Hospital Final Exam zasu fara daga nan kuma wanda yayi passing ya wuce School final inda daga nan kuma za’a turasu asibiti waiting results...har basu son tuna Council din nan sbd hakan yana nufin sun kusa rabuwa da besty...hatta Billy da ba wani shiri sukeyi sosai ba tana tunanin rabuwar nan sbd Sa’eed is one of the best things that have ever happened to them in Kano..sam basu san ya rayuwa zai kasance bayan babushi ba..wnn dalilin yasa Aysha har kuka takeyi idan ta tunada haka...kawai she is going to miss him like crazy...a 6angaren Bobby kuwa fita harkanta yayi completely sbd kwata kwata baison jin abubuwan da yakeji gameda ita...so yake ya dawo da tsanar da yayi ma Fulani ya dora mata amma sam zuciyarshi taki bashi hadin kai and baisan meyasa ba...sai suyi sati ma basu hadu ba sai idan da wani dalili idan sun hadun ma kuma dinke fuskanshi yakeyi tsaf wai kar ta rainashi...tsakaninshi da daddy kuwa zumunchi suke sosai don every Friday yana mishi sending friday text message snn yana kiranshi yana gaishesheshi once in a while haka..sosai yakejin mutumin na sake kwanta mishi a rai sbd mu’amala da yake dashi me kyau da mutane...har yanxun kuma bai dena mamakin how he end up giving birth to Lamido da tunda yake bai ta6a ganin fitinanniyar yarinya irinta ba.
Yau Saturday tun safe Aysha ta tashi ta ciwon baya da kafa as a result of period dinta da yaz..tun safen kuma take kwance kan gadon Billy tanata faman murkususu tana rikeda bayan nata tana hawaye...Billy dake zaune kusada ita ajiyar zuciya ta sauke tun daxu take fama da ita ko dan pcm tasha taki sha kuma uk tabi ta isheta da kuka sai kace small girl...daga karshe mikewa tayi tana cewa"bari in dauki waya in kira Ammi in fada mata ni bazan iya wnn wulakancin naki ba..or better still in kira Proprietor in fada masa kawai yazo komai kukanda zakiyi ya danqara maki allura kowa ma ya huta"...tana rufe baki Aysha dake kuka wiei tace"dan muhammadu manzon Allah kada ki kirshi Billy..sai kace bakisan halinshi da mugunta?.."Billy tace"yo ya kikeso in miki kin sani a gaba tun dadu kinamin kuka...kiranshi zanje inyi wlh ni bazan iya da ta6ararki ba"...da sauri Aysha ta sake fadin"dan Allah don’t call him..kawai ki kira baby yazo ya kaini asibiti tunda nasan besty yanxu suna karatu"...disgusting look Billy ta watsa mata tace"seriously?..ke yanxu ko kunyan yasan kina period bakiji?.."daure fuska tayi dukda hawaye da takeyi tace"kawai dan nace ya kaini asibiti sai akace miki zuwa zanyi nace ga abunda ke damuna?..nidai ki dauki wayata ki kirashi kar in mutu"...Billy bata sake mgn ba ta dauki wayan nata ta fita..cikin ranta tace"zakiga karyar iskanci ba babyn da zan kira wlh"...searching contact din Bobby da tayi storing as Mr.Wicked tayi yana fitowa kuwa ta danna masa kira.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
24
Yana zaune bedroom dinshi yana aiki da MacBook kiran ya shigo...mamaki sosai ya kamashi ganin ita ke kira..tunda yake da ita bata ta6a kiranshi ba shima kuma bai kiranta sai idan tayi wani abun ya kirata tazo office dinshi ya kare mata tatas snn ta juya ta tafi...to yau kuma meyasa ta kirashi?..wata zuciyar tace mishi"kilan batada lafia"..da sauri ya dauki wayan daya tunada hakan...har zaiyi picking sai kuma kaman wanda ya tunada wani abu yaki dauka yana kallo har ya gama ringing dinshi wani kiran ya sake shigowa sai a snn ya daga baice komai ba...a daya 6angaren Billy tayi kokarin tattara jarumtarta tace"good afternoon Sir..Sunana Bilkisu"...shiru yayi na wani lokaci kafin yace"umhum what is it?.."saida ta sake nutsuwa snn tace"Sir Lamido ce dama tun safe batada lafia kuma nayi nayi da ita ko pcm tasha taki sha..shine nac..."bata karasa ba yace"kun kaita Clinic?.."da sauri tace"taqi yadda wlh..ba yanda banyi da itaba wai ita bazata jeba sbd kar ayi mata allura"...shiru ya sakeyi a cikin ranshi yace"wato har yanxu bata dena kukan allura ba koh?.."a zahiri kuma yace mata"tell her that nace tazo Clinic yanxu..idan ta bari na rigata zuwa kuma zataga abunda zai faru"...yana gama fadan haka ya kashe wayarshi tareda mikewa daga inda yake ya shiga Closet dinshi ya sanyo kaya snn ya fito ya dauki waya da keys dinshi ya fita..sam baida intension din zuwa ko ina yau din nan..niyyarshi kawai sai around 4 ya shiga Hospital daga nan kum ya dawo gida abunshi amma yanxu wancan ta sanyashi doleya fita ba don yanaso ba...sallama yayi dasu Mummy snn ya bar gidan...yau da kanshi ma ya tuka motarshi sbd ya riga ya sallami driver dinshi cewar sai da yamma zai fita...da yake cikin sauri yake driving din nan da nan sai gashi a makarantan...yana gama parking ya bude motar ya fita kai tsaye ya wuce clinic don ganin sun karaso ko basu zoba...tun kafin ya karasa dakinda suke yajiyo sautin kukanta tana cewa"nidai dan Allah bana son injection plss..wlh zai dena da kanshi ko bansha magani ba"...Nurse din dake kokarin bata paracetamol tasha tace"ki daure dai kisha zaki dan samu sauki ko yayane..daure kinji"...ta bude baki zata kwaso wani magiyan idonta ya sauka a kanshi aiko ba shiri ta tsuke bakin nata hawaye na sake gangarowa face dinta...fuska a murtuke ya karaso ciki bayan sun gaisa da Nurse din yace"bring the injection tray"..ba musu Nurse din ta wuce ta hada masa komai dazai buqata kan tray din snn ta dora kan trolley ta kawo mishi...hannu Aysha ta fara yarfawa ganin da gaske alluran zaiyi mata hawaye nata ‘yar tsere akan face dinta...daukan hand glove yayi ya fara sakawa yana dubanta sternly yace mata"get up"...hawaye sosai takeyi wani kan wani har yanxu kuma bata dena yarfa hannu ba...ya sake daure fuskanshi yace"bazaki saukoba?.."dirowa tayi daga gadon da sauri saura kadan ta fadi kasa sbd yanda legs dinta suka rike...Billy dai juyawa tayi ta fice daga dakin sum sum sbd kar masifan ya biyo ta kanta...itama Nurse data tabbatar ta kawo duk wani abu da zaiyi amfani dashi gabanshi saita juya slim alim ta fita daga wurin ya rage dagashi sai ita a cikin dakin...yana gama sa safarshi ya dauki alluran yayi withdrawing ya cire air bubbles snn yayi recapping syringe din yana kallonta yace"juya.."kuka ta saki sosai tana cigaba da yarfa hannu tace"Sir dan Allah dan Annabi kayi hakuri"...fuska a daure yace mata"ina wasa dake?.."girgiza mishi kai tayi da sauri yace"then kindly turn your back before i loose my temper"...juya bayan nata tayi tana cigaba da kuka tana yarfa hannu...baice mata komai ba ya dauki swab dake ajiye sai kuma ya kalli dogon rigan dake jikinta yace"daukeshi sama"...hawaye takeyi sosai gashi da kyar take iya tsaiwa sbd legs din a rike suke...ya sake fadin"i said ki dauke riganki sama..wane irin abune ma zaisa kisa dogon riga keda za’ama allura?..knn haka kike zuwa kina bude jikinki gaban ko wane kato koh?.."hawayenta ta goge tana turo baki ganin a wnn situation dinma saiya mata masifa tace"nifa ba haka nake zuwa ba..kuma ai inada wando a ciki"...tsaki yaja tareda fadin"naji..now dauke rigan in samu in maki i have something important to do"..sake turo bakin tayi tana hawaye takai hannu ta dage rigan nata daga can kasa..idanunshi ya sauka kan pure white legs dinta da suka bayyana..dauke ido yayi da sauri gabanshi har wani faduwa yayi kaman bai ta6a ganin farar fata ba sai a kanta...saida takai rigan iya waist dinta snn ta rikeshi a gun tana sake rushewa da kuka..tsaki ya kara saki yanajin kukan nata na damunshi ya risina ya danyi clearing injection site din da swab kafin yakai alluran ta saki rigan tana sakin wani shegen kara tace"wayyo Allah Sir i beg u in the name of Almighty kayi hakuri..plssss"..tsaki ya saki tareda kai hannunshi ya dago rigan nata cikin tsawa yace mata"rikeshi..and kika sake sakinshi wlh sai nayi doubling injection din"...tun kafin ya rufe baki ta kama rigan gam ta rike tana runtse idonta jikinta har shivering yake...kallon yanda ta matse jikinta yayi yasan idan bata saki jikin ba kuma ana iya samun matsala sai kawai ya girgiza kai ya sake risinawa daidai bombom dinta dake sanyeda pink leggings iya guiwa...lumshe idonshi yayi tareda kai hannu ya sauke mata leggings din kasa kadan snn ya bude idon yayi sauri ya zura needle din kafin ta kara sakin rigan..tanajin shigan needle din jikinta ta saki wani azababben kara lokaci daya kuma sai tayi dif ta tafi luu zata fadi yayi saurin kamota jikinshi Allah ya taimaka ya zare alluran daga jikinta...rungumeta yayi sosai ganin kmr ko numfashi batayi...gabanshi ya bada sautin dammmm kardai ace yarinyar nan suma tayi?...yana rikeda ita da hannu daya ya durkusa ya zura syringe din a safety box snn ya juyo da ita tana facing dinshi ya shiga girgizata yana fadin"Hey.."ganin ko motsi batayi yakai hannayenshi ya rike cheeks dinta dasu yana kallonta sai kawai yaji tayi kasa zata fadi sai ya dagata cak ya dora a kan gado...kallon very cute face dinta dake tsaya mishi a rai yayi...bakinta na nan a tsuke kaman ba suma tayi ba sai kuma kananun gashin goshinta da sajenta da suka kwance luf luf kaman na jariria...lumshe idonshi ya sakeyi ya bude a kan dogon gashinta dake nan a barbaje dan dan veil data yafa tuni ya zame ya fadi kasa..Bobby kasa controlling kanshi yayi..duk yanda yakai da son ya dauke idonshi akan gashin kasawa yayi and he couldn’t help it saida yakai hannu a hankali ya dora a gashin kaman wanda zai dora a wuta...lumshe ido ya sakeyi dayaji gashin nata da dan karen laushi..dunia ba abunda yakeso a jikin mace kaman gashi..yanason yaga gashin kan mace da tsayi da laushi and wnn da yake ta6awa is even more softer and longer than he thinks...kawai shafawa yake that har ya mance wacece kwance nan kusa dashi ya kuma mance Clinic suke and mutum na iya shigowa at any moment...a hankali ya gangaro da hannunshi kan sajenta nanma ya lumshe ido..ya dade yana ayyana yanda sajen nan nata yake domin duk yanda zata janyo hijab dinta saidai gashin goshinta su rufe amma ba sajenta ba...lokaci daya kuma ya dauke hannun nashi da sauri tareda wani irin mikewa a rikice kaman wanda ya tunada wani abun...zaro idanunshi yakeyi ya shiga girgiza kai yana tafia da baya da baya kaman wanda yaga abun tsoro cikin zuciyarshi yake fadin"Noo..not me plss..what have i done..what just happened?..innalillahi wainna ilaihi rajiun..Ya Allah forgive me..Astagfhirullah ya Rahman forgive me"..daga haka ya juya da sauri ya fita daga dakin...yayi kokarin daidaita kanshi snn ya karasa inda Billy ke zaune ba tareda ya kalleta ba yace"ki watsa mata ruwa idan bata farfado ba ki kirani"..yana gama fadan haka ya wuce Billy kuma ta koma dakin da sauri tana mamakin wai Lamido har suma tayi sbd injection?...tana shiga ta sameta kwance a kan gado kaman gawa dan haka tayi dispensing ruwa ta watsa mata a fuska...lokaci daya ta saki wani numfashi mai karfi tareda mikewa zaune da sauri tana kalle kallen dakin...Billy ta karasa kusada ita ta zauna tareda kamo hannunta tace"sannu ya jikin naki?.."kwace hannunta tayi a fusace ta wani daure fuska ta sauka daga gadon...taku daya tayi ana biyun taji kafanta ya sake rikewa dan haka dole ta nemi wuri ta zauna tana cigaba da hawaye..a hankali takai left hand dinta can inda akayi alluran ta dan dora a wurin tana murzawa a hankali da sunan ana mulmula alluran kuma har yanxu bata bar hawaye ba...Billy da taga haka sai tayi zaune abunta tana binta da kallo kmr sabuwar halitta...after like 12 mins Sa’eed yazo daukansu..saida ya shigo har dakinda suke snn ya samu ya lalla6a bestyn nashi ta mike suka fita dan kememe kin kula Billy tayi ita a dole tanajin haushin kira mata Proprietor da tayi...idan kaga yanda take tafia zakayi zaton karyewa tayi a kafan ko kuma wani babban matsala dai kafan ya samu har yayi affecting tafiyanta...suna isa inda motarshi ya bude maya front seat ta shiga Billy ta shiga back seat shima ya shiga driver seat snn ya tayar da ita suka wuce.
Cikin ikon Allah washegari haka ta tashi garau kaman ba ita ke kukan ciwo ba jiya...kuma abunda mamakin shine yanda ko injection site din baya mata ciwo unlike before da duk akayi mata injection sai wajen ya kusa shekara yana damunta amma shi nashi yana gamawa ta dena jin ciwon wurin...she remember last time daya mata alluran ma hakan ya faru don a ranar ta warke garau babu ciwon kafa ko ciwon bayan snn kuma babu ciwo da dan swelling din da wajen allura keyi mata...tunda take bai ta6ayin wani abu ya burgeta ba amma this time around ta jinjina mashi kwarai don tunda aka haifeta ba’a ta6a mata allura wurin baiyi ciwo ba sai a kanshi...hakan ya nuna mata he isn’t only a qualified doctor he has magic handa too...tana zaune daki ta tasa pringles da babynta ya kawo kawo cikin shopping da yayi mata daxun saici takeyi kaman ba gobe...Billy suka shigo dakin tareda wata ta karasa ta dauki iron dinsu dake ajiye ta bata snn ta juya ta fita ita kuma ta karasa kusada Lamido ta zauna tana murmushi tace"wai Lamido har yanxu fushin ne?.."murguda baki Aysha tayi batace komai ba...Billy ta kara sakin smile kafin tace"dama Ammi ne tace idan baki kulani ba in kirata in fada mata"..tun bata karasa ba Aysha ta juyo tana kallonta da mamaki sosai tace"yanxu zuwa kikayi kika hadani da Ammi Billy?..sai kace bakisan halin fadanta ba?.."daria Billy ta saka tana mikewa daga inda take tace"dama mgn nakeso kiyi kuma kinyi..ba wata Ammi dana fadawa"...pillow dake kusada ita Aysha ta dauka ta wurga mata shi kaman zatasa kuka tace"amma kin shiga haqqina wlh..kinsan irin tsoron da naji kuwa?.."daria kawai Billy keyi ta fara rage kayan jikinta ta shiga bathroom.
Zaune yake a parlonshi waya rike a hannunshi sai jujjuyashi yake kaman wanda yake tunani...tun daxun yake zaune nan wurin yanaso ya kira yaji ya jikinta yake amma wani zuciyan na hanashi wai idan ya kira zata iya misunderstanding dinshi...yayi kokarin kira kusan sau goma yana fasawa sbd zuciyarshi dake raya mishi cewa kar ya kira...tsaki ya saki yayi wurgi da wayan snn ya kwanta nan kan sofa da yake zaune yana wani daure fuska kaman Lamidon tana gabanshi yanxu haka...sam bayason yanda zuciyarshi ke saqa mishi abubuwa a kanta...ya rasa dalilinda yasa tun jiya ya kasa macewa da halin daya barta a ciki kiri kiri yana son kira kuma ya hana kanshi...har yanxun bai dena jin uban laushin gashinta a hannunshi ba kaman yanda bai ta6a mance cute face dinta dake tsaya mishi a rai ba...lumshe ido ya sakeyi cikin ranshi yana ayyana ko mutuwa zatayi bazai kirata ba..to meye ma ruwanshi da rashin lafiyarta da har zai bi ya damu kanshi?...juyi ya sakeyi yana dafe head dinshi duk a kokarinshi na ganin ya hana kanshi kiran nata saidai abunda bai saniba shine duk taurin kanshi heart dinshi bazai dauka ba sbd yafishi taurin kai don haka dole ne yayi mata abunda takeso idan har yana son zaman lafia...kasa daurewa yayi daga karshe ya sake mikewa zaune ya dauko wayan nashi...yayi dialing number dinta yana wani hade rai kaman tana ganinshi...tana kwance daki suna waya baby kiran nashi ya shigo sbd tsabar dadin hira ko noticing kiran nashi ma batayi ba...Bobby da yaji an buga masa wani abu kaman guduma a cikin heart dinshi sakamakon busy da yaji alaman tana waya...haka har ya gama ringing dinshi bata dauka ba hakan kuma ya mugun 6ata masa rai dan yasan da kyar idan bada namiji take wayan ba...sake kira yayi still bata dauka ba sai a na uku ne akayi sa’a taga shigowan call din dan haka tacema baby ya bata two minutes zata kirashi...picking call din tayi da sauri bayan tayi hanging wancan tana wani turo baki kaman tasan yanda ya hade ranshi shima...tana kokarin gaisheshi taji yace"dawa kike waya?.."murguda baki tayi cikin ranta tace"ina ruwanka?.."a fili kuma tace"Hamma na ne"..shiru yayi ba mgn as gaba daya ma mgnr baisan sanda ta fito ba..shi kanshi saida yaji wani iri daya tambayeta amma ba yanda zaiyi ne shiyasa ya tambaya...baisan meyasa abubuwa irin haka suke son su dinga faruwa dashi ba yanxu..shi da sam ba haka yake ba wlh...jin bai sake cewa komai ba tace"hello"...wani mgnr ne ya sake su6ucewa daga bakinshi ba tareda ya shirya ba yace"ya jikinki?.."ita kanta saida tayi mamaki jin tambayar amma bata nuna ba tace"naji sauki"..bai sake cewa komai ba ya kashe wayarshi yana dafe kanshi da yaji kaman zai rabu biyu sbd ciwo...da yasan abunda zai faru knn da bai kirata ba wlh...kawai yana zaman zamanshi ya janyoma kanshi 6acin rai..ko waye Hamman data fada ma oho..a iya saninshi dai idan ance Hamma ana nufin yaya namiji saida i baisan meyasa jikinshi ya kasa amincewa da yayanta take waya ba...sam yasan ba haka bane ta fada ne kawai don ta gujema fadanshi amma zaiyi wahala idan bada daya daga cikin boy friends dinta take wayar ba...wnn tunanin kadai ya sake dagula mishi lissafi.
Kwanakin da suka biyo baya shirye shirye sukeyi sosai na End of Year Presentation da suka saba gabatarwa duk end of session.
Bobby kuwa tun daga wnn ranan bai sake kiran Lamido a waya ba..ko a hanya suka hadu ko kallonta baiyi dan ko gaisheshi tayi bai amsawa wai duk a kokarinshi na ganin yayi yaki da abunda yake ganin bai kamata ace yanaji ba kuma a kanta...yau friday tun safe ya shigo college din sbd meeting da yake dashi da entire staff karfe 10...bayan sun fito Nur ya biyoshi har office dinshi yana mishi bayanin Presentation da za’ayi next week...ya gama sauraranshi tsaf snn ya bar office din shi kuma sai a lokacin wani tunani ya fado masa...yasan zaiyi wahala wnn abun ace ba’ayi selecting Lamido ba dukda dai kowane department voting sukeyi a tsakaninsu ko wanne class tun daga year 1,2 da 3 zasu bada mutum daya da suka yadda da brain dinshi sai a hadasu su ukun ayi masu test kowa akan gaba daya courses dinshi na shekarar duk wanda yayi winning a cikinsu shine zaiyi representing gaba daya department...baisan meyasa haka nan jikinshi ke bashi ita zatayi winning ba..kawai shidai baya sonta da wnn abubuwan ba don komai ba sai sbd shegen rawar kan daya lura tana dashi snn abune wanda a gaban mutane za’ayi shi hadda wanda ba daga makarantan suke ba..shi kuma yanxu baisan meyasa yaki jinin yaga tana wnn abubuwan ba..sam bai son yaga tanata wnn rawar kan nata a gaban mutane suna kallonta hakanba karamin 6ata mishi rai yake ba...sanin zaiyi wahala idan batayi din ba ya lalabo numberta ya danna mata kira don yayiwa tufkar hanci...shiganta class knn taga kiran nashi ta wani zare ido sosai tana sake kallon screen din to make sure ba idonta ke mata gizo ba...to me yake nema a wurinta yanxu kuma?..ta samu ta huta da masifarshi a yan kwanakin nn shine yanxu zai wani kama ya kirata salon ya wargaza mata jin dadi...ganin ya kusa tsinkewa ta daga tareda kai wayan kunne tana turo baki..kai tsaye yace"meet me now"...bai jira cewarta ba ya kashe wayar..ita kuma ta mike tana kwaikwayonshi”wani wai meet now...as if i am his child..inyamurin banza dan rainin hankali kawai"...mikewa tayi tanata sababi ta fita zuwa office din nashi...secretary dinshi na ganinta ta dauke kai bata kulata ba itama batabi ta kanta ba ta tura kofa ta shiga da sallama...yana zaune kan seat dinshi yana dan juyawa a hankali idanunshi kan kofa...kai a kasa ta karaso gabanshi ta tsaya snn ta gaisheshi still ba tareda ta dago idonta..shima bai damu da ta dago din ba ya nuna mata seat dake bayanta a nutse yace"seat.."dagowa tayi ta kalleshi da mamakin abunda ya fada dan bata ta6a zuwa office dinshi yayi mata tayin seat ba sai yau...janyo kujerar tayi a hankali ta zauna still idanunta a kasa tana wasa da fingers dinta...ba yabo ba fallasa yace"akwai end of year presentation da za’ayi next week nasan kin samu labari koh?.."gyada mishi kai tayi alaman ta sani...yace"then so nake koda anyi selecting dinki a cikin participants kice you won’t do it"...sake dagowa tayi tana kallonshi da mamaki tace"but why sir?..already an riga anyi choosing dina and I can’t say no because I don’t want my department to loose"...kallonta kawai yakeyi yanda take wani explaining mishi bata san kome zata ce ba ganewa zaiyi ba...ya wani hade rai yace"i said you are not going to do it and that’s final"...sake dagowa tayi tana kallonshi da mamaki shima kallon nata yakeyi wai ko zata fahimci abunda yakeji ta cikin idanunshi amma sai yaga ta kauda kanta tareda daure fuskanta itama tace"nidai I can’t say no"...tun kafin ta rufe baki yace"haka kikace?.."shiru tayi tana kallonshi ya sake fadin"haka kikace kou?..fine..we shall see"..dan marairaicewa tayi tana mishi puppy eyes tace"yanxu sir fisabilillahi kawai sai inje ince musu bazanyi ba bayan an riga anyi selecting dina?.."cikin fushi yace"na fada maki baza kiyi ba and if u like go and do it kiga what will happened..just try me and see"...kallonshi kawai takeyi yanda yake mgn ita kam kome zaiyi saidai yayi wlh amma bazata fasa yin abunda tayi niyya ba..besides ko daddy zai fadama tasan bazai hanata ba tunda ba wani abun rashin kyau bane and sai tayi abunta wlh...ganin kallon da yake mata sai tayi kasa da idonta a hankali tace"shikenan zan fada musu su samu wani"...ajiyar zuciya ya sauke a 6oye dan wani irin relieve yaji ya samu jin abunda ta fada ita kuma ta sake dubanshi cikin nutsuwa tace"ina iya tafiya?.."baice komai ba sai kofa daya nuna mata alaman she can...mikewa tayi a hankali ta fita saga office din cikin ranta tace"in your widest dream ba..ai wlh sai nayi abuna saidai kawai ka ganni kan stage..shknn sai ince na fasa kilan aje a dauko wanda bata iyaba ta kayar da department dinmu..to bada A’i za’ayi wnn wautan ba..dan rainin hankali kawai".
Ranan Monday tana shigowa school ta wuce office din Nur da safe...yana zaune yana signing wasu papers ta karasa ciki ta zauna bayan sun gama gaisawa tace"Sir dama alfarma nazo nema wurinka"...Nur ya ajiye pen dake hannunshi yana kallonta sosai yace"ohk ina jinki"...tayi kasa da kai tana wasa da fingers dinta tace"Sir so nake dan Allah ko mgn zai hadaku da Proprietor kada ka nuna mishi ni zanyi representing midwifery a presentation din nan"...kallonta Nur yake da mamaki karara a face dinshi yace"amma why?.."tana turo baki tace"cewa yayi wai ko anyi choosing dina ince banyi and ni kuma inaso inyi shiyasa banaso ya sani saidai kawai ya ganni kan stage"...gyada kai Nur ya shigayi alaman gamsuwa before yace"no problem ur secret is safe with me..he won’t know inshaAllah"..murmushi ta saki tareda mikewa tace"thank u sir"..yana mata murmushi yace"u are welcom"..daga haka tayi mishi sallama ta bar office din...Nur ya bita da kallo cikeda mamakin abunda ta fada...shi bai gane kan wani dalili Bobby zai hanata participating ba..dama these days ya lura kaman abu na damunshi and bai ta6a fada mashi ba..."ko dai son Lamido yake?.."ya fada a fili trying to figure it out amma ya kasa...daga karshe sharewa yayi kawai cikin ranshi yace"kilan idan tayi wari ni zan faraji"..da haka ya kaida tunanin daga zuciyarshi.
Bobby kam hankalinshi kwance yake sosai data ce mishi bazatayi ba...har wani nutsuwa yaji ya samu na musamman wnn dalilin yasa bai sake yunkurin nemanta sbd ya sake jaddada mata ba...ranan Thursday ya kama zaayi presentation din and tun safe Lamido suka shigo school sbd shirye shirye da ake...auditorium dinsu na nan a cike maqil da mutane participants kawai ake jira domin hatta malamai duk suna nan ciki...as usual Bobby da Nur tare suka shigo kowa ya samu wurinshi ya zauna...Nur ne ya danyi briefing jama’a yanda tsarin abun yake...kowane participant za’a rubuta sunan topics kaman guda uku cikin courses da sukayi a shekarar snnayi folding dinsu ya za6a and duk wanda ya dauka akanshi zaiyi presentation din...bayan dogon jawabi ya sake daidaita mike zuwa zaitin bakinshi yanda mgnrshi zai fito radau snn yace"and our two participants are Sa’eed Mukhtar Makarfi from Nursing department and Aysha Ahmad Lamido from Midifery department”...wani irin dammm Bobby yaji kaman saukan aradu a cikin heart dinshi...gaba daya saiya shiga rudani jin Nur ya ambaci Aysha Lamido and idan ba wai mancewa yayi ba da bakinshi ya ta6a fada mashi kta kadai take bearing da Lamido a college din...shi kuma yasan sunyi mgn da ita tace mishi bazatyi ba amma why zaizo ya kira sunanta kuma?..kodai watace mai suna irin nata bai saniba?...kafin ya samu amsan tambayanshi ya hangota ta taso daga inda take zaune zuwa seat da aka tanadar musu...sanye take cikin uniform dinta fari qal sai shinning yake sbd iron...dan hijab dinta daidai chest dinta sai gashin goshi da sajenta da suke nan waje as always...wani irin sanyi yaji yana lullu6eshi kaman fever zai kamashi...ya lumshe ido ya bude yana sake jin ciwon karyar da tayi mashi har cikin ranshi.
Rano✨
Wnn litafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a turo evidence of payment via 07063800556.
25
A hankali take takawa wanda Bobby kejin each taku kaman a kana zuciyarshi take yinshi...wani irin nauyi yaji zuciyar tayi mashi kaman wanda keda heart problems...sake juyawa yayi ya kalleta nan take kuma yaji wani abu ja sake tokare makoshinshi...ko baa fada ba yasan gaba daya mazan wurin nan kallonta suke...hakan kuma yasa yaji kaman ya harbi kanshi ya huta...finally ta karasa seat da aka tanada dominsu ta zauna kusada Sa’eed daya rigata karasawa...sake runtse ido Bobby yayi yanajin ciwon zama kusa dashi a tayi...ya ganeshi sarai shine yaronda tayi acting as his wife ranan da sukayi drama and shine the same yaron da ta bama ruwa ranar da akayi sports...yanxun nan din ma a rasa da wanda za’a hadata sai dashi?..kodai wani hu ke tsakaninsu dashi ne wai?...bayan sun zauna daya daga cikin malamansu mata ta taso da wani box a hannunta mai kyau ta kawo wurinsu tace Sa’eed ya dauki daya tunda shine first presenter...ba mus ya zura hannu cikin box din ya dauko paper daya cikin guda uku da suke ciki snn ya bude...sunan topic din ya gani a rubuce dan haka ya mike daga inda yake yana nuna mata ita kuma ta amsa daga hannunshi ta nunawa malamai then back to students snn ta koma wurinta ta zauna...dan matsawa yayi jikin white board dake ajiye nan wurin ya rubuta sunan topic din nashi snn ya fara presentation dinshi a tsanake...gaba daya hall din yayi tsit voice dinshi kawai akeji...Bobby dai na zaune kaman gunki sbd tsabar abubuwa da suka taru suka mashi yawa...yasan yanxu ko bindiga za’a zare ace ya fadi abunda yaron ke fada bazai iyaba as hankalinshi baya wurin gaba daya...kawai yanajin ciwon deceiving dinshi da tayi tace mishi bazatayi ba...ruwa dake ajiye gabanshi ya dauka yayi sipping ya ajiye tun yanxun yanajin haka idan ta fara nata kuma kilan zaucewa zaiyi...baisan meyasa Allah zai dora mashi wnn masifan a kanta ba...Sa’eed saida ya cinye 40 minutes da aka deba mishi snn yayi handing over mike din ya koma ya zauna anatayi mas tafi dan yayi kokari sosai ba kadan ba...bayan Nur ya gama praising dinshi snn ya sake kiran Aysha Ahmad Lamido data karaso tayi nata itama...kaman dazu wnn matarta mika mata box itama tayi picking one a cikin papers uku dake cikin box din snn ta mike a hankali zuwa inda board yake...kallonta kawai Bobby yake kaman bai ta6a ganinta ba sai yau...glasses data sa a idonta ya zauna daram shi sai yaga kaman ma bai ta6a ganin kyan da glass din yake mata ba sai yau...ya sake daga eyes dinshi zuwa goshinta da kusan rabin gashinta ke waje sbd ita ba gwanar sa dankwali ba hula bane..sam bata sonsu sbd suna takura mata shiyasa hijab kadai take zurawa ta tafi abunta...ciwo yakeji sosai yasan yau kaf wurin kowa saiya gama ganin gashinta..kowa kuma sai yaji voice dinta to his satisfaction...tunanin hakan yasa wani hadadde zafi ya kunno kai cikin sanyin da already ya faraji...lumshe ido kawai yayi ysna karanta duk addu’a da yazo bakinshi for he don’t want to loose it kamar yanda yayi ranan festival...sam bayason a fara zargin ko da wani dalili yake aikata haka while baya da wani dalili kawai dai yarinya ce Allah ya jarabceshi da ita da ko kusa bata son ya zauna lafia...idanun nashi a rufe yaji ta fara presetation din cikin sweetes voice dinta...sake runste idon yayi yanaji kaman yaje ya toshe kunnen kowa dake wajen yanda ba wanda keda daman jin muryan nata sai shi kadai...kwata kwata baya fahimtan abunda take fada shidai kawai yasan mgn take in a sweet tone amma ko za’a kasheshi bai iya fadin ga abunda take cewa...tsoron bude idonshi yake sbd gudun abunda hakan zai haifar amma daga karshe kaman idon nashi sunfi karfinshi ne dan ji yayi sun bude kansu da kansu basu fada ko inaba kuma sai a kanta...nan kuma ya tsayar dasu a kanta yana kallon yanda take mgn tana demonstration da hands dinta...gashi sai dan matsawa take from one place to another hakan kuma yasa jikinta ke dan shaking as if she’s doing it intensionally ga kuma gashinta koshi yana iya ganoshi daga inda yake...baisan lokacin daya rike kanshi da yayi mishi wani azababben sarawa ba...har wani jiri yaji yana daukanshi all of a sudden...addu’a kawai ya shiga jerowa dan samun sassauci amma abun kaman gaba ma yakeyi...ita kuwa Aysha presentation dinta take hankali kwance as ba wani sabon abu bane a wurinta...gaba daya tama manta da wani Bobby and his masifa abunda yake gabanta kawai takeyi...bayan ta cinye 40 mins dinta itama ta koma ta zauna anata aikin yi mata tafi wanda hakan ke kara ta’azzara yanayin da Bobby ke ciki...daya daga cikin malamansu ne ya amshi mike yayi ‘yan jawabe jawabensa kafin a sake mika musu box kowa ya sake daukan paper daya this time around 20 mins zasuyi instead of 40...kaman daxu Sa’eed ne ya fara yin nashi yana gamawa itama ta mike ta fara...zuwa yanxu abunda Bobby keji ya ninka wanda yakeji daxu kusan sau uku...har wani gumi ke tsatsafo mishi sbd azaba don zazza6i sosai ya rufeshi kaman wanda yayi kwana da kwanaki yanayi...bai sake gigin bude idonshi ba har ta gama snn yaji hall din ya kaure da tafi...kafin ayi announcing wanda yayi winning a cikinsu wani babban mutumi daya saba halartan taron duk shekara yace a fadawa Lamido ya bata kyautan sabon MacBook hade da 50k a matsayin tukuici na burgeshi da tayi...aikuwa ana fada hall din ya sake kaurewa da ihu da tafi...masu jin dadi nayi masu rashin jin dadi ma duk sunayi...Bobby da yaji abunda mutumin ga fada kaman saukan aradu baisan time daya bude idonshi ba...daidai lokcin kuma Sa’eed ya dan kai bakinshi kusada kunnenta yace"congratulations besty..seems baby ya samu new rival"...da juyawa tayi tana kallonshi ta dan saki murmushi kafin itama ta matsar da nata bakin dab da kunnenshi tace"ai mai iya takara da baby saiya shirya besty..i am his and his alone"...ta karasa mgn tana blushing as ta tuna da habibie noorul qalbinta...wani azababben tari Bobby yaji ya sarkeshi babu gaira babu dalili...numfashinshi har yi yake kaman zai dauke sbd azaba...ya rasa da wanne ma zaiji...da wancan tsohon banzan daya bata kyauta ko kuma da wancan karamin kwaron dake mata rada a kunne itama tanayi mishi...kuma don iskanchi hadda yi mashi murmushi kaman qanin ubanta...ita kuwa bata ma san yanayi ba wai kunu a wani gida...bayan hayaniya ya dan ragu Nur ya amsa mike yayi godia wa wnn mutumi snn ya fadi scores dinsu inda Lamid ta dara bestyn nata da maki biyu...tun kafin a gama fada midwives suka hau ihu suna tafi sbd sunyi winning...sake juyawa Aysha tayi tana kallon Sa’eed sake zaune gefenta tayi mishi gwalo...daria kawai ya saki yana daga shoulders dinshi...daga nan dai aka sallamesu suka fara fita yayinda wnn mutumi yace a tsayar masa da Aysha yanason mgn da ita...Bobby na zaune yana jinsu amma uffan baice ba as shima ta kanshi yakeyi yanxu...ba musu Nur yayi mata mgn ta tsaya shi kuma mutumin ya taso zuwa inda take yanata smilling yace"yammata sannu da qoqari"..dan murmushi ta saki batace komai ba..yace"saqonki yana nan zuwa gareki gobe inshaAllah..zan iya samun phone numberki?.."shiru tayi tana tunani kanta kasa sai kuma ta dago kan tana bude baki zatayi mgn idanunta suka fada cikin nashi da sukayi wani irin jaa yana kallonta dasu kaman zasu fadi kasa...sauke idonta tayi da sauri sbd jin wnn abun da bata qaunar ji duk suka hada ido dashi...turo bakinta tayi dan ko baa fada ba tasan har yanxun idanunshi na kanta...shi kuma mutumin jin batace komai ba sai ya zaro card dinshi ya bata yana cewa"make sure kin kirani dan Allah...I want to discuss something with u"...gyada mishi kai tayi tana murmushi tace"zan kira inshaAllah"...daga haka ya juya yana murmushi ya koma inda yake...itama juyawa tayi zata fita Bobby ya tashi da sauri kaman ana tunkudashi yabi bayanta a kan idon Nur dake monitoring dinshi tun daxu...sbd saurin da yakeyi kafin ta fita hall din ya cimmata sai ya danyi slowing down ba tareda ya kalli gefenda take ba yace"meet me now"...daga haka ya sake daga kafa yayi wucewarshi...ita kuma ta bishi da harara kaman idon zasu koma jikinshi...cikin immitating dinshi tace"wai meet me now..sai kace durkusawa yayi ya haifeni masifaffen banza inyamuri kawai"...kai tsaye office dinshi ta wuce daga nan tana rikeda wayarta a hannu...tana shiga Bobby daketa sintiri cikin office din ya juyo yana kallonta voice dinshi na fita da kyar sbd zazza6i da 6acin ran da yakeji yace mata"are u satisfied?..kinje kinyi presentation kuma kin samu abunda kikeso hope u are now satisfied?.."dan turo baki tayi tana kauda kanta tace"aini ba sbd kowa nayi ba sbd department dina ne"...tun kafin ta rufe baki a fusace yace"if u dare say another word saina kwada maki mari a wurin..am i ur mate?.."shiru ta sakeyi tana cigaba da turo bakinta..ita fa kome zaiyi yanxu bazai daga mata hankali ba tunda ta riga tayi abunda takeso kuma sunyi winning...shi kuma ganin yanda taketa faman hade rai tana turo baki cikeda wani haushin yace"dama it’s what you’ve always wanted to get Men’s attention and now sai ki zuba ruwa kasa kisha tunda kin samu abunda kikeso...you think duk biye biyen maza da kikeyi banida labari kou?..well i am aware of every single thing da kikeyi kawai zuba maki ido nayi inga iya gudun ruwanki kuma na gani...sbd haka bear it at the back of your mind today babu abunda zai hanani sanar da Dad dinki duk iskancin da kikeyi?..so get ready for it"...ya karasa mgn har yanxu yana huci kaman angry lion...Aysha kuwa tunda ya ambaci kalmar biye biyen maza taji gaba daya ranta ya 6aci...wato ma kallon da yake mata knn?..idan akace biye biyen maza fa ana nufin karuwanci knn?..so this is what he thinks of her shiyasa komai sai yace zai hadata da daddy?..lokaci daya wasu hawaye suka ciko idonta dan sosai taji ciwon mgnr daya fada...ta dago idanun ta zuba masa su cikin nashi hakan kuma ya bawa tawagar hawaye da suka cika idanun nata damar saukowa fuskanta...bata damu da goge su ba tana kallon tsakar idanunshi yau ko wnn tsoron da idanun ke bata bataji ba sbd tsabar 6acin rai...shima kallon nata cikin idon yake yanaso ta gane 6acin ran data haddasa masa sbd abunda tayi..shine shi data cuta baiyi kuka ba sai ita da baiyi wa laifin komai ba?...cikin tsananin 6acin rai da bai ta6a ganinta ciki ba tace"so this is what u think of me?..karuwa mai biye biyen maza right?.."kallonda take mishi ne yaji ya kasa jurewa abunda bai ta6a faruwa dashi ba all his life kawai sai ya dauke kan daga gareta yana sake jin sabon kunchi na rufeshi zuciyarshi kaman zaiyi bindiga sbd kumburan da yake...juyawa kawai tayi zata fita daga office din a fusace yace mata"come back here?.."ai ko sauraronshi batayi ba ta bude kofa ta fita da gudu bayan ta bugo mishi kofan da mugun karfi har saida ya runste ido sbd karan da yayi...zuciyarshi na sake tafarfasa ya dunkule hannunshi ya kaiwa table dinshi duka yana fadin"damn it"...wani jiri yaji ya fara daukanshi dan haka ya karasa kam sofa ya zauna da sauri yana dafe head dinshi da yaji ke barazanar rabewa gida biyu...bude kofa akayi secretary dinshi ta shigo tana cewa"Sir pro..."bai bari ta karasa ba ya daga mata hannu har yanxun yana dafe da head dinshi yace mata"get out"...sake bude baki tayi zatayi mgn a fusace yace"i said get the hell out of my office..are u maddd?.."juyawa tayi da sauri ta fita daga office din jikinta har ya dauki rawa sbd tsawar da yayi mata...after like 5 mins Nur ya shigo office yana fadin"wai Bobby what’s wrong with u ne these days?..what is the matter with you?.."a fusace shima ya dago yana kallonshi da eyes dinshi da suka koma kaman garwashi sbd ja ya nuna mishi kofa yace"malam get the hell out of my office..leave me alone"...daure fuska shima Nur yayi yace"ni kake kora office dinka Bobby?.."a fusace ya sake dagowa yace"to hell with u an koreka din me zakayi?..kaga malam leave my office before I loose my temper with you"..ya karasa mgn yanaji kaman ya kwada masa mari..kawai haushinshi yakeji that har ya wani dakatar da ita sbd tayi mgn da wani qaton sbd shi baisan ciwon kanshi ba...Nur da ranshi ya gama 6aci shima yace"well tunda haka kace am not going anywhere until u loose it with me..fight with me if that’s what u want"...dafe goshi Bobby yayi yana dan murzashi abhankali feeling extra hot inside...kawai bayason ya biyema haushin da yakeji yanxu dan ba karamin tashin hankali zasuyi ba idan ya biyema hakan...mikewa yayi a fusace zai bar mashi office din Nur ya wani irin jawoshi ya dawo dashi baya yana cewa"where are u going"...fizge hannunshi Bobby yayi yana nunashi da finger dinshi yace"Fuck you"...daga haka ya juya ba fita daga office a mugun fusace...kai tsaye inda driver yayi parking motarshi ya nufa saidai bai ha driver din ba..sake dafe kanshi yayi ya jingina jikin motan yana sauke numfashi a jere sbd tashin hankali...can ya hango drivern ya taho dan haka yana zuwa bai bari ya fara masa dogon jawabi ba yace"open the damn car"...da sauri yasa key ya bude motar Bobby ya bude back seat ya shiga shi kuma driver ya rufe mashi kofa snn shima ya shiga side dinshi ya tasheta suka tafi...saida suka hau kan titi yace"Sir where are we going to.."a takaice yace dashi"home"...driver bai sake mgn ba ya kama hanyan airport road...suna isa gida ya bude mota ya fita still yana dafe da kanshi ko wayoyinshi daya ajiye nan kusa dashi bai dauka ba...Mr Obi ya kwashi wayoyin da suit dinshi yabi bayanshi dasu...yana shiga kai tsaye ya kama hanyan part dinshi bai ko lura da Mummy dake zaune parlor ba...ganin yanda yake tafiya yana hada hanya kuka ga head dinshi dake rike har yanxun Mummy ta kira sunanshi"Bobby"...juyawa yayi yana kallonta still yana rike da head dinshi yace"Mummy"...nuna masa kusa da ita tayi tace"zo nan"..ba musu ya juya zuwa cikin parlon...ya zauna nan inda ta nuna mashi snn ya sauke hannunshi daga kanshi yana kokarin daidaita kanshi wai kar su fahimci yana cikin wani hali...Mummy da duk kokarinshi saida ta fahimci halinda yake ciki da igbo tace"what is wrong with u?.."kakalo murmushi yayi kafin yayi mgn tace"karka fara cemin you are fine nasan you are not..why kake rikeda head dinka haka?.."lumshe idonshi yayi tareda dora head dinshi kan shoulder dinta yana sauke numfashi...hannu takai tana shafa head din nashi tace"fadamin meya sameka Bobby?.."dago kan nashi yayi a hankali yana kallonta kawai sai yaji hawaye sun ciko mashi ido...baidai bari sun zubo ba amma idanun sai shinning sukeyi sbd hawayen dake cikinsu..ganinshi a gabanta sai yaji damuwan na sake mishi yawa zuciyarshi yayi wani irin rauni da sam baiyi irinshi ba daxu...hankalin Mummy ya tashi da ganin kwalla a idanunshi a rikice ta sake bude baki zatayi mgn ya kuma maida kanshi shoulder dinta murya can kasa yace" i just want to be alone Mummy..please!"batayi yunkurin hanashi ba ta dago kan nashi tana gyada kai tace"it’s ohk u can go..we’ll talk later"...bai sake cewa komai ba ya mike yana sake dafe head dinshi ya wuce flat dinshi yana takawa da kyar sbd nauyi da legs dinshi sukayi mashi...da kyar ya iya kai kanshi parlor ya fada kan three seater yana sauke numfashi...har yanxu wani irin ciwo heart dinshi yake mishi..wani irin zafi yakeji a cikinta kaman ana hura huta a ciki...shidai yasan da kyar idan Lamido batayi ajalinshi ba...baisan meyasa Allah zaiyi masa irin wnn jarrabawa a kanta ba...shi har yanxu ko kusa zuciyarshi bai ta6a bashi cewa there is a reason behind abunda yakeji ba kawai gani yake sbd amanarta da daddy ya bashi ne...da kyar ya iya mikewa ya kai kanshi ciki tareda fadawa bathroom ya sakar ma kanshi ruwa batareda ko kayan jikinshi ya cire ba...saida ya gama jikewa tsaf snn ya rage kayan yayi wanka ya fito daure da towel a waist dinshi...jallabiya kadai ya iya zurawa a jikinshi ya maida towel din bathroom snn ya dawo ya kwanta kan sofa yana sake jin yanda ciwon kanshi ke karuwa...baifi minti shidda da kwanciya ba bacci yayi gaba dashi...dama shi haka yake indai 6acin rai yakai 6acin rai kanshi zaiyita ciwo sai ya samu yayi baccin nan yake samun saukin ciwon.
Lamido na fita daga office din nashi kai tsaye inda classes dinsu yake ta nufa tanata faman kuka kaman wanda akama duka dan bazata iya komawa can wajen ba...a hanya suka hadu da Sa’eed da Billy da suka fito nemanta...tana hada ido dasu ta sake rushewa da kuka...yana mata ciwo that ya kirata da mai biye biyen maza a takaice dai yana nufin ita karuwa ce...tunda take ba’a taba fada mata mgn daya tsaya mata a rai kamn wnn ba...wato dama duk kallon da yake mata knn amma ya cuceta...tambayan dunia sunyi mata amma taki tsaida kukan ballantana ta fadi abunda ke damunta...saida kyar aka samu ta dakatar da kukan tareda yi musu bayanin abunda ya faru...gaba daya sukayi shiru Billy ta juya ta kalli Sa’eed shima ya kalleta suna hada ido kowa ya shiga kunshe daria...dagowa tayi tana kallon Bily ganin yanda daria ke neman kufce mata ta sake juyawa ga Sa’eed shima taga the same thing kawai saita kifa face dinta akan hannayenta ta sske rushewa da kuka...mikewa Sa’eed yayi da sauri ya karasa inda take yace"besty nidai ba ruwana wlh..Billy ce naga tana daria"...tun kafin ya rufe baki itama Billy ta matso inda suke tace"nima ba ruwana wlh..aishi kika ga yana daria"...dagowa tayi tana goge hawayenta bata cewa kowa komai ba kawai ta mike a fusace ta fice daga wurin sukabi bayanta da sauri ita kuma da taga haka kawai ta kwasa a guje ta haura sama...har kusan durkushewa suka kusa yi sbd daria...yanda ta fita a gujen ne ya basu daria sosai ba kadan ba...saida sukayi mai isarsu snn suka haura saman suma...kai class dinsu suka shiga basu sameta a ciki ba...ita kuwa dama tana haurawa can kusada class din karshe taje ta tsaya tana cigaba da hawaye...tana ganin shigarsu class dinsu tabi ta dayan staircase dake nan kusada inda take ta sauka qasa...kai tsaye gate ta nuf ta fita daga makarantan daga ita sai uniform dinta a jiki da wayanta a hannu...tana fita tayi dialing number baby...yana kan hanya shida driver dinshi yaga kiranta...yana dauka kafin yace wani abu yaji sheshshekar kukanta..muryanta na fita da kyar tace"Babyyy..."hankalinshi ne ya sake tashi sosai yace"baby meya faru?..why are u crying?.."da kyar ta sake cewa"baby kazo makarantan mu..ina bakin gate"...tun kafin ta rufe baki yace"gani nan zuwa yanxun nan..just stop crying okay?.."daga mishi kai kawai tayi tana kashe wayan...ganin zasu iya hangota daga nan inda take tsaye sai ta dan matsa gaba kadan ta samu inda ta tabbatar bazasu iya ganota daga cikin school din ba ta zauna...after like 20 mins Prof ya karaso makarantan...tun kafin ya kirata ya hangota nan inda take dan haka yace ma driver dinshi yayi parking mota shi kuma ya bude ya fita ya tsallaka titi zuwa inda take...tana ganinshi ta mike tana sakin wani kukan kaman wanda uwa da ubanta suka mutu...hankalinshi ya sake tashi sosai yana isa kusada ita yayi kasa da voice dinshi yace"baby girl a bar kukan haka mana indai baso kike ki karasar min da dan ragowar nutsuwata ba"...hannu takai ta share hawayen nan yaga idanunta sunyi suntum face dinta yayi jajir sbd kuka...da kyar ya samu ta dakatar da kukan suka tsallaka titi zuwa inda motarshi yake...da kanshi ya bude mata back seat ta shiga shima ya shiga driver already dama yana ciki dan haka ya tada motar suka wuce...bayan sun dau hanya ya tambayi inda zai kaisu Prof yace"ka kaimu valentino"...ba musu ya kama hanyan Valentino dasu...har suka isa baice mata komai ba banda kallonta da yakeyi yanajin kukanda ta kasa dakatarwa ba ta6a masa zuciya...suna isa ya bude mota ya fita itama ya bude mata ta fito...ya debo kudi masu yawa daga pocket dinshi ya bama driver yace"ga wnn ka samu ka koma gida malam Lukman idan mun tashi tafia zan tuka da kain"..ba musu malam Lukman ya amsa kudi tareda godia snn ya juya ya tafi...shi kuma ya nuna mata hanya alaman ta wuce ba gardama itama tayi gaba yabi bayanta...Vip section yayi musu reserving ba tareda yayi ordern komai ba don duk hankalinshi tashe yake sbd kukan nan da yaga tanayi...bayan sun zauna yayi facing dinta cikeda damuwa yace"baby idan baso kike ki fasamin zuciya ba ki bar kukan"...ba musu tayi kokarin tsayar dashi tacigaba da goge hawayenta...ya zaro handky daga aljihunshi ya shiga goge mata tears din dashi...batace komai ba sai lumshe ido da tayi har ya gama snn yace"now tell me abunda ya faru"...bata 6oye komai ba ta fada masa duk abunda ya faru tun daga ranan da yace bazatayi participating ba har zuwa daxu da maganganun daya fada mata...tunda ta fara mgn Prof yayi shiru yana kallonta har takai aya bai iya cewa komai ba...kallonta kawai yakeyi while gaba daya hankali da tunaninshi suna wani wajen...tsoro yakeji kada ace proprietor din nasu sonta yakeyi don a wnn labarin data bashi yasan definitely akwai lauje cikin nadi..bai yiwuwa ya dinga kishinta kawai sbd mahaifinta ya bashi amanarta...hankalinshi yaji ya tashi sosai sbd baison wani yazo ya kwaceta daga gareshi...ganin yanda yayi zurfi cikin tunani Aysha ta kira sunanshi..ya dago yana dubanta tareda sauke ajiyar zuciya still ya rasa abun cewa...turo baki tayi kaman zataci gaba da kuka tace"yanxu baby bazaka ce komai ba?.."wani ajiyan zuciyan ya kara saukewa kafin a hankali yace"inso inyi mgn da daddynki plss..when zaki hadani dashi?.."shiru tayi tana kallnshi cikeda mamaki tace"is that all u could say?.."kamo hannunta yayi for the very first time a rayuwarshi yace"baby duk wnn abun da kikaga yanayi its all out of love..kishinki yakeyi sbd yana sonki ni kuma banaso wani ya kwaceki daga gareni shiyasa nakeso ki bani dama inje Gombe muyi mgn da daddy"...kallonshi kawai takeyi full of suprise..like how on earth ma zai fara wnn tunanin..how could all that masifa da bala’in da yake mata turned out tobe love...how could this happened?..ina wnn zance akwai gayara cikinshi..sam bazai ta6a yiwuwa ba hakan bazai ta6a faruwa ba...ganin yanda tashin hankali da tsoron rasata ke tubuce kan face dinshi sai tayi kasa da murya tana binshi da kallon daya kusan zautar dashi tace"baby calm down plss...calm down wnn abunda ka fada sam ba haka bane...there is no way da za’ace wnn mutumin yana sona..bazai ma ta6a faruwa bane so relax..babu wanda zai kwaceni daga gareka am only yours"...girgiza kai ya shigayi still hankalinshi ba kwance ba yace"baby you won’t understand..na tabbata ko rantsuwa nayi yaron nan sonki yake bazanyi kaffara ba..idan ba haka ba why zaisa maki ido haka?..why zai hanaki participating kan abunda yasan ba laifi bane"...dafe goshi Aysha tayi tanajin yanda duk ya fadi kalmar son nan takejin wani irin radadi a zuciyarta..ita tanada yakinin ba sonta yakeba kawai yanayi ne sbd daddy ne ya bashi daman hakan amma ita tasan babu wani abu makamancin love a tsakaninsu...ganin yanda tayi shiru ta dafe kanta yace"so yanxun ma bazaki barni inje wurinshi ba kou?..baby anya kuwa kina sona?.."da mamaki ta dago tana kallonta ta wani kwabe fuska kaman zatasa kuka tace"haba baby how could you say this.."tana rufe baki yace"to baby idan bance haka ba me kikeso ince?..idan da gaske kina sona why kike gudun haduwana da mahaifinki?..why bakison inje sbd mgnr auren..."tun kafin ya karasa ta rufe mashi bakin da hannunta tana kallon tsakiyar idonshi da nata idon da har yanxu bai dawo normal ba tace"dan Allah baby stop saying this?..how could you say bana sonka?..wlh ina sonka..i love u sosai"...ta karasa mgnr hawaye na ske ciko idanunta...zuwa tayi gareshi sbd tasan zai share mata hawaye kuma yasa ta manta da damuwan da take ciki amma shima sai gashi yana neman kara mata akan wanda take ciki...hankalinshi ya sake tashi ganin zata fara mishi kuka yace"Noo..karki bari su zubo dan Allah"...ai kamar cewa yayi ma su zubo nan suka shiga sintiri kan fuskanta...sake matsawa yayi jikinta sosai ya lumshe ido kawai sai ya janyota jikinshi yana sauke numfashi...soyayyarta yakeji na sake ratsa ko ina na jikinshi...yana sonta fiyeda tunani amma gashi kiri kiri yana nema ya rasata sbd tsoron ta hadashi da mahaifinta...kuka takeyi sosai a jikinshi tayi wani luff kaman jariria..baiyi yunkurin hanata kukan ba sai shafa bayanta da yakeyi a hankali...saida suka dauki lokaci mai tsaho a haka kafin ya samu ta tsayar da kukan snn ya dagota daga jikinshi ya shiga goge mata hawaye...idanunta lumshe har ya gama snn ya sake yin kasa da murya yana kallon bakinta da take pouting yace"Aysha please!..ki bani dama inje in ganshi kada wani yazo daga baya ya shiga tsakanina dake"...sake kwa6e fuska tayi zatasa wani kukan da sauri yace"dan Allah Noo..why kikeson tayar min da hankali ne.."baki a tunzure tace"ni ka dena mgnr za’a kwaceni daga gareka banaso..mgnr zuwa wurin daddy kuma ka bani lkci in fara mgn da Hammana duk yanda mukayi dashi zakaji"...kallonta yake kafin yace"U sure?.."ta wani langabe kai tana kallonshi tace"yes sure"...murmushi ya saki mai kyau tareda fadi"na yadda dake my baby..yanxu me kikeso a kawo maki kici.."murguda baki tayi tana makale shoulder dinta tace"ooh bazanci komai ba tunda har yanxun baka yadda ina sonka ba"..another smile ya kara saki kafin yace"sam ba haka bane baby kawai dai inajin tsoro ne..kinsan duk lokacinda kake son mace mai kyau hankalinka bazai ta6a kwanciya ba idan ba daura maku aure akayi ba"...dan murmushi itama ta saki murya can kasa tace"to ka kwantar da hankalinka in Allah ya yadda Aysha Ahmad Lamido batada mijinda ya wuce Professor Ahmad Kurawa"...sake fadada smile dake fuskanshi yayi yace"to Allah ya nuna mana ranan da Aysha Ahmad Lamido zata zama property din Prof Ahmad Abdu Kurawa"...murmushi itama ta saki shima yanayi kaman ba sune ke 6acin rai a while ago ba...nima kaina da nake dauko maku rahoto bansan lokacin da na furta"soyayya ruwan zuma"..akace idan kasha kaba masoyi...i hope dai gaba dayanku kunya ba masoyanku?🤪...lol
A can makaranta kuwa Billy da Sa’eed hankali tashe suke nemanta sun kuma rasa inda ta shiga...duk inda suke tunanin zasu ganta sun duba basu ganta ba...wasa wasa har yamma yayi likis basu dena nemanta ba kuma basu ganta...hankalinshi idan yakai dubu duk a tashe suke gashi mutane har sun fara raguwa cikin makarantan ba Lamido babu dalilinta...Billy kaman zata sa kuka take dubanshi tace"nidai wlh ba ruwana kaine ka farayi mata daria bani ba..kan wane dalili ma zaka fara mata daria bayan kasan bataso?.."da mamaki sosai yake kallonta yace"Seriously?..gaba daya laifin zaki dora a kaina sbd ga sarkin laifi koh?.."cikin tsiwa tace"laifinka ne mana tunda ka fara mata daria..yanxu idan bamu ganta ba ya zanyi ni Bilkisu?..dan Allah ina kake tunanin zataje?.."shiru Sa’eed yayi yana tunanin inda zata iya zuwa can yace"bakida number babyn nan nata?.."girgiza kai Billy tayi tace"bani dashi"..shiru ya sakeyi yana tunani Billy tace"ko Proprietor din zamu kira ko yasan inda take?.."girgiza kai yakeyi yace"i don’t think zaisan inda take gaskia..besides ke kanki kinsan besty ba fada mai zatayi ba"...cikin hankalin dake karuwa Billy tace"nasan bazata fada mashi ba amma at least zai iya taimakawa wajen gano inda take..dole muna buqatan taimakon wani babba and sanin kanka ne bazan iya kiran gida in fada ba amma shi idan na fada mishi na tabbata zaiyi wani abu akai tunda daddy ya bashi amanarta kuma shine yayi sanadin komai dake faruwa"...gyada kai yakeyi cikeda gamsuwa yace"yea kinada point..amma a ina zamu number dinshi?.."tace"bamu dashi amma sai mu tambayi provost ya bamu"...zaro waya Sa’eed yayi daga pocket dinshi yace"let me call Dr Aslam nasan bazai rasa numbershi ba"..daga haka yayi dialing number da yayi saving as Dr Aslam a wayarshi...yana fara ringing doc Aslam ya daga nan Sa’eed yace mishi number Dr Bobby yake nema babu 6ata lokaci kuwa ya turo mashi...message din na shigowa ya dubi Billy da har yanxu hankali ke tashe yace"yauwa gashi ya turo..dauko wayanki ki kirashi"...ba musu Billy ta dauko wayanta ta kwashi numbers din da aka turo snn tayi dialing...har ya gama ringing bai dauka ba sai ta sake kira...a takaice saida ta jera missed calls kusan 7 bai dauka ba hakan kuma ya sake tada hankalin hajia Bilkisu...bata hakura ba haka tayita jera masa kira har saida taji ya daga...tana jin ya dauka tayi saurin cewa"Sir sunana Bilkisu Muqaddas nice muke tareda Aysha Lamido..sir wlh tun daxun muke nemanta school din nan bamu ganta ba gashi har dare ya fara shine nace we should call ko akwai taimakon da zaka iyayi mana"...tunda ta fara mgn Bobby da har yanxun yake kwance baice mata qala ba..sauraronta kawai yakeyi yanajin yanda maganganunta ke shiga direct to his heart suna sake lalata mishi ita...ciwon kan daya fara mishi sauki nan take ya sake dawowa...da kyar ya iya bude bakinshi yace"where are u now?.."da sauri tace"school.."yace"will be coming right away"...da sauri tace"mun gode sir..Allah ya saka da alkhairi"..shidai bai sake cewa komai ha ya kashe wayarshi.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 220891344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
26
Mikewa ya samu yayi daga kwancen da kyar yanajin yanda ciwon kan daya samu ya fara raguwa na sake dawowa sabo...shikam baisan dalilinda yasa Allah ya hadashi da Lamido ba amma for sure ya fara tunanin ba alkhairi bane haduwan nashi da ita..gaba daya nema take ta zame mishi tauraruwa mai wutsiya da tunda ta shigo rayuwarshi take kokarin canxa mishi ita...yana mikewa wani jiri ya sake daukanshi don saura kiris ya fadi a kasa yayi saurin dafa wall da yake tsaye kusa dashi...da kyar ya karasa first aid box dinshi ya dauki maganinda yasan zaiyi saurin saukar mashi da headache da dizziness din yayi dispensing ruwa yasha snn ya koma kan sofa ya sake kwantawa for like 10 mins kafin ya dan ji dizziness din ya ragu dan haka ya mike ya dauki car keys dinshi ya fita...Mummy da har yanxun ke zaune parlor tana ganinshi ya fito da keys a hannu ga kuma yanda yake tafiya shows har yanxu akwai sauran matsala tattare dashi tace"ina zakaje kuma?.."kallon inda take yayi kafin yace"Hospital zanje Mummy...ba dadewa zanyi ba"...cikeda concern tace"amma bazaka iya driving a haka ba Bobby..kaga yanda kake tafia kuwa?.."dan murmushi ya saki ba karfin hali yace"Mummy don’t worry ba abunda zai faru..ya zama dole ne fitan shiyasa zanje"..bata sake cewa komai ba sai kai kawai data gyada mishi...shi kuma ya juya ya bar parlon walking slowly sbd kar taga yanda jirin da yakeji ke neman affecting tafiyan nashi...yana fita ya fada mota yayi mata key ya fita daga gidan...a hankali yake tafia sbd gudun problem don yasan idan yace zaiyi gudu a halinda yake ciki tsaf za’a iya samun matsala...cikin 35 mins ya iso makarantan bai shiga ciki ba yayi parking nan bakin gate snn ya kira number da Billy ta kirashi dashi daxu...tana dauka yace"am at the gate"..snn ya kashe wayan...Billy ta mike da sauri tana duban Sa’eed tace"kaji proprietor har yazo..yana bakin gate"...Sa’eed baice komai ba ya mike suka fita bakin gate din...suna tsallako titi suka nufi inda suka hangi motarshi...kanshi na hade da starring motan ko noticing dinsu baiyi ba saida Billy tayi mgn...da kyar ya iya dago kan nashi yana kallonta da eyes dinshi da sukayi jaa sbd headache da kuma damuwa yace mata"so kince kun duba ko ina baku ganta ba?.."da sauri tace"eh wlh tun dazu muke nemanta bamu ganta ba"...da kyar ya sake fadin"kuma baku tunanin she might have gone to someone a nan cikin gari like a friend or family?.."gaba daya shiru sukayi can Sa’eed yace"ina tunanin zata iya zuwa wurin baby"...juyawa Bobby yayi yana kallonshi da kyau yace"who was that?.."kai tsaye Sa’eed yace"saurayinta ne..sunanshi Professor Ahmad"...kallonshi kawai Bobby keyi yana kankance idanu tsabar bala’i...yanxu rashin hankalinta har yakai ta dauki kafa takai kanta wajen saurayi?..innalillahi wainna ilaihi rajiun?..wnn wace irin yarinyace?..lokaci daya ciwon kan daya samu saukinshi ya sake dawo mishi kaman zai rabe biyu...shima dizziness din kaman jira yake a fadi wnn mgnr sai ya ninku akan wanda yakeji a baya...6acin ranshi ya fito karara wanda hakan ya basu mamaki sosai...maida kallonshi yayi ga Billy dake gefe murya a cushe yace"have u tried calling her?.."da sauri Billy tace"tun daxu naketa kira bata picking".."ki sake kira"...ya fada mata feeling extra hot inside...ba musu Billy ta dauko waya ta sake dialing numberta..tana kokarin kaiwa kunne yace"put on speaker"..still batayi mashi musu ba tayi putting a speaker din nan sukaji kiran ya fara shiga amma har ya katse bata dauka ba...ta sake kira still no answer sai a karo na kusan takwas Prof da yaga anata jera mata kira tun daxu yace"yanxu baby bazaki picking calls dinki ba?.."turo baki tayi tace"nidai bazan dauka ba nasan Billy ne ko besty ke kira kuma fushi nakeyi dasu ni"..girgiza kai kawai Prof yayi tareda kai hannunshi ya dauki wayan..daidai lokacin wani kiran ya sake shigowa dan haka ya dauka ganin Billy ce ke kira...a daya 6angaren sunajin an daga Billy tayi saurin cewa"Lamido ina kika tafi kika barmu cikin tunani haka?..and why aren’t u picking my calls?.."dan murmushi ya saki jin yanda take mgn da damuwa yace"Bilkisu relax kinji koh?..tana tare dani yanxu haka"...wani irin darammm Bobby yaji kaman saukan aradu a cikin ziciyarshi..knn da gaske wurin saurayin nata ta tafi?..Billy da taji abunda ya fada ta sauke ajiyar zuciya kafin tace"shiknn Prof nagode..tell her idan ta bari raina ya 6aci saina hadata da Ammi ko daddy wlh"...Prof yace"No inshaAllah bazai kai ga haka ba...yanxu xan dawo muku da ita"..gyada kai kawai Billy tayi ta kashe wayarta Sa’eed kuma na daga gefe baice komai ba...juyawa sukayi ga Bobby daya jingina kanshi da kujera ya dora right hand dinshi kan chest dinshi daidai saitin heart dinshi da yaji kaman zai faso kirjin ya fito sbd irin bugawan da yakeyi...wani irin zafi yakeji that har zata kwashi jiki taje inda saurayinta..abun yanayi mishi ciwo sosai fiyeda tunanin mai karatu...har yanxun eyes dinshi are closed don ji yakeyi kaman duniyan na zagayawa dashi...kanshi kuma na wani irin sarawa kama ana doka guduma akai...duk wani abu da yake tunanin yanaji daxun wnn da yakeyi yanxu is far more than wancan...ashe daxu somin ta6i ne kawai akayi mashi dan bai farajin komai ba sai yanxu..yanxu ne yakejin real ciwon kai da zuciya suna neman su hallakashi...daga Billy har Sa’eed tsayawa kawai sukayi suna binshi da kallo..yanda yake jujjuya kanshi from side to side da kuma hand dinshi dake dafe da his heart shows ba karamin ciwo yakeji ba...kamar yasan tunaninda sukeyi ya samu ya dago kanshi da kyar ya bude idanunshi a kansu wanda ba shiri gaba daya sukayi kasa da nasu don idon babu kyawun gani sam..idanunshin that ko lafia lau ma suke firgita mutum inaga kuma sun sauya launi haka?..bai damu da dauke idon nasu ba ya maida glasses dinshi sama tareda kwantar da kanshi jikin starring su kuma ganin haka sai suka tsallaka titi suka koma makaranta abunsu...saida ya dauki lokaci mai tsaho yana fama da kanshi kafin ya dago yana kokarin kunna motan...kawai haushin kanshi yakeji na fitowa da yayi ma at the first place..yasan da baizo ba ba yanda za’ayi yaji labarin tana wurin saurayinta ma balle ya karama kanshi bala’i cikin masifan da yake ciki...tada motan yayi ya haura kan titi yana tafiya slowly sbd yanda yakejin jikinshi...tafiyan minti uku kadai yayi yaji motan na barazanar kwacewa daga hannunshi sbd dizziness da har yanxun bai sakeshi ba..dole haka ya gangara gefen titi yayi parking tareda kashe motan ya sake kwantar da kanshi da starring...tunanin wanda ya kamata ya kira yake tunda dai yasan ko yasha giyan wake bazai fara daukan hanya yana a wnn halin ba..shidai wnn yarinya Lamido take ko Gidado ta cuceshi wlh..sam ya rasa abunda tayi mashi da yakejin irin wnn abun a kanta...sunyi fada da Nur daxu so bazai ma fara kiranshi ba..driver dinshi kuma yasan yanxu yana gida tareda iyalinshi shi kuma sam bai son ya katse mishi jin dadi ga Sab yana school da sai ya kirashi..Mummy kuma koda wasa bazai fara kiranta ba sbd yasan tambayoyi ne zai shasu kaman yana court...daga karshe dai daukan wayanshi yayi ya kira aunty sumy ya fada mata inda yake yace tazo ta daukeshi that he can’t drive...hankali tashe kuwa ta fita daga gida ta dauki drop din napep har zuwa inda yake...tana sauka ta biya mai napep kudinshi snn ta nufi inda ta gano motan nashi..saida tayi knocking sau uku snn ya samu ya bude mata...tana shigowa ciki ta shiga binshi da kallo ganin yanda lokaci daya kamanninshi suka sauya cikin igbo tace"Bobby lafia kuwa?..meya sameka haka?.."da igbo din shima ya amsa mata da"it’s nothing serious..just headache"...girgiza kai ta shigayi tace"ban yadda da abunda ka fada ba gaskia..you seems disturbed..kodai you are hiding something?.."girgiza kai ya shigayi shima cikin karfin hali duk a kokarinshi na kar ta dauki abun da zafi yace"aunty sumayya i am fine believe me..headache ne kawai ke damuna and am sure it’s stress..da zaran na samu bacci zai dena"...kallonshi kawai aunty sumy keyi kaman bata yadda da abunda ya fada ba...shi kuma bude motan yayi ya fita daga driver seat ya zagaya inda take zaune itama ta fito ta nufi driver seat shi kuma ya bude nan inda ta fito ya shiga ya jingina kanshi da kujera yana lumshe ido..bayason jin another tambaya da zai fito daga bakinta dan baisan amsan da zai bata ba...right now ba abunda yake bukata kaman yajishi alone..so yake ya ke6e shi kadai koya samu yayi jinyar zuciya da gangar jikinshi da kyau dan ji yake kaman sun dena aiki na wucin gadi...shi kadai yasan what is taking place in his heart sai kuma Allah daya halicci zuciya ya kuma baiwa kanshi kadai daman ganin abunda ke cikin kowacce zuciya...itama lura da hakan da tayi yasa ta tayar da motar kawai ta harba kan titi...har suka isa gida ba wanda ya sake mgn cikinsu..bayan tayi parking kafin ta bude ta fita yace mata"aunty karfa ki gayawa Mummy wani abu please..kinsan yanda take yanxun kina ce mata kinzo kin daukeni duk tashin hankalinta zatayi"..girgiza kanta tayi tace"bazan fada mata ba amma da gaske ban yadda da abunda ka fada ba Bobby..sam ban yadda onlh headache ke damunka ba..kaga yanda ka koma kuwa?.."dafe head dinshi yayi yanajin yanda ciwon kan ke neman karuwa sbd wnn maganganun da yake..kwata kwata ko bude bakinshi bai sonyi sbd azaba..shi kadai yasan halinda yake ciki...aunty sumy ta bude mota ta fita shima ya fito suka nufi entrance din gidan...Mummy na zaune parlor itada su Miemie da Ilham su suna kallo ita kuma hankalinta gaba daya na wani wajen data kurama id tana tunani...tanajin sallamarsu ta dago tana kallonsu Bobby bai yadda ya hada ido da itaba ya wuce flat dinshi sbd bayada amsan tambayoyin da yasan matukar yaje inda take sai tayisu...idonta a kanshi har ya shige flat dinshi snn ta maida hankali kan aunty sumy dake karasowa parlon..tana zama ta dubi su Miemie da suka hada kai suna kallo tace"Miemie kuje parlona ku cigaba da kallon"...ba musu Miemie ta mike ta kama hannun ‘yar uwarta suka bar parlon...bayan sun fita Mummy ta dubi aunty sumy hankali tashe tace"ya fada maki abunda ke damunshi?.."girgiza kai kawai aunty sumy tayi tace"yaqi fada Mummy..wai headache ne kawai ke damunshi amma ni nasan karya yake there is more to it..Mummy ko zaki gwada tambayanshi ko zai fada maki?.."sauke ajiyar zuciya Mummy tayi tace"nima dazu dana tambayeshi bai fadamin komai ba amma i will try again zuwa safe ko zai fada"..cikeda gamsuwa aunty sumy tace"eh hakan ma yayi..and Allah sa ya fada"..Mummy tace"Ameen"..cikin raunin murya sosai..kwata kwata batason abunda zai ta6a mata yaranta ko kadan musamman shi daya kasance guardian dinsu..kuma bata ta6a ganinshi cikin yanayi irin wnn ba tun bayan rasuwan mahaifinsu..to menene wnn dayasa shi fita daga hayyacinshi haka?..me yake damun yaron nan ne?..(nidai nace da kyar idan ba love bane mummy).🤪
Washegari ganin har wajen 11 bai fito ba Mummy ta hada breakfast dinshi ta nufi flat din nashi...yana zaune kan gado ya jingina jikinshi da jikin gadon idanunshi a lumshe dagashi sai singlet da shorts a jikinshi...Mummy ta karasa ciki ta ajiye abincin data shigo dashi kan table snn ta karasa gefen gadon nashi ta zauna kuma har ta zauna din baisaniba sbd nisa da yayi cikin tunani...kallonshi Mummy ta tsaya yi for like 5 mins tanajin tsananin taysayinshi yana ratsata...dukda bata san ainihin abunda ke damunshi ba ta tabbata abune mai girma tunda har ya saka abun cikin ranshi haka...yanada sa abu a rai sosai shiyasa duk wani abu da zai zame mishi damuwa bata kaunar ya ra6eshi sam..hannu takai ta dora forehead dinshi tanaso taji ya temperature dinshi yake aikam taji shi zafi zau kaman ana hura huta...a hankali ya bude idonshi yana kallonta hankalin Mummy ya tashi sosai da ganin idanun nashi...tun yana yaro tasan idan har idanunshi suka sauya din nan to ciwon da yakeji yakai ciwo knn...nan take hawaye ya cika idonta tana kallonshi da kyau tace"Attahir..."da kyar ya iya bude idanunshi ya saukesu a kanta..tace"meyake damunka?.."idanunshi ne suka ciko da hawaye dan yana ganinta yaji wani irin rauni ya dirar mishi kawai sai ya matsa jikinta ya rungumeta yana runste ido...kwalo idanu Mummy tayi waje tanajin yanda ya matseta jikinshi kaman zai 6allata wnn ma is another reason da ya sake tabbatar mata da cewa yana cikin damuwa...hannu takai tana shafa kanshi a hankali tanajin yanda heart dinshi ke beating da karfi kaman zai fito waje...shiko Bobby bakin kokarinshi yake na ganin bai fito da hawayen daga idonshi ba sbd a ganinshi yin hakan ba karamin abun kunya bane a gareshi..wai duk fadin dunia ya rasa wanda zai zubda hawaye kanshi sai Lamido?..yarinyar da dama ya tsaneta from the beginning..jiya ko baccin kirki kasayi banda abubuwanda suka faru ba abunda yake tunawa..gaba daya komai yayi masa tsaye cak and abunda yafi bashi haushi knn sbd yana ganin kwata kwata bai cancanta yana jin wani abu makamancin haka a kanta ba..sam bai dace ba shiyasa shi kanshi yakejin haushin kanshi kuma dui kokarin na yaga yayi stopping abun kasawa yayi...saida suka dauki lokaci mai tsaho a haka kafin ya dago daga jikinta a hankali yana yin kasa da ido sbd kar ya hada idanu da ita..Mummy takai hannu ta dago idanun nashi tana dubanshi sosai tace"fadamin..what is the matter with u?.."hannunta ya kamo ya rike cikin nashi yana kallonta shima ya rasa abunda zai fada..kawai tunani yake me zaice mata yana damunshi dan dai da kunya yace mata kan yarinya karama yake wnn abun...shidai zuciyarshi batayi mashi adalci ba wlh...ganin kallon da ya zuba idanu yana mata ta sake kiran sunanshi...ya lumshe ido ya bude cikin ranshi yana addu’an Allah yasa ta bar zancen amma sam Mummy ta dage sai taji damuwanshi...ganin ba hakura zatayi ba ya tattaro duk wani karfin hali da dakiya irin nasu na maza kafin yace mata"dama..mummy..it’s about a girl"...tun bai rufe baki ba Mummy ta wara idanu tana kallonshi tace"u mean kana son wata yarinya?.."girgiza kai ya shigayi da sauri yana wani ta6e baki jin abunda ta fada yace"Mummy Noo..wata yarinya ce kawai mahaifinta ya bani amanarta shine ita kuma take kokarin tasamin ciwon zuciya"...kallonshi Mummy keyi full of suprise don har yanxu bata fahimci inda zancenshi ya dosa ba..shima ganin kallon da take mishi sai ya shiga bata labarin tun haduwar da sukayi da daddy a college zuwa yanda ya gane shi son din Col Attahir ne da irin maganganun daya fada kan mahaifin nashi har zuwa yanda yace ga amanarta ban ya bashi yanaso ya kula da ita sbd batajin mgn...Mummy tayi shiru tana sauraronshi har ya gama kallonshi kawai takeyi dan she smells something cikin maganr nan nashi...tasan wanene shi sarai dan haka tafi kowa fahimtan halinda yake ciki fiyeda kowa a dunia and cikin maganganun daya fada ta tabbata ko ba son yarinyar yakeyi ba tabbas yanada interest akanta har tunda yake kishinta haka?..ita kuwa inama zataga wnn yarinya ta samu tayi mgn da ita?..inama Allah zai kar6i addu’anta ya zarginda takeyi ya zama gaskia?..inama zat...bata kai ga karasawa ba taji hannunshi a jikinta yana dubanta yake fadin"Mummy tunanin me kikeyi ne wai?.."dan murmushi ta saki tareda kama nashi hannun itama still tana smiling tace mishi"yama sunan yarinyar kace?.."hade rai yayi yana kallonta yace"Mummy me zakiyi da sunanta kuma?..yarinyar da ina fada maki tana kokarin halakani shine kikeso kiji sunanta?.."murmushi ta kara saki tace"nidai fadamin sunanta plss..watarana ma so nake ka kawomin ita mu gaisa"...da mamaki sosai ya tsaya yana kallonta jin abunda tace...shi bai gane me take nufi ba sam ya ya kawo mgnr da ya kamata ta tayashi jaje amma sai behaving take kaman wani abun celebration ne ya faru...daddagewa yayi ya kwa6e fuskanshi kaman zaisa kuka yace"Mummy manaa..meye haka kikeyi plss?.."daria sosai ta saki kafin ta dakatar dashi tana sake dubanshi tace"to yanxu tell me meya kamata muyi?.."gyara zama yayi yana dubanta in a serious tone yace"shine abunda ban saniba Mummy..na rasa wace irin yarinyace ita..wlh jiya ko bacci banyi ba sbd haushin data kunsamin shiyasa har yanxu kaina bai dena ciwo ba..na rasa meyasa na kasa mantawa da komai har zuwa yanxu"..sake kamo hannunta yayi ya rikesu gam idonshi na sake canxa launi yace"Mummy ya zanyi in manta plss...inaso in manta"...ajiyar zuciya ta sauke tana kallon yanda duk yanayinshi ya sake sauyawa dan haka ta kwantar da murya tace"karka damu watarana zaka manta inshaAllah..ni wnn damuwan naka ne banaso kaga har yanxun jikinka akwai fever..inaso ka nutu ka kwantar da hankalinka sosai snn kayima kanka treatment kuma ka dena damuwa dan idan baka denaba ko kayi treatment dinma a banza zai tashi..ko kanaso wani ciwon ya kamaka ne?.."girgiza kanshi yayi da sauri yace"definitely not because of that stupid girl"...Mummy tace"then ka dena damuwa..yanxu ga breakfast na kawo maka ka shiga kayo brush zanyi serving dinka"...baiyi musu ba ya mike tsaye da kyar snn ya shiga takawa a hankali zuwa bathroom dinshi...mummy tabishi da kallo tana tausaya mashi..cikin ranta tana addu’an Allah yasa dai ba soyayya ne zai wahalar dashi ba don a yanda taga alamunshi soyayya zaiyi matukar bashi wahala sbd yanda yake da riko da kuma sanya damuwa cikin ranshi.
Bayan sati daya...
Tun daga wnn rana Lamido bata shiga sabgarshi ba..dan gaisuwan ma da take mishi idan sun hadu a hanya ta dena snn idan zai shekara kiran wayanta bazata dauka ba...yau tsahon kwanaki uku knn dayake kiranta bata dauka..tana ganin wayan zaiyita ringing amma ko kallonshi bazatayi da sunan dagawa ba...yanayi mata ciwo duk ta tuna da kalmar daya jefeta dashi ranan..wai tana biye biyen maza bi ma’ana dai tana karuwanci..lokaci daya duk wnn tsoron nashi taji ya ragu dan cikin kashi dari tasan yanxu da kyar za’a samu kashi hamsin a cikinshi...su Billy kuwa saida suka dauki lokaci kai tsah suna bata hakuri snn suna saku ta hakura suka cigaba da gudanar da rayuwarsu...shirye shirye sukeyi ma na zuwa Kd bikin Lubna fa za’yi next week suna dawowa kuma ba dadewa zasu fara exams daga nan sai Clinical posting sai kuma su shiga level 3...tsakaninta da babynta kuwa sai sambarka dan soyayya sai kara karfi yakeyi kullum.
A hankali ya shigo parlon yana tafiya a hankali kaman mara lafia hannunshi rikeda briefcase dinshi sai dayan kuma rikeda suit dinshi...kallo daya zakayi mashi ka gane bashida lafia sbd dan karen raman da yayi kaman wanda yayi wata a kwance...ya kara wani irin haske da idan ba saninshi kayi ha u will think ko bleaching ya fara...Miemie da Sab ne kadai zaune a parlon suna labari kaman basune ke fada kaman suna ganin hanjin juna ba...he is so lost in thought that har ya kama hanyan Flat dinshi bai lira dasu a parlon ba...Sabeer da bai dade da dawowa ba ya dan daga muryanshi da igbo yace"uncle Bobby sannu da zuwa"..dakatawa yayi tareda juyawa a hankali yana kallonshi yace"yaushe ka dawo?.."Sab yace"ban dade da shigowa ba..ya aiki?.."a takaice yace dashi"fine"..snn ya juya yacigaba da tafiyarshi walking slowly..dagashi har Miemie dankallo suka bishi sbd yanda yake tafia da yanda sukaga damuwa karara kan face dinshi shows kodai wani ya 6ata mashi rai ko kuma yana cikin serious rashin lafia idan akayi laakari da raman da yayi...yana shiga Mummy ta fito daga parlonta tana dubansu tace"kaman muryan Bobby naji yanxu"...Sab ne yace"shine..amma Mummy kinganshi kuwa?..bashida lafia ne?.."Mummy bata iya cewa komaiba ta bishi zuwa part din nashi...yana zaune gefen gado yana kokarin cire takalman kafanshi ta shigo dakin...saida ta isa har ciki ta zauna nan kusada shi snn ta dubeshi da kyau kafin tace"yanxu Bobby bakaji duk fadan da nayi maka ba daxun koh?.."rausayar da kai yayi yana kallonta kaman zaisa mata kuka yace"Mummy to yanxu me nayi?.."tace"kaki ka kwantar da hankalinka ka dena sama kanka damuwa mana...yanxu kana tunanin wnn damuwar da kake zaiyi sorting things out ne?.."rai a 6ace yace"Mummy yarinyar ce ta rainamin hankali...har wace ita da zan dinga kira tana ignoring min call?..har rejecting calls dina fa ta farayi sbd taga ban hadata da babanta ba"...murmushi Mummy ta saki tana kallonshi tace"kenan dai idan na fahimceka ignoring calls dinka da take bai maka dadi ba..u want her to be answering ur calls koba haka ba?.."da sauri ya shiga girgiza kanshi yace"Mummy don’t misinterpret me plss..that’s not what i mean"...tace"then why all this damuwa idan abun bai dameka ba?..why ka kasa cire abun a ranka har yake saka rama haka?.."shiru kawai yayi baice komai ba as basan mezai fada mata ba..sam bashida abun fada..shi kanshi yana mamakin kanshi wai the whole him ne yake damuwa sbd wata can tana ignoring calls dinshi...abun ya dameshi sosai bai abunda bai ta6a tunanin faruwa dashi ba har abada...ganin yanda yayi kicin kicin da fuska Mummy ta kara sakin smile tana cewa"nidai i want u to take it easy on urself plss..i told u kana bata hakuri komai wucewa zaiyi amma baka yadda ba"...tun kafin Mummy ta rufe baki yayi spitting yana fadin"over my dead body"..murmushi har yanxu takeyi tana girgiza kai...wnn hakilon nashi karamin daria yake bata ba wlh..kiri kiri ga abu yana feeling amma dan banzan ego dinshi bazai bari yayi admitting ba...mikewa tayi ta fita daga dakin don kawo mishi abincinshi tunda da dadewa ya yayema kanshi cin abinci tare dasu.
Ranan Tuesday karfe biyu ya bar Hospital zuwa College sbd yanason mgn da Nur...tunda incident din nan ya faru basu sake haduwa ba...yasan tunda yaji shiru Nur ko a waya bai nemeshi ba fushi yakeyi dashi...da kanshi ma yayi driving sbd driver dinshi baida lafia...yana shiga cikin premises din bayan yayi parking ya nufi Office din Nur yanata baza ido wai ko zai ganta a nan waje amma ko mai kamada ita bai ganiba.
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
27
Yana shiga ya iske Nur zaune kan office chair dinshi yana aiki da laptop yana ganinshi ya wani hade rai yanacigaba da aikin gabanshi ko kallon inda yake baiyi ba...Bobby ya karasa ciki ya zauna yana kallon yanda yake wani ciccin magani kawai saiya saki murmushi yana girgiza kai yace"Man how far?.."banza Nur yayi dashi yacigaba da aikinshi...Bobby ya sake cewa"Man meye haka ne plss?..stop acting like a kid"..tun bai rufe baki ba Nur ya dago yana kallonshi rai a 6ace yace"oh really?..wato I should stop acting like a kid sai kace kai ka manta wulakancin da kayimin harda korana office dinka ba"...saida ya barshi ya gama snn a nutse yace"I wasn’t on my sense..I was furious kai kuma kazo kana so kayi adding to what i was going through shiyasa nayi reacting that way amma am sorry"...wani harara Nur ya dago ya watsa mashi snn yacigaba da aikinshi...Bobby ya dan dafe goshi yanajin kanshi na wani sarawa sbd wnn abunda Nur yake..baisan meya sameshi ba amma shi yanxu sam bayason hayaniya..sam baison matsala idan ba hakaba head dinshi yayita mishi ciwo knn kaman me hypertension...after like 3 mins ya sake dagowa yana dubanshi yace"yanxu bazaka hakura ba dai knn?.."ba tareda ya dago ya kalleshi ba yace"ba haka ake bada hakuri ba ai..kai kanka kasan abunda kayi is uncalled for amma ya zanyi dakai?.."dan murmushi Bobby ya saki yana shafa lallausan gashin kanshi yace"to nace am soryy shikenan?.."sai yanxu Nur ya dago yana dubanshi yace"to yanxu kam na hakura..amma on one condition"...kallonshi Bobby yayi sai kuma ya dauke kai alaman baison wani mgn again..yasan tambayan da zaiyi mishi shi kuma sam bashida amsan bashi...tunanin nashi bai dire ba Nur yace"tsakaninka da Allah meya 6ata maka rai ranan?.."shiru kawai Bobby yayi as bayason fada mishi abunda ya faru...shi kuma Nur dage shoulder dinshi yayi yacigaba da aikin gabanshi yace"idan tayi naji"..qala dai baice mishi ba ya mike hands dinshi a aljihu...Kallonshi Nur yayi yace"so wucewa zakayi?.."yace"yes dama abunda ya kawoni knn?.."Nur ya sake daga shoulder dinshi yace"alright sai Thursday..my regards to Mummy dasu pretty"...Bobby ya amsa da"zasuji"..snn ya fita a office din..Nur ya bishi da kallo yana murmushi yace"dan rainin hankali zama ka gama guje gujenka ka dawo kan hanya ne...waya fada maka Borno gabas take?.."yana gama fadan haka sai ya kwashe da daria hadda su buga table ya sake cewa"su Dr Bobby in love har na matsu naga karshen love story din nan..da yake novice ne shi har dan ramewa naga yayi sbd damuwa..kai amma Lamido ta hadu wlh..kin gama min komai tunda kika fara daidaita wnn dan iskan"..ya karasa yana ske rushewa da daria...shikam ko baa fada mishi ba yasan definitely son Lamido yake sbd abubuwan da yaga yanayi dama wanda ita kanta Lamidon ta fada mashi.
Yana fitowa yaci karo da ita ta fito daa office din Sir Abdool aikam tana ganinshi ta wani hade rai tayi wucewarta abunta ko kallon inda yake batayi ba...saida takai bakin kofa sai kuma ta juyo idonta a kasa tana sake daure fuska murya a ciki ciki tace"ina yini"..kallonta kawai Bobby keyi without blinking...wasu irin ramuka da baisan dasuba a cikin heart dinshi yaji suna ciccikowa just by seeing her...haka nan yaji ganin nata gladen his heart sai a wani 6angaren kuma yaji ciwon zuwa office din Abdool da tayi...idan bai manta ba da bakinta ta ta6a furta mashi Abdool din sonta yake kuma shine zata biyoshi har office dinshi sbd batada hankali...ganin ta gaisheshi bai amsa ba ta juya zata wuce yayi saurin dawowa hayyacinshi snn ya dan daa murya ya kira sunanta"Aysher"...juyowa tayi tana dubanshi da mamaki...this is the very first time da taji sunanta a bakinshi..ko Lamido bata ta6ajin ya kirata dashi ba balle kuma Aysha da dama ba kowa ke kira a college din ba...takawa ya shigayi a hankali zuwa inda take..ya juya tabbatar ba kowa inda suke kafin ya sake juyowa yana kallonta ba yabo ba fallasa ya nuna mata hanyar office dinshi yace"muje"...turo baki tayi tana sake cin kunu tace"sir nifa class nakeso in koma"...bai sake ce mata komai ba kawai ya zuba mata idanunshi da yasan bata isa ta sake mishi gardama idan har ta kallesu...lokaci daya ta wani hade rai ganin yana kokarin yasata yin abunda batayi niyya ba bayan duk wulakancin da yayi mata hadda kiranta karuwa shine yau zai wani zo yace mata muje kaman shi ya haifeta...kallon da taga bazata iya jurewa ba ta wuce zuwa office din nashi yana binta a baya...da kanshi ya bude office din ya shiga snn itama ta shigo ya maida kofan ya rufe..ya karasa kan sofa ya zauna itama ya nuna mata wanda ke opposite dinshi yace"seat"..rungume hannunta tayi tana sake hade ranta tace"am comfortable here"..baice qala ba ya mike daga nan inda yake ya karasa ya tsaya dab da ita har suna jin kamshin perfumes din juna ya rungume hannu idonshi na kanta yace"fushi kikeyi dani?.."da mamaki sosai ta dago tana kallonshi don batayi excepting such mgn daga bakinshi ba..shima kanshi Bobbyn baisan lokacin da mgnr yayi escaping lips dinshi ba..it’s like mgnr ya fito direct from his heart bawai a baki kadai ya tsaya ba...ganin yanda suka hada ido kuma sai taji kunya ta sake yin kasa da kanta tana turo baki...shikam bai iya dauke idanunshi kanta ba ya sake cewa"say something mana..are u mad at me?.."sake kautar da kanta tayi tana cigaba da turo bakinta tace"cewa fa kayi ina karuwanchi"...wara idanu yayi cikeda mamaki yana kallonta yace"Nii?..when did i say that?.."wani irin bacin rai taji ya rufeta na ba gaira babu dalili kawai sai tayi kasa da idonta...Bobby da duk yaji hankalinshi na neman tashi cikin wani irin murya dashi kanshi baisan yana dashi ba yace mata"Aysher speak manaaa"...runste idanu Lamido tayi nan take taji hawaye na neman ciko idanunta...a take hankalin nashi kuwa ya karasa tashi cikin wani irin rauni da baisan daga ina yake fitowa ba yaji yana ce mata"dont cry plss..ki fadamin yaushe nace maki kina karuwanchi?.."hannu takai tana goge hawayen nata baki a tunzure tace"ba haka kace ina biye biyen maza ba..kuma ni ba biye biyen mazan da nakeyi ko Sir Abdool da ka ganni dashi shi yake sona bani nake sonshi ba"..baisan lokacinda bakinshi ya furta"shi kuma wnn dayan fa?.."dagowa tayi tana kallonshi dan bata gane wa yake nufi ba..ya wani hade ranshi kafin yace"that boy..wanda kikayi acting as his wife ranan da kukayi drama"...dan murmushi ta saki da wet face dinta jin wanda yake nufi tace"bestie na nefa"...kallonta kawai yake rai a 6ace ya rasa ma abunda zaice mata...ganin ta sake maida fuskanta ta dinkeshi tsaf kmr ba ita ta gama murmushi yanxu ba yace"is that why u are not picking my calls?.."tana turo bakinda ya zame mata sabo ta daga alaman eh..yace"then i am sorry...da nace kina biye biyen maza i never meant that kawai raina ne a 6ace..are we good now?.."shi kanshi yana mamakin kanshi yanda ya kwantar da murya yana mgn da ita...kai ta sake daga mishi alaman eh snn kuma tace"amma sir dan Allah ka denamin masif.."bata karasaba sai tayi saurin rufe bakinta tana kallonshi tace"sorry ina nufin fada..kuma ka dena kallona da idanunka yana bani tsoro"..murmushi kawai ya saki abunda ya mance yaushe rabonshi da yayi kawai ya koma kan sofa ya zauna yana cigaba da binta da ido..har wani ajiyan zuciya ya saki a 6oye sbd wani irin relieve da yaji just by patching things up with her..zuwa yanxu duk taurin kanshi yasan tabbas bazai iya daukan tana fushi dashi ba sbd ya fuskanci zuciyarshi bata san wnn karatun ba...ganin ya koma seat dinshi ya zauna itama ta dan kalleshi gamida kauda kai tace"sir zan tafi"...kallonta still yake yanajin kaman kar ya barta ta tafi...sam bai gaji da ganinta ba amma ko kusa yaki yin addmitting hakan..sbd ya karyata zuciyarshi da take ta mishi ihun cewa Lamido wani 6angare ce mai girma na cikinta kawai sai ya nuna mata kofa tareda fadin"u can leave"...yana rufe baki ta juya ta fita tana mamakin wai yau proprietor ne yayi mgn da ita haka ba wnn masifan nashi har yana bata hakuri..lallai kuwa za’ayi ruwa da qanqara...shi kuma Bobby sai yaji kaman an sauke mashi wani abu mai nauyi cikin zuciyarshi just by patching things up with her...baisan meyasa ba amma sai yajishi garau duk wnn damuwowi daya sanyama kanshi na kusan sati guda babu su...ranan har 'yan gidansu sun fahimci yana cikin nishadi don yanda yake murna da farin ciki says it all...Mummy dai sai binshi da kallo take cikin ranta tana"Allah dai ya tabbatar min da alkhairi"...nikuwa nace mata"Ameen Ameen Mummy".
Tun daga ranan sai suka koma mutunchi sosai da Proprietor dan yana daukan lokaci mai tsaho baiyi mata bala’i ba amma yanajin zancen saurayi ko something like that bai iya daurewa sai ya dan zazzaga mata yakejin dadi...yanxun ya koya mata duk ta shigo college da safe taje ta gaisheshi idan yana cikin makarantan..haka kuwa take zuwa ba don ranta naso ba..wani lokaci idan yana nemanta ko ta kashe waya ko bata shigo cikin makaranta dashi ba saidai kawai ta ganshi a class dinsu yazo ya wani hade rai yace yana nemanta..haka zatayita ture turen bakinta tabishi tana zabga mai harara ta baya..wnn dalilin yasa da yawa daga ‘yan class dinsu ke zargin akwai wani abu tsakaninsu wasu kuma sunyi zaton dan uwanta ne kamar yanda idan aka tambayeta sai tace"dan uwan daddyna ne fa".
Yau Thursday tun 3 Sa’eed ya daukesu zuwa gidan lalle sbd gobe zasu wuce kaduna bikin Lubna...amarya sai damunsu take da kira wai suyi sauri suje itafa ba wasu qawaye gareta ba...basu samu gamawa da gidan lallen ba sai after six dan haka Sa’eed na daukosu direct ya kama hanyan college dinsu..a hanya yaketa kallon lallen da Aysha ke nuna mashi tana fadin"besty lalle na yayi kyau koh?.."Sa’eed dake driving dinshi yace"sosai ma kuwa besty..aike din dama mai kyau ce so duk wani abu da zakiyi dole ma yayi suiting dinki"...Lamido ta saki murmushi tanata blushing tace"godia nake besty nah..shiyasa nake sonka wlh..besty bansan wane irin missing dinka zamuyi idan ka tafi ba"..ta karasa kmr zatasa kuka...shi kuma dan murmushi ya saki ba tareda yace komai ba don kuwa shi kanshi yasan dole yaji a jikinshi duk ranan da akace ya bar FCNM..yasan duk lokacinda yaso ganinsu bazaiyi mishi wahala ba ya dauko mota ya taho kano amma yasan bazai ta6a samun enough time dasu kaman yanda suke samu a yanxu ba...bayason zancen yayi tsayi sbd karyar mishi da zuciya suke dan haka ya kallo Billy ta mirror yana sakin smile yace"Billy banji kince komai ba"...harara mai kyau ya samu daga wurinta hakan kuma ya bashi daria sosai dama yasan abunda zatayi knn..shi tunda yake bai ta6a ganin wanda abun harara bai mata kadan kaman Hajia Bilkisu ba..ya tabbata zaiyi missing dinta fiyeda tunaninshi sbd wnn draman dake tsakaninsu...har suka karasa hostel ba wanda ya sake cewa komai a cikinsu..suna zuwa ya saukesu sukayi ciki shi kuma ya juya kan motarshi ya koma gida.
Washegari suna room dinsu sunata faman hada kaya a akwati yau ko makarantan bazasu shiga ba sbd da wuri zasu wuce...Aysha nata kiciniyar kulle akwatin da suka cikashi 6am da kaya kaman wanda zasuyi shekara a kaduna yayinda Bilkisu ke zaune gefen bed dinta ta zuba uban tagumi tana tunani..kamar daga sama taji tace"Lamido nifa har yanxu tsoro nakeji wlh..ina tsoron wani abu ya samemu a hanya bayan ko gida basu san zamuje kaduna ba"..tsaki Lamido ta saki tana cigaba da sabgar gabanta tace"matsalana da Billy dawo da mgn wlh...tun jiyafa muka gama mgnr nan na fada maki wlh kika sake gida sukaji zancen tafiyar nan bazasu bari muje ba kuma dai kinga idan mukayi haka bamuma Lubna adalci ba tunda da kunnenki dai kikaji tace batada qawaye sai mu..and koba wnn ba ko don besty bai kamata muki zuwa bikin nan ba nasan in Allah ya yadda lafia zamuje mu dawo lafia kawai dan kinsama ranki abun ne amma inshaAllah lafia zamu dawo kuma ba tareda kowa ya sani ba"...gyada kai Billy tayi cikeda gamsuwa dan har wani ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sake cewa"to Proprietor kuma fa?..did u tell him?.."da sauri Aysha ta shiga girgiza kai tace"waye ya aikeni in fada mishi salon yace babu inda zamuje knn..kema dai kinsanshi Billy wlh indai ya samu labari bazai bari ba"..Billy tace"amma kina ganin baza’a samu matsala ba?..ina nufin zai iya yuwa har muje mu dawo baiyi noticing ba?.."Aysha na gyada kai tace"of course mana..ai kinsan ba kullum yake zuwa makaranta ba gobe ne kawai mu kuma monday inshaAllah zamu dawo so he won’t know in Allah ya yadda"..gyada kai kawai Billy tayi saidai har yanxun cikin zuciyarta tanajin tsoro..har mamakin yanda ita Aysha bata damu ba take sai wani shiri takeyi tanajin dadi zataje garinda bata ta6a zuwa ba..tsakaninta da kaduna saidai ta wuceshi idan zasuje Abuja amma bata ta6a shigan garin ba.
Karfe 10 da wani abu suka kama hanyan kd...ita da Billy ne sai wani cousin din Sa’eed suka tafi gaba daya a motar Sa’eed din...ko a hanya Billy hankalinta ba kwance yake ba dan koya taji sun shiga gargada zata hau sallallami tana zare idanu wai a tunaninta ko hatsari ne zai ritsa dasu.😂
Basu samu isa kaduna da wuri ba sbd holdups da sukayita cin karo dasu a hanya sai kuma shi kanshi hanyan da ba wani kyawu kwarai ne dashi ba...lokacin da suka shigo kd was after one sosai dan har wasu masallatai sun fara sallahn jumu’a...kai tsaye unguwansu ya wuce dasu bayan ya kira Lubna ta shaida mishi cewa tana gidan wani uncle dinsu dake nan kusada gidan nasu...saida ya isa har kofar gidan snn ya sake kiranta nan da nan kuwa sai gata ta fito tana ganinsu ta daka tsalle ta wani cacimesu sai kace ba amarya...bayan sun gama cacime cacimensu suka karasa cikin gidan Sa’eed yabisu da kayansu ciki snn ya fito zuwa gidansu don yaje ya shirya sharp sharp ya wuce masallaci don ana idar da sallahn jumu’a za’a daura aure.
Suna shiga ciki Lubna ta kaisu suka gaisa da matar gidan snn ta jasu zuwa dakinda take ita kadai din da gaske ba wasu qawayen kirki gareta ba...mai make up na zaune tana jiranta tun daxu akaso farawa tace sai sunzo tukun za’a fara...zaunawa tayi aka fara mai aikin gidan kuma ta kawo masu abinci da drinks bayan sun gabatar da sallah suka zauna suka faraci...ko kafin a gama mata make up sun gama dan haka kowacce ta mike ta fara shiryawa don ‘yan daurin aure suna gab da dawowa.
Tare suka shiga gidan gaba daya su ukun bayan an gama cancada ma amarya kwalliyarta...Sa’eed da kanshi ya kaisu suka gaisa da Mom dinshi dukda taron jama’a dake gidan...daga nan kuma angwaye sukazo aka shiga daukan hotuna...su Lamido sai iyayi akeyi to abun nema ya samu...sai bayan sallahn asr suka koma can gidan uncle din amarya tareda few daga cikin friends dinta...karfe takwas na dare aka fara tafiya dinner...sudai suna tareda amarya tace qafarta qafarsu shi kuma Sa’eed yace lallai saidai ya tafi dasu..haka sukaita fafatawa daga karshe dai dole Lubna tayi hakuri ya wuce dasu bayan sun gama shiryawa...suna sanye cikin lace dinsu sea green iri daya duk cikinsu ba wadda tayi make up amma fadan kyawun da sukayi is a waste of time...tun daga mota Aysha ta dauko wayanta ta fara musu snap kala kala wani suyi gaba daya su ukun wani itada Billy wani kuma itada besty...koda suka isa hall din dinner ma cigaba da gashi sukayi...basu bar nan wurinda suke ba saida amarya da ango suka karaso...bayan an gama tsara masu shiga dasu Billy taja baya zatayi musu video Lamido kuma as usual tana sahun farko na wanda zasuyi rawa...ana sakar musu kida suka fara takawa zuwa ciki..Billy dai na gaba tana tafiya da baya baya tanata daukan video a wayanta...har suka raka bride and groom mazauninsu bata dena dauka ba...Aysha kuma bayan amarya da ango sun zauna ta nufi table din da ta hangesu zaune..videos din Billy ta hau nuna mata suna daria..Sa’eed ya kalli yanda take rawa yace"besty knn..na rasa wane irin soyayya ke tsakaninki da rawa wlh"...murguda mishi baki tayi batace komai ba...a takaice kafin a bar wajen dinner Aysha tayi rawa har jikinta saida ya gaya mata...pictures da videos kuwa tasha su a wajen Billy har ma da wanda bai kamata ba...saida suka koma gida suka nutsu kowa yayi shirin kwanciya snn Aysha tayi selecting wasu daga pics da videos da sukayi tayi posting a status dinta bayan tayi blocking duk wani wanda tasan idan ya gani labarin zai iya isa ga parents dinta...tana gamawa da whatsapp ta shiga instagram nan ma tayi posting snn ta kira babynta a waya sukasha hira abunsu..suna gamawa kuma bacci yayi awon gaba da ita.
Kano...
Tun safe Bobby ya shigo College dukda cewa saturday ne koda ya shigo bai samu zama ba don meeting suka shiga da staff bayan sun fito shi da Nur suka sake zama da wasu masu fili da yakeso ya siya a kusada college din daga nan kuma suka shiga hostel so gaba daya bai samu zama ba saida suka dawo daga sallahn jumu’a...yana shiga office driver ya kawo lunch daga gida snn ya fita...baa jima ba kuma sai ga Nur ya shigo..tare sukaci abincin a nan bayan sun gama ya kira driver ya tafi da ragowan shi kuma ya zaro phone dinshi ya shiga whatsapp sbd tun safe bai duba messages dinshi ba...reply ya farayi duk wani message mai muhimmanci yayi replying har zai ajiye wayan sai kuma ya fasa ya fara duba status..he is not a fan of viewing or uploading status amma yau haka nan yaji he should just check yaga what people are posting...na aunty sumy ya fara dubawa yaga picture dinshi ne a farko sai na ilham sai kuma na Sab da Miemie a hade...daga nata ya duba na Nur yaga pictures da Public Relation Officer na college din yayi musu daxu during meeting da sukayi ne duk yayi posting..dan ta6e baki yayi snn ya sake yin gaba har zai bude na wani colleague dinshi Dr Michael sai kuma ya fasa sbd ganin sunanta da yayi cikin jerin wanda sukayi posting...ba tareda tunanin komai ba ya danna sunanta nan take kuma picture din farko ya bayyana..ita kadaice a pic din tayi daria both dimples dinta sun fito..wani irin abu mai nauyi yaji yazo ya tokareshi a throat..dannewa yayi ya wuce gaba sai yaga itada Billy suna kallon juna still suna daria har dimples dinta sun fito...wnn karon zafi ya faraji all over his body ganin again ko mayafi babu a jikinta and ta fito da gashinta waje as usual..the next one kuma su uku ne a jiki ta turo bak tana kokarin sanya glasses dinta Billy kuma nayi mata mgn Sa’eed yayi musu selfie..na gaba kuma video ne ita kadai tanata dirkan rawa Billy tayi mata...sbd tsabar 6acin rai baisan lokacin da ya buga table dake ganashi ya furta"what the hell"da mugun karfi ba...daga shi kuma sai another video data daukesu su uku sunata murmushi sun sanya Sa’eed a tsakiya sai wanda aka daukesu tareda amarya da ango...haka dai yayita binsu daya bayan daya yana gani har saida ya gama gani tsaf snn ya ajiye wayar kan table ya dafe kanshi da both hands dinshi...Nur da tunda yaji abunda ya fada dazu ya dago yana kallonshi amma sai yaga all attension dinshi yanaga wayanshi yace"lafia dai?.."banza Bobby yayi dashi yana dafe da kanshi...wani irin zafi yakeji tun daga cikin zuciya zuwa gangar jikinshi..shidai ya rasa wace irin fitinanniyar yarinyace ita?..baisan wane irin rashin ji gareta ba?..yanxu kuma fisabilillahi ina taje sukayi wann pictures haka?..sbd tsabar batada hankali har rawa taje tayi a bainar jama’a..yasan kusan duk wanda ke wurin ya gama ganinta kilan ma baza’a rasa wanda yace yana sonta ba...tunanin hakan yasa yaji wani irin abu mai nauyi yazo ya tsaya mishi a kahon zuci...numfashi ma da kyar yake yinsa sbd azaba..shidai yasan Lamido idan ba nutsuwa tayi ba tana iya haifar mashi da ciwon zuciya watarana sbd abubuwan nan da yakeji a kanta sun fara wuce tunaninshi...duk wani jarumta da karfin halinshi na yaga ya 6oye abunda yakeji sbd Nur dake zaune wurin kasawa yayi...wani irin tari ya farayi sosai yana dafe da chest dinshi..Nur ya mike daga inda yake da sauri ya dauko ruwa daga fridge ya mika mishi yana cewa"sannu..have this zakaji sauki"...baiyi masa musu ba ya amsa ruwan dan shi kanshi yasan yanada buqatan duk wani abu mai sanyi a halin yanxu sbd turirin dake fita daga cikin zuciyarshi...tunda ya kafa goran ruwan a baki bai sauke ba saida ya shanyeshi..Nur dai na tsaye yana kallonshi har yaga ya dan samu nutsuwa snn ya zauna nan kusa dashi yace"mene wai..meka gani ya tayar maka da hankali haka?.."girgiza kai kawai Bobby yayi don baijin zai iya bude baki yayi mgn a halin da yake ciki...hannu Nur yakai ya dauki wayan nashi sai yaga sunan Lamido a jerin status da yayi viewing...bai tsaya wata wata ba shima ya shiga ya fara gani..saida ya gama tsaf snn ya dago yana kallon Bobby da har yanxu idanunshi ke lumshe yana dafe da head dinshi yace"so kishi ne ya motsa knn?.."wani irin kallo ya watsa masa kafin ya sake maida idonshi ya rufe...Nur ya fashe da daria yana cewa"idan ba kishi ba me kakeyi Dr Bobby?..you better wake up wlh"..ya karasa yana sake kwashewa da daria...Bobby dai diff yayi yana sake jin 6acin ranshi na karuwa...a fusace ya nunashi da yatsa yace"how dare you zakazo ka sani a gaba kanamin daria?..are u madd?.."ya karasa mgn da wani irin ihuu da saida Nur ya dora hannu a kunnenshi...bayan ya gama dariyarshi yace"continue deceiving urself kaji?..just keep on denying the fact that u love her..idan bakayi wasa ba kana zaune zata auri wani and ba yanda ka iya"...tun bai karasa ba Bobby ya sake buga table dake gabashi cikin karajii yace"how dare u?..how dare u talk to me like this?..nina fada maka ina sonta?.."gigiza kai Nur ya sakeyi yana shafa gemu cikin shakiyanci yace"har yanxu baka wahala ba shiyasa kake wnn kumfan bakin..idan kaji wuya da kanka zakazo ka sameni kayi kasa da voice dinka kace Nur i don’t know what to do plss help me..bansan yaushe na fara son yarinyar nan Lamido take ko Gidado?..".Ya karasa mgnr yana wani ta6e baki exactly irin yanda Bobbyn keyi kafin ya sake fashewa da daria...qala Bobby bai iya cewa ba ya mike ya kwashi wayoyinshi ya fice daga office din..idan ya tsaya ya tabbata za’a iya taruwa azo kallonsu don yanda zuciyarshi ke a kusa yana iya kwada mashi mari wlh..kawai takaici yakeji na wnn pictures da tayi posting ?..is she mad or something?..kwata kwata bata san kishin kanta ba..wai ma ina sukaje har sukayi pictures din at the first place?..yana buqatan ya kirata amma a wnn lokacin idan ya kirata kilan zaginta kawai zaiyi sbd yanda yakeji...kai tsaye motanshi ya nufa driver ya bude mishi ya shiga snn shima ya shiga suka fice daga makarantan..dama duk abubuwan da suka kawoshi college din ya gama..rabon zaiga wnn bakin cikin nema kila ya zaunar dashi.
0 comments:
Post a Comment