Ko cikakken 30 minutes baayi ba Nur ya karaso gidan..yana shiga ciki kai tsaye ya wuce flat din Bobby don bai samu kowa central parlor ba...saura kiris daria ya kufce mishi sbd ganin yanda sukayi wani tsuru tsuru suna kallonshi sai kace wanda akace musu ya mutu...karasawa yayi ciki yana kallonsu with smile yace"ya jikin nashi?.."Mummy ce ta mike daga inda take tana nuna Bobbyn da har yanxun ya juya musu baya tace"gashi nan dai..ka fara dubashi muga"...baiyi musu ba ya isa inda sphygmomanometer da stethoscope din Bobby ke ajiye ya daukosu snn ya dawo gefe gadon ya zauna ya ajiye kayan snn yakai hannu zai ta6a forehead dinshi ya wani daddage ya kwade mishi hannun aiko Nur ya fashe da daria sosai..bashi ba hatta su Mummy ya basu daria ganin yanda yakejin jiki amma har yanada energy din rigima haka...yana sake kai hannu Bobby ya kuma make hannun nan kuma Mummy ta daure fuskanta tace idan bai tsaya an dubashi ba zataci mutuncinshi..ba yanda ya iya haka ya mike zaune yana cika yana batsewa fuskan nan ba sarari kaman wanda aka aikoma sakon mutuwa...Nur bai damu da hade ranshi ba ya bude sphyg din ya zaro curf din ciki snn ya zurashi hannun Bobby yana tieing dinshi a hankali...bayan ya gama ya makale stethoscope dinshi a kunne tareda kama hannun nashi snn ya fara pumping...yana gamawa ya zare abun daga kunnenshi snn ya shiga kwance curf daya daura mashi yana duban su Mummy yace"Blood pressure dinshi is normal amma idan bai dena sa damuwa ba yana iya hawa nan gaba kadan"..Mummy ta gyada kai alaman ta fahimta shi kuma Nur ya mike zuwa first aid box dinshi ya dakko wasu drugs snn ya koma inda yake..Mummy tasa aunty sumy zuwa ta hado tea shima ya wani sake hade rai yace bazaisha ba saida Mummyn ta zauna da kanta itama ta daure nata fuskan snn aka samu ya sanyeshi tas ta amsa drugs din suma ta bala mashi yasha snn tace ya kwanta...ba musu ya sake juya musu baya ya kwanta yanajin yanda zuciyarshi keta harbawa sbd kular dashi da sukayi...bayan few minutes bacci ya daukeshi dan hadda maganin bacci aka hada mishi sai a lokcin suma suka fita daga dakin...kafin Nur ya tafi Mummy ta zaunar dashi tana tambayan ko wani abu ya hadashi da Bobbyn...Nur da har yanxu attitude din abokin nashi bai dena bashi daria ba yace"wlh ba wani abu Mummy love ne kawai yake dawainiya dashi kuma yaki admitting "..kallonshi Mummy keyi nan take kuma jikinta ya bata akan Lamido ne dan haka tace"u mean akan wnn yarinyar ne?.."Nur yace"a kanta ne wlh..kinsan halinshi da kafiya na fada mashi sonta yake yana maidani dan iska and the most funniest part of al’amarin shine azabar kishinta da yake wai amma har yanxun yaki accepting the fact that yana sonta..pics dinta fa kawai tayi posting a status shine yake wnn zazza6in"..gyada kai Mummy ta shigayi cikin ranta tace"lallai biri yayi kama da mutum"..a fili kuma sai tace"yanxu ya kake ganin za’ayi?..ni bansan irin Bobby ba wlh"..su Nur hadda gyara zama yace"nidai ina ganin dena mishi mgnrta kawai zamuyi..kuma idan kunayi ku dena nima daga yau ban kara fada mishi yana sonta..mu zuba mishi ido kawai na tabbata idan abun yafi karfinshi da kanshi zaizo ya fada"...shiru Mummy tayi tana nazari kafin tace"amma kana ga baza’a samu matsala ba?.."Nur yace"inshaAllah ba matsalan da za’a samu..a yanda halinshi yake indai za’a cigaba dayi mishi zancen yana sonta to ita kanta yarinyar zaiyita sauke mata masifanshi ne sbd zaiga kaman ita take janyo ana fada mishi haka..amma idan mukayi biris da al’amarin watarana da kanshi zaiyi admitting yana sonta"...gyada kai Mummy tayi tace"shknn Allah ya zaba mana mafi alkhairi..ni da zaka taimaka ka kawomin yarinyar ma in ganta"...yace"Kaii Mummy kinaso Bobby ya dena kulani knn?..a yanda yakeda kishin nan idan yaga na daukota a motata ai inaga kisan mutuwa zaiyi"..ya karasa mgn yana daria...aunty sumy da batsan da zancen ba sai yanxu tace"lallai Nur kasan kan abokin nan naka da yawa"...yace"ai aunty qanin naki ne kinsan zuma ne saida wuta"..daria suka saka kafin Nur yayi musu sallama ya wuce suma kowa ta nufi dakinta kafin a jima su sake zuwa ganin jikinshi.
Har gari ya waye Bobby bai denajin zafin da yakeji ba...ya samu dai headache da fevern sun sauka amma zuciyarshi dai tana nan a jagule yanda take tun jiya kuma duk kokarinshi na ganin yayi maganin hakan gagararshi yayi...ko yau da safe sau uku yana kiran numberta switch off hakan kuma ba karamin sake tunzurashi yayi ba..sbd batada hankali ta kwashi jiki ta tafi har kaduna biki sai kace bikin ‘yar uwarta?..kuma yanada tabbacin a gidansu ba’a sani ba dan haka jira kwai yake ta dawo ya sauke mata nauyin dake cikin zuciyarshi.
A can kaduna kuwa Lamido tunda tasan yasan inda sukaje hankalinta bai sake kwanciya ba dan ko bikin ma dena enjoying dinshi tayi..tsoronta Allah tsoronta kada ya kira daddy ya fada masa tasan yana fada itakam ta gama yawo..da farko kin fadawa Billy da shi kanshi Sa’eed din tayi sbd tasan zasu dora mata laifi musamman Billy amma daga baya dole suka gane akwai abunda ke damunta dan haka ta fada musu exactly yanda sukayi dashi...hankalin Billy ya tashi matuka dan ko ita Lamidon bazata gaya mata shiga tashin hankali ba dama yanda kasan farar kura haka take wajen tsoro...basuyi niyyan barin kd ranan sunday ba amma haka Sa’eed ya tattarosu suka wuce sbd yana guje musu matsalan da zasu iya fuskanta wajen proprietor dama kuma biki ya kare tunda ankai amarya...haka suka tafi ko sallama basuje sunma amaryan ba...karfe uku da wani abu suka dauki hanyan kano and basu suka shigo birnin dabo ba sai around six..suna ganin an dauki hanyan FCNM hankalinsu ya sake tashi musamman Aysha da cikinta har wani juyawa yake sbd tashin hankali...har tsoron kunna wayanta take sbd tasan tana kunnawa zai kira and hakan na nufin masifa da bala’i dan kuwa tasan idonta idon Dr Bobby saiya cinye mata mutunci tas tunda dama ba yanxu ya saba ba..kawai tsoronta kada ya hadata da babanta amma dan ta masifarshi mai sauki ne dan idan da sabo yaci ace ta saba dukda cewa yanxu sam bai cika mata ihu ba..wani lokaci ko abu ya kama na fadan ne da idan baiyiba bazaiji dadi ba sai yayi mata shi a nutse kaman ba fada yakeyi ba amma yau kam tasan idan akwai abunda ya wuce ihu ma zaiyi shi tunda ta gama kular dashi...har suka isa hostel babu mai kwarin guiwar yin mgn cikinsu shi kanshi Sa’eed din addu’a yakeyi Allah yasa bazasu samu matsala sbd shi ba tunda shine wanda ya daukesu zuwa kadunan and Allah ya sani da yasan basuyi informing parents dinsu ba ba dalilinda zaisa ya kwashesu har kd saidai rashin sani...kafin su rabu ya sake kwantar musu da hankali tareda assuring dinsu cewa inshaAllah komai zai tafi normal..sukam gaba dayansu jinshi kawai sukeyi amma gani suke dole fa sai wani abu ya faru either big or small.
The next day sukayi shirin school kowa tasa uniform dinta suna jiran school bus saidai ba wanda takeda walwala a cikinsu...baa jimaba bus dinsu yazo ya kwashesu sukayi cikin makarantan...ana ajiyesu suka fice yau har rige rigen fita daga bus din suke a takaninsu sbd gudun haduwa dashi dukda ma sunsan monday ba ranan shigowarshi bane...daga nan direct class dinsu suka wuce basu sake fitowa ba har suka fara lectures.
Karfe tara daidai yayima Bobby a college din dukda cewa Monday ne ga kuma jikinshi da bai gama sauki ba amma ko hospital ya kasa zuwa sbd yanaso ya ganta...kai tsaye sama ya haura zuwa class dinsu don yasan idan yace har saiya sameta a waya to bazai taba samunta ba dan ba kunna wayan zatayi ba...wani lecturer ya samu a class din yana musu lectures dan haka kai tsaye ya fada class din fuskan nan a tamke kamar baisan menene daria ba...hannu ya mikawa lecturer din suka gaisa snn ya maida hannun aljihu yana baza idanu yanaso ya hangosu amma ko daya daga cikinsu bai gani ba...hankalinshi ya maida kan ‘yan class din fuska ba fus yace"where is Lamido?.."da sauri suka nuna inda take can baya tana sunukuyar dakai..baice kala ba sai takawa da yayi har gaban seat din nata ya zuba mata idanunshi ko kadan bata sonsu snn a kausashe yace mata"mike.."ba musu ta mike tsaye kai a kasa..ya sake cewa"ina Bilkisu?.."da sauri itama ta nuna seat dinda Billy ke zaune itama kallon nata yayi tayi saurin dukar da nata kan snn ya juya still hands dinshi a aljihu yace musu"follow me"..sum sum suka bi bayanshi kaman marasa gaskia..yana gaba suna binshi dukda bai juyaba yanajin footsteps dinsu ta bayan nashi dan haka kai tsaye ya wuce office dinshi suna biye dashi..a hanya ya kusa cin karo da Nur ya wani wara ido yana kallonshi then su Lamido dake biye dashi sai kuma ya saki dan murmushi yana maida dubanshi gareshi yace"so ka warke knn?.."ko kallonshi Bobby baiyi ba ya wuce office dinshi...yana isa ya bude kofa da yake bai shigowa Monday so secretary dinshi bata zoba...shine ya fara shiga ciki snn sukabi bayanshi...a kan sofa ya zauna yana kallon yanda sukayi wani cirko cirko a gabanshi sai ya sauke idanunshi kan Billy da yake ganin kamar tafi hankali yace"Bilkisu hadda ke?.."da sauri Billy da kanta ke kasa tace"wlh sir ba laifina bane ba yanda banyi da ita akan mu fada a gida ba tace wai baza’a fada ba"..yace"then meya hanaki kirani ki fadamin?.."Billy da har ta fara hawaye tace"shima cewa tayi bazan fada ba wai sbd hanawa zakayi?..sir dan Allah kayi hakuri wlh bazai sake faruwa ba"..gyada kai yayi dan ya yadda da ita yace"next time kina ganin zatayi anything stupid just give me a call ai kinada number na"..gyada kai Billy tayi tace"inshaAllah sir"..yace"shknn u can leave"..Billy tayi godia snn ta juya zata fita Aysha tabi bayanta da sauri wai tunaninta ya sallamesu gaba daya amma sai taji cikin cunkushashen voice dinshi yace"who ask u to leave?.."juyowa tayi a hankali tana dubanshi kaman zatasa kuka tace"sir dan girman Allah in tafi"...ya sake hade rai yace"C’mon comeback here before i loose it with u"..juyawa tayi a hankali ta daw ciki idonta na cikowa da hawaye...kallon hawayen dake silalowa daga idon nata yayi nan take ya lumshe ido yanajin yanda hawayen ke sauka har cikin zuciyarshi...baisan meyasa these days ko tayi laifi tana fara kuka jikinshi ke mutuwa ba..so yake yayi mata masifa son ranshi amma yana ganin hawayen nan yaji zuciyrshi yayi waji weak...kujera ya nuna mata idanunshi a kanta yace"seat"...batayi musu ba ta zauna inda ya nuna mata tana hawaye na sake ambaliya akan face dinta...dafe goshi Bobby yayi hade da lumshe ido yanajin yanda takeso ta sake haddasa mishi ciwon kai da wnn kukan nata yace"For Gods sake me akayi makai na kuka ne wai?..nayi maki wani abun ne?.."girgiza mashi kai tayi still tana hawaye yace"then why are u crying?..nida kika haddasa ma rashin lafia banyi kuka ba saike zaki sani a gaba kinamin kuka?..kinama da hankali kuwa?.."turo baki tayi jin abunda ya fada wai ta haddasa masa rashin lafia..ta sake tale baki tana dan kallonshi ta gefen idonta tace"nidai dan Allah karka fadawa daddy plss"...kallonta yakeyi yace"naji I won’t tell him amma inaso ki dena kukan nan muyi mgn dake"..ba musu takai hannunta ta goge hawayen duk yana kallonta snn tace"na goge"..gyara zama yayi still idonshi kanta yace"tambaya nakeso inyi maki and i want u to be fair to yourself..idan da a Gombe kike gaban parents dinki would u do what u where doing now?.."girgiza mishi kai tayi a hankali alaman bazatayi ba...yace"then why kikeyi a nan sbd ba gabansu kike ba?..tsakaninki da Allah da ace wani abu ya sameki a hanya what do u want me to tell ur dad daya bani amanarki?..ko sbd kina ganin baki ta6a yin wani abu na sanar dashi ba?.."girgiza kai ta shigayi da sauri tace"sir wlh ba haka bane..gani nayi Lubna friend dinmu ce sosai and ko sbd besty bai kamata muki zuw..."bata karasa ba ya katseta cikin karaji yace"in your entire life karki sake mentioning min besty idan muna mgn..ina ruwana da wani besty ni ke na sani bashi ba and idan bakiji abunda na fada ba kuma you will see the other side of me"..ya karasa mgn har wani huci yake kaman tsohon zaki...Lamido dai kallonshi kawai take tana mamakin yanda yake changing forms within minutes..yanxun nan fa yake mata mgn a nutse kmr bashi ba within a second kuma ya dawo mata asalin proprietor data sani...kauda kanta tayi tana turo baki ita gara ma ya dingayi mata masifan kmr yanda ya saba ba yasata a gaba yanayi mata mgnr dake sa jikinta yana mutuwa ba...ganin yanda itama ta hade rai tana turo mishi baki ya danyi kasa da voice dinshi yace"wai meyasa bakijin mgn ne ke kam?..meyasa fitinanki yayi yawa?.."sake turo baki tayi tana gunguni kuma akan idonshi kawai sai ya rufe idanu tareda jingina jikin kujera yana karanta innalillahi a cikin ranshi...kamar yanda ya fada ne idan baiyi wasa ba yarinyar nan saita haifar mishi da ciwon zucia sbd abunda yakeji kanta is beyond his control...kawai yana ganin Allah ne ke jarabtarshi da ‘yar Gombe sbd tsananin kiyayyan da yakema ‘yan Gomben.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
29
Kallonshi Aysha keyi ganin yanda ya dafe goshi ya lumshe ido aikuwa ta daddage ta maka masa wani harara sai gashi karaf ya bude idon nashi...ta wani zaro ido hadda dora hannu a bakinta tace"sir i swear bada kai nakeba"..bai iya cewa komai ba sai kallonta da yakeyi nan kuma tayi kasa da idanunta tanajin idanun nashi har cikin brain dinta...ta rasa meyasa har yanxun ta kasa sabawa da idanun mutumin nan..sam bata kaunar ya zuba mata su sbd sawa suke tanajin wani iri wlh..sai su saka nutsuwar da baka shirya masa ba...shiko Bobby kallon nata yakeyi yana tattaro duk wani abu da yasan yanaji akanta yana dorasu cikin idon nashi wai ko Allah zaisa taga illar da take nemanyi mishi ta zubar da makamanta...sun dauki lokaci mai tsaho a haka har zaman wurin ya fara isanta kafin kuma taji yace"bani wayarki?.."juyawa tayi ta kalleshi sai kuma ta kwar da idon da sauri ta zaro wayan da aljihunta ta mika mashi..ya amsa ya duba sai yaga babu key a jiki dan haka kai tsaye whatsApp dinta ya shiga yayi deleting gaba daya status dinta daga nan ya shiga gallery nan ma yayi marking all pictures dinsu na kaduna yayi deleting snn ya shiga bin duk wani picture da sukayi itada besty yana deleting dinsu...a garin haka yaci karo da wani da sukayi itada Prof ya zuba mata ido yana kallonta da murmushi itama tana murmushin aka dauki picture din...wani abu mai daci yaji yazo ya tokareshi a makoshi..sai yayi zuru yana kallon pic din yana sakejin zuciyashi ma tafarfasa amma bai nuna mata ba yayi deleting pic din ya muma cigaba da abunda yake...bayan ya gama da wnn foldern ya fito ya shiga wani sai yaci karo da pictures din ‘yan Manchester rututu musamman Pogba dan nashi sunfi na kowa yawa a matsayinshi na best player dinta...tsayawa kawai yayi yana kallon pics din kaman gunki..yana yin minimizing ya sake cin karo da hoton pogba akan screen din wayan nata datayi making as wallpaper ai baisan lokacin da yayi wurgi da wayan nata ya fadi kasa ba...Lamido ta wara ido tana kallonshi idonta kmr zasu fado don mamaki kawai sai taga ya mike ya fada bathroom ya wani buga kofan da mugun karfinda saida ya tsorata ta...jiki na rawa ta mike ta fita daga office din ko takan wayanta da yayi rugu rugu a kasa batabi ba...shiko yana shiga samun wuri yayi ya zauna yana dafe head dinshi wani azababben kunchi na sake rufar mishi...ya tabbata da yaci gaba da zama a wurin nan ita kanta yana iya yin ball da ita sbd kuncin da yakeji...ashe rashin hankalin nata har yakai ta ringa tsayawa tana hoto da ko wane banza and to top it all har tara hotunan ‘yan kwallo takeyi a wayarta kaman ta hada wani abu dasu?..hadda wani sanya picture din namiji a wall paper dinta wai meke damun yarinyar nan ne kam?..waye wani Pogba da take mugun sonshi haka?..me akai akayishi ma gaba daya..anya kuwa yarinyar nan bata samu ta6in kwakwalwa ba?..idan ba haka ba why zatana abubuwanda ba kowace mace ce keyi ba..meya hada mace da kallon ball idan ba tsabar rashin hankali ba...saida ya dauki lokaci mai tsaho nan cikin bathroom kafin ya fito..bai sameta a office din ba amma wayanta na nan inda yayi wurgi dashi sai yanxu kuma yaga bai kamata ya fasa mata waya ba..kaman yayi overreacting amma shi kanshi ba laifinshi bane baisan meyasa yake kasa controlling abuna yakeji akanta ba...gaba daya ma sai yaji dana sanin zuwa college din yake at the first place kawai sai ya juya ya fita daga office ba tareda yabi takan wayan daya farfasa mata ba.
Karfe hudu da kusan rabi ya baro hospital kai tsaye yacema driver ya kaishi FCNM zai shiga hostel yayi wani abu...driver ya dauki hanyan college din shi kuma Bobby yayi relaxing a back seat idanunshi lumshe yana sake sake cikin ranshi...tun daxu yasa aka kawo mashi sabon waya irin nata sak shine yakeso yakai mata tun kafin taje ta fara yamadidi dashi cewar ya fasa mata waya...bakin kokarinshi kawai yake na ganin abunda yakeji bai kwantar dashi ba amma ko Allah yasan ba karamin mawuyacin hali yake ciki ba...suna isa cikin hostel din yasa akayi mishi mgn da daya daga cikin matrons dinsu ya bata wayan bayan yace mata ta bada a kaiwa Lamido...daga haka gida ya koma dan ko ganinta bai sonyi ballantana ta sakeyin wani abun zuciyarshi tazo tana bugawa...koda ya koma gida yaki kwanciya kokari yakeyi sosai ya yaki abunda yakeji gameda ita yasan yana bari ya kwanta shknn ciwo zai samu galaba a kanshi.
Haka kwanaki sukaita tafiya suna zama weeks..weeks kuma suna zama watanni har suka fara second semester exams...zuwa yanxu Bobby ya tabbata ko ba sonta yakeba to definitely he’s attracted to her and tunanin hakan kadai yana iya samai zazza6i sbd tsabar takaici...zuciyarshi kwata kwata bata mai adalci ba amma alqawari ne ya daukan ma kanshi bazai bari koma me yakeji a kanta yayi tasiri a zuciyarshi ba...da wnn alkawari ya samu yake yaqar abunda yakeji dukda cewa ba karamin wahala bane yake bawa kanshi...har suka gama exam suka tafi hutu bai sata a idanunshi ba hakan kuma ba karamin tada hankalinshi yayi ba abun har mamaki ya bashi...da farko gani yake kaman rashin ganin nata shine mafi a’ala amma zuwa yanxu ya tabbatar idan ba ganin nata yayi ba yana iya samun gagarumin problem...haka a daddafe suka cinye two weeks dinsu na holidays zasu dawo school Sunday..Monday kuma kowa ta fara zuwa Clinical Area...baisan hospital da za’ayi posting nata ba dan haka yau Saturday yana barin Hospital ya kira Nur yace yanaso su hadu a College that yanada mgnr da yakeso suyi dashi..Nur baiyi masa musu ba yace su hadu a college din...karfe biyar saura ya shiga cikin makarantan a lokacin ma ko Nur din bai karaso ba dan haka ya jirashi nan cikin mota ya karaso snn suka wuce office din Nur din gaba daya...bayan sun zauna Nur yace"to Dr Bobby ina sauraronka"...ajiyar zucia Bobby ya sauke yana tunanin ta inda ya kamata ya fara dan bayason iskancin Nur ko kadan dan haka ya dinke fuskanshi tsaf yana wani babbasarwa snn kai tsaye yace mishi"wane Hospital akayi posting Lamido?.."Nur yayi kuri da ido yana kallonshi yana daria cikin zuciyarshi yana tausayi abokin nashi amma bai nuna mishi komai ba a fili yace"well ina tunanin bazai wuce General Hospital ba..kasan rural posting ne"...da sauri Bobby yace"inaso a dawo da ita Freedom"...kallonshi dai Nur yacigaba dayi yana tuno ranan da tazo tace a canxa mata posting amma yace baza’a canxa ba yanxu kuma gashi da kanshi yakeso a canxa mata posting din..kamar zai tsokaneshi sai ya tuna yanda sukayi dasu Mummy dan haka ya basar tareda fadin"shknn zanyi mgn da isaac zaa canxa mata inshaAllah"...wani ajiyar zucia Bobby ya saki sai yaji kaman an sauke mashi wani nauyi...yanada reasons da yasa yace a kawota Freedom sbd yasan ba hankali ta cika ba kilan zuwa zatayi taita kule kulen maza tana abunda bai kamata ba shiyasa yake sonta a kusa dashi yanda zaisa mata ido...Nur dai nata kallonshi yana kunshe daria a haka sukayi sallama kowa ya shiga motarshi ya wuce.
Washegari misalin 12 suka iso makaranta tareda Hamma daya dawo dasu as usual...kowa taje ta duba posting dinta suna murna zasuje rural posting amma sai sukaga an sake posting dinsu Freedom again...aikuwa gaba daya murnan da suke ciki sai ya koma ciki musamman Lamido da ko kadan last posting da tayi a Freedom din bataji dadinshi ba infact that was the most difficult and boring posting data ta6ayi a rayuwarta..lokaci daya duk wnn farin cikin na tafi rural ya koma ciki...kallon Billy tayi tana wani misti misti da ido sbd 6acin rai tace"zo muje mu samu provost mu fada mashi wlh..kan me za’a wani sake kaimu Freedom bayan ko last time can mukaje"...girgiza kai Billy tayi tace"nidai babu inda zanje and ina bakin shawaran kema ki hakura kawai..if u could remember last time ma kinje a canxa maki posting din hakan bai yiwu ba so yanxun ma ba canxa maki zasuyi ba"..sake hade rai Aysha tayi tace"amma nidai an cuceni wlh..dukma wanda ya bada shawaran a barmu a Freedom Allah ya isa tsakanina dashi wlh"...dan murmushi Bily ta saki kafin tace"nasan bazai wuce proprietor ba"..Aysha dai batace komai ba haka suka karasa cikin hostel kowa rai a 6ace.
Ranan Monday tun seven Bobby ya bar gida zuwa Hospital ko breakfast bai iya tsayawa yayi ba duk yanda Mummy taso yayi hakan kuwa...so kawai yake ya sanyata idonshi ko zai samu ya cike wasu gurabe da yakejinsu so empty a cikin zuciyarshi...su kuma basu karaso Hospital ba sai after eight...bus dinsu na gama parking duk suka firfito zuwa cikin asibitin kowa sanyefa uniform dinshi...daga bakin office dinshi ya hangosu suna tafia and duk yawan nan nasu idanunshi basu sauka kan kowa ba sai ita..nan take kuma yaji wani irin sanyi mai hade da zafi yana mamaye zuciyarshi..shi sanyin dai na ganinta da yayi ne after a long period of time while shi kuma zafin na jin ciwon yanda tazo asibitin ne daga ita sai dan hijab dinsu na uniform da ko chest dinsu bai gama rufewa ba...wasu sukan dora hijab ko mayafi akai idan anzo makaranta ko asibiti sai a cire amma Lamido koda wasa bai ta6a ganin tayi irin wnn ba...haka take yawonta a college da hospital tana tallata surar jikinta kowanne jick and jerk yana kallo...gashi ya kasa dauke idanun a kanta tunda yake bai ta6a jin ciwon kananun hijabs din nan nasu ba sai yau..gaba daya jikinta a waje yake sararin Allah...har sukazo suka wuceshi bai dena kallonta ba saida suka shiga office din da za’a yi musu posting...already yayi mgn da CNO yace ayi posting dinta theatre yanda zai dinga samun ganinta sosai..idan basuda aiki kuma ta tafi Office dinshi dan yasan tsaf zai iya zuwa ya samu tana hira da doc Gabriel ko doc Vivian...kaman yanda ya tsara din kuwa haka akayi..tanaji anyi posting dinta theatre hankalinta yakai kololuwar tashi dan har yanxu bata mance suman da tayi last time da suka shiga theater ba..sbd tsabar wulakanci duk fadin asibitin nan a rasa inda za’ayi posting dinta sai theater?..aiko billahillazhi bazata zauna a theater ba saidai duk abunda za’ayi ayi...suna barin office din kowa ya nufi various post dinshi including Billy dake maternity...ita kuma sai ta nufi office dinshi da nufin ta hadashi Allah annabi yasa a canxa mata posting...da sallama ta shiga ciki kanta a kasa ta gaisheshi...ya shiga binta da kallo sama da kasa yana wani 6ata rai kaman baiji dadin ganinya ba ya nuna hijab din jikinta yace"shi wnn mezai hana ki cireshi sai ki dinga yawonki a haka kawai"..kallonshi takeyi kallo irin na mamaki jin mgnr daya fada kafin tace"sir in cire hijab dina fa kake nufi"..a fusace yace"to meye amfaninshi tunda dama jikin naki kikeso a gani ai saiki cireshi kawai yanda zaa samu daman kallon jikin naki da kyau"...daure fuska tayi tana turo jin inda zancen nashi ya dosa tace"nidai bazan iya yawo babu hijab ba"...yace"if u are referring wnn abun dake jikinki to a hijab then you are deceiving yourself..ke ko irin asa babban hijab akan uniform baki iyaba..u always come out like this kamar dai tallan jikin naki kike"...sake daure fuska tayi jin maganganun da yake fada..indirectly fa zaginta yakeyi knn?..ita batasan ma tsautsayin daya kawota office dinshi ba tunda tasan halinshi and bazai ta6a canxawa ba...juyawa tayi zata fita a fusace yace"come back here"..ba yanda ta iya haka ta juyo ta dawo tana tutturo baki...mikewa yayi ya shiga wani kofa dake office din can sai gashi ya dawo da coffee hijab mai girma a hannunshi yana zuwa ya mika mata...batayi musu ba ta kar6a saidai fuskan nan har yanxu ba fus...komawa seat dinshi yayi ya zauna ita kuma ta sake juyawa zata fita yace"dawo kisa hijab din nan"...kaman zatayi kuka ta dawo ta zura hijabin..shi kuma yana zaune yana kallonta har wani dan murmushi ya saki ganin hijab din yayi covering dinta yanda yakeso yace"perfect...now seat saiki fadi meke tafe dake?.."zaunawa tayi tana sake marairaicewa tace"Sir dan Allah so nake kayi mgn CNO a daukeni daga theatre..tsoro nakeji wlh"...murmushi sosai ya saki wanda har ya bata mamaki dan zaiyi wahala kaga murmushinshi shiyasa idan yayi ma sai ta ganshi wani daban kmr ba proprietor data sani ba...saida ya gama smiling dinshi snn ya sake relaxing kan seat dinshi yana kallonta kamar ba gobe yace"yanxu me kikeso inyi Lamido?.."da sauri ta sake dagowa tana kallonshi dan ita wlh bata ta6aji ya kirata da Lamido ba..ko sunanta ma ita baya kira saidai yace ke ko wani abu amma yau shine da kiranta Lamido?..duk yau sai taga kaman bashi ba..kaman canxashi akayi sbd yanda yake behaving is so unlike him...ganin yanda tayi wani zuru tana kallonshi sai yadan hade rai yace"meye?.."da sauri tace"sir cewa fa kayi Lamido"...ya sake hade ran yace"eh ba hakane sunanki ba?..ko kinfi so kiji nace Aysher?.."wani mamakin ya sake kamata da alama yau dai Dr Bobby na cikin farin ciki...saita dan saki smile itama kafin tace"sir you are in a good mood today"..yana cigaba da smiling dinshi yace"of course..rabona da jin farin ciki kaman na yau har na mance"..dan wara idanu tayi irin abun mamakin nan sai kuma tacigaba da smile dinta tana gyada kanta tace"to sir albarkacin farin cikin da kake ciki kayi mgn a canxa min posting dan Allah"...girgiza mata kanshi yayi in a serious tone yace"no..kawai kiyi hakuri kije tunda can aka kaiki"...kaman zatasa kuka tace"sir suma fa nakeyi idan naga ana yayyanka mutum"...murmushi ya kara saki before yace"zaki dena inshaAllah..kuma I promise idan naga kin maida hankali kin nutsu sosai da kaina zanyi posting naki inda kikeso?.."nan da nan face dinta ya washe da fara’a tace"dan Allah da gaske?.."yace"yea i mean it..kawai so nake inga kin nutsu"...yana rufe baki kuwa ta hau gyada kanta tana fadin"nama nutsu tun yanxu wlh..i will be behaving gently"...yace"ni kuma zanyi posting naki inda kikeso"...sake gyada mashi kai tayi tana murmushi sai kallon yanda shima ya kasa dena murmushin take...mamaki take ashe haka murmushi ke bala’in mishi kyau amma baya yi?..kam ai da itace ta gane murmushi nayi mata irin kyan da yake mishi da kullum cikin murmushi zata kasance wlh koda cikin bacci ne kuwa...shi kuma kallonta kawai yake yanajin yanda yau ta ware dashi ba tsoro ba fargaba ko 6acin rai a tattare da ita...shi kanshi so yake ya gina kyakyawan alaqa tsakaninshi da ita yanda ko sun koma college bazata na gudunshi ba snn bazata na daure mashi fuska ba...yayi na’am da wnn shawara na zuciyarshi dan haka ya daura damarar gina shakuwa tsakaninshi da ita.
Cikin lokaci qanqani sai shakuwa ya shiga tsakaninsu kamar dai yanda Bobby ya daura damara a farko...sam yanxu basu fiya fada ba dan tanabin kusan duk abunda yace tayi sbd ya canza mata posting...ranan da farko da aka sake shiga theater da ita saida tayi wnn suman saura kadan ta fadi Bobby yayi saurin tareta ta fada jikinshi...gaba daya hankalinshi dama yana gareta sbd yasan something like this might happen...dole sai fita sukayi da ita suka kira wata tayi replacing dinta amma daga baya a hankali sai ta fara sabawa...gaba daya tsoron sai ta dena jinshi tunda gashi za’a shiga theatre da ita har ayi a gama bata ji jiri kota suma ba saidai dan wanda baza’a rasa ba...a zaman kuma ta koyi abubuwa da dama dan sai yanxu take gane ashe zama a theater din yanada amfani...a haka ta cinyeshi two weeks dinta a theatre.
Yana zaune office dinshi yana duba patients wayanshi ya fara ringing bai daga ba saida ya sallami matar ta fita..ya saki dan murmushi ganin wanda yake kira snn yayi picking ya gaidashi with respect...a daya 6angaren daddy yace"Attahir kana lafia?.."yace"ina lafia sir..ya aiki?.."daddy yace"Alhamdulillah..kana gida ko asibiti?.."yace"ina asibiti"...daddy yace"alright send me the address na shigo kano sai inzo mu gaisa"..da sauri yace"right away sir..itama tana asibitin yanxu haka"..murmushi daddy yayi kafin yace"ni kai zanzo gani ba itaba"..murmushin shima yayi kafin suyi sallama ya tura mishi address din...cikin mintina qalilan daddy ya karaso hospital din..Bobby da kanshi ya fita ya shigo dashi yanata yaba kyau da tsaruwar asibitin har suka dangana a office dinshi...zaunawa yayi shi kuma Bobby ya bude fridge ya kawo mashi ruwa da lemo snn shima ya zauna suka sake gaisawa...daddy yayita janshi da hira yana yaba asibitin nashi shidai tun yana jin kunya har ya sake ya shigayi mishi bayanin yanda suke gudanar a aiki a asibitin..har Schools da Colleges da yake dasu a sauran states saida ya fada mashi...ya kuma sanar dashi cewa yanxu haka yana preparation na bude Freedom University a Lagos...daddy ya jinjina ma kokarin yaron sosai ya kuma jinjinama kwazonshi da yake iya hada aiyuka da dama haka shi kadai..dukda cewa yana assistant a ko ina shima ba karamin kokari yake ba..nan take yaji ya sake burgeshi matuka..soyayyarshi ta ninku a cikin zuciyarshi fiyeda na baya..saidai ko kusa baiyi mamaki ba sbd yasan jinin Col Attahir zai iya aikata fiyeda haka ma a doron kasa matukar ya gaji mahaifinshi...suna zaune suna wnn hira Aysha ta shigo office din tana kokarin zaro wayanta daya dameta da kara sakamakon kira da akeyi tace"ko uban waye wnn yake damuna da kira oho?.."a tare suka juya suna kallonta jin abunda ta fada...daddy yace"sannu shugaban masu hankali"..batasan lokacinda ta saki waya da jakan nata ya fadi kasa ba sbd muryan wanda taji..sam batayi tunanin ganinshi ba wlh...lokaci daya kuma ta saki murmushi bayan ta dauki bag da wayanta ta karasa cikin office din tace"daddy sannu da zuwa"..girgiza kai kawai daddy yayi yana kallonta..can kuma ya juya yana duban Bobby da kanshi ke kasa yace"nasan kana nan kana fama da ita kou?.."dan dagowa yayi ya kalleta sai kuma ya saki murmushi yana girgiza kai yace"ai tayi hankali yanxu"..daddy yace"kana dai kareta amma ni nasan akwai abubuwanda dole saita yisu zataji dadi"..murmushi kawai Bobby yayi baice komai ba..ita kuma ta wani turo baki a cikin ranta tace"wato da kallon mara hankali sukemin knn da za’a wani ce nayi hankali yanxu"...muryan daddy ya dawo da ita daga tunaninda take nan ta gaisheshi snn yace taje ta kira Bilkisu..bayan few minutes suka dawo tareda Billy itama ta gaida daddy yana tambayarsu ya posting sukace Alhamdulillah...bayan sun gama yace suje kafin ya wuce zai nemesu zaiyi mgn da proprietor dinsu ba musu suka bar office din..shi kuma daddy ya shiga tambayan Bobby if da akwai abunda takeyi wanda ya kamata ya sani Bobby yace sam tayi hankali yanxu ta dena rashin ji..daddy yaji dadi sosai ya kuma ce still dai yanaso yacigaba da monitoring dinta har zuwa lokacinda zata bar makarantan domin koshi a yanxu yaga canji tattareda ita hakan kuma alamane na Bobby ya rike amanar daya bashi knn...Bobby ya amsa mashi da zai kula da ita sosai can cikin zuciyarshi kuma wani abu yaji yazo ya tokare mashi wuya...tunda daddy ya ambaci har zuwa lokacinda zata bar makarantan yaji wani irin sanyi ya kamashi...ashefa watarana gama karatun zatayi ta koma garinsu koh?..shi wlh sam baya kawo hakan a cikin ranshi...baisan ko sbd yanxu yana son kasancewa tarea ita ba amma sam tunanin haka bai taba zuwa mashi ba..yanxu kuma da daddy ya fada saiya tuna mashi cewa watarana da gaske zata bar college dinshi dama kano gaba daya kuma hakan na nufin bazai sake ganinta ba har abada...tunanin hakan saida yasa gabanshi yayi mummunan faduwa..to meyasa bayason rabuwa da ita?..meyasa a kullum yakejin sabbin al’amura gameda ita?..meyasa kuma idan ya ganta da wani yakejin kaman ya rataye kanshi sbd kunci?..for sure zuwa yanxu yasan kishinta yake saidai ko kusa bayaso yayi admitting yana sonta sbd hakan na nufin wargajewar abubuwa da dama a tare dashi..yayi nisa cikin tunani har baiji lokacinda daddy ya mike yana mishi mgn ba...saida ya dafa shoulder dinshi snn firgigit ya dawo hayyacinshi...daddy ya zuba mashi ido sosai yana kallon yanda duk yanayinshi ya sauya lokaci guda...bai tambayeshi dalilin hakan ba sbd a ganinshi ba huruminshi bane dan haka yayi mishi sallama yace zasu wuce Gombe...Bobby yayi mashi rakiya har inda motocinshi suke bayan ya sallami su Aysha ya shiga motar suka fita daga asibitin...Aysha kuma kai tsaye ta bishi office dinshi sbd mgnr changing posting da yace zaiyi mata.
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba... masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
30
Kallonta kawai yakeyi tunda ta shigo office din zuwa yanxu...duk yanda yaso ya dauke idonshi a kanta kasawa yayi...baisan meyasa yakejin wani new feeling tattare dashi ba...baisan meyasa mgnr daddy ya tsaya mashi a rai ba..abu daya daya sani shine ko kusa bayason rabuwa da ita..baiki ta dawwama tana karatu a FCNM ba sbd ya dinga samun ganinta kullum amma saidai sam hakan ba mai yiwuwa bane...sanin kanshi ne hakan bazai ta6a yiwuwa ba koda a garin ga6a ga6a suke kuwa...watanni kadan da ya tabbata basu kai shekara ba suka rage mata ta gama karatunta and this means watanni kadan ya rage masa a tareda ita..watanni kadan ya rage masa kafin ya dena ganinta har abada tunda shidai yasan nor matter the situation bazai ta6a kai kanshi Gombe ba balle watarana yace zai nemeta su gaisa tunda ya shiga garinsu...gaba daya wadan nan tunanin sun cika mashi zuciya sun kuma hanashi sukuni...Aysha da taga idanunshi ne kadai a kanta amma mind dinshi is elsewhere ta dan buga table dake gabanshi tace"Sir am talking"..da sauri ya lumshe idanunshi kafin kuma ya budesu a kanta yanayi mata kallonda zata iya rantsuwa da Allah tunda suke bai ta6ayi mata irinshi ba...voice dinshi can kasa yace"what happened?.."narkewa tayi tana wani kallonshi kasa kasa tace"sir kace fa idan nayi two weeks zaka canxamin posting"...dan wara idonshi yayi a kanta kafin yace"then ki dawo office dina"..ta wani turo baki tace"nidai no dan Allah..cewa fa kayi duk inda nakeso zaka kaini?.."gyara zama yayi still yana kallonta yace"to ina kikeso?.."da sauri tace"eclamptic ward nakeso naje nayi two weeks..the remaining two weeks kuma sai inyisu a Ante Natal Clinic"...gyada kai yayi alaman ya gamsu kafin yace"zakije inda kikeso but on one condition"...da sauri tace"meye condition din?.."yace"bazaki shiga harkan kowane doctor ba a wurin..infact bama doctors kadai ba kowane staff indai namiji ne i want u to stay far away from him"..da sauri ta shiga gyada kai tana murmushi tace"bazan shiga harkan kowaba wlh..aini bana da interest kan doctors ko health workers sbd son matan su yayi yawa..besides inama da wanda zan aura"..fuska a tamke yace"to waya tambayeki?..nace maki inason ji ne?.."dan turo baki tayi tace"to kayi hakuri nidai"..yace"tashi ki barmin office"..ta marairaice tace"sir posting dinfa?.."yana nuna mata kofa yace"i said out"...maimakon ta fita saita fara bubbuga legs dinta a qasa zata fara mishi kuka tace"toba kai kace zaka canxamin idan ma nutsu ba?..alqawari fa ka dauka"...kallon yanda take tale baki yayi kawai sai ya saki murmushi hade da girgiza kai...wnn yarinya shidai bai ta6a ganin irinta ba wlh...ita kuwa kuka ta fara na karya kafin ya dakatar da dariyan da yakeyi yace"da nace saikin nutsu ai ba nutsuwan kikayi ba..yanxun fa kika gama min rashin kunya a nan"...ta wani zaro ido tana cewa"rashin kunyan me nayi?.."fuska a dan daure yace"kikace baki son doctors da health workers..sbd tsabar rashin kunya hadda cewa kinada wanda zaki aura"..if u see yanda ya karasa mgn face dinshi daddaure zakayi tunanin bashi ne ya gama daria a while ago ba..abun yayi mashi ciwo da har ta iya bude baki ta wani ce mishi tanada wanda zata aura?..sai kace cewa yayi shi zai aureta?...ganin yanda ya sake dinke fuska sai tayi kasa da murya tace"to am sorry"..a takaice yace"naji..tashi ki tafi"..kaman zata tashi sama haka ta dauki jakanta ta fita daga office din nashi rai a 6ace tanata faman bambami ita kadai...shi kuwa tana fita ya kifa kai da table din gabanshi ya shiga sauke numfashi.
Washegari haka tazo office din nashi fuskan nan cunkus dashi kaman bata taba daria ba...sbd presence na Dr Aslam yasa bai nemi jin dalilin fushin nata ba yayi mata posting dinta kawai ta tafi...ranan har ya bar hospital din bai sake sanyata idonshi ba...washegari ma same thing happens kuma har ward din da take yaje bai sameta ba..duk jinshi yake wani iri da bai samu ganinta ba...a haka suka cinye satin nan tas bai sake ganin Lamido ba...damuwan da ya shiga a dalilin haka har mamaki yake bashi...yaudai yayi alqawarin dukma ina take zuwa ta 6oye idan ta ganshi sai ya nemota tunda ya tabbata zai iya samun matsala wajen bacci matukar bai sanyata a idonshi ba...cikin toilet dinsu aka ganota wai ashe tana hangoshi ya taho sai tayi wuf ta fada bandaki kuma bazata fito ba har sai ya fita..yaudai asirinta ya tonu dan har office dinshi yajata snn yace ta zauna suyi mgn..idanunshi a kanta kaman yau ya fara ganinta yace"why are u doing this?.."dan turo baki tayi tace"ba kaine ba"..yace"me nayi?.."ta sake turo bakin batace komai ba..shi kuma ajiyar zuciya ya sauke mai karfi kafin yayi lowering voice dinshi sosai yace"to kiyi hakuri"...dagowa tayi ya kalleshi da mamaki...ya sake cewa"kinji?.."murmushi ne ya kwace mata ganin yanda ya maida face dinshi abun tausayi...murmushin shima ya saki mai kyau yana kallon dimples dinta da yakejin kaman ya saka finger dinshi a wurin...ya sake yin kasa da murya yace"kin hakura?.."tace"eh mana..amma zaka denamin masifa koh?.."kallonta ya tsaya yi for some minutes kafin ya sauke numfashi yace"idan kin nutsu kin dena aikata abunda zanyi maki masifan ba?.."murmushin dai ta kara saki tareda fadin"na dena".
Bayan sati hudu...
Tuni sun gama posting dinsu sun koma makaranta...’yan year 3 su besty kenan tuni suma sun rubuta Hospital Final exam dinsu wanda sukayi passing sune suka fara rubuta council exam cikin satin nan...gaba daya Aysha ta zama wata iri daga ita har Billy ba karamin missing Sa’eed suka fara ba tun ma kafin ya tafi...kuka kuwa yana shanshi dan kullum ne idan suka hadu sai anyi mishi kukan nan hadda Billy data kasance abokiyar rigimarshi...shi kanshi shima ji yake kaman yayi kukan amma bazaiyi ba sbd namiji da dauriya aka sanshi amma only Allah knows yanda yakejin zafin rabuwa da zaiyi dasu...ranan Thursday bayan ya fito daga exams yaje hostel ya kwashesu suka fita wai yanaso su ragema juna radadin rabuwa da sukeji...duk inda yasan suna so saida ya kaisu including market da Lamido bata da burin da ya wuce ta shiga kasuwa a kano idan ta koma Gombe tayita bada labarin taje kwari taje sabon gari taje singa taje wambai taje bakin asibiti saidai wnn karon yawon sam baya masu armashi as kowa yanada damuwa cikin ranshi...a takaice sun shafe almost 3 hours suna abu daya kafin daga bisani ya saukesu gidan Hajia itama kuwa hadda dan kwallarta wai ta kusa dena ganinsu tunda Sa’eed zai tafi...kuka sosai sukasha a gidan nata kafin ya sake daukansu sai hostel dinsu..a bakin hostel din ma sun kwashi lokaci mai tsayi yanata aikin rarrashi da basu baki amma har suka rabu baiga alaman zasu dena kuka ba...the next day which is friday ranan sukayi final exam ma’ana sun gama da council saura waiting results kuma...ranan ma haka suka hada kai sunata faman kuka a cikin makaranta har mutane na kallonsu...saida akayi da gaske snn aka samu suka daina kukan yayi musu rakiya da kanshi har cikin hostel dinsu.
Washegari Saturday tun safe Bobby ke kiran wayarta sbd saqo da babanta ya aiko mata dashi amma bata dauki waya ba...saida ya kiraya kusan sau shida snn yayi sa’a ta dauka...kafin yayi mgn Billy tace"sir nice..batada lafia ne bazata iya daukan waya ba"...zaro idanu yayi sosai hankalinshi a tashe sosai yace"meya sameta?.."a takaice Billy tace"fever.."yace"kun kaita clinic?.."tace"sir kasan halinta ai..taki yadda"...da sauri yace"kice mata nace ku sameni a clinic yanxun nan"..Billy ta amsa da"toh.."snn ta ajiye wayar tana duban Aysha da tun daxu ta kudundune cikin bargo ko oxygen na kirki bata shaka...as usual sai da kyar da sidin goshi ta samu ta mike suka tafi clinici din...tun kafin su shiga Bobby dake zaune cikin motanshi ya hangosu..gabanshi yaji ya fadi da yaga situation da take ciki dan ko tafiya ma da kyar take yinshi ga wani irin haske da yaga ta kara tun daga nan inda yake...bude motan yayi kawai ya fita kafin su karasa ya iskosu hankalinshi a kanta yace"kin tabbata only fever ke damunta?.."Billy tace"maybe baza’a rasa headache ba tunda kuka taita yi har yasa mata zazza6i"..kallonta kawai yayi kamar zai tambayi dalilin kukan sai kuma ya fasa...Billy ta sake cewa"sir ciki zamu shiga?.."girgiza kai yayi hankalinshi gaba daya na ga Aysha data samu wuri ta zauna tana sauke numfashi yace"i think saidai muje hospital sbd inaso ayi mata test shi kuma lab din nan ciki sun tashi..ki sata a mota kawai"...ba musu Billy ta sake kamata zuwa inda motarshi yake ta sakata a back seat snn ta rufe kofar...karasowa yayi shima ya shiga yana dubanta yace"ke bazaki jeba?.."girgiza kai Billy tayi tana murmushi tace"no sir..inaso inyi mata girki kafin ku dawo"..gyada kai kawai yayi ya rufe glass dinshi snn ya tada motar suka tafi Billy ta bisu da kallo tana fadin"love birds".🤪
Kai tsaye Freedom ya nufa da ita...yana shiga ciki ko parking daidai bai tsaya yi ba ya bude motar da sauri ya fita zuwa cikin asibitin...few minutes later ya dawo tareda wasu nurses mata guda biyu suna tura trolley bed...bude motan yayi matan suka taimaka mata ta fito suka dorata kan trolleyn snn suka shiga ciki...direct office dinshi suka kaita suka dorata kan bed da yake scanning da other examinations akai snn suka fita...maida kofa yayi ya rufe bayan sun fita ya shiga takawa a hankali zuwa inda take...idanunta yaga a kulle amma still hawaye basu dena fitowa daga cikinsu ba...hannu yakai forehead dinta yaji akwai zafi sosai dan haka ya koma seat dinshi yayi using landline ya kira lab yace a kawo mashi sample bottle...babu wasting of time aka kawo mashi..ya bude wani drawer nan cikin office din nashi ya dauko 5cc syringe da tourniquet kana ya koma inda take...hannunta ya kama a hankali ya daura tourniquet din a jiki aikuwa da sauri ta bude idanu tana kallonshi..ya wani hade rai tareda rike hannun nata da kyau dan yasan tsaf zata iya sawa yaji mata ciwo snn ya soka needle din cikin vein dinta...wani irin kara data saki saira kiris ya ya zare needle din daga jikinta sbd shiganshi da karan nata yayi...haka tana buge buge tana kuka ya dauki sample din nata ya zuba cikin sample bottle da aka kawo snn ya bada yace mp/widal yakeso ayi mashi yanxun nan...bayan fitar mutumin yayi checking vital signs dinta yaga all normal snn ya koma seat dinshi ya zauna waiting for the results...ana kawo mishi ya duba yaga da akwai malaria kadan babu typhoid dan haka ya rubuta drugs da injection da zaiyi mata ya bada aka amso mashi a pharmacy...saida ya gama withdrawing alluran da zaiyi mata snn ya karasa inda take yana tunanin ta yanda zaiyi alluran nan ba tareda ta tara mishi jama’a ba..kallonta kawai yakeyi yanda bacci ya fara daukanta yasan yanxu yana tashinta tayi ido hudu da allura ba karamin rikicewa zatayi ba...hannu yakai forehead dinta ta bude idon a hankali...tana ganin injection a hannunshi ta mike zaune da sauri idonta na cikowa da hawaye tace"Allura zakaimin?.."shiru yayi yana kallonta duk sai yaji ta bashi tausayi yanda tayi tambayar...zaunawa yayi kusada ita yana kallonta a hankali yace"bakya so?."da sauri ta hau gyada kai tana goge hawayenta...yace"amma Aysha alluran ne kadai zai saukar da wnn temperaturen naki da wuri?..bakiji yanda jikinki yayi zafi ba?.."ta shiga yarfa hannayenta hawaye na ambaliya fuskanta tace"nidai banson allura"...kallonta yacigaba dayi not knowing what to do or say...harga Allah yafison ya mata allura sbd fevern zaifi sauka da wuri amma kuma tausayi take bashi da wnn kukan da takeyi...lalla6ata ya shigayi da bata baki amma sai botsarewa take wai ita baza’a mata allura ba...nan kuma yayi abunda bayaso wato forcing dinta dan matseta yayi yayi mata alluran tanata rizgar kuka tana ihu bai saurara ba saida ya gama...sai kuma ya hadata da jikinshi ganin yanda legs dinta ke trembling murya can kasa yace"am so sorry"..kuka kawai take har breathe dinta yana kamar zai dauke...zaunar da ita yayi kan gadon shima ya zana gefe tareda cupping fuskanta yana kallon cute face dinta yace"stop crying mana..yanxu fevern zai sauka kinji?..am sorry"...kasa ce mishi komai tayi sai hawaye da sukaki tsayawa...Bobby ya lumshe ido ya bude shima kaman zaisa mata kukan yace"nace fa am sorry Aysher..kukan ya isa haka mana"..hannu takai tana goge tears din nata baisan lokacinda ya daga hannunshi ba kawai sai ganinsu yayi akan fuskanta yana goge mata tears din...saida ya gama snn ya sake kasa da murya yace"zakici abinci?.."girgiza mishi kai tayi tana turo baki shi kuma ya saki murmushi kafin yace"toki kwanta abinki..idan fevern ya sauka sai in maidaki hostel"...batayi masa musu ba ta juya masa baya ta kwanta shi kuma ya sake lumshe ido yanajin wani abun mai kamada magnet na kokarin janshi gareta...ganin ta cure legs dinta wuri daya ya janyo kujera ya zauna bayan ya gyara mata kafan sai ya tallabi cheeks dinshi yana kallonta...ta dauki almost an hour tana bacci shi kuma yana nan zaune inda yake yana kallonta..he just can’t take his eyes off her baisan meyasa ba...he drives pleasure staring at her..har wani smile yake saka akai akai ba tareda saninshi ba...a hankali yaga ta fara mosti kaman zata bude ido saita fasa ta wani turo baki inda kasan idonta biyu...daria sosai ya saki ganin yanda ta turo bakin..ya lumshe ido tareda kai hannunshi a hankali ya aza kan lips din nata sai kuma ya janye da sauri yana yarfa hannun idanunshi a kanta sbd wani abu da yaji kaman electric shock...sake juyawa tayi nan hulan dake kanta ya zame tareda faduwa kasa black silky hair dinta da bata cika yima kitso ba ya bayyana...saida breathe dinshi ya dauke na wucin gadi ganin gashin nata...da dadewa yasan tanada gashi tunda ya ta6a ganin kan nata amma sai yaga kaman daga wancan lokacin zuwa yanxu an kara mishi tsayi da baqi dan har wani daukan idonshi yakeyi...sake lumshe idonshi yayi a karo na ba adadi kawai sai ya mike daga wurin ya koma kan sofa ya zauna because abubuwan nan da yakeji bana lafia bane ya sani...tsaf zai iya mancewa ya aikata abunda daga baya zaizo yana regretting so it’s better he leaves kafin azo a samu matsala...haka yayaita zaune yana duban agogo saida tayi baccin 3 hours cur snn ta tashi tana wani yatsine fuska kaman wanda taga poopoo...mikewa yayi daga inda yake zaune ya karasa kusada ita yana dubanta with concern yace"how are u feeling now?.."a hankali tace"da sauki..inajin yunwa"..murmushi ya saki tareda sunkuyawa ya dauko hulanta dake kasa ya mika mata yana cewa"ki shiga bathroom ki farayin brush kafin a kawo abincin"...batayi mishi musu ba ta sauko daga gadon zuwa bathroom dinshi...da mouth wash tayi amfani da wanke bakinta snn ta dauro alwala ta fito rikeda hulan nata a hannu...kallon gashinta daya sauka shoulders dinta yayi yace"ya kika cire hulan kuma?.."turo baki tayi ta mayar da hulan batace komai ba...carpet ya shimfida mata da kanshi snn ya dakko jilbab dinta daya cire mata daxu shima ya mika mata..amsa tayi ta zura ta tayar da sallah shi kuma ya koma ya zauna waiting for abincin da yayi mata order yazo...tana idar da sallah ta sake dubanshi tana kwabe fuska tace"yunwa fa nakeji"...murmushi ya kara saki yace"Aysher ki kara hakuri mana..nayi ordern abincin ne and nasan suna hanya inshaAllah"...gyarawa tayi zata kwanta nan kan carpet din yayi sauri tasowa daga inda yake yace"karki kwanta kasa"..ba musu ta mike ta koma gado...bayan few minutes akayi delivering abincin nata dan haka ya mika mata gaba daya snn ya zauna yana kallonta...ita kuwa cik abincinta take hankali kwance sai kallon dimples dinta dake lotsawa idan tana tauna abincin yake...ba kanta ya fara ganin dimples ba amma nata kullum shi yake tempting dinshi yaji kaman yaje yasa finger dinshi a wurin...tana gama cin abincin tasha drink din kadan snn ya bata drugs suma tasha badon tanaso ba...saida yaga ta nustu ta dawo hayyacinta snn yace"can we talk now?.."kallonshi tayi batace komai ba...shi kuma yana kallon eyes dinta da sukayi luhu luhu sbd kukan da taci yace mata"what happened to ur eyes?.."raurau tayi da ido zatasa mishi kuka yace"I didn’t ask u to cry...cewa nayi meya samu idonki?.."tana kwabe fuska tace"kuka nayi"..."kuka?.."ya maimaita abunda ta fada kafin yace"me aka maki kikai kuka da har ya sanya maki zazza6i haka?.."lumshe ido tayi nan hawayen dake ciki suka silalo kan fuskanta tace"Bestie ne zai tafi"...cak yaji komai nashi ya tsaya including breathe dinshi...nan take face dinshi ya sauka murya a dakile yace"sbd shi kike kuka knn?.."cigaba da kukanta take tace"tafiya fa zaiyi ya barmu...ba sun gama council ba"..a kufule ya mike zuwa inda ya ajiye wayoyinshi yace"sai ki bishi ai"...harara ta watsawa bayanshi tana turo baki...ya dauki wayoyinshi daya ajiye nan wurin snn ya kama hanya zai fita yace mata"fito mu tafi"...da kallo kawai ta bishi tana mamakinshi..har yanxu bata bar mamakin yanda he can change forms in a blink of an eye ba..he can be nice for a second and become annoying the other second...shiyasa kwata kwata bata gane mashi...mikewa tayi ta zura jilbab dinta snn ta fita daga office din..a bakin kofa ta sameshi yana ganin ta fito yayi locking office dinshi snn ya wuce parking space...motanshi ya bude ya shiga itama tana karasowa ta shiga sai turo baki take...bayan sun dauki hanya ta dan saci kallonshi ganin yana driving..tunda suke bata ta6a ganin ya tuka kanshi ba saidai yayi d’urum a baya mota ana driving dinshi yau kuma wane salon ne yasa shi driving din oho?...motan yayi tsit ba abunda kakeji sai sanyin ac dake tashi...wayanshi dake ajiye kan dashboard ne ya fara ringing...yayi connecting Bluetooth snn ya daga..daga daya 6angaren da igbo Mummy tace"Bobby where are u?.."shima da igbo din yace mata"ina kan hanya Mummy..what happened?.."tace"jikin yarinyar nan ne naga kaman gaba yakeyi wlh..ko asibitin zamu kawota?.."yace"aah Mummy gani nan zuwa gidan yanxu"..Mummy tace"to kayi sauri dan Allah"..yace"toh.."snn ta kashe kiran...Lamido data kasa kunne tana jinsu bata fahimci komai a zancen nasu ba tace"kilan mamarshi ce"...yaji abunda ta fada sarai kulata ne kawai baiyi don a yanda ta kular dashi tsaf zai iya kwada mata mari wlh...haka ta ringa baza ido tana kalle kalle har suka iso kafar gidansu...maimakon ya shiga da motar ciki sai yayi parking a nan waje ya bude motar ya fita ya wani sake hade ranshi yace"saura kuma ki fito daga ciki kiga me zanyi maki"...tabe baki tayi ta kauda kai shi kuma ya juya ya nufi gate..kwankwasawa yayi mai gadi na lekowa yaga shine ya bude mishi da sauri ya shige cikin gidan...Lamido na ganin ya shiga ta bude motar ta fito tana karema gidan nasu kallo tace"ai wlh saina fito na bawa idona abinci"..sake juyawa tayi tana kallon zabgegen mansion din tana girgiza kai tace"gaskia mutumin nan me kudi ne..ji gida kaman ba’a Naija ba ni Aisha"..karasawa tayi jikin gate din ta shiga lekawa ta wata ‘yar karamar kofa kamar daga sama taji an danne mata horn ta bayanta...a rikice ta matsa daga wurin tana kallon motar dake kokarin shiga gidan sai tayi saurin komawa inda motarshi yake kafin ta shiga taji ance"yammata"..juyawa tayi tana kallon matar duk sai taji kunya ya kamata tana leka musu gida..ta shiga washe baki tace"ina..ina yini"..aunty sumy ta bude mota ta fito zuwa inda take tana kallonta da fara’a tace"lafia lau yammata..zaki shiga ciki ne?.."da sauri tace"aah tareda proprietor muke shine nake jiranshi"..ta karasa mgnr duka daburce kaman matsoraciya...aunty sumy ta saki smile jik tareda Bobby suke tace"to mu shiga daga ciki mana saiki jirashi a can"..tun kafin ta rufe baki Aysha tace"aa ba saina shiga ba wlh..yace kar in shiga"..dafa shoulder dinta aunty sumy tayi tace"karki damu bazaiyi maki komai bafa..aini nace ki shiga sbd haka muje plss"...narkewa tayi tana kallonta kafin tayi mgn aunty sumy ta sake fadin"please!.."haka nan ta bita suka cikin gidan ba don tanaso ba...mai gadi taba key ya shigo mata da motar snn suka wuce...matar ce tayi mata kwarjini wlh amma ita sam bata son shiga yazo yana wulakantata...suna shiga compound ta ware idonta tana kallon lafcecen compound din dake zube da uban motoci kaman na siyarwa..cikin ranta tace"babban burin inyamuri a dunia kenan..a danqara gida snn a hau motoci"..ganin bata daga kafa aunty sumy ta kama hannunta suka nufi entrance...basu samu kowa central parlor ba dan haka direct ta nufi parlon Mummy da ita...Mummy na zaune da Ilham akan cinyarta shi kuma yana rikeda hannun ilham din yanayi mata alluran jijiya..yarinyar tayi luf jikin Mummy sai sauke numfashi take...saida suka isa ciki aunty sumy ta saki hannunta tana doka wani uban murmushi tace"Mummy ga bakuwa na kawo maki"...dagowa Mummy tayi tana kallon yarinyar da kanta ke kasa kafin tace"to bismillah zauna kinji bakuwa"..karasawa tayi ta zauna a hankali har yanxun kanta yana kasa...Bobby da sai yanxun ya gama mata alluran yana dago kanshi yayi ido biyu da ita tana zaune kusada aunty sumy sai wani sussunne kai take...cikeda mamaki sosai yake kallonta yace"ke bakida hankali ne?..waya baki izinin shigowa gidan nan?.."juyawa Mummy tayi tana dubanshi tace"ka santa ne?.."dauke kai yayi yana huci ya kasa cewa komai...tambayoyin nan ne bai shirya amsawa ba shiyasa yace tayi zamanta cikin mota amma sbd tsabar rashin ji irin nata saida ta fito...yanxu shknn yasan ya shiga uku da tambayoyi a wurin su Mummy...ganin bazaice komai ba aunty sumy tace"ganinta nayi fa a cikin motarshi shine na tambayeta tace tare dashi suke amma yace ta zauna nan cikin mota karta fito"..juyawa Mummy ta sakeyi ta kalleshi sai taga ya sake hade rai yana muzurai sai ta maida dubanta ga Aysha da har yanxun kanta ke a kasa lokaci daya ta saki wani murmushi dan tasan zaiyi wuya idan ba itace Lamido ba dan haka tace"yammata meye sunanki?.."a hankali tace"Aysha"..Mummy ta shiga gyada kai tace"MashaAllah Aysha me babban suna ce ashe?.."daga kai kawai Lamido tayi tanajin kamar ta saki fitsari a wando sbd yanda takejin idanun Bobby nata kaiwa da kawowa a kanta..ko baa fada ba tasan kallonta yake...Miemie ce ta shigo parlon rikeda tea data hadoma Ilham..tana karasowa ta mikawa Mummy snn ta zauna tana kallon Aysha dake zaune tace"Mummy bakuwa mukayi?.."Mummy da har yanxu bata bar smiling ba tace"wlh bakuwa mukayi Miemie”..Miemie ta matsa kusada ita tace"sannu da zuwa ina yini?.."dan dagowa Aysha tayi ta kalleta kafin tace"lafia lau"..wara ido Miemie tayi da taga face dinta tace"laa Mummy ai na ta6a ganinta a FCNM wall..."bata samu karasawa ba sbd wani kallo da Bobby ya watsa mata ba shiri taja bakinta yai tsit..aunty sumy da tun daxu take kallonshi ganin yanda duk yabi ya takura kanshi kawai ta saki murmushi..ita bata ta6a ganin mai hali irin na Bobby ba wlh..kiri kiri ga abu kana sonshi amma wai kake kaiwa kasuwa?...mikewa Mummy tayi ta ba aunty sumy tea din Ilham tace"ki bata tasha"..snn ta karasa inda Malama A’ee take zaune ta kama hannunta ta mike tsaye snn ta jata zuwa dakinta tace"tashi muje mu gaisa ‘yata"...daga haka suka shige bedroom din Mummy..Bobby yabisu da kallo kaman idanunshi zasu koma jikin kofar dakin...hankalinshi yaji ya tashi kardai Mummy taje ta fadama yarinyar nan abunda zaisa ta rainashi fa..gabanshi har wani faduwa yakeyi wlh...kaman wanda aka tsikara yabi bayansu zuwa dakin da sauri kamar zai tashi sama...
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
31
Yana shiga ya marairaicewa Mummy yace"Mummy dan girman Allah mu tafi..bama ta da lafia shine na kaita asibiti"...murmushi Mummy tayi kafin tace"to ka jiramu a waje yanxun nan zata fito"..da sauri ya canxa yare yace"Mummy me zaki fada mata?.."da yaren itama tace"akwai abunda kake 6oyewa wanda bakaso ta sani ne?.."girgiza kai yayi da sauri duk yabi uzzurawa kanshi babu gaira babu dalili...kofa Mummy ta nuna mishi alaman ya fita haka ya juya ya bar dakin yana sake sake...bayan fitarshi Mummy ta dawo da dubanta ga Aysha tace"zauna mana Aysha"..maimakon ta zauna saita risina har kasa tana kallon kasan tace"Ina yini"..Mummy ta amsa da"lafia lau..ya karatu?.."tace"Alhamdulillah"..Mummy tace"to dawo nan ki zauna tunda mun gama gaisawa"..ba musu ta mike ta zauna inda ta nuna mata...kallonta kawai Mummy keyi taji ta shiga ranta sosai...irin wnn kyau da take dashi ai ba Bobby ba kowane namiji ma yana iya samun matsala idan aka jarabceshi da qaunarta...tana cigaba da dubanta tace"da gaske bakida lafia?.."kai kawai ta iya dagawa...Mummy tace"to Allah ya baki lafia..yanxu bari a kawo maki abinci kici"..da sauri tace"wlh mama na koshi banajin yunwa"...Mummy ba girgiza kai tace"aah dole kici wani abu"..daga haka ta kwaloma Miemie kira...tana shiga Mummy tace"jeki kawo mata abinci"...kafin ta fita Aysha tace"wlh ban dade da cin abinci ba banajin yunwa"..Mummy tace"to shknn dukda haka dai ko tafiya sai kinyi dashi...Miemie ki samu abu ki zubo mata pepper chicken sai ki hada mata da lemo"..ba musu Miemie ta fita don yin yanda aka sata...suna nan zaune ta dawo da wani bag mai kyau datasa pepper chicken din a ciki...Mummy tace"to ki rike mata saiki rakata waje dashi"..a hankali tace"toh.."snn ta juya ta fita...mikewa Mummy tayi zuwa wadrobe dinta ta dauko wasu turaruka masu kyau guda biyu ta zuba mata su cikin dan karamin jaka mai kyau snn ta bude drawernta ta dauko two sets na sarkoki suma masu azabar kyau duk ta zubasu cikin jakan...hajia indo dai tana zaune kai a kasa kamar munafuka..hannunta Mummy ta kama suka fita daga dakin...Bobby daketa safa da marwa ya juya yana kallonsu kamar idonshi zasu fadi kasa..saida daria ya subucewa Mummy sbd ganin yanda duk yabi ya addabi kanshi ba gaira ba dalili..shi kuma ya wani kwabe fuska da igbo yace"Mummy me kike ce mata dan Allah?.."bayan ta staida dariyarta tace"gata nan ka maidata kuma wlh ban yadda kayi mata fada ba Bobby..idan kayi kuma zai dawo kunnena"..daure fuska kawai yayi baice komai ba...aunty sumy ma ta fito daga dakinta rikeda wani dan box mai kyau tana karasowa ta mikama Aysha tana murmushi tace"to ga wnn Aysha..i hope zaki sake kawo mana ziyara?.."murmushi kawai tayi bata iya amsawa ba duk sun sata jin wani iri wlh..sunada kirki sosai unlike Proprietor da sukayi hannun riga da kirki...ta amsa abun tayi godia..Mummy tace"ai zai sake kawota mu gaisa"..aunty sumy tace"kwarai kuwa..idan ma bai kawota Mummy da kaina zanje har hostel dinsu in dauko mana ita"..shidai yana fsaye fuskan nan a tamke baice musu kala ba...after long surutunsu finally ya samu aka bashi ita suka fita..Miemie ta rakata har mota da kayanta ta zuba mata su back seat snn ta zaga inda take da nufin tayi mata sallama Bobby dake cika yana batsewa ya wani 6alla mata harara tareda fadin"bar nan"..ba shiri ta koma ciki tana turo baki...tada motar yayi da wani irin gudu suka bar layin nasu..Ita dai a tsorace take sai rarraba idanu take...suna hanya wayanta ya fara ringing ganin wanda ke kira sai tayi silencing wayar taki dauka sbd gudun masifanshi...sake kira akayi ta kuma sawa a silent shi kuma ganin batada niyyar dagawa yakai dubanshi kan wayar dake cinyanta sai yaga baby boo kan screen aikuwa ya sake dinke fuskanshi tsaf yana sake figan motan a guje kmr zai tashi sama...gani take kaman tsoron dunian nan a kanta ya sauka wnn uban gudun da yake idan yaje ya watsar dasu fa?..bata dai ce masa komai ba har suka isa gate din hostel...ya cire mata lock ba tarefa ya kalleta ba yace"fita"..da sauri ta kama kofar zata bude sai kuma taji yace"bana hanaki kiramin wani besty idan muna mgn ba?..ke wato bakyajin mgn koh?.."da sauri tace"kayi hakuri"..yace"sbd kinga banaso shiyasa kike fada wato koma me zanyi inyi koh?.."ta dan lankwasa wuya tace"sir nace fa kayi hakuri"...dauke kanshi yayi daga gareta yace"fitamin daga mota"..ta sake langabewa tana kwabe fuskanta tace"sir i said am sorry mana..kayi hakuri bazan kara ba"...juyo da kanshi yayi yana kallonta yace"idan kika kara inyi maki me?.."hannu takai tana shafa cheeks dinta kafin a hankali tace"ka mareni"..murmushi kawai ya saki tareda jinginar da kanshi jikin kujera..dama yasan fushin ma ba wani iyawa zaiyi da ita ba..itama murmushin ta saki tace"sir kacigaba da smiling dan Allah..yana maka kyau"..bude idonshi yayi ya zubasu a kanta..wasu sabbin al’amura yakeji suna zagayawa cikin jini da tsokarshi...mikewa yayi daga inda ya jingina still yana dubanta ina serious note yace"da gaske banason jin wani besty ko waye a bakinki..banaso idan kuma kika sake kiramin shi muna mgn marinki zanyi kaman yanda kika fada"..murmushi take tace"bazan ma kara ba inshaAllah"..yace"shknn u can go..and make sure kinsha drugs dinshi akan lokaci kuma banda skipping idan ba haka ba kuma alluran da bakiso shi za’a kuma yi maki"...bude motar tayi ta fita still tana murmushi tace"aah banason allura zansha maganin..saida safe"..kanshi kawai ya iya daga mata snn ta juya ta tafi bayan ta kwashi kayanta dake baya...saida yaga shiganta ciki snn yaja motarshi ya kara gaba.
Tun daga wnn ranan suka sake dinkewa abunsu...tanajin magananshi sosai and hakan ba karamin farantawa Bobby yake ba..zuwa yanxu ya gama admitting ya kamu da soyayya..soyayya kuma na bafulatana data fito daga jihar Gombe..what a miracle..tunda yake bai ta6a tunanin zaiso wata mace ba ballantana ‘yar Gombe amma ita sai yaga kaman turota akayi dan tazo ta wargaza duk wani tanadi da alqawura da yayima kanshi...shida yake shiga college only Thursdays da Fridays amma yanxu kusan kullum sai ya shiga sbd kawai ya samu ya ganta domin ganin nata shine kadai samun nustuwarshi...yanayi mata sonda shi kanshi bai tunanin yana yiwa kanshi amma har yanxu ya kasa nuna mata dukda yasan wani lokacin actions dinshi suna nunawa sbd kasa controlling kanshi da yake amma ita kota fahimta bata ta6a nuna mishi ba...abu biyu dake damunshi sune na farko amanarta da mahaifinta ya bashi yana gudun kada mgnr sonda yake mata ya fita shi kuma mahaifinta yaga kamar bai rike mashi amana ba tunda har shi da kanshi zaice yana sonta..sai na biyun kuma shine Gombe..bayan kasancewarta ‘yar Gombe muma tazo a bafulatana..har yanxu bai mance yanda ‘yan uwan dad dinsu fulani sukayi treating Mummy ba..shima yana tsoron kada yaje neman aurenta ace dan inyamura ne shi baza’a bashi ba..ga kuma su kansu ‘yan uwan daddyn da matukar zaiyi aure dole saiya nemi inda suke sbd su shige mishi gaba kan mgnr saidai sam baiji zai iya zuwa ya samesu ba..har yanxu yana nan akan bakanshi na babushi babusu amma kuma tayaya zai samu auren Lamido ba tareda sa hannunsu ba?..gaba daya ya zama wani iri yanxu ko abincin kirki baici..aiyukan nashi ka neman tsaywa suke cak sbd damuwar da yake ciki..har dan ramewa yayi sbd tunani..Mummy tayi tayi dashi ya sanar mata abunda ke damunshi amma kullum mgnrshi daya shine babu komai...ganin yana neman rasa nutsuwarshi yau dai ya yanke shawaran zaije ya samu Nur suyi mgn ko yanada solution da zai bashi...gashi itama yarinyar wahalar dashi takeyi these days baisan laifin da yayi ba duk ya kirata a waya bata dauka...hankalinshi ba karamin tashi yayi ba yau kusan 5 days knn baiji muryanta ba kuma bai ganta ba dan haka yake jin kanshi kaman mara lafia..baisan meyasa take mishi irin wnn ba..haka nan babu laifin zaune babu na tsaye saita dauke mishi wuta sai yayita binta yana lallashi snn zai samu kanta amma this time around yace bazai ske nemanta ba inyaso sonta yayi ajalinshi shima sai ya samu ya huta.
Yana shigowa College zuwa office din Nur da yace mashi yana jiranshi a ciki...da sallama ya shiga yana takawa da kyar sbd matsaloli da suka taru suka cika mashi brain...Nur na ganinshi ya mike ya koma kan sofa shima karasawa yayi ya zauna nan kusa dashi tareda jingina da jikin kujeran yana lumshe ido...Nur yace"kace zamuyi mgn i hope dai lafia?.."girgiza kai Bobby ya shigayi tareda bude idanunshi yace"ba lafia ba Nur..ina cikin damuwa"..gyara zama Nur yayi yace"to inajinka"..ajiyar zuciya Bobby ya sauke yana shakar iska da kyar yace"it’s about Lamido..i think..i think i’ve fallen for her"...dukda Nur ya dade da sanin yana sonta yayi mamaki sosai jin a yanayin daya fada mashi...kamo hannunshi Bobby yayi yana kallonshi da idanunshi da suka sauya kala muryanshi cikin raunin da Nur zai iya rantswa bai ta6ajinshi a ciki ba yace"i am in a serious mess Nur..na rasa nustuwata gaba daya..komai bayamun dadi..komai banajin dadinshi abu daya da yake keeping dina company shine tunaninta..zuciyata ta cuceni duk iya kokarina na ganin na kaucewa abunda nakeji abun yafi karfina Nur..bansan meya kamata inyi ba nasan yarinyar nan bazata ta6a sona ba"..yana rufe baki Nur da yaji asalin tausayinshi na ratsashi ya dafa shoulder dinshi yace"Man take it easy plss..idan kana wnn damuwan kana iya samun problem ka sani..nayi maka alqawarin i’ll help you in anyway possible dan inga ka samu soyayyarta..wnn matsalan nake guje maka shiyasa tun farko naso ayima tufkar hanci baka bani dama ba"..sake damke hannunshi yayi yace"yanxu na baka do your best plss..ka taimakeni before i loose my sanity..inajin zafi sosai duk lokacinda na ganta da wani..yanxu haka da nake mka mgn ko wayana bata dauka kuma bansan laifinda nayi mata..nasan kilan Allah yanaso yayi punishing dina ne kan abubuwanda nayi mata a baya amma wlh bada son raina bane..bansan meyasa ina ganinta raina yake 6aci har yasa nayi mata abubuwanda nayi ba"..rungumeshi Nur yayi cikeda tausayinshi sosai yace"it was all the love Bobby ganewa ne bakayi ba..tun daga ranan da tacemin kace baza tayi presentation ba nasan da akwai wani abu a ranka gameda ita..Lamido is a good girl..tanada hankali sosai and am sure ko bata soka yanxu ba watarana zata soka"...dagowa yayi daga jikinshi yana kallonshi with a wide smile jin abunda ya fada yace"nagode sosai Nur..thank u..kasan a da nayi tunanin sonta kake sai kuma daga baya naga ba haka bane"...Nur yace"well a gaskia bazan boye maka ba i once had a crush on her amma tunda ja fahimci kana sonta saina hakura sbd nasan sonda kake mata yafi wanda zan mata..kuma dakai tafi dacewa bada ni ba and inshaAllah i will do my possible best inga na hada wnn soyayyan..ba karamin matching couple zaayi ba kai da Lamido"...murmushi sosai Bobby yake wanda ya manta when last yajishi so lively haka...maganganun da Nur ya fada sai yajisu tamkar diamond da gold sbd tsananin dadinsu da yaji...cikin murmushin da yaki bajewa fuskanshi yace"thank u so much friend..u are really a friend indeed"...shafa kai Nur ya fara yana wani murmushin shakiyanci yace"gaskia ya kamata ayi saluting Lamido data canxaka haka?..yau Dr Bobby ne da godia haka ba kakkautawa?.."murmushin shima ya kara saki shi kanshi ya dade yana mamakin kanshi..ya dade yana mamakin yanda ya canxa ta 6angarori da dama duk kuma a dalilin Lamido...Nur dake kallon yanda yake blushing yace"amma wait..laifin me kayi ta dena daukan wayanka?.."da sauri Bobby yace"nima i dont know..haka nan ta daukemin wuta rabon dana samu peaceful sleep tun ranar dana ganta last..ina cikin damuwa sosai Nur ka taimakamin dan Allah..I really want to see her..na dade ban ganta ba"...wani murmushin Nur ya saki kafin yace"karka damu yanxun kuwa zaka ganta..let me call her"..yana fadan haka ya dauki wayanshi dake kan table ajiye snn ya nemo numberta yayi dialing..da sauri Bobby ya matso kusa dashi yana kallon wayan kamar zai ganta ne a ciki..Nur yasa a speaker nan kuma sukaji kiran ya shiga..tana dauka tace"Sir ina yini"..Bobby ya wani lumshe ido yanajin yanda muryan nata ke zagayawa cikin dukkanin systems dinshi..he missed her like crazy..jin muryanta kuma sai ya sake kwadaita mishi son ganinta..yasan yau idan bai ganta ba matsala zai samu gaba daya..he don’t think zai iya daukan rashin ganin nata anymore..he just can’t..he need to see her...idon Nur na kallonshi yana kallon yanda ya fada duniar shauki sbd jin muryanta yace"hajia Lamido manyan mata..ya studies?.."tace"Alhamdulillah sir dama inaso inzo wurinka akan mgnr malam Mukhtar"..yace"then kizo office yanxu dama nima nemanki nake"..tace"ohk gani nan"..daga haka Nur ya kashe wayar yana duban Bobby yace"she’s coming"..kai kawai Bobby ya iya daga mashi yana tunanin yanda zasu kwashe da ita...mikewa Nur yayi ya koma seat dinshi yana zama sai gata ta shigo office din sanyeda uniform dinta as usual da glasses dinta a ido...tana gama kulle kofa ta juyo zata nufi inda yake zaune kawai idanunta duka hango mata shi a zaune ya waniyi crossing hands dinshi yana kallonta kaman wani soko...dan daure fuskanta tayi ta dauke kai snn ta karasa gaban table din Nur tace"Sir i think zanje sai in dawo some other time"..da sauri Nur yace"amma why?.."bata amsa mashi ba ta juya da sauri zata fita Bobby ya mike da saurin shima yasha gabanta...ta dago tana kallonshi fuskan nan a kwabe tace"nifa wucewa zanyi"..mai mata bazan sai aikin kallonta da yake kaman ba gobe...matsawa tayi zatabi gefenshi ta wuce nan ma ya sake tare mata hanya kawai saita dago tana kallonshi kaman zatasa kuka...Nur da yaga wasan nasu ya fara daukan zafi sai ya mike daga inda yake ya ra6a ta gefen Bobby zai fita daga office din ya dan rankwafa saitin kunnenshi yace"Man karka raga mata wlh..make her fall for u"..yana gama fadan haka ya fice daga office din Lamido tabishi da kallo kamar zatasa kuka...sake matsawa tayi zata wuce shima ya sake tare mata hanyar...tayi kasa da kanta kawai tana turo baki kawai sai jin mutum tayi dab da ita dan har numfashinshi a jikinta ke sauka..ta matsa baya tana sake turo baki shima ya sake matsawa inda ta matsa din..ta sake taking two step backward shima yayi haka kawai saita shiga yarfa hannunta tace"sir ni me nayi?.."baice mata komai ba sai binta da yacigaba dayi har ta fada kan sofa..maimakon ya zauna kan sofa sai ya janyo table dake wurin ya zauna a kai yanda zaina kallonta da kyau..muryanshi kasa kasa yace"why are u ignoring my calls?..no why are u ignoring me?.."sake turo baki tayi tace"sir ni banyi ignoring dinka ba"..yace"shi kuma kin daukan wayana na meye?.."tace"ba komai"..kallonta ya tsayayi for like five minutes kafin ya sauie ajiyar zuciya ya sake yin kasa da muryanshi yace"nayi maki wani abun ne?.."ta girgiza kai...yace"then why all these?..why are u doing these?..if saboda na kwace maki rings dinki ne zan maido maki kayanki amma ki dena wahalar dani haka plss"...kallonshi tayi jin abunda ya fada kafin tace"nifa bakayi min komai ba..kawai naga mutane sun fara tunanin soyayya mukeyi shiyasa na dena kulaka"..diff yayi yana kallonta jin kalamanta...yace"yanxu sbd ana tunanin muna soyayya shine zaki dena daukan wayana?.."tace"to sir muda ba soyayya muke ba meyasa zamu ba mutane kofar da zasuyi tunanin soyayya muke?.."tana rufe baki yace"nina fada maki haka?..ko kinsan mind dina ne?.."dagowa tayi ta kalleshi da mamaki sai kuma ta kawar da kanta tana wani daure fuska tace"wlh ba soyayya muke ba"..cikin 6acin ran da yaji ya fara diran mishi yace"wai yaushe kika rainani ne haka?..kinsan zuciyata ne?..well idan baki saniba to let me tell you now..i love you..i love you with my whole heart kuma i want to marry u"..a rikice ta sake dagowa tana kallonshi taga yanda ya tsareta da ido kawai saita rufe fuska da hannayenta ta rushe da matsnancin kuka...hankalinshi yaji ya tashi sosai ga wani irin rauni da yakeji kawai saiya dafe goshi yana sauke numfashi..wai dama haka soyayyan yake ko kuwa nashi ne yake zuwa mishi da wann problems haka?..yana kokarin solving matsala sai kuma ga wani ya kawo kai sun taru suna neman fasa mashi zucia..ganin da gaske kuka takeyi yayi kasa da murya yace"yi hakuri i was kidding..bana sonki..amma seriously idan baki dena ignoring dinaba zaki sani cikin matsala wlh..koma meye ya faru I apologize and idan laifi nayi maki you are free to punish me amma ki dena bani wnn attitude din i beg of u plss"..dakatar da kukan tayi tana kallonshi hawaye sha6e sha6e a fuskanta tace"kace da wasa kake?.."da sauri yace"yea wasa nake..i never loved u"..ajiyar zucia ta sauke tana goge hawayen idonta tace"thank you"...kallonta kawai Bobby keyi yanajin wani irin daci a bakinshi sbd 6acin rai..yanxu tsanar da tayi mishi har yakai tasa mishi kuka sbd yace yana sonta?..anya kuwa zai samu soyayyar yarinyar nan?..anya kuwa zai iya jure wnn matsalolin?..ganin ya tafi wani dunian daban ta mike tsaye tana dubanshi tace"sir ni zan tafi"..dagowa yayi ya kalleta from head to toe before saying"ina hijab dinki?.."kallonshi tayi tace"wane hijab?.."rai a dan 6ace yace"ba nace ki dinga sa hijab idan zakizo makaranta ba?..wato mantawa kikayi koh..?"da sauri tace"nazo dashi fa yana class"..nuna mata inda ta tashi yayi yace"to zauna bamu gama mgn ba"..ba musu ta koma ta zauna tana wani ta6e baki tace"amma dan Allah kayi sauri ana jirana ne"...kallonta kawai yake dan baisan amsan da zai bata ba..wai shi yarinyar nana take gayawa mgn haka...idan ba ruwa daya daki babban zakara ba ita ta isa ta zauna gabanshi tana fada mashi mgn haka bai gaura mata mari ba..amma yanxun wai shine nan zaune tana zuba mishi iskanci iri iri kuma bai iya ta6uka komai ba sbd soyayya..amma soyayya baima Dr Bobby adalci ba wlh...saida ya bari ta gama ta6e ta6en bakinta snn yace"kinaji?.."tace"ehh.."yace"dan Allah inaso daga yanxu duk nayi maki laifi ki fadamin ba kije kiyita fushi kinakin daukan wayana ba..banajin dadi..snn kullum kika shigo school ki dinga zuwa office ina ganinki kinji?.."kallonshi tayi kaman zatasa kuka tace"sir kullum kuma?..ai ba kullum kake shigowa ba..kumani banaso inzo kayita min fada fa"da sauri yace"ina shigowa kullum mana..every morning zan shigo idan muka gama gaisawa sai in wuce hospital...kawai nidai ki dinga picking calls dina and ki dinga zuwa ina ganinki?..fada kuma indai ba ganinki nayi da wani ba ba abunda zaisa na miki..duk abunda kikaga na maki rashin jinki ne ke janyowa"mamaki sosai ya bata jin abunda yake fada...ba tareda ta kawo komai a ranta ba tace”zanzo..kuma ni ai bana kula kowa..besty ma da ya taf..."bata karasa ba yace"enough..zaki fara kou?.."da sauri ta dora hannu kan bakinta tace"yi hakuri toh..na dena"..kofa ya nuna mata yace"jeki"..da sauri ta mike ta fita shi kuma ya lumshe ido tareda jingina da kujera...shidai zaiga ranara da za’ayi mgn na minti goma da ita ba tareda tayi mentioning wnn bestyn ba...duk yanda yakai da son ganinta da kuma son kasancewa da ita gara ta tafi akan dai ta zauna tana mishi hiran wani wai besty..shi tunda yake bai ta6ajin ya tsani wani kaman yanda ya tsaneta da bestyn nan ba...ya samu ganinta kuma yayi mgn da ita maimakon ya samu farin ciki sai yajishi akasin haka..sam abunda yakeji is not close to farin ciki...wai shi soyayya dai haka yake cikeda rudu da matsaloli dama?..meya jefa kanshi a ciki ne?..innalillahi wainna ilaihi rajiun..yaketa maimaitawa a cikin ranshi...Nur na ganin fitarta daga office din ya dawo ciki yana kallon Bobby yace"Man how far?..ka samu ka shawo kanta?.."ba tareda ya bude idanunshi ba yace"for where?..yarinyar nan tanada rigima wlh..maimakon in samu sauki fa karamin tayi akan damuwan da nake ciki"...zaunawa Nur yayi kusa dashi yana murmushi yace"ai dama da ganin Lamido nasan mijinta sai yaci ubanshi wlh..at times sai inyita tunanin da wnn shagwa6an nata ya takeyi da boyfriend dinta ne kam?..i never tought it’ll turn out to be you sai yanxun"...kallonshi kawai Bobby daya bude idanunshi yakeyi..yasan abunda yake fada gaskia ne..shi kanshi ko a da din ya kanyi tunanin ya mijinda ya aure ta zaiyi coping da wnn halayyan nata sai gashi ya tsinci kanshi cikin tafkin sonta tsundum kuma baya fatan fitowa har abada...fatanshi ya samu ya shawo kanta idan tayi accepting love dinshi to duk abunda zai biyo baya mai sauki ne.
Ita kuwa tana fita ta kama hanyan class dinsu tana fadin"kam lallaima mutumin nan wani wai yana sona?..to ni ko rasa miji nayi me zanyi da inyamuri Allah na tuba...Allah ya kiyaye na auri dan yaro ma kamanshi wlh..aini matar manya ce ba matar irinsu kananun yara ba..dan rainin wayo kawai".
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
32
Da misalin 9 na dare yana zaune dinning yasa abincinshi a gaba amma ko loma daya ya kasa kaiwa bakinshi...goshi ya dafe da both hannayenshi yanatunanin abubuwanda suka faru...kawai gani yake dalilin kauracewa yan uwan daddy da yayi Allah yakeson ya hukuntashi da ita...shi gani yake wnn abun da yakeji gameda ita yayi yawa...tunda yayi mgn da ita zuwa yanxu bai samu peace of mind ba sbd yanda tayi reacting da yace yana sonta..kawai tasa mishi kuka sbd da gaske ta tsaneshi ne ko kuwa sbd tsabagen ta6ara da yake dawainiya da ita...yayi zurfi cikin tunani har baisan sanda Mummy tazo ta zauna kusadashi ba sai hannunta da yaji ta dafa shoulder dinshi..da sauri ya dawo hayyacinshi tareda daukan spoon dake nan cikin abincin nashi da sauri ya shiga cin abincin kamar mayunwaci..bayason ta gane halinda yake ciki baisan kuma ta riga ta gano ba...batace mishi komai ba sai kallon yanda yake tunkuda abincin take tana jira ya gama suyi mgn dan yau ko yaki ko yaso saiya sanar da ita damuwarshi...tausayi yake bata yanda yake kokarin 6oye suffering dinshi bayan bayyanawa kadai ne maslaha...bata katse mishi cin abinci ba saida ya gama ya kora da drink snn ta kira sunanshi...kasa amsawa yayi sai juyawa da yayi yana kallonta...kallonshi takeyi itama sosai tace"Bobby wai meye matsalarka?..why kake kokarin 6oye abunda ba kai ka dorama kanka ba kuma 6oyewan bazai haifar maka da komai ba..kanaso ciwon zucia ya kamaka sbd wnn damuwan daka dorama kanka ne?..baka tunanin halinda ni da ‘yan uwanka zamu shiga idan wani abu ya faru dakai?..duk bakayi wnn tunanin ba kake kokarin cutar da kanka koh?.."shiru kawai yayi yana kallonta yasan duk mgnr data fada gaskia ne..da gaske abunda yakeji bashi ya dorama kanshi ba..kuma kokarin 6oye hakan ba abunda zai haifar mashi sai dana sani amma ya zaiyi?..soyayya ne Allah ya jarabceshi dashi na yarinyar nan kwata kwata bai ganin zata soshi..shi kuma so yake ya yakiceta daga zuciyarshi amma zuciyar taki bashi hadin kai dama tun ba yanxu ba yasan zuciyarshi tafi shi kanshi taurin kai sbd yanda yayita kokarin dakatar da abun tun yana dan karami abun bai yiwu ba har yanxu aka kawo wnn matakin...yasan yanxu tana gama makaranta kilan a hadata da wani ta aura ko kuma ta fitoda wanda takeso tunda tasha fada mishi ita tanada wanda zata aura...tunanin hakan yasa yaji wani irin nauyi a cikin zuciyarshi...idonshi suka kada sukayi jaa har wani shinning suke sbd dan kwalla daya cikosu...da sauri ya kifa kanshi jikin Mummy ya sauke wani ajiyar zuciya irin na wanda yaci kuka ya koshi...numfashinshi ma da kyar yake shaqa sbd kokarin 6oye hawayenshi da yake...baison Mummy ta gani shiyasa yayi haka amma yasan da kyar ma idan bata gani ba...saida ya dauki almost 3 minutes a haka kafin ya dago daga jikin nata yana sauke kanshi kasa...wnn raunin da yake zuwa mishi duk yayi mgn da itane bayaso shiyasa bai cika son yin mgnr da itaba..da akwai wani irin rauni da karyewar zuciya dake zuwa ma mutum duk yake gaban mahaifiyarshi idan ya tsinci kanshi cikin wani yanayi mara dadi...baisan ko kowa haka yakeji ba amma shidai haka yake tun yana dan karaminshi...hannu Mummy takai ta dago fuskanshi tana kallon idanunshi da har yanxun suke shinning sbd hawaye da suka kuma taruwa a ciki tace"let them out son..zakaji sauki"..da sauri ya sauke kanshi yana sake kokarin mayar dasu amma wnn karon sai yaji kamar turosu akeyi da gayya dan haka ya sake maida kanshi jikinta da sauri daidai lokacin kuma hawayen suka silalo kan fuskanshi...bayanshi Mummy ta shiga shafawa a hankali itama nata muryan a raunane tace"cry as much as u want zaka samu sauki"..shidai bai iya cewa komai ba sai hawaye da har yanxu basu dena zubowa fuskanshi ba...mamaki da haushin kanshi suka dirar mishi lokaci guda...shi kanshi he can’t remember when last ya zubar da hawaye da idonshi amma wai yanxu shine ke kuka sbd karamar yarinya..wnn wace irin jarabawa ce?..some months back idan kace mishi zai kamu da soyayya kuma har yayi kuka sbd wata mace kallon you are not normal zaiyi maka amma yanxun gashi dumu dumu cikin soyayya snn kuma gashi yanata kwararar da hawaye abunda zai iya cewa rabonshi dayi tun bayan rasuwar mahaifinshi...Allah ma yasoshi ba kowa a wurin da kunya zaiji wlh...Mummy ce tasa hannu ta dagoshi tana goge mishi hawayen da yayi saura fuskanshi kafin tace"fadamin..what exactly happened?.."hannunta ya kama duka biyun yana dubanta cikin voice dinshi daya fara disashewa yace"she doesn’t love me Mummy..she despise me..da bakinta tacemin tanada wanda zata au.."kasa karasawa yayi sbd wani abu dayazo ya tokare mishi wuya..sake dora kanshi yayi shoulder dinta yana jujjuaya kan nashi from side to side yace"mutuwa zanyi Mummy...wlh duk ranan da ta auri wani i won’t survive zuciyata bugawa zatayi in mutu Mummy ki taimakamin please!.."rungumeshi Mummy tayi itama nan take hawaye suka ciko idanunta tace"u won’t die inshaAllah..Bi’iznillah batada mijin aure sai kai sbd haka ka kwantar da hankalinka"...girgiza kai yacigaba dayi yace"Mummy wlh i can’t..dan bakisan yanda mukayi da ita bane..she even cried da nace ina sonta kuma nasan halinta Mummy da gaske bata kaunata shiyasa takemin haka...bansan meyasa Allah zai..."bai karasa ba Mummy tayi saurin rufe mishi baki tana cewa"karkayi sa6o Bobby..kayi hakuri mubi komai a sannu inshaAllah komai zai wuce..komai zai zama tarihi"...wani numfashi ya sauke mai karfi tareda fadin"Allahumma Ameen Mummy..Allah sa ya zama history kaman yanda kikace"..tace"Ameen InshaAllah..yanxu tunda ka gama cin abincin ka samu kaje ka kwanta naji jikinka da zafi anya ma zaka iya bacci a haka kuwa?..kodai muje asibiti?.."girgiza mata kanshi yayi kafin a hankali yace"don’t bother haka yakeyi dama"..da mamaki tace"u mean haka kake kwana da fever kullum kuma bakayi kokarin kayi wani abu ba?.."dagowa yayi ya kamo hannunta yace"Mummy ai bai dade da farawa ba..for the past few weeks ne kawai and inashan magani"..girgiza kai Mummy keyi tace"ban yadda ba..nasan ba maganinda kakesha"..yace"da gaske inasha Mummy..kinsan bazanyi wasa da lafiyana ba"...tace"ya kamata dai kar kayi wasa dashi din idan kuma baso kake Lamido tace batason mai yawan rashin lafia ba"..da murmushi ta karasa mgnr aikam shima saiga wani hadadden murmushi kwance akan fuskanshi...Lamido kawai da aka kira yaji kaman anyi mishi gagarumin kyauta wnn baisan yanda zaiji duk akace ta zama matarshi ba...ganin yanda Mummy ta tsareshi da ido sai ya mike yayi mata sallama ya kama hanyar Flat dinshi...da kallo Mummy ta bishi tausayinshi na sake kamata..ta tabbata authentic so yakema yarinyar nan har tunda taga yayi abunda ita kanta ta manta yaushe rabonda yayi shine hawaye...addu’anta bai wuce Allah ya karkato da hankalin yarinyar kanshi ba snn yasa ayi komai da komai cikin sauki da kwanciyar hankali.
Shiko Bobby yana shiga Flat dinshi kulle kofanshi yayi ya wuce direct zuwa bedroom dinshi...bayan yayi wanka yasa pyjamas dinshi snn ya kwanta ya dora wayanshi kan kirji wani sashe na zuciyarshi sai azalzalanshi yake ya kirata ko muryanta yaji yasan zai danji sauki yayinda daya sashen kuma yake cewa idan har ya kirata bayan duk wulakancin da tayi mishi daxu to ya tabbata a kirashi da mara zuciya...shiru yayi gamida runtse ido yanajin shawarwarin da ko wane sashe na zuciyar ke bashi...shi kanshi yayi na’am da kin kiran nata dan haka ya sake kulle ido ya lullu6e da duvet shi a lallai bacci yakeso ya daukeshi sbd kwata kwata bayason yawan tunanin nan da yake amma kememe bacci yace baiga daman daukanshi ba..haka ya karaci juyi yana rungume pillow daga karshe dai dole kasa daurewa yayi saida ya danna mata kira...har ya gama ringing bata dauka ba dan haka ya sake kira..yana gab da katsewa ta daga cikin magagin bacci tace"baby ka bari in tashi daga bacci sai muyi waya kaji?.."wani irin abu yaji yazo ya tokareshi a wuya har numfashinshi na barazanar daukewa...bai iya ce mata komai ba ya kashe wayarshi gaba daya...ita kuma jin baice komai ba ta dago wayan tana kallon screen sai taga proprietor a jiki nan take baccin dake idonta ya wartsake ta wani zare ido tareda fadin"na shiga uku"...sam bata duba wanda ya kira ba tayi zaton shine tunda daxun yace mata idan ya isa gida zai kirata..hankalinta taji ya tashi tasan yanxu da kyar idan basuyi rigima dashi ba..sake kiran wayanshi tayi amma har ya gama ringing bai dauka ba..data sake kira kuma sai taji wayan gaba dayanta ma swicth off...haka nan ta hakura ta kwanta tana tunanin yanda zasu kwashe dashi gobe...shi kuma Bobby tsabar 6acin rai ne ya hanashi mgn...sbd wulakanci shine zai kirata ta wani kirashi da sunan saurayinta sbd bata da hankali..haushin kanshi ka yaji ya kamashi ga zafi da zuciyarshi ke mishi..shidai ya hakura da yarinyar nan kawai inyaso idanma mutuwa zaiyi sbd ya mutu amma bi’iznillah bazai sake nuna yanada wani feeling gameda itaba tunda ita batasan mutuncin hakan ba...wnn daren ma kamar sauran saida dare ya tsala sosai snn ya samu bacci.
Washegari Thursday ranan shiga college dinshi ne amma yana sane yace bazaije ba sbd bama yaso ya ganta ballantana ya karya alkawarin daya daukan ma kanshi...ko a gida bai zauna ba ya shirya ya tafi hospital sbd yasan idan Mummy ta ganshi a gida zata tashi hankalinta ne and shima kanshi yana bukatar ya fita ko dan wani wurin ne yaje at least zai shaki fresh air.
Lamido na shigowa makaranta ta nufi office dinshi kaman yanda yace kullum taje ta gaidashi da safe and ita kanta tanada bukatar yin mgn dashi akn abunda ya faru jiya..ga mamakinta bata sameshi office dinba haka ta koma class tana sake trying numbershi yana shiga amma bai dauka ba...suna fitowa break ta sake komawa office din nashi still baya nan kuma tanata kiran wayanshi har ta gaji bai dauka ba...hankalinta ya tashi sosai tasan yanxu kilan yace zai hadata da daddy...tasan dan abu karami ke 6ata mishi rai amma ita ai bada niyua tayi ba...ranar har suka bar school bata ganshi ba kuma bai dauki wayanta ba...hankalinta ya tashi fiyeda yanda take zato duk sai taji wani iri dan tunda suke bai ta6ayi mata haka ba...a ‘yan kwanakin nan da yake mata mutunchi ta fara fahimtan waye shi...sure tasan yanada fada amma kuma yanada kirki and yasan darajan mace...gaba daua jinta take wani iri addu’anta bai wuce Allah yasa kada ya hada da daddy ba.
Washegari friday same thing happens shima har suka tashi Lamido na nemanshi bata ganshi ba wayanshi kuma tun yana kin dauka har ya fara rejecting call din...hankalinta yayi mugun tashi har hakan yaso bata mamaki dan bata taba tunanin zata damu haka ba...da dadewa tasan ta saba dashi amma batasan sabon yakai hakaba sai yanxu...koda yake bataso ya hadata da daddy ne shiyasa hankalinta yaki kwanciya...a takaice saida ta kwashi three days tana nemanshi bata samu ganinshi ba...ranan Sunday tana zaune dakinsu itca kadai saida ta bari Billy ta fita snn ta kira Nur a waya sbd tasan idan sukayi mgn a gabanta zatacigaba da cewa soyayya ne tsakaninta dashi ita kuma bata son haka..yana dauka tace"sir dama ina neman proprietor ne"..Nur yace"baki sameshi a waya ba?.."a hankali tace"baya dauka"..da mamaki Nur yace"ban gane baya dauka ba?.."tace"sir inata kira bai dauka..rejecting call dinma yakeyi"..Nur ya danyi shiru for some minutes before yayi adding"kinyi mishi laifi knn?.."a hankali tace"sir kawaifa kirana yayi bansan shi bane na zata baby ne shknn fa yaketa fushi dani har yanxu..kuma sir ni ina tsoron kar ya hadani da daddyna"..shiru Nur yayi yana saurarnta yana murmushi...addu’a yake Allah yasa itama ta damu dashi koda baikai rabin damuwar da yayi da itaba..saida ya gama smiling dinshi before yace"bani two minustes inyi mgn dashi"..a hankali tace"toh"snn ta kashe wayar...suna gama mgn Nur ya dannawa Bobby kira..ringing biyu ana uku ya daga da sallama...Nur yace"maza ina ka shigane kwana biyu?.."Bobby yace"wlh banjin dadi ne shiyasa kajini shiru..ya aiki".."Alhamdulillah kana gida ne?.."Nur ya tambayeshi kai tsaye shi kuma ya amsa da fadin"no ina hospital"...da sauri yace"ohk gani nan zuwa asibitin yanxu..bakada lafia ne naji muryanka somehow?.."ajiyar zuciya Bobby ya saki before saying"sai kazo din dai kawai"..Nur ya amsa da"ohk"..daga haka kowa ya ajiye waya..sake kiran Lamido Nur yayi tana dauka yace"munyi mgn dashi yace yana hospital yanxu haka..ko zaki shirya in kaiki?.."shiru tayi tana nazari for a while sai kuma a hankali tace"toh.."yace"ki shirya yanxu gani nan zuwa"..ta sake amsawa da"toh.."snn ta kashe wayar..mikewa tayi ta dora dogon hijab akan jessy da straight skirt dake jikinta..tazo fita daga dakin saiga Billy ta shigo ciki..kallonta takeyi from sama zuwa kasa tana ta6e baki tace"ina kuma aka nufa hakia indo?..fushin ya kare knn?.."wani irin harara Aysha ta watsa mata snn ta bangajeta ta fice daga dakin Billy ta bita da kallo baki bude tana cewa"anya kuwa Lamido batada aljanu?.."
A hankali take tafiya har ta iso first gate na hostel din dan haka Nur na karasowa bai karasa ciki ba yayi picking dinta a nan suka wuce...suna hanya da yaga yanda tayi shiru ta zubama spot daya ido yace"duk Dr Bobby ya sanyaki a damuwa koh?.."da sauri ta daga kai tana cewa"eh mana..kumafa ni banga abun jin haushi a mgnr dana fada ba"..murmushi Nur yayi yana girgiza kai cikin ranshi yace"ai bazaki ganiba dama"..daga haka ba wanda ya sake mgn cikinsu har suka iso Freedom...yana gama parking duk suka bude mota suka fita zuwa cikin asibitin...saida sukazo daidai office dinshi taji wani irin faduwar gaba ya risketa..ko wane kalan masifa zai sauke mata oho?...Nur ne ya fara tura kofar ya shiga kafin itama tabi bayanshi...Bobby dake kwance kan sofa ya bude idanu a hankali ya saukesu kan Nur then back to Lamido dake tsaye bayanshi sai faman sunkuyar dakai take...da sauri ya mike zaune yana kallonta da kyau duk idanun nan a waje kaman yaga abun tsoro..yakai hannu yana murza idanuwan nashi wai ya tabbatar ba mafarki yake ba ba kuma gizo take mishi kmr yanda ta saba ba..ganin da gaske itam ce nan tsaye a gabanshi baisan sanda ya wani daure fuska yana kallonta ba...a hankali tayi kasa da idonta tanajin yanda tsatstareta da wnn idanun...kafin tayi mgn ya nuna mata kofa yace"out of my office"..da sauri ta dago tana kallonshi wnn karon shi ya kawar da nashi idon kafin ya sake fadin"i said ki fitarmin daga office"...kafin tayi mgn Nur yace"Haba Bobby"..k kallonshi baiyi ba ya sake nuna mata kofa ita kuma tayi tsaye taki tafia kawai sai ya dafe head dinshi da hannu bibbiyu yana sauke numfashi...ganin haka Nur ya dan matsa kusada ita murya can kasa yace"karki yadda kibar office din nan ba tareda kun daidaita dashi ba..idan yacigaba dayi maki masifa kawai kuka zakisa shknn kinyi maganinshi"..yana gama fadan haka ya juya ya bar office din..jin karar kofa ya sashi bude ido sbd yana tunanin itace ta fita amma sai yaga Nur ne...sake dawo da kallonshi yayi gareta murya can kasa yace"ba cewa nayi kibar min office ba?.."da sauri tace"sir dan Allah kayi hakuri"..girgiza mata kanshi yayi yace"kimin laifi ne kike bani hakuri?.."kwabe fuska tayi zatasa kuka tace"nifa bansan kaine ba Allah"..kallonta kawai yake ganin zata fara mishi kuka bayan ba abunda yayi mata..shi baisan dalilinda yasa ma Nur ya daukota ya kawo mashi ita har nan ba..ajiyar zuciya ya sauke gamida dauke kanshi daga gareta ya sake komawa ya kwanta kan sofa...ita kuma ganin yanda yaba banza ajiyarta sai ta daddage ta rushe da kuka kmr yanda Nur yace tayi..da dadewa tasan bayason kuka tasan kuma shine kadai abunda zatayi ya saurareta...sake runtse ido yayi jin yanda take mishi kuka ya dauki throw pillow ya danne face dinshi dashi wai ko zai denajin kukan nata amma a banza..da dane ya tabbata ko zata shekara tana kuka a gabanshi bazai dameshi ba amma yanxu wani irin rauni kukan nata ke haifar mashi..sai yaga kaman yayi mata wani abun alhalin kuma ba uwar da yayi mata..har cikin zuciyarshi yakejin kukan..kasa daurewa yayi ya mike zaune yana kallonta da idonshi da sukayi red yace mata"wani abun nayi maki da zaki sani a gaba kina kuka?.."cikin kuka tace"sir kaine fa kaki hakura"..yace"cewa nayi ban hakura ba?..ni bakiyimin laifin komai ba kawai kije I don’t want to see u"..haushi sosai mgnrshi ya bata dan haka ta juya a fusace zata bar office din garin sauri ta take hijab dinta dake jan kasa aikuwa ta tafi luu saura kiris ta fadi Bobby yayi hanzarin mikewa ya tareta a jikinshi...ta runste ido tana sauke numfashi dan yanda ta gama tsorata ta gama sadakarwa zata jita a kasa sai kuma taji ba haka ba...shi kam kallonta kawai yakeyi kaman an aikoshi...the more ya kalleta the more yake sake ganin asalin beauty dinta wanda da bai cika gani ba sam...zuciyarshi yaji tayi wani tattarewa ta dunkule waje daya sai wani irin harbawa take da mugun karfi...ya lumshe ido ya bude still yana kallon yanda har yanxu ta kasa bude idanunta baisan ya akayi ba kawai shidai yaji ya hadata da jikinshi..rungumeta yayi da kyau yana sauke numfashi a jere kaman wanda yayi race tareda lumshe ido yanajin wani irin mixed feeling tattare dashi...Lamido kuwa mutuwar tsaye tayi jin yanda ya cacimeta sbd tsabar tsorata kasa ko motsi tayi balle tayi kokarin kwatan kanta..Bobby kuwa is far gone sam bai ankara da abunda ya aikata ba saida yaji ta fara mutsu mutsu a jikinshi..sakinta yayi da sauri yakai hannu ya dafe head dinshi tareda fadawa kan sofa...sai sauke ajiyar zuciya yake kmr wanda yayi tsere..he just can’t believe what happened..he can’t believe he hugged her after all alqawuran daya daukan ma kanshi...runtse ido yayi yana salati dama abunda yske gudu knn shiyasa tun farko yace ta tafi amma taki tafiya...yasan idan yacigaba da ganinta abubuwanda yake 6oyewa suna iya kokarin tona mashi asiri and now see what happened..ya kasa controlling kanshi har yayi hugging nata wanda yakeda tabbacin mutuncinshi ja iya zubewa a idonta...Aysha kuwa shiru tayi ta kurawa spot daya ido kawai tana mamakin abunda yayi mata...gani take kodai aljanu sun shafeshi ko kuma yana fama da serious rashin lafia tunda ga alama nan ta gani yanda yake dafe da kanshi..kuma tasan yana cikin hankalinshi bazai aikata abunda ya aikata ba for she trust him..tasan yanda suke rigima dashi ko wani ya gani tareda ita so ta tabbata bazaiyi hugging dinta for his selfish interest ba..kilan yayi haka ne don ya taimaketa ko kuma sbd wani abu dake dawainiya sam bata kawo wai da gaske sonta yake ba...ganin har yanxu bai motsa ba ta karasa a hankali ta zauna kan one of kujerun office din tana dubanshi murya a hankali tace"sir ai ka hakura koh?.."a hankali ya bude ido yana kallonta..ta wani sake langabewa tace"nace fa bansan kaine ba"..gyada kai kawai yayi kafin ya safe maida eyes dinshi ya rufe..tace"kuma bazaka fadama daddy ba?.."nan ma kan ya daga mata without saying anything..shiru sukayi a office din shi yanajin kaman ya fallasa mata asirin zuciyarshi ita kuma tana tunanin wane irin ciwo ke damunshi da duk yabi ya canxashi haka?..mikewa tayi tana murmushi tace"sir zan tafi"...kai kawai ya sake daga mata ta juya ta fita shi kuma ya sake dafe kanshi yana cije lips dinshi...baisan garin ya yayi loosing control dinshi ba wlh..Allah dai yasa yarinyar nan batayi masa muguwar fahimta ba.
0 comments:
Post a Comment